DOCTOR EYSHA CHAPTER 8 BY FANAN_A.A

DOCTOR EYSHA CHAPTER 8 BY FANAN_A.A

Www.bankinhausanovels.com.ng 

bakiji abinda Na fada bane haka nace *Luxury ward* ko bazaki iya bane ” ya faɗa yana juyi akan kujerar sa .

“kaima kasan halin dad bazai taba yadda da wannan Batum ba, Na Waare ɓangaren Masu kudi a hospital dinsa ba ,kasan matsayi ɗaya ya ɗauki mutane gaba ɗaya ,kasan dai bazan iya ba try to understand please” takai ƙarshen zancen murya a sanyaye .

” yayi kyau doctor zahra nagode sosai kina iya tafiya” ya fada yana nuna Mata hanyar fita.

“kayi hakuri Zan faɗa masa kuma inshaallahu zai amince ” ta faɗa jiki a sanyaye yayin da take haɗa files ɗin gabanta.

*Dr Aryan*

Zaune yake a ɗakin sa yana hada duk wani abinda yake buƙata A Wajen aiki, Dan gobe ne zai koma bakin aiki , white coat dinsa CE ya ɗauko daga drawer, Abu ne ya faɗo daga cikin aljihun rigar , duƙawa yayi da niyar ya ɗauko abinda ya faɗo,

Ƙwasham abin daure gashin *doctor eysha* ya gani murmushi yayi Wanda ya bayyana fararren haƙuransa “Eysha rigima yaushe kuma abin ɗaure gashin ta Wanda tafi so yazo nan ” tunawa yayi ɗazu da suka haɗu a Wajen wannan accident ɗin anan ne abin ɗaure gashin ya shiga nan “Turkashi ! ,Yau komin dare nasan sai tazo Neman sa ,Dan kuwa bata Wasa dashi , saboda Shi kadai ne abinda take gani tana Tina iyayenta.

(Kada Ku manta fans gaba daya a Kashmir hospital Babu Wanda yasan asalin Eysha sai doctor Ibrahim da kuma doctor Aryan kasancewar sa shine babban abokin ta kuma halin su tazo ɗaya, sai kuma doctor kaseem Wanda Shi Dan Jin ƙwaƙwaf ne da bin diddigin mutane ).

*Doctor zahra*

Tunda ta fito daga office din Dr kaseem Babu inda ta nufa sai office din Dr Ibrahim, tayi sa’a kuwa Babu kuwa a office ɗin,bata jira aka bata iKON shigowa ba kawai ta faɗa .

” daddy Na Wajen ka nazo ” .

“Nasan waje Na kika zo mana tunda Ni kaɗai ne a office din , Zahra wai yaushe ne zakiyi hankali ne ki ƙoyi sallama ” ya faɗa Rai aɓace .

” daddy look Naga fa Babu kuwa a office din, kaga Ni shiyasa Na shigo kuma ai nan din office din daddy nane ba sai Na jira an man izinin shugowaba” ta fada tana murguda baki wai ita Dole haushi take ji “kuma Aida Dr maryam CE Na tabbbata ita bata yin laifi a Wajen ka nasan ai baza kayi Mata ihu akai ba .

Shuru yayi yana mamakin Hali irin Na diyar tasa ,Dan yanzu Al’amarin ta ya fara bashi tsoro abu kullum sai lalacewa yake , Indai gatan daya nuna Mata shine yasaka ta koma haka Allah wadaran gata a duniya ,”yanzu ba wannan ba menene ya kawu ki Dan nasan banza kawu banza kasuwa “.

“daddy dama wani abu ne ya kawu Ni dama so nake a bude Luxury ward a Kashmir hospital” ta fada cike da ƙarfin gwiyewa .

” What! Me kika CE , impossible Dan kuwa badai a Asibiti Na ba Dan bazan taba yadda da wannan haukan ba ” ya fada Rai abace .

“okay ,well that’s good yayi kyau daddy yau ka nuna man matsayi Na a Wajen ka ,yanzu ka nuna man ba ka ƙyauna ko kadan , tohm yau ina so ka kwana da sanin Dole ka zaɓi daya tsakanina da Dr maryam, ka zaɓi daya ɗiyar ka ko budurwar ka” ta faɗa yayin da take tashi tsaye .

Tun lokacin da Dr zahra ta shigo office din Dr Ibrahim, Dr maryam take Wajen a tsaye saboda bata so ta shigo office din ran Dr zahra ya ɓaci Dan tasan Dr zahra bata ƙyaunar ta ko kaɗan , ganin yanzu zata fito daga office din yasa Dr maryam saurin barin Wajen amma hakan baiyu ba Dan har ta fito, 

Wata muguwar harara Dr zahra ta watsa Mata ,ita kuma sai ta mayar Mata da murmushi .

Dr maryam ƙoƙarin barin Wajen tayi Dan yadda taga ran Dr Ibrahim yake a ɓace ba kula ta zaiyiba, Babu ɓata lokaci kuwa ta juya zata tafi , bazata taji murya Na fito wa daga office din Dr Ibrahim ” ina zaki je ne ki dawo Dan Na ganki……..

“kada ki tafi Na ganki Dr Maryam”

Doctor Ibrahim ya faɗa,yayin da yake cire gilashin fuskar sa .

Juyawa tayi ta shiga office ɗin ,Dan tasan ya Riga da ya ganta “Dr ya akayi akan Ina nan wajen ” ta fada tana tsaye Dan har yanzu Bai bata damar Zama ba .

“Dr Maryam Kenan, kina tunanin Akwai Inda zakiji ne kuma nima Ina wajen Na kasa gane ki ,lalai kam” Yakai karshen zancen yana nuna mata waje alamun ta zauna.

Wuri ta samu ta zauna kamar yadda ya umarce ta sannan, cikin sanyayar murya tace ” Amma Dr, ya akayi kake gane Ni idan Ina waje wannan abun yana bani mamaki”.

Juyawa yayi Inda ya fuskance ta suna kallon juna sannan yace “Dr Maryam Kenan, kina so kisan tayaya nake ganewa idan kina waje Kenan?” ya tambaye ta.

” Ehh doctor ” ta fada a takaice.

“Dr Maryam Kenan kamshin turaren ki Na Jasmine yana daya daga cikin abunda yake sakawa Ina gane ki amma nima kaina bansan sauran ba “.

“Dr yanzu shekaru sun jaa ba sosai amma har yanzu baka manta ba “.

“Dr Maryam idan kinji ance an manta Abu tohm gaskiya zan iya cewa ba’a dauki abunda mahimmanci ba Dr ” Shafa gefen fuskar sa yayi sannan ya cigaba da cewa ” Maryam in..”.

Saurin katse shi tayi da ” sir dama patient NO:212 ne Ake bukatar yi masa surgery shine Na kawu maka paper kayi singing” takai karshen zancen da Mika masa takaddar hannun ta.

Amsa yayi yana cewa “okay kiyi ma Dr eysha da kuma Dr Aryan magana akan wannan surgery din Dan kinsan heart transfer saidai kwararrun likitoci”.

“okay sir ” ta faɗa yayin da take barin office din ,har takai bakin ƙofa kuma sai ta juyo ” Dr idan ba damuwa Ina so muyi wata magana dakai Dan Allah”.

“okay go ahead” ya faɗa a taƙaice.

“Dr dama magana ce akan Zahra ” hannuwanta biyu ta haɗa Alamun magiya “please sir please,Accept her request” takai karshen zancen tana Zama akan kujerar da ya nuna mata ,sannan ta cigaba da “Dr karamar yariyace har yanzu nasan Dr Ibrahim yana amfani da ita A Matsayin Karen farauta , Amma babu yadda za’ayi A janyo ta A jiki sai ka nuna mata so da kyauna Dr”.

“abunda kike so Kenan tohm zanyi , nace Zanyi koba shine kike so ba ” ya fada rai aɓace .

“Dr ba haka bane amma indai zaka amince Ni banida damuwa,sabuda babu abinda nake so fiye da farincikin ƴata Dr”.

“ke kika ɗauke ta a Matsayin ƴa amma ita ai bata ɗauke ki a Matsayin mahaifiya ba .

Da ƙyar ta shawo kansa ya yadda sannan ta tafi.

Doctor Yusuf ne tare da Dr meera tsaye a gaban wani patient Wanda ya gama Jin jiki sannan aka kawu sa asibitin, da ƙyar suka shawu kan ciwon nasa har suka samu nasarar yi masa Allurar bacci .

” Nurse Amira ” Dr Yusuf ya fada yayin da yake daidaita ƙarin ruwan dake jikin patient din .

Amsawa tayi cikin girmamawa ” na’am , Dr Yusuf ” ta fada tana maida hankalin ta gareshi.

Juyowa yayi yayin da yake hada Allurar da zaiyi ma patient din ” wannan matar taji jiki sosai gaskiya,abinda ya kamata ki kula da ita sosai kinji “.

” okay sir inshallah zan kula da ita har ta samu lafiya” .

Bayan sun gama duba patient din ,suna shirin tafiya shida doctor meera sai ga doctor umar , doctor abdulmajid tareda Aryan sunzo wajen ,

Fuskar doctor Yusuf kallon doctor Aryan yake fuskar sa ɗauke da farincikin ganin aminin nasa , matsawa yayi ya rungume shi ,shima doctor Aryan din murnar ce a fuskar sa , rungume junan su sukayi kowa cikin su yana farinciki ,

Doctor Yusuf ne ya juya ya kalli doctor umar tareda doctor abdulmajid yana cewa ” ya akayi Baku fada man ba ?.

Dariya doctor umar yayi yana cewa ” haba abokina ai idan Na fada maka abun ya tashi daga surprise ai “.

” kaima ka fada masa yoo tayaya ma za’ayi hakan ma “.

Gabadaya daya dariya sukayi a lokaci daya 

Doctor Meera ce ta fara magana ” ku tsaya mana gaba daya yan team dinmu sunan amma Banda *Doctor EYSHA*

Gaskiya ya kamata ace mun Nemo ta ” kafin takai karshen zancen har Na zo wajen, kuwa maida hankalin sa yayi akaina ,lokaci daya gabadaya suka ce ” yar halak kinƙi ambato “.

Kallon su nayi fuska ta dauke da Alamar tambaya( ?) “gulma ta kukeyi ko ?” .

“Ehh gulmar ki Ake sai Akayi yaya ?” doctor Aryan ya fada yana kallo Na .

” kaga Ni yanzu ba wannan ya kawu ne ba , abin ɗaure gashi Na ne yasa nazo ,kuma nasan yana wajen ka Dan Allah ka bani ” Na faɗa Ina marairaice fuska .

” hhhhh yariya nifa babu abinda zan baki sai kinyi kuka sannan” ya faɗa yayin da yake saka hannun sa A aljihu Dan ya dauko mani ,amma ya duba bai gani ba sai haƙura yayi ya fiddo hannun sannan yace ” EYSHA wlh Kinga ban zo dashi ba amma gobe inshallahu zan kawo maki shi”.

” nidai gaskiya ban yadda ba, nasan hanani abuna kawai kayi ” Na fada fuska a ɗaure.

“kinga idan baki yadda ba zo ki duba da kanki ” ya faɗa yana daga hannuwan sa sama .

Babu musu kuwa Na saka hannuwana cikin aljihun Dan Na dauko ,Ina saka hannuna nayi karo da ……….

Fanan A.A??????

About AIS

Check Also

DOCTOR EYSHA CHAPTER 4 BY FANAN_A.A

DOCTOR EYSHA CHAPTER 4 BY FANAN_A.A Www.bankinhausanovels.com.ng  Wasu zafafan hawaye ne suka Fara Ambaliya a fuska …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *