ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

             Www.bankinhausanovels.com.ng 


Tsawon zaman da muka yi a gurin muna cikin zulumi da sauraro, babu wani daga cikin ZURI’A dinmu da ya zo idan ka cire Hafsat matar Alh. Habibu data samu labarin zuwan mu ta buga masa waya kasancewar yana Lagos gurin aikinsa, shi ne ya bata damar ta zo, domin shi ne kadai bai juya mana baya ba, yana mu’amala damu don ma zamansa ba a nan yake yinsa ba, jifa-jifa yake zuwa amma iyalinsa ya barsu a nan.

Awa kusan daya da rabi muka_shafe domin ,har mun saki ranmu da muka samu labarin farfadowarta, zuwa can kuma sai ga wani likita mai suna Dr. Shafi’u ya nufo inda su Mustapha suke, yana zuwa duk suka miKe mu muna daga can gefe muna jiyo abin da suke cewa. Alh. Mustapha sai dai fa kuyi haKuri, domin rai ya yi halinsa, Allah Ya yi mata cikawa sakamakon toshewa da zuciyarta tayi da jini”. Cewar likita. “


Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”. Abin da duk muka shiga fadi kenan, nan – take Ammin ku ta yanke jiki ta fadi sumammiya, ~ nan aka shiga KoKarin ceto ranta. Tsananin tashin hankali a lokacin mun shige shi, domin sai muke ganin kamar abin cikin mafarki ne.
Tsabar dakiya da juriya gurin Mustapha kasa kuka ya yi sai bamu haKuri da yake yi akan mu daina kuka.
: Tun kafin a fito mana da ,gawar Aziza Hafsat tayi KoKarin komawa gida don ta sanar da
‘yan uwa da maigidanta, domin itama tayi mugun rudcewa da jin mutuwar. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tana zuwa estate babu gidan da ta fara zuwa sai gidan Alh. Jafar, ‘da kukanta ta shiga nan ta iske su da sauran ‘yan uwa suna ta hira, nan take sanar da su mutuwar Aziza. Nan take hankalin kowa ya ‘ashi, dai-dai lokacin da Hameed ya shigo, yana ji ya rude ya shiga sumbatu, da Kyar“ Haj. Asiya ta. riKe shi tana kuka. Mukullin mota ya zara kafin su ankara har ya fice ya dauki motar, jin Karar tashin mota duk suka fito cikin tashin hankali domin su tsayar da shi, amma ina! har ya yi mata (key) ya fita..
Hankalin Alh. Jafar ya yi matuKar tashi, nan take ya dauki motar sa suka bishi a baya cikin mugun tashin hankali. ° Tun da Hameed ya fito daga cikin gida tuki yake kawai amma bai san inda kansa yake ba, bai ma san ina zai shiga ba, tsananin rudani ya kasa sanin ina ma zai je, domin sam tunaninsa ba ya jikinsa. Yana shawo kan kwana zai hau babban titi sam shi ya manta wane hannu zai bi, cikin gigita bai yi aune ba sai kawai ganin Daf ya yi gabansa, ya yi KoKarin kauce mata amma ina! haka Daf din nan ta hau kan motar sa. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji‘un!”.
Abin yana faruwa Alh. Jafar na kawo kansa gurin, domin dama suna hango motar tasa da ya hau, shima Allah ne Ya kiyaye shi da anyi biyu, domin wani mahaukacin birki ya taka. Raga-raga aka kawo Hameed cikin asibitin, domin lokacin an gama komai an bamu gawar Aziza muna shirin fitowa mu tafi, domin har motar (Ambulance) ta zo nan muka hango _ Alh. Jafar cikin jini duk ya wanke masa rigarsa.
Mustapha ne ya fara hango shi, nan ya yi, sauri ya nufo gurinsa tsabar Kaunar dan’uwansa, nan yake tambayar sa me ke faruwa? Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin kuka, domin ya gama rudewa, ya ce, “Hameed yayi hatsari kan hanyar shi ta zuwa nan”.
Salati ya shiga yi yana kuka, nan take ya ga an turo shi akan gadon asibiti, nan ya yi sauri ya mike suna turawa domin duk ya rude kamar ya manta abin da ya faru da shi. Minti sha biyar da shigarsa aka fito aka fada mana cewa shima Allah Ya yi masa cikawa.
Wayyo Allah Raihana, a lokacin tun da muke bamu taba shiga tashin hankalin da muka shiga a wannan ranar ba, mutuwar mutum biyu lokaci guda kuma mutanen da suka fi soyuwa ’ cikin zuciyar ZURI’A dinmu, ba don sabanin da .” ya shiga tsakanin mu ba”.
Nan fa Granny ta shiga kuka, haka itama Haana domin sai suke jin kamar abin a wannan lokacin ya faru. Haana ma kuka ta shiga yi domin mutuwar tayi mugun tsaya mata a rai, sai take jin kamar yanzu abin ya faru a gabanta. Har Granny ta tsayar da kukan Haana ba ta tsayar da nata ba, domin jin labarin gaba daya ya tsaya mata a ranta, da Kyar ta samu ta daina kukan don taji Karshen labarin.
Granny ta goge hawayenta, ta ce, “Lokaci guda muka dawo da gawa biyu gida, mutanen da muka samu a cikin rukunan gidajen mu abin har bamu mamaki ya yi. . Dole gidan kakannin ku aka wuce da su aka je aka suturta su, amma har aka hada Hameed jini bai gama zuba daga jikinsa ba. Addu’a kowa ya yi musu duk muka yafe musu, lokacin masallaci ya yi da yake ranar Juma’a ne, haka aka wuce da su da anyi sallah a – kai su kushewar su. Babu yadda zamu yi muna
Www.bankinhausanovels.com.ng kallo aka dauke su tare aka fice da su, kuka kuwa babu wanda bai yi ba amma ya za muyi? Dole sai dai hakuri tun da haka allah Ya tsara mana, sai dai muyi musu fatan dacewa da samun aljannar . Firdausi. –
Duk komai tare aka yi na zaman makoki a guri guda ake karbar addu’a. . Tun faruwar al’amarin Alh. Jafar ba yaiya yiwa kowa magana, duk ya zama wani iri. Maganar gaskiya mutuwar Hameed tayi mugun daga masa hankali, yaron da ya gama dora. dukkan son duniya da kowane irin buri akansa, yau gashi ta Allah ta kasance akan sa. Haka kawai shi kadai ana zaune zai shiga kuka kamar wani Karamin yaro.
Tunda aka gama zaman makoki kowaya watse Alh. Jafar ya shiga gida bashi da wani aiki sai na kuka, babu wanda yake iya zuwa gurin da yake. °
Wata uku da rasuwar Hameed da Aziza lokacin tuni zuciyoyin mu sun gama sabawa da dangana da tawakkali, sai dai har yanzu babu wani canji da muka samu daga gurin ‘yan uwa, domin wata jita-jita da muke ji shi ne wai Alh. Jafar ya ce ba zai taba yafe jinin dansa ba, domin a sanadiyyar ‘yarmu dansa ya rasa ransa, kuma dama ya fada a baya idan ya rasa ran dansa akan ‘yarmu sai ya dauki mataki. Wata rana muna zaune a falo muna hirar duniya sai ga Mustapha ya shigo ciki rai bace, nan muka kama shi da tambaya me ke faruwa? Nan ne ya shiga fada mana cewar ga abin da ya hada su da Alh. Jafar, tara masa jama’‘a ya yi yana cewa bai yarda ba, shi ne ya kashe masa dansa don haka ya jira ganin sammaci daga (court). . Fada na shiga yi ina kumfar baki domin tunda ake abin nan ban taba nuna zafi na akai ba, to amma duk abin da zai yi yaje ya yi.
Ba jimawa sai ga mota har gida da (police) wai anzo tafiya da Mustapha akan wai ana zarginsa da cewa shi ne ya yi sanadiyyar cire Www.bankinhausanovels.com.ng
birki jikin motar Hameed ya shiga ranar da abin ya faru. Muna tsaye a Kofar gida mukace jin wannan labarin kamar almara, na zo zan yi magana kenan ‘yan sandan suka dakatar dani.
Mustapha ne ya ce nayi shiru, dole na kasa shiru na shiga gaya musu duk irin abin da ya zo bakina. Nan suka bukaci ya shiga motar su tafi, na ZO na sha gaban su na ce. Idan kun ga na barshi ya shiga motar nan to sai dai idan tare da ni za ku hada ku tafi, to shi “ne zan barku”. ‘ Babu irin roKon da Mustapha bai yi ba amma naki yarda, da suka matsa dole sai sun tafi da shi haka suka haKura na shiga motar aka tafi
dani.Kai sai daga baya ne ma muka samu labarin cewa duk gidan ya ce a kwashe mu a kaimu tsabar bashi da mutunci. Awar mu guda a can’ babu wanda ya saurare mu, zuwa can sai ga Mukhtar ya zo cikin
fushi, nan ya shiga cikin damuwa ganinmu a – bayan kanta. Nan take ya shiga zub da hawaye – ganin tausayi Sai da muka yi awa biyu babu wanda ya Saurare mu, muna cikin haka sai ga Alh. Habibu cikin bacin rai yana zuwa mutumin da ya sama kan kantar ya dauke da mari a take ya ce duk mutumin da yake (duty) a wannan ranar ya yi a bakin aikinsa, kasancewar shi babban police ne. Ciki ya shiga ya ciwa D.P.O din mutunci, ya kuma ce ya saurari abin da zai je ya dawo. Haka ya fito rai Bace ya ce mu zo mu tafi. Wani sabon tashin hankali da Kiyayya shi ne ya Kara yankowa cikin ZURI’ar mu, sam kowa ya Kara juya mana baya, sun koma jikinsa tunda shi ne mai kudi. Duk wata hanya ta muzgunawa babu wadda ba a bi an musguna mana ba, amma babu abin da ya faru damu domin duk mun dauke su jahilai masu rangwamen ilimi, ko da yake ba ilimi ne basu da shi ba, son zuciya da kwadayin abin duniya ne. Shekara guda muka yi a haka da su babu wani sauyi, rana tsaka muka wayi gari muka ga duk suna shirin barin estate din nan, wai za su bar mana shi sun koma Kaduna gaba dayan su. Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk Alh. Jafar ne ya dauki nauyin haka, wai duk don su muzguna mana.
Abin da suka yi mana ya yi mugun daga mana hankali, domin muyi tunanin cewa Kiyayyar da tasu bata kai haka ba.Kuka ni shiga yi Abban ku da kawun ku Mukhtar su ne suka shiga bani hakuri hade da kwantar min da hankali, dole na haKura da na tuna cikin yarana nake, ban rasa komai ba. To amma idan na tuna zaman sabon da muka yi na shekaru da dama da suka wuce sai na ji babu dadi. °
Abban ku ya ce, “Umma kada ki damu, insha Allah zan gina wani sashe ba cikin estate din nan, da yardar Allah sai na cika su da ZURI’Ar mu, nasan kowa na cikin ZURI’Armu manyan ciki sun kasa wani abu a ciki don son zuciya da gudun kada Alh. Jafar ya daina tallafa musu shi ne suka Ki yin magana, to ki yi haKuri insha allah a hankali nima zan yi gini naje can Rano na debo ‘yan uwa su dawo mana nan da zama mu Kara rayuwa guri guda cikin farin ciki”.
Shekaru uku baya haka su Abban ku suka hadu su uku suka hada Karfi da Karfe suka jera gidaje masu tarin yawa a nan, haka kowannen su ya debo wanda suke son biyo su suka Kara hada Weni (estate) din da yake akwai yalwar fili na gaske a gurin. Sun yi nasara duk wanda suke tunanin ya dawo gurin su anyi nasara sun dawo gidajen kowa da suka rufe babu wanda aka waiwaya, haka muka dawo cikin farin ciki, ga wani girma da ganin mutuncin mu da ake yi.
A wannan shekarun Allah Ya daga mahaifinki, arziki mai matuKar yalwa wanda mu kanmu abin har mamaki muka dinga yi, domin duk abin da ya rasa sai da ya samu ninkin ba ninkin. Www.bankinhausanovels.com.ng
A shekarar Kawun ki Mukhtar ya koma Katar da zama shi da iyalinsa, domin (lecturing) da ya samu a can. Haka muka rage daga gidan Maryam sai namu muke zaune cikin fadin estate din nan har kawo yau da muke ciki. Tun wannan lokacin da zaman yayan ki Abba ya dawo hannun Abban ku, tsabar son da yake masa ya mayar da shi tamkar dansa.
Tun bayan rasuwar Aziza babu wanda ku ka shaku da shi irin yayanki Abba wanda a lokutan da ki ke rigimar neman Aziza shi ne zai dauke ki ya yi ta rarrashin ki har sai kin manta, domin babu wanda yake iya rarrashin ki sai shi, don haka ta wannan bangaren ya Kara janyo so da Kaunar sa ga;Abban ki, don duniyar nan kaf babu abin da yake wa so da Kauna irin ki, shi yasa ya Kara daukar Kaunar Abba yasa a ransa don ganin irin kulawar da yake baki. Ga kuma wani sabon shaKuwa da kuka yi da shi, ta hakan ne ma har ki ka haKura da neman ‘yar’uar ki.
Tun da ki ka fara girma komai na ‘yar uwarki Aziza na halaye da kamanni duk suke ta bayyana a gare ki, domin duk wanda ya san Aziza idan ya ganki zai dauka ita ce ta dawo mana tsabar tsananin kamar da kuke da juna, tamkar dai tagwaye haka ku ke. A yanzu haka da nake ganin ki hankalina a kwance yake, don sai nake ganin kamar Azizan nake tare da ita, ko tare aka haife ku ba lallai ne kamar ku tayi trin
wadda ku ka yi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
To dama haka tsarin Allah yake, mun rasa
Aziza mun kuma samun Aziza. Yau tsawon
Shekara ashirin da faduwar wanmah al’amari amma har yau bamu Kara jin duriyar su ba. Tun da Alh, Habibu ya zo a shekarun baya bamu Sake haiduwa da “su ba, Kiri-Kiri an dasa gaba da Kiyayya a tsakanin mu, babu wani da yasan rayuwar wani bare a yi tunanin samun hanyar dawowa a shirya. Haka kullum tunanina da buri na ya za ayi mu shirya mu janyo ‘yan – uwanmu mu dawo ZURI’A DAYA kamar yadda muke a baya, amma har yanzu babu wata hanya
. da zan bi ko na samu mataimaki. To Raihana kinji yadda labarin ZURI’A . dinki yadda ta kasance tsawon shekarun da suka gabata, kuma naji dadin damar da na samu na bayyana miki komai, domin Abban ki bai son ana tuna masa baya, hakan yasa baya son a fada miki duk abin da ya faru.
Shi yasa ko hotunan Aziza bai bari an aje su inda za ki gani ba bare har ki yi tunanin kina da wata ‘yar uwa, duk don gudun kada ya saki damuwa domin a duniyar nan bai son abin da zai daga miki hankali, hakan yasa duk yadda zai yi sai ya ga abin da kike so shi zai yi miki, yana

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsayadaga idanunta sai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *