ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya 

kuma bai fada miki da bakinsa ya na sonki ba har ya kama gabansa. Sai dai kuma idan so ki ke ki jefa rayuwarki cikin damuwa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ina son ki cire son shi tun da wuri, kar abu ya zo bai samun yadda ki ke so ba ki shiga cikin wata damuwar, tun da dai babu wanda ya san ranar
dawowarsa. Don ni kaina da ki ka ganni nan, babu irin binciken da ban yi miki ba a kansa, don dai kawai na nemo abin da zan fada miki ki samu farin ciki.
Amma kowa na tambaya sai ya ce min gaskiya ba shi da tabbacin dawowarsa. Don haka mu cigaba

da addu’a, duk abin da zai zamo miki Alkhairi cikin rayuwarki shi muke fata”’.
“Zahra duk na ji, na kuma fahimci abin da ki ke fada min. sai dai kumi bana jin zan iya son wani da namiji kamar yadda nake jin M.J a raina, na dai yarda cewa addu’ar ita ce zan cigaba da yi, sai kema ki tayano da hakan, idan har da Alkhairi akan hakan Allah ya datar da ni, sai dai kuma ban yi miki alKawarin daina son shi ba”
Sun jima sosai suna hira, daga nan suka rabu bayan sauran dalibai sun fito daga dakin jarabawar an dauki hotuna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin sallama ta shiga cikin falon, a nan ta iske
_kowa ana zaune sun sanya Sameer a tsakiya ya na ta ba su labarai na ban dariya, cikinsu kuwa har da Granny wacce ta dora dukkan hankalinta a kansa.
Fuskarta cike da damuwa ta yi cilli da jakarta sannan ta samu waje ta zauna hade da furta ‘““Wash Allah!”. Duk sai suka juyo suna kallonta.


Nan ta turo baki gaba alamar shagwaba ta ce “Kuna ta ji na ina ta kwada sallama amma babu wanda ya amsa min, kun mayar da hankalin ku waje guda sai shan story ku ke yi Da wani ne ya yi haka da tuni an fara yi masa fadan an yi sallama bai amsa ba”,
Gaba daya Kannenta suka amsa mata da cewa “Sorry Aunty Haana ba mu jiki ba, labari Yaya Sameer yake ba mu mai dadi
Cikin murmushi ita ma Granny ta ce “Yi hakuri Raihanatu, hankalinmu ne bai kai ga jiba”
Ai kuwa ta sake murtuke fuska sannan tace “Ai shikenan”. Miss Haana barka da dawowa, a yi haKuri ba mu ji bane amma ai da mun amsa miki”
Ta dan sassauta fushin nata sannan ta ce “Babu komai Mr. Sameer ya wuce ai, amma Next time babu wanda zan yiwa uzuri, don na Ki jinin hakan”
“Za mu kiyaye hakan insha Allah miss Haana”’.
“Zai yi kyau idan aka yi hakan Mr. Sameer”.
Ai kuwa Granny ta yi Kwafa, “Kai ni fa kun isheni da wani mis mis, sai kace ma su _ kiran kyanwa. Ko irin yadda ‘yan uwanki ke kiransa da Yaya ma bakya yi don shashancin kawai”’Www.bankinhausanovels.com.ng
Ai kuwa gaba dayan falon aka kwashe da dariya harda sauran yaran. Sameer ne ya yi Magana
“Hajyiya Granny, ki barmu kawai mu dinga kiran kan mu _ haka, tunda dai muna jin dadin hakan”:
*““Ai kuwa sai ku yi ta yi, wai ku nan ‘yan bokon Karshen zamani, sai ku je ku Karata”.
Tan. gama fadin hakan ta miKe Raihanatu na yi mata tsiya. Ba ta bi ta kanta ba, saboda dama ta saba da hakan indai Rathanatu ce.
Imran ne ya kalleta sannan ya ce, “Sister Guest what?” Uhumm, me ya faru?, fada min kawaina ji’.
“Kin san wai dama Yaya Sameer dan polo club ne?”’,
serrous Imran, shi ya fada maka haka?”’.
“Eh mana, shi yada mana, maganar ce ma muke yi kika shigo. Ya fada mana shi ne sport din da ya fi so a ransa. Sannan kuma yanzu ma wasan kofi (cup) suke yi, har ma na ke fada masa cewa kina matuKar Kaunar game din’”’.
““Shakka babu lallai Mr.Samcer za mu je da kai, ashe ina da hero a gida ban sani ba.
Gaskiya na ji dadin labarin nan, ga shi har na ji ya korar min da damuwar da nazo da ita’. Nan Sameer ya bita da kallo fuskarsa dauke da murmushi ganin yadda ta nuna murnarta kan abin da ya zamar masa passion dinsa. Hakika ya ji dadi sosai da sosai
“Kina son polo miss Haana?”’.
Girgiza masa kai ta yi sannan ta ce .
“Sosai ma kuwa Mr.Sameer, don dai ba ka san yadda nake son shahararren dan polo din nan bane wato Devid Brown na Kasar Portugal. He is my hero, ya na birgeni sosai da sosai
Da ace Abba mai sauki ne sosai, da wallahi wata rana sai naje har can Kasar na je ganin wasan su da za su yi a Karshen shekarar nan”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi ya yi mai kama da yaKe sannan yace,
‘““Gaskiya kam miss Haana, yanzu-na fuskanci kina kallon polo. Sai dai kuma ina ganin daga yau zaki daina son kowa, tunda ga na ki hero din har gida. Ba sai kin saka Abba ya Barnatar da kudinsa
ba, ni kadai na isa na saka ki farin cikin da wancen katon arnen ya ke saka ki. Ku shirya yau sati mu je ku ga wasan mu da ‘yan Kaduna da Kano wanda za mu yi a polo club”.“ serious M.r Sameer?. Gaskiya na ji dadin wannan maganar taka. Bari na kira Rauda don da ita za mu yi wannan tafiyar. Suma su Imran suka kama mura, Allah ya taimake su yau Alhamis Malaminsu ba zai zo ba.
Falon sai ya rage su biyu saboda kowa ya shiga ciki don fara yin shiri tun yanzu. Shi kuma Imran ya nufi wajen Mas’ud Kanin Rauda don ya fada masa.
“Miss Haana haka dama ki ke da son polo?, na ga kamar har Kannenki duk kin dora su akan hakan, so Amazing ’. Ya karasa fada ya na murmushi.
Murmushi ta yi itama, sannan ta ce. “Haka abin ya ke Mr.Sameer dinmu. Muna rayuwa da soyayya kan abu guda daya, don haka muka taso muna yi a cikin gidanmu. Duk abin da dayan mu ya keso to duk gaba dayan mu za mu hadu mu so abin, kuma babu babba ba Karami. Tun muna yara Yaya Abba da iyayenmu suka saba mana da haka.
Haka ma farin cikinmu da bakin cikinmu, gaba daya muke sharing dinsa. Shi yasa duk cikinmu idan mutum ya nuna ga abin da ya ke so, to gaba dayanmu za mu nunawa abin so, kai da ka kawo abin ma sai a nuna maka kamar an fika son abin
naka. Don haka idan ka ga wani abin nan gaba, kada ka yi mamaki. Jini daya kenan”.
Sai kawai ya saki murmushi shima, sannan ya Kara dora maganarsa shima Www.bankinhausanovels.com.ng
“Gaskiya ne Miss Haana, nima yanzu sai a fara Sharing din komai da ni tunda dai nima tsatso ne daga cikin ZURI’A DAYA. Ko ba haka bane?”. Ya fada ya na mai Kara yin murmushi. “Haka ne mana, tunda kai ma jininmu ne wannan babu damuwa”. Ajiyar zuciya ya yi, sannan ya kalleta da wani yanayi na son jin abu mai muhimmanci ya ce.
“Miss Haana ni kuwa zan so na ji wacce irin damuwa ki ke dauke da ita da na ji kina fada dazu?”.
Runtse idanuwa ta yi, sannan ta dan huro siririyar iska daga bakinta mai dan zafi sannan ta dora da magana cikin yanayin jimami.
“Kai dai bari kawai Mr.Sameer. Next time sai mu tara, ina son na manta da damuwar ne at this time, Duk da kuwa nasan ba zan taba iya korar damuwar daga zuciyata ba. Ka share kawai, kar ka damu, babu wata matsala.
Obh! Mr.Sameer, ka ga cikin ku babu wanda ya yi min maganar last paper ta, kuma duk kai ne ka jawo. Da ban sameka ba nasan da kowa sai ya tambayeni ya ya paper. Bari na je na samu Granny, itama ta yi min laifi Binta kawai ya yi da kallo fuskarsa dauke da murmushi har ta shige ciki. Girgiza kai kawai ya yi
ya ce. “Haana ina son wannan style din naki da yadda ki ke shagwaBarki son ranki kuma ake biye miki kamar ba kece babba ba. Ina son hakan”’
Nan take ya dinga jinsa ya na shiga cikin wani irin yanayi da shauki duk kuma a kan Haana dinsa. Wani abu ya ji ya na taso masa a can Kasan zuciyarsa ga me da ita.
Motoci guda biyu suka dauka aka nufi polo club. Haana ita ce ke jan motarsu ita da Rauda ne, sai kuma wasu daga cikin Kannensu. Sauran kuwa kowa cewa ya yi motar Yaya Sameer zai shiga, haka kuwa suka cika ta taf.”
Shiga mai kyau Haana da Rauda suka yi. Dogayen Riguna ne a jikinsu, sannan suka rufe kansu da dankwalin rigar. Haana nata kayan kalar (colour) ja ne, ita kuma Rauda (pinch). Idan ka
. gansu kamar wasu larabawa, shigar ta yi musu kyau Kwarai, kai da ganinsu ma kasan yaran manya ne.
Ta ko ina hutu ya bayyana a tare da su. Haana ta yi kyau sosai, ta sanya bakin glass a fuskarta wanda ya Karawa fuskarta kyau matuka kamar ita ce Hameeda ta HAMSHAKIYA. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kyawun da Sameer ya ga Haana ta yi masa shi ya sanya shi rudewa har ya so ya saki baki ya furta mata wasu kalamai.
“Ya salam! Miss Haana wannan kyau da ki Ka yi kamar za ki je cin gasar sarauniyar kyau. Kwarai shigar taki ta yi min kyau sosai’’.
“Himmm! Mr.Sameer ka yi a hankali, na fuskanci kana da magana da yawa, ba ka gani ka yi shiru. Idan har kana so mu shirya da kai ka daina tankawa shigata, don ni haka nake.
Kuma ba ka ga komai ba sai lokacin da Hero na ya dawo cikin rayuwata, lokacin ne za ka gane wace Haana a wajen yin gayu. You know . Mr.Sameer, ina son gayu da komai na yin gayu”’.
Ya bude baki zai yi magana sai kawai ya hangi har ta yi gaba ta barshi a wajen tana Karasawa wajen Rauda wacce ta fito za ta Karasa wajen mota. Tun da suka shigo polo club din suka ga yadda ake wani nan-nan da Sameer. Nan ya shigar da su yana nunawa mutanensa cewa wadannan ‘yan uwansa ne.
Ya na fada kuwa ana mayar masa da, ai ko ba ka fada ba kowa ya ganka ya san ZURI’A DAYA ku ke. A saman v.i.p aka yi musu masauki gaba dayansu. Haka kawai Haana ta dinga jin nishadi a zuciyarta saboda yau ga ta ga wasan da ya fi komai birgeta a rayuwarta.
Duk gilmawar da za su yi Sai jama’a sun sanya musu idanu, ba ga manya ba balle yaran, saboda wajen ya cika da manyan mutane masu_ kudi, saboda dama wasan polo na manyan masu kudi ne da ‘yan sarauta. Abin dai gwanin sha’awa.
Kafin Sameer ya bar wajen don zuwa su yi shirin wasan, ya dan ranKwafo ta kunnen Haana ya ce mata.
“Miss Haana ki hankali fa da jama’ar wajen nan, don naga duk kin dauke mu su hankali. Bana son kuma ki baiwa kowa fuska”.
Dan harararsa ta yi ta gefen idanuwanta sannan tace
“What is wrong with you Mr.Sameer?, ka je abinka, babu wani abu da zai faru. Ban zo wajen nan don na saurari kowa ba, saboda babu wanda ni zan saurara a rayuwata bayan…..
Sai kuma ta yi murmushi kawai. Shi ma din murmushin ya yi, sannan ya ce mata. “Bayan wa?”.
Dariya kawai ta yi masa ta ce “Please ka je kawai abinka kar ka bata lokaci”.
Da sauri ya juya yana dariya, sai kuwa duk Kannen suka ce. “Yaya Sameer we wish you all the best’. Suka fada cikin hada baki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hannunsa ya sumbata sannan ya dago mu su shi alamar jinjina yana dariya.
Haana kuwa murmushi ta yi sannan kuma ta yi shiru ta Kurawa sararin samaniya idanu, nan take  tunanin Malam M.J ya fado mata. Haka kawai sai ta dinga ganin Mr.Sameer ya na yi mata yanayi da shi. .
Take ta ji wata irin kewarsa da Kaunarsa suna shigarta . nan kuwa ta shiga addu’ar Allah ya dawo mata da Malam M.J dinta cikin rayuwarta.
Tsananin fargaba kuma da damuwa su suka cika zuciyar Rauda don ganin yadda Haana dinta da Sameer suke yi duk kuma akan idanuwanta. Shin ina za ta iya saka ranta idan dai har Haana
itama ta kamu da son abin da ta ke matuKar so da Kauna da kuma burin mallaka a matsayin ABOKIN RAYUWARTA.
Muddin hakan ta kasance kuwa , za ta yi rayuwa cikin Kunci sosai, don ba za ta iya rayuwa da wani namijin ba idan har ba shi ba. A yadda ta ke jin son Sameer na nuKurKusar zuciyarta, ba ta jin za ta iya rayuwa idan ba da shi ba.
Daga Raudan har Haana din sun tafi wata duniyar ta tunani, ko wacce da irin abin da ta ke saKawa. Can suka jiyo ana ihu da sowa. .
Da sauri duk suka dawo da hankulansu wajen. Gaba daya wajen sai Dan fillo ake ta kira manya da yara. A nan ne suka fahimci-da Sameer ake, sunan ne ma jikin rigarsa. Wato dai sunan Family dinsu ya ke amfani.
Tunda aka fara wasa, idan banda sunan Dan fillo babu sunan da jama’a suka fi kira, saboda duk Kwallon da ya dauka sai ya kaita har cikin zaren abokan hamayyarsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka aka tashi daga wasan su ne da nasara. Tarin masoya kuwa ba za ta fadu ba don Bata lokaci ne. haka Haana da sauran ‘yan uwanta suka wanzu cikin farin ciki don Yayan su ya yi matuKar birgesu.
Dakyar da sidin goshi jama’a suka barshi suka baro wajen saboda yamma ta yi ga magariba ta na kawo kai, A daddafe suka dawo gida, a ranar kuwa an sha hira da murna,
Haka kawai kuma sai Haana ta ji Sameer yana birgeta, ta kuma yaba masa kan KoKarin da ya yi a wajen wasan. Kwanaki uku suka yi suna zuwa kallon wasan, kullum kuma suka je sai sun dawo da farin ciki.
A rana ta uku ne, manyan Alhazawan suka takurawa Haana da Rauda, dakyar suka samu suka sarara mu su. Duka abin da yake faruwa ashe a idanuwan Sameer ya ke faruwa.
Ai kuwa da suka dawo gida sai kawai ya hau su da fada kamar zai cinye su. Yadda ya nuna zafi a kai sai abin ya taba zuciyar Haana, har ta ji ya fara ba ta haushi, don da ya san yadda ta ke ji a zuciyarta kan wani namiji ya kawo kansa wajenta wanda ba Malam M.J dinta ba, da bai ma yi mata wannan hayaniyar ba. Don haka sai ta yi KoKarin Boye fishinta, don kar ta nuna bacin ranta ya kuma ji babu dadi.
Ita kuwa Rauda abin da ta fuskanta shi ne, tsabar kishi ne ya fito Karara a tare da shi, to amma kuma ganin itama bai barta ba sai take tunanin kishin dai kawai ya fi nunawa a kansu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Take kuma wata zuciyar ta fada mata cewa kishin Haana ya ke yi, kawai dai ya yi miki haka ne don kar ki fahimci ya fi baiwa Haana kulawa ne.
Dole ta hadiye wani abu da ta ji ya taso mata a can Kasan zuciyarta. A Bangaren Haana kuma, ta Kudire a ranta, daga wannan rana babu abin da zai sa ta sake zuwa wajen nan balle kuma ta dauko wa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Suna cikin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *