ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

BIRNIN LONDON

Zaune yake cikin (garden) na (Hilton ; Whatford Hotel) dake birnin London, yana — kallon (Rushing waterfall) din da aka yi (designing) cikin hotel din.
Ya harde Kafa daya kan daya, duk wanda ya hango shi-a lokacin zai dauka yana kallon kyan (waterfall) din ne yana yabawa, sai dai abin ba haka yake ba, asali ma idanunsa da tunanin sa sun tafi ga rikicin da Haaya take.son jefe shi da wannan jarrababben son da take masa wanda ya

kawo masa tsaiko da karan tsaye a cikin rayuwar Sa. A zahirin gaskiya bashi da wani sauran (feelings) shauki da zai iya bawa wata mace, saboda ya riga da ya bawa Haana dukkan wani shaukin sa, soyayyar sa, Kaunar sa, tunaninsa, kukan sa, dariyar sa, kai da duk wnai (emotions) dinsa, don haka tuni zuciyar sa ta gama cike duk.  wani gurbi na yadda babu wata mace da zata samu wani matsayi da sunan ya Ce yana sonta.
Ta kai fiye da minti biyar tana kallon sa, shauKin son shi na dibanta, ta Karaso gabansa tayi masa sallama, amma bai ji ba, sai da ta dan bubbuga

kafadarsa sannan ya yi firgigit ya juya yadubeta.
Sanye take cikin riga da siket na atamfa wanda suka yi matuKar karbar jikinta, domin _ dinkin ya yi (fitting) dinta sosai, ta dora jacket baKa akan rigar wadda ta tsaya iya Kugunta, don yau garin na London da sanyi, amma ba. mai shiga jiki sosai ba. .
Ta sanya hannayenta cikin aljihun jacket din tana masa wani kallo hade da murmushi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bubanta ya yi sannan ya cira kansa ya mayar da kallon sa ga (waterfall) din, sannan ya yi kamar ba zai magana ba, zuwa can sai ya ce. Ba zaki zauna ba ne kin tsaya haka?” “Musty ka wahal dani gurin neman ka, naje duk inda nake tunanin zan ganka duk baka nan, kuma ga wayarka rufe”. Ta fada bayan ta samu ta zauna kusa da shi
“Nan na yanke shawarar nazo nan ne don nayi tunanin zaka Zo nan din ne, domin sanin kafi son wannan yanayin don samun nishadi”. Cira kai yayi ya dubeta cikin yanayin damuwa, ya ce. ,“”Nishadi fa kika ce? Ai ni bani da wani
nishadi matuKar ba za ki janye wannan nacin son da kike fada kike min ba, na tabbata idan ba Kasar nan na bari ba bani da wani nishadi. Tun tuni na sha fada miki a ra‘ayina da damuwa ta amma kin Ki janyewa, tunda kuwa baki janye ba ina zan samu wani farin ciki? Haka kuma tuni ya kamata ace na koma gida don na jima da kammala karatu na, amma fitinar ki ta hana min tafiya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hawaye ne suka taru cikin idanunta don haka bata yi KoKarin hana su zuba ba, domin . zubar su shi ne za su janyo sammun saukin jin irin furucin da ya yi mata da kuma daina jin Kunar da zuciyarta take yi.
Hawaye na zuba ta cira kai ta fara yi masa magana dacewa, Mustapha da zan iya jure irin ciwon son da nake maka da tuni na haKura; a duk lokacin da ka jefeni da wadannan kalaman masu kama da saukan aradu sai naji kamar na furta na hakura da kai da zarar nayi wannan tunanin sai naji idan na rabu da kai Matuwa zan yi, domin tuni zuciyata tayi zurfi cikin so da Kaunar ka, tunda nake ban taba jin ina Kaunar wani mahaluki kamar kai ba.
(Please) Mustapha kada ka juya min baya, meye aibu. na da zaka ce baka so na?” Sarai yaji tausayin dukkan kalaman ta, amma dole ne ya nuna mata jan ido ko ta haKura ta rabu da shi, don ya ga alamar idan bai yi haka ba bashi da wata mafita a tattare da ita. Nan ta ci gaba da cewa, “Bani da wani buri a duniyar nan da ya wuce a ce yau ka zamo
ABOKIN RAYUWATA. Tuni zuciyata ta gama saKa min kaine kadai wanda zan iya rayuwar aure da shi, domin kai ne ku ka na, kai ne dariya ta, kai ne farin ciki, damuwata, walwalata, kai kaine duk wani abu da zai zama idan na kalle ka zuciyata zata nutsu.
Matukar ka bar Kasar nan ba tare da ka karbi tayin soyayyata ba, to zan mutu ne domn bani da sauran wani fann ciki a tare da ni tunda ka fita daga cikin rayuwata”Cira kai ya yi ya dubeta, kana ya mintse idanunsa ya buso wani irin numfashi mai zafi, ya ce. ‘
“Haaya ki dawo cikin hayyacin ki mana, ‘domin naga alama kin fara zautuwa, kuma da gangan za ki zautar da kanki domin tun farkon faruwar wannan al’amarin ban rufe ki ba sai da na fada miki ina da matar da zan aura tun tana Karamar ta naji ina sonta har zuwa yanzu babu abin da ya sauya sai ma Karuwa da yake yi, don haka bai kamata ki zamo mai son kai ba”Cikin Kunar zuci ta dube shi, idanunta cike da hawaye, ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Baka yi min adalci ba idan ka kirani da mai son kai, domin kaima abin da yake ranka kake fadi, hakd nima. Sai dai ka hada ka kirawo mu da masu son kai, don naka kan kai ma ka sani ba nawa (feelings) din ba.
Ka manta ka fada min cewa Haana bata taba sanin cewa kana sonta ba illa dai ta san kana ji da ita da nuna mata so na matsayin yaya da Kanwar sa? Ka bari ne sosai ka koma zaka fada mata kana sonta, to kana tunanin har zuwa wannan lokacin ace ita bata da wanda take so? , Kayi kuskure Mustapha, ka rabu da Haana . taje ta samu wani don jiki na ya bani tana da wanda take so tunda bata san kana sonta ba”.Cikin zafin rai ya ce, “Wa ya fada miki haka? Haana ba zata taba son wani ba idan ba yaya Abbanta ba, ina tabbatar miki ko wa Haana ~ take so idan na Ce ina son ta zata rabu da shi ta dawo gare ni, don irin so da Kaunar junan da muke wa juna, matuKar bamu auri juna ba to bamu more ba, don aure tsakanin mu shi ne zai fi dacewa damu”.
“Shi kenan Musty, naji na.yarda ka auri haana daga baya sai ka zo ka aure ni, don ba zan
Zamo mai son kaina ba duk da kuwa irin zafin kishin furucin ka da nake ji, da na rasa ka gaba daya gwara na haKura na zauna da kishiyar tun da ita ce zabin ka ni kuma kai ne nawa, don ba zan taba rayuwa idan babu kai ba”.
“Haaya, ban yi miki wannan alKawarin ba gaskiya, kamar ni na ce zan yiwa Haana kishiya? Idan nayi haka ban kyauta mata ba, ni dai ki yi hakuri Allah Ya baki wanda ya fini sau dubu”.
Cikin hawaye ta mike bata sake cewa da shi komai ba, ta fara tafiya. Mai taxi ta tsayar ta
“hau ta bar gurin tana goge hawayen.
Binta ya yi da kallon tausayi don ya yi matuKar tausaya mata, domin duk abin da yake gaya mata Karfin hali yake yi, tabbas idan ba hakan ya yi mata ba bazai samo ta sakar masa mara ya yi fitsari ba.
Hakika ya yarda Haaya tana masa so mai tsanani, tabbas da ba Haana cikin rayuwar sa babu dalilin da zai sa yaki dubanta a matsayin ABOKIYAR RAYUWAR SA. To amma ina! tuni ya yi zurfi cikin shaukin sonta, babu wani abu da yake so a rayuwar sa sama da Haana dinsa, domin ita ce dukkan burinsa da farin cikin Www.bankinhausanovels.com.ng
sa. Nan dai ya tsaya yana ta tunanin sa, yawaitar zubar dusar KanKara (snow) shi ne yasa ya mike ° ya bar wurin zuciyar sa cike da tunani barkatai.

* * *

Mustapha Aliyu hamza wato (Ya Abba) matashin saurayi ne da ya kammala karatun sa da ya zo yi a U.K, a nan (Kings Collage London University) inda ya karanci (Business management) wanda anan ya yi (degree) dinsa, yanzu kuma ya kammala (MSC) _ dinsa (Masters) yana shirin komawa gida * Nigeria a nan ya hadu da Haaya Jafar. Itama ‘yar Nigeria ce iyaye da kakanninsu, sai dai gaba daya ita da (family) dinta anan London din suke rayuwa. Tun da ta shigo makarantar tasu ta ganshi ta kamu da tsananin Kaunar sa, domin lokacin da ta shigo a shekarar ya gama (degree) dnsa na farko. Sun shaKu ne da ita sosai domin tace yana matukar yi mata yanayi da babban yayanta, hakan yasa yake sakewa da ita har shaKuwar su tayi Karfi sosai, sai daga baya ne ta fara nunawa tana son su Kulla soyayya. Bai Boye mata ba ya fada mata yana da wadda zai aura, duk sai ta dauki abin da wasa.
Daga Karshe da yaga da gaske take ya shiga dakatar da ita akan ta fita daga cikin rayuwar sa, amma ina! haka ta dage akan dole idan ba shi ba sai dai ta mutu ba aure. Haka dai suke har tsawon wannan lokacin ta kasa haKura da shi, tausaya matan da yake yasa take ganin ba zata iya haKura da shi ba. Bashi da wata matsala da a yanzu indai ba matsalar Haaya ba, hakan yasa ya yanke shawarar nuna mata jan ido don tayi fishi ta haKura da shi. Sam ba wai baya son Haaya bane, tana da kirki da nutsuwa ya yaba da tarbiyyarta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai dai kash! Babu wanda zai samu wani matsayi a cikin zuciyar sa idan ba Haana ba, don ko kadan babu wata mace da zuciyar sa take so da gani idan ba Haana dinsa ba, don haka ya yanke shawarar sulalewa ya bar Kasar ba tare da _~ Haaya ta san shirin sa ba, domin idan ya tsaya tausaya mata haka zai yi ta zama ba tare da ya duba abin da ya dace da rayuwar sa ba.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE            …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *