AMANAR MU CHAPTER 8

AMANAR MU CHAPTER 8

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bud’e idanuwan ta tayi tagan ta cikin wani irin  yanayi. da sauri wata mata wacce a k’alla zata kai kimanin shekaru 50 a duniya ta shugo d’akin hannunta rike da Kofi Mai cike da magani saurin k’arasowa wajenta tayi  ta rik’eta tana fad’in:

“Salamatu !Salamatu  kin farka?

“Sannu?” a rikice matar take tambayar da hade da zuba mata kananun idanuwanta. Mamaki fal fuskar salamatu take

Kallan matan ta. Lumshe idonta tayi tana son tuna kanta, da sauri ta kalli saman d’akin ta kalli k’asan Shi cike da tashin hankaki ta fara tunanin shin ita wacece? Salamatu?any’a kuwa.?  Salamatu ! Takara nanata sunan.  itace Salamatu?toh in itace Salamatu wacece wannan tsohuwar?”

Tsohuwan nan ganin halinda Salamatun ta shiga ne yasata saurin fad’in:”sannun kinji,sannu!” hannunta ta kalla bandge daya hannun tasa ta shafo kanta Dan nauyi taji yayi mata Shima bandage din taji ,yunk’urin motsawa ta shigayi tsohuwar tayi saurin rik’ota tana cewa:

“Yi a hankali, karki motsa dayawa jikin ki duk raunuka ne. “+

K’uri ta k’urama matar idanu tana ta kallanta “wai  shin ita da  wannan matan suwa Nene.?”

“Ki kwantarda hankalinki ungo wannan ruwan maganin ki sha kinji in Sha Allah zaki warke.”

Kafa mata kofin abaki tsohuwar tayi saida ta tabbatar cewa tasha sannan ta cire kofin abakin salamatun wacce itakam sai kallanta kawai take tayi.

************************************

Sosai Umar ya tada jijiyoyin wuyansa akan lalle lalle fa sai Dady ya fiddo da dukiyarsa ya bashi abinsa,Momy da Daddy tsananin mamakin sauyawan Umar d’in yak’i barin zuk’atansu ace matarsa ta rasu ko kwana bakwai da mutuwar batayi ba har yana tada jijiyoyin wuyansa,  akan sai an basa dukiyarsa,rana tsaka kawai ya bijiro masu akan abasa dukiyarsa.  Tun shekaru aru aru bai ce abasa ba sai yanzun rana tsaka kowa na cikin grieve d’in mutuwa yace a fito da dukiya abasa tamkar ba shi bane matar sa tarasu, a gadaran ce yake masu magana baya shakkan ya6a masu dukkanin abinda ya fito daga bakinsa. ba Momyn  ba Daddyn ba!

tun lokacinda Umar ya bijiro masu da Auran Zee rana tsaka lamuransa suka fara tsoratasu sun kuma rasa dalilin da yasa suke maraba da auren. Zukatansu babu  haushin Zee akan auran masu mijin ‘ya da tayi.

Sosai Umar yatada hankalin kowa akan a bashi dukiyarsa kuma fafur Umar ya kafe akan lalle lalle fa dukiya duka nasane babu ko sisin Dady aciki acewansa ai mahaifinsa ne mai kud’in ya mutu yabar masa shikuma baida wayon juya uban dukiyoyin shine babban dalilin daya sa Dady ke juya masa ita. yanzun kuma ya mallaki hankalinsa he needs his inheritance back.

Sosai Dady ke mamakin wannan al’amari dukiya dai yasan ba duka bane na UMAR ya za’ayi yace gaba d’aya dukiyar tasace. Bayan  dukiya ta babansu ce shida mahaifin Umar d’in da ya rasu aka raba masu gado dan haka dukiya tasuce susu biyu bawai na mahaifin Umar kawai ba!

Achan baya mahaifin Umar d’inne  ke rik’eda dukiyar yana juyawa tunda shine babba uwa d’aya uba d’aya !

Dukiyan kowa 50 fifty ne!

Shi kuwa Umar ya dage akan cewa ba haka bane. har ma UMAR d’in ya shigarda k’ara kotu akan lalle dukiya fa gaba d’aya ta babansa ne. Alamarin da ya rikita familyn kenan kowa na cike da zullumi da mamakin yau sune ke cikin tashin hankali a daidai lokacin da suka rasa gudan jininsu tsokarsu Aisha Humaira. Duk wani masoyan familyn ya tausaya musu ya kuma jinjina al’amarin hade da adduar Allah ya sassauta musu ya kawo musu sauki. Hakan tasa.

Barrister bashir da kansa yaje ya sama Dady akan yanaso ya tsaya masa amatsayin lauyansa shizai shige mai gaba,ranar da zaa shiga kotu Dady yace aa shi zai d’auki lauya na daban.

****************************

Zamfara*********

Barrister bashir bayan sadakan bakwai washegari ya tafi zamfara wajen iyayen sa  duba jikin baba yayi mugun tsanani  hakan ne ma ya hana Maman zuwa abj amman kam ranar taci kuka har k’arin ruwa aka mata. Baba ma k’in sanar masa akai gudun ya shiga wani hali nadaban.

STORY CONTINUES BELOW

Mama saida tasha ledan ruwa uku sannan ta d’an murmure amman kullum tana kan sallayanta tana ma Humy a duar samun rahma,dan tasan anmata abubuwa dayawa na zalunci Kuma tabbas  sai Allah yabi mata hakkinta. Cikin tashin hankali

Barrister bashir ya karaso gidan nasu Kai tsaye ya shiga cikin gidan hade da sallama. Mama na zaune kan sallaya ta buga tagumi Baba na kwance kamar matacce. Da sauri ta kalli sa hade da amsa sallamar jikinsa a sanyaye ya zauna hade da kurawa Maman Ido ta Dan rame kadan ga damuwa Nan far tare da ita. Tambaya ya jefo mata.

“Wai mama ya za’ayi Zainab tayi aure amman bazaku sanar min ba?” kura masa Ido tayi cikin kankanin lokaci ta fashe da kuka

hankalinsa tashe yake kallanta yace:

“Mama pls, sanardani wai shin maike faruwa ko nace mai ya faru?karki 6oyemun komai ki gaya mun.”

Mama tana sheshek’an kuka ta d’ago ta kalli Baba dake kwance yana bacci tamkar matacce runtsa idanunta tayi sannan ta maida kallanta wajen Bashir tace:

“Na rasa tayadda za’ayi nagaya maka wannan al’amarin bashir, saboda bama mu bane muka d’aura mata auran ba, shi baban Humairah shi yazama waliyyin Zee shiya d’aura mata aure,kaga da kuny’a ace mu cigaba da zama a gidan shi duk irin cin fuskan da ‘yar mu tayi ta aure masu mijin ‘yarsu Shi yasa kaga tunda babanku ya yanke jiki ya fad’i na d’auko shi nace zamu dawo garin nan dan da kyarma ya barmu ma akan cewa zamu dawo amasa magani anan d’in k’ila mu dace.

Wlh zainab ta cuce mu, ta cuce mu! Ta cuce mutanenda su suka taimake mu, suka agazamana suka ceci rayuwan mu, daga k’arshe ga abinda zainab tayi. zata saka masu da tsiya ,gashima Humairan ta mutu  ta barmata duniyan sai taci abinda zataci ,Amman bashir ya za’ayi ace munada rai muna rayuwa wai ace da yardar mu da amincewan mu zee ta aura Umar haba ai AMANARMU sai tayi k’aranci sai butulci ya shugo ciki !”

Nisawa bashir yayi sannan ya shiga baiwa mahaifiyar sa dukkanin labarinda ya faru daga lokacin Zuwansa har tattaunawan sa da Zee da kuma rashin mutuncin da Umar keyi akan sai Dady yabasa dukiyar sa!

Kuka sosai mama tashigayi tana cewa:

“Hàba wlh koda chan lokacin da naga yariny’an nan tazo ta soma janmu ajiki sai da jikina ya bani any’a? saboda dai ni wannan yariny’an yanda kasan bani na haifeta ba!”

Barrister bashir yace:”Subhanallhi mama bai kamata kice haka ba “

Tace:”wlh Kaman ba jinina ba ace nice na haifi yariny’ar data zama musiba da bala’i innalillahi wa’inna ilaihir rajiun. inata adu’a akan Allah yabani ‘ya mace gashi ‘ya macen ta zamemun bala’i,wlh ga babanku nan tunda yariny’an nan tazo masa da zancen auran nan yayi fafur yace wlh wlh bada shi ba. babu wannan maganar  kuma inda ransa bazai bari ta auri Umar ba ,toh yarinyannan tunda tasa k’afa ta tafi ba’afi kwana Uku ba babanku ya yanke jiki ya fad’i na rasa wannan masifa.”

Mama na kaiwa nan ta kuma fashewa da kuka sai hango baba dake kan gado sukai idanunsa na fitarda hawaye alaman idanunsa biyu sannan kuma yana sauraren duk abinda suke tattaunawa kuma dagske kuka yake yi chan cikin zuciyansa!

Hankali barrister bashir ne yayi mugun tashi wannan wani kalan musiba da bala’i ne ace yariny’ar da bata fi 21 zuwa 22 ba yau itace tabi ta dagula farin cikin kowa?wlh sai ya mugun gyarama Zee zama. dashi take zancen. Zuciyar na suya da kyar ya iya lallashin iyayen

“Baba, mama. dan Allah kuyi shuru in Sha Allah yanda Zainab ta tarwatsa rayuwan farin cikin gidanan wallahih nima sai nasan yadda nayi na tarwatsa irin mugun nufin data d’ora ma kanta “

Daga haka ya mik’e azuciye yama mahaifiyar sallama, daganan yayi shigewan sa mota dan yau yau d’innan zaibar garin zamfara dan baiga ta zama ba wlh sai ya durk’ushe Zee da ita da nufinta! Bata isa ta tozarta rayuwan wa’inda suka taimakesu suka fiddo su daga cikin rana suka maidosu inuwa ba.

*************************************

Tun daga wannan ranar tsohuwar nan take kulada Salamatu in dare yayi zata kawo mata abinci ita dakanta ke bata abaki sannan inta gama tabata wannan ruwan maganin ta kora dashi sannan kuma tana kiranta da suna Salamatu!

Ita kuma salamatu sam bata san kanta ba. A haka har tayi kwana biyu tareda wannan tsohuwar. salamatu Bata da aiki  saidai ta zauna shuru tayi jugum. yauma hakan ce ta kasan ce Salamatu na zaune jugum a d’aki dan ko nan da chan bata zuwa ko magana ba tayi saidai ido,tsohuwar matar ce ta shigo d’akin ganin ta a haka yasata d’an murmusawa ta k’araso wajenta tace:

“Kinata tunani ko Salamatu?sannun kinji Allah sarki Salamatu ubangiji Allah ya tashi kafad’un ki ‘yata Allah ya baki lafiya “

Saurin kallan matan Salamatu tayi jin tace mata ‘yata

“‘Yata ‘yata?’yata?

Shi Salamatun ta ruk’a fad’i a cikin zuciyanta “kenan wannan babartace?”

Kaman tsohuwar tasan abinda salamatun ke tunani sai tace:”kinsan mainene Salamatu ni yaar babar kice ,ni ‘yar uwar kice kuma kina d’aukeda ciki mijin ki ya mutu kuma ke sunanki Salamatu “

Itadai Salamatu kawai gatanan  gata ne duk abinda tsohuwar ta fad’i mata saitaji ta amince da shi .

**************************

Zee kishingid’e akan soffan d’akinta ta mimmik’e k’afafu sai wani fresh takeyi tana cika takara k’iba dan ta sanarma Umar ciki ne da ita hakan ya sashi d’aukan son duniya ya d’aura mata ya shiga bata tattali da kulawa ta musamman ko nan da chan sai ta kama take zuwa dan komai yi mata shi ake kullum sai dai taci mai kyau ta sha mai kyau ta kwana waje mai kyau mijinta na mugun son cikinta da tattalinta dole hankalinta yayi mugun kwanciya komai masu aiki kemata!bata aikin komai!

Wayanta dake kusa da ita ta d’auka sannan ta danna lanban wayarta ta shiga Kiran layin.

***********************************

Ringing d’in da wayanta nokia keyi ne yasata d’an kallan mai kiran nata,ganin wanda ke kiranta yasa ta saurin kallan Salamatun data kafeta da idanu tana kallanta!

Saurin mik’ewa had’ida cewa:

“Ina zuwa Salamatu karki tashi kije ko’ina kinji,ki bari sai kin k’ara warkewa kinji?”

Da sauri matar tafita daga d’akin ita kuma Salamatu tabi ta da kallo!

A tsakar gida ta tsaya sannan

Ta danna amsan kiran wayar tace:

“Na’am hello uwargijiya ta ya akayi?”

Uwargiyan nata tace:”yeah tananan kuwa?”

“Eh tananan”

Uwargiya:”tana samun kulawa?”

Tsohuwa:”eh “

Uwargijia:”ta farka?”

Tsohuwa:”eh ta farka “

Tace:”toh shikenan ki cigaba da kulawa da ita na gaya maki bakida matsala,kin san dai d’aukoki nayi kina bara na baki wannan aikin domin na rufa maki asiri,toh idan kikai min aiki mai kyau toh kam tabbas zan tabbatar maki da cewa keda bara har abada kuma zan tallafa maki,amman fa sai kinyi abinda nakeso “

Saurin gyad’a kai tsohuwan tayi sannan tace “in sha Allah bazan baki kuny’a ba zan maki aiki mai kyau iya yine za kuma kiji dad’ina “

“Good “

Daga haka suka katse wayan tsohuwar tayi saurin shigewa cikin d’akin wajen Salamatu!

*********************

Zama ta kuma gyarawa sosaii ta shiga k’eta dariya sai da tayi mai isanta sannan ta d’an tsagaita tana rik’e ciki tace:

“Kai wlh amman kam I am very smart,wlh inada basira inada kwakwalwa ,inada tunani mai zurfi hhhhhhh wlh Hu……..:……….✍?Ajiyar zuciya tayi Mai karfi cikin huro iska ta furta. “Humairah sai kin gane  shayi ruwane, sai na dagula rayuwar ki, sai na k’untata miki, Humairah. sai na hassasa bak’in ciki a duk lamuranki”+

shek’ewa da dariya tayi ta cigaba da cewa:

“Wato duniya  idan kanada kud’i babu abinda mutane ba zasu maka ba” jinjina Kai tayi tana hasasho duk abubuwan da ta shirya.

*******************************

Tunda Suka fitarda Humairah a cikin gidan, bayan shugo wansu  ciki,Zee ta saki Umar ta haura sama cikin d’akin sa, tayi wani kalan diran jin dad’i a kan gado tana lumsa idanu wayar hannunta dake ruri ta d’aga tana sakin murmushi sannan cikin mak’ewan murya gudun kar wani yaji abinda take fad’a tace: “kawai ku ruk’a bin bayanta har lokacinda zata wuce tashan. d’aya daga cikin ku ya tuk’a acha6an yakaita chan kasuwan baccin karku bari ta sama acha6an da zai kaita kawo. kasuwan bacci zaku   kaita sannan inkun isa already dama zaku riga wanda zai kawo Humairan chan kasuwan,kuyi Parking moto cin ku yanda masu lodin matafiya suke,sannan ku zauna a gefe kuna hira,bayan mai acha6an ya ajiyeta shi zai nuna mata inda zata samu motan da zai kaita abj, dan nasan babu inda Humairah ta sani a kaduna sosai. Zata nufo inda kuke dan tambayan motan dazai kaita abj ku kuma a wannan lokacin ku nuna sam baza ku kaita ba dan yamma tayi kuma hany’an abuja ba Shi da kyau musamman da yamma. daga nan nasan zata ruk’a rok’anku tana magiya akan ku taimaka ku kaita dan bazata k’ara koda kwana d’aya a kd ba gidansu zata koma, duk da rok’on nata a gareku kada ku amince ,sai inhar ta fidda ran babu wanda zai taimaka mata.Nasan daga haka zata juya tana hawaye dan tafiya,anan ne d’aya daga cikin ku zai mik’e ya kirata yace zai kaita amman kud’inta dubu goma,Na san dagudu zata amince inta Humy ce ma ayadda nasanta zata ce zata linka kud’in .Daganan sai ta shiga motan duk wanda zai tuk’a acikin ku sai ya d’au hanyar abuja!.Ku kuma sauran sai ku shiga motocin ku sannan kubi bayan su.Bana so sam ku isa abuja garinda za’a shiga kafun isa abuja nan zaku tsaya dan isa cikin k’auyenda malam yake! Direban zai watsa mata wannan farin hodan dana baku a daidai saitin fuskanta ta yanda har hancinta zai shak’a! Daga nan Humairah zata fita daga cikin hayyacinta,sauran aikin ya rage gareku ,kudai tabbata Humairah ta kwana a k’auyen su malam. “

Tun tsirewa da dariya mazan sukai sannan cikin muryar  rikakkun yan iska suka ce:”A gaskiya hajia ko shaid’an sai ya jinjina maki ke d’in kina aiki da kwakwalwa tamkar na’urar computer ,shaid’anu kansu munsan a duk inda suke suna masu jinjina kaidi irin naki,Allah dai yaja da ran Hajia Zainab Uwargidan Umar. “

Dariya sosai Zee tayi tana kad’a k’afafun ta tana jin dadin yabon da sukai mata lumfashi taja sannan ta d’aura fuska tace: “ku tafi ku fara binta nasan yanzun kam duk inda take taje naiman kud’in mota,and kuruk’a keeping d’ina updated.Bakuda matsala da kud’i in aiki yayi kyau zan cika maku bujenku da bugun abuja!”

“Angama ranki ya dad’e aiki kaman anyi angama ne “

Daga haka ta katse kiran tayi rangwad’a da wayan hannunta,tana mai sakan ma kanta murmushin da ita kad’ai tasan sirrin kayanta!.

A yanayin yanda Zainab d’in ta tsara masu a hakan sukai,bayan Humy ta shiga motan aka ja suka kama hany’an abj sauran kuma suka biyo su a baya,Zee nadaga cikin d’aki suke keeping d’inta update.dan gayyama tsirowa  tayi da cewa wai Umar yaje ya siyo mata ice cream,dan ta samu ma tayi magananta dasu sosai!

A haka suna dai ta keeping d’inta update hardai taji sun fara salati da kirawo sunan Allah ,a tsorace ta shiga tambayan su ko lfy d’aya daga cikin sune yace “Wlh Hajia wata tirelace tashiga kan motarsu Humairan,motarma gata tayi tankal tankal ta shiga daji “

A kid’ime cikin masifa Zee tace:”Toh ku kuma uban me kuka tsaya yi kuyi hanzarin shiga dajin a fiddo Humy dole I need her alive nace ku fita kuje kuga halinda suke ciki”

STORY CONTINUES BELOW

da saurinsu suka k’araso cikin dajin inda motarsu Humyn ke bige da wata bishiya murfin bayan motar suka gani a bud’e saurin lek’owa sukai direban kam ya bige sosai baya koda motsi kallan bayan inda Humyn take sukai bata nan. A tsorace d’aya daga cikinsu yace :

“Kumuyi sauri mu keta cikin dajin k’ila gangarawa tayi”

Kutsawa sukai da gudu cikin dajin Basu yi nisa ba suka hangota tana gangarawa cikin mugun yanayi har  ta bige da wata bishiya.

Da sauri suka k’arasa wajenta saurin ta6ata sukai sukaga tanada rai  wata ajiyar zuciya sukayi dan uwargijiyarsu tace she need her alive Amman kam sosai ta bugu kanta sai fidda jini yake ta kuma k’ukk’urje a jikinta.

Koda suka sanar wa Zeen abinda ya faru cewa tayi suyi maza maza su shak’a mata hodan nan sannan kuma suyi saurin kamata subar gurin kar mutane su fara zuwa!

hakan sukai. suka shak’a mata abinda malam yace a shak’a mata wanda zata manta da kanta zata mance ko ita wacece.

Dogon lumfashi Zee ta saki data tuno abinda tayi a wanchan lokacin har kowa yayi tsammanin cewa Humy ta rasu. dariya tayi hade da lumshe ido zuciyar ta cike da jin Dadi dan ita kad’ai tabar ma kanta sanin yanda akayi ta samu dead bodyn da yayi raga-raga tayanda baza’a gane cewa ba Humyn bace.

Kyalkyalewa tayi da dariya hade da kwanciya sosai tana jinjina wa kanta  dan wannan lamarinma ita kad’ai tasan gwagwar -mayan data sha duk da bata tsanmanin zasuyi hatsari ba amman sai take ganin cewa gwarama da hatsarin ya faru,dan daa ace tabbas a yanda ta tsarane na 6atarda Humyn. Idan aka  yawaita bincike zaa iya gano inda take. yanzun kuwa  tabbas kowa zaiyi  zaton tayi hatsari ta mutu. kai Allah ma yana bayanta shiyasa ya kaddara Faruwan hatsarin. (kufaji Zee dawani alkaba’ir?)

Zatayi aikinta ta kuma cikar burinta cikin ruwan sany’i !

Cigaba da tuna abinda ya wakana a wannan lokacin tayi:

Da jin hakan  taga Wannan opportunity ne Mai kyau a gareta.sai ta fito tabi motar haya tawuce sulejaa ta wuce inda aka kai Humy chan gidan malaminta dake mata aiki !

A haka malam ya kunsa mata yanda zata cigaba da gudanar da al’amarin,sannan ya had’ata da wata tsohuwa mai bara yace itace zata ruk’a zama da Humyn,nan dai duk suka k’ulla yadda zasuyi abunsu saida Zee ta tabbatar babu wata matsala sannan MALAM ya sheda mata cewa ya aika wasu aljanu chan inda akai hatsarin su zasuyi handling komai karta damu kowa zai sha Humy ce ta rasun (Aljanu sukai suffan Humyn kenan anan Zeen tasama dead bodyn da take magana)

Murmushi Zeen tayi sannan ta furta a fili:

” tunda har MALAM ya gaya mun cewa idan harna kashe d’an  cikinki toh zai zama sanadiyar  tonuwan asirina !.ba kuma zan sake cin nasara a kanki ba!, toh zaki haihu Humairah wannan shine daidai da abinda na yanke”!

Kuma tuntsurewa da daria Zeen tayi tana mai shafan tunbinta data sa ya fito dan dole ita anan wai mai ciki hhhhhhhhhhh

*****************************

Kaduna!

Barrister bashir straight kaduna yayi ma diran mikiya sannan ya wuce chan unguwan su Zeen da kwatancen Yaah Khalil dana mutane ya gane gidan!

Koda maigadi yayi mai iso cikin gidan straight falan gidan ya shiga da sallamansa.Suna zaune mak’ale da juna anata romancing juna,jin sallaman da’ake yine ya katsesu Umar ya amsa ta reda bada izinin shugowa!

Shugowa bashir yayi ganinsu lilik’e da juna yayi saurin kawarda kansa gefe yana mai tsananin mamakin wannan wani kalan iskanci ne ace kaman basu bane akai ma rasuwa da alama-ma yanda suke ayanzun nan maybe sun manta da mutuwar, Hmmm  in kanada ran ne kawai akeyi dakai in kuma bakada shi kwana 1 zuwa 7 za’ayi amance dakai (Allah sa mu dace)

Ganin Barister bashir saida ‘yan hanjin Zee suka kad’a amman dake ‘yar duniya ce sai ta wayince ta sake Umar dake kallan Bashir d’in da mamaki.

“Laaa ashe yaah bash ne, sannu da zuwa yaya.ashe kaine tafe shine ko sanarwa babu,ga guri bismillah ka zauna “

STORY CONTINUES BELOW

Ta ida maganar tana mai murmusawa had’ida nuna mai wurin zama,zaman yayi ba tareda yace masu uffan ba sai binsu da kallo kawai yake wanda ya k’unsa ma’anoni daban-daban.Ita dai Zee wlh batai marhaban da zuwan nan nasa ba, dan tasan akwai dalilin nasa na zuwa bawai hakan bane.Muryan sane ya katseta daga tunanin da take yi: cikin wata irin murya me wahalar fassara ya fara magna

” fisabilillahi abunda kuke yi d’innan aganinku ya dace?”

Ya ida maganar yana mai kafesu da idanuwan sa,kallan juna Zee da Umar sukai alamun mai sukeyi ?

Cigaba yayi da cewa:

“Kai Umar yanzun dan bakada mutunci har dady kake zuwa kana ma rashin kuny’a da rashin mutunci,any’a Umar hankalinka d’aya kuwa?ba wani abun akai aka juyar maka da kwakwalwa ba?toh kasani koshi asiri wlh baya tasiri ajikin mutum sai ya tadda hali,dan haka kayi maza ka farga kuma ka tashi daga nauyayyan baccin da’aka saka,karnan gaba kayi danasani “

Cikin d’aga murya Umar yace:

“Kaga Bashir wlh ina kuny’ar ka dan kana wan ZEE amman duk da hakan ina maka kashedin kayi gaggawan barmun gida wlh tun kafin nasa a fiddamun kai daga cikin gidan,dan bazan yarda kazo ka tarwatsamun farin cikin gida akan Zee babu abinda bazan aikata ba koda ace da raina ne zan iya fanshe mata koma mainene,so now get out of my house “

Murmushi Barrister bashir yayi dan wlh alamu sun rigada sun gama nunawa tsaf ajikin Umar asiri ne ke bid’e da shi amman ba komai ita kanta Zee d’in tasan ya fita hatsabiban ci zai yi anfani da kwakwalwanshi da kuma dukkanin dabarun sa na lauyoyi wlh sai ya yak’a Zee dashi take zancen!

“Bama sai kasa anzo an fiddani daga cikin gidanka ba ,dan nima banzo nan da shirin zama ba kawai nasiha nazo na maka ka tashi tsaye ka kuma dage da sallolin dare da adu’oi da sadaka wa’allah abinda ke jikinka sufara daina tasiri akanka,dan da alamu sakaci sosai kakeyi da adu’oi “

Daga haka Barrister ya mik’e had’ida juyowa ya kalla Zeen datayi sororo tana sauraran sa,kallan tsana da trrr da hali irin naki yayi mata sannan yace mata:

“Muzuba wlh saita durk’ushe duk wani k’udiri naki,makira kawai “

Daga haka ya saka kansa ,yayi ficewan sa daga gidan gaba d’aya ransa na matuk’ar suyaa.

Tsaki Umar ya buga sannan yayi juyawan sa ya haura sama ya shiga d’akinsa rai 6ace!

Tabbas in bata tashi tsaye ba wannan yaah bashir d’in zai 6ata mata komai da komai tafi kowa sanin waye Barrister bashir ta kuma san abinda zai iyayi tasan yafita basira da nazari mai zurfi kuma tasan shi mutum ne maibin kwakwafin tsiya duk abinda yasa agaba toh in sha Allahu be ta6a hutawa harsai ya binciko mafarin abin kuma sai yasan yadda zaiyi ya tarwatsa abun.Nisawa tayi sannan tace:

“Lallai Barrister bashir ni Zee ni zaka shiga gonata,Humm tabd’i jam babana ma namaidashi yanda yake ayanzun ballantana kai,akwai wanda ya isa ya dakatar dani?aini na rigada nayi alk’awarin wallahi sai nazama multi-billionaire,dukiyar Umar sai ta dawo hannu na.Kuma Umar k’iyayyar da yamun dukda inason shi nima sai naci mutuncinsa! Yanda ya azabtar dani,yake hantarata yake nuna tsananin k’iyayyata agaban kowa wlh shima sai na d’au fansa.Kusan shekaru nawa na d’auka ina kwasan kayan bak’in ciki ni talaka,ni ‘yar gidan nak’asaishe,ni kowa baya sona sabida Humairah!,yanzun d’inma ina cikin sama-ma kaina farin ciki kowa baya sona,wai mai Humairan nan take da shi wacha irin yariny’a ce Humairan?ga ba ranta amman ga barrister bashir uwa d’aya uba d’aya amman har yana shan alwashin sai yayi waye sai yayi waye,dan dai duk saboda humairah!wannan wacha iriyan macece? Ni barima na kashe wannan Humairan nahuta,kai wlh da sake!”

Cikin azama da k’unan rai ta fisgo wayanta ta shiga danna ma malaminta kira bugu d’aya ya d’aga bayan sun gaisa ta shiga kwararo ma malam bayanai akan yayanta yana son yarusa mata tsari,bayan ta gama mai bayani tayi shuru shikuma ya d’an murmusa yace:

“Zainab karki damu ai kinada ni.kuma tunda har kina mana abinda muke so muma zamu maki abinda kike so kada ki damu zamu 6atar mai da hankali daga kan maganan duk da dai shid’in mai mugun rik’o da adu’o’i ne samun kansa zaiyi wuya,amman karki damu tunda muka 6ada na umar toh na kowama bazai gagara ba!.

Daga haka ya yanke wayan ita kuma Zee tasake murmushin jin dad’i dan daga yanzun tasan kuma yaah bashir ba matsalanta bane,itafa wlh ko kashe mutum zata iyayi muddin har zai mata katsalandan akan burinta ba tak’i koma waye ta sharesa a doran k’asa ba dan wlh zuciyanta a bushe yake.

**************************************

*K’auyen Anchau *

Salamatu da baba tsohuwa zaune a bakin wani titi sun kasa farantin dake cike da breadi da alamu saidawa suke dan jefi-jefi mutane na zuwa suna d’auka su siya su baiwa Salamatun kud’i .Ita dai Salamatu kullum idan suka zo suka kasa breadi inta sama guri ta zauna sai ka ganta shuruu,zuciyanta sai taji kaman tana son ta tuna mata wani abu amman sai takasa,sai dai tayi ta irin wasu tunanai,saidai tayi shuru gashi sam bata yawan ibada,ita dama baba tsohuwa bata damu da salla ba,ita kuma salamatun wataran tayi salla ko tayi salla akan lokaci ko kuma baza tayi ba.ita dai gata nan ne dai.tana zaune koda yaushe in anzo siyan biredi in ansiya abata kud’in,in yamma tayi su tashi ita da baba tsohuwa sukoma gida.A haka dai akwana a tashi har cikin salamatu yakai wata tara!

Ranar wata jumma’a ta tashi da nak’uda……::::.:::.::::✍?Zaune suke suna hira,gefe d’aya kuma Umar na mata tausa a k’afafunta data dage tace masa yana mata ciwo har wani kumburi yake,yana mata ita kuma tana lumshe idanuwanta saboda dad’i.muskutawa Umar yayi sannan ya sauke idanuwansa akan cikin Zee d’in daya d’an 6ulluk’o kamar mai cikin wata 4 nan ko a yadda ta sanar masa cikin ya kai wata 9 kuma ta kusa shiga BCG d’inta.Sosai Umar ke mamakin rashin girman cikin nata amman sai nuna masa take  ai ita cikin ta ba irin mai fitowa d’innan bane rid’ed’e ,kuma k’iban da tayi ne ya shany’e cikin shi yasa yake ganin cikin nata ba irin na sauran mata bane.Duk dai hany’an da Zee tasan cewa Umar zai iya d’agowa ba tada ciki sai data san yadda tayi ta dak’ule hany’ar. Haka dai Zee tamai wayau da dabara da d’an tunbin daya fito mata.Shi kuma sai ya bita a hakan dan yasan ko wacce mace da irin nata ya nayin jikin.Murmushi yayi sannan ya shafa goshinta yace:

“Zeetah wannan cikin naki gaskiya kyau ma ya maki,duba fa sai kace ba mai cikin wata 9 ba ,ji cikin ki d’an k’ararrami?”

Ta6e baki Zee tayi sannan ta d’anyi murmushi tace masa:

“Eh wlh kaidai bari kawai rabin ran,ai daga jikin ne,kasan mutum mai kyau ai ,toh jikin sama zai kasance mai kyau “

Murmushi yayi yace:

“Hakane kam tawan “

********************************

Ranar Jumma’a

Ita dai tasan ta fara rashin lafiya daga k’asan cikin ta har bayanta da k’afafun ta duk suka rik’e mata kuma tasan cikin ta sai matuk’ar juya mata yake sosai,harda kwallanta ,dan tunda ta farka ta iske ta acikin gidan baaba tsohuwan nan bata magana,sai dai taga mutane nayi ita kam kullum gum-gum take.(toh muguwa Zee ta kulle bakin maganan)??‍♀️

Sai ita baba tsohuwa ce ta sanar mata da cewa nak’uda takeyi,ita dai salamatun bawai sanin mainene nak’udan karan kansa bane tayi kawai dai tasan babaaa tace mata  nak’uda take!

Ruwan wani magani baabaa tsohuwa ta baiwa salamatun inda take shaida mata inhar tasha wannan ruwan maganin toh in sha Allahu haihuwan zai zo mata da sauk’i.ita dai tunda tasha wannan maganin bata sake sanin inda kanta yake ba,sai farkawa tayi kawai ta ganta acikin d’akin baabaa tsohuwa.da sauri Baaabaa ta k’araso cikin d’akin,fuskanta duk damuwa ta zauna kusada Salamatun sannan ta rik’o hannunta,ita dai Salamatu kallan baabaa kawai take da idanuwan ta tana mamakin ganin sauyin fuskan baabar amman ba bakin tambaya.

“Sannu ko Salamatuna sannu da sauka,sannunki da k’ok’ari “

Da idanu kawai Salamatu ke bin baabaah tana son sanin mai ya faru da ita babar take mata sannu,”

“Nasan baki gane mai nake nufi ba ko salamatu?toh ina nufin kin haihu,kuma Allah ya saukeki lfy “

Jin ance mata ta haihu kawai sai ta tsinci kanta da saurin kallan cikinta,amman sai taga wayam babu k’aton cikin nan da take da shi ,kenan haihuwa tayi?toh mainene haihuwa kuma?”

Shine tambayan da take ma kanta amman takasa sanin tayaya ma zatayi tunanin gano mai ake nufi da haihuwa!

Ji tayi babaa ta kuma cewa cikin muryan kuka:

“Amman fa Salamatu yaron da kika haifa baizo da rai ba ya mutu kuma d’a namiji kika haifa,kiyi hak’uri kinji haka Allah ke tsara lamuran sa ki d’au hak’uri da dangana “

Maganganun baabaa musamman da ambato MUTUWA sai da gaban Salamatu ya yanke ya fad’i haka kurum taji zuciyanta na buguwa ,harga Allah bata san mai hakan ke nufi ba amman sam taji ba dad’i musamman kuma da taga hawaye a fuskan baabaa hakan ya tabbatar mata cewa shi Mutuwan ba abu bane na farin ciki!

STORY CONTINUES BELOW

Hawayene kawai ke silalo mata daga fuska haka dai tsohuwa ta ruk’a tausan Salamatu da maganganu na kwantar da hankali!

Har ta samu Salamatun ta saki jikinta.

Daga hakan kuma sai taji ta wasai bata damu da abinda tsohuwa tace mata ba dan ita sai ma taji tafi jin dad’in jikinta yanzun dan wasai take jinta ba kamar daah da ciki ya 6ulluk’o mata ba.ita dai fa gatane kawai hauka-hauka kuma ita ba mahaukaciya ba!

*********************************

7:30Am

Da baba tsohuwa ta farka da safe ta iske kaman nak’uda Salamatu keyi sai tayi saurin danna ma uwargijiyar ta kira (Zee)ta sanar mata lalle lalle fa Salamatu kaman nak’uda take,Zee cikin sauri tace mata:

“Toh maza maza bata wannan ruwan maganin tasha yanda kota farka ba zata shaida cewa ta haihu ba sai kece kawai zaki gaya mata cewa ta haihun amman d’an ko ‘yar ta mutu,ni kuma yanzun yanzun nan ina kan hany’ar zuwa wajen naku,kiyi gaggawar kar6ar haihuwar kar wani abu yazo da matsala inba haka ba abakin aikinki,zaki koma bara “

Daga haka Zee ta katse kiran sauri sauri gudu gudu taje wajen Umar tace masa lalle lalle fa ita sai ya kaita Zaria akwai wasu kaya da take so ta siya,cike da mamaki Umar yace mata:

“Yanzun kirasa inda zaki je kisaya kayan babies sai a zaria duk kayayyakin kaduna bazaki siya anan ba sai a zaria?”

Tace:”eh”

Ganin kaman ranta nason 6aci kawai sai Umar tace toh muje nakaiki “

Hakan ko akai suka shiga mota suka nufa zaria!

Bayan sunzo Zarian ta sauka tabar Umar acikin motan dan dama ta shaida mai akan yana zuwa yana ajiyeta zai koma inta gama zata dawo da kanta,shidai baison yayi laifi hakan yayi yana ajiyeta abakin store d’in yayi tafiyan sa!

Ita kuma Zee ta kira tsohuwar inda ta shaida mata Salamatu na nan tana nak’uda yanzun haka Asibity zasu kaita,nan Zee tace su jirata gata nan k’ara sowa anchau d’in!

Mota taxi Zee ta d’au drop ya nufa da ita Anchau,har cikin gidan ta shugo akasa Salamatu a mota aka nufa asibity da ita.Chan wani private hospital Zee tasa aka kai Salamatun.bayan an amsheta akayi d’akin haihuwa da ita!

Zee kuma ta wuce taje ta sama wasu nurses agurin inda ta siye wata nurse a gurin da mak’udan kudi!

3hrs letter!

Bayan Salamatu ta haifa santalelen d’anta mai kama da Umar sak aka d’auka aka bama Zee!

Wacce ita ma ke kwancen akan gado kamar mara lafiya aka bata d’an duk da ta tsani yaron amman ganin kamannin sa da Umar yasata d’an sakewa ta runguma d’an tamkar ita tayi nak’udan sa.Salamatu kuma na chan wata duniyan na daban,bama tasan inda kanta yake ba dan an sake 6atar mata da hankalinta!

Nan Zee tasa tsohuwa ta wuce da Salamatu anchau!

Ita kuma tayi kane kane da d’a tamkar nata sai dai abin mamakin shine,bayan tafi yansu Salamatun,yaro ya fara ratsa kuka yana tsotsan hannu alaman yunwa yake ji.Nurse tace ma Zee ta bashi nono,ba musu Zee ta cire maman ta daga cikin bro ta fiddo shi ta gyara babyn yanda zaiji dad’in sha.Amman sai mai Zee tayi -tayi yaro ya amsa nono ya sha yaron nan yak’i sai ma cigaba da tsala kukansa na jarirai yake.Wasa Zee ta shiga mai wai ko zai amsa nonon amman fafur da Zee ta tusa mai bakin nono sai yak’i kar6a ya fiddo bakinsa.Kallan nurse Zee tayi itama Nurse din ta kalla Zee mamaki fes a fuskokinsu.

Zee kaman ta kwad’e yaron da duka haka takeji wannan in ace agaban Umar ne fa?yake nan?

“Nurse yaron nan fa yak’i kar6an nonon nan kodai haka yara keyi?in anfaifo su sabo?”

Girgiza kai nurse d’in tayi sannan tace:

“Abun da mamaki kam,wasu yaran kam basa za6an nono amman wannan naga kaman yasan abinda akai yak’i amsa “

Cikin narai-narai da idanu Zee tace:

“Toh nurse yake nan zanyi?mai abin yi?in yaron nan yak’i amsan nono na bansan ya zanyi bafa.”

Dagon lumfashi Nurse d’in taja sannan tace:

“There is only one way out (akwai hany’a d’aya tak)but kaman zaiyi wahala “

Saurin kallan Nurse d’in Zee tayi sannan tace:

“Nurse wani hany’a kenan?fad’imun am ready to do anything just to keep my secret ,koma mainene zanyi kud’i  ba matsala ta bace!ko nawane zan iya kashewa indai za’a samo mafita “

Nisawa nurse d’in tayi tana mai jinjina k’arfin hali irin na Zee ,amman yaza tayi an rigada an siye ta da kud’i!

“Hany’a d’ayan shine sai dai ki…………✍?

About AIS

Check Also

AMANAR MU CHAPTER 7

AMANAR MU CHAPTER 7 Www.bankinhausanovels.com.ng  “Laaa Zee yaushe kika dawo?” Humy ta ida maganar tana …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *