HEEDAYA CHAPTER 27 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 27 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zainab ta mike jin ana knocking din kofarsu ta bude, ganin Shuraim tsaye bakin kofar tace “Ina yini Ya Shuraim” 

Aisha da Nafisa duk suka kame kansu a dakin kuma bbu wanda ya kallesa cikinsu, cikin few seconds ya gama bin 

dakin da kallo snn ya amsa gaisuwar Zainab yace “Lafiya” Heedayah dai na kwance saman gado tayi backing din 

kofar gabanta sai faduwa yake, karasawa cikin dakin yyi cike da kasaita ya nufeta yace “Bani jakar ki” kamar jira 

take ta mike xaune da sauri ta dau jakar ta mika masa, ya amsa ya bude ciki, bbu komai sai kudi da awarwaro with 

different chocolate, tunda ta mika masa jakar bata yrda ta kallesa ba, xuciyarta kamar xai fito don tsoro, ya jefar da 

jakar saman gado ya juya ya fita, Zainab ta xauna gefen Heedayah tace “What is he looking for?” Heedayah tayi 

tagumi tace “Ohon masa” Zainab ta tabe baki bata ce komai ba ta fita dakin. Har karfe dayan dare Heedayah bata yi 

bacci ba, amma bbu wanda xai ce ba bacci take ba, ita da Farida da Zainab sai Aisha ne a dakin, Mumy ta kwashi su 

Rabi’ah sun wuce gida tun karfe goma saura wai baxa su kwana gidan ba, a kashe wutan dakin yake almost an hour 

ynxu, kowa na dakin taji alamar yyi bacci, Heedayah ta sauka saman gadon a hankali ta nufi kofa ta bude very 

careful not to make any sound that will wake anyone sannan ta fita, bbu kowa parlon ta karasa tsakar gida taga har 

sannan murhu na ta ci ga manyan tukwane ana dafa kayan miya, sai da ta tsaya tayi naxarin inda xata bi snn ta xaga 

ta nemo dai dai windown bandakin su Zainab a bayan gidan, wayar na nan inda ta jefar amma screen din yyi raga 

raga ba na wasa ba, shi kansa wayar ya gurgurje, a hankali ta duka kamar xata yi kuka ta dau wayar tana jujjuyawa, 

har ranta taji ta tsani Shuraim din nan, meye xai wani sa mata ido, Ina ruwansa da ita wai ma, dudduba wayar tayi 

taga yana yi, ta turo baki ta xagayo gaban gidan ta shiga ciki ta koma can dakin da suke, a hankali ta bude press din 

su Zainab ta durkusa ta saka wayar a can kasan kaya sannan ta hau gado ta kwanta. Washegari juma’ah xa ayi dinner, 

Da rana duk ‘yan matan suka shirya cikin daya daga ankon bikin, ana ta shagali a gidan, abinci iri iri aka girka ranan 

sae kace ranan ne yinin bikin, Duk Heedayah ta xo wucewa sai Mumy ta bi ta da kallo kmr idanuwanta xa su yi 

magana, duk inda ta bi idonta na kanta haka ma kawarta Sadiya, nan ko ita ta kagu a kare biki ta san na yi, ko kiris 

bata kaunar duk abinda xae sa Heedayah farin ciki, barin gashi ta ganta fes fes alamar hankalinta a kwance yake, ba 

komai ya kara tsaya mata a rai ba sai irin kyan da Heedayah ke da shi, wnn idan ta jera da su Rabi’ah sae a dauketa 

sau goma ba a daukesu sau daya ba, Mumy ta sauke ajiyar xuciya tana ci gaba da rabon abincin da take. Heedayah ta 

shiga daki dauko mayafinta xa su je dauko bak’i a bakin titi ita da Aisha kamar yanda Hajiya Hauwa ta umarcesu, 

Zainab ce kadai dakin duk kowa ya fita har ynxu tana make up, Zainab ta juya ganin Heedayah tace “Ke kika ajiye 

waya kasan kaya, yana ta vibrating??” Heedayah ta xaro ido a tsorace ta nufeta ta duka kusa da ita tace “Da gaske? 

How did you hear it?” Zainab tace “Kawai Ina son daukan takalmina kasan press din yanxun nan na ji vibration din 

sai na duba naga waya, and nasan Farida na tare da wayarta ynxun nn ta fita” Heedayah ta fara kalle kallen dakin, a 

hankali tace “Ke da wa ku ka ji vibration din plss?” Zainab tace “Just me, yanxu ma fa aka kira” Heedayah ta 

marairaice tace “Toh don Allah don’t tell anybody about this Zainab, not even Farida” Zainab ta gyada mata kai tace 

“I am giving you my words” Fiddo wayar Heedayah tayi tana dubawa, Zainab tace “But saurayin ki ne ya baki waya 

kike boyewa” Heedayah ta girgixa kai tace “Ba saurayina bane” Zainab tayi murmushi tace “Toh sai ki kira” 

Heedayah xata yi magana wayar ya fara vibrate kuma… Kallon Zainab tayi da sauri, Zainab tayi tagumi tana 

murmushi tace “Pick…” Tana fadin haka ta tashi ta kulle kofar dakin ta sa makulli, Heedayah ta daga kiran ta kai 

kunne, she could hear him suspire but still bai ce komai ba, a hnkli tace “Hello…” Cikin cool voice dinsa yace “Who 

was he Heedayah?” Heedayah tace “Yayanmu ne” Yace “Really?” Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace 

“Hope he didn’t suspect you” a hankali tace “He did” yace “And how did it went?” Tace “Ni ba mu hadu da shi ba 

har ynxu” yace “Yaushe xa ki bar gidan??” tace “Kilan anjima da daddare” yace “Wa xai maida ki?” Tace “Daga wajen dinner xamu wuce gida” yace “Ke da wa?” Tace “Farida” ya d’an yi shiru snn yace “Ohk, where is the venue 

for the dinner?” Tace “Ban sani ba sai na tambaya” Yace “Do ask plss, Kar ki katse kiran kawai ki ajiye idan kin 

tambaya ki dawo” ta kalli Zainab da ke ta kallonta don tana jin komai da suke cewa, Heedayah ta cire wayar a kunne 

tace “Ina ne venue din dinner din?” Zainab ta gaya mata, Heedayah ta maida wayar kunne ta gaya masa, yace “Who 

did u ask?” Tace “My sis” yace “Ur sis??? Kuna tare ne?” Tace “Yess” yyi kasa da murya yace “Why?? You 

shouldn’t have…” Sai kuma yyi shiru, can yace “Will call back later keep the phone close to you” daga hka ya katse 

kiran, Heedayah ta kalli screen din sannan ta kalli Zainab, Zainab tace “Waye shi? And why is he bothered because 

you are talking in front of me” Heedayah ta kirkiri murmushi tace “Sbda ya ga ina tsoro…” Zainab tayi shiru, sae 

kuma ta kalli Heedayah tace “But he shouldn’t be bothered, idan yana son ki ya xo gidanku mana, why is he making 

it confidential??” da sauri Heedayah tace “Noo he isn’t, and wllh ba saurayina bane, beside Mami will punish me if 

she gets to find out, kawai dai….” Zainab tace “Uhn kawai dai me?” A hankali Heedayah tace “Ba saurayina bane 

wllh” Farida ta d’an yi murmushi bata ce komai ba, kamo hannunta Heedayah tayi tace “But promise me that you are 

saying nothing to anybody Zainab” Zainab tace “Trust me” Heedayah ta jira har Zainab ta gama kwalliyar sannan 

suka fita dakin. Da yamma ana ta shirye shiryen tafi wajen dinner da xa a fara bayan Magrib, Su Heedayah suka sa 

ankon lace dinsu tare da su Zainab duk suka yi kyau sosai, Su Rabi’ah dama wanda ya fi wnn tsada Mumy ta siya 

masu ga jaka da takalmi duk sababbi, Har sannan Farida ta ki yrda ta shiga harkan Heedayah a gidan, hakan ya d’an 

fara damun Heedayah don basu ta6a haka ba tunda suke amma dae bata ce mata komai ba, kuma bata da intention 

din ce mata dama. Ana ta kwalliyan tafiya dinner wajajen karfe shidda, mai make up aka kawo gidan tayi ma yan 

matan make up, Heedayah dai tace baxata yi ba, ana gamawa Zainab kwalliya aka hau yi ma Aisha, Heedayah ta bi 

Zainab gun madubi a hankali tace “I want to talk to you Zainab” Zainab tace “Ohk” Fita Heedayah tayi Farida ta bi 

ta da kallo, Zainab ta bi bayan Heedayah, Heedayah ta kamo hannunta a hankali tace “Plss can I get spare gate 

pass?” Zainab tace “For who?” Shiru Heedayah tayi tana kallonta, Zainab ta d’an yi murmushi tace “Ohk I get, but 

aiki ne babba fa, kinsan gate pass din ba shi da yawa, but let me try….” Daga haka ta wuce dakin da amaren suke ana 

shirya su cikin hadaddun kayan dinner dinsu, cikin dubara Zainab ta jawo jakar Aunty Safiyya dake gefenta ta bude,

gate pass biyu ya rage da xata ba wasu schl frnds dinta, Zainab ta xare daya ta mayar mata da jakar ta fita da sauri, ta 

mika ma Heedayah dake tsaye tana jiranta tace “It was easy but not funny” Heedayah tayi murmushinta me kyau 

tace “Thanks Zainab” daga haka ta sa gate pass din a jakarta, tana jin wayarta ya fara vibrate ta fita parlor da sauri ta 

xaga ta dauka kafin ya katse, sallama yyi mata tace “How will you collect it?” Yace “Ohk kin samu?” Tace “Ehh” 

yace “We will meet there, but ki ajiye wayar kusa dake plss” tace “Toh, ana jirana” daga haka ta katse wayar ta 

mayar cikin jaka, har ta fara tafiya ta ji ance “Heedayah” gabanta ya wani irin faduwa ta juya da sauri ganin ba kowa 

sai ta kalli sama, Sudais ta gani bakin windon dakinsa tsaye yana kallonta, Kasa cewa komai tayi xuciyarta sai 

bugawa yake ta marairaice xata yi kuka, da sauri xata bar wajen yace “Jiran ni a nan, kar ki je ko ina” bata iya ta ce 

komai ba ta tsaya hawaye na sakko mata, bayan kusan minti uku sai ga shi, har ya iso inda take bata yadda ta kallesa 

ba xuciyarta sai bugawa yake, yana facing dinta ce “Ke da wa kike waya?” Kamar jira take ta fashe masa da kuka ta 

ki cewa komai, ya hade rai yace “Ni ban ce ki min kuka ba answer my question now” Cikin rawar murya tace “A 

frnd” yace “Frnd?” Where did you know him from” hawaye kawai take ta ki cewa komai, yace “I asked where did 

you know him from” Ta kuma fashe masa da kuka tana kallonsa, yace “Schl??” ta gyada masa kai, yyi shiru yana 

kallonta, can yace “Ur classmate?” Ta girgixa masa kai, yace “Toh waye?” Ta ki cewa komai, strictly yace “Answer 

me now Heedayah” Cikin rawar murya tace “A hanya na san sa” yace “Mami ce ta baki waya?” Murya can kasa tace 

“Shi ya bani” yace “Amma Mami ta sani?” Ta girgixa masa kai, da mamaki yake kallonta, can yace “Farida fa?” Nan 

ma ta girgixa masa kai, ya fi second talatin yana kallonta with surprise, can yace “Bani wayar to” ba musu ta bude 

jakar ta fiddo wayar ta mika masa, yana kallonta yace “Why Heedayah, Don’t you know u are too young for this, 

idan kika gama secondary school babu wanda xai hanaki waya da wani, seriously bana son in sake ganin haka, face 

ur studies, in a year time after ur secondary schl you can speak to anyone… provided Mami ta sani kuma ta amince 

da hakan” cikin sanyin murya tace “To Yaya” Yace “Shi a ina yake?” Ta girgixa masa kai tace “Nima ban sani ba” 

Yyi shiru yana kallonta, can ya kara duba wayar yana kallon hotonsa duk da wayar ta fashe sosai, but he still can see 

him a little, mika mata wayar yyi yace “Bude min” tace “Ban san password din ba” Da mamaki yace “Baki sani ba? 

Haka ya baki wayar?” Ta gyada masa kai, yace “Me yasa bai bude maki ba” tace “Nima ban sani ba” yace “Baki ce 

masa ya bude maki ba?” Tace “Nace masa amma bai bude ba” yace “Toh xai kira kuma xan yi warning dinsa, bbu ke 

bbu shi, idan kuwa kika sake kulasa sai na hada ki da Mami and even Abba” Hawaye ya kawo idonta tana girgixa 

masa kai cikin tashin hankali tace “Don Allah kar ka gaya mata wllh dukana xata yi, don Allah Yaya kayi hkuru” 

yace “Toh naji, but karki sake kulasa anywhere, and hope bai san gidanku ba” Ta d’an kallesa sai kuma da sauri tace 

“Aa bai sani ba” Yace “Good, I will warn him if he should call, I don’t think mutumin kirki ne da baxai ki baki 

password ba, and plss bbu ruwanki da maxa sai kin gama secondary schl Cutie, is that clear?” a hankali tace “Toh 

Yaya” yace “You can go” a hankali ta fara tafiya har ta d’an yi nisa sai kuma ta juyo da sauri tace “Yaya don Allah 

har Yaya Shureen kar ka gaya ma” Murmushi yayi yace “Baxan gaya masa ba” ta marairaice tace “Plsss” yace “I promise” juyawa tayi ta ci gaba da tafiya ta koma cikin gida. kaka ta gama shirinta tsaf ita ma cikin wani lace dake 

ta walkiya ta kima uban dankwali a kai ga katon mayafinta da ta amsa gun Safiyya da dai daya dayar jakarta na gado 

da xa a iya xura jariri a ciki, takalmin kafarta ma me d’an tudu ne, Heedayah na hango kaka duk da tashin hankalin 

da take ciki sai da ta nemi kujera ta xauna ta dinga kyalkyala dariya Zainab da Nafisa na taya ta, kaka ta nufi gun 

Umma dake ba frnds dinta pass tace “Dama kada a kuskura a raba ma tsofaffi fass din nan, kar su je su cika mana 

waje a shiga uku, kuma wani motar xa mu hau da Ta salla? Ta kirani tace kila tana hanya” Umma ta kalleta daga 

sama har kasa snn ta kauda kai tace “To ai motocin ake jira, kowa ma motar yake jira” Kaka tace “Toh a ajiye mana 

daya da Heedayah da Zainab da Farida” tana fadin haka ta koma canxa jaka ganin kowa da sabon jaka yake yawo ita 

kadai ce me tsohon jaka, Sudais ne ya bita dakin bayan Ummarsa taje ta samesa a dakinsa ta lallabasa yaje yyi mata 

magana duk da baya son fitowa sbda mata da suka cika gidan, ganinsa Kaka tace “Kai baxa ka bane Sudess, gashi 

kowa na ta shiryawa, shi dama Shureen bakin hali baxai bari yaje ba, barin yanxu kuma da yake tunanin ya xama 

soja” yace “To me xan je inyi” tace “Oho” yana kallonta daga sama har kasa yace “Duk kwalliyar xaman gida ne 

kika yi hka Hajjaju” Kaka na nemo sabon jakarta a kwallayenta na daki tace “Wani xaman gida, ga can an je kawo 

motoci xa mu dinner, Ta salla ma kila a can xa mu hadu” Sudais yace “Ynxu ke fisabilillahi godai godai idan ance ki 

tafi dinner sai ki tafi?” Ta mike tana kallonsa baki bude…. yana kallonta da kyau yace “Idan ma xaki tube kayan nan 

ki tube ki saka na xaman gida, don bbu wanda xai kai ki wani dinner, Abba da Baffa sunce bbu inda xa ki yanxun 

nan suka kirani, idan kuma basu isa da ke bane sai mu ji, meye kuma dinner tsofe tsofe da ke xa ki ce sai kin je cikin 

jikokin ki” yana fadin hka ya fita dakin ba tare da ya jira cewarta ba, yana fita su Umma da kawayenta na shigowa 

da manyan kuloli dakin. Bayan Magrib duk aka watse gidan xuwa wajen dinner, Ko kadan kaka bata wani tada 

hankali ba ganin duk namomin bikin gobe da kaji su Umma suka kawo dakinta a manyan kuloli har ma da cartoons 

din malt da lemu iri iri, ga ganda da aka soya da naman saniya, sae cewa take kuyi maxa kada ku makara bbu ddi. 

Har suka isa gun dinner Heedayah bata da walwala, bayan sun sauka motar su Farida da Nafisa sun shiga cikin event 

center din Zainab tayi kasa da murya tana kallon Heedayah tace “Kin samu kin basa gate pass din?” Hawaye ya 

kawo idon Heedayah a hankali tace “Ya Sudais ya amshi wayar” Da mamaki Zainab ke kallonta, can tace “Ya aka yi 

ya gani?” Heedayah tace “He caught me at the backyard” Zainab tace “To yanxu ya xa ayi? And baki da number tasa 

ko?” Heedayah ta gyada mata kai a hankali, Zainab tayi shiru don ita ma bata ji dadi ba, can ta d’an yi tsaki tace “Ya 

Sudais din nan na da matsala wllh, duk ya bi ya takura mutum, mu ma fa haka yake mana har duka ya ta6a yi ma 

Nafisa wai sai mun gama waec, amma ga su Rabi’ah su yi ta waya da samari kala kala Ya Shuraim baya ce masu 

komai wllh, a gabansa ma suna iya daukan phone call he won’t even look at them” Dallaro su aka yi da fitilar mota 

lkci daya kuma aka kashe, duk suka kalli motar dake parke daga opposite dinsu.

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *