AMANAR MU CHAPTER 6

AMANAR MU CHAPTER 6

Www.bankinhausanovels.com.ng 

7:30Am

Tun farkon kiran sallan assalatu Humy ta farka dan yau sai taji dalilin sa na fita aiki da wuri,tashin Zee tayi domin tayi salla ita kuma ta wuce kitchen dan had’a breakfast,Zee ne ta shugo kitchen d’in ta iske Humy sai faman girki takeyi gashi gidan duk ya baje da k’amshin girkinta dan Humy ba k’arya gwana ce a iya girki!

Murmushi Zee tayi sannan ta k’araso cikin kitchen d’in bakinta na furta “Morning matar Faruq “

D’agowa daga wanke naman da takeyi akan sink tayi,ta zuboma Zeen many’an idanunta dake rikita duk wani wanda take kallo dasu lumfashi taja ba tareda tace uffan ba tamaida kanta ta cigaba da wanke meat d’in .Murmushi Zee tayi sannan ta k’araso inda Humyn take ta dafa ta sannan tace:”kiyi hak’uri in Sha Allah zamu san abinyi zamu naimo mafita “

Dogon lumfashi Humy tasake sannan ta girgizama Zee kai alaman ok dan yau d’innan sam sam bata son magana bakinta yayi nauyi!

Kafun 6:30 suka gama had’a komai suka jera a dining sannan Zee tasa Humy shiga tayi wanka bayan tafito Zee ta fiddo mata da kaya na k’ece reni tasa mata tamata kwalliya sosai Humyn tayi kyau dan ko mak’iyinta yaganta sai ya kyasa,fitowa sukai suka zauna a dining d’in suna jiran fitowan sa!

Wani kalan rikitaccen k’amshi ne ya soma karad’e falan kaman daga sama suka soma jin k’amshin turaren Humy ce ta kalla Zee tace:

“Kinji wani k’amshin turare kuwa kaman anbud’e kamfanin turare “

D’aga kan da Zee zatayi taga Umar ne da sauri ta ta6o Humy wacce hankalinta ke kan k’ofa tana tunanin ko yau tun kafun sallan assalatu ya fita?

Kallan Zeen Humy tayi signal Zee tama Humy da ido alaman ta kalla inda take kallo ,aiko bin inda Zeen ke kallo Humy tayi tsananin mamaki ne shimfid’e a fuskanta kallansa kawai take tamkar yau ta fara ganinsa a rayuwa!

Sany’e yake da wata dakakkiyar boyel dark blue anmai rigar d’inkin 3 qauter hulan kansa ma dark blue hakama ta kalminsa yayi kyau iya kyau ma sha Allah dan umar ba’a baya ba wajen kyau! Gashi sai tashin k’amshin turarukan oud yake .

Bin duk tafiyan da yakeyi suke har ya idasa saukowa daga matakalan benen,straight wajen k’ofan falan ya nufa yasa kansa yayi ficewan sa a gidan ko kallan inda suke baiyiba!

Mik’ewa Humy tayi da saurinta zata bi bayansa Zee tayi saurin rik’ota itama ta mik’e tsaye tana fad’in

“Ina zaki?”

“Zee baki ganin fita yayi ko kallan inda muke baiba? Ko breakfast baiyi bafa duk uban abinda na zauna nagirka ya tsallake yayi ficewan sa kiga fa yadda yaci kwalliya yayi fitansa tamkar baida mata a cikin gidansa “

Kamo hannun humy Zee tayi sannan ta k’arasar dasu cikin falan ta zaunarda Humy wacce hankalinta duk yana waje so kawai take taganta gaban Umar!

Dafata Zee tayi sannan tace “abin nan da d’aurin kai Humy nikaina na fara gasgata magananki any’a ba aljana bace ta shiga jikin sa ba?”

Share hawayen dakeson silalo mata a ido tayi sannan ta kalla Zee cikin muryan ban tausayi tace:

“Any’a Zee yaah umar ba naiman mata ya fara ba?! Any’a ba Emmata suka fara chanza mun shi ba? Kiga fa yadda yaci kwalliya da uban turare kaman wani wanda zashi gasan kyau “

STORY CONTINUES BELOW

Lumfashi Zee ta sauke dan gaskia itama wannan al’amari ya fara kwance notikan head d’inta tama kasa tunanin komai ta kasa saka Umar d’in a kowani mizani duk tunanin da tayi dan ganin ko harkar daya fara kenan sai zuciyanta yak’i amincewa dan tabbas indai Yaah umar d’in da suka sani a daa ne bazai aikata hakan ba!

“Humy kidaina zargin mijinki da bin mata ,kema kinsan Yaah umar babu wacce yakeso a duk duniya kaman ki,kidaina zarginsa sam kawai dai yazama dole mu tashi sama musan mai ya chanza sa all of a sudden “

Lumfashi Humy ta sake sannan ta kwantar da kanta a kafad’an Zee tana sauke lumfashi,ita kuma Zee tasa hannun damanta tana shafa bayan Humyn dan samomata natsuwa!

*********************************

Kullum haka Umar ya tsira yanzun baya dawowa sai 12 nadare kuma ko ya dawo ya tarar dasu a falan daga Zee d’in har Humyn basu ishesa kalloba totally ya chanza ma Humy tamkar ba shi bane Umar d’in dake mugun son Humy da tattalinta,haka da safe ma tun 7 yake barin gidan basu kuma sany’asa a idanu sai 12 Na dare,Humy ta mugun sa abin a tunaninta kullum cikin tunanin abinda ya chanza mata yaah umar takeyi baya bata face samsam bare ma har tasamu ta tambayesa dalilin da yasa ya chanza mata.Duk ta rame ta fige tayi baqi dan ma wai Zee na nan tana d’ebe mata kewa,Zee ce kawai ke kwantar mata da hankali gashi Zee tayi,tayi akira a fad’i masu Dady Humy taqi acewanta yaah umar d’in zai chanza maybe akwai dalilinsa nayin hakan!

“Harwani uban daliline zai sa shi yana halin wawanci Humy?kigafa ya chanza totally ko magana baya maki fa dakeda kashi duk d’aya kuke a wajensa,gaskia Humy da sake in bazaki bari na fad’i masu Dady ba wlh wlh gbe gbe zan tafi abj wlh sai na sanar masu “

“Zee……………

Tsakin da Zee ta buga tayi tafiyanta d’akine ya katse Humy daga maganan dazata fad’ima Zeen,girgiza kai kawai tayi tana roqon Allah daya kawo mata mafita!

******************************

2wks later!

Zaune suke kaman yadda suka sama akoda yaushe insun dawo daga aiki Zee ta kalla Humy wacce yanzun duk tadawo kaman wata figaggiyar Kaza duk tasa tunani a zuciyanta!

“Wash wlh Humy na gaji k’asusuwana ciwo suke “

Daria Humy tayi sannan tace “Allah kawo maki sauqi dai “

Murmushi Zee tayi sannan tace “Amin ameen “

K’amshin turarensa da yasoma karad’e falan ne ta tabbatar masu da dawowansa,kallan Humy Zee tayi sannan tace “yau kuma mai dawo dashi karfe 2 na rana?”

Kafun Humy takai da bama Zeen amsa ya idasa shugowa yau d’inma ko kallo basu ishesa ba yayi haurawan sa sama,yabarsu da binsa da kallon mamaki dasuka saba mai a kullum.

Humy ta lumfasa tace “Allah kaine Allah yaah Raab “

Itama Zee ta sauke lumfashi amman kafin bakinta ya furta wata kalma kaman wanda aka jefo kawai suka gansa a gabansu,da mamaki suka zuba mai idanu suna jiran jin mai zaice!

Kallansu yayi duka su biyun a k’ask’ance dan basu ishesa kallo ba wlh,ba tareda shakka ko tsoron abinda zai fad’a mata baya kalleta ido cikin ido yace:

“Aure zanyi,na fita hakk’inki karkice ban fad’imaki ba!”

Chak dukkanin wasu na’urori na jikinta suka d’auke na wasu secons bata so ta gasgata abinda kunnuwanta suka jiyo mata a yanzun so take ta k’aryata abinda kunnuwanta suka jiyo mata!

“AURE?”!

Da kyar ta iya had’a kalman aure ta furtasu a fili!

“Yes kaman yadda kunnuwanki suka jiyo maki,aure zan k’ara nanda sati uku “

“Innalillahi wa’inna ilaihir  rajiun hasbunallahu wal ni’imal wakil la ila ha illa anta subhanaka inni kunta minal zalimin “?

Shine kawai abinda Humy keta furtawa ga6o6in jikinta babu inda basu rawa tamkar mai rawan sany’i bakinta narawa taketa faman nanata wannan aduaan.Zee ko mutuwan zaune tayi kawai kwakwalwanta ya tsaya chak takasa koda kwakwaran motsi aduaan dataji Humy nayi ne kawai tasamu itama bakinta yasoma bitansu!

“Yaah Umar aure zakayi?aure zaka k’ara?mai namaka?mai nayi dazaka min kishiya wata 4 kawai da auran mu?eh wat did i do to deserve this frm u yaah umar??eh plss tell me mainama?u just changed all of a sudden and u kept queit baka mun magana baka had’a shimfid’a dani bare ka sanardani abinda nama! Yaah Umar shin haka *AMANARMU* zata kasance? Haka dama kad’au AMANARMU? Shin hofintar da amanan mu zakayi?ka manta alk’awarin dakamun ranar farkon auran mu?

_Humy kece sarauniyar matana a aljannah a kuma duniya kece kawai matar Umar_

Tell me Yaah umar kamanta da wannan maganan nakane?why why!why all this?mai nama?mai na rageka dashi?why me uhmm dan Allah tell me wat did i do wrong to deserve this wata 4 da aure sai k’ara kishia?ko ciki banda shi fa?Yaaah umar wat the hell namaka?tell me inason sanin abinda nama!”

Allah sarki Humairah duk zantukan nan da takeyi babu inda baya rawa a jikinta hawaye duk ya gama 6ata mata fuska she is just despondent ? (Allah saka maki Humy)

Kallan tsana Umar ya bita da shi sanan ya nunata da d’an ya tsa yace “toh uwata Naheedah kingama?nace are u done?ko nad’ako maki bulala ki zaneni ne?dan zuciyanki ya kwanta?aure dai babu fashi sai nayi!kina tambaya mai kika mun na sauya maki koh?if ke ba dak’ik’iya bace sai ki binciko wa’allah kisan mai yasa na sauya maki!Aure babu fashi sai nayi shi “

Daga haka ya waiga ya bankama Zee itama harara wacce itakam a wannan lokacin tamkar mutum mutumi ta dawo bama tasan da hararan tsanan daya mata ba! Yayi ficewan sa a gidan gaba d’aya zuciyansa fal farin cikin auran dazaiyi!

Lagwaf Humy ta fad’a kan kujera tama kasa sanin abinyi abu d’aya yake ta nana tawa!

“Aure…………Aure zan k’ara……..nanda sati uku! Aure…………”

Girgiza kanta ta shiga yi kaman mahaukaciya hakan ya dawoda Zee duniyan mamakin Umar data lula ,saurin kamo Humyn tayi ta rungumeta Humy kaman jira take kawai ta fashe da kuka tana fad’in:

“Zee wai kinaji Umar aure zaiyi ?aure wai zai k’ara kishiya zaimun Zee,mai namai?eh Zee mainayi zaimun kishia rana tsaka”

“Innalillahi wainna ilahir rajiun “

Shine abinda Zee ke furtawa lallai namiji ba d’an goyo bane wlh!

D’agoda Humyn Zee tayi ta shiga share mata hawaye Duk Humyn ta fara shid’ewa kaman mai shirin mutuwa!

“Lallai namiji ,kai maza tsinannu ne,namiji d’an kunama ne ,wlh wlh Humy innice ke sai Umar ya sakeni nabar masa gida wata 4 da aure har zai kuma aure ko ciki bakida faa kai amman maza basuda imani wlh “

Share hawayenta Humy tayi sannan tace “wlh Zee inason Umar inasonshi sosai bazan iya rabuwa dashi ba kuma bazan iya rayuwa babu shiba……..

Katseta Zee tayi tace:

“Ai gashi,shi ya nuna zai iya rayuwa ba tareda ke ba duk irin wulak’anci da rahin mutuncin da umar ke maki acikin gidan nan kice zaki zauna?”

Zee ta ida maganan cikeda tak’aicin Umar sam sam abinda yama Humy bai dace ba kuma Allah sai ya bimata hakkinta,bawai dan auran dazai k’araba aa saidai dan irin muzgunawan dayake ma Humyn.Muryan Humyn ce ta katse Zee daga tunanin da takeyi!

“Wlh Zee zan iya zama zan zauna dashi a hakan dan Humairah bazata iya rayuwa babu Umar ba amman ina jira bari naga wace tsinanniyar zai kawomin cikin gida……….Wa shegari da safe Humy ta tashi da matsanacin ciwon kai dan kwana tayi kuka raba dare tayi tana kai kukan ta ga ilahu.+

D’akinsa ta wuce ta iskesa kwance yana ta faman waya,yana zabga murmushi dake fidda asalin kyawunshi,wani kalan baqin kishi ne ya soma turnuk’eta dan babu ko shakka da mace yake waya da wacce zai aura yake magana sai faman langwa6ar da harshe yake yana magana kaman wani basarake,she cant handle it ji take wlh kaman zuciyanta zaiyi bindiga ya fashe.ita kanta ba zata iya cewa ga yadda akayi tayi diran mik’iya a kansa ba,daga ita har shi,ji kawai sukai wayar kunnensa ta fad’a a tiles tayi ragaraga,d’agowa yayi da sauri dan ganin wanda ya aikata mai hakan!

Ganinta tsaye sai faman huci takeyi kaman zaki,yasa shi mik’ewa fuskansa a had’e tamau baiko tsaya tambayanta komai ba ya tsinketa da marin da har saida jinta ya d’auke na wasu dak’ik’u ba tareda d’ayan marin ya saketa ba ya kuma wanka mata wani lafiyayyan mari.Wanda har saida ta fad’a k’asa,nunata da yatsa yayi sannan cikin muryan fad’a fad’a yace:

“Kee! Wlh muddin in baki fita daga harkata ba wlh saina illataki,ni sa’an wasanki ne ina waya kizo ki fisge ki yarmun waya ta fashe?saboda ke kika siyamun?wawiya jaka dak’ik’iya kawai,stupid human being “!

Daga haka ya tsallaketa yayi ficewan sa a d’akin ransa a jagule har ya mance ya d’au wayan tsaban tak’aicin abinda tamai!

Allah sarki Humy kuka kawai mai ban tausayi ta fashe da shi,tama rasa tunanin da xatayi yau itace Yaah umar ya d’au hannunsa har biyu ya wanketa da maruka? Bazata mantaba wlh sanadiyyar bugunta da Zee keyi lokacin suna yara shine ummulhaba’isin hassasa wutan k’iyayyar Zee a zuciyan Yaah umar d’in dan yatsana yaga hawayen Humy! Amman yau shine harda nunata da yatsa yace mata wawiya dak’ik’iya wannan abu da mai yayi kama?any’a zuba masa idanun da tayi ba tareda ta sanar masu dady sauyawan sa ba ta anfana kanta??wlh dole sai taje Abj yau yau d’innan dan yaah umar shine farkon karya record a family d’insu Na k’ara aure zata iya rantsewa tsaban boko daya ratsa danginsu kaf d’insu babu wanda yake k’ara aure ba ta ta6ajin ance mata kawunta wane ya k’ara aure ko antyn ta wacce anmata kishia ba!

Why sai ita?mai yasa yaah umar zai fara karya dokan k’ara aure a kansu? Shin wai damai ta ragesa a duniyanan?!

Saurin share hawayanta tayi jin k’araman wayansa dage side drawer na ruri,da sauri ta mik’e har tana tuntu6e wajen d’aukan wayan!

_My Zahraa _

Tagani rubuce 6aro6aro a screen d’in wayan saurin d’auka tayi danjin muryan shegiyar dake son aure mata miji har tayi sanadiyan sauyamata miji!

“Hayaty chajinka ne yak’are naji muna waya kiran ya katse,yaushe zaka zo kt d’in d’azun muna maganan kiran ya katse “

K’it Humy ta kashe wayan wasu zafafan hawaye suka shiga bin kuncinta wlh zata rantse muryanta yafi na wanan Zaraan dad’i toh muryan tane yake so komai?dad’i muryan Zahran tafi tata komai?”

Saurin shiga inbox d’in wayan tayi tasoma karanta messages d’in da suke turama juna babu wanda yafi tokare mata wuya kaman wanda yake cemata:

“Haba fatimatul Zahra’uta yau fishi ake da mijin pls am sorry kinji baran sake ba,pick my call I want to hear your damsel voice I love u so much “

Ai saurin wurgarda wayan akan gado tayi,tafito a d’akin da sauri dan wlh inta cigaba da karantawa saidai azo a d’auki gawanta,da sarsarfa ta sauko daga matakalan bene ,fridge d’in dining area tayi saurin nufa ta bud’e ta d’auki goran faro ta bud’e tasa a bakinta saida ta shany’e kaf tsabagen yadda zuciyanta ke tafarfasa da kyar ruwan sany’in ya soma saukan mata rahma,dafe kanta tayi sannan ta bar dining area ta wuce falo ta zauna bitar sunan yariny’an ta shigayi a fili:

STORY CONTINUES BELOW

“Fatimatul zahra’u, My Zahraa “

Muryan yariny’an ya kuma ringing a kwakwalwanta sam Muryan yariny’an ko dad’i babu amman shine a text d’in ya dage yana rok’anta Allah da annabi ta d’au wayarsa toh acikin muryan nata ubanmai zaiji?”

Mik’ewa tayi ta leqa windon falan dan ta k’osa tashugo tagaya mata abinda tagani!

“Oh plss Jabeer kabar Zee haka ta shugo yau dole abj zan kwana I cant take it”

Ta k’arashe maganan cikeda muryan kuka!

Jabeer da Zee ko suna zaune wajajen parking lots suna zuba soyayyarsu dan yau tun 12 Jabeer ya iso kd kuma straight yazo wajen sahibarsa!

Ganin Jabeer baida niyyan barin Zee gashi tanason yau la’asar ya mata a abj kar yadawo ya isketa a gida yasata dokama Zeen kira wacce itama ta k’agu tashugo ciki dan ganin halinda Humyn ke ciki dan taga sadda Umar d’in ya fito kaman zai tashi sama yashiga mota yajata da k’arfi ko gaisawa da Jabeer bai tsaya sunyi ba!

“Zee kizo ciki pls”

Humy ta ida maganar cikin kuka da sauri Zee ta katse kiran sannan tacema Jabeer “pls bari na shiga ciki gbe zanzo chan side d’in ma had’u”

Bata jira amsan sa ba tayi saurin rugawa ciki,Jabeer ko mamakin abinda yasata rugawa ya tsayayi!

“Subhanallah Humy mai ya sama fuskanki kinga shatin hannu a face d’inki kuwa kinga yadda Fuskanki ta kumbura?!”

Zee ta ida maganan cikeda tsoro da mamaki fashewa da kuka Humy tayi sannan ta karantoma Zee duk abinda ya faru! Tsananin mamaki Zee kasa cewa komai tayi wlh Umar yafara zarta zatonsu wlh yafara bata tsoro!

“Wlh Zee Abj zan tafi a yau bazan iyaba wlh na cigaba da zama a gidan nan wlh zuciyata zata harba zan matu wlh zanje na sanarma su Dady mutafi naje yau la’asar a abj zanyi “

Tana maganan tana hawaye tana jany’o hannuwan Zee alaman tazo ta rakata d’aki ta d’au kud’i,rik’eta Zee tayi sannan tace:

“Saida na fad’amaki tuntuni ai Humy musanarma su dady tun abinnan baiyi nisaba nake kwa6arki akan sanardasu amman kink’i ai gashi Umar zai samaki hawanjini a banza wlh k’arama dake ya illata maki zuciya dubeki yadda kika susuce kika dawo yanzun tamkar wacce batada jini a jiki,”

“Muje Zee muje plss karya dawo ya iskemu “

Nan suka wuce sukai duk abinda zasuyi suka d’au abinda zasu buk’ata suka fito suka tare adaidaita ko mai gadi basu fad’ima inda zasu ba straight station d’in jirgin k’asa suka nufa suka shiga suka wuce abuja!

**************************************

4:30pm

Daidai suka iso garin abj straight suka d’au taxi ya diresu har gida,shiga sukai suka iske Momy da mama zaune suna hira dan yau satuday momy bata je aiki ba Dady kuma da baba yau sun fita tare,!

Ganinsu kawai ko sallama babu sai ganinsu akansu sukai ko wacce kaman wanda aka cirema lakka ajiki!

Mama tace “lfy Zee da Humy?zuwa babu sanarwa?”

Momy ce ta k’urama Humy ido dan ganin yadda d’iyar tata tafige tayi duhu kaman wacce jini yayi k’aranci a jikinta!

“Magana fa nake kun wani tsastsayeni da idanu “

Ragwaf Humy ta zauna akan kujeran da Momy ke zaune ta d’an kwantarda kanta akan kafad’un momyn,Zee kuma tazauna akusada kujeran dake fuskantan su!

Haka kawai momy taji gabanta ya fad’i dan tasan Humy bata kwanto mata a kafad’a haka saidai in akwai babban al’amari da yasameta takeson sanar mata toh shine zata kwanta mata a kafad’u da kyar momy tace:

“Humy mai ya sameki?ina Umar ba tare kuke bane?”

A tak’aice Humy tace:

“Aure zai k’ara “!

STORY CONTINUES BELOW

A take Momy da mama suka had’a baki wajen fad’in:

“Aure! Zai k’ara?”

Gyad’a kai kurum Humy tayi dan wlh ba tada k’arfin magana,kallan Zee su mama sukai alaman suna son k’arin bayani,.Aiko dama ita Zee abunda take jira kenan ta sanardasu A-Z duk abinda Umar kema Humy har izuwa marinta da Yayi!

Sallalami su Mama suka shigayi mamaki fal ransu ganin kaman Humyn na lumfashi a fisge a fisge yasa Momy cewa Zee takaita d’akinsu ta samu tayi bacci anjima insu Dady sun dawo sai ayi maganar!

********************************

“Tabbas nida kaina na nema ma Umar auren da zai k’ara Humy da sanina akai ,inada masaniya akai dama kobakizo abujan yauba inada niyyar turawa akawomin ke dan maki nasiha dabaki shawarwari “

Sororoo kawai Humy ke bin mahaifin nata da kallo dan bataga inda zata sa zantukan nasa a kwakwalwanta ba brain d’inta sunk’i fahimtan mai ya fad’a any’a kuwa ba manta watannin auranta da UMAR yayi ba?wata 4kawai fa da aure za’a mata kishia amman shine mahaifinta ke cewa shida kansa ma ya naima ma Umar d’in auran tirk’ashi! Wannan shine ake cewa gaba da gabanta!

“Dady aure faa yaah UMAR zai k’ara kuma dady karka manta watanmu hud’u ne kawai fa da aure amman shine Dady zakace kaine ma dakanka ka naima masa auran?”

“Dakata Humy kinga ni bazan hana Umar k’ara aure ba saboda bani keda ra’ayinsa ba dan haka ki tattara kikoma gidanki gbe banson shashanci “

Daka haka Dady ya sany’a kansa yayi ficewa a falan!

Fad’awa jikin momy Humy tayi tana kuka tace “Momy kinji abinda dady fad’a kuwa?kinfaji cewa yayi shima ya goyi bayan Yaah umar ya k’ara aure!

D’agata momy tayi sanan tace “wai nikam Humy kanki ne farau k’ara aure?ko kuma kinyi yar jejeniya da Allah cewa ke kad’aice matar Umar? Kece kawai aka ta6a k’arama aure da wuri?anji bai kyautaba yayi saurin k’aro aure amman ina ruwanki?akanki zata zauna?ko kuma kece zaki ciyarda ita?kowa da halinsa zai zauna! Dan haka kiyi maza ki koma d’akinki dan mukam bamuda abinda zamu maki anan d’in dan ko nan kikazo kika tare umar kam auransa zaiyi!”

Daga haka momy ta mik’e tabar falan!

Tunda momy tasoma magana Humy ke binta da kallan mamaki iyakar gaskianta take fad’i kawai take gani a idanun momyn Yaah salam wat all this wai mai haka?iyayenta ma sunbi bayan umar har suna ce mata bakanta farau kishiya ba!

Da kyar ta iya bacci ranar dan sai take ganin abubuwan duka tamkar a mafarki!

Washegari ta kira Yaah Khaleel da yaah fareed tasanar dasu dan tasan if iyayenta sun goyi bayan umar sukam bazasu goyaba amman to her suprise suma umar suka goyama baya sukai mata fad’a tas akan ai ba ita kad’ai aka soma yima kishia a duniya ba sosai suka ruk’a mata fad’a suna ce mata to mainene idan Umar yace zai k’ara aure da ita kawai take so yazauna?”

kaman basu bane yayyinta dake mugun k’aunanta sai take ganin kowama ya juya mata baya!

Wannan wacha kaliyar masifa ce?”

Dafata Zee tayi sannan tace “komai yayi Zafi maganinsa allah Humy ki tashi mu koma Kd Dady yace kar yadawo ya iskemu a gida kibarsu,su fifita soyayyar umar akanki dan kawai ana su ganin faranta ran maraya sukai “

Hakadai Zee tasamu ta ta lalla6a Humy suka shirya suka dawo kd!

Koda suka sauka a station adaidaita sahu suka hau suka ce masa malali!

Basu mintuna 30 ba suka isa anguwan nasu daidai suka hangosa zaune akan motarsa yana waya yana lumshe idanu alamun yana magana da Fatima zaraa kenan!

Da kyar Humy ke had’iyan yawu shiko kaman ance ya d’aga kai kawai ya hangosu cikin napep nan da nan fuskansa ta chanza kashe wayan yayi ba tareda ya mata sallama ba ya diro daga kan motar tasa idanunsa har sanja launi sukai zuwa jaaa tsaban fushi!

Gaban sune ya shiga dukan 3 uku ganin yana damfaro inda suke ,ai bata kaiga fitowa daga cikin napep d’in ba ya fincikota daga cikin napep d’in sannan ya damqota yace:

“Daga gidan uban wa kike?”

Muk’ut ta had’iya wani zazzafan miyau dan dama ita fil azal akwaita da tsoro barin yau ace Yaah umar ne maa dakansa

Ya tsoratata  sosai, dan yanda ya rikid’e ya zama kaman wani mayunwacin Zaki tsaf sai yama kowaye lilis barin ita dake damqe a hannunsa da kyar tace:

“Daga Abj nake “

“Da izinin uban wa kika tafi chan abujan?”

Bai jira ta basa amsaba yad’auki hannunsa ya shafta mata mari sannnan ya hankad’ata,ta fad’a k’asa ya kuma damqota ya shiga kaimata duka a ko ina ya sama dama!

Zee kasa sanin abinyima tayi shin tayi ihu ne akwawo masu d’auki kota d’au dutse ta bigamai a kai?ganin babu kowa a layin mai napep ma ya gudu yasata k’arasowa da gudu ta shiga tsakaninsu !

Cikin d’aga murya tace “Wai mai haka kake wani dukanta kaman mara gata “

Shima cikin d’aga  murya yace:

“Kimatsa awajen nan nace maki “!

“Baxan matsaba wlh saidai ka had’amu kaduke mu amman baxan matsaaba………haba wai shin baka ganin abinda kake ma yariny’anan ba kyau bane ?duka hakan basu ishekaba harsai ka ruk’a had’a mata da duka kaman baiwarka “

Kifa Zeen da mari yayi sannan ya shureta ta fad’a akan Humyn dake k’asa tana gabzar kuka kaman zata shid’e!

Wucewa yayi,ya shige mota ya tada yabar layin tareda barba d’esu da k’urar motarsa!

Zee kuka Humy kuka ganin ba mai lallashin su ,Humy ta rungume Zee wacce duk a dalilinta Umar ya mari Zeen dakyar suka iya shiga cikin gidan ko wacce na zubda hawaye!

Zaunarda ita Zee tayi sannan ta goge hawayenta tace:

“Kiyi hak’uri Humy haka halin ‘ya’ya maza yake,sai ka sakankance ka basu amananka k’arshe su watsama ruwa a ido wlh duk maza ba ‘yan goyo bane.Allah zai saka maki “

************************************

Koda ya dawo gidan iskesu yayi zaune Humy na kuka Zee na hawaye tana lallashin Humyn tsaki yayi sannan yad’aga murya yadda zasu jiyo shi yace “kuma kisani aure babu fashi nanda sati biyu chur zaa d’auramun aure kiyi duk abinda zakiyi aure ba fashi……………After one week!+

Abuja!

Mama zaune akan kujeran tsakar gida tayi tagumi da Hannun daman ta,tana tunanuka kala kala!

Jin ihun mutum dakuma buguwan mutum ya sata mik’ewa da sauri ta nufa wajen da ta jiyo k’aran ihun!

“Innalillahi wainna ilahir raji’un Baban zainab lfy ?!”

K’arasowa tayi da gudun ta wajen Baba dake kwance ruf ak’asa,salati kawai Mama ta shiga yi ganin Baba ya kasa koda motsi ita azatonta ma mutuwa yayi,ai da saurinta ta fito daga part d’in ta wuce part d’in su momy.Ganin mama cikin tashin hankali yasa momy da dady dake zaune suna firan yadda bikin umar zai kasance dan yau kwata-kwata saura 1wk d’aurin auren,da hanzarin su suka tarbo mama suna tambayanta mai yafaru itako mama sai nuni take masu da hannunta,tana kuka takasa magana tsananin tashin hankalin da take ciki! ,da sauri su Dady suka rantamo part d’insu mama iske baba sukai akwance baya koda motsi tamkar gawa,da sauri Dady ya shiga bubbuga shi amman shuru babu alaman lumfashi a tattare da baba da gudu dady ya kirawo masu gadi suka d’au mai baba akasa shi a mota suka wuce asibity da sauri,mama kam babu abinda takeyi sai disgan kuka,yau in baba ya rasu inazata sa kanta?mai faru dashi har yayi irin fad’a wannan?taga dai lafiya tabarshi a falan yana kallo toh mai ya faru? Tunowa da babu abinda yafi k’arfin Allah a dak’ik’u da baza su wuce biyu bama zai iya jarabtan bawa da koma mainene,yasata saurin kauda tunanin ,ta shiga adu’a a ranta!

Dasauri likitoci suka amshesa akayi Hany’an emergency da shi sukuma suka tsaya a bakin k’ofan d’akin kowa da abinda yake tunani a ransa!

**********************************

Kaduna!

Suna zaune fiki fiki ko wacce abinda yake zuciyanta ta fahiceshi ,dan Humy kam in ka mata kallo d’aya tak bama zaka sake son kuma kallanta ba,tayi rama kullum aikinta shine kuka ba tada aiki sai kuka da rok’on Allah mafita a irin yanayin data riski rayuwanta!

Yanzun kam yaah umar zata iya cewa tunda auran nasa ya matso baima cika kwana a kd ba tafi zaton yana katsina tunda a chan amaryar take,tun tana damuwa har tazo ta daina saka abin a ranta tunda taga da gaske fa Umar aure zaiyi ita dai yanzun nata shine zuba masa idanu tunda bata da hakkinsa tasan rabbi zai saka mata!

Amman kam tsananin chanzawan Umar kullum yana liqe a zuciyanta da shi take kwana take tashi,kowai zata iya d’ago abinda yasa shi sauyawa amman inaa ta kasa!

Bugun wayan Zee da’ake  yine yasa su dawowa duniyan tunanin da ko waccen su ta fad’a ,da sauri Zee ta kai dubanta kan wayan momy ke kiranta hakan yasa ta kallan Humy wacce itama Zeen take kallo sannan daga bisa Zee ta danna answer tace:

“Hello momy “

Cikin muryan tashin hankali momy tace:

“Zee kuyi maza -maza kuzo Abj yanzun nan jikin Babanku ya motsa muna private hospital abuja emergency room “!

Ai zee bata bari momy ta idasa fad’in sunan asibitin  ba,ta kwala wani uban k’ara had’ida wurga wayan tana furta sunayen Allah duk wanda yazo bakinta!

Da sauri Humy ta matso wajenta cikin tashin hankali ganin yadda Zee ta rikid’e a lokaci guda tace:

“Zee mai faru eh?waya kiraki?”

Kuka kawai Zee ta fashe da shi mai tsuma rai sannan tayi zaman dadiro a k’asan tiles d’in falan,tama kasa sanar mawa Humy abinda ya faru! Ganin Zee bata fad’in komai yasa Humy saurin zuwa wajen da Zee tayi wurgi da wayan tayi saurin d’auka call logs ta shiga dan ganin wanda ya kira Zeen ganin Momy ne yasa gaban Humy fad’uwa ras-ras dan wlh babu abinda tunaninta ya zomata face yaah umar yayi hatsari dan tasan yayi tafiya,kuma inba bad news momy tasanar mawa Zeen ba k’aramin abu ke gigita Zee,dasauri hannunta na rawa ta danna kiran momy bugu d’aya momy ta d’aga murya na rawa Humy tace:

STORY CONTINUES BELOW

“Momy mai yafaru?”

“Babankune jikinsa ya tashi wlh yanzun haka muna emergency room rai wajen Allah “

Sosai Humy ma ta rikid’e bugun zuciyanta ya yawaita innalillahi wainna ilaihir rajiun taruka nana tawa kafin ta fashe da kuka,Zee nayi itama tanayi aka rasa mai lallashin wani,Humy ce dai tayi ta maza ta shiga consoling Zee da kyar, Zeen sai kuka take suka shirya suka wuce abuja!

Ko acikin jirgin ba abinda Zee keyi sai risgan kuka ace yanzun son da takeyi iyayenta suyi kud’i yana son rushewa saida takusa cinma burinta sannan mahaifinta zai kuma fad’awa wani rashin lfyn rai wajen Allah,duk wlh saboda wannan auran da Umar zai k’ara ne yasata zaman kd dan bama Humy baki if not Humy zata iya zaucewa tunda har iyayenta da yayyinta sun juye mata baya! ,sai take ganin tamkar da’ace tana abj duk hakan bazai faru ba! ?(kuji fa)

Koda suka isa asibitin likitoci basu fito ba , itakam mama sai take ganin kaman mutuwa mijin nata yayi shiyasa likitocin ke 6oye masu suka k’i fitowa!

Zee kam sai safa da marwa take humy kuma tun gaisawan dasukai da kowa ,tasama guri tayi zamanta ta zabga tagumi tana tunani wanda yazama abokinta yanzun!

Saida likitoci sukakai kusan 2hrs akan baba sannan suka fito duk suna zufa,Dr mansur shi yamasu bayanin akan babu abinda ya sama Baba kawai dai akwai tunaninda yasa aransa da yak’i cirewane shine ya hassasamai hawanjin kuma suna tsanmanin Hawan jinin nasane ya tashi shiyasa ya kasa resisting kafun akawo mai d’auki ya fad’i sudai jira farkawan sa a gani takun!

Hakan ko akayi kowa yayi zaman jugum jugum ana jiran farkawan Baba!

In taqaice maku dai a asibityn mama,Zee,Humy suka kwana Momy da dady suka koma gida!

Sai washe gari misalin 9 na safe Baba ya farka amman anyi anyi yayi magana ya kasa kuma yakasa motsa dukkan nin ga6o6insa tamkar gawa,dan ko babu mara bansa da gawa!

Da ido kawai yake binsu da kallo Zee ya kafe da idanunsa ganin yadda duk ta shid’e sai kuka take tama rasa yadda zata fassara wannan al’amuran dake dunfano rayuwansu itada Humy!

Likitoci sun duba baba sannan sukace zasu basu gado amman in abin yak’i saidai sukoma suyi na hausa wa’allah adace dan sun kasa binciko abinda ya hassasa rashin maganansa!

Humy yau tayi shirin komawa kd dan kar umar yadawo ya iske bata nan dan yau sora 6days bikin nasa,Tabar Zee a chan asibitin dan tace zata zauna tayi jiny’an mahaifinta sannan tama Humy nasiha sosai akan ta kwantarda hankalinta akan umar ta fiddashi a lamuranta yanda shima ya watsar da ita daga lamuransa,mama itama tamata nasiha kuma tace karta damu in sha Allahu rabbi zai saka mata!

Yanda iyayenta suke wani shashareta yafi tsaya mata awuya dan harta dawo ko maganan auran umar ko kwantar mata da hankalinta sam basuyi ba iyakarsu gaisuwa shima sai take ganin ba kaman yanda suka saba amsa mata bane!

*****************************

Koda ta dawo gidan bainan hakan ya sata wucewa d’akinta tayi zamanta a chan!

Tsuramata idanu yayi yana kallanta sannan a hankali ya idasa shugowa cikin d’akin ya kira sunanta:

“Humairah mik’e kizo ina jiranki a falo “

Daga haka yasa kansa ya fita a d’akin binsa da kallo tayi tana mamakin yaushe ya dawo gidan kodama yana nan ne?”

Saurin zuwa falan tayi gudun kartayi laifi yanzun nan ya duketa dan yanzun yin hakan agaresa mai sauk’ine !

Tunda ta shugo falan take bin kayayyakin dake zube a center carpet d’inta take da kallo har tazo cikin falan tanaima guri tazauna ba tareda tace masa uffanba ganin ba tada niyyan masa magana ya sashi gyaran murya sannan ya dubeta yace:

“Abincine baki ci komai?duk kin tsustsuke kaman wata kwashoko,mtseww anyways ba wannan bane a gabana abinda yasa na kirawoki shine,dama akwatunan danna k’irji, na bid’an kishiya na kawomaki gasunan,sai ayi fitan biki dasu “!

STORY CONTINUES BELOW

Ya ida maganan yana kawarda kwayan idanunsa akanta yana mai nuni da akwatunan!

Bin akwatunan tayi da kallo akwatuna ne many’a guda uku,ta6e baki tayi dan sai take ganin anata bikin akwatuna har nawa ya mata haryau zata rantse bata bud’e sauran akwatunan taba bare tasa kayan ciki,shine wani yanzun zai zo mata da akwatuna uku yace mata wai kayan danne k’irji nabid’an kishiya, wlh umar ya mugun raina mata wayau!

Jin batace uffanba ya sashi mik’ewa had’ida fad’in “yau saura kwana 5 bikina”

Daga haka yasa kai yayi ficewansa a gidan!

Ko kallan akwatunan bata sake yi ba tasa kanta saman kujera ta fashe da kuka mai ban tausayi

“Bakomai yaah umar kaje lokacine “

Ita yanzun tama cire abin aranta ta mik’a ma Allah lamuranta!

***************************

2days to the wedding!

Ana saura kwana 2 bikin shar Humy tasoma danne zuciyanta take walwalanta kuma tana fita wajen aikinta inta dawo takira Zee awaya dan jin lafiyan jikin baba Zeen ke shaida mata an sallamesu sundawo gida dan likitoci sunce sun kasa gano abinda ya sany’ashi rashin magana ba dan sunmai test komai yana nuna positive,yanzun ma haka mama tace garinsu chan zamfara zasu koma ayi na hausa ko Allah zaisa adace!

Sosai Humy ta tausayama Baba ita sai take ganin tamkar Baba yanada wani mak’iyine dake dagule rayuwansa bai son yaga cigaban baba shi yasama achan baya yasan maybe yadda zaiyi EFCC suka kwace dukiyoyin baba,yanzun kuma da yaga baba yasama lafiya zai iya kuma tsundumo wa cikin kasuwanci again yasa maqiyin nasa kuma durk’ushe rayuwansa!

Kai Allah rabamu da hassada ameen!

Mik’ewa tayi ta shiga toilet dan tayi wanka dan yau ta d’ebo gajia a office!

Fitowanta daga bayi sai tashin k’amshi sabulun wanka take,goge gashin kanta data jik’ashi da ruwa takeyi da d’ayan towel d’in dake hannunta!

Tsaye tagansa bakin k’ofanta yana wani k’are mata kallo yana lasan le6en sa kafun tayi wani tunani kawai tagansa a gabnta kafun kuma tayi wani aune tajita kawai akan gado ya shiga cukurkud’ata iya san ransa daga k’arshe yaci k’arfinta ya sadu da ita!

Ganin ya biyama kansa buk’ata yayi nak ya tashi yayi wucewansa d’aki yayi wanka had’ida fita a gidan gaba d’aya dan yau zai bar kd ya wuce chan inda zaa d’aura auransa (garin matar) nanda kwana 2! Dan abokansa ma jiransa suke a chan guest house d’insa dan tafiya!

Humy taci kuka harta gode Allah,da kyar ta iya mik’ewa dan yau yamugun chukurkud’ata (niko nace yau she gamo ai dole umar ya zage damtse ?ya baki wedding gift)

Wankan tsarki tayi sannan tacika sink d’in wanka da ruwan zafi ta shiga gasa jikinsa sosai.Saida tasama natsuwa sannan ta fito da kyar tana jin relive a jikinta.!

*******************************

Yau take salla wajen Umar faruq bakinsa har baka dan yau ana saukowa daga masallacin jummaa zaa d’aura masa aure !

Tunda yayi mata fin k’arfin nan ya sadu da ita daga ranar bata sake ganinsa ba!

Yau jummaa kuma tasan yau ne ranar d’aurin auren nasa!sosai taci kuka amman taruk’a roqon Allah akan yasa mata sassauci acikin zuciyanta,ita babu abinda yafi bata mamaki ma sai rashin kira da iyayenta da yayyinta sukai akan auran nan wai su bata baki sam inbanda Zee da suke waya babu wanda yake kiranta awaya totally qilama hidiman bikin Umar d’in momy da daddy suke shiyasa ma basuda lokacin kiranta su bata baki,sai take ganin itafa tamkar yanzun ma iyayenta sama sama suke damuwa da ita.Basu naimanta sam!

Ta rasa wannan wata kaliyar rayuwace ta tsinta kanta aciki!

Ringing d’in wayan tane ya katseta daga tunanin da takeyi share kwallan idanunta tayi sannan ta d’au wayan

Bak’uwan lanbace hakan yasata d’auka ammanjin muryansa sai ya tabbatar mata dashi ne ya kirata,ba tace masa uffanba sai taji yana ce mata:

“Yau an d’auramun aure da abar k’aunata farin cikin zuciyata,kuma yanzun haka ana kan hany’an kawomun amaryata zuwa gidana,sai ki tsaya ki tabarba k’anwar taki kuma abokiyar zaman ki “

K’it ta kashe wayan dan inbaiyi wasa ba wlh yadda takejin kanta a yanzun zata iya antayomai ashar d’inda har ya mutu bazai mance ba katse kiran shine zaman lfyn su!

Mik’ewa tayi ta d’au gelenta tayi ficewanta zuwa gidan mak’otansu dan Wlh ba zaman da zatayi acikin gidannan da sunan wai zata tarbi kishiyanta!

Dan kam sai ma dare zata shugo gidan yanda ma baza taga abin tashin hankali ba!

Masu kawo amarya ankawota ansha shagali aka juya akabar amarya agidanta!

Sai wajajen 10 na dare Humy ta dawo cikin gidan lokacin ba kowa kallan d’akin yaah Umar d’in tayi sannan tayi saurin d’auke idanunta dan ta tabbata yanzun kam suna ciki da amaryar tasa sanan kuma tasan ba naimanta zasuyi ba hakan yasata shigewa cikin d’akinta cikeda baqin ciki ranar kwana tayi salla tana rok’on Allah ya kawomata d’auki acikin wannan k’angin data tsinci kanta!

**************************

Washegari

Wanka tayi abinta tasa doguwan riga ta chanchara d’aurin ta ,Amman ko hoda bata murza ba balle tasa kwalli a idanun nata ba kitchen ta wuce ta d’aura abinda zatayi kari dashi,ranta fal mamakin ita amaryar agarinsu ba’a had’o amarya da kayan kitchen bane ko kayan falo ko kuma maybe a part d’in bak’i aka danka mata kayan nata oho dai ita bai da meta ba!

Bayan tagama toastin bread d’inta ta soya kwai sannan ta tafasa ruwan tea ta had’a komai da komai ta fito ta zauna akan dining tasoma cin abincinta!

D’agowa tayi ta zuba mata idanunta, kwalliyanta tayi cikin wasu shegun english wears tayi shar shar da ita tayi kyau kam!

Cikin murna da farin ciki Humy ta mik’e ta iso gareta tana sakan mata murmushi harta k’araso wajenta sannan tace:……………….??‍♂️✍?

About AIS

Check Also

AMANAR MU CHAPTER 8

AMANAR MU CHAPTER 8 Www.bankinhausanovels.com.ng  Bud’e idanuwan ta tayi tagan ta cikin wani irin  yanayi. …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *