AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Hafsat ta yi shiru, ya ci gaba da matsowa gabanta. Har ya zamanto space din da ke tsakaninsu taki biyu ne kacal. Yatsunshi biyu ya sanya ya dago habarta cikin kankanuwar murya ya ce,

 Hafsah!

Ta bude fararen idanunta tarrr! Ta dube shi, da wani irin kallon so da ya tsirga har babban yatsar kafarsa wanda ita bata san ta yi ba. Umarni ne na zuciyarta kawai zuwa idanunsa. Da azama ya rungume ta, ya soma magana cikin kunnenta da sauti mafi tsananin taushi da ya mallaka.

Kin ce in shafa in ji ko? Ni da Mammah wa ke aurenki?Ok Hafsat lets find out……”.

Dago kantayayi daga rungumar da yayi mataya sanya fuskarta cikin tafukansa ya somasumbatarta cikin wata irin siga (wani abu data lura ya fi kwarewa a kai muddin ya samu damar hakan tun a gidansu wato sumba. Ta fahimci wannan shine abinda cikin kowanne hali yake ciki (bacin rai ko akasinsa) baya iya fasawa a kantawato dai baya gajiya da sumbatarta). A yanzun kuma yana yi ne cikin yanayin da ke nuna tsananin kewar ta da yayi, da matukar son sa da hakan. A wannan

lokacin ita kanta Hafsat bata da banbanci da shi na jin cewa tayi kewar tasa don dai ita mace ce, kuma maabociyar kawaici da alkunya. 

Saidai ita ta san bata wannan fannin kadai tayi kewar Abdulazeez ba. Ita in general komai da ya dangance shi take kewar;fadansu, jayayyar su, kalamansa, murmushinsa da komai nasa… Daga shi har Hafsat sun fita a duniyar su sun afka wata sabuwar duniyarda dawowa daga cikinta abu ne da zaidauke su lokaci.

“…..Ina son in nuna miki bambancina da ita ne, da abin da ta ke sanyawa kina missing…!!!. 

Abin da ta iya fahimta kawai kenan cikin tarin tausasan kalamansa cikin kunnuwanta.Hafsatta fahimci abin da Abdulazeez ke kokarin yi next shi ne raba ta da sittirun jikinta. Idan hakan ta faru kuma bata san me zai biyo baya ba; bata san iya ina alamarin zai tsaya ba. Ta tuna a inda suke, a gidan waye, kuma a tsakanin wadanda za ta kwana. Wani karfin zuciya ne ya zo mata ba don ta cancanci mallakarsa ba, sai don tunanin rashin dacewar abin da suke shirin yi cikin gidannan ya rinjayi halin da ta tsinci kanta. Daman kuma a tsaye suke don haka ta tattara dukkan karfin da ya saura mata ta tura shi baya ya fada gadonsa. Ta yi mamaki da ta ji kamar ta hankade karamin yaro, ba wani sauran karfi a tare da shi.

Da azama ta isa ga kofa ta murza key din ta fice. Sai da ta tabbatar she is safe sannan ta tsaya jikin hudar kofar ta ce, I’m Sorry Yaya Azeez!. Ta gyara tsayuwarta, ta yi lullubinta sannan ta daidaita numfashinta, ta lallaba kamar mara gaskiya ta shige ciki.

Cikin saa ba ta gamu da kowa ba, ta murda kofar dakinta a hankali ta shige. Dada ta kashe fitila sai jan rago ta ke (munshari). Hamdala ta yi ta fada bandaki don ta yi wanka. Amma me?

 Ba ta son ta wanke scent din Abdulazeez daga jikinta, wani kamshi da ta fi so fiye da kowanne a rayuwarta. Fasa cire kayan tayi. Tajingina da kofar bandakin ta lumshe idonta komai da ya faru a yan daqiqan da suka gabata ta ke tunowa daki-daki tana sakin murmushi. “…Ina so in nuna miki bambancina da ita ne, da abinda ta ke sawa kina missing….!!!. Ta tuno kalamansa,wadanda suka sanya ta kara zurfafa murmushinta kamar wata sabuwar mentally retarded.Wato ta fahimci wani aji na musamman Abdulazeez ya gina, ya dauki Mammah ya ajiye ta cikimai kama dana kishiyar sa.  Kai Yayan Haleem  sai a  barshi.

Daga karshe dole ta yi wankan don ta san in bata yi ba bazata iya barci ba sabida dawainiyar jamaa data sha yau.Ko da ta yi nafilolin da ta saba ta hau gado, kasa baccin ta yi. Yau ne ranar da ta yi dakacen kwace wayarta da Mammah ta yi. Muryarsa kawai ta ke so ta ji, da halin da yake ciki. Ji ta yi kamar ta yi kuka saboda tausayinsa, amma can a karkashin zuciyarta ana gaya mata hakan da ta yi shi ne daidai, su maza babu ruwansu ita kadai za ta kwana a ciki. Ta tuno halin da ta kasance a ciki ranar da suka je Rock view ko ruwan sha da kyar yake wucewa a makogaronta a gidannan sabida kunyar Mammah. 

Ta dauki kwanaki ba ta iya hada ido da ita. Balle yau a cikin gidanta? Ta sani ko ya yi fushi zai huce, duk da ta san fushinsa a kan irin haka ba mai sauki ba ne. Ta tuno sanda suka yi irin haka a gidansu ba ta ji da dadi ba na kwanaki masu yawa. Muguwar gaba ya kulla da ita sai ranar da Allah ya kawo Mammah gidan suka shirya dole.Abdulazeez bai iya fushi ba, kuma in ya tashi yi mara dalili yake yinsa wanda kuma in an bi salsala shi ne at fault.

Da kyar bacci barawo ya iya sace ta. Zuciyarta fal da so da kaunar mijinta, wanda watanni goma sha shidda irin wadannan a baya ba ta taba tsammanin wai wata rana irin haka na zuwa da za ta so shi ba. Bata taba daga ido tayi masa wani kallo bayan na Yayansu ba; Yayan ma irin wanda baa so! Wanda da da hali da an canza shi daga yayan cikin Mammah!Ba ta san ma mene ne son ba, amma yau a kansa ta koye shi ba tare da wani ya koyar da ita ba. Shi kansa bata zaton ya taba attempting yin wani abu da gangan ba don ta so shi! Bai taba yin wani abu da sunan ya ja hankalinta kansa ba. Ta so shi ne don radin kanta bisa umarnin zuciya, ruhi da gangar jiki. Don haka ta rattaba soyayyah a matsayin wani abu da turawa suka kira naturalistic phonemenon; wani alamari da ke faruwa bisa kudurar Ubangiji, da hikimarSa. Wanda karfinsa tamkar chemistrydin gravity.

                       *****

Washegari mutanen Jimeta suka yi harama aka yi sallama cike da begen juna. Sun tafi tare da Ismael da Usman wadanda za su yi musu jagora zuwa gidan Malam Abdullahi Dakata. Su Inna Hafsatu tuni sun san da zuwansu, don haka tarba aka yi musu ta girma, irin wadda wannan family suka gada, su din maabota karamci ne kwansu da kwarkwatarsu. Sai suka samu iyalin Hashim Babba Jimeta suma da nasu nauin karamcin. Godiya ce dai da adduaoin alkhairi suke ta yi babu iyaka duk a kan rikon Hafsat da inganta rayuwarta da suka yi, suna rokon Allah subhana ya saka musu da mafificin alherinSa.

Sun so su wuce Jimeta a ranar yamma ta yi, dole sai da suka kwana. Kasancewar gidan babban gida mai sassa daban-daban ya kwashe su tsaf, maza sun kwana a dakunan maza, haka mata. Washegari asubanci suka yi suka koma Jimeta. Su Ismael suka juyo Abuja dauke da sakonnin Mammah daga jamaar gidan da abubuwan da Inna Hafsatu ta saba aika mata wanda ke musu wuyar samu a Abuja. Duk da ma dai lokacin zuwansu Kanon ya kusa, suna zuwa a kowanne bikin sallah karama ko sanda Daddy ba shi da ayyuka.

Bayan tafiyarsu gidan ya yi tsit! Ya koma yadda yake, sai Hafsat da ke kewarsu. To ita ma ba ta samun zama ba a satin bakidaya. An kafe musu exams time-table nan da kwana hudu za su fara, wanda ya yi daidai da ranar tashin Abdulazeez zuwa kasar Amurka. In ba ta dakin lacca tana dakin karatu na makaranta ita da Mami Sada, Mami ta lura yanzun ba ta ganin Abdulazeez na kawo Suhaanah makaranta ko zuwa daukarta, wani saurayin matashi ne mai tsananin kama da shi. Saidai shi fari ne tas. Kallo daya za ka yi masa ka gane kaninsa ne, ko dai wani immediate relation dinsa. Hafsat-Suhaanah tana ba ta mamaki, zurfin cikinta ya yi yawa, a sabon da suka yi yanzu kamata a ce ta san wani abu da ya shafe ta, amma ina! Ko lambar wayarta ba ta da ita. Ba ta da sakewa da bare, hudubar Mamanta ke nukurkusarta kullum, cewa 80% babu aminci tsakanin kawaye yanzu ta kiyaye su. Duk da ta san Mami is good kuma matar aure ce ita ba ta iya surutu ba, har gobe zaman da ta yi tun daga haihuwa har girma a kasashen ketare na tasiri a cikin rayuwarta ta yanzu da yanayin muamalarta da mutane. Rayuwa ta kowa ya yi ta kansa, kowa tasa ta fissheshe shi. 

Akwai sanda Rabia ta yi fushi da yadda Hafsat ta ki gaya mata tsakaninta da Abdulazeez ta fita shaaninta wajen sati guda, sai ta fahimci Hafsat din ko a kwalarta ta ci gaba da harkokin karatunta ba tare da ta kara bi ta kanta ba. Da kanta ta warware suka ci gaba da alaka don ita kam Allah ya sanya mata kaunarta. Abin da ta fahimta game da ita shi ne, a yi abin da ya hada, amma banda personal life.

Abdulazeez ya je Kano sallama ya kwana biyu. Ko sallama bai yi mata ba, ita da kanta abin ya dame ta. Ta fahimci fushi yake yi da ita, abin da ya hana ta sukuni kwana biyun nan. Ko karatun da ta ke yi na first exam dinta ba sosai ta ke fahimta ba. A bakin Usman ta ji yana Kano sai gobe da yamma zai dawo. Da ya dawo ma bai shigo gida ba, Maitama ya wuce gidan Uncle Abdulkarim, a can ya yi sallar maghriba da isha. Tana lissafe da kwanaki daga lokacin da Imamu ya ce mata saura kwana bakwai ya tafi har zuwa yau. In lissafinta daidai ne gobe ne tafiyarsa. Mammah ba ta yi mata zancen ba a tunaninta tunda ta sakar musu mara ba ta shiga shaaninsu ya gaya mata da kansa, sai dai ta lura ko hanya ba sa hadawa tun tafiyar mutanen Jimeta. Wannan ba damuwarta ba ce, shirin da ta ke na komen Hafsat din shi ta sanya a gaba. Tafiyar Abdulazeez ta yi mata dadi za ta yi komai a tsanake, ita kadai ta san shirin da ke ranta.

Sai karfe tara ya shigo gidan, kai tsaye wajen Daddy ya wuce sun dade suna magana a kan yadda tafiyar za ta kasance, da inda zai zauna a can. Daddy ya ce ya dauki nauyin gidan da zai zauna a garin da jamiar su ta ke, zai kama masa kusa da makaranta a matsayin gudunmawarsa. Kudin accomodation da aka basu ya rike abinsa. Abdulazeez ya ce ya fi so ya zauna a cikin makaranta zai fi maida hankali sosai, ba ya so wani abu ya raba masa hankali. Daddy ya ce.

 Kai da ka ke da iyali? Idan uwarta ta barta ta zo fa?

Kansa ya shafa ya shiga murmushi nan da nan, kafin ya ce.

 Ai abin ne da kamar wuya Daddy!.

Murmushi ya yi shi ma ya dau waya ya kira Mammah, suna kitchen tare da Hafsat ta sakar mata komai ta wanke hannu ta tafi. Tana shiga ta ce. 

Yaushe ka dawo?

Ya hau gaisheta ta amsa kafin ya ce, Tun karfe shidda ina cikin Abuja, na je Maitama ne. Ga sakonki ma in ji Anty Zuwaira.

Ya mika mata wata leda. Ta samu waje gefen Daddy ta zauna ya dube ta da gefen ido, idanunsa a yau basu boye tausayin dansa bada tsananin haushin ta da yake ji yana sakaya mata, a dan kausasheya ce.

“Shin wai Maryama ku ba kwa afuwa ne a rayuwarku?

Tun faruwar alamarin da maida auren, sai yanzu ne ya furta kalma makamanciyar wannan (nemawa Abdulazeez afuwa indirectly) daga gare ta.Cikin nuna soyayyar sa ga dan sa. Yi ta yi kamar ba ta gane ba, sabida a cikin maganar sa yayi amfani da kawaici kwarai wanda ya nuna yau an kure shi, ta ce. 

Afuwar meye ba ma yi? Kuma ni da wa?

Idanunsa ya tsare ta da su masu kidima ta tun tana (sweet 16) har gobe kuma in ana bukatar abu daga gare ta komai tsaurinsa da su ake lallashinta.

Ya ce a hankali. 

Biko muke yi!!!.

Da farko dauke kanta ta yi wani gefen, sannan ta juyo ta dube shi da nata lumsassun idanun wadanda su ne Abdulazeez ya gado.

A kara min lokaci. 

Ta ce a takaice.Sannan ta mike tsaye.  

Shi kenan zan iya tafiya?

 Tsohon Ambassador bai ce komai ba sai Abdulazeez ne ya ga gara ya yi amfani da wannan damar, watakila kaifin idanun mahaifinsa su yi mata tasiri. Sannan da alama yau cikin lamarinta akwai sassauci. Dagowa ya yi ya dube ta da idanun bidar afuwa.

Ina neman afuwarki Mammah!For all the inconveniences!!. I promised you something like that will not happen again!!!”.

Daga tsayen da ta ke ajiyar zuciya ce ta kwace mata, ta dubi mijinta Prof. Dr. Hamzah Dakata, sannan babban dansa BARR. ABDULAZEEZ HAMZAHATIKU; wasu mazaje guda biyu da cikinsu har yau ba ta san wanne ta fi so ba! Sune farin cikin rayuwarta, sune komai nata;they made her realised how a dream come true….The dream of being a mother, a wife and a brave mother in-law. Abu daya ya rage shi ne su taimaka mata ta yi actualizing the dream of becoming a grand mother daga ADDARTA ….., wanda kuma ta san a halin yanzu a shirye suke da yin hakan. Murmushi ta yi mai zurfi idonta saitin Abdulazeez amma bata kalli kwayar idanunsa ba.

“Allah ya yi mana gafara bakidaya.

Sai yau ya ji wata irin nutsuwa wadda ya san ya dade da rasawa. Ya ji cewa, zai iya bata lokaci, zai iya ci gaba da jiranta ta ci gaba da hucewa a hankali har nan gaba dashekara kafin ta dawo masa da Hafsat! Ba son Hafsat yake don ya karbi hakkin aure ba, sai don ya ci gaba da rayuwa da itaa gefensa till eternity. Ta zama uwa ga yayansa, kaka ga jikokinsa, cikamakon farin cikin rayuwar da zai yi anan gaba bakidayanta.

******

HAFSAT 

Ko wanda ke fama da lalurar bugun zuciya ya fi ta nutsuwar zucia daren yau. Sabida shi nasa heart-beat din is treatable wato wanda zaa iya controlling dinsa, amma ita nata ba shi a fannonin medical sciences bakidaya balle a san kalar treatment dinsa. Faruwa yake akai-akai daga umarnin zuciya da kwakwalwa. So ta ke kawai ta ganshi, a kalla su yi bankwana ko da na kalma biyu ne amma ya ki ba ta damar hakan. Bai neme ta a gidan ba har karfe goma sha daya na dare. Tana da tabbacin morning flight zai bi a safiyar gobe zuwa Amurka. In laifin da ta yi masa ne ba ta zaci ya yi girman da zai cancanci wannan hukuncin ba, ya tafi wata uwa duniya ba tare da sun yi sallama ba. Tafiyar da ba ta san ranar da zai dawo ba. Mikewa ta yi daga kan katafaren gadonta ta leka harabar gidan a karo na takwas kenan ko za ta ga gilmawarsa, akalla ko daga nesa ne ta ganshi, ko ta ji sanyi a zuciyarta.

Babu shi, amma motarsa tana nan, wanda ke nuni da yana cikin gidan. Sabida shi ta riga kowa halartar dining-table yau, amma Usman din da ya je kiransa ganin shiru-shiru bai fito ba ya dawo ya ce da Mamma, hes o.kya ci a Maitama. Babu wanda ya kara damuwa a cikinsu sai ita, kowa ya shiga cin abincinsa. Mammah na lura da ita ko cokali uku kwarara ta kasa, ta tausaya mata a zuciyarta don ta san tafiyar Abdulazeez ke damunta, shi ya sa ta yi saurin bin Daddy part dinsa yau don ta ba ta dama ta yi sallama da mijinta. Ta dade a falon cikin kyakkyawar kwalliya mai sanyi, wadda kallo daya Mammah ta yi mata ta san wannan kwalliyar ta musamman ce, amma har ta ci awanni biyu a falon babu ko kamshinsa, dole ta koma daki ta shiga kulla wa kanta mai yiwuwa, tunda leken taga ma ba shi da wani amfani a gare ta.

Mafitar guda daya ce, takawa zuwa dakinsa na gidan, abinda ba ta taba yi a zamansu cikin gidan ba. Take kuma kallonshi a matsayin mafi darajar rashin kunya daga gare ta. To amma banda shi babu wata hanyar sake sanya shi a idanunta kafin ya tafi, sai dai ta wayi gari babu shi a gidan, ba ta da hanyar sake dora idanu a kanshi na tsayin lokacin da ba ta sani ba.

Mantawa ta yi da komai (tunanin Mammah, Baba Azumi, Ismael ko Usman wani na iya ganinta) musamman su Usman din da dakunansu ke daura da na juna. Idan ta mutu kafin gobe iyaka su rufe ta su binne su bi ta da addua babu mai dakon zunubanta da ba ta gama istigfarinsu ba kafin mutuwa ta riske ta. Shi wancan din shine kadai yardarsa zata kaita aljannah. Sanda ta hau jefa kafafunta don isa ga dakin nasa bata gama yiwa zuciyarta umarni ba.

Ga mamakinta ma har ta isa dakin ba ta ga kowa ba, tana dai jiyo karar talabijin daga dakin Ismael alamar shi din bai kwanta ba. Dakunan guda hudu ne a jere, biyu na kallon biyu cikin wata doguwar baranda in ka fito daga main parlour. Nashi da na Ismael  na kallon na Usman da na Haleem. Sallama ya kamata ta yi, amma tsoron kada Ismael ko Usman su ji muryarta ya sa ta yi knocking kadan sau biyu, daga ciki ya amsaa hankali.

“Yes.

Ba tareda tsammanin itace ko kadan ba, yafi zaton Ishma ne,sai ta murda kofar ta shiga.

Dakin ba shi da girma sosai, amma an kawata shi da abubuwa masu ban shaawa daidai da bukatar matasa yan boko kuma  yayan gata ire-irensa. Daga can gefe akwai study-table da fitilar karatu dauke da manya-manyan littattafai da suka shafi aikinsa, kuma a gefensu ya dora kwanfutar kan tebir (desktop), dakin dai ba neat yake ba amma a tsaftace yake, Baba Azumin da ke sharewa ba ta san inda za ta aje masa wasu abubuwan ba don haka ta ke dagawa ta share ta mayar ta aje. Parmanent kamshin Creed-Aventus shi ya sanyaya dakin. Sannan sanyin da volt-care(air condition) ke fitarwa a speed na karshe ne. Ta san zai iya zama illa a gare ta a matsayinta na mai nimoniya, amma wannan ba shi ne gabanta ba; kallon hadarin kajin da ta karba daga Abdulazeez ne. 

Tsaye yake jikin wardrove ta jikin bangon dakin yana fidda kayansa yana jerawa a trolley din matafiya. Da farko ta ci gaba da tsayuwa a jikin kofa bayan ta maida ita ta rufe. Amma ganin ba shi da niyyar ce mata komai kamar ma bai yi noticing shigowar mutum ba sai ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi. Da gaske fushi yake da ita har yau, fushin da ba ta ga dalilin yinsa ba. Takowa ta shiga yi har gaban gadon ta zauna ta jawo trolley din ta shiga gyara masa kayan ganin dannawa kawai yake ya daina jera su yadda yake yi da farko tun shigowarta. Dakatawa ya yi rike da trouser dinsa ya fasa jefawa.

Malama na sa ki ne? Ko na ce ina neman agaji?

Ba ta kalle shi ba, tana mai cigaba da kimtsa kayan ta ce. 

Its my duty!.

 Cikin mamakinsu ita da karfin halinta yace.

Cikin thousandsof duties din gaya min wanne da wanne ki ka sani? Ke nan har kina da guts na bugun kirji ki ce kina da wani duty na matar aure?

Ba ta ce komai ba, kayan ta ci gaba da fiddowa tana jerawa, ta lura rigima yake so su yi, ita kuma ba abin da ya kawo ta kenan ba. Ba irin sallamar da ta ke so su yi kenan ba. Jinta ta ke kamar a kan gajimare, tana shawagi a cikin sky-blue rainbow.At least dai ga shi a gabanta.Fada yake yi kamar ba shi bada kakkausar murya da bai taba yi mata magana da ita baamma a kunnenta ji ta ke kamar sarewa yake busa mata. Duk da haka ba ta kallonshi aikin shirya kayan kawai ta ke yi.

Tsayawa yayi akanta hannayensa biyu bisa kugu.

Malama. Nace ki bari ban sa ki ba, afterall ba ki san wadanda nake da raayin diba ba, sai faman danna min kaya kike.Cigaba ta yi ba ta fasa ba.Hakannan bata dago ta dube shi ba. Kafin kuma insubdued(cikin karayar murya) tace.

 Sunana Hafsatu ba Malama ba!!!.

Tsaki ya yi. Ki fita don Allah akwai abubuwan da ke gabana ban gama dasu ba,kada ki kara min tension”.

Kyawawan idanunta ta dago gabadaya ta zube su a kanshi cikin wani irin slowmotion.

Abdulazeez korata ka ke yi???”

Cikin ido suke duban juna, da wani irin yanayi cikin idanun su, wannan karon shi ya fara kawar da kansa kada ta hango weakness dinsa. Yana kallon wani gefen daban yace.

“Im not sending you out, kawai ina gaya miki kin sa dakin ya yi min kadan.

Kiran sunansa na asaliin full(cikakke) ta yi a yau ya fi komai kassara shi.She spells the name correctlyfiyeda kowa a duniya.Ci gaba ta yi da shirya kayan, sai da jakar ta cika taf! Sannan ta zuge ta. Mikewa ta yi ta tsaya a gabansa, bai fi taki biyu ne ratar dake tsakaninsu ba, idonta fal hawaye. 

 Tunda nasa dakin ya maka kadan, zan tafi, dama sato jiki na yi na zo duk da risk din da hakan ke da shi in Mammah ta gane na zohar nan,don kawai in ganka, (in yi bankwana da kai), in nemi afuwarka ko na yi maka wani laifi ina sane ko bana sane. Yaya Azeez na ji za ka yi tafiya ne shiyasa na zo, wadda ban san ta mece ce ko zuwa ina ne ba(ko ta tsayin wane lokaci ce). All Icometo say is; all the best. Allah ya yi jagora.

Ta juya za ta fice daga dakin, sai da ta kama handle din kofar dakin ya kira sunanta muryarsa na sarkewa. Kafin ta yi aune hawayen data ke ta makalewa sun zubo, sharr!. Gefen mayafinta ta sanya ta tare su, sannan ta murda kofar ta fice ta rufo masa kofar silently.

Gadonta ta fada ta soma kuka, ba kukan gwasalen da ya yi mata ta ke yi ba, kukan rashin sanin ina za ta sanya kanta in ya tafi ne. Wani irin so ke bin jikinta tun daga ranar da ya furta saki a gare ta, zuwa rana irin ta yau zuciyarta bata taba hutawa ba.Watakila Allah ke hukuntasu su duka kan kuskurensu, da wannan azabtacciyar soyayyar. Ga jarrabawa a gabanta. Ta yi zaton zai biyo bayanta su sasanta, amma har wayewar gari babu ko mai kama da shi balle scent dinsa cikin dakinta. Ko dai wannan na nufin….. wannan na nufin… son da ta ke zaton ya fara yi mata ya daina???

Wannan tunanin ba karamin tashin hankali ya zame mata ba, saboda in ya daina son nata ita yanzu zuciyarta ta sa damba a sonsa da kaunarsa! Idan kuma hakan jarrabawarta ce tana rokon Allah ya ba ta ikon cinye ta da A1s, amma hakika za ta bashi sarari kamar yadda ya bukata.

Washegari ita ce farkon fitowa. Tun shidda ta yi wanka ta shirya, takwas na safe za ta shiga dakin jarrabawa ta fito goma na safe. Ta shirya tsaf ta fito kitchen cike da tunanin wa zai kai ta makaranta yau? Dole Usman zai kasance tare da Yayansa a airport. Salisu shi ne last hope dinta, amma ba za ta iya tuna rabon da ya kaita wani waje ba, Mammah ba ta sanya shi, amma dole yau shi din za ta nema. Burinta ta riga Abdulazeez fita daga gidan nan. Cikin ikon Allah ta tadda Usman a kicin ko me yake yi? Oho! Kayan barci ne a jikinsa yana tsaye jikin firji yana shan ruwa. Ido ya gwalalo,yana mata duban tsoro. Hey! Mrs Mungo park! Ba dai har kin shirya ba? Ba sai 8am za ki shiga paper din ba?.

Marairaice fuska ta yi yadda zai ji tausayinta. Ban karanta komai ba ne jiya shi ya sa nake so in je da wuri in nutsu in durawa kaina wani abu kafin lokacin ya cika, don Allah ka taimaka. Ba ta taba nadamar rashin koyon tukin mota ba sai yau. Mammah ta yi-tayi da ita sai ta ce tsoro ta ke ji. Ya rufe firjin ya ce. 

Kin yi sallama da mijinki?

A gajarce ta ce. Na yi.

“Wouldnt you take him to airport?

“You are too inquisitive. Ta ce a gundure.

Kada kafada ya yi irin na (bai shafe ni ba), sannan ya ce. Mu je.

A kofar(library) ta zauna ta bude handouts dinta. Ita a dole ba ta da damuwa banda ta yadda za ta tsarge course din. Amma sai me? Shafi bayan shafi, layi bayan layi fuskar Abdulazeez Dakata ne yana murmushin nan nasa. A karshe rufewa ta yi ta sanya kanta cikin cinyoyinta ta baiwa tunanin nasa da soyayyar tasa fili su sha sharafinsu, ta bar wa Allah komai. Idan tana da rabon cin wannan course (Introduction toHuman Geographies) Allah ya yi kudurarsa a kanta.

A kan idonta masu kula da labirare suka bude. Ita ce farkon shiga, a can ta cinye lokacinta, ban da tunani da bege babu komai a cikin kanta. Tunanin ko za ta sake ganinsa nan kusa? Ko zai sake tunawa da ita, ko kuma wata sabuwar Muazatun zai je ya samo? Ko suna da rabon sake zama tare? Ko Mammah ta datse auren kenan har abada? Tunaninnika ne ga su nan fal wadanda ba ta da amsar ko daya. Ban da zafin zuciya da azabtar da kwakwalwa ba abin da suke sanya mata. Agogon hannunta na bakar fata samfurinpolo ta duba sai ta ga saura mintuna talatin a shiga paper. 

Wani irin kuzari ya shige ta da taimakon Allah ta soma fahimtar bugaggen rubutun takardar da wanda ta yi jotting da hannunta. Kafin karfe takwas ta cika ta samu abin da ta samu da yake shes born gifted. Sau uku in ta bi topic kawai komai yawansa ya zauna mata.

Sai takwas ta tattara ta fito daga dakin karatun. A kofar lecture hall ta hango Rabia Sada, daga nesa suka daga wa juna hannu, sannan kowacce ta shige.

Usman bai zo daukarta ba sai karfe goma sha biyu na rana. Daga airport suka zarto bayan sun ga tashin Abdulazeez. Abin mamaki ta gansu (full house) duk a cikin motar. Motar da Daddy ya fi ji da ita duk cikin motocinsa. Wata ash-colour (Hyundai 2018 model) mai cin mutum takwas. Mami ba ta kara tsinkewa da lamarin Hafsat Dakata ba sai yau. Daddy ne a gaba, sai Ismael direba. A kujerun baya Usman ne da Mammah. Tare da Rabia suka iso jikin motar ta gaida su Mammah, ta amsa da faraa haka Daddy ya sa mata albarka.

About AIS

Check Also

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng  Dumi ya ji a bayansa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *