ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

motsin komai take ji ba sai na dan da yake – ~ cikinta, domin yau cikinta ya kai wata biyar ko shida.  ‘Hankalina ya yi mugun tashi, nan take na ce.“To ki bari Abban ki ya dawo saiki fada — masa, sai asan me za ayi miki”Ta yi-murmushi ta ce, “To Granny, Ammi _ -da na fada mata itama haka ta ce. Granny kuma _ba kya ganin yadda na koma, duk nayi fari na

Na canza kamar bani ba idan na kalli (mirrow)”.
Wani murmushin yake nayi, nace, . “Rashin lafiyar da kika yi ne kwanakin baya shi ne yasa”. Ta yi murmushi tace”Tunda naji sauki yanzu ai zan, dawo yadda nake, kuma bayan  sallah insha Allah zan koma makarnata domin nayi (missing) dinta, don Abba ya hana ni _komawa da tuni na koma” “Kada ki damu ya yi hakan ne-don ki ‘gama jin Karfin, jikin ki sosai, tunda gashi kin — – fara warwarewa, damuwa ta fara sakin jikin ki”. . Nan, take na shiga nusar da ita da nuna.  mata yadda Kaddara take, da kuma nuna mata ‘matsayin yafiya ga duk mutumin da aka yiwa ~ laifi, sannan kuma da daukar Kaddara kowacce


‘. iri. Na nuna mata cewa Shi Allah Yana jarrabar ~ dukkan Mumini ta kowacce irin hanya. To ke ki dauka ta nan hanyar Ya aiko taki jarrabawar, don haka kiyi haKuri da abin da duk ya faru da ke a baya, ki dauka Kaddara ce ta faru da ke tun da lokacin hakan ya faru to ki dauka babu mai goge hakan sai allah. Ki yi hakuri ki yafewa dan’uwanki, matukar’ ki ka yafe
masa to zaki ga sakamakon yafiyar ki. gurin Www.bankinhausanovels.com.ng
– Allah ranar gobe Kiyama, domin Allah,Yana son masu afuwa”, Jikinta ya yi sanyi, nan’ take ta ce, “Granny da nayi alKawari da zuciyata ba zan taba yafewa Ya Hameed abin da ‘ya yi min-ba har Karshen
‘ rayuwata, amma tunda kin ‘yimin nasiha to na
haKura na-yafe masa.-Amma na roke ki da ki fada masa kada ya kara ‘kuskuraya. shiga . rayuwatea,-yaje can ya yi rayuwar.sa shi kadai, ni
“dai na fitar da shi cikin rayuwata-har abada”. + Murna‘ta sa a‘janyo ta jikina‘ina hawaye
~ ina sa mata. albarka, ashe Amminku tana labe tana. jinmu, itama ta shigo tana-saka mata albarka akan yafiyar.da tayi~ ‘Kasancewar Mustapha baya kasar-yaje. Japan kan batun harkokin.kasuwar sa ‘da suke yi, hakan yasa. Aziza ‘bata ‘sake’ mana_maganar motsin da take jia jikinta ba, bawai don ta ‘daina  ji bane a’a sai don kawai mun-ce mata sai Abbanta _ ‘ya dawo ta fadamasa asan me za ayi, tunda ‘motsin da take ji ba ciwo’ya zamo mata ba.
. Tun ranar da tayi mana wannan bayanin kullum da abin muke kwana muke tashi, haka zanje. wata rana ina leKenta ta (window) idan tana bacci ko motsin’ da take ji ya hana ta barci, Cikin ‘ikoh “Allah ta’ fara sakkowa daga fushin da take yi’da Hameed, domin kullum yana . tare damu babu yadda mahaifinsa bai yi da shi ba akan ya daina zuwa amma ya “Ki, don. haka. – ‘dole ya rabu da shi don yaga zuwan yana sawa _ yana wartsakewa: daga:tarin damuwar da yake ‘tare. da -ita amma:’ba.a son ransa ba, don dai -kawai babu. yadda-zai -yi-da shine Shi-yasa. Tun‘Aziza‘na kin amsa duk gaisuwar da . yake .mata ‘domin idan ana. hira yana saka baki .zata ja nata tayi-shiru, har ta zo ta’ fara jin son ~ sakewa ayi hirar da ita, domin babu yadda. zata yi da nacin sa da kuma duba da nasihar da ake . mata akan rikon da take -dashi. ranar.‘da-yaso ya bata hakuri. akan . abin da ya faru a baya sai ta katse shi ta nuna – – bata son maganar.’ Sun fara. shiri sama-sama, amma ba don _ son ranta ba sai.don roKon da ni da.Ammin ku. ‘muke mata, don wata rana idan muna ‘mata sai ta  sa kuka tace kamar mun Www.bankinhausanovels.com.ng manta da abin da ya faru da ita ta sanadiyyar sa. Nan take sai jikin mu yayi sanyi mu kasa cewa da ita wani abu, muma sai mu tuhumi kanmu akan wai me yasa mu ma idon mu ya rufe muke son su shirya ne?
Idan muka tuna cewa jini daya muke duk sai muji muna. manta da zafin abin da ya faru tunda idan ma fallasar ce kowa cikin dangi yana – da tabon ba don zumuncn yanzu ya zamo sai kai da na jikinka ba.
Lokacin.da Abban ku ya dawo ya ga sabon al’amari domin zuwa ya yi ya ga Aziza da ni muna ta hira har da Hameed, sai yaji duk tsanar da yake ji na Hameed ya dan sauka duk da kuwa ya yafe masa amma idan ya ganshi yana jin wani ciwo a ransa, ba don yana son ganin * nishadin Aziza ba da ba zai taba barin wata alaKa ta shiga tsakanin su ba. To sanin dama can su abokan juna ne da kuma samun labaran da Ammin ku take bashi na cewa ita da kanta ta ce ta yafe masa, ba don haka ba babu yadda zai yi ya barshi yana shigo masa, amma duk da haka sai da ya same shi ya fada masa tunda ta yafe
masa to daga yau ya janye Kafarsa daga gidansa, yaje can ya ci gaba da rayuwar sa, ya manta da ita. ‘ Jin wannan furucin ya yi masifar daga masa hankali, nan take ya shiga kuka yana rokon sa akan kada ayi masa haka, a raba shi da Azizan sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ya daga masa hannu, ya yi masa jan ido hade da nuna masa bacin ransa akan ya janye Kafar sa daga cikin gidansa tunda abin da yake nema anyi masa
Ba komai ne yasa ya yi masa haka ba sai dalilin rashin amsar tambayr da Aziza tayi masa na me aka.ce yana damunta a cikinta ranar da  suka dawo daga asibiti? Don dama ya ce kada  likitocin su fada mata suka fice tare da ita. Sannan kuma da maganar da Ammin ku . tayi mata na cewa tayi jéro mata wasu tambayoyi da suka daga mata hankali dangane da daukewar al’adarta tsawon lokaci da ta dawo cikin hayyacin ta, duk wadannan tambayoyin da suka rasa amsar da za su bata shi ne suka hadu suka Kona masa rai ya rasa yadda zai yi yasa yazo ya dakatar da Hameed zuwar masa gida, duk shi ne ya janyo musu wannan rashin kwanciyar – hankalin. Kullum da wannan maganar da zulumin amsar da zamu bata muke kwana muke tashi, haka itama ta shiga wata damuwa domin ta rasa gane me iyayenta suke Boye mata, duk ta gamsu basa son sakewa da ita, ni kadai ce wadda nake iya zama da ita ina tunatar ta da manta son jin amsar tambayar da take son ji daga wurin su.Ganin kamar yaki jin maganar sa ya kirawo shi ya ce masa. .
“Ka sani Aziza bata san tana dauke da cikin da ke jikinta ba, don haka ya zama dole ka janye jiki da zuwa gidan nan, domin lokaci ya yi da za mu sanar da ita halin da take ciki, dole ne idan taji zafa tsane ka, za kuma ta shiga damuwa don haka zamu sanar da ita don haka kada ka sake kazo a kwanakin nan har sai mun shawo kanta ta huce ta dauki Kaddara sannan sai ka zo”. Jikinsa ya yi sanyi, nan take kunya ta kama shi yaji dama bai zo ba dole ya ce to zai janye zuwa. Haka ya tafi yana jinjina irin saukin kan da Abban nasa yake da shi, tabbas yasan da _ baya Kaunar sa da ba zai taba haKuri da abin da Www.bankinhausanovels.com.ng
ya faru a baya ba, don haka yasa yake Kara jin tsanar mahaifinsa da ya dauki zafi akansa don haka ya yankewa kansa ba zai Kara shigowa gidan ba har sai ranar da aka ba shi izinin shigowa. Tun daren ranar Alhamis muka gama – yanke shawarar washe gari zamu sanar da Aziza cewa tana dauke da ciki wata shida ba kadan, bayan shawarwari da muka zauna muka yanke a junanmu, ba don komai ba sai don ganin yadda take shiga damuwa da rashin sakin jikintadamu. Ranar dai kowannen mu da zulumn abin ya kwana, to amma babu yadda zamu yi dole ne mu sanar mata don hakan shi ne kwanciyar hankalin mu baki daya, saboda ko da yaushe – abin yana cikin ranmu, bamu da walwala. Washegari ita ce ranar tashin hankalinmu, ranar da har yau idan muka tuna ta sai mun ji babu dadi. Da mun san bayyanawa Aziza halin da take ciki zai zamo mana tashin hankali da bamu fada mata ba da bari muka yi ta gano komai da kanta, to amma babu yadda za muyi da abin da Allah Ya rubuta tun fil’azal. °
Zaune muke misalin Karfe goma na safe falon ya cika duk muna zaune Mustapha muke jira ni da ‘yan uwansa biyu Maryam da Mukhtar da mijin Maryam din, Ammin ku da ita kanta Azizan ta zauna tayi jigum, kana kallonta zaka ga kamar mara lafiya.
Lokacin da ya shigo sai da naji wani irin faduwar gaba na kuma rasa na ko meye ne dalili, addu’a na shiga yi. Yana zaunawa aka sake gaisawa sannan ya fara cewa. “Aziza na, ina son ki tsaya ki nutsu ki bani hankalinki ki fahimci abin da zan fada miki. Da farko ina so ki yarda da Kaddara ki kuma sani cewa
duk abin da ya faru da bawa da sanin Allah babu wanda ya isa ya yi maka wani abu sai allah Ya nufa, tun da tun farko haka Ya tsara zai faru da bawan sa. MatuKar lokacin faruwar hakan ya yi to babu tsumi babu dabara sai hakan ya faru da bawa, to don haka ki sa a ranki cewa abin da ya faru dake Kaddara ce matuKar kin yarda da haka to kin cinye jarrabawar da Allah Ya yi miki, domin kowane bawa da irin tashi jarrabawar, to ke kuma ta nan Allah Ya nufi taki, don haka ina son ki yarda da Kaddara”.
‘Murmushi tayi ta ce, “Abba na barwa Allah komai tun tuni, kuma na dauki Kaddara kuma na yafewa Ya Hameed tun tuni, sai dai bana son wani abu ya Kara shiga tsakanin mu ban da gaisuwa, ya yi rayuwar sa nayi tawa”. “Shi kenan zamu fada masa, kuma dole ya bi abinda kikace masa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan kowaya shiga saka mata albarka, murmushi ta shiga yiwa kowa.
“Sai abu na gaba wanda muke son sanar da ke tsawon lokaci muka kasa gaya miki wanda mu ma.bamu sani ba ‘sai da abu ya yi ‘nisa sakamakon burin mu muga kin rayu a lokacin da abin ya faru da ke, ba munyi haka bane don mu bata mik rayuwa ba
Ammi sakamakon abin da ya shiga — tsakanin ki da yayan ki Hameed ya nuna miki rashin tausayi, to ashe ciki ya shiga bamu sani ba har sai da ya kai wata uku lokacin ya wuce zubarwa, don ‘haka dole muka hakura gudun – kada mu fada cikin fushin Ubangiji muyi kisan kai shi yasa bamu raba ki da shi ba, saboda haka shi ne kike jin motsin da kike ji a jikin ki, yau cikin ya kai wata biyar ko shida kenan”.
A razane ta mike ta dafe Kirji ta ce, “Yau na shiga uku! Abba me kace ina dauke da shi?”
Nan take hawaye ya zubo a fuskar sa, ya ce, “Ammi na hakuri za kyi, haka Kaddara*take, dole mu yi hakuri mu rungume ta duk yadda ta zo mana”.
Dafe Kirjinta tayi tai wata irin ajiyar zuciya, anan take ta fadi sumammiya.
A rude gaba dayan mu muka yi kanta hankalin mu a tashe, babu wanda baya zubar da hawaye. Nan take Abban ku ya rungumota a sandare muka yo waje, cikin dugunzuma muka nufo gurin mota don muje asibiti a ceto rayuwarta. ;
– Nan da nan Mukhtar ya dauko motar sa aka saka ta
a ciki sai asibiti, mazan duk suka yi gaba mu kuma muka shiga motar Maryam ta  Jamu muka rufa musu baya.  Cikin tashin hankali muka Karaso asibiti kai tsaye (emergency) muka nufa, muna zuwa nan take likitoci suka karbe mu suka yi daki da ita, mu kuma muka tsaya a gurin.
Duk dauriya irin ta Mustapha sai da ya kasa daurewa, kuka yake yi kamar wani Karamin yaro, mu ne muke bashi haKuri duk da muma din kowanne hawaye ne ke zubar masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsawon fiye da minti arba’in babu wanda muka gani cikin likitocin, nan hankalin mu ya Kara tashi, ban da addu’a babu abin da muke tayi. Duk jikinmu ya yi sanyi, mun barwa Allah ikonsa, domin Shi ne mai yadda Yaso kuma duk yadda Ya yi shi ne gaskiya._ – .
Muna cikin wannan sauraron can sai muka ga wani daga cikin likitocin ya fito, gaba – dayanmu muka nufo shi. Cikin sauri Mustapha ya ce, “Doctor (please) Ammina a wane (condition) take?”
Decotor ya ce, “(Relax) Alhaji, maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin (critical condition) sakamakon razanar da tayi, hakan yasa zuciyarta kumbura, yanzu haka dai muna nan muna KoKarin ceto rayuwarta, ku dai taya – mu da addu’a”.
Daga hannu yayi yana salati, nan take ya yi Kasa hawaye na fita daga idanunsa, duk cikinmu aka rasa wanda zai rarrashi dan’uwansa
. kowa da abinda yake ji cikin zuciyar sa, haka duk muka rude muka shiga yin addu’a akan Allah Ya tashi kafadarta.
Yawan kai komo da likitocin suke yi shi ne ya Kara daga mana hankali, domn haka zaka gansu sun zo sun wuce, kana yi musu magana ba Sa Wani tsayawa su saurare mu sai wuce ki dan Kara yin hakuri muna cikin aiki ne.
Babu yadda zamu yi dole sai dai zubawa sarautar Allah ido, domin sai yadda ya yi damu.
Duk fitowar da likitocin za su yi sai mun yl musu magana sai suce damu mu Kara hakuri har yanzu suna nan suna KoKarin ceto ranta ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsawon zaman da muka yi a gurin muna cikin zulumi da sauraro, babu wani daga cikin ZURI’A dinmu da ya zo idan ka cire Hafsat matar Alh. Habibu data samu labarin zuwan mu ta buga masa waya kasancewar yana Lagos gurin aikinsa, shi ne ya bata damar ta zo, domin shi ne kadai bai juya mana baya ba, yana mu’amala damu don ma zamansa ba a nan yake yinsa ba, jifa-jifa yake zuwa amma iyalinsa ya barsu a nan.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsayadaga idanunta sai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *