ABU A DUHU CHAPTER 1

 ABU A DUHU CHAPTER 1

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Azra yarinya er kimanin shekara 18 da haihu wa taci kwalliya cikin lashinta, Wanda yayi dai dai da jikinta, yakuma fiddo da asalin kyaunta. Azra chocolate colour ce irin kalan nan me dauke hankalin me kallo, tana da dara daran idanuwa mashaAllah, da hancin ta me kyau haka ma bakinta yaje dai dai da fuskarta, tana tsawo ma tsakaici ,komai nata tabarakallah MashaAllah bugu da qari me nutsuwa ce me kuma alkunya..+

Tashirya ne zata tafi bikin qawarta Fatima , Amma kash se dai driver dinsu bayanan kuma bata iya driving ba ga momynta bata nan haka nan de ta hakura ta yanke shawarar Hawa taxi ta tafi.

Tafi awa daya tsaye akan titin nan bata ga me taxi ba ga kuma hadari da alama Ana Shirin ruwan sama ne, sannan kuma zuciyarta bata amince mata da ta hakura da zuwa auren nan ba, nan take wata dabara ta fado mata, waya ta lalubo ta Kira amaryar tace sis fatima wallahi bansami me kawoni ba har yanzu inaga kawai karkujirani kucigaba da shirye shirye..

Daga can bangaren amaryan tace: habba de sis azra kinsan dai wallahi wannan bikin bazai taba armashi ba in ba ki, Amma barin Kira Ahmad(ango) ya aiko a daukoki, dnt worry just a minute..

Suna katse wayar juyawar da zatayi kawai ganin wata mota tayi a tsaye a gefenta, da alama yajima da tsaya wa awurin, yace As salamu alaiki baiwar Allah. DanAllah ina tambaya..

Tace wa alaikumussalam, Allah yasa nasani..

Yace kimma sani sede ko in zaki Qi fadamin.. tace ah ah wallahi zan fada maka in nasani..

Yace sunan baiwar Allah da nake magana da ita nake son sani.  Se kuma ina zata tafi domin in rage mata hanya…

Murmushi azra tayi tace sunana azra ,nafito ne zani bikin qawata. Nagodeh .. tana kawowa nan tawuce,yana cikin binta yana jimana Sai ga me adaidaita sahu, tana ganin sa tace Alhamdulillah Lagos street zaka kaini, yace 200 tace muje ba matsala..

Haitham hankalinsa tashe yana tunanin ai ta kubce masa ina zai sake ganin ta? Take dabarar binsu yafado masa.. da sauri yabisu har suka Isa gidan bikin..

Haitham na waje yana jiran fitowar azra tin da tabiyo su tin karfe goman safe gashi yanzu har hudu ta gota..

Nan yayi sallah yana jiranta aiko Sai gata sunfito rakiyar wasu qawayensu..

Yana ganin ta ya miqe tsam yace azra.. azra.. cikin Mamaki ta waiga tana kallonshi.. tace mallam lafiya kake Bina haka? Me namaka??

Yace lafiya ba lafiya.. dam zuciyarta ya fadi.. ta zazzaro idanunta masu qara rudashi tace me me yafaru?

Yace wallahi kin sacemin zuciyata..

Please kibani numban ki..

Wani murmushin taqaici tayi tace Bani bace na  sace maka zuciya.. gara kaje kanemo ta tin dare Bai maka ba.. batun phone number kuma Bani badawa sannan  in ka qara bibiyata wallahi hukuma ce zata rabamu

Haitham yayi murmushi, yace azra hukuma tayi kadan ta rabani dake. Ki taimaka kibani numban ki danAllah, ni bandamu da a kulleni a cell ba in dai zaki ban numban ki..
Daga bayanta taji anacewa
08033447788, qawarta ce Zainab(baniaz) tace ga numban ta nan, haka nan take wai ita bata kula samari, tayi ta koransu , kayi hakuri bawanAllah wannan miskila ce, yayi murmushi yace zainab nagodeh sossai, Allah yasaka miki da alkhairi..tace Amin tawuce.. ita kuma azra da ta kai qololuwa cikin bacin rai tace dashi shikenan kuma sekadaina bibiyata.. yayi murmushi yace ki huta lafiya sarauniya ta..+

Ya Riga da ya riqe numban a ka, yaqara maimaita wa 08033447788 yace as special as the owner.. Allah yaban sa’a..
*Bayan kwana biyu*
Wayar azra ne tayi ringing sabuwar number ce ta dauka cike da nutsuwa tace Assalamu alaikum da zazzaqar muryarta me kwantad da hankalin me sauraro, yace wa alaikumussalam warahmatullah.. dam zuciyarta ya tsinke,tsaf tagane me magana Amma gudun kadan ta bada kanta se tace wanene.. yace haitham ne.. tace bangane ka ba.. yace Wanda kuka hadu ranan bikin qawarki.. that’s two day back, tace Au Allah sarki.. yace nabugo ne in gaida ki in kuma cemiki wallahi ni inason ki tsakani da Allah..

Tace nagodeh ta katse wayar ta..
Haka haitham yayi ta bibiyar azra har yasamu ta amince da soyayyarsa..

About AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *