AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ta ce, Mommah ita ce ta yi covering dina duk abubuwan da suka wuce ni lokacin da na dawo daga Jimeta.

Madallah-madallah Mami Sada, Allah ya saka da khairan.

Daga nan suka yi sallama, sun ce ta zo su sauke ta, ta ce mijinta yana hanya, Mammah ta ce a ina suke zaune? Ta ce  a Kubwa.

Insha Allah watarana Hafsat za ta zo gidanki, Allah ya yi albarka.

Sosai Maami ta ji dadi, a yadda ta gansu high class haka ba ta zaci za su yi wannan saukin kan ba. Daga ganin Baban nasu ba karamin mutum ba ne. Ta fadi a zuciyarta.

Suna tafe a hanya Daddy ke tambayarta ya

jarrabawa? In ce ko ta rubutata da kyau? Murmushi ta yi, wannan jarrabawa ai sai taimakon Allah, in ta samo C she deserves a medal! Mammah ke gaya mata Haleem na zuwa gobe. A ranta ta ce, Wani na zuwa wani na tafiya, wanda Allah ya baiwa yaya da yawa nagartattu ya gama masa komai a rayuwa. Ko ba komai ta ji dadin albishir din zuwan Haleem din. Ta tabbata zai debe mata kewa, abokin kokawa, abokin wasan tseren keke, abokin kowacce dabdalar kuruciya.

Washegari Haleem Dakata ya iso, har da ita aka je filin jirgin saman Abuja dauko shi. Ya kara tsayi sosai, sai dai yaan nan da lange-langen jikinsa. A da tana ganin Usman ya fi kowa kama da Abdulazeez, ashe akwai wanda ya dame shi ya shanye cikin yayan gidan. Wannan har tsayuwarsa har tafiyarsa, har murmushinsa Abdulazeez Dakata ne. Yana saukowa daga jirgi ya cimmasu, babu Daddy tare da su yana office, su Ismael ya hau rungumewa, ya rungume Mammah har da kwanciya a kafadunta, ita ce ta ji kunya ta ture shi.

Ya ce, Mammah ki bar ni in ji duminki, wa ya yi dadewa irin tawa ba tare da ke ba?

Ta ce masa, Ka girma. You are no more a child now. You are Arch. HaleemDakata.

Lumshe ido ya yi, sannan ya iso ga Hafsat, Addar Mammah, an kara tsufa, kin haihu?

Harararsa ta yi, ta ce.Da na san abin da za ka yi min kenan da ban zo tarenka ba.

Yi hakuri, kada ku kai ni kotu, whereis he?

“I dont know!”. Ta sha kunu sosai ta zumburo masa baki. Dariya ya yi, ya ce, Mammah ina mijinta?

“In the U.S. Ta fada a gajarce, sannan suka rankaya suka nufi mota. Sai hira yake saki kamar rariya.

Anyi girke-girke na musamman don tarbar Haleem. A raayin Hajiya maryam ba ta da son yan aiki barkatai su cika mata gida. Tun tana amarya yar aiki daya ta ke dauka a cikin gida, sai maza na waje don kula da harabar gida da aike,guest house da sauransu. Sai ko maigadi, hatta wanki da guga dry-cleaning suke kaiwa duk don kada ta cika gida da hadimai. Tana da kwazo, juriya da himmar hidimtawa iyalinta. Da wuya a yi mata girkin mijinta da yayanta sai bisa lalurori irin wanda dan adamya gada, kamar rashin lafiya ko tafiya. 

A tasowar Hafsat-Suhaanah sai suka hada hannu musamman da suka dawo Nigeria inda Hafsat din bata zuwa makaranta. Ayyukan Baba Azumi sun fi karfi ga wanke-wanke da share-share, goge-goge da wankin bayan gida. Sai sauran hidimar kicin. A yanzu Azumi shekaru sun tura karfinta ya ragu sosai, tana so ta samu lokaci ta gaya mata ta samo mata wata cikin iyalinta mai kuruciya ba don ta sallame ta ba, sai don yanzu abubuwa da yawa nauyin shekaru ba ya barinta ta yi mata su yadda ya kamata. So throughout ranar saboda zuwan Haleem ta zama busy ba ta samu lokacin zama ita kadai ba balle tunani ya aure ta, kuma ba ta da paper, inda duk ta gifta don kawowa Haleem abin da yake bukata sai ya tsokane ta, kiranta yake Senior Aunt. Shi yanzu ya daina kokawa da ita. Shes lookingolder and older saboda aure. Mammah kadai ke tare mata, ta ce su din ma watanni uku ta ba su su fiddo matan aure, ban da shi tunda bai gama ba. Ismael sai ya shafo kai ya ce,

 Mammah mu ai mun dade da wuce wurin. Na gaya miki kullum zance nake zuwa a Apo gidan su Wasila. Ke kawai muke jira ki ce kule mu ce casss.

Usman sai ya yi tsaki, ya ce, Kai wallahi ban ga me ka gani a Wasilar nan ba, yarinya baka kirin mai kirar samudawa? Ni Mammah ai irin auren Yaya Azeez za ki min, ki je Kano cikin yaran nan ki dubo min kawai.

Mammah ta dinga shi masa albarka. Ismael ba ta hana shi ba, amma har ranta ba ta son auren bariki, balle irin wadda Ismael ya kallafawa rai, ba ta zaton za a samu yadda ake so daga gare su a gidan aure saboda budadden ido da gata da yayi musu yawa. Sannan su zo su janye dan daga jikin uwarsa da yan uwansa. Ta sha wahala a kan soyayyar Abdulazeez da Muazatu, ba ta fatan a sake maimaitawa.

Da daddare bayan sun yi dinner, Haleem ya ce da Suhaana yana son kunun gyada, Mammah ta ce Azumi ta yi masa ya ce shi sam na Suhaanah yake so ba na tsohuwa ba, ko ita Mammah da kanta ta yi masa. Ta ce ita ta gaji da tsirfarsa tunda ya zo bai barsu sun huta ba.

Hafsat ta ce, Mommah, bari in yi masa mana? Bakonka Annabinka.

Ta mike ta shiga kitchen.

Tana cikin aikinta ta jiyo ihun Haleem cikin murna yana fada wa Mammah Yaya Azeez na kira, a sailin wayar Mamman ce a hannunsa yana daukar lambobin yan uwa da abokan arziki da ba ya da su don ya kirasu ya gaishesu, kawai yaga kiran lambobin U.S. Hafsat na jin yadda rigima ta kaure a kan wanda zai fara magana da shi. Daga karshe dole sai a handsfree aka saka kiran suka taru har Mammah. Kafin ya ba wa daya amsa daya ya jefo tasa tambayar. Duk dai a kan yadda ya sauka ne da yadda ya tadda wajen, how much suka yi kewarsa da sauransu.

Runtse idanunta ta yi tana jin wani irin fili fetal a zuciyarta. It was like babu komai a birnin zuciyar sabida kewa. Kamar an yashe komai da ke cikinta. Birnin zuciyar is just empty! Wanda ya yi gininnika a cikinta ya yi kaura tare da komai da ke cikinta. The feeling is emotional mai ratsa zuciya da ruhi. Ba ta kara gane me ta ke yi a cikin kitchen din ba ko me ya kawo ta. Ta ga dai shigowar Mammah da sauri ta nufi gass da azama ta kashe wuta na tashi daga cikin karamar tukunya. Ta dauke tukunyar da karamin towel ta jefa ta a sink ta kunna mata famfo. Ta dubi Hafsat da ta yi tsuru-tsuru ta ce,  Addah are you alright?”

Daga mata kai ta yi, To tunanin me ki ke yi haka na ji shirunki ya yi yawa? Daga dama kunun gyada, I then decided to check on you, sai ganin wuta na yi na tashi daga tukunya, in ce ko lafiya ki ke?

Kai ta daga mata cikin sanyin jiki ta gaza cewa komai. To ta ce me? Your son is drivingme crazy? Ba ni da tunanin komai sai nasa, ya maida ni emotional ya gudu ya bar ni? Da ta tabbatar ba za ta yi magana ba sai ta ce, Ki je daki zan yi masa. At least ta gode Allah Hafsat din ba ta kone ba. 

Ba ta da bakin musu ita ma ta fi son ta gusa daga gaban nata, don ta santa kamar mai gani har hanji ta ke a kan dukkan alamuransu. Ba ta sani ba in dai Mammah ce an riga an yi walkiya ta ganta.

Karfe goma na dare ta gama komai na shirin kwanciya, tana so ta tashi karfe ukku daidai na dare don mika kukanta ga Sarki Allah, ba ta da wani buri yanzu a rayuwa bayan shi, bayan neman sauki cikin alamarinsa, bayan neman soyayyarsa da kuma samun tasa soyayyar. Ta sani ba abin da ya fi karfin Rabbi, Shi mai kawo sauki ne cikin kowannen alamari muddin ka amince zai ba ka dukkan abin da ka roka yanzu ko anjima, ko ya jinkirta maka zuwa lokacin da yake ganin ya fi dacewa da kai. Tana neman sauki cikin soyayyar da ta yiscattering(yin dai-dai) da ruhinta, ta yi mata katutu a zuci, ta ke addabarta a kirji, ta ke dawainiya da duk fitar numfashinta.Ta ke neman maida ita wata tababbiya-tababbiya-mai-hankali-mai-hankali. Abdulazeez didnt deserve all these, zuciyar da ta damu da kai ta kuma san kana yi ita ta cancanci a yi wa irin wannan mahaukacin son don za ta karbi response in return.

 Wanda zai sanyaya ta tasan ba aikin kawai ta ke yi ba, amma banda ta Yaya Azeez din da ba shi da damuwa a kan komai nata. Ba a kanta kawai ba, it seems like komai na duniya bai fiya damunsa ba ban da lauyancinsa, da tunanin hanyar da zai bi ya kara gogewa da kwarewa a cikinsa, ta hanyar karbar cases na marassa galihu masu tsauri da ko a manyan lauyoyin gwamnati ba kowa ke yarda ya karba ba, musamman idan suka lura client din babu mamora.

Tunanin da ta ke yi kenan ta ji an murdo kofarta an shigo. Daga kan filo ta dago ta dubi mai shigowar, Mammah ce.

Waya ce a hannunta, tana shigowa ta iso har inda ta ke. Wayar ta mika mata, Ungo wayarki, Daddy ya dawo miki da ita. A sha soyayya lafiya.

Zuciyar Hafsat ce ta yi wani tsalle ta fita daga kirjinta tayi shawagi sannan ta dawo. Kafin ta gama farfadowa Hajiya Maryam ta yi ficewarta. Wayarta ta kalla da dumbin shauki. Wani farin ciki ya rufe ta. Ba ta yi zaton da charge a ciki ba amma tana kunnawa ta ga Mammah ta shake mata ita da lantarki. Da sauri ta duba kudi, naira dubu goma cas! Sweet Mommah. Ta fada a fili. Abbanta ta soma kira.

“Ghaaji, yau ke ce a waya?

Wani dadi mara misaltuwa ya ratsa zuciyarta, wato soyayyar ma kala-kala ce, kuma ta iyaye daban ta ke. Ina ma! Ina ma!! Ina ma ta rayu da wannan Habiban? Ina ma Habiban tana tare da Abba? A hakan ma ta gode Allah da tarin niimomin da ya yi mata. Na bar mata wadannan dimbin masoya zagaye da ita. His blessings upon her are countless, endless, limitless. 

Alhamdu lillah!.

 Abin da ta furta kenan a fili, kuma Abban ya ji. Shi ma wani abu ya taba zuciyarsa, kusan tunani daya suke yi (Habiba) a dai-dai wannan lokacin. Daga bisani kowanne ya ware suka shiga hira. Suna yin sallama ta kira Daada, daga ita sai Malam Babba, Imamu, Abdurrahman da Yaya Modibbo. Ta yi musu ya suka je gida, ta ji lafiyar kowannensu. Sannan ta kira Kawunta Sagir shima ta gaisheshi. Cikinsu babu wanda bai nuna yabawarsa da karimci irin na iyayenta kuma surukanta ba. A zuciyarta ta ce. “Sun wuce da tunaninku, ba ku ga komai ba daga zuriar Malam Abdullahi Dakata.

Sai a lokacin ta bar wayar ta huta. Ta kashe fitila, so ta ke ta yi bacci, don kada ta kasa tashi qiyamul-layl da adduaoin ta kamar yadda ta kudurta. Ba ta jima ba bacci barawo ya sace ta.

Uku daidai na sulusin dare alarm din wayar da ta saita ya tada ta. Alwalah ta shiga ta dauro ta fuskanci alkibla. A yau adduoI da dama ta yi, ta yi wa uwarta da ke kabari, ta yi wa Mammah ta fatan gamawa da duniya lafiya, ta yi wa Daddy na yalwatar arziki da lafiya, ta yi wa kanta adduoI masu yawa. Ta yi wa Daada da Malam na nisan kwana da lafiya madauwamiya. Sai dai me? Instead(maimakon) ta yi adduar da ta tashi don ta yi, wato rokon Allah ya rage mata son Abdulazeez, ya sa masa soyayyarta shima, sai ta samu kanta da yi masa addua. In tace addua to tana nufin addua a kan komai; a ciki ta roki Allah Ya kare shi a duk inda ya shiga, Ya shige masa gaba a kan duk abin da ya sa gaba. Ya cika masa burikansa na alkhairi, Ya ba shi dukkan alkhairin rayuwa Ya bashi nisan kwana…… Sannan Ya kare mata shi daga ZINA da sauran ayyukan sabo masu kamanceceniya da ita.

Hannunta a sama ba ta kai ga shafawa ba ta ji wayarta na kira da tune din takbeer da ta saita kiran wayarta da shi. A nutse ta kammala adduarta ta shafa ba tareda damuwa da kiran ba, zuwa lokacin wayar ta katse har sau biyu ta sake ci gaba da ruri. Sai da ta koma gado ta kwanta, sannan ta jawo ta. Lambobi ne rututu da suka fara da (+917) da ba ta shaida code din ko ina ne ba. Da farko ta yanke shawarar kin dagawa, amma ganin ba a da niyyar fasa kiran sai ta daure ta yi sliding answer button’ din.

Assalamu alaikum. 

Ta fada a nitse. Jin mai kiran ba shi da niyyar yin magana. Cike take da mamakin wanene zai kirata da sulusin dare irin haka? Sai da ya ja fasali har tana tunanin kashe wayarta don ta fara tsorata da yi wa kanta fadan me ya kai ta amsawa ma, kira cikin talatainin dare da international number. Sai ji ta yi murya a ciki, kamar wanda aka yiwa dole yayi magana, ya ce. 

Ba dole ba ne na amsa sallamarki a fili ba ai, tunda na amsa cikin raina.

Wani numfashi mai tsayi ta zuqa ta furzar daga huhunta. Mutum na karshe da ba ta kawo zai kara bi ta kanta ba, she feels like smiling amma ta hana kanta, ita ce mace ba shi ba, ita ya kamata ta yi jan ajin da yake yi mata. Amma anya za ta iya?

In ma ba ki iya ba ki koya, Abdulazeez sai an bi hankali. Ja zarenki  a sannu Addar Mommanta!Bi shi a yadda yazo. 

Zuciya mafi hankali da nutsuwa ta shawartar. Don haka sai ta yi shiru, ba ta ga dalilin da za a kira ta ba, kuma ya yi mata kasaita da iko ba.

 Kiran wayata ma sai kin ga dama za ki dauka ko? Tunda ke bazaki kira ni ba bayan an gayamin an baki waya. Wannan duk a cikin rashin tausayinki ne da kika kware akai, ko a cikin fannonin rashin so irin naki?

Murmushi ta yiwa kanta mai ciwo, ita Abdulazeez yake yi wa korafin rashin so!Bata ma manta ba, bai neme ta ba sai da ta neme shi. Ta je ya yi mata wulakanci, sannan yanzu yana fadin ba ta sonshi, ba ta tausayinshi. Shiru ta kara yi masa wanda ya fi komai fusata shi. Da zai iya da ya kyale ta, amma ina! Ba zai iya nutsuwa ba sai ya ji muryarta ko da kuwa abin da za ta fada mishi din ba mai dadi ba ne.

Ya tabbatar Hafsat bazata ce masa komai ba, kuma bata da niyyar hakan, sannan ya tabbata tana jin sa. Don yana iya jin saukar numfashinta wanda ke fita akai-akai.

“Shi ke nan Hafsah, zan barki ki yi rayuwarki the way you want it (yadda ki ke sonta), amma ki ke sanya wa a ranki akwai wani mutum far away (a nesa) da ya damu da ke da yawa, yake fatan jin ko da kalma guda daga gare ki a yau to keep him companyhar wayewar gari amma ya kasa samu. Wannan mutumin ba wani bane face mijinki Abdulazeez Dakata.Stayblessed. 

Ya yi maganar ne da wata murya data nuna rauninsa a yau, ba tareda ya san raunin ya bayyana kansa ba cikin intonation din sa, mai tasirin kashe jiki da gabban kowaccediya mace, balle ga macen aure ga mijin da ta ke matukar so. Macen ma mai rauni irin Hafsat-Suhaanah. Mijin kuma ba kowa bane Abdulazeez din ne data hana idonta bacci saboda shi, saboda ta roki Allah ta samu kwatankwacin wannan soyayyar da wannan kulawar daga gareshi. Kafin ta yi wani yunkuri, ya kashe. Shefeels like calling him back..amma wata zuciyar ta hana. Barshi shima ya ji in rashin kulawar da dadi. Zuciyarta ta ciko ta yi tantsan da farin cikin jin kalamansa, daga wannan emptiness din da ta ke ji a baya, wani irin nishadi ya lullube ta. Da haka ta samu barci mai nauyi da dadi ya yi awon gaba da ita. Wanda ta dade ba ta yi irinsa ba.

Washegari paper har biyu ta zana (Regional Geography and Rural Geography). Tana fitowa daga dakin jarabawar ta kunna wayarta, sakon sms ne ya fara shigowa. Yau Haleem ne ya zo tafiya da ita. Tana tafe zuwa motar ta bude sakon saboda ta gane lambar da Abdulazeez ya kira ta jiya ce. Hannunta har rawa yake yi, ko me ya rubuto? Ga mamakinta, fatan alkhairi ne a kan jarrabawarta.

As you strive hard to achieve this goal, heres hoping that you excel in every course,with hope in yourself and this strong determination of yours,with me In mind.. and the assurance of my inexpressible love to you I believed that success will surely come your way.

-Abdulazeez.

Ita kadai ta hau blushingtun daga baki har kunne. Sakon waya mafi daraja data taba karba a rayuwarta. Sakon waya da ya sata farin cikin da wani sako bai taba sata ba. Ya goge gabadaya memories na wancan black sakon data taba karba a rubuce. Ta kusa yin tuntube da za ta shiga motar. Haleem ya ce.

 Tsohuwa yi a hankali, doguwa,  hankalinki a gwiwa!. Ta harareshi, amma farin cikin data ke ciki ya hanata ramawa. Suna hanya banda maimaita karanta sakon ba abin da ta ke yi. Haleem na ta mata hira bata san me yake cewa ba. Hatta Mammah ta lura Hafsat yau cikin farin ciki take. Ta san ta canka daidai in ta ce waya na aiki. Addua ta ke yi a zuciyarta wadda ita kadai ta san me ta ke roka musu, wanda ba zai wuce zaman lafiya da zuria mai albarka, da soyayya mai dorewa har abada ba.

Ta riga kowa shigewa daki bayan cin abincin dare, manne ta ke da wayarta tana jiran Abdulazeez ko zai kira? Ko karatun paper din gobe ta ki yi, ba ta da nutsuwar yinsa. Haka ta yi ta zaman jiran gawon shanu amma hudubar jan ajinmu na mata da zuciyarta ke ta yi mata ya hana ta yin sadaukantaka ita ta kira shi. Sai karfe hudu na asubah kamar jiya tana bisa sallayarta ta ga shigowar kiransa kamar a mafarki. Ba ta iya ta jinkirta ba ko na minti daya wannan karon wajen amsawa.

 Tana iya jiyo ajiyar zuciyarsa, ita ma ajiyar zuciyar ta yi ba da saninta ba. Hafsat bazaki kira ni ba, in ni ban kira ki ba? Ya fada da dukkan concern da muryarshi ke iya badawa, haka kawai yake ji a zuciyarsa abubuwan da yake mata bai kyauta ba, shi kuma yana yi ne don ya nuna mata fushinsa na abin da ta yi masa rannan duk da ya san ta fi shi gaskiya.

Yaya Azeez na ga text, na gode!. 

Abin da ta iya furtawa kenan cikin kankanuwar murya,cike da tsoron kada yau ma ya katse maganar tasu irin jiya, ya barta da shaukin da ita kadai tasan adadinsa. Ba tare da ta bashi amsar tambayarsa ba, don ita kanta bata da amsarta.

Fadan namu ya kare ne? 

Ya tambaya da yanayin da ke nuna yana tsananin son jin amsarta wannan karon.

Murmushi ta yi ta kwanta sosai a kan sallayarta maimakon zaman sallar da ta yi akan kafafunta. Sannan tace.

 Its inconclusive!”. 

Dariya ta ba shi sosai. What made it inconclusive bayan gashi na karbi laifin bakidayansa yanzu?

Saboda ni har gobe ban san laifin da na yi maka ba ka ke hora ni haka Yaya Azeez,zuciya ta a kanka mai rauni ce, idan nace rauni ina nufin rauni; ba komai ta ke iya dauka ba musamman fushin ka, tun daga ranar da ta soma son k……..

Hannu ta kai ta toshe bakinta jin sakin layin da ta keyi. How sure she is yanzun yana sonta baka da zuci kamar yadda Mammah ta ce da za ta fara gaya masa sirrin zuciyarta? Wanda daga ita sai Ubangijin ta suka sani duk da cewa ya furta mata kalmomin dake nuna soyayyar? Ta ji kamar ta  dawo da abin da ta fada cikin bakinta, inda hali ta bi bakin da zare da allura. A can bangaren Abdulazeez wayar ya canza wa position daga dama zuwa hagu yana jin wani kududu da ya dade da tsayawa a makogaronsa na melting gradually (narkewaahankali). Zuciyarsa ta shigaimaginatingHafsat a gabansa, da shi kadai ya san da me zai yi tukwicin wannan kalaman da bai taba jin mafi gardinsu daga gare ta ba.

Ina jinki Hafsah, ki karasa don Allah… Ya fada da wata kankanuwar murya,  muryar sa har rawa takeyi.

Yaya Azeez, alamarin na zuci ne, sirri ne irin na zuciyar mutum, da ba lallai a zahiri ya zama hakan ba. Zuciyar mutum,Birnin sa.(Sunan wani littafin TAKORI ).

Ina so in san wannan alamarin sosai, don in tantance ko irin wanda na ke fama da shi ne? Ni tawa zuciyar wani irin radadi ta ke mini in na tuno bana tare da HAFSAT-SUHAANAH, in na shafa na ji babu ita a gadon barci na. Daga sanda ta tafi Jimeta na koma gidan ni kadai, ni da zararre ba mu da maraba. A dakinta nake kwana a kan gadonta in lulluba da duvets dinta. Wadannan lausasan duvets din nata kala-kala. A kan Hafsah na san so na hakika, a kan Hafsah na san mutum na iya bada komai da ya mallaka don ya dawo da abin da ya rasa guda daya!

Hafsah you are special. I love that your tender heart and everything of you, and be rest assured that Abdulazeez lovesyou so much, to an extent Hafsah ……Nayi rantsuwa ki yarda da ni!Kada ki tambaye ni yaushe hakan ta faru, ni kaina ban sani ba. Wannan fushin da ki ka ce ina yi kuwa Hafsah? Let me put it in concret and tangible example for you; fushi ne irin wanda yaron da ke tsananin jin yunwa ke yi in an raba shi da jikin uwarsa ba tare da ya koshi ba. Kina tunanin wannan yaron zai karbi wani uzuri ne a kan uwar da ya riga ya san cewa tasa ce,bai da wata uwar sai ita,bai taba samun sukunin rabarta ba ne da niimomin da Allah ya mallaka masa tattare da ita?

Abdulazeez ya mance Hafsat ba ta gane wahalalliyar Hausa, she didnt get him right to where he wants to, cewa ta yi.

 Ni bana jin hausain disguise, kuma ni ban haihu ba.

Ya ce Za ma ki ji ne. Kuma zaki haihun. Dole ki bude kwanyarki ki gane abunda nake nufi yau. Ni ma bana jin Dutch, not even Flemishballe in yi miki bayanin dana ke so ki fahimta.Shiyasa na yi miki da yaren dana iya kuma dole ki gane. Girl,bari in miki dallah-dallah toh. Ni Abdulazeez mijinki ne, miji kuma na aure, wanda Ubangiji ya dora miki nauyin dukkan  hakkokinsa,amma Hafsat guduna kikeyi, a dalilin ki da ban sani ba, kina min rowar abin da ya zam halalina. Hafsat banda wata matar sai ke, ban iya neman mata ba kullum kuma ina rokon Allah kada ya dora mini. Tun a Sun-city ki ke min wannan azabar. Hafsah in ban zo wajenki ba ki gayamin wajen wa zan je? Shekaruna kusan talatin da hudu ban taba hutawa daga wannan ukubar ba. Ko babu soyayya ina da wannan hakkin a kanki. Hafsa ko kina so in kara kallo wata yar kwalisar in makale mata, in ce ina so in ba ita ba sai rijiya?

Yadda yake maganar yanzun cikin wani irin lallashi ne da shi kansa bai taba zaton ya iya ba. A rayiwarsa bai taba lallashin Muazatu ba sai dai ya cedo and donts.To ko wannan shi ne bambancin matar sunnah da budurwar waje? Shi kansa bai sani ba. Hafsat ta yi shiru, ilahirin jikinta ya mutu, wani irin chemistry na bin gabban jikinta. Ta tabbatar yau da Abdulazeez a gabanta yake zai samu abin nan da ya dade yana burin samu daga gare ta whatever their contract! Saboda ya gama samun duk wani weakness dinta.Kawar da zancen ta yi saboda sosai ta ke jin kunya, wata irin kunya da bata taba ji ta Abdulazeez ba, ko sanda yake gabanta. Kuma ba ta son zancen wata din nan da ya soko suna cikin hirarsu mai dadi.

Yaya Azeez bari zancen watayar gayuka ji? Ka gaya min duk irin gayun da kake so I will be doing.Mammah ta hakura ne? A muryarta akwai trembling (gargada) sannan akwai kuruciya, sokonci da kishi a fili duka a lokaci daya.

Dadi ne ya kashe Abdulazeez  a kwancen da yake.Dadin Hafsat na kishinsa,  ko da yake da dade da sanin hakan tun ma kafin ita ta san soyayyar tasa na farautar ranta.Amma bai nuna ba don kada ta ji kunya ta fasa hirar. Rikon wayar ya canza daga kunnen damansa zuwa na hagu. Yana yawan yin hakan in yana waya. Na bari Hafsah tunda ba kya so, kuma nima fa na fada ne wai in miki misali. Banda haka ma ni idona ai ya dade da dusashewa akan ki Hafsah, in ya ga mata ma rufewa yake yi.Da ba ta hakura ba za ta sakar miki mara ne har ta baki waya? Wannan over-discplined Maman taki! Hummm! 

Keni fa yau hirar mata da miji nake so mu yi Hafsah, irin wadda bamu taba yi ba, hirar real Abdulazeez da real Hafsat in their real self! Ki bude baki ki ba ni amsa. Are you feeling what Iam feeling?

Hafsat ta daburce, wata irin daburcewa mai cakudeda jin kunya, ta wara ido sosai daga lumshe sun data yi  tana kallon dama da hagunta da bakin kofa ko wani yana jin abin da Yaya Azeez ke cewa??? Hijabinta ta janyo ta rufe fuskarta tana ji masa kunyar. A take ta tuno abubuwa da yawa, wasu da suka faru a ‘Sun-City’, wasu a Rockview da halin da ta ke samun kanta a irin wadannan ranakun. In haka ne kuwa ita ma tana da wani extraordinary feeling a kan Abdulazeez wanda daga ita sai Ubangijinta suka sani, amma wani alamarin tsakanin mutum da zuciyarsa ne, ta ya ya zai ce sai ya ji?

Hafsah!. Ya kira sunanta. Kafin ta samu sukunin amsawa ya dora.

In ba ki ba ni amsa ba na rantse gobe zan dawo Nigeria!.

Gabanta ya fadi, in Abdulazeez ya dawo ya ce da iyayensa me ya dawo da shi? Ya fasa karatun? Bayan makudan kudaden da aka narkar a kan tafiyar daga iyayensa har gwamnatin tarayya?After all ba ta bukatar dawowarsa a yanzu bata gama planning da fuskar da za ta karbe shi ba a matsayin tabbataccen miji a karo na biyu, wanda babu yarjejeniyar komai a tsakaninsu sai auren sunnah tsurarsa. Aure na har abada! Rayayye wanda babu ranar macewarsa sai ranar da rayuwar dayan su ta kare.

In haka ne ta yi abin da yake so don a zauna lafiya.

Don Allahkayi hakuri Yaya Azeez,ba sai ka dawo ba zan fada Allah.Ina jinki Ya fada a gajarce exhaustedly. Hafsat ta ja numfashi sannan ta runtse ido tace.

“I really have it for you alsoI mean the feelings…. and its  just..just unexpressable!.

Ta fadi kowacce kalma dallah-dallah, daban daga jikin yar uwarta kamar mai koyon vocabulary. 

Murmushi ya yi cikin mamakin yau Hafsat ke magana haka.

“Then let me come, and make it vivid to me, sai a banbance na wanda yafi tsanani tsakanin Abdulazeez da Suhaanah!. Ya fada cikin wata murya da ta kasa yarda ta Yaya Azeez ce.

Na yi alkawarin bayyanawar a duk ranar da muka hadu. Hafsat ta fada cikin jin kunya.

Yaushe ce wannan ranar Hafsa idan ba ki yarda na zo ba? Shekara daya ba nan kusa ba ce, Ive one year aheada gabana kafin na kammala. Jiranta zai zama kamar jiran ranar busa kaho a gare ni. Gaskiya bazan iya ba!.

About AIS

Check Also

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng  Dumi ya ji a bayansa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *