ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 1  BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

              Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya
Hamza ka rufe min bakin ka a gurin nan, bari na gaya maka babu wanda ya isa ya hana ni aiwatar da abin da nayi niyya tun da abin ya shigo da munafurci da rashin imani. To bari na fada maka, ko kasan.cewa Hameed shi ne ya yiwa Ammi na fyade har ciki ya shiga wata uku?” . Www.bankinhausanovels.com.ng
Gaba dayan su rudewa suka yi, Alh. Hamza da Lukman duk suka fito da idanun su waje, tsananin mamaki da tashin hankali ne ya bayyana a fuskar su. Nan take suka shiga raba idanu da kallon juna.
Nan take ya zayyane musu duk abin da ya faru, jikin su yayi sanyi, yana fada musu hawaye na zuba a fuskar shi. BOOK 1 KARSHE

Hameed ya mike yazo gabansa yana bashi hakuri akan ya yafe masa, wallahi ya tuba yayi . kuma nadama. Yana fadi yana kuka, yana cewa. . “Abba kayi hakuri ka yafe min”. Saka hannu yayi ya ture shi, yace, “Kada ka Kara kira na Abba, domin ni ba Abban ka bane, kaje can ka nemi Abban ka da bai baka tarbiyya – ba da har ka samu ka yi irin wannan rashin . tausayin”. . Cikin tsawa Alh. Jafar ya ce, “Mustapha! Ka bar min Kofar gidana, na gaji da jin irin Www.bankinhausanovels.com.ng – .wadannan munanan kalaman da kake jifa na da ‘shi, bana jin tsoro ka je-duk kotun da kake ganin idan kaje zata yi maka maganin. abin da aka yi maka, bana jin tsoro da dana, idan ka tsayawa – ‘yarka nima zan tsayawa dana, babu wani fyade da ya yi mata, da son ranta suka yi hakan, jin tsoron abin da zai biyo baya ne yasa tayi masa sharrin cewa fyade ya yi mata. Maganar tarbiyya da kake yi da na bashi da ita to ai kaima taka ‘yar bata da shi, saboda ita
ce ta bashi hadin kai. Karya take yi babu abin da zan ji tsoro, muje kotun ai da bai fi da ba”. Yana gama fadin haka ya ja hannun Hameed suka shiga ciki, ya turo Kofar gate dinsa ya rufe abinsa. ~ hawaye ne suka soma zubowa a fuskar sa, nan take ya zube Kasa yana kuka, ‘yan uwansa ne suka tsaya suna bashi baki akan ya yihakuri. Cikin kuka ya ce, “Lukman, Hamza, a gaban idanun ku kunga abin da ya yi min, ni aka cuta amma ni ake fadawa haka”. ; Lukman yace, “Yaya Mustapha don Allah kayi haKuri, insha Allah komai zai dai-dai ta, za mu binciki yadda abin yake”. . ‘ ‘Jin Karar budewar (gate) din yasa duk hankalin su ya yi gurin, Hameed suka gani tsaye, yace.  “Uncle duk abin da Abba ya fada muku gaskiya ne, nine mai laifi, ni na cutar da Aziza _ ba ta yarda dani ba dole nayi mata.  A ranar da abin ya faru ban boyewa Daddy ba sai da na sanar da su, amma bai…” Tasss!!! : Tsananin marin da ya sakar masa shi ya hana shi Karasa furucin da ya yi niyya.
“Za ka wuce mu shige gida ko sai nayi kasa-Kasa da kai anan?” Cewar Jafar, yana magana yana huci.
Hameed rike da kuncin sa domin zafin marin ya yi masifar ratsa shi, yace. “Daddy mene ya yi saura? Gwara ka barni na gama fada musu tunda abin da baka so shi ne ya faru”. Dai dai lokacin da Alh. Aminu da Alh. Shehu suka Karaso gurin Www.bankinhausanovels.com.ng
“Daddy ka yarda cewa danka shi ne da laifi kuma wanda ya kamata a hukunta. Daddy ni nayi laifi kai ma ka sani, ni ne na cutar da Aziza ba da son ranta ba. Abba ina son ka sani cewa ba Daddy ne ya sani ba ni nasa kaina, sharrin zuciya da shaidan ganin halin da na bar Aziza a ciki yasa na tsorata, da suka same ni yasa na fada musu gaskiyar abin da na yi mata. Laifin Daddy daya anan da ya hana ni na fadawa kowa cewa ni ne _ nayi mata fyade don kada asirina ya tonu. Daddy. hakuri da neman yafiya ya kamata mu yi a gurin su Abba ba tsayawa mu sake bata musu rai ba”. Nan ya yaye jikinsa ya nuna musu bulalar da aka yi masa wanda hakan ne yasa ya gudu aka neme shi aka rasa. “Hameed ka rufe min baki na ce, Mustapha bai isa na bashi haKuri ba domin bai biyo ta hanyar da zan bashi hakuri ba, tunda tozarta ni ya sa yi a idanun.jama’a, don haka duk . abin da zai yi yaje ya yi bana jin tsoro, muje kotun”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Jafar haka zaka ce? To mu zuba da kai, wallahi tunda ka fadi haka nima ba zan yarda ba  ko da zan rasa komai nawa sai na gurfanar da kai – gaban kuliya tunda ta haka ka biyo”
“Subhanallahi! Haba Jafar, Mustapiia, duk me ya yi zafi haka? Abin duk a tsaye muka jishi, mu tsaya mu warware matsalar mu a junanmu ba wanda ya ji, domin rufin asirin mu.
Kada ku manta fa dukkanin mu ZURI’A DAYA muke, matuKar bamu tsaya mun gyara matsalar dake tsakanin mu ba ba zamu fitar da ita duniya ta ji ba, wannan matsala ta ZURI’A ce
mu zauna a fahimci juna mai laifi a bashi laifin sa, mai gaskiya shi ma a bashi.Mustapha ‘kai ne Karami dole haka zaka – hakura tun da mai afkuwa ta riga ta afku, jini daya ku ke, a bar maganar ta wuce kada a daga . ta kowa ya ji, domin gyara DANGANTAKAR MU, gudun abin da zaije_ya dawo nan gaba”. *~”Yaya Aminu kana tunanin cewa na bar maganar nan na huce bayan irin furuci mara dadi da shi ya jefe ni da su don kawai ina Kasa da shi? Sam ‘wannan ba shari’a bane, baka ji abin da yake fada ba kenan? Shi fa sam ya Ki nuna cewa dansa ne da laifi”. Ba zan nuna ba, na fada maka kaje duk inda zaka, kai din wanene? Na sake fada ba laifin dana bane na ‘yarka ne”
“Jafar mu zuba ni da kai mu gani, aga wanene zai yi nasara tunda kana taKama da kanka cewa kai wanine”.“Daddy kada ka yarda ya kai kotu don’ba zamuyi nasara ba”.Hameed! Kada na Kara jin bakin ka anan, zo ka bace min a gurin nan”.
Mustapha juyawa ya yi yai tafiyar sa ya bar su a gurin zuciyar sa na faman yi masa Kuna da zugin abin da yake faruwa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kai tsaye gidan sa yajc sya bude ya shiga ransa Bace ya rasa abin da yake masa dadi, haka yaji zaman gidan ba zai iya yinsa ba dole ya fita da niyyar komawa asibiti. A hanyar fitowar sa ne nan ya hangi ‘yan uwansa sun taru Kofar gidan Alh. Jafar manyan su da yaran ‘su, bai bi ta kansu ba ya ja motar sa ya yi ficewar sa Zaune yake a cikin asibitin ya gama zayyana mana yadda suka yi da shi.
Dubansa nayi cikin damuwa na ce, “Mustapha matuKar zan fada maka magana kayi amfani da ita to na roKe ka da ka janye maganar kai dan uwanka kotu, wannan ai tonawa juna asiri ne. Tun da Allah Ya Kaddari hakan babu abin da zamu yi sai haKuri mu rungum Kaddara tun da haka Allah Ya so, babu kuma wanda ya
isa ya hana afkuwar wannan masifar. Tawassali za muyi da hakan akan Allah Ya tsare mu, Ya kuma kare mu da faruwar wani abu makamancin hakan.
Ko me ‘yan uwanka za suyi maka kada kace zaka dauki mataki a hannun ka, ka duba zumuncin da yake tsakanin ku sai ka yafe musu.
Tabbas ban ji dadin furucin da Jafar ya yi akansa ba, to amma duk ka manta ka duba cewa dan uwanka ne, shi da kansa nan gaba zai ji kunya ya dawo ya nemi afuwar abin da ya yi maka.
Sannan na roKe ka da kada ka Kara daga maganar nan a cikin Zuri’a, mu barwa Allah ikonsa, da sannu zamu ga sakayya tunda son zuciya ya shigo ciki, mu zuba musu idanu muga gudun ruwansu tunda dai rayuwa ce ke juya mu gaba daya mu da su”.
Wasu hawaye ne masu dumi suka zubo masa, ya sa hannu ya goge, ya ce.
“Shi. kenan Umma tunda haka kike so nayi, sai dai tashin hankalin da nake hango mana ya za muyi da Aziza ranar da ta gano cewa ciki ne a jikinta? Duk abin da ya faru a baya a gurina duk ya wuce, wannan zulumin shi ne tashin hankalina na gaba”.
Ajiyar zuciya nima na sauke domin hango damuwar da tashin hankalin da Aziza zata shiga
idan taji cewa tana dauke da ciki a jikinta, da wanne zamu ji? “Mustapha babu yadda zamu yi, addu’a ita ce kawai abin da zamu yi gurin Allah, tun da dai Allah Yasa cikin ba na wani bane da ‘bamu san daga ina ya fito ba, Allah Ya Kaddara daga cikin Www.bankinhausanovels.com.ng
– ZURI’A dinmu yake, jininmu ne ai da sauki. To mu karbi Kaddara, haka Allah Ya nufa Ya kuma shirya. Hakuri shi ne abin da ya fi dacewa da mu tunda bamu zubar da cikin ba Allah Zai isar mana da abin da yafi dacewa damu da rayuwar ita Aziza din. . Addu’a kawai za muci gaba da yi, idan muka yi.haka Allah Ya ganmu Ya kuma san abin da muke so a gare shi, cikin sauki zai kawo mana mafita, zai kuma Kissima hakuri da dangana a cikin zuciyar ta da mu kanmu ta yadda Kuncin da muke ciki zai ragu a gafe mu. Mu daina yarda cewa Kaddara ce ta kawo haka, kuma da sanin Allah”. aan : Goge hawayen ya sake yi, yace. “Shi kenan Umma, mun dogara da Allah, Shi ne mai iko akan kowa da komai”.
Albarka na shiga saka masa tare da bashi hakuri akan cewa Allah Yana sane da mu, Yana kuma ganin halin da muke ciki
‘A ranar dai mun yi kwanna Kunci da takaici da damuwa, domin a ranar duk a asibitin muka .kwana tsabar damuwa, domin Mustapha haka yace ba zai iya komawa gida ba. .
Abin mamaki babu wanda ya zo daga, cikin ZURI’A don yi mana jajen abin da ya faru da kuma murnar cewa Aziza ta dawo cikin tunaninta, nan take sai zuciyata ta bani cewa ko babu wanda aka fadawa gaskiyar al’amanrin. Shiru nayi babu wanda na fadawa, domin ni ce babba kada na basu Kofa su yi tunanin anyi musu laifi, domin ban son wata matsalar ta Kara faruwa.
Karfe sha biyun rana likitoci suka bamu sallama, domin sun gama tabbatar mana cewa Aziza tana cike da nutsuwar tunaninta, babu. kuma wani abu da yake damunta, don haka zamu iya komawa gida. Mun yi murna haka muka gama shirin mu sai gida.
KwAnar mu guda da dawowa babu wani mahaluki da ya shigo yi mana sannu da zuwa yaro ko babba, nan take abin ya shiga bamu ~ mamaki. .
Bayan mun sha fama da Aziza inda ta birkice mana akan ita ba zata iya zama a cikin dakin ba don gani take abin da ya faru da ita zai sake faruwa da ita karo na biyu. Da Kyar muka samo kanta dole sai da aka chanza mata daki sannan muka samu nutsuwa, ban da aikin kuka babu abinda take yi duk sai mu ma muka samu damuwar.
Bayan komai ya nutsa muna zaune sai muka ga Mustapha ya fito daga dakinsa ya nufi waje, babu wanda ya tambayi inda za shi. Yana fita z
ya dawo ya ce. Umma zan fita, Yaya Aminu ne yake nema na”. Nan take yanayi na ya canza, na ce, “Shi Aminun bai san mun dawo ba, ba zai shigo ba ya tsaya waje?” ya ce, “Umma na fita kenan naga dan aiken da ya turo, ki jira naje na Www.bankinhausanovels.com.ng
dawo naji akan me ya yi min kiran, domin nima ina da abin da zan ce da shi”. Babu laifi, sai ka dawo, muna jiran ka”. Na fada.
“To Aliah Yasa”. Ya fada cikin ladabi sannan ya juya ya fita. Zaune ya iske shi cikin falon baki yana duba jarida da (glass) a idanunsa. Sallama ya yi masa ya amsa, ya nuna masa guri ya zauna. Sun gaisa bai tambaye shi ya mai jiki ba  bare ya ce ashe kuma kun dawo. Mustapha, me ka yanke a ranka na maganar kai Yaya Jafar Kara?” . Www.bankinhausanovels.com.ng
Jin furucinsa sai abin ya bashi mamaki, domin bai tambayi halin da diyarsa take ciki ba sai wannan maganar ya jefe shi da ita. Nan take yaji ransa ya baci, amma sai ya tuna shi din gaba yake da shi, dole yana girmama shi tun da sun taso da wannan tarbiyyar a gidan su.
“Yaya banyi tunanin cewa da wannan maganar zaka fara yi min ba, tun dazu muka dawo babu wanda ya zo ya duba jikin Aziza

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsayadaga idanunta sai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *