AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 9 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 9 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Hafsat wadda duk ta bi ta tsorace da abubuwan da yake yi masu kama da na sabon kamu, ta ce, Aa, ban sani ba.

Har na soma hango ki kina breastfeeding Hafsat. Oh me! Ya rungume ta.

Hafsat wadda ta ji zancen a baibai ba ta fahimce shi sosai ba. Rokonsa ta ke ya gaya mata abin da yake nufi da hakan amma ya ki, hanyar faranta ran junansu yake bi kala-kala, lungu da sako kusufa-kusufa. Ranar yau ta kasance cikin jerin ranakun farin cikinsa a rayuwa, ba zai taba mantawa da ita ba. Its a SECOND day in history bayan ranar dawowar ta cikin rayuwarsa. Abin da ya ce mata kawai kenan. A karshe da suka koma cikin consciousness ya damka mata passport dinta da tikitinta. Muryarsa abin tausayi ya ce.

 Na amsa wa Daddy da Mammah za ki koma gobe. Hafsat na ba ki amanar kanki da kanki da ta abin da ke cikinki. Ban yarda ki jigata shi saboda bokon nan naki ba. Ni ko third class ki ka fiddo in dai BABY na zai zo cikin koshin lafiya Allah ya sanya albarka. Aclass of degree ba shi ne matsayin ilmi ko kokarin dalibi ba. It determines the condition da dalibin yake ciki a yayin karatun, duk da kokarin ma yana taka muhimmiyar  rawa. Iwill come soon… and I will miss you soon. Ya kwantar da kai a kafadunta. Yayi shiru.

Hafsat is speechless. Cikin tarin zantukansa masu kama da wasiyyar bankwana sentencedaya ta tsaya mata a rai, Amanar kanki da ta abin da ke cikinki. Which means ……an gaya wa Yaya Azeez she is pregnant a asibiti, dalilin farin cikinsa haka kenan. To shi cikin haka ake samunsa cikin dan lokaci kalilan? Kamar kiftawar ido? Kamar a majigi? Shekara daya da doriya ba a same shi ba sai yanzu? Zancen zucinta ya subuce ya fito fili.

Dariya sosai ta baiwa Abdulazeez ya dago kansa daga kafadunta ya dube ta cikin ido da idanunsa da ke sanyaya mata zuciya.

Saboda wancan lokacin its a crime in Nigeria. Yanzu kuwa baa Nigeria muke ba,it is allowed here in the U.S.

Ita ma sai abin ya ba ta dariya, ta tuno lokacin da ta zauna tana zancen da shi babu ko kunya. Kai ta rafka wauta a baya, kada Allah ya maimaita. A daren ya hada mata kayanta da tsarabar da ta dade tana jida. Har Baba Azumi ta samu dogayen riguna biyu masu kyau na masu jini a jika. A daren gabadayansa cikinsu ba wanda ya runtsa…, The farewell is very very emotional (bankwanan ma taba zuciya ne). Soyayyar cikinsa is an extraordinary (babu kamarta a tarihin rayuwarsu). Alkawururruka suke daukarwa juna kamar ba za su kara haduwa ba sai a Darussalam. Duk da bakin Hafsat ya mutu, tun daga jin labarin ta kusan zama UWA, uwar ma ta jikokin Hamzah Atiku da Maryam Dakata; mutane mafiya darajar girma da kima a gare ta fiye da kowa a duniya in ka cire wadanda suka yi silar zuwanta duniya. Shin ko adadi nawa za ta so wannan Dan? Mai cin tudun soyayya uku a zuciyarta???

Na farko na kasancewarsa Dan da ya fito daga mahaifarta, na biyu na kasancewarsa daga jinin jikin ABDULAZEEZ Hamzah Atiku; wani kwayan mutum guda daya da ta ke so da dukkan ruhi da zuciyarta da soyayyah marar misali. Na uku kasancewarshi jikan Mammah. Jikan ma na farko da bata taba dauka ba sai a kansa.

Sai da aka sanar cewa za a rufe jirgin sannan Abdulazeez ya raba Hafsat da jikinsa. Suna daga tsaye ya kowa ya shige ya barta. Ita ce karshen shiga ta zauna a (first class seat) dinta yadda tazo daga barin dama ta barshi tsaye ya zuba hannayenshi cikin aljihun bakin wandonNordstrom da ke jikinsa da farar T/shirt Tommy Hilfiger. Har ta bace wa ganinsa murmushi ne a kan fatar bakinsa, image din wannan yanayin da wannan ranar ya zauna mata a zuciya. Lokacin da jirgi ya karci kasa ya lula sama cikin hazo sai ta sa hannayenta biyu ta dafe cikinta. Wata amana da ta karba da hannu bibbiyu ta ke rokon Allah ya taya ta rikonta. Ta zame musu sanyin idaniya dukkaninsu, kuma nauin farin ciki ga iyayensu.

                         ******

Hafsat ta sauka lafiya a Abuja. Kwananta biyu ta huta gajiya, sannan ta koma makaranta. Ta tarar Haleem ya koma makaranta, Ismael da Usman na shirin tafiya hidimar kasa. Baba Azumi jikin girma ya motsa ba ta da lafiya, yarta Harira ta zo daga Sokoto wadda ta zauna da ita a gidanta tana amarya tana taya Mammah kula da ita, Mammah ta yi sabuwar mai aiki Jummai daga Minna ta ke. Ita da Harira suke zaune da Mammah kafin Harira ta koma Sokoto, saboda ta baro mijinta da yaranta. Jummai na da kirki sosai da faram-faram nan da nan suka saba. Ta ji dadin ganin Harira matuqa, Mammah ta gaya mata kullum sai ta yi zancenta. Nan da nan suka taru suka debe mata kewar Abdulazeez kasancewar daga Harira har Jummai masu son barkwanci ne na a buga a jarida. 

Mammah kula ta ke da Hafsat da mugun cin abincinta yadda ya kamata da duk abin da mace mai juna biyu ke bukata. Salisu ke kai ta makaranta ya dauko ta, da daddare in za ta kwanta sai ta girke mata (food flask) a gefen gadonta saboda tashinta cikin dare cin abinci. Bayan wannan ba ta fuskanatar wata matsala, ko kwana biyu ba ta yi ba daga Jummai har Harira sun gane matsalar Hafsat din duk da Mammah bata fada musu ba. Sai suka kara zage damtse wajen taya ta kulawa da surukuwarta ko kofi ba sa bari ta wanke. 

Baba Azumi na jin jiki sosai, ciwon kafa da ciwon baya daga karshe sai kwantar da ita aka yi a asibiti gabadaya. Kullum da daddare suna midnight call dinsu don lokacin ne kadai Abdulazeez yake free, komai ta yi a rana sai ta sanar da shi, shi ma duk abin da yake ciki sai ta ji. Harira ce ta ke kwana da mahaifiyarta Azumi, Mammah da Jummai na jigilar abinci, Hafsat ma kullum ta taso makaranta can ta ke fara biyawa sai dare suke komawa gida tare da Mammah. Asibitin yana da kyau sosai wanda iyalan gidan ke zuwa ne (Diff hospital) Hafsat ma anan take ganin likita, tana samun kulawa sosai. Kullum sai Hafsat ta gaya wa Abdulazeez damuwarta a kan ciwon uwar goyonta, ko tafiya ba ta iya yikuma Mammah ba ta bari ta kwana. Hakuri yake bata, ya ce. Ke ma patient ce. Insha Allah za ta tashi, girma ne.

Washegari Mammah ta tura Salisu da babbar mota har Sokoto ya debo yayan Azumi gabadaya su zo su duba ta, suka kuwa taho kwansu da kwarkwatarsu da yayansu sai da Salisu ya biya kudin motar haya bus guda daya suka taho tare, saboda motar ta gagara kwashe su. Baba Azumi sai budar ido ta yi ta ga yayanta maza da matan zagaye da gadonta kamar a mafarki. Sai da ta yi kuka don dadi, ta yi ta yi wa hajiya Maryam adduar alkhairi.

A tsakiyarsu ta hango Hafsat rungume da daya daga cikin jikokinta ta saje a cikinsu sai hira suke yi. Hawaye ya kara zubo mata ta ce a kirawo mata ita, hannunta ta kama tana ta yi mata addua tana fadin Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya ba ki dan albarka irinki. Allah ya zaunar da ku lafiya ke da mijinki. Allah ya cika miki burikanki na duniya da lahira. Tabbas ke yar halak ce wadda ta san halacci, kin so ni kamar ni na haife ki, mijinki ya kaunace ni kamar ni na haife shi. Allah ya hada kawunnanku ku rayu tare, rayuwa mai tsayi da albarka.

Duk dakin amsawa suke yi da, Ameen-ameen. Ban da Hafsat da haka kawai jikinta ya yi sanyi da wannan doguwar addua da Baba Azumi ke kwarara mata a yau a bainar jamaa. Zamewa ta yi ta koma can karshen dakin ta zauna kanta yana sarawa, don ko ya ya ta yi doguwar tsayuwa sai ta ji hajijiya da ciwon kai. Hirar ta koma tsakanin Azumi da yayanta da jikokinta har Mammah ta iso kawo abincin dare. Ta kuma ce da su su yi sallama ta tafi da su gida su huta gajiyar hanya, su ci abinci.

A guest house dinsu aka sauke su duka, Jummai da Harira na ta shigar musu da abinci na alfarma. Suka kwana cikin jinjina mutunci irin na Maryam Dakata. Uwarsu kam ta zauna da mutanen kirki babu irin alherin da ba ta samu a jikinsu ba, su ma kansu sun huta da su ba wanda bai ci arzikinsu ba. Da safe bayan sun karya kumallo kowa ya yi wanka aka yi shirin komawa asibiti. Sai aka bugo wa Hajiya Maryam waya, Azumi rai ya yi halinsa da asubahin ranar.

Iyakar kidimewa Maryam ta rude, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai ta ke ambata, wayar ta sulale ta fadi daga hannunta. Ta zame ta zauna a gefen gadonta tana ci gaba da salati da dayanta Allah. Ina za ta nemo karfin gwiwar kallon idanun yayan Azumi da jikokinta ta gaya musu gushewarta a doron kasa? Ga Hafsat mai yaron ciki… kawai sai ta fashe da kuka.

A haka Jummai ta same ta, jinta shiru-shiru kowa ya shirya ita ake jira a tafi asibiti. Hafsat ba ta nan tana makaranta. Jummai ta samu Mammah tana gursheken kuka. Tuni jikinta ya ba ta, Mammah ta ce ta hada wayar da ta tarwatse ta miqo mata. Kuka ta ke hawaye sun hade da majina. Jummai ta yi yadda ta ce, ta kira Daddy shi a lokacin ya isa office. Ta gaya amsa, shi da yake namiji ne cewa ya yi, ga shi nan zuwa. Asibitin ya nufa ya karbo gawar don yau Harira ma ba ta kwana wajenta ba, ta ga yan uwa kuma jikin nata ya fi na kowacce rana samun sauqi. Sai ta biyo su. Da nufin a dawo tare gabadaya da safe. 

Suna tsaitsaye a harabar gidan duk sun sha wanka sun ci kwalliya, masu goyo sun goya yayansu sai gani suka yi get ya bude, motar asibiti zungureriya ta shigo. Kofofinta suka bude, malaman asibiti biyu suka sauko da gawar a kan gado. Babban danta Yushau shi ne mai karfin halin karasawa ya bude fuskarta da aka lullube. Ai kuwa ya fasa kuka wanda ya tabbatar wa sauran yan uwansa da zatonsu. Daidai lokacin da motar Daddy ta biyo baya, sannan ta su Ismael.

Gida ya rikice ta koina hatta Ismael da Usman kuka suke yi. Yushau ya matsa kusa da Daddy ya yi kuka ya koshi, Daddy na bashi baki, ya roke shi suna so su tafi da Azumi gida Sokoto su yi janaizarta a can. Daddy bai musa ba, nan ya shirya motoci har da shi da yayansa suka dauki hanyar Sokoto, Mammah ta ce za ta biyo bayansu daga baya saboda Hafsat ba kowa a gidan.

A kan hanyarsu ta dawowa gida ta ga Salisu ya dauki hanyar gida maimakon ta asibiti, ta ce, Salisu mu fara zuwa asibiti in ga Baba tukun.

Bai juyo ba ya ce, An sallame ta. Kamar yadda Mama ta tsara masa.

Hajiya Maryam kokari ta yi sosai ta danne alhinin da ta ke ciki, amma ba ta yarda sun yi tsayuwar minti biyar tare ba. Ta tambaye ta Salisu ya ce an sallame ta, kuma na zo gida ban gansu ba daga ita har bakin. Ba tare da ta dube ta ba, ta ce, Sun wuce gida Sokoto da ita, sun ce a can za su karasa jinyarta tunda ta samu sauki. Ni ma gobe zan bi su in kara tabbatar da samun saukin nata.

Ta ce, Mu tafi tare Mommah, na san ba za ki wuce kwana daya ba.

Kai ta girgiza, Kwana uku zan yi, ki zauna saboda makaranta, ko in kai ki gidan Hajiya Halima ko gidan Kawunku?

Ta girgiza kai don ba ta son harkar gidan Anty Zuwaira ba tun yau ba. Zan yi zamana ni kadai, ni da ba wuni nake a gidan ba?

Mammah ta ce, ba zan iya barinki ke kadai ba zan dauko Saadiyya yar hajiya Halima ta taya ki zama.

Ba tare da damuwa ba ta amince.

A  daren direban Hajiya Halima ya kawo Saadiyya, budurwa ce ita ma a Nile ta ke karatu. Da suka gane yan makaranta daya ne, sai suka saki jiki da juna suke ta hirarsu. Mammah ta jaddadawa Saadiyyah yadda za ta kula da abincin Hafsat ita abin har kunya  yake ba ta, yadda Mammah ke treating dinta ko a gaban waye kamar wata karamar yarinya.

Ta ce, Kai Mommah ita kadai za ta dinga girkin? Tunda mu biyu ne mu yi tare mana.

Ta ce, Ban yarda ba, kin ji na gaya miki. Saadiyyah ko ferar dankali kada ki bata.

Tana dariya ta ce, Toh Mammah.

Hafsat akwai shagwaba, Mammarta ta daure mata kugun yinta.

Da safe Salisu ya kama hanyar airport da Mammah, bayan sun sauke su Hafsat a makaranta, suka wuce zuwa Sokoto.

              *** ****

Bayan sadakar ukun Azumi mutanen gidan suka dawo gabadaya duk jikkunansu a sanyaye cike da kewar tsohuwa Azumi. Abdulazeez ya san da rasuwar, shi ma kuma ya fi kowa jin dadin hukuncin da Mammah ta dauka na rashin sanar da Hafsat. Adduar da ba ta yi mata ba ya hada yake yi musu su biyu. Har Azumi ta yi arbain da rasuwa Hafsat ba ta sani ba. Ranar sadakar arbain Daddy ya aika wa iyalinta kudi masu yawa a sayi duk abin da ya kamata a yi sadaka, da ma kuma sun tafi da komai nata da ke gidan. Rayuwa kenan, Azumi kamar ba a yi ta ba a gidan tsohon Ambassador Hamza Atiku. Allah ka sa mu cika da kyau da imani, mu gama lafiya da kowa, amin.

                  ******

Hafsat ta ci gaba da rainon cikinta karkashin kulawar uwa/suruka ta gari Hajiya Maryam Hamza Atiku. A gefe tana ci gaba da karatunta cike da kwazo. Semester ta kare suka yi jarrabawa amma hutun na sati biyu kacal. Wannan karon ko Yola ba ta je ba balle ace America, Mammah ta ce ita da hawa jirgi sai ta haihu kuma. Ga hutun daman ba yawa, shi ma a nasa bangaren da ya gama semester din farko ya so ya zo gida, amma yana da dissertation da zai rubuta a cikin hutun, dole ya hakura tunda kullum suna tare a waya da daddare. Sai da cikin Hafsat ya cika watanni bakwai Mammah ta gaya mata gaskiyar rasuwar Babarta Azumi. Hafsat ta sha kuka kamar ranta zai fita, kamar a lokacin aka yi mutuwar, hatta Abdulazeez ta yi fushi da shi kan shi ma bai gaya mata ba, Mammah ma an yi fushi da ita na kwana biyu tana ta lallashi tana bada hakuri. Abdulazeez ya ce.

 We want to save lives, wasu na tafiya wasu na zuwa! Haka rayuwar ta gada, take heart sweetheart.

                   ******

Ranar wata litinin Hafsat ta sankato katon danta a asibitin (DIFF) mai tsananin kama da ubansa. Lokacin watanni biyu suka rage wa Abdulazeez ya gama L.LM dinsa. Fadin farin cikin da wannan family suka samu kansu a ciki ba daga su ba, ba daga mutanen Yola ba, ba zai misaltu ba. Zo ki hango jika a hannun tsohon Ambassador Dr. Hamza Atiku Dakata yana ta tofe shi da addua ya hana Maryam dauka wai in ta ga ya fi shi kyau sakinshi za ta yi. Gefe ta koma tana bai wa Hafsat tea a baki tana fadin.

 Ka yi ka gama Daddy, ga sabon jini ba abin da zan yi da tsoho mai furfura.

Duk da Hafsat cikin hajijiyar haihuwa ta ke sai da ta yi wa maganarsu dariya a fili. Daddy ya haskawa Baby camera da galleliyar wayarshi ya dana masa hoto ya tura wa ubansa. Wannan ya faru tun a asibiti kafin su dawo gida. Kwanansu hudu suka tattaro bakidaya suka yo Kano inda Mammah ta ce a can za a yi taron suna.

Adda Hafsatu ta girka garwa a murhu ta soma wanke Hafsat da ganyen dalbejiya da runhu. Babyn ma ita ta ke masa wanka safe da yamma. A dakin Addar suke kwana ita da Mammah suna gado ita da jaririnta, Mammah na bisa carpet ta jefa filo bisa. Duk kukan darensa ba ya hana ta barcinta domin kuwa sun san yadda suke yi masa ya yi shiru. Azababben jego Addah ke mata har kuka ta ke yi in ana wankan nan na runhu da gashi da zaman ruwan zafi.

Ana i-gobe suna gidan ya kacame da shirye-shiryen abincin gobe, duk kannen Hajiya Maryam sun zo da yayansu gidan ba masaka tsinke, Aunty Mariya ta goye babyn ta rufe shi ta fita da shi dakin da suke.  Hafsat ta fito daga wankan yamma ta shirya cikin atamfa (Vlisco) ruwan goro da ratsin blue ta daura dankwalin sama-sama ta kwanta tana hutawa. Tunanin Abdulazeez ta ke yi, rabonta da shi tun ana i-gobe za ta haihu, zafin nakuda ya sa ba ta tuna da wayarta ba sai bayan ta haihu. Da aka sallamo su ta neme ta a dakinta ta rasa har suka taho Kano ba ta tambayi Mammah ba saboda kunya, ta san da ta ji tana cigiyar waya ta san wanda ta ke so ta kira shi ya sa ta biyo gida (fillanci) ta yi shiru kawai.

Tana kwance tana wannan tunanin ta ji iskar da ta ke shaka tana sauyawa da wani atmosphere mai dadi da kwantar da zuciya;the familiar scent of creed aventus, idan mafarki ta ke yi tana rokon Allah kada ya tada ita daga wannan daddadan mafarki. Tattausan hannunsa ta ji cikin nata ya matsa shi sosai yatsunsa sarkafe da nata. A hankali ta ke bude idonta don tsoro ta ke ji kada ta bude idon gabadaya ta ga ba haka ba, gradually idanuwan suka washe a dakin hasken kwan fitila ya haska mata shi sosai. The last person da ba ta yi tsammanin gani nan kusa ba. Taimaka mata ya yi ta mike daga kwanciyar, abinka da danyen jiki koina ya yi taushi tubus ya yi wani irin fresh kamar da ka taba ta jini zai yi tsartuwa, ta zama kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba. Gefenta ya dawo ya zauna kafafunsa na zube a kasa ya ciccibo ta gabadayanta ya aza bisa cinyoyinsa. Kallonta yake cikin ido da wani irin yanayi cikin kwayar idonsa. Kunya ta kamata sai kokarin guduwa ta ke yi, sai ji ta yi ya fara kissing dinta gabagadi ta inda duk ya samu a matukar dokance. Aunty Mariya da ta shigo kawo yaro ta yi kyakkyawan gani ai ba shiri ta juya sai ta ci uban tuntube da robar wankan baby da ba a dauke ba saura kadan ta fadi, ta dafe babyn da ke bayanta da iyakacin karfinta. Da sauri Hafsat ta dire kasa, shi kuma ya hau yi mata.

 Sannu Aunty Mariya, dan waye a bayanki?

Wata uwar harara ta zuba masa, ta ce, Danka ne! Ina ma na fadi mun fadi ni da shi in ga ta karshen soyayya a cikin mutane?

Da ya yi wata zabura sai ga shi a gabanta, What? Jaririn kwana shiddan ki ke goyawa? Idan kafarsa ta lankwashe fa? Sauko shi, maza sauko shi.

Ya soma kokarin kwanto goyon daga jikinta da kansa. Kunya ta lullube Hafsat shaf! Ya manta da wa yake magana, kanwar mahaifiyarsa ce ba yar mace da dan namiji suke ba balle ya ce abokiyar wasansa ce. Shi yake abin kunyan, amma ita ke jin kunyar a jikinta. Mariya ta kwance masa dansa tana harararsa bai ko san tana yi ba ya tafi duniyar kallon kyautar da Allah ya yi masa kamar ya yi khaki ya tofar. Aunty Mariya ta fice tana ta fadace-fadace wai Abdulazeez ya yi mata rashin kunya saboda ta goya dansa.

Zo ki gani Hafsat yana tsotson bakinsa yana murmushi, may be he is saying welcome to me.

   Tuntsirewa ta yi da dariya.

Ai tun jiya yake tambayarka.

Da gaske? Shi ne ba ki min waya kin gaya min ba?

Abin sai ya koma bai wa Hafsat tausayi, saboda shi tsakaninsa da Allah ya yarda. Fathers love. Ta fada a hankali har ya shiga kunnuwansa.

Which is like no other. Ya ba ta amsa, sannan ya sanya hannun hagunsa ya janyo ta barin hagunsa ya hada su ita da jaririn ya rungume ya lumshe idanunsa.

Allah ya yi muku albarka, Allah ya taya ni kulawa da ku. Idan bana nan Allah ya kula min da ku. Allah ya sa mahaddacin Alqurani ne, sanyin idaniya ga iyayensa da kakanninsa, abin alfahari ga alummah….

Hafsat na ta amsawa da Ameen-ameen. Cikin jin kunya.

Karkata kunnensa ya yi zuwa bakinsa yana masa kalmar shahada, ya yi masa khutbah da sunan da ba ta sani ba. Ya ciro dabinon da ya yo guzuri na (ajwa) daga aljihunsa ya tauna ya sanya masa a baki, yaro ya kama lashe baki, cike da annashuwa ya ce, Hafsat zo ki gani, ya san zaki.

Ta waiwaya ta sake waiwayawa bakin kofa da window. Yaya Azeez, don Allah ka bari kada a jiyo mu, za a ce kana rashin kunya, ko ba ka ji me Aunty Mariya ta fita tana fada dazun ba?

Wata banzar harara ya yi mata, ya ce, To hell with the kunyar, in samu Dan kaina na farko ba zan gode wa Allah ba? Ba zan yi farin ciki ba? Saboda kada ace banida kunya?

Sassauta murya ta yi cikin lallashi, Ba haka nake nufi ba, nufina ka boye kada ka bari a ji sai in kuna ku biyu kai da shi. Nan kuwa gidan iyaye ne kowa na iya ji.

Babban yatsansa ya sa na tsakiya da na farko ya dalle mata baki, ta dafe bakinta don azaba nan da nan ya kumbura. Idanunta sai da suka yi ja.

Ya ce, Gobe ki kara gaya mini traditional folkloresirin wadannan goya shi zan yi in fita tsakar gida kunyar ta makanta ki.

Ta ja baya tana kumburi dafe dda bakinta, bata kara magana ba don lebenta ya yi mata nauyi sai ga Adda Hafsatu ta shigo kawo mata gasasshen nama sai tiriri yake ya ji albasa da yajin daddawa, ta mika mata, Cinye maza kafin a kwashe tuwon.

Ta kalli jaririn da yake ta tsotson baki da hannu, ta ce. Shin yaushe rabonki da ba shi abinci?

Zumburo kumburarren bakinta ta yi, Adda wallahi da zafi, da karfi yake zukowa sai na yi hawaye.

Adda ta dube shi sai juya yaron yake a hannunsa yana kare masa kallo kamar bazai daina ba. Kai bata shi ta ba shi abincinsa, tun azahar rabon da ta shayar da shi, yaro mai hakuri amma sai kin kure hakurinsa, yau kwana shidda ana abu daya, haka za ki daure nan da kwana goma zai daina zafin.

Kallon Adda ya yi cikin mamaki. Nonon ne sai an roke ta take bayarwa?

Addah Hafsatu ta ce Wallahi haka ake fama da ita kullum.

Idanuwa ya watso mata.

Mugunta ki ka koma?

Ta kawar da kai nan ya yi nasarar ganin yadda bakinta ya kumbura daga dalli daya. Dariya ta kama shi amma ya dake, Adda kin ga matso ki rike min yaron nan, danneta zan yi wallahi sai ya sha ya koshi.

Adda kuwa ta karbi yaro ganin ya mike ya nufo ta da karfi ta ce.

 Adda kawo shi!.

Ta yi dariya ta dora mata shi a cinya, juya masa baya ta yi ta janyo katon hijabi suka shige ciki ita da jaririn, ta bayanta ya leka, Adda za ta toshe masa hanci fa?

Adda ta harare shi, ta ce, Abin da ka yi wa Mariya za ka yi min ni ma? To ta toshe din, ko ka taya ta nakudarsa?

Da sauri ya tare ta tun kafin ta kai ga rufe baki. Amma ba don ni ba ai da ba a samu cikinsa ba…

Salati Hafsat ta saki daga cikin hijabinta, Addah ta tattara kwanuka ta bar dakin kunya kamar ta nitse. Mariya ba karya ta ke ba, Abdulazeez haihuwa ta sa ya zama fitsararre.

Tana fita ya sassauta murya.

Don Allah, don Annabi ki cire hijabin nan in ganku, Hafsat don Allah. Its something Im always dreaming of tun dawowarki.

Kamar za ta yi kuka ta ce Idan ka takura ni yin haka a gidan nan ka shiga hakkina Yaya Azeez.

To shi ke nan na hakura, amma in mun koma gidanmu ba za ki dinga rufewa ba ko?

Shiru ta yi ta kyale shi, inda Allah ya cece ta shi ne isowar mutanen Jimeta da aka zo aka fada wadanda suka wuni a hanya, dole ya tashi ya bar dakin ba don ransa ya so ba don sun soma tuttudowa dakin.

An yi suna na gani na fada a washegari a gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata. Fulanin Jimeta sun hade da kanawan Dabo. Tafe suke da motocin gara mai ban mamaki ta aure daban, ta haihuwa daban har da manyan bajimai da ransu guda biyar a motar shanu. Aka dinga saukewa a tsakar gidan don dakin da Inna Hafsatu ta ce a zuba ya cika. Gidan suna sai ya koma gidan wani gagarumin biki don su kam kamar yanzu suke ji sun zo auren Hafsat. Baffa Atiku fada ya hau yi a kan garar nan a cewarsa an riga an wuce gurin kuma su Hafsat ba surukarsu ba ce yarsu ce. Daada ta ce sun san da hakan su ma ba su ce yarsu ba ce, abin da alada ta gadar ne suke son a yi musu alfarma su yi ko yaya ne. Shi kansa Abdulazeez ya sha bandiran shaddoji manya-manya, hatta Daddy da Mammah nasu daban, jariri akwati biyu fal da kayan sawa masu kyau da tsada, haka mai jego akwati guda na turamen zannuwa da lesuka. Kakanni ma ba a barsu a baya ba. 

An ce wai ko kogi ba ya kin yayyafi wannan gaara ta yi wa iyalin Dakata dadi duk da ba su taba kawo hakan a ransu ba. Na Baffa Atiku daban, na Adda Hafsatu daban. Aunty Zuwaira ta zo suna don Uncle Abdulkarim ya bude mata wuta wannan karon kuma a kan idonta aka yi komai. Tana zaune a gefen gadon da Hafsat ta ke lokacin da Ibrahima autan su Mammah ya shigo ya ce mahaifin Hafsat zai shigo ganin jariri, sosai ta muskuta ta baza ido a kofa.

 Prof. Bashar Mai-Jamaa Numan ya daga labulen dakin da sallama, zaratan matasan yayansa uku na biye da shi. Kwarjini da kamala da tantagaryar boko ya dallare idanunta. Ita da kanta ta dauki jaririn ta kai masa a kujerar da ya zauna daga can farkon dakin. Hafsat baki ya ki rufo, ga kunya tana ji wai ita ce ta haihu Abba ya dau jika. Imaamu na ta tsokanarta wai ta zama Maama, Abdurrahman ya ce jariri bai dauko su ba da ya fi haka kyau. Aunty Zuwaira yau har da cewa da Abdurrahman.

 A gabana? Ai kuwa Abdulazeez ya fi Addah kyau, fari kawai ta fi shi.

Hafsat na kallonta a ranta tana mamakinta. Tunda ta taso ta san Aunty Zuwaira, ba ta taba yi mata kallon arziki ba, kalma mai dadi bata taba shiga tsakaninsu ba. Iyakaci ta gaisheta ta amsa a wulakance. Yau ita ce da yin wasa da dariya da yan uwanta don ta ga idon mahaifi. (Ya Allah ka barmu da iyayenmu ba don halinmu ba, ka kara musu tsawon rai da lafiya. Wadanda nasu suka rigaye mu Allah Ka sabunta rahma a gare su, ka jikansu ka yi musu gafara kama Rabbayaany saghirah).

Dr. Bashar ya dago ido ya dubi yarsa Hafsah cike da kauna.

 Kina ina ki ka bari Abdulazeez ya kwashe komai shikadai bai sammana ko kadan ba?

Dariya ta yi ta rufe fuska, ya karanto adduoi ya tofawa baby. A bakinsa ne ma ta ji sunan yaro Abubakar-Sadiq (Khalipha) sunan da mahaifinsa ya zaba masa kenan.

Suna da kwana biyu yan Jimeta suka koma, yan Abuja suka soma nasu shirin. Adda Hafsatu ta yi tsalle ta dire ta ce nan za a bar mata masu jego ba za a lalata mata aiki ba. Mammah ta je tana mata wanka da ruwan (gass-cooker). Su tafi in ta yi arbain su zo su dauka. Mammah ba ta yi musu ba don ba ta jayayya da mahaifiyarta a kan komai, kuma ta yarda sai sun fi samun kulawa a nan fiye da wajenta.

Abdulazeez dama kwana uku zai yi ya koma U.S sai nan da watanni biyu zai dawo gabadaya.

A daren da su Mammah ke shirin komawa Abuja a washegari, shi ma a daren yake nasa shirin komawar. Jirgin da zai bi na asubah ne daga Kano, zai yi transit a Ethiopia. A dakin Uncle Idris na da yake kwana a soron gidan  na farko. Wanda shi yanzu gidansa yana nan cikin gidajen likitoci na asibitin Malam, iyalinsa da su aka yi sunan Khalipha.

Mammah da kannenta mata hudu Luba, Mariya, Furairah, Murja da Hafsat dake can saman gado tana shayar da jaririnta. Sun saka mahaifiyarsu a tsakiya ana hirar bankwana kasancewar gobe ita Mammah za ta koma Abuja ita da Jummai mai aikinta, Abdulkarim da iyalinsa sun koma tun jiya. A cikin hirar ne Mammah ta sako zancen da ya dade yana cinta a zuci, ya kuma fi karfin a yi shi a waya sai yau da Allah ya hada su ido da ido. Ta dubi mahaifiyarsu ta ce.

Addah!

Ta ce, Naam.

Ki tambayi Mariya da Luba shin ko Saima da Halima sun tsayar da mazajen aure ne?

Addah ta ce, Ai da kunnuwansu, kuma sun ji ki.

Mariya ta ce. Halima sarkin ruwan ido? Tana nan tana ruwan idon nata wai mijinta ma ba a haife shi ba. Ni abin da ya sa ban damu ba ganin bana ne ta kammala secondary tana da sauran lokaci a gaba, amma Babanta ya fi so ya yi mata aure.

Luba ta ce, Saima dai akwai wani yaro da ta ke so, sai dai bana jin auren nan zai yiwu?

About AIS

Check Also

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng  Ta ce, Mommah ita ce …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *