FARAR WUTA CHAPTER 1 BY AISHA MAHMOOD

FARAR WUTA CHAPTER 1 BY AISHA MAHMOOD

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wajen karfe goma sha biyu na rana, matar dake cikin kitchen ɗin da aka zagaye da langa-langa daga ɗan madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani ɗaurin itace dake gefe ta ƙara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ƙiyasi.

Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa.

Sai da ta tabbatar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ƴarta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da komai.

Ƴar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai ɗaukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an ɗiga wani abu a cikinsu.

“Yi sauri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a ɗora don yanzu zaki ji su sun dawo.”2

Amina ta buɗa labule ɗakin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace.

“Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi.”

“Garin ne ba zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki.”

Da murmushi tace.

“Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta.”

Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen ruwa da ita tana fadin.

“Ki cigaba da addu’a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah.”

Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi kyau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ƙulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba.

Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta daɗe da soke Jami’a a lissafinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa wajen kula dasu da ɗan abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ƴaƴan sa zasu huta da duk wani gata na duniya.

Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ƙarama inda zata dan koyi aikin lafiya… Don mahaifiyarta tasha faɗa mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye da ace ta zauna bata yin komai.2

Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ƙarshe yake a can wata jami’ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kuma hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ƙanwarsa.

Mu’amalarsu daban take da yadda take ganin tsakanin ƙawarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko ɗaga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu’amalarsu aure zata kai.3

“Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa.”3

Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin.

STORY CONTINUES BELOW

“Ta nawa?” Ta tambaya.

“Ta naira Ashirin.”

Sai ta ajiye farantin waken ta miƙe ta karbi kudin, watanni hudu kenan da fara sana’arta ta saida alawar madara, gullisuwa da kuma albishir, kuma ciniki take yi sosai don a kwana uku kawai take sake yin kowannensu na dubu biyu. Wannan shine babban abinda ke ɗebe mata kewa da kuma faranta ranta ganin yadda take iya yin wasu bukatunta da kanta har ma ta taimakawa ƙannenta da ɗan kuɗin kashewa, saɓanin a watannin baya da bata komai.

Lokaci shine rayuwarka ta duniya da kuma lahira, babu amfani ka barshi yana tafiya haka sakaka… Kalaman Ammansu kenan a kullum idan tana bayanin abubuwan da suka dace da rayuwar mutum.

Ta ɗebowa yaron gullisuwar hade da canjinsa, ta fito daga falon nasu da babu komai sai shimfidadden carpet daidai lokacin da Fatima tayi sallama ta shigo.

“Amma ina wuni.”

Ta gaishe da Ammar dake wanke bayan tukunyar data dauka.

“Lafiya kalau Fatima, Hajiyan ta fita ko tana nan?”

Hajiya mahaifiyar Fatiman ce, kuma tana zuwa jinyar kakar Fatiman ne da aka kwantar a asibiti kullum.

“A’a bata fita ba, girki take yi tukunna.”

“To bari in gani nima idan na gama nawa ko zan iya bin ta, tun jiya nake waƙar ya kamata in koma wallahi.”

“Ai jikin nata ma da sauki.”

Cewar Fatiman tana nufar hanyar ɗakin su Amina rike da ledar hannunta, ganin hakan yasa Amina ta dauko farantin waken da ta gama gyarawa, ta nufi wajen rijiya ta zago ruwa ta wanke shi sannan taje ta zuba a tukunyar dake gab da tafasa.

“Kaya Ahmad ya kawo min jiya da yazo.”

Tana bude labulen ɗakin Fatiman ta fada, da fara’arta kuwa ta goge ruwan hannunta a jikin doguwar rigar da ta saka sannan ta ƙarasa gefen katifarta inda Fatiman ke fito da kayan, atamfa ce har guda biyu da kuma farin mayafi ɗaya sai kayan kwalliya.

“Gaskiya ne Fati, wallahi ki gode Allah, Ahmad na ji dake.”

Fatima ta juya idanunta alamun dadi tana murmushi. Fara ce ita sosai, farin da take alfahari dashi a kodayaushe, tana ganinshine silar samuwar abubuwa da yawa a rayuwarta, don iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne sosai.2

“Ni kaina wallahi na sani Amina, shi yasa nake gode masa kullum.”

“Allah kuwa yana da kyauta, Allah ya saka masa da alkhairi… Kai wannan tafi kyau wallahi.” Ta fada tana daga wata.

“Kamar kin san nima nafi ganin kyanta, har cewa nayi ko in barta sai Sallah kawai muyi ankonta ni dake.”

Amina ta bude kwalin wata hoda sannan tace.

“Sallah fa da nisa, ki ɗinka abarki kawai. Ma yi wani ankon idan lokacin yazo.”

“To shikenan.” Fatima ta gyara zama tana kallon yadda take kallon kayan, sai kawai tace.

“Wai yaushe rabon Abdallah da ya miki kyauta ne Amina?”1

Amina bata bar kallon kayan kwalliyan ba tace.

“Shi da yake dan makaranta ta yaya zai iya wata dawainiya yanzu, in dai sallah tazo ai yana min kaya kin sani.”

Fatima ta tabe baki.

“Wannan fa daban, kyauta kuma daban. Ni wallahi Amina na sha gaya miki ki ƙyale Abdallah nan, da tuni kin fara ganin wadanda suka fishi, don naga alama yanzu idanunki basa ganin kowa.”

Sai a lokacin Amina ta kalle ta.

“Fatee, ke fa kin san ni duk wannan abin ma ba a gabana yake ba, shi yasa nake son mu’amala ta da Abdallah saboda shima yanzu karatunsa yake son gamawa, baya takura min nima kuma bana takura masa.”

STORY CONTINUES BELOW

“Wai har yanzu kina ganin zaki cigaba da karatun ne?”

Ta daga kanta.

“Wallahi ban fidda rai ba Fatee, duk da  na san Baba ba zai iya ba, kuma babu wanda zai yi min bayan shi din.’2

“Shi yasa nake gaya miki ki hakura kawai, ba komai mutum yake samu a rayuwa ba, a yanzu auren kawai ya kamata kiyi, ki ragewa su Baba nauyi sannan kema ki sami wajen da zaki iya ɗaukar ɗawainiyar wasu ma.”

Kallonta kawai Amina take tana murmushi don ta riga ta sani cewa ba zata taba fahimtar abinda take ji a zuciyarta bane, sai da ta kai ƙarshe sannan ta shiga haɗa kayan tanafaɗin.

“To shikenan, ki bari sai bayan maulidi, idan mun fara kai ki, sai in fara wannan lissafin.

Jin haka yasa ba shiri itama tayi murmushi tana kara juya idanunta, don kamar yadda aka tsayar da rana, bayan maulidin ne bikinta ita da Ahmad din.

“Baki san wani abu ba ma, wata mata na samu mai sayar da magunguna a can layin…”

Da haka ta shiga bawa Amina labarin da yasa ta bar hada kayan ta zare idanu tana kallonta kafin  ta shiga ɗaka mata duka alamun bata son zancen, ita kuma tana kyalkyala dariya.

Mahaifin Amina mai suna Alhaji Sulaiman dattijon mutum ne mai sana’ar harkar aikin katako, ya samu wadata a da, don gidan da yake zaune da iyalansa na kansa ne, amma a yanzu abubuwa sun tsaya masa ta yadda ya ɗauki hakan ya sanya a ransa har ya zama shine damuwarsa a kodayaushe. Ƴaƴan sa biyar tare da matarsa Halimatus- Sadiya bafulatanar Niger da iyayenta suka dawo Nigeria da zama.

Amina ce ta farko, sai Aminu, Maryam, Adam da kuma autarsu Hafsa. Maryam, Aminu, da Adam suna matakin secondary ne a karatu yayin da Hafsa kadai take Primary, amma da yake makarantar da suke zuwa wata community school ce dake waje ɗaya, tare suke tafiya dukkaninsu tare suke dawowa.

Babban damuwar Alhaji Sulaiman a yanzu shine ganin ƴaƴan sa na ƙara tasawa kuma harkar samun sa na ƙara yin baya, karayar arziƙin da ya samu ta taimaka ƙwarai wajen karya zuciyarsa akan komai, kullum cikin lissafi yake da kuma damuwar da ƙarara kowa ke gane ta duk da irin nuni da kuma nasihar da matarsa ke yi masa a kullum.3

***

Ƙarfe Biyu da rabi.

“Yaya dan girman Allah zaki bani naira dari? Ƙunshi zanyi.”

Maryam ta fada lokacin da take ƙoƙarin cire uniform ɗin ta bayan sun dawo daga makaranta. Amina na zaune tana ninke kayan wankinta tace.

“Ƙunshin me zaki yi?”

“Bikin yayarsu Na’imah fa, kin manta jiya nazo da katin.”

Jin tayi shiru yasa ta sake tambaya.

“Zan baki Maryam, Allah ya kaimu gobe.”

“Me za’a bayar? Idan ana ƙaunar Allah nima a taimaka mun.”

Aminu ya fada yana shigowa cikin ɗakin.

“Kaima ƙunshin zaka yi?”1

“Me kyau ma kuwa, don kin san sai yafi fitowa a hannu na ma akan bakar fatarta.”

Ya fadi hakan sanin cewar shi fari ne, don ƴan mazan biyu su suka yiwo mahaifinsu sak a kammani da kuma hasken fatan, matan kuma Suka yo mahaifiyarsu, har gwara Maryam ma ana cewa idonta irin na babansu ne, amma Amina da Hafsa babu abinda suka bari a kammanin Amman.

“Wallahi ni ba baƙa bace kaima ka sani, irin wannan kalar fatar sai ka zagaye garin nan kaf baka samu irinta ba.”

“To idan ma an samu me za’ayi da ita? Da dai irin ta Amina kika ce sai in yarda, amma ke duk gidan nan ma akwai mummuna kamar ki.”1

STORY CONTINUES BELOW

Maryam ta kara haɗe ranta tana saka hijabin data ɗauko. Amina ta jefo masa wata riga dake hannunta tana murmushi.

“Haɗa mu kayi kawai kake zagi Aminu, dani da ita ɗin me ya banbanta damu, ka takurawa Maryam wallahi.”

“Haba ya zaki hada kalar ki data wannan fingilar? itama ta hakura ta karɓi kanta yadda take ne taƙi, sai faman iyayi fal ciki.”

Da ƙunƙuni Maryam ta faɗi wani abun kafin ta tayar da sallarta. Hakan yasa shi dariya don shi kansa ya sani girman dake tsakaninsu ne kawai yasa take raga masa a azababbiyar magana da kuma rashin kunyar dake cikinta.

“Sai yaushe zaka fita yau?”

Amina ta tambaya sanin cewar da ya dawo baya dadewa a gidan yake tafiya can inda yake koyon gyaran mota a can hanyar gidan zoo, har  ma ya fara kwarewa don kusan shekara biyu kenan da Baba ya kai shi wajen.

“Sai na ƙarbowa Baba, kayansa daga wajen guga…” Ya shafo kansa.

“… Tun dazu ma fa ya kamata in je, sun ce sun gama.”

Kafin Amina tayi magana, Hafsa ƙaramar ƙanwarsu ta shigo gidan hannunta riƙe da ƙullin farar ledar atturuhun data siyo na girkin dare da kuma takardar yashin madina tana zubawa a ɗaya hannunta tana lashewa. Amina ta ɗaga murya ta kirata ganin bata da alamun shigowa.2

“Ki shigo ki cire kayan nan ki saka na islamiyya, ga uku nan har ta kusa, Adam har ya tafi kina nan.”

Tana jin hakan Idanunta irin na Amina suka kaɗa a take sannan muryarta ta koma ta kuka, ta shigo ɗakin da sauri tana faɗin.

“Dan Allah kice Ya Maryam ta raka ni, wallahi zane ni za’ayi…”

Kafin Aminan ta amsa, Aminu yace.

“Saka kayan muje in raja ki daga nan sai in wuce.

Ai kuwa da murnarta ta ruga da gudu zuwa dakin Amma inda kayanta suke, ta sani ba wanda ya isa ya dake ta makarantar tunda Aminu ne zai raka ta.

Aminu ya ciro Naira dari biyu daga aljihunsa ya cilla kan sallayar da Maryam ke sallah yana faɗin.

“Gashi nan kije a zana miki abinda ba ganinsa za’ayi ba.”2

Amina tayi murmushi tana godewa Allah a zuciyarta, tana son yadda suke tallafar junansu akan irin ƙananun buƙatun nan.

Hafsa bata dawo ba suka tsinci sallamar mahaifinsu, dukkaninsu suka kalli juna a lokaci guda sanin cewa lokacin ba lokacin dawowarsa bane, ƙa’ida ne sai bayan sallar magriba kullum yake dawowa don har Aminu yana yawan riga shi isowa ma.

“Allah yasa kar ya tambayi kayan nan…”

Aminu ya faɗa yana dafa kansa.

Ta tsakanin raga-raga labulen Amina ta hango yadda mahaifin nasu ya dafa kan Hafsa da ta taho ta rungume shi, sannan kai tsaye ya nufi hanyar ɗakinsa.

Taga Amma ta fito daga falo sanye da hijabi alamun salla tayi ta bin bayansa tana fadin sannu da dawowa.

“Ke maza ki dauko takalminki mu fita.”

Cewar Aminun, sannan ya juyo ya kalli Amina.

“Kice masa tun dazu na tafi karɓi kayan.”

Ai kuwa yana sanya kafarsa waje suka ji Baban yace.

“Fita ce ta kama ni Halima, ina kayan da nace a karbo min?”

Basu ji amsar da Amman ta bayar ba sai muryarsa da ta sake dagawo wajen kiran Aminu.

“Aminu! Yana gidan nan?”

“Na shiga uku..”

Cewar Aminun, kuma Amina na kallon sanda Maryam ta murmusa a sallarta don daɗi.

STORY CONTINUES BELOW

“Baba sannu da zuwa, wani abu ne ya faru ka dawo yanzu?”

Ta tsinci muryarsa da yayi sauri ya tsugunna yana shafa kai ganin ya fito.

“Ni da gidana don na dawo sai ka tambaye ni me nazo yi? Ina kayan da nace ka karbo min?”

“To, to, bari aje a karbo.”

Ya fada kamar sai a lokacin yace ‘je ka karbo din,’ kuma bai jira ya sake cewa komai ba ya kama hannun Hafsa da ta gama shiryawa suka yi waje.

Alhaji Sulaiman ya girgiza kansa kawai saboda takaici sannan ya kalli Amma dake tsaye a gefensa.

“Hajiya Kilishi ce yanzun nan ta kira ni tace tana son ganina.”

Daga cikin ɗakin Amina zata rantse daga ita har Amman a lokaci guda suka yi murmushi.

Hajiya Kilishi ƴaruwar Baba ce, mace ce mai kirki da son kyautatawa, ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu ta kowanne fanni, tun kafin Mahaifinsu ya rasa arziƙinsa har bayan komai ya cakuɗe musu, don hatta kuɗin rubuta jarabawarta ta fita daga secondary ita ta tallafa aka biya, babban taimakon da tayi musu na kwanan nan shine lokacin da Maryam ta kamu da rashin lafiyar ciwon ciki, wanda daga ita har su kowa ya wahala kafin a gano cewar wani ƙari ne ke fito mata a gefen cikin kuma yayi girman da har sai an cire shi.

A wannan lokacin komai nasu ya riga ya ƙare wajen jinya, don hatta abinci sai daga gidan wan Baban ake kawo musu kullum ko tukunya basa dorawa, ɗan abinda Baba ya samu da kuma na wajen Amman daga ƴan sana’o’in da take yi duk a asibitin suke karewa.

Don haka a dole Baban ya shiga neman bashi ƙofa-ƙofa, ƴanuwansa suka hada masa iya abinda zasu iya amma ko kwata ba’a shafe na lissafin ba, Hajiya Kilishi ita taji labari a danginsu, ta kira Baban har gida ta bashi tallafin naira dubu ɗari uku, kuɗin aikin har da ɗoriya akai, tun daga wannan lokacin zuciyoyinsu suka kara girman darajarta a wajensu.

Mijin ta wani babban mai kuɗi ne kuma sanannen mutum ne, itace matarsa ta biyu kuma ƴaƴan ta biyar dukkaninsu mata, amma ance saboda zaman amanar da suke yi da uwargidanta babban ɗanta ma a wajen Hajiya Kilishin ya tashi tun yana yaro ta yadda ba kowa ne ya san cewa ba itace ta haife shi ba, Baba yasha gaya musu cewar ko gidan yaje baya iya banbance ƴaƴan ta dana uwargidan.1

“Shinkafa da wake kuka yi? A zubo min dan Allah kafin yaron nan ya dawo.”

Muryan Baban ta katse tunanin Amina daidai lokacin da Maryam a gefenta ta idar daga sallah, ta sake kallonsa ta cikin labulen sanda da yake cewa.

“Allah yasa Amina ta daka yajin nan nata mai daɗi.”

A lokaci guda murmushi ya suɓuce a fuskarta, sai kawai ta mike tana faɗin.

“Akwai Baba, Bari in kawo maka.”

***

Royal Brompton Hospital.

Sydney St, London SW3 6NP, United Kingdom.3

…So I took your hand, back through lamp-lit streets,

I knew,

Everything led back to you

So can you see the stars over Amsterdam?

You’re the song my heart is beating to…

Waƙar a hankali take fitowa daga cikin labtop ɗin dake ajiye a wani ɗan ƙaramin tebur da kujerarsa dake can jikin dogon windon ɗakin, ɗakin asibiti ne da banda gadon mara lafiyar da kuma tarin computers ɗin gefe dake auna lafiyar wanda ke kwance, babu komai sai wata drawer daga can gefe wadda aka yi mata ado har da wasu ƴan fulawoyi, ɗakin a gyare yake tas yana kuma ƙamshi mai daɗi, ga room heater dake fitar da wani ɗumi mai daɗi sakamokon sanyin ƙanƙarar snow ɗin dake zuba daga waje.

STORY CONTINUES BELOW

A hankali idanun mara lafiyar dake kwance akan gadon suka buɗe, kuma duk da lumshewar su girman su ya fito a lokaci guda, matashi ne mai siririyar fuska, yana da yalwar gashin kai da kuma na gira kamar yadda na idanunsa suke dogwaye ta yadda idan ka kalle shi zaka ga kamar baya iya buɗe idanun nasa ne sosai.

Ya ɗago da hannunsa dake maƙale da allurar ruwan drip ɗin gefe, ya kalli hannun tsawon wasu sakanni kafin yasa ɗaya hannun nasa ya murza goshinsa alamun takaici, sannan a lokaci guda ya fizge drip ɗin daga jikinsa ya mike zaune, jini ya shiga fitowa daga inda allurar ta fita amma bai ko bi ta kai ba ya kalli rigar dake jikinsa, rigar asibitin ce wadda ake bawa kowanne mara lafiya.

Ya shiga ƙarewa ɗakin kallo a hankali har zuwa kan drawer dake can gefe, a lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa da jakar da Ishaq ya ajiye a ciki jiya don haka ya mike tsaye, jiri ya so ɗaukarsa amma ya dage ya tsaya akan ƙafafunsa sannan ya isa ga drawer.

Ya buɗe ciki ya fito da wata baƙar jaka ya shiga fito da kayan ciki, ƙamshin turarensa na ‘Dior Sauvage’ shi ya tabbatar masa da cewar kayansa ne tun kafin ma ya gane su, kala biyu ne sai kuma wata ƙatuwar rigar sanyi wadda ke zuwa har gwiwa, bai yi tunanin komai ba ya shiga canjawa zuwa kayan, sai da yazo ɓalle maɓallan rigar saman sannan ya kula da jinin dake fita daga hannunsa.

Don haka ya saka rigar asibitin da ya cire ya goge sannan ya ɗora daya rigar, ya kuma jawo rigar sanyin ya dora akai, bai ko ɗauke rigar asibitin dake kasa ba ya saita facing Cap ɗin da ya ɗauko a ciki daidai fuskarsa sannan ya nufi hanyar kofar ɗakin, ya san duka wayoyinsa basa nan kuma Ishaq bai bar tasa a gefen labtop ɗin ba don haka ya nufi ƙofar ya buɗe, dogon korido ne a wajen mai dauke da kofofin ɗakuna da kuma mutane dake ta wucewa ta cikinsa, ya tabbata babu ma’aikatan da suka san shi a cikin waɗanda ke wucewa don haka kansa tsaye ya bi ta cikin mutanen dake tafiya ya saje, yana mai nufar hanyar waje.

Iskar dake kaɗawa a wajen mai tsananin sanyi ta ratsa fuskarsa sanda ya fito daga asibitin gabaɗaya, dare ne lokacin, ga fitulu a koina, na kan titi dana motoci, ga mutane birjik musamman na ƙafa sai faman wucewa suke.

Haka ƙofar asibitin take a kullum, tun daga shekarun da ya fara zuwansa har yau. Sanyi ya shiga ratsa kunnuwan sa dake buɗe sannan a lokaci guda yaji wata irin yunwa ta mamaye shi, sai kawai ya saka tafin hannayensa duka biyu ya gefen fuskarsa lokacin da idonsa ya sauka akan sunan wani kanti daga can tsallake, kantin da yake yawan yin siyayya duk lokacin da yazo kasar.

“24 dollors.” (Dubu goma.)

Baturen dake kan kantar ya faɗa a lokacin da ya gama lissafa abubuwan daya ɗebo.

Ya kai hannunsa bayan aljihu kamar zai fito da wallet sai kuma ya dawo dashi, ya matso daidai jikin kantar yana kallon mutumin yace.

“You know me right?” (Ka san ni ko?)

Kallon da mutumin yake masa yasa ya cigaba da cewa.

“I used to come around, from that hospital…(Ina yawan zuwa, daga wancan asibitin..)”

Ya juya ya nuna asibitin sannan ya dawo ga fuskar mutumin da bata canja ba, sai kawai ya daga hannayen sa sama alamun sallamawa sannan yace.

“What I mean is my brother is coming to pick me from here… So do you mind If I just wait for him while I eat these? Because honestly I dont have anything with me right now but I assure you he’s going to pay when he arrive….”

(Abinda nake nufi shine ɗan uwana zai zo yanzu ya dauke ni anan… so ba zaka damu ba idan naci wadannan kafin yazo, don bani da komai a jiki na yanzu amma ina tabbatar maka shi zai biya ka idan yazo…)

Mutumin ya saka hannunsa ya danne kayan da yake shirin ɗiba, sannan da sautin muryarsa da yafi kauri a yanzu ya sake maimaita masa adadin kudin.

“24 dollors.” (Dubu goma.)1

Har ya haƙura ya ɗauke hannunsa yana shirin juyawa sai kawai mutumin dake tsaye a bayansa yace.

“You’re holding up the line, man! If you can’t pay just leave.”

(Malam kana riƙe mana layi, idan baza ka iya biya ba ba ka bar wajen mana.)

A sakannin da mutumin ya rufe bakinsa, a sakannin wani irin naushi ya ziyarci fuskarsa, naushin da ya kusan kaishi har kasa, ya ɗago jini na fara zuba ta hancinsa lokacin da wata mata a gefensu ta ƙwalla ƙara shi kuma ya furta kalmar zagi yana share jinin, kuma baiyi wata-wata ba ya nufo kansa da nasa naushin shima dsya haddasa fada a tsakaninsu ba shiri, kuma kowannensu yaji lokacin da mai kantin ya kwalla ƙara yana faɗin.

“Someone should call the police!” (Wani ya kira ƴan sanda!)

****

British Transport Police Station

No. 2 Melton St, London NW1 2BW, United Kingdom.

“Kun tabbata dukkan waɗannan bayanan file ɗin gaskiya ne?”

Ɗan sandan ya tambaya daga tsallaken teburin da Ishaq ke zaune tare da wani ma’aikacin asibiti a gefensa.

“Da gaske muke ranka ya dade, mara lafiya ne ya fito ba tare da an sallame shi ba, kuma a yanzu haka ma ba’a hayyacinsa yake ba.”

Ɗan sandan ya kalli ma’akacin asibitin da yayi magana, ya kara kallon ID Card ɗinsa da ya mika masa sannan ya gyada kansa yana sake kallon cikin file ɗin.

“Naga dukkan wasu bayanai na cewar yana da matsalar kwakwalwa, amma banga wani bayani ko sau daya na abinda ciwon ke saka shi ba…”

“Ai da yake yallabai, mu  a asibiti cutar kawai muke bayani ba abinda zata haifar ba.”

Jin haka yasa Ɗan sandan ya dawo da hankalinsa ga Ishaq dake zaune yana kallon can gefe inda aka ƙulle tarin mutane a cikin wani budadden cell da aka zagaye da karafa kawai.

“Kai ɗanuwansa ne ko? Zaka iya gaya mana abubuwan da yake yi, don mu san cewa ba da gangan yayi abinda muka kama shi yanzu ba?”

Ishaq ya gyara zamansa bayan ya dawo da hankalinsa nan, sannan cikin harshen turanci shima yace.

“Yayi abubuwa da yawa yallaɓai, waɗanda suka fi wannan ma, ba tun yanzu ba…”

“Misali…” Ɗan sandan ya katse shi. “Misali zaka bani ba wani bayani ba.”

Jin haka yasa Ishaq haɗiye yawu ba shiri, ya juya ya sake kallon idanun da suke kallonsa daga cikin cell ɗin sannan ya gyara zamansa kaɗan, muryarsa can kasa yace.

“Yallabai, a karo na ƙarshe da ciwonsa ya tashi saura kaɗan yayi kisan kai.”1

Idanun ɗan sandan basu canja ba, ya cigaba da kallonsa na wasu sakanni kawai kafin ya gyaɗa kai, sannan ya nuna file din dake hannunsa.

“Zan baku belinsa ne yanzu saboda wannan kawai, amma ku tabbatar bai sake barin asibitin nan ba sai da cikakkiyar lafiyarsa. Idan ba haka ba idan muka sake kama shi, mu zamu riƙe shi har sai ya warke.”

Dukkaninsu suka gyada kai alamun sun fahimta kafin ya juya ya kira wani ɗan sanda dake ƙoƙarin wucewa.

“Stone! bring the Black one out.” (Stone! Fito da baƙin cikinsu.)

Stone ɗin baya bukatar wani karin bayani don wanda aka nuna masa shi kaɗai ne baƙi a cikin tarin turawan cell din, don haka ya zaro muƙullai daga jikinsa ya nufi wajen.

Ɗan sandan ya sake kallon file ɗin hannunsa a karo na ƙarshe, idanunsa suka sauka akan sunan dake rubuce a jiki.

Ma’aruf Mansour Bakori!”Kowanne ɗan adam yana da tarin ƙalubale a rayuwarsa, amma ga wanda suke da cutar ‘Bipola disoder’ nasu ƙalubalen daban ne. Bipola disoder cutar ƙwaƙwalwa ce dake canja yanayin mutum a lokaci guda, ta canja ƙarfinsa, yanayin tunaninsa har da ɗabi’arsa. Cuta ce dake iya taba rayuwar mutum ta bangaren aikinsa, karatu,  zamantakewa har ma ta iya dakushewa mutum hanyar cigaba a rayuwarsa, don tana yawan tashi ne akai-akai.+

Cutar tana farawa ne daga lokacin ƙuruciya, kuma duk da cewar babu takamaimai maganinta ana samun saukinta ko kuma ƙaruwarta idan har ba’a bin ƙaidojin magani daidai. Tana da matakai huɗu kuma na ƙarshen da ake kira da “Mania” shi yafi kowanne hatsari.

A matakin ‘Mania’ mara lafiya yana jin tsananin ƙarfi da jin cewa zai iya komai, da kuma tsananin fushi da yawan tunanin abubuwa barkatai, wanda ke jawo mutum ya harzuƙa ta yadda babu mai iyawa dashi, mara lafiyar yana samun ƙarancin bacci da kuma rashin nutsuwa sannan wasu ƙwaƙwalwar su tana buɗewa ta yadda za su yi abinda idan a lafiyarsu ne baza su iya ba. Matakin dake bi wa wannan kuma shine ‘HypoMania’….”1

Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga wata Tv dake kafe a saman harabar wajen, ƙaton wajen jira ne na asibiti inda tarin ma’aikata ke wucewa wajen wasu gadaje daga can baya da aka kwantar da marasa lafiya, labulayen da aka sassaka a tsakanin kowanne gado sune kadai abinda ya raba gadajen.

Bayanin dake fitowa daga Tvn, na irin rashin lafiyar ƙwaƙwalwar da ake dubawa a wannan ɓangaren asibitin ne, masu jiran kuma na zaune suna saurarar bayanan da ake yi mai dauke da hotuna don sauƙin fahimta ga marasa lafiyar da kuma masu jinyar, Ishaq yana ɗaya daga cikin masu jiran, yana zaune daga karshen kujerar kamar mai jiran ƙiris! Ya mike, kafarsa ta bangaren dama yake faman bubbugawa yayin da gefen bakinsa yake a cije.

A bayyane yake ga duk wanda ya kalle shi cewa jira kawai yake likitocin dake tsaye a wajen gadon ɗan’uwansa su fito daga bayan labulen da aka zagaye gadon dashi. Sun taru kusan su bakwai a ciki har da Nurses don hankalinsu ya tashi jin cewar daga police station aka taho dashi bayan an neme shi an rasa.

Ya sani cewar dukkaninsu tsoro suke yi game da ciwonsa, don Ma’aruf ya riga ya kai mataki na karshe a ciwon ƙwaƙwalwar tasa, ya riga ya kƙure komai a Bipolar Disoder, don idan har akwai wani mutum a duniya da baya taimakon kansa to Ma’aruf ne. A shekaru goma da cutar nan ta same shi babu irin fadi tashin da ba’ayi ba daga kowanne ɓangare na iyaye da kuma ƴanuwansa amma rashin tasa tallafawar ya haɓɓaka ciwon har sai da ya ƙaraso matakin ƙarshe, ‘Mania Stage’.

A baya bai fi ƴan awanni ko kwana ɗaya zuwa biyu ba yake yi idan ciwon ya taso masa, amma a yanzu sati guda cur, har suka zo ƙasar nan Ma’aruf ba’a hankali sa yake ba, hakan yasa dole aka kwantar dashi a asibitin da alluran bacci wanda suka taimaka, ya farka cikin hayyacinsa yanzu.

Don duk da cewar a police station suka je suka same shi, idanunsa kawai ya kalla ya san cewar ya dawo hayyacinsa tun kafin likitocin ma su gane, shi yasa ya matsu da fitowarsu a yanzu don yaje ya same shi, ya sauke maganganun dake zuciyarsa tun daga ranar da Mami ta kira shi muryar ta na rawa taje ya taho gida Ma’aruf ya shigo musu da gawar wani.

Likitocin duka fito a daidai wannan lokacin, kuma bai tsaya jiran komai ba ya zagaya ta ɗaya hanyar da wandanda ba ma’aikata ba ke wucewa ya nufi wajen gadon.

“Minti biyar! minti biyar kawai na fita Ma’aruf amma kayi tsalle daga asibitin nan zuwa police station!”1

Ya faɗi hakan da harshen hausa daidai sanda ya bankaɗa labulen da aka zagaye gadon. Dama abinda Ma’aruf ɗin yake jira kenan, ya riga ya sani cewar ya daɗe a waje yana kaɗa ƙafa yana jira likitocin su fita ya shigo da tarin ƙorafinsa, don haka hankalinsa a kwance ya ɗago da idanunsa ya kalle shi.

STORY CONTINUES BELOW

“Kaima sani bana iya rike yunwa, na tafi in samu abinda zanci ne and you left me with nothing, ba dole su kaini police station ba.”1

Ishaq ya girgiza kansa.

“Ma’aruf ba a Nigeria muke ba, ko baka gane bane da ka farka? me kake tunani idan suka kama ka a ƙasar nan?”

Maimakon ya bashi amsa kai tsaye, sai ya koma da baya a jikin gadon, ya zura hannayensa duka biyu cikin gashin kansa sannan yace.

“Na sha gaya maka kana damuwa da yawa Ishaq, kana damuwa akan abubuwan da suke faruwa dama wanda basu zo ba.”

“Kuma matsalar kenan, kai da baka damuwar, baka damuwa da kanka balle kuma na kusa da kai, shi yasa har muka zo wannan matakin Ma’aruf! Mania!”

Ya faɗi sunan mataki na karshe a cutar da Ma’aruf ɗin ke fuskanta, kuma ga mamakinsa, a lokaci guda Ma’aruf ɗin ya juyo ya kalle shi, sannan a cikin sakan biyu idanunsa suka haska da wani abu da Ishaq ɗin zai rantse da ubangijin dake busa musu numfashi cewar bai taba gani a idanunsa ba. Tsoro da kuma fargaba! Sai kawai ya girgiza kansa sannan ya cigaba da faɗin.

“Shekara biyu da suka wuce a asibitin nan ko HypoMania test ɗinka basu kai ba, baka da lafiya amma babu wanda ya sani babu mai ganewa, muna ɓoye komai daki-daki don rayuwarka ta tafi daidai. Amma yanzu ka gaya min me kayi kafin mu taho nan Ma’aruf? Daniel ka yiwa dukan da har ya suma akan baiyi maka submitting takardu a office ba, ka dake shi har ya suma Ma’aruf sannan ka sako shi a mota ka kaishi gida, ka shiga dashi har falon Baffa kana gaya masa wai ka kawo shi ya kore shi daga aiki!” (Mahaifinsa.)1

Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da ɗaukacin jama’ar da suka sanka, waye bai san kana fama da ciwon ƙwaƙwalwa ba Ma’aruf?

Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da duk ɗaukacin kewayen da mutane suka sanka, waye a yanzu bai san cewa kana fama da matsala a ƙwaƙwalwa ba? Waye bai san cewa kana da wannan nakasar ba Ma’aruf?”

Muryar Ishaq ɗagawa take a lokacin da yake fadar hakan, sautin ta na fitowa cike da wani irin daci da takaicin duk abubuwan da yake faɗa din, kuma har a lokacin yana ganin adadin kifta idanun da Ma’aruf ke yi alamun cewa kowacce kalma tana bada ma’anar da yake son ya gane a ƙwaƙwalwar sa. Bai ce komai ba ya cigaba.

“Ka san me ya fitar dani ɗazu? Ka san abinda yasa na bar ɗakin har kaje ka aikata abinda kayi?…”

Ya tambaya kamar yana jiran ya bashi amsa.

“… Office din likitan ka naje, shi ya kira ni personally Ma’aruf! Yayi min dukkan bayanin halin da kake ciki, kuma albishirin ka abinda kake so zai faru, idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma’aruf! Kana gab da rasa komai gabaɗaya…”

“And so what idan na rasa?!”

Yadda Ma’aruf ɗin ya katse shi a lokaci guda da tasa sautin muryar ya bashi mamakin da har sai da ya haska a idanunsa. Kallonsa yake har a lokacin da nasa idanun da suka canja, yanayinsu na kara lumshewa kamar kodayaushe idan yana cikin ɓacin rai.

“Nace sai me idan na rasa komai? Idan dai har ragowar lokacin da nake dashi zai bani dama na iya cimma abinda ke gabana sai me idan na rasa hankalina?”

Sai ya girgiza kansa kawai yana cigaba da kallonsa.

“Nasha gaya maka Ma’aruf ya mutu shekaru goma da suka wuce Ishaq, kaƙi ka yarda dani ne, amma Ma’aruf ya riga mutu, babu shi anan.”

Ya ƙarasa yana nuna ƙirjinsa, daidai lokacin da labulen dakin ya buɗe, wani bature ya leƙo fuskarsa a murtuƙe yace.

“What the in the world are you two talking abou…”

STORY CONTINUES BELOW

Bai karasa ba sakamakon kallon da su duka biyun suka juyo suna yi masa kowanne ransa a ɓace, sai kawai yayi sauri ya maida labulen ya juya, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya alokaci guda.

Shiru ya ratsa wucewar sakan ɗaya, biyu, uku… kafin Ishaq ya ƙaraso a hankali ya zauna a gefen sa.

“Kwana na nawa a asibitin nan?”

Ma’aruf ya katse shirun da sautin muryarsa da ya koma daidai, mai zurfi dake fitowa can kasa.

“Huɗu, you were unconscious for three days a Nigeria kafin mu taho.”

A hankali ya haɗiye yawu cikin maƙogwaronsa sannan ya ƙara tambaya.

“Me Baffa yace?”

“Ransa ya ɓaci sosai, ransa ya ɓaci fiye da duk yadda kake tunani, kullum sai ya kira waya ya tambaya idan ka farka, kuma yace da zarar ka dawo hayyacinka mu koma gida.”

Yaji lokacin da ya zuƙi numfashi ya fitar sannan ya koma da baya ya jingina da gadon bai ce komai ba, don haka shi ya cigaba da cewa.

“Mami kusan duk bayan awa guda take kira Ma’aruf, suna can ne amma hankalinsu anan yake, kowa ya damu, Hajiya tace hatta Abdurrahim jiya gidanka ya tafi ya kwana, dan Allah Ma’aruf, dan Allah ka taimaka ko don waɗannan mutanen ka tallafi rayuwarka, dan Allah.”

Kai tsaye maganganun suka shiga har wani waje dake can ƙasan zuciyar Ma’aruf, kuma yana jin yadda tasirin su ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinsa yana tafiya tare da gudun jinin cikinsu, sai kawai ya sake cusa yatsunsa cikin gashin kansa sannan ya runtse idanunsa.

Ishaq yana kallonsa, yana jin yadda tausayinsa ke bin zuciyarsa kamar kullum, ba sauki bane rayuwa da irin wannan cutar ya sani, ba sauki bane daurewa irin abinda ke zuciyar Ma’aruf din, ba sauki bane yadda yake iya daurewa abubuwa tsawon shekarun nan, ba sauki bane ba zama Ma’aruf din da yake gabaɗaya ya sani… Shi yasa fatansa a kodayaushe bai wuce Allah ya tallafi rayuwarsa ta wata hanya daban da take sabuwa ba, domin Allahn ya sani cewa su sun gwada duk wata hanyar da take a tunaninsu amma babu wani sauki.

Ya haɗiye yawu a hankali cikin maƙogwaron sa yana cigaba da kallonsa yace.

“Nayi mana booking flight, gobe zamu koma.”

Kuma ba don kallonsa yake ba ya tabbata ba zai ji sanda ya amsa da ‘Allah ya kaimu’ ba.

Saboda haka kai tsaye sai ya sake tambaya.

“Yaya kake ji?”

Ma’aruf yasa yatsu biyu ya shafo saman hancinsa har a lokacin bai buɗe idonsa ba yace.

“Ina ji ne kamar zan mutu saboda yunwa, nace ka taimaka min da abinci amma kana ta masifa, Idan na sake fita daga nan kar barni kawai kar kaje beli na.”

Ba shiri wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskar Ishaq ɗin na tabbas ɗin da yake dashi cewar ya dawo daidai, don har abada irin Ma’aruf guda daya ya sani a duk tsayin rayuwarsa.

Ma’aruf yaji lokacin da ya fita amma duk da haka bai bude idanunsa ba, hoto ɗaya ne ke yawo a cikin kansa, hoton ɗakin bincikensa, yana hasko tarin takardu da kuma hotunan da suke cikin ɗakin nan, sannan yana hasko yadda hanya ta ƙarshe da yake tunanin zata kai shi ga nasara bayan shekaru huɗu ta rushe har garinta, wanda takaicin haka shine sanadiyar tashin ciwon nasa da abinda yayi har suka taho nan.

Wata jijiya daga gefen kansa ta bullutso cike da wani sabon takaicin da ya sake ratsa shi, sabon takaici… Don wannan ɗauke yake da wani layi na fargaba da kuma tsoro, tsoron da bai taba ji a ransa game da ciwon nasa ba tsawon shekaru goma da suka wuce, maganganun Ishaq suka sake haskawa a cikin kansa.

…idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya, kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma’aruf!1

*

STORY CONTINUES BELOW

Alhaji Muhammad Mansour Bakori, sanannen mutum ne wanda yake da babban Kamfanin yin robobi a garin Kano tare da ƙaninsa Alhaji Usman, wanda su biyu ne kacal a wajen iyayensu, mahaifinsu ya rasu shekaru da daɗewa amma mahaifiyar su tana raye.

Alhaki Mansour Bakori yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha ɗaya, yayin da Alhaji Usman bai taba haihuwa ba tsawon shekaru talatin da aurensa, wanda hakan ya faru ne sakamakon wani hatsari da yayi tun kafin tun yana saurayi har ya zame masa sanadin hakan, shi yasa kowa a danginsu yake girmama matarsa Hajiya Madina da kuma jinjina mata na zaman da take dashi a duk shekarun nan alhali ita lafiyarta ƙalau.

Matan Alhaji Mansour biyu, Uwargidan itace Hajiya Maimuna, wata mata mai kirki da kuma alkunya, ɗanta na farko Jamal ya rasu shekaru goma da suka wuce, daga shi sai Ma’aruf wanda shi a wajen kishiyarta ya girma, sai Shukra, Munaya, Abdurrahim wanda shi tun yana shekaru biyu a duniya ya kamu da matsalar rashin magana amma yana ji kamar kowa, sai kuma autarsu Zahra.

Hajiya Kilishi itace mata ta biyu a gidan, wata mace ce mai tsananin kirki da kyautatawa, don faɗa ko da na rana guda bai taɓa haɗa su da Hajiya Maimuna ba tun zuwanta gidan, wani irin zaman lafiya da mutunta juna ne a tsakaninsu tun farkon zuwanta gidan, hakan yasa basu kaɗai ba ko wanda yake nesa ba zai taba cewar su ɗin kishiyoyin juna bane idan ya gansu tare.

Ita ta raini Ma’aruf tun daga watannin da aka yaye shi har zuwa girmansa na yanzu. Hajiya Maimuna, mace ce mai hali irin na mutanen da, tsananin kawaici akan abinda suke ganin shine daidai, don haka tun daga ranar da Hajiya Kilishi ta karɓe sshi bata ƙara nuna cewa shi nata bane, a suna kawai Ma’aruf ya santa a matsayin mahaifiyarsa, amma a wajen Hajiya Kilishin da suke kira da Mami ya samu dukkanin wata kulawar da ɗa ke samu daga mahaifiyarsa.

Ita ta raine shi da ƙarfin jikinta da kuma na zuciyarta, har zuwa girmansa kuwa ya zama tsakaninsa da Hajiya Maimuna gaisuwa ce kawai amma Mami ce komai nasa, duk da ƴadda wasu daga cikin ƴanuwan Hajiya Maimunan suke nuna rashin jin daɗin su akan hakan a yanzu da ya zama shine kaɗai namiji babba a gidan.

Ƴaƴan Hajiya Kilishi biyar ne, dukkaninsu mata kuma dukkanninsu harafin sunansu ya fara ne da harafin S, Safiyya, Salma, Surayya, Samira da kuma Sahla kamar yadda take so, don a wajen Daddy babu ruwansa da raɗin suna, duk wanda iyayensu mata suka zaba shi zai saka ba ruwansa. Zahra ce ma kawai taci sunan Inna Danejo ‘Fatima’ kamar yadda Hajiya Maimunan ta nuna tana so a saka.

Hajiya Maimuna ta sami matsalar shanyewar ƙafafu bayan ta haifi ƴarta ta ƙarshe Zahra, kuma babu irin maganin da ba’ayi ba a ƙasashe daban- daban amma ba nasara, don haka a dole yanzu sai akan Wheelchair take yawo.

Gidan Alhaji Mansour dake unguwar NNDC quarters a garin Kano, ƙaton gida ne mai ɗauke da bangare-bangare, akwai ɓangaren iyalansa guda biyu wanda kowanne iri daya ne, ƙaton falo da ɗakuna hudu kowanne da banɗakinsa a ciki da kuma sauran wajaje irin Kitchen, store, courtyard da dai sauransu, sai bangarensa inda shine waje na farko a gidan mai ɗauke da ɗakuna biyu da falo da kuma wajen meeting ɗinsa inda yake ganin baƙi a gida.

Akwai bangaren boys quarters inda masu a gidan suke zaune sai kuma wajen Inna Danejo kakar gidan, wato mahaifiyarsu Alhaji Mansour inda itama take da ƙaton falo, ɗaki ɗaya da kuma toilet, sai ɓangaren ƴan aiki, sai kuma bangare na karshe daga gefen hagu na harabar gidan, wato bangaren Alhaji Usman da suke kira da Alhaji Baba, wanda shima da a gidan yake tare da matarsa daga baya sai ya siyi wani gida gaba dasu kaɗan ya koma, don haka wajen a ƙulle yake babu kowa.

Ishaq abokin Ma’aruf ne kuma ɗan’uwansa, don da Mahaifiyar Ishaq ɗin da Hajiya Maimuna iyayensu ɗaya, asalin mahaifinsa ɗan Kaduna ne kuma shi kaɗai iyayensa suka haifa, mahaifinsa ya daɗe da rasuwa amna mahaifiyarsa sai da yazo matakin shiga Jami’a ne sannan Allah ya ɗauki ranta, don haka da shawarar Mami, Hajiya Maimuna ta tambayi Alhaji Mansour da kowa ke kira da Baffa, Ishaq ya dawo gidansu da zama daidai lokacin da Ma’aruf ke kokarin shiga Jami’a.

STORY CONTINUES BELOW

Mamin tayi haka ne don ganin ta samowa Ma’aruf sauki akan halin alhinin ɗanuwansa da har a lokacin bai gama warkewa daga ransa ba, don haka tare da Ishaq ɗin Baffa ya ɗauki nauyin karatunsu a wata Private University dake London har suka kammala, kuma hakan ya sanya shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da cewar ɓangare daban-daban suka karanta. Ma’aruf ya karanci harkar Kasuwanci ne yayin da Ishaq ya karanci ɓangaren aikin lawyer kamar yadda yake da buri tun yana yaro.1

***

Washegari…

No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Qauters.

.07:30 Pm.

Tun daga ƙofar gidan zaka gane cewar anyi wani taro ne a gidan an watse, don hatta gate din a bude yake gabaɗaya sannan ga motoci daga ciki suna kokarin fitowa.

Idan ka biyo ta cikin mutanen, zaka wuce ko’ina hanya ta kai ka har ɓangaren Hajiya Maimuna inda taron mutanen yafi yawa musamman a ƙaton falon ɓangaren da zaka tarar wanda yake cike da tarin mutane gabaɗayansu mata, kowa na zaune da abokin hirarsa yayin da ƙamshin turarukansu ya haɗe da ƙamshin daddaɗan abincin da aka gama ci a falon, don ga tarin plates nan wasu ma har da ragowar abincin sannan kuma a can gaban Tv stand na ɗakin akwai wasu manya-manyan flasks cike da snacks kala-kala ga duk wanda yake so ya diba.

Sai dai duk wannan ba shine abin kallo a dakin ba, tarin akwatunan dake zube a makeken carpet din tsakiyar falon ne, an buɗe kowannensu dake cike da kaya fal.

Lefen Babbar ƴar Hajiya Maimunan mace da suke kira da Shukra ne, amma ba zaka banbance adadin yawan ƴanuwan Hajiya Maimunan ko kuma na Hajiya Kilishi a falon ba, sun riga sun zama ɗaya dukkanninsu don ko a sati biyu da aka karbi lefe biyu na ƴaƴan Hajiya Kilishin Safiyya da Salma, duk sune dai a wajen, shi yasa a yanzu ma rabi hirarsu ta shirye-shiryen  bikin da aka saka nan da wata guda mai zuwa ce.

Hajiya Kilishi ta ratso ta cikin mutanen, sanye take da wata doguwar rigar lace daya sha adon stones sai wulgawar kyalli yake a cikin hasken fitulun dakin, ta karaso inda Hajiya Maimuna ke zaune akan kujerar Wheelchair dinta tana hira da wata ƴaruwarta, ta sunkuyo daidai saitin fuskarta sannan tace.

“Hajiya su Ma’aruf sun iso, yanzu na tura Malam Sani (direba) ya ɗauko su daga airpot, mukullin store dinki zan karba na ajiyemusu abinci ɗazu, Hajiya Madina ce tace zata tafi nace idan direban nata ya sauke ta sai ya karasa ya kai musu abinci don na san baxa su shigo yau ba.”

“Toh Alhamdlilah, Muƙullin yana hannun Sameera ita ta karba dazu wai sun ajiyewa ƙawayenta abinci su ma.”

Hajiya Maimunan ta amsa a hankali itama. Dukkaninsu sun sani cewa a duk tarin jama’ar gidan babu wanda bai san abinda Ma’aruf ɗin yayi ba da kuma cewar baya ƙasar don labari baya taba ɓuya, amma duk da haka gwara ace basu fallasa zancen ba duk kuwa da cewar duk ƴanuwa ne a gidan, amma hakan ba zai hana cece-kuce ba.

Daga nan ɓangarenta ta nufa, inda babu mutane sosai, kuma ƴanmatan gidan da wasu kawayensu suka tare suna ta hayaniyar da jiran a ragu don suma suje su buɗe nasu babin kallon kayan. A falo ta tarar da Zahra da Sahla ƴan autan gidan kuma sa’annin juna sun baje litattafansu suna ta aiki kamar basu san da bidirin da ake yi a gidan ba, dama yayyensu sun riga sun manna musu sunan Allazi boko 1 da kuma Allazi boko 2, don mayun karatu ne kamar ba gobe, yanzu suka shiga SS1 amma abinda suka sani ko Abdurrahim da yake SS3 bai sani ba, kwanaki har Surayya dake level three suka koyawa wani abu a Biology.

Har Hajiya Kilishin zata yi musu maganar abinci sai ta kula da plate din snacks dake tsakiyar litattafansu, ta sana aikin Mama Rabi ne hakan, wata dattijuwa ma’aikaciyar gidan da har yanzu bata daina kula dasu ba kasancewar ita ta yaye su tun suna ƙanana.

Don haka ta amsa sannu da shigowar da suka yi mata kawai ta wuce. Ta nufi kofar dakinsu Salma inda ƴanmatan suke, hayaniyarsu tun daga falon zaka ji ta, cike da raha da kuma nishadi kamar an fara bikin, kuma duka hirar da suke ta tsare-tsaren bikin ce da suka daɗe suna yi tunda wannan shine karo na farko da za’a aurar da mata a gidan, kuma har guda uku a lokaci guda.

STORY CONTINUES BELOW

“A’a ranar kunshi ne fa za’ayi style iri daya, ranar Kamu kamar kowa zaiyi style dinsa ne ko?”

Muryar Munaya ta tambaya cikin hayaniyar.

“Ranar kunshi fa shi babu anko Munaya kin manta ne kowa kayansa zai saka, da Kamu ne za’ayi har style ɗaya.”

Wata kawar Salma, mai suna Aysha ta bata amsa.

Hajiya Kilishi ta buɗe kofar dakin daidai lokacin da Munayan ke gyara glass din idonta tana kallon wayar Sameera dake hannunta inda take ƙoƙarin banbace tarin atamfofi da kuma lesukan da zasu yi ankon dasu.

A ƙaton gadon ɗakin gabaɗayansu suke a baje dasu da tarin plate din snacks din da suke ci, sai wadanda basu sami waje bane suka zauna daga kan bedside drawers.

“Ni fa wallahi gani nake kamar wata ɗaya ba zai isa duk wannan shirye-shiryen ba.”

Shukra ta faɗa tana danna tata wayar.

“What?!” Salma ta mike daga kwance tana kallonta.

“… Ai Ya Shukra kar ma ki fara wannan zancen don wallahi Imran ba zai taɓa yarda a ƙara mana ko sati ɗaya ba.”

Salma ta faɗa wanda hakan yasa dukkaninsu yin shewa a lokaci guda, don duk cikin amaren tafi kowa ɗokin bikin, yayarta Safiyya ba ruwanta don ita dama ba mai magana bace tun farko, kuma wanda zata aura mai mata ne da ƴaƴan sa biyu duk da cewar ba wani manyan ta yayi ba. Shukra kuma dake kan matakin masters dinta a bayyane yake cewa hankalinta yafi tafiya ga Project work din da take kan gaɓar yi fiye da bikin, duk kuwa da irin rawar kafar da  Suraj ɗin da zata aura ke yi shi, wanda dan wani abokin aikin Baffa ne.

Har Salma zata sake cewa wani abu Sameera dake gefenta ta daka mata duka, wani duka da idan zata yi ɓaram-ɓaramarta Mamin tazo wucewa suke yi mata shi, don haka a lokaci guda ta juyo ta kalli kofa inda Hajiya Kilishin ke tsaye tana kallonsu da murmushi.

“Mami ina wuni…”  Duka kawayensu na ɗakin suka hada baki wajen gaishe ta don tun zuwansu basu ma ganta ba.

Da murmushin ta amsa musu sannan ta kira Sameera.

“Ina muƙullin store dinsu Munaya? Yayanku sun dawo yanzu, kizo ki tayani mu debo abincinsu a saka a motarsu Hajiya Madina.”

Da wani irin murmushi mai faɗi Sameeran ta amsa, don Allah ya sani duk da kowanensu yayi waya dashi tun a jiya, da kuma hayaniyar gidan ta yau, suna cike da tunanin halin da Ma’aruf ɗin ke ciki, don abinda yayi wani abu ne da basu taɓa gani ba tsawon rayuwarsu duk da sun san cewa kuwa yana da wannan cutar.

***

Mallam Aminu Kano International Airport 

08:30 PM.

“Wata nawa aka saka bikin yaran nan ne Malam Sani?”

Ishaq ya tambaya a lokacin da yake kokarin saka jakar kayansu cikin boot ɗin motar da Malam Sanin ya buɗe.

“Wata ɗaya aka saka wallahi, ai gidan ma har yanzu yana nan a ɗinke, shi yasa Hajiya tace ba sai kunzo ba, kawai in wuce daku gida.”

Ishaq ya gyaɗa kansa yana rufe boot ɗin.

“Ai dama bamu da plan din zuwagidan nan yau, amma Lallai su Baffa sun shirya, har su uku ne fa a wata ɗaya kawai.”

“To ai rufin asirin Allah ake ciki kullum kuma shi ke rufawar.” Cewar Malam Sanin yana dariya.

Duk maganar da suke yi, Ma’aruf na zaune a cikin motar daga baya, wayarsa na riƙe a hannunsa haskenta na haska siririyar fuskarsa da a cikin ƴan kwanakin ta ƙara ramewa, message ne kawai ke tururuwar shigowa da kuma tarin emails tunda ya kunna wayar har zuwa yanzu, ya lumshe idanunsa kawai sai kallonsu yake a lokaci guda kuma yana jin hirar su Ishaq ɗin daga waje.

STORY CONTINUES BELOW

Allah ya sani gabaɗaya ya manta cewa shirye-shiryen bikin akeyi sai a jiya da Mamin ke tuna masa cewa yau ne za’a karbi lefen Shukra, kuma jin cewa gidan a cike yake yasa shima baiyi tunanin ya kamata su je ɗin ba, amma kuma ya kamata yaga Baffa a yau, idan yana gidan kuma fa? Sai yasa yatsan sa ɗaya ya share dukkan messages ɗin sannan ya lulubo nambar mahaifin nasa amma sau biyu ya buga bata shiga ba, don haka ya nemo ta Mami.

Bugu ɗaya kuwa muryarta ta shiga kunnensa.

“Mai gaskiya na, kun taho?”

Ta kira shi da sunan data laƙaba masa tun yarintarsa.

Sai ya sake lumshe idonsa ya koma da baya jikin kujerar lokacin da Ishaq da Baba Sani suka buɗe ƙofofin motar suka shigo.

“Eh Mami, Baffa yana gida kuwa?”

“A’a yana office shima har yanzu. Na bayar direban Hajiya Madina zai kawo muku abinci yanzu, wataƙila ma kuyi daidai dashi.”

Wani abu ya motsa a kirjinsa, don yayi kewar irin wannan kulawar tata a ƴan kwanakin nan, sai dai kafin ya saurari abinda ta cigaba da cewa hankalinsa ya kai ga abinda Ishaq ke cewa cikin wayar sa da aka kira ya amsa.

“To shikenan gamu nan insha Allahu…”

“… Akwai maganar da zamu yi Ma’aruf, nima nafi son ka samu hutu sosai zuwa goben.”

Sauran maganar Mamin ta shiga kunnensa bayan Ishaq ya kashe wayar da yake yi.”

“Ma’aruf, kana jina kuwa? Da kaci abinci ka sha magungunan da aka baka “

Yaji ta sake faɗa lokacin da Ishaq ke cewa Malam Sani…

“Sakataren Baffa ne yakira, wai Baffan yana son ganinmu a office ɗinsa kafin muje gida, ka juya ta wanna U-turn ɗin sai mu koma.”

Ba shiri Ma’aruf yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaronsa, don tun bayan farkawar sa sau ɗaya kawai yayi waya da Baffan, a jiya daya kira ta wayar Ishaq, ya tabbatar masa da cewar lafiya yake jin kansa shikenan bai kara nemansu ba, amma ko Baba Usman ya sake kira a safiyar yau kafin su taho.

Yana jin yadda Mamin ke cigaba jero masa tarin tambayoyi ta cikin wayar amma hankalinsa sam baya kanta har Malam Sani yasha kan U-turn din da Ishaq ya nuna wanda zai komar dasu baya zuwa hanyar Office ɗin Baffan, wani ƙaton branch na kamfanin su inda iya ma’aikata ne kawai a wajen.

“Muhammad…”

Muryar Baffan ta kira shi kuma a lokaci guda amonta ya ratsa har cikin kansa bayan sun isa Office ɗin, bayan sun shiga ciki kuma Baffan ya sallami wasu mutum biyu da yake tare dasu a lokacin, sannan bayan Ishaq ya dauki wata wayar ƙarya ya fita don dukkaninsu sun fahimci cewa dashi kadai yake son magana. Don haka ba shiri Ma’aruf yaji maƙogwaronsa ya bushe a lokaci guda, saboda Baffa baya taɓa kiransa da wannan sunan sai idan har wani zance mai muhimmanci zasu yi, kuma rana ta karshe da zai iya tuna ya kira shi da hakan shine ranar da aka daura auren sa.

Ya gyara zama a hankali yana jin yadda Baffan ya cika masa office din ta koina saboda kwarjini.

“Sun turo min da takarda wadda take bayanin ciwon naka.”

Ya san takardar shima, sun tura ta email ɗinsa sannan sunyi printing ɗinta a cikin tarin takardun da aka sallamo shi dasu.

“Sun ce a cikin shekaru biyu kawai ciwon ka ya kara haɓɓaka har ya kai matakin karshe, shi yasa abinda kayi ya faru…”

Baffan ya faɗi haka sannan kuma yayi shiru, wannan dai al’adar ta manya. Ƙarar sautin shigowar saƙo daga wayar dake aljihun Ma’aruf ya cika shirun dakin kafin ya cigaba.

“Ko zaka iya gaya min a shekaru biyun baya kana ina Ma’aruf?”

Sai ya gyara zamansa a hankali, yana tuno ranar da Baffan ya naɗa shi a matsayin manajan kamfanin ‘Bakori Enterprises’ ranar da burinsa na farko ya fara cika a duniya.

“Baffa… Shekaru biyu baya shine lokacin da ka bani matsayin manaja a kamfanin nan.”

Bai kalle shi ba, amma yaji sanda ya girgiza kansa.

“Ba wannan ba, rayuwarka personally Ma’aruf, kana ina?”

A yanzu ya rikice, yana jin kamar ma bai warke ba gabaɗaya, kamar ya sake bin jirgi ya koma asibitin nan ya kwanta.

“Ka manta?”

Ya tambaya amma bai bari ya amsa ba ya cigaba.

“… Bari ni na tuna maka, shekaru biyu baya kana tare da iyalinka Ma’aruf, shekaru biyu baya kana tare da matar da naje na karba maka aurenta har ma da yarinya, a shekaru biyu baya kai cikakken mutun ne mai kamala da mutunci a idon mutane, kuma a tsawon shekarun da kayi cikin wannan mutuncin,  hankalinmu da naka bai taba tashi kamar yadda yayi a yanzu ba.”

Wani abu ya zarce a maƙogwaron Ma’aruf, yaji wani ɓangare na ƙwaƙwalwar sa na gaya masa cewa wannan ce damarsa, yau shine lokacin da zai gayawa Baffa abinda shi da ishaq suka dade suna ɓoyewa, yau ya kamata ya gayawa Baffa cewa ba haka bane, abinda ya faru a zamansa da Ruƙayya har zuwa rabuwarsu ba yadda suke tunani bane sam.

“Na san da wannan tunin da nayi maka ka fahimci abinda ni dama duk sauran al’umma suka fahimta Muhammad, don haka kaje ka fara shirye-shirye, nan da wata guda zan karɓa maka wani auren tare da na ƙannenka.”

Sai da aka shafe sakanni kafin maganar ta shiga cikin ƙwaƙwalwar Ma’aruf, da wani irin ƙarfin da sai da yayi da gaske kafin ya iya jawo iska ta shiga ƙirjinsa, sannan a karo na farko tun bayan fitar Ishaq ya ɗago idanu ya kalli mahaifin nasa.

Sai dai me? Maimakon fuskar Baffan, sai hoton wajen ya canja a idonsa da wani lokaci da ya faru a shekaru biyu da suka wuce…

Lokacin daya shaƙe wuyan Rukayya da duka hannyensu biyu, yaji ƙarar sautin karkarin da take fitarwa a lokacin da kuma yadda hawaye ke zuba daga idanunta yayin da take kallon ƴarsu da bata fi watanni shida a sannan ba… Babyn da ya karɓe daga hannunta ya wancakalar da ita a cikin falon, kanta ya bugu da kujerar gefe ta shiga ƙwallara kukan daya karaɗe gidan gabaɗaya, wannan sautin kukan da a kowanne daren duniya, dashi yake kwana a kunnuwan sa!

***

Me ya faru shekaru goma da suka wuce?1

Wane bincike Ma’aruf ke yi da har ya kai ga tashin ciwonsa?

Wacece Rukayya? Me ya faru da ita da kuma ƴar ta?

Sannan wacece amarya ta huɗu a bikin iyalan gidan Alhaji Mansour Bakori?

About AIS

Check Also

FARAR WUTA CHAPTER 3 BY AISHA MAHMOOD

FARAR WUTA CHAPTER 3 BY AISHA MAHMOOD Www.bankinhausanovels.com.ng  Ana gobe sallah ne ranar, ita da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *