ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya
hanya da zan bi don cikar burina sai . tahanyar ki. Don haka zan yi KoKari na kawar da tsanar da na fara fuskanta a gurinki don kada tayi yawa”.“Raihana, na shigo cikin rayuwar ki ne ba don mugunta ba sai don alheri, na tsaya nayi Www.bankinhausanovels.com.ng binciken wane hanya zan bi don ganin na cika burina, ban samu ba sai da na gano ke ce kadai _hanyar da zan bi ta kaini ga ‘samun abin da ya kawo ni Kasar nan, don haka ina neman hadin kanki”,
Duk wadannan kalaman na Malam M.J duk cikin zuciyar sa yake yinsu tamkar a gaban
Haana din yake. – Sallamar da aka yi cikin (office) dinsa ce ta dawo da shi daga dogon tutanin da ya tafi firgigit! ya yi ya dawo duniyar da ya bari, ya taf

Can. Bangaren su Haana kuwa su Salma ne suka sa ta gaba akan me ya hana ta zuwa (class)? Ta ce, “Kun san dalili, mene ne naku nayi _ min magana? Na sha fada muku cewa na haKura da (coursé) din nan sai wani takura min ku ke, ana dole ne? Tunda mutumin’ nan baya son na shigar masa aji to meye? Dole sai na shiga ya wulaKanta ni? Yaje abinsa Allah Ya nuna mana next year) na zo na sake zaunawa”… Zahra ta ce, “Allah Ya shirya wannan taurin kah naki”.Ameén”, Ta fada kai tsaye. Yau sati na biyu kenan da ya ci ace Haana tuni ta koma ta ci gaba da daukar darasin ta, amma sam ta Ki komawa, domin fushin da tayi ba Karami bane, domin a ganinta ya KasKanta ta sosai, duk yadda. take da KoKarin nan yadda kowane (lecturer) yake yabon

kwazonta, sai .gashi shine kadai mai son ya dakile ta, ya ki bari sam ta nuna Kwazonta gare shi, don tabbas da yasan irin kwanyar da Haana take da shi da bai’yi gigin korarta ba. Sauri take ta yi ta karbi wasu (question) da take so tayi (research) akansu a (office) din Dr. Junaid, don ta kira wayar sa yake fada mata yana (office) kuma yanzu zai fita, kuma baya jin  idan ya fita zai dawo yau, don haka yace tayi . ‘ Sauri ta zo fita zai yi. Dole haka ta Ki shiga (lecture) din da suke da ita a yanzu ta yi saurin tahowa don ta yi ta koma,Www.bankinhausanovels.com.ng saboda ta bar su Zahra sun shiga ita ta taho karba.  Kofar (office)’ din a bude take, ta yi. _ Sallama ta shiga. Ga mamakinta sai ta ga Malam M.J zaune a (office) din. .Dam! ta ji gabanta ya fadi, domin tun -ranar da ya wuce tana zaune bata Kara ganinsa ba, ko da yake duk ita ce ta dauki wadannan matakan na kaucewa duk wata hanya da za ta sa su hadu. ° . . Kamar ta juya sai kuma ta tuna dalilin zuwanta, don haka ta daure ta Karasa. Dr. Junaid ta gaisar da farko yake – tambayar ta ya su Abbanta? Ta amsa masa da cewa suna lafiya, cikin fara’a suke gaisawa. Sam bata kalli inda Malam M.J yake ba, gudun kada Dr, ya yi mata magana sai ta dan daga idanunta ta dubi Malam M.J a dan daurewar fuska ta ce, Sir barka da rane”, ‘ “Bana amsar gaisuwar ki”, Ya fada shima – cikin rashin sakin fuska, .cikin sauri Dr. Junaid ya ce, “Mr. Muhammad me ke faruwa kai da dalibar taka naji ka yi warnan furucin? Ko dai laifi tayi maka?” “Eh Dr. bata da kirki ne, laifi tayi min shi ne na dakatar da ita shiga aji na, da lokacin da na dibar mata ya cika bata Kara komawa ba har ” yanzu, yau ina ganin tayo sati biyu bata shigo ° ba”.
«Zaro idanu ya yi Waje, ya ce, “Raihanatu garin yaya haka ta faru? Yaushe ne ki ka fara ‘wasa da karatun ki? Kina tunanin idan mahaifin ki ya ji kin soma wasa da karatun ki zai ji dadi?”
_ Girgiza kai tayi tace,”A‘a”. “To gaskiya kada ki kuma haka, idan na sake jin ance kin samu sabani da wani malamai  da kaina zan hukunta ki, kinji na fada miki ko?
Kai kuma Malam Muhammad kayi hakuri, hakan ba zai sake faruwa ba, zata koma daukar darasinta tunda nayi mata fada Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shi kenan Dr. diyar taka ce naga kamar ta cika rawar kai da rashin kunya, shi yasa nayi mata haka”. .
Murmushi ya yi, ya ce, “(I know) Raihanatu tana da sauKin kai da ladabi, ina
’ tunanin don baka fahimce ta ba, don mutane suna yawan yabon ta gare ni, don mahaifinta abokina ne sosai. Amma insha Allah ba zata sake ba (still) dai kayi haKuri”.
“Dr. Insha Allahu nima komai ya wuce, zan kiyaye gaba”. Cewar Haana, domin jin ta tayi duk ta. matsu tana son komawa.
Nan ya harhada mata dukkan takardun da ta zo karba, ta juya zata fice cikin sauri, Malam M.J ya ce. . “Idan ban ganki a (class) ba ranar zan kawo Kararki gurin Dr.”.. Ta juya ta ce, “Naji, Allah Ya nuna mana lokacin, zan’zo”.
Dr. Junaid ya yi murmushi ya ce, “Aj ba zata Ki ba tunda ta ce maka zata zo”. Shigewarta tayi, nan ta barsu suna hirar SU. Kan hanyar ta komawa ta shiga yiwa Allah godiya da Malam M.J bai fada masa dalilin tsamar su ba, da fada zai mata sosai tunda har ya fara kai Kararta gurin Dr. to. kuwa tasan_ dole ta shiga taitayinta domin Doctor Junaid uba ne babba gareta, domin shi ne ya yi mata komai ‘ na zuwanta (law) domin abokin Abbu dinta ne na sosai, don muddin ta ci gaba da yin taurin kai to zai dinga saka wa yana mata fada. Kasancewar wani sauyi da aka samu . yanzu (lecture) din Malam M.J ya dawo musu – sau uku a sati, don haka ya zamana dole ne tana shiga. Da murna sosai suka tare ta da suka ga ta . shigo ajin, don sun fitar da ran zuwanta, don tuni ta fada musau yadda suka yi da Dr. Junaid da ya kai kararta gurinsa. – _ Zahra ta harare tata ce, “Munafuka mun. goede Allah da Dr. ya yi mana maganinki, yanzu sai muga ta zafin kai, don da zarar kin yi ba dai- dai ba mu da kanmu zamu je mu fada masa ya yi mana maganin ki Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi tayi ta ce, “Allah Ya baku ikon Zuwa”.
Rufe bakinta kenan sai ga Malam M.J ya shigo, gaba daya sai taga kowaya nutsu sosai, duk an wani mai da hankali gare shi. Tabe baki tayi ta ce, “Kai Zahra, dubi  yadda ku ka yi, duk kun wani rude kamar wasu Kananan yara”.
‘” “Don Allah Haana ki yi mana _ shiru, mutumin naki wallahi wani zafi. ya kuma yi mana, babu wanda yake saurarawa, don (last week) kar ki ga irin mutanen da ya yiwa rashin mutunci”.”(Okay) kuma yanzu kun fara gane cewar ~ bashi da mutunci? (Nice) Hajiyata, haka nake so”.
Kamar. yadda ya saba yau ma hakan ya yi musu, sai da ya dawo da hankalinsa gare su sannan (class) din duk ya dauki shiru.
Nan da‘ nan ya fara bayanin abin da ya — kawo shi, sama-sama ya dinga jin surutu na tashi. Kai tsaye ya kira sunan Haana, take ta ji
gabanta ya fadi ras! don ta gama yanke tunanin cewa rashin mutunci zai mata tunda ta shigo ajin sa.
Yanayin kallon da tayi masa ya san a tsorace ta yi masa, don bata san me zai ce da ita ba.
“Ke da Kawarki ku dawo nan gaba, don bana son ina jin kuna surutu, don na fuskance ki kamar zuwanki zai zamo kina raba min aji gida biyu”. .
Kala bata ce ba sai dai haka kawai take jin gabanta yana faduwa, suka mike ita da Zahra suka yo gaba. Mutum biyu ya tasa ya mayar da su baya, su kuma suka zauna a gurin. Nan fa ya shiga bayaninsa sosai, ga wani turanci da yake fitarwa mai dadin sauraro, haka (class) din ya dawo tamkar (debate) ake yi, haka zai dinga jero tambayoyi ana amsawa.
Haana shiru tayi tana ji bata um bata umum, bata yi aune ba taji ya cillo mata wata tambaya, da har tayi kamar ta maze ta ki fada, sai kawai ta ce, “Kai bari dai na ce wani abu don kada mutumin nan ya dauka bana ja, domin duk
abinda yake fade wasu na sansu wasu ban sani ba”.
Kai tsaye ta miqe ta shiga yin bayani na dalla-dalla, nan take ya cika da mamaki don bai yi tunanin zata iya masa wannan jawabin ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun da ya fara musu (lecture) yau ne rana ta biyu da ya nuna alfahari da dalibansa, sannan akwai wani cikin maza da ya burge shi har sai saida ya yi masa kyauta, domin wani (question) ya yi aka rasa mai amsawa sai shi ya yi masa bayani
cikakke wanda yasa ya yi matukar farin ciki da . gamuwa, to sai yau da Haana ta yi masa abin da bai zata ba. Shi da kansa ya tafa mata, take a nan ya ce ta fanshi kanta da (marks) din baya daya hanata su.
~ Su kansu ‘yan ajin sun yi matuKar jin dadi yadda wannan ta bashi mamaki, domin su kansu . Sun ji haushin abin da yayi mata a baya. Lokacin da ya fadi haka sai da tayi murmushi, ta ce. Thank you sir”.
: Sannan ta je ta zauna, ba jimawa nan ya Kara jero mata wasu tambayoyin, biyu ta iya amsawa dayan kuma wannan namijin ne ya amsa.
Kai ranar dai ita kanta Haana ta ji dadin ajin, domin dama haka take son kowane (lecturer) ya zamo ace yana wasawa dalibai kwanyar su. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ko da suka fito su Salma suma sun nuna farin cikin su da abin da ya faru, hakan yasa suka fara. tunanin cewa insha Allahu za su daina ‘yar tsama a tsakanin su. Hira suke Zahra ta ce, “Haana gaskiya naga kin burge mutumin ki fa yau, kinga yadda ya mai da hankalin sa sosai yana sauraron ki da ki ke bayanin nan”. Hmm! Ke dai Zahra bari, mutumin nan yana da (brain) tabbas da bana (research) da ya_Kure ni, kuma da ban bashi amsar ba da sai ya raina ni, domin zai ke dauka na (empty head) ce. Amma .fa da farko na dan rude, sai daga baya na tuna dole na dage don na fitar da kaina kunya, don naga alamun sa dan kwafsa mutane ne idan baka yi masa yadda yake so ba”. Salma ta ce, “Ke dai Bari, ai ya sha kwafsa mana, amma mu din ma da Kyar muke sha gurinsa, amma dai yau kin burge kowa”.
“Haka ne wallahi, dole mu nutsu gaba daya mu dage mu mayar da (course) dinsa mai sauki duk da kukan da ake da shi, don kada ya raina mu, don ke Zahra na sanki da saurin sarewa ba za ki janyo ya rainaki ba domin idan ya rilaina ki mu ya raina”.
“Ai karatu muke yi sosai domin abin nayi ne inda shi ne, don ya ce wallahi babu ruwansa idan mutum ya ci (pass) wallahi yar da shi zai yi, babu ruwansa”,. °
‘”Kin ji mugu ko? To insha Allah babu mai faduwa, yaje can da baKar aniyar sa”. – Dariya suka shiga yi mata ganin yadda ta wani bata rai tana hararar gefenta kamar yana

**********

Sallama tayi ta shigo dakin nata domin ta ji shiru har yanzu bata fito ba, bayan ga yadda suka tsara shirin (break fast) din da za suyi, sau biyu tana shigowa-dakin tana -ganinta a kwance, —don haka dole ta barta tunda ta san gajiyar makaranta ne ta makarar ca ita, gashi kuma yau hutun Karshen mako dole sai kukun ta tasa suka gabatar da wani abu.
Kai tsaye kanta ta nufa don ta taho, ta zo ta dora hannunta don ta tashe ta, can idanunta suka yi mata arba da wani hoto da sai da ya fadar mata da gaba da sauri ta sa hannu ta dauka, tana shirin dubawa sai ya fadi, nan ta kai hannu don dauka, sai ta iske wani hoton Kasa yashe. Tsananin faduwar gaban nata ne ya dadu, take man da nan wasu hawaye suka ciko idanunta.
Dole samun guri tayi ta zauna gefen gadon hAwaye suka cika mata idanu, ba hoton kowa bane illa hoton Aziza da Hameed, yaran da soyayyar sa da Kaunar su har yanzu take ransu, don har yanzu tunanin su yana nan zaune cikin zakatan iyayensu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kuka Haj. Aisha ta shiga yi domin famin da zuciyarta tayi, nan take ta shiga tunano abin da suka shude shekaru da yawa, taji kamar a lokacin abin ya faru. Nan ta shiga tunanin a ina Haana ta same wadannan hotuna da har ta dauke su take kwana da su haka?
Sauri tayi ta fito ta nufi gurin maigidan ta don sanar da shi da nuna masa abin da ta gani.,
Miqa tayi hade da salati lokaci guda, nan da nan takai idanunta kan agogon dake manne jikin garun dakinta. Da sauri ta mike don tabbatarwa da tayi ta makara da abinda suka shirya yi ita da Amminta. Dirowa tayi daga kan gadon tayi sauri ta shiga (toilet), (brush) tayi sannan ta wanke fuskarta.
Dawowa tayi ta shiga duba hotunan da ta mayar dasu abokan kwananta wanda kullum suna Kasan filo dinta, idan ta zo bacci ta kalla tayi kuka tayi musu addu’a, haka idan ta tashi ma da safe tayi musu addu’‘a tayi tana kukatace..
_”Ya Hameed da Yaya Aziza_ anayi (missing) dinku sosai, Ubangiji Ya yi muku rahama, Yasa aljannar Firdausi ce makomar ku”.
Wannan addu’ar haka take kullum a gurinta babu fashi, nan take hankalinta ya tashi domin bata ga hoton ba. .
Da sauri ta fito kai tsaye kicin ta nufa don ta san Amminta na cantana zuwa ta iske bata nan sai kuku ta gani suna ta aikin su.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsayadaga idanunta sai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *