ABU A DUHU CHAPTER 3

ABU A DUHU CHAPTER 3

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin kidima azra ta ajiye call din da tayi receiving ta tsala ihu.. a rikice mummy ta shigo dakinta tace ke azra lafiyanki???+

Azra tace mummy he had an accident.. mummy because of me..

Mummy kitaimakeni..haitham .. haitham.. kawai se tafadi a wurin sumammiya..

Mummy da tagama rudewa se salati take tayi tace ta rasu..shikenan Alhaji babba yayi sanadiyan mutuwan tilon diyata.. shikenan.. a guje taje tasami baban azra tace shikenan burin dan uwanka Alhaji babba yacika.. azra dai ta mutu.. shima haitham din ance yana can yayi hadari..

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai ya iya furtawa.. yace ina azra din? Mummy ta nuna masa hanyan dakinta.. cikin sauri qafafuwansa na hardewa har ya iso ga qofan dakin yace azra.. azra.. shiru..sede da alaman low heart beat.. da ya ciccibeta se asbiti nan take aka bata taimakon gaggawa tadawo cikin hayyacinta wuf tamike tace Abba ina haitham.. Abba number na ne farko a wayarsa ni aka fara sanarwa..

Abba Kar kucemin ya mutu..

Kunji abba..

Da Jin maganarta kunsan a kidime take..

Haka tayi ta musu sunbatu na tsawo kwana biyu kan kuma ta tafi axumin magana.. dan azra tadena magana da kowa.. sede tabisu da Ido tagama zaucewa..

Fannin shikuma haitham bayan ankira azra akaji shiru Sai aka Kira mahaifiyarsa.. kan kace kwabo se ga danginsa sunzo, shima saida yayi kwana biyu yafarka kuma azra kadai yake furtawa..

Ansallami su azra sundawo gida bayan an tabbatar komi nata lafiya.  Haka shima haitham an sallameshi sauran jinyan hannu..

A en kwana kin nan in kagansu duka kasan sun canza.. Abu kaman hadin baki sun daina cin abinci.  Kullum azra se kuka shikuma haitham ba walwala.. komi nasa ya ja baya..

Yau ma kamar rannan azra ta tashi kenan zatayi sallah se ganin ta sukayi sumammiya.. ankoma da ita asbiti sunce damuwa ce yai mata yawa kuma zuciyanta na gab da failing.. a taimaka a riqa kwantar mata da hankali.. likitar ta tambayi ko sunsan dalilin shiganta wannan yanayi??

Mummy ta amsa da yes dr..

Likitar cikin Mamaki tace shine Baku magance mata ba? Menene musabbabinsa da aka kasa maganceshi..inji likitar..Mun san matsalarta likita.. soyayyace Amma iyayen ta Maza sun haramta mata, ya zamuyi!

Ya zakuyi?? Inji Dr.. yazakuyi fa Kika ce? Kin gwammace kenan diyarki ta mutu? Wallahi to ni dai a shawarce nabaku Shawaran gaggauta yiwa yarinyar nan abinda takeso  in dai be sa ba Sharia ba.. mummy ta numfasa tace Dr. DanAllah kitaimakeni in Abbanta yazo kiyi masa explaining vividly, may be musami dacewa..

Dr tace inshaAllah, Amma in ba abin su bama ai an daina yayin auren dole. Allah dai yasa a gane..+

Kamar yadda mummy kanemo dr. Da tayi hakan kuwa dr.rahima tayiĜŒ tasami daddy tayu convincing dinsa sossai, akan ya amince wa azra da zabin ranta, su su hakura,takuma bayyana mishi halinda Ake ciki kuma ta qara da cewa  lallai lallai in ba a barta ta auri Wanda takeso ba za a iya rasata gaba daya..

Abba ya gode yace inshaAllah zaiyi Qoqarin samun dan uwanshi su tattauna..

Abba ya Sami danuwansa Wanda suke Kira da baa kura ko alhaji babba, da wannan zancen.. se dai kash Abu baiyi dadiy ba dan wannan shine sanadiyyar fadan Alhaji babba da Abba, domin alhaji babba gani yake abba kawai ne bayason a aurad da azra ga danshi. Dama dan nashi na da matsalar shaye shaye,shine yaso ayi auren tuwona maina a rufawa juna asiri..

Abba na barin wurin Alhaji babba ba inda ya nufa se gidansu haitham.. sun masa tarba na mutunci in da yake shaida musu cewa yazo ne yabasu hakuri kuma ya amince ayi auren wadannan masoya guda biyu nan da sati daya..

Cikin Mamaki haitham ya tashi yayi sujadar godiya, yakuma godewa Abba. Tuni ya mance da ciwon da yake yi,  dama har an ware hannunsa..

Kowa na farinciki da walwala a gidan dan Basu da farincikin da ya wuce suga haitham na walwala..kasancewarsa mutum ne me barkwanci da raha ga kirki ga son jama’a..

Bari mudawo ga azra..

Ita kuma azra labari na isowa gareta se miqewa tayi tsam.. ji take ciwon da take ji a zuciyarta kaman an wanke mata shi TAs.. se tafaara kuka farin ciki a take kuma ta rufe fuskarta wai kunya(nace bayan me..lol).. ta qara kwana biyu a asbitin har se da aka tabbatar ta wartsake aka sallameta tare da bata shawarwari masu amfani Wanda ciki harda tarage sa damuwa a ranta..  biki saura kwana 5 inshaAllah .. shiri akeyi ba kama hanyun yaro. Mummy zata aurad da er tilon diyarta me hazaqa tarbiyya kyau da nutsuwa…

Anshirya yin

events kala kala abin ba a cewa komai

Yau ya kasance ranan asabar ashirin  ga watan Maris shekara ta dubu biyu da shida ,rana ne ta tarihi ga masoyan nan biyu wato azra da haitham, Aranan aka saura auren su Wanda farincikin su a bayyane yake, kowa ya shaida, andaura aure ankai amarya gidanta da ke Old G.R.A circular road na nan garin Maiduguri.

Gida yayi kyau tabarakallah MashaAllah, an watse Anbar amarya da ango bayan en shawarwari da nasihu da akayi musu..+

Rayuwa ce tsaftatacciya cike da so qauna da kulawa, ba Wanda zai ga ma’aurata biyunnan baiji sun burgeshi ko sun bashi sha’awa ba, kuma duk hakan yafaru ne sabida tsananin so da qauna da suke wa juna da kuma haquri and tolerance above all.

Kwanci tashi ba wuya Allah ya albarkaci azra da haihu war baby girl, son duniyar nan Azra da haitham da danginsu sun daura akan baby afra. Rayuwa ta cigaba , abubuwa na ta faruwa Amma soyayyar nan ta azra da haitham kamar qara musu akeyi, Basu sake haihu wa ba se bayan afra tayi shekara biyar, ansami Diya mace me suna amra..

Kwanci tashi ba wuya inji bahaushe ,  amra shekararta daya yanzu

About AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *