ZABI NA CHAPTER 8 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 8 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

AHMAD MUHAMMAD FADOUL RESIDENCE

MAITAMA-ABUJA+

Tsaye take a tangamemen kicin din gidan..

Wannan kicin dai babba ne sossai wanda ya hadu iya haduwa.. Komai na cikin shi fari ne sol sai dan touch of black.. Idan ka kalli bangon kicin din zaka rantse da glass aka gina shi.. Floor din ma gani zakayi kamar idan ka taka shi da qarfi zai iya fashewa.. POP kuwa ban ma taba ganin irin shi ba.. Ga wasu lafiyayyun chandeliers da recess lights da aka jera stylishly a jikin POP din wanda ya bada ma’ana sossai. Na’urorin yin girki da suke kicin din masu kyau da tsadan bala’i, wasu ma idan ka gani ba lallai ka san abinda ake yi da su ba.. Kicin din spotlessly clean kamar kullum.. da ganin wannan kicin din ka san cewar mai shi tana ji da shi.

Hajiya Aisha wadda suke kira Ammi ita ce tsaye gaban cooker tana qoqarin kammala Shredded chicken sauce din da take yi.. Gaba daya kicin din ya dauki qamshin girke-girken ta as usual.

Farar bafillatana kyakyawa, idan ka kalle ta zaka rantse bata wuce shekaru talatin da biyar ba amma shekarun ta Arba’in da tara a duniya.. Hutu ne sossai ya bayyana a jikinta domin kuwa fatar ta tamkar ta jarirai saboda laushi da kyau.. Ga jikinta har yanzu intact.

Ammi dai she spends more of her time a kicin domin kuwa mace ce da take bala’in son dafa abinci.. she likes feeding people. Yanzu haka ita ce take da wannan shahararren gidan cin abincin nan wanda ake ji da shi a garin Abuja mai suna CILANTRO..

Ammi dai a yanzu haka duk arzikin su ita take dafa abincin gidan ta.. she does it with passion.. A kullum idan dai tana kicin zaka ganta ita daya babu mai aiki ko daya, iyakan su sai idan ta gama su jera a dinning sannan suyi serving.. Wani ikon Allah kuwa duk yaran ta set of twins guda biyu babu mai sha’awar dafa abinci sai Namijin cikin su.. haka kawai yayi developing interest in cooking and yanzu haka he has become a great chef (thanks to Ammi) to the extent that ko aure yayi matar bazata nuna mishi iya girki ba.

Hankalinta yayi nisa a kan girkinta ne ta ji an rungume ta very tight ta baya..

“uhmmmmm… how I missed this aroma. Ya salaam.. Allah ya sani nayi missing din abincin ki my dearest Cutie” ya fada yayinda yayi mata kiss a kumatu sannan ya kwantar da kanshi bisa kafadarta..

Ammi dai ta dade tana jin qamshin turaren shi amma ta danganta hakan da bala’in missing dinshi da take yi..

Wani sanyi ta ji ya ratsa ta jin muryar dan nata.. Allah ya sani tana bala’in son Zayd.. Sossai ta shaqu da shi, Qila ko don shi kadai ne namiji a yaran nata oho!

Shafa kan shi tayi tana murmushi yayinda ta juyo ta fuskance shi.. Ba tare da tace komai ba ta janyo shi ta rungume shi very tight tare da sakin ajiyar zuciya..

Zayd dai ya saba da haka.. A duk lokacin da ya kwana biyu bai zo gidan ba haka take yi mishi, Tana masifar son shi kamar yadda shima yake masifar sonta.

Kusan tsawon minti biyar suna a haka yayinda ta qi sakin shi..

Zayd wanda ya kula abincin nata zai iya qonewa ne ya miqar da hannu ya kashe cooker din yayinda ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “I missed you so much..”

Ajiyar zuciya ta saki for the second time sannan tayi breaking hug din ta juyo ta tallabo fuskar shi tana shafawa kamar wani qaramin yaro tace “what took you so long without coming home??” tana shafa wuyan shi ta cigaba da fadin “..Baby kana cin abinci kuwa.. ya na ga kamar ka dan rame?? me na fadi maka akan ka rage stressing kanka.. ko kayi rashin lafiya ne kuma??”1

STORY CONTINUES BELOW

“Sssshhh.. relax Ammi, I am fine. It’s just stress, I own a company with 3 offices in the country remember??? it’s normal! kuma fa kar ki manta I was in Abuja even before i travelled to Dubai. Yanzu dai tell me, how have you been??” ya fada yayinda ya dafa kafadarta sannan ya duqo yayi mata kiss a goshi wanda ya sa tayi murmushi.

“I am fine, I just missed you.. don Allah ka daina tafiya kana dadewa haka”

Cike da tsokana yace “toh Ammi idan nayi aure wai ya za’a yi kenan???”

Hararar shi tayi tace “Matar da har yau ka kasa samun wata kuma?? ni na rasa dalilin da ya sanya baka dauki maganar aure da muhimmanci ba.. Ko kallon matan nan fa baka yi balle ka samu wadda zaka ji kana so… hala ni zan qara nema maka wata?” ta fada cike da masifa kamar ba ita tayi creating emotional scene ba yanzu.1

Zayd wanda ya saba da mood swing dinnan nata ne ya fashe da dariya yace “kar ki manta Ammi, the last time you did.. it failed”

Ajiyar zuciya ta saki sannan ta qara rungume shi gam tace “I am so sorry My baby.. ni kaina idan na tuno Na’eema hankali na tashi yake yi, da na rasa ka a wannan lokacin ya zan yi??”

Murmushi yayi yace “Kar ki damu Ammi, it’s in the past.. Addu’a is key to every…”

Kafin ya qarasa magana ne suka jiyo ihun Maheera da Meher wadanda suka rugo a guje..

“Akhiyy…”

Breaking hug din suka yi yayinda ya juyo ya ware hannun shi yace “Marhabaan taw’amun Ammi..” (hello ‘yan biyun Ammi)

Suka shige yayinda suka rungume shi da qarfin su..

“Innana naftaqiduka Ya Akhiyy..” (mun yi kewar ka Yaaya) Meher ta fada cikin shagwaba.

“aishtaqat ilayk ‘aydaan my princesses” (nima nayi kewar ku) ya fada yayinda yayi musu kiss a bisa kawunan su.

A lokacin kuwa Ammin su ta juya ta cigaba da girkinta yayinda Zayd ya dan yi shiru yana jiran ‘yan biyun suyi releasing din shi.

Ganin basu da niyya ne yace “toh sarakan qarfi.. ku sake ni haka nan”

Ammi ta fashe da dariya yayinda suka sake shi suma suna dariya.

Sai a yanzu ne nayi ma yaran kallo sossai.. ‘yan biyu ne very much identical. Da ganin su basu wuce shekara goma sha biyar ba.. Kyawawan gaske sannan farare sol, da ka gan su ka san suna da jinin larabawa..

Maheera ce tace “toh wai wanne qarfi gare mu? kai dai kawai kana yi mana wulaqanci ne don ka ga muna sonka”

Tabbas babu wanda ya kai Zayd farin jini a gidan.. Gaba dayan su daga iyayen shi har ‘yan uwan nashi bala’in son shi suke.. it’s obvious don kasancewar shi namiji tak a cikin su..

Kumatun ta ya ja yace “Nima ina son ku.. I swear”

Murmushi suka yi yayinda suka cika da murna.

“So tell me, how are you??”

Meher ce tace “we are fine.. mun yi missing dinka sossai”

Shi dai Zayd mamaki yake yi na yadda suke fadin sunyi missing dinshi.. a kullum fa suna video call but they keep telling him they miss him.. he will forever be grateful for having them as family!

“toh ai gani nan na dawo dukda ba dadewa zan yi ba..”

Da sauri Ammi ta juyo tace “ban gane ba dadewa zaka yi ba.. ina zaka je kuma??”

Murmushi yayi yace “Lagos zan je Ammi..”

Gani yayi ta bata rai yayinda ya koma wurinta da sauri yayi hugging dinta ta baya yace “I have a suprise for you.. na san zaki ji dadi sossai idan na fadi muku”

STORY CONTINUES BELOW

“then what are you waiting for? just tell me already” ta fada yayinda ta qagara ta ji news din.

Maheera da Meher ma suka matso suna fadin “please tell us Akhiyy..”

Yana murmushi ya karbi stirring spoon din hannun Ammi ya cigaba da motsa mata sauce dinta sannan yace “I will amma ba yanzu ba.. sai a dinner idan Abbu is present. Yanzu dai muyi sauri mu kammala dafa abincin nan kafin lokacin kiran sallah”

Ammi ta koma wurin Oven dinta yayinda Maheera da Meher suka koma kan kujerun Island suka zauna..

Zayd wanda ya kula da su ne yace “Ya haka?? wai kuna nufin har yanzu baku canza hali ba??”

Ya kalli Ammi yace “Ammi meyasa bakya engaging dinsu a kicin ne har yanzu?? I thought we talked about this”

Ammi ta girgiza kai tace “ni kam ai ban san yadda zanyi da su ba.. Nayi fadan na gaji na koma lallashi amma sam.. Kana ganin babu abinda suka sa a gaba sai hidima da gadgets din su”

Zayd wanda ran shi ya baci ne ya kalle su yace “Kuna so in dauki mataki akan ku ne?? do you want to see the other side of me??”

A rude suka girgiza kai, da alama sun tsorata da yanayin shi a yanzu.. Gani nayi idanuwan su sunyi glass alamun any moment zasu iya fashewa da kuka.. Yaran dai dama tun asalin su matsorata ne.. abu kadan sai ya sanya su kuka..

Shi kanshi da ya kula da hakan sai ya dan saki fuskar shi yace “so kuke yi idan aka aurar da ku mijin ku ya auro muku kishiya don baku iya dafa abinci ba???”

Da sauri suka girgiza kai alamar a’a

“toh get yourselves busy right now..” ya fada yayinda ya juya ya cigaba da abinda yake yi.

Aikuwa da sauri suka tashi suka nufi wurin Ammin su suna tambayan ta abinda zasu yi.

A haka dai suka kammala abinci kala-kala sannan suka bari masu aiki suka yi setting a table.

Kamar kullum idan Zayd yana gidan shi yake ja musu Sallah.. Gaba dayan su suka yi shiri suka nufi wani sashe a gidan wanda aka kebe shi don yin sallah.. more like a mini-mosque very cool, cute and super neat! wurin ya qawatu sossai..

Tare da his excellency Ahmad Muhammad Fadoul- Abbun su suka yi sallar!

☆☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe takwas da rabi suna zaune a Luscious luxury dinning room na gidan wanda ya hadu iya haduwa.. Gaba daya kalan dinning din Golden ne da white.. Komai ka kalla zaka gan shi classy and elegant.

Babu qarya ginin gidan as a whole ya bala’in yin kyau.. it was specially designed by Zayd, haka interior din gaba daya shi yayi.. Shi kam mai gidan iyakan abinda ya bayar sune ‘ya’yan banki wanda kuwa ba qanana ya ajiye ba..

Abinci ne aka jera kala-kala a kan table din.. Masu aiki a tsaye suna ta serving din su kamar kullum.. Gaba daya qamshin lafiyayyen girkin Ammi ne yake ta tashi..

Bayan sun kammala serving dinsu ne suka yi excusing kan su.. Daga nan suka yi addu’a suka fara ci.

Maheera wadda ta kalli plate din yayan nata ne tace “Akhiyy kai dai kullum plate dinka da abinci kala-kala in very small quantity.. wato dai komai sai ka dandana shi ko??”

Dariya suka yi yayinda Zayd yace “princess bana so inyi ta cin abu daya ne at a time shiyasa..”

“Kayf hal shughlaka??” (Ya aikin ka?) Abbu ya tambaye shi.

“Alhamdulillah Abbu..” Zayd ya fada cike da girmamawa.

“Masha Allah”

“Qult ‘ina ladayk ma tukhbiruna bihi Akhiyy…” (Kace akwai abinda zaka fadi mana Yaaya) Maheera ta fada tana kallon shi..

STORY CONTINUES BELOW

Da alama dai sun qagara su ji ko meye.

“Oh yes..” Zayd ya fada tare da kallon Ammin shi da Abbun shi yace “Dama ina so in fadi muku cewar na samu matar da nake so in aura..”

Da sauri Ammi ta ajiye cokalin hannunta tace “Dagaske???” yayinda ta cika da murna.

‘yan biyu suka tafa hannu tare da fadin “Yeeeey..”

Shi kuwa Abbu murmushi yayi sannan yace “a ina take? hope she is from a good and reputable family??”

Zayd wanda yake murmushi shima yace “Yes Abbu.. A Kaduna take, sunan ta Ameera..”

Daga nan ya dan basu taqaitaccen labarin Ameera da iyayen ta.. a cikin labarin shi kuwa bai fadi part din Layla ba, he didn’t even mention her at all!

“Ka tabbatar ba irin Na’eema bace ko??” Ammi ta fada yayinda take kallon shi.

“Yes Ammi, Ameera is just so different… Kamar yadda na fadi muku yanzu haka bata ma san ko ni waye ba but her Dad knows tunda maganar aure abu ne ba na wasa ba I can’t lie to him anymore..”

“Toh masha Allah, Wallahi na ji dadi sossai, finally ka zama serious har ka samu wadda kake so zaka yi settling ka samu magaji” Ammi ta fada yayinda ta cika da murna.

Shi kam Zayd murmushi kawai yake yi yana mamakin kanshi wai yau shine ya kawo zancen mace gidan su… is it for real??

Abbu wanda yayi gyaran murya ne yace “Dama fa ke ce kika qi yin haquri.. ai aure lokaci ne, idan lokaci yayi nobody can stop it. Besides yaron nan is just 29years old”

Ya kalli Zayd yace “sai ka cigaba da addu’a Allah yasa this time kayi sa’a”1

“Insha Allah Abbu”

“Yanzu weekend dinnan kake so mu je nema maka auren ta kenan??”

“eh Abbu if you are not busy.. and please I want you to fix a date.. ko nan da 2 weeks ne..”

“what??? 2 weeks??” Ammi ta fada cike da mamaki.. “Gaskiya 2 weeks yayi kadan Baby na.. ina ka taba ganin an yi irin haka?”

“Ammi please ayi within 2 weeks din.. the most important thing is tana so na unconditionally as a pauper. Kin ga I am scared if she finds out ko ni waye zata iya fasawa and at this point I cant afford to lose her.. I really want to get over with maganar auren nan in huta”

Ya kalli Abbu yace “But Abbu you need to apply pressure on her Dad akan wannan maganar domin kuwa na kula kamar bai shirya aurar da ita ba yanzu.. please help me Abbu..”

Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Abbu yace “Zan yi iyakar qoqari na.. la tuqaliq” (kar ka damu)

“Shukraan Abbu” (Nagode Abbu) ya fada cike da murna.

Meher ce tace “Akhiyy baka nuna mana hoton ta ba..” Maheera tace “Yes Akhiyy, we want to see her”

Gani nayi yana murmushi ya dauki daya daga cikin wayoyin shi qirar Iphone 12 pro max (the latest and most expensive iPhone wadda ko wata daya bata yi ba da ta fito) ya bude gallery dinshi sannan ya tura musu wayar yace “here you go”

Aikuwa har rige-rigen daukar wayar suke yi yayinda su Abbu suke ta yi musu dariya.

Ni kuwa nace Iyyeh.. har hotunan Ameera yana da su?? ina ya samo su??1

“Wooow..” Meher ta fada yayinda Maheera tace “She is small and so cute Akhiyy”

Suna ta swiping hotunan Ameera wanda a dukkanin su tana sanye cikin Hijabi ne na ji Meher tace “and I am sure she is very religious just the way Akhiyy wants”

“We like her Akhiyy.. cant wait to have her as a siter in-law” Maheera ta fada yayinda yace “thanks princess.. I am glad you like her”1

Ammi ce tace “toh ku bani nima in ga sirikar tawa mana..”

Zayd da Abbu suna ta dariya yayinda Meher ta miqa ma Ammi wayar.

“Masha Allah, da ganin yarinyar zata yi hankali da natsuwa.. very beautiful with a beautiful skin color.. I am proud of the fact that you went for the innermost beauty and not physical appearance Baby na. Cant wait to have her as a daughter in-law. Allah ya sanya alkhairi yayi muku albarka gaba daya..”

“Ameen Ammi..” suka amsa

Ko da suka kammala Dinner Abbu ya wuce sashen shi a dalilin wani important call da yayi receiving.

Su Maheera kuwa karbe ma Zayd waya suka yi wai zasu tura hotunan Ameera zuwa wayoyin su..

Ammi ta janyo wayarta tace “bari in kira Zaheera dukda dai na san ta riga ta sani.. wannan irin shaquwa naku ko hanta da jini sai haka..”

Zayd yana dariya ya miqe tare da fadin “kar ki manta ke kika shigo da mu duniya lokaci daya..”

“Hala ma shigowarka garin nan sai da ka je gidan ta??” Ammi ta fada tana murmushi

Kashe mata ido daya yayi tare da fadin “Yes Ammi.. shiyasa kika ga hankali na a kwance ai”

Ya kalli su Maheera yace “idan kun gama ku kawo mun waya na sashen Abbu”

“okay Akhiyy..”

Ya kalli Ammi yace “ni bari in je in ji abinda qasashen mu suke ciki wurin Abbu, kin san idan dai kina neman latest news akan Nigeria da Saudi Arabia toh Abbu zai baki”

Ammi wadda take dialing lambar Zaheera tana murmushi tace “toh Babyna, sai na shigo”

Ko da ta Kira Zaheera a waya dai kamar yadda tayi zato confirm ta san labarin abinda yake faruwa.. (Harda ma wanda ita Ammin bata sani ba)

Zayd da Zaheera ‘yan biyu ne kuma dukda suna opposite sex babu wani sirrin junan su da basu sani ba.. they share a very strong bond.. Gaba daya labarin Layla da Ameera ta sani.. ta San dukkan abinda ya faru tsakanin dan uwan nata da kuma step sisters din… So automatically she knows more that they know!!

Aikuwa hira sossai suka shiga yi na abubuwan da za’a shirya na bikin kama daga kayan lefe da kuma shagulgulan da za’ayi..GIDAN MALLAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI+

Da daddare wuraren qarfe tara saura Ameera tana zaune a qasan dakin su tana kawo Haddan karatun Al-qur’ani mai girma. Dayake batada tsarki tunda tana al’adarta babu daman riqe Al-qur’ani don haka ne take karanto cikin surorin da ta haddace.

Layla ce ta shigo dakin ta haye kan gadon ta yayinda take chatting da qawayen ta a watsapp group dinsu

A daidai lokacin kuwa wayar Ameera tayi ringing wanda bata duba ba har sai da ta kai qarshen ayar da take sannan.

Zuciyarta ce ta buga ganin sunan mai kiran.

ZAYD!

Da sauri ta amsa kiran.

“Assalam Habibty”4

Ameera dai Zuciyarta ce ta tsaya cak na dan lokaci a dalilin jin sunan da ya kira ta da shi.. HABIBTY!!

Allah ma ya sani tana bala’in son sunan.

“hey, are you there??”

“yes Ya Zayd.. wa’alaikas salam. Ina wuni” ta fada cikin wata murya wadda ita kanta bata gama tantancewa ba.

Layla dai jin sunan Zayd duk sai jikinta yayi sanyi.. Tun ranar da ta ji yace zai turo a nema mishi auren Ameera take jin wani iri.. ta rasa dalilin da ya sanya Zayd ya tsaya mata a rai when she doesn’t even love him..

Gani nayi ta mayar da hankalinta kan Ameera tana sauraron abinda take fadi.

“Lafiya.. how are you? nayi missing dinki”

Ameera dai zuciyarta ce take ta bugawa.. toh yaushe suka wani hadu da har zai yi kewar ta.

“toh meyasa baka zo ba? tun ranar fa baka qara zuwa ba kuma..” sai tayi shiru yayinda ta kasa qarasa maganarta.

“kuma me? ko da na zo fa kasa kallona kika yi balle kiyi mun magana.. I was the only one talking shiyasa nake gani kamar I am making you uncomfortable..”

“toh kayi haquri ka zo.. zan dinga magana”

“kin dai yi missing dina kenan kema?? the feeling is mutual Habibty.. Yanzu dai bana nan nayi tafiya.. na je neman kudin auren mu tunda dai ba ajiyewa nayi ba balle in dauka ko??”

Shiru ta dan yi yayinda ya bata tausayi..

“Yaya kar ka ba kanka wahala.. duk abinda ka samu no matter how small please manage it.. kuma ma ai akwai lokaci tunda ba yanzu za’ayi auren ba”

Shiru ya dan yi sannan yace “kar ki damu Habibty, insha Allah ma zan samo. Tell me, how are you?? me kike yi??”

Ita dai Ameera bata saba da irin wannan ba.. sai jin ta take yi wani iri..

STORY CONTINUES BELOW

“ina karatun Al-qur’ani ne”

“Masha Allah.. kin dai yi sallah ko?”

Nan da nan ta daburce da wannan tambayar tashi.. toh me zata ce mishi?? qarya zata yi?? (abinda bata iya ba)

“a’a” ta fada kai tsaye

“Meyasa baki yi ba?? kenan ba kya sallah a kan lokaci ko?? baki san muhimmancin yin sallah akan…”

Ameera wadda hankalin ta ya tashi jin yadda yake magana ce tace “Yaya don Allah kayi haquri, wallahi ina sallah akan lokaci.. Yau din bana yi ne shiyasa”

“ba kya yi?? ban gane…” can kuma yayi shiru sannan ta ji yana dariya yace “okay na gane.. I am sorry, you must be on your monthly cycle kenan. My bad”

Ameera dai shiru tayi yayinda ta cika da kunya.. Ji tayi ma kamar ta kashe wayar.. Yanzu shikenan ya san halin da take ciki presently.. sai ta ji dama tayi mishi qaryan kawai?

Layla dai tana ta sauraron abubuwan da Ameera take fadi.. to her they are irrelevant stuff wanda hakan ya bata mamaki sossai.. Ya za’ayi Zayd ya dinga cinye kudin wayar shi just to talk nonsense??

“Hey tell me about yourself..”

“me kake so ka ji Yaaya?”

“everything.. tun daga lokacin da kika yi wayau har zuwa yanzu”

“Yaaya ai labarin zai yi tsawo.. kar ka cinye katin wayarka”

“Kar ki damu MTN sun bani bonus.. just go on”

Daga nan kuwa Ameera ta fara bashi labarin ta.. tun bata saki jiki da shi ba har ta zage ta dinga zuba mishi hira.. Gaba daya duk wani abinda take so a rayuwarta da wanda bata so ta fadi mishi..

Idan tayi surutu na tsawon lokaci sai ta tuna mishi da katin wayan shi da yake tafiya amma sai yace mata bonus din bai qare ba..

Tsawon kusan awa biyu suna maqale a waya.. Layla dai sossai wannan abu ya bata mamaki.. Zayd ne ya dade a waya haka? mutumin da idan yayi wuta ya sa mata katin waya na naira dari biyu.. how is this possible??

“Yaaya har yanzu bonus din basu qare ba??” ta jiyo muryar Ameera tana tambayan shi.

“basu qare ba Habibty, qila sun manta da ni ne. Kin gaji da yi mun hira ne??? ko bacci kike ji?”

“a’a Yaaya.. ni fa ban qi muyi ta hira ba har asuba..”

“we can do that ai… your wish will always be my command Habibty”

Zaro idanuwa Ameera tayi tace “kana nufin bonus din bazai qare ba har asuba??”

“Zamu gwada mu gani Habibty.. idan ya qare shikenan. What say??”

Murmushi tayi tace “toh mu gwada..”

Daga nan kuwa suka cigaba da hira sossai..

Ita dai Layla ta kasa ta tsare tana ta sauraron yadda Ameera take ta yi mishi labarai iri-iri.. tun tana jira su gama wayar har bacci ya sace ta..

Ameera da Zayd dai har kusan qarfe Uku na dare suna maqale a waya.. A dalilin zai yi sallar dare kamar yadda ya saba ne suka yi sallama ba don bonus din nashi ya qare ba kamar yadda Ameera tayi zato.

Wani ikon Allah kuwa har gari ya waye bata yi bacci ba.. tana ta tunanin hirar su da suka yi.. Allah ya sani tana son Zayd.. Burinta shine ta kasance matar shi har abada.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Days later!!

A yau Saturday ya kasance ranar da His excellency Ahmad Muhammad Fadoul tare da abokanen shi guda biyar zasu zo gidan su Ameera. A bangaren su dai zasu zo nema ma Zayd auren Ameera ne sannan a sa ranar biki.. A bangaren su Abba kuwa zasu zo ne a sada zumunci sannan a tabbatar musu cewar za’a ba dan su auren Ameera.

STORY CONTINUES BELOW

Tun da safe su Umma suka gyara gidan tas.. Su Mama dai nasu kallo.. abun har mamaki yake ba Layla wai yau dangin Zayd zasu zo gidan su akan maganar Ameera.. abun kamar wasa.

Ko da suka sauka a Airport tuni manyan Range Rovers sabbi gal guda uku suna jiran su tare da Mustapha wanda zai jagoranci tafiyar tunda ya san gidan (a dalilin kwatance da Zarah tayi mishi)

A dalilin Zayd ya roqi Abbun shi akan kar ya je da security dayawa ne ya sanya basuyi convoy ba don haka silently suka shigo layin gidan su Ameera.

Abba ya gayyaci abokanen shi har guda hudu wanda suka karbi baqin nasu.

His excellency Ahmad Muhammad Fadoul yayi shiga ta larabawa kamar kullum..

Abokanen Abba dai sun girgiza matuqa ganin cewar Abbu shine sirikin abokin nasu… babban mutum kuma sananne a qasar mu Nigeria. sossai suka yi mamakin ganin shi..

Ibrahim da Aliyu ne suka dinga fito da kayan ciye-ciye da na sha iri-iri. Cikin girmamawa suka gayar da su Abbu sannan suka bar falon suna mamakin yanayin mutanen da suka zo a matsayin iyayen Zayd.

Bayan sun gaisa sun gabatar da juna ne suka shiga hira..

A wannan lokaci kuwa idan ka kalli wadannan mutane da yadda suka saki jiki da juna suna ta hira zaka rantse ba yau suka fara haduwa ba.. Sun dan Jima suna hira sannan suka dawo kan ainihin abinda ya tara su.. maganar ZAYD da AMEERA.

Abbu da kanshi ya gabatar da buqatar su sannan ya nemi alfarmar ayi bikin nan da sati biyu.. Abba kuwa qin amincewa yayi da maganar biki nan da sati biyu tunda dai ba shiryawa suka yi ba.. ya dai yi musu alqawarin zai ba Zayd din Ameera amma aure ba yanzu ba..

A nan fa aka fara dragging da Abba wanda ya dage akan lallai bazai aurar da Ameera nan da sati biyu ba yayinda su Abbu tare da abokanen shi suka dinga lallashin shi.. a qarshe kuwa dole ya haqura ya amince..

Abbu da kanshi yayi godiya tare da alqawarin zasu riqe Ameera cikin amana.. Anan dai suka ajiye naira dubu dari biyar kudin gaisuwa wanda Zayd ne yace a bayar da hakan don kuwa baya so Abba ya ga kamar ana neman a siye su da kudi ne… A hakan ma sai da Abban ya gwada sunyi yawa amma aka lallaba shi.

Sun jaddada ma su Abba cewar su Ameera kawai suke so don haka sun hutar da su duk wani kayan daki tunda dama al’ada ce ta zo da hakan ba addini ba.. Sun sanar da su cewar iyaye mata zasu zo da kayan lefe kafin ranar bikin.

Abba dai har aka gama wannan taro ba wani dadi ya ji ba domin kuwa baya so ko alama mutane su ga kamar kwadayi da son abun duniya ya sanya ya amince da wannan auren.

Aikuwa bayan su Abbun Zayd sun tafi ne abokanen Abba suka dinga yabawa tare da sa albarka a al’amarin..

Duk wannan abu da ake yi Ameera tana dakin Ummanta yayinda itama Layla take dakin Mama.

☆☆☆☆☆☆☆

Bayan abokanen Abba sun tafi ne ya tara iyalin shi a falo don yayi musu bayanin abinda ya wakana tsakanin su da dangin Zayd.

Ya sanar da su komai amma banda kudin gaisuwa da aka kawo.. bai fadi an kawo ba saboda bayyanar da wadannan kudin zai iya wargaza alqawarin da yayi ma Zayd na alfarmar da ya nema a wurin shi.

Aikuwa tunda ya fara magana na ga Mama da Layla sun dan yi sanyi..

Tambaya anan shine, ina Zayd ya samu kudin da har yake so ayi bikin su nan da sati biyu?? again ya yafe kayan daki?? Idan dai Zayd din da Layla ta sani ne ai Naira dubu goma ma gagarar shi zata yi balle har ya iya hada kayan aure sannan ya yafe kayan daki…

Ameera kuwa tunda aka ce za’a yi bikinta nan da sati biyu ta bi ta rikice.. Yanzu shikenan nan da sati biyu zata bar gidan su?? toh wai ita ta shirya ne??? Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda hawaye suka fara wanke mata fuska..

STORY CONTINUES BELOW

“Ameera ya kike kuka kuma??? ko auren ne baki so??” Abba ya tambayeta.

“Abba na ga kamar yayi kusa ne. Ni fa bana so in tafi in bar ku”

Umma wadda tun tuni tayi shiru ce tace “nima dai Abba na ga abun yayi sauri dayawa.. sati biyu ai yayi kadan.. wannan wane irin gaggawa ne haka??? gaskiya yakamata a duba”

Kafin Abba yayi magana ne Mama tace “ni kam ina da tambaya.. wai yaron nan da nake ji an ce ya yafe kayan daki sannan yana so ayi biki nan da sati biyu.. wai ina ya samo kudi ne?? shin kun bincika ba sata ya fara yi ba??”

Abba ya girgiza kai yace “kar ki damu da wannan Maman Layla, Yaro dai nayi bincike sossai akan shi kuma ina mai tabbatar miki da cewar duk kudaden da zaki ga ya kashe halaliyar shi ne.. da gumin shi ya samu”

Ya juya ya kalli Umma yace “ke kuma Umman Ameera ina so ki fahimci cewar kamar yadda na fadi miki a baya.. aure dai lokaci ne, idan yayi babu mai tsayar da shi.. idan har haka Allah ya tsara babu yadda muka iya.. Ameera dai Allah ya kawo mata miji don haka ban ga dalilin da zai sa mu hana ta aure ba ko don saboda muna tunanin lokaci bai yi ba.. mu cigaba da addu’a akan Allah yasa hakan shi zai zama mafi alkhairi”

Ni kuwa nace shikenan Abba ya gama magana!!3

☆☆☆☆☆☆

Kwance take a kan cinyar Ummanta tana kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.. ita dai har ga Allah tana son Zayd amma bata shirya yin aure ba a yanzu.. sai yanzu take gane abinda yake nufi da yace mata zai turo a nema mishi aurenta.. ita tayi tunanin kawai yana so a San da shi ne sannan a tabbatar mishi da za’a bashi ita ba wai kawai ace an sa ranar bikin su ba nan da sati biyu..

Abun qarin haushin tana ta kiran wayar shi amma switched off..

“anya Ameera ba gwara a fasa auren nan ba tunda baki son shi???” Umma ta fada yayinda take shafa kanta.

“a’a Umma, Ke ma kin san ina bala’in son Ya Zayd.. kawai dai auren nake so a daga.. Yanzu fa shikenan daga sati biyu zan bar gidan nan? zan bar ku?? ni fa gaskiya..” Kuka ne ya ci qarfinta.

“Ki daina kuka Ameera, don kinyi aure kin tafi gidan mijin ki bai zamanto shikenan kin rabu da mu ba.. a kullum idan kina so ki zo na tabbatar Zayd zai kawo ki.. ni kaina bana son auren nan da wuri haka amma kuma kamar yadda Abban ku ya fada lokaci ne.. idan ya zo babu wanda ya isa ya tsayar.. Yanzu dai ki kwantar da hankalinki ki cigaba da addu’a Allah ya sa shi yafi zama alkhairi a gareki”

“toh Umma”

“Bari gobe zan yi waya da Hajiya Maimuna ta kira mun mai gyaran jikin da tayi ma ‘yarta Rabi’at lokacin da tayi aure sai ta zo ko na sati biyun ne tayi miki.. ni abinda ya fi bani mamaki ma yadda yace ya yafe kayan daki.. ko meyasa ya fadi hakan??”

Ita kanta Ameera tayi mamakin hakan amma kuma da ta tuna yace yayi tafiya kuma yana sa ran zai samu kudi qila ya samu ne..

Hehehehe..

☆☆☆☆☆☆

Zaune take a dakin Mama yayinda tayi tagumi..

Mama ce tace “toh wai meye na ga duk kin bi kin damu?? ko son Zayd din kike yi ne kuma??”

“Ba haka bane Mama, kawai fa ina mamaki ne na yadda abubuwa suke tafiya.. kin ga fa ranan ya kira ta a waya suka yi kusan awa shidda suna hira.. don wallahi har wuraren qarfe biyu da na farka na ji su suna waya.. a ina ya samu katin waya da har suka dade haka nan?? Yanzu kuma kin ga fa wai yana so ya aure ta nan da sati biyu.. ina ya samo kudin da zai yi aure??? Sannan yace kayan dakin ma da za’a yi ya yafe.. anya Zayd ba wani mutum bane daban kuwa??”

Mama tayi shiru tana juya kalaman ‘yarta.. ita kanta tayi tunanin wannan.. da alama dai bata so ta yarda cewar haka din ne..

“Ki daina wannan tunanin Layla.. ni fa na fi kyautata zaton ya fara wata sana’a ce ta banza.. wa ya sani ma qila ya shiga cikin wadannan mugayen mutanen masu dauke mutane suna garkuwa da su?? kika sani ko sana’ar yankan kai ya fara?? maza ki cire wannan tunanin a kanki.. Yanzu lokaci ne da zaki samu saurayi mai arziki ki kawo shi gida mu sha biki.. banda don wancan sakaran Habib din ya bata rawar shi da tsalle ai da saidai su ga ke ma ana shirin naki bikin”1

Jin sunan Habib kuwa duk sai jikin Layla ya qara yin sanyi qarara.. Allah ya sani tana regretting abubuwan da tayi da shi musamman idan ta tuno ba da ita kadai yake mu’amala ba… Yanzu shikenan bazata iya gyara wannan kuskuren da tayi ba???1

????

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI+

Zaune take a kan gadonta tare da qawarta Zarah wadda tunda ta zo take cike da farin cikin da ta kasa boyewa.

“Ni kuwa sai na ga kamar kin fi ni murnar wannan bikin Zarah.. why is that??” Ameera ta tambaye ta cike da curiosity.

“Wallahi haka kawai I am happy zaki auri love of your life ne.. kin san kuwa babu abinda ya kai wannan dadi?” Zarah ta fada yayinda ta sa ma Ameera idanuwa.

“Yeah haka ne but the idea of 2 weeks dinnan ne bana so.. kuma fa kin ga har yanzu ban gane dalilin da ya sanya yace ya yafe kayan daki ba.. I know that Ya Zayd ba qarfi gare shi ba, why did he say that toh?”

“Kika sani ko ya samu wasu ‘yan kudi ne? besides dont think too much about that.. the most important thing is you are getting married to him, maganar sati biyu kuwa ai lokaci ne yayi, da bai yi ba ai baza’a yi ba…”

“toh me zaki ce a game da rashin kira na a waya da yake yi?? kin ga fa tun ranar da ya zo ya fadi mun zai turo a nema mishi aurena sau daya kawai ya kira ni.. har yanzu shiru” Ameera ta fada cike da damuwa.

Zarah dai ta san cewar a wannan bangaren za’a samu matsala don kuwa ta sani sarai hidimar da ke gaban Zayd ta fi qarfin shi.. Shi kanshi baya samun lokacin kanshi da har zai tuna yakamata ya kira wani a waya musamman idan ya je Lagos. It’s like he gets very much busy a Lagos compared to Kaduna da Abuja..

Tabbas ta sani cewar it will be very difficult for him to adjust with irin wadannan abubuwan. Ta qudurta a ranta idan ta koma gida zata fadi ma Mustapha don yayi mishi magana..

“Ba kin ce da kuka yi waya yace yayi tafiya ba? qila network din inda yake babu kyau.. again, was it not just few days ago?? kar ki damu na tabbatar zai kira ki” Zarah ta fada hoping Ameera ta fahimci abinda tace

“Hmm, lallai ma Zarah.. I cant believe kina ta defending Ya Zayd haka.. mutumin da baki ma taba gani ba..”

“ba haka bane qawa ta.. na ga kina bala’in son shi ne ai kuma you are my friend don haka dole ne inyi supporting dinki..”

“Haka ne.. ina bala’in son Ya Zayd but the rate at which things are moving is what confuses me.. na so ace da ni da shi mun fahimci juna sossai kafin maganar aure ta shigo.. sometimes gani nake yi kamar don ya rama abinda Ya Layla tayi mishi ne ya sa yace zai aure ni.. I just.. I really dont get this…”

toh fa…

“Kina ina ake yi ma mace da namiji auren hadi, auren da basu san juna ba har sai ranar da aka kai macen gidan mijin?? A haka kuma suke zama su fahimci juna har su qulla soyayya mai qarfi… Balle ke da kun san juna kuma kina son shi yadda na tabbatar shima yana son ki, da baya son ki I doubt he will come and propose to you bayan ya sani sarai Layla ba son shi take ba balle har ta ji haushi… Uhm, Ni dai I am so looking forward to your wedding my friend. Allah ya sanya alkhairi” Zarah ta fada yayinda unlimited happiness ya bayyana a fuskarta.1

Umma ce tayi sallama ta shigo dakin.. Bayan sun gaisa da Zarah ne ta sanar da su mai gyaran jiki ta kira a waya tace nan da minti talatin zata iso.

☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI SANI DAURA RESIDENCE

UNGUWAN RIMI

Kwance take a kan gadon dakinta cikin Duvet yayinda Yusrah take kwance itama a gefen ta. Layla kuwa tana zaune a gefe bisa gadon itama sai Haleema da ta kishingida a kan resting chair.

STORY CONTINUES BELOW

A yau dai sun zo duba qawar tasu ce wadda zazzabi ya kwantar da ita.. babu laifi ta ji sauqi sossai amma dai likita ya bata shawarar ta samu isashen hutu..

Suna nan suna ta hira yayinda suke ta latse-latsen wayoyin su.

Haleema ce ta kalli Layla tace “qawa wai dagaske dai kin rabu da Habib for good??”

Layla ta bata rai tace “waye shi???”

Yusrah da Maryam suka kalli juna cike da mamaki yayinda Yusrah tace “ban gane waye shi ba.. har kin manta Habib din naki da kike qin shiga class saboda shi?? kun yi fada ne?”

Tsaki Layla ta ja sannan tace “ai nayi regretting dating dinshi.. wallahi he is a big fool” ta kalli Haleema tace “I can’t believe kina tare da abokin shi har yanzu.. kodayake na ga ke din..”

Da sauri Haleema ta dakatar da ita tace “madam it’s okay abeg.. sai kinyi tone-tonen asiri ne?? chill abeg.. tunda dai bakiyi da Habib ai shikenan”

Maryam ce tace “ku dai kuka sani.. ni kam na san cewar wannan relationships din naku won’t end well right from the onset especially naki Layla..”

“Whoa… finally!!” suka ji Yusrah ta fada yayinda ta tashi zaune tana kallon wayarta.

“Me ya faru?” “what happened??” dukkan su suka tambayeta yayinda suka sa mata idanuwa.

“ZAF the multi-millionaire is getting hooked”

Maryam ce tayi saurin fadin “dagaske??? ki ce za’a sha biki a qasar nan..”

“Waye wannan???” Layla tayi tambaya.

“Hmm.. Zayd Ahmad Fadoul CEO na CITY-SHELTERS.. ever heard of the name before??” Maryam ta tambayeta.

“CITY-SHELTERS?? wannan glass story building din da yake Ali akilu road?? thesame one da aka ce is owned by the only son of the Saudi Arabian Ambassador Ahmad Muhammad Fadoul?” ta jero musu tambayoyi.

“yes dear.. thesame one” Maryam ta fada tana kallon Haleema tace “thesame one da Leema take ta crushing akai amma har yau Allah bai bata ikon ganin shi ba.. ko ba haka ba??”

Haleema ta girgiza kai tace “ai baki sani ba, daga baya ma PA dinshi Bilal nayi targetting amma ya gagare ni.. tun daga nan nayi giving up”

“Me nake gani?? wannan ba Ameera ba ce??” Yusrah ta fada tana gyara zama.

“wacce Ameera??” Maryam ta tambayeta

“qanwar Layla.. dama zata yi aure shine baki fadi mana ba??” ta fada tare da kallon Layla da sauri

“Wai ban gane ba, kina nufin Ameera ce matar da ZAF zai aura??” Haleema ce tayi tambaya yayinda Layla ta kasa gane abinda suke fadi.

Yusrah tace “gashi nan sister dinshi Maheera tayi posting a Instagram page dinta.. wannan ba Ameera bace??”4

Gaba dayan su suka taru a kan wayar Yusrah.

Zuciyar Layla ce take bugawa da qarfin gaske yayinda jikinta yake ta rawa… Gani nayi ta karbi wayar hannun Yusrah tana kallo closely.

Tabbas hoton Ameera ne aka yi collage da hoton wani farin balarabe kyakyawan gaske.. bata taba ganin namiji wanda ya kai ko rabin kyan shi ba.

Qara qura mishi idanuwa tayi ta ga Kamarnin..

ZAYD??

“Wallahi ba shi bane..” ta miqe tsaye a rude yayinda ta jefar da wayar kan gado.

“ba shi bane kamar ya?? ba Ameeran ku bace?? dama zata yi aure ne???” Yusrah ta jero mata tambayoyi yayinda ta dauki wayarta.

STORY CONTINUES BELOW

Hawaye ne ke bin fuskar Layla wadda take tsaye ta kasa motsi… Gaba daya jikinta yayi mugun sanyi.

“ba shi bane, it cant be… na shiga uku. Wallahi Zayd dina ne” daga nan ta rushe musu da kuka yayinda ta dafe kanta.3

Haleema wadda take kusa da ita ce ta kamota ta zaunar da ita kan gado yayinda su Yusrah suka matso kusa da ita.

“Hey babes, relax. what are you saying?? kina nufin ZAF saurayin ki ne?? shine bamu taba sani ba?? toh ya akayi kuma yayi ending up da Ameera??” Haleema ta tambaye ta.

Layla tana kuka ta fara basu labarin haduwar ta Zayd har zuwa lokacin da ta kore shi da kuma yadda ya koma ma Ameera har magana ta kai ga an sa ranar bikin su..

Gaba dayan su dai shiru suka yi suna mamaki..

“Haba!! ni dai nayi ma gayen nan kallon sani ranan a school da ya zo wurin ki.. ina ta tunanin inda na san shi.. ashe ZAF ne in disguise?? kenan nayi ido hudu da ZAF amma ban gane shi ba?? Wallahi kin kwafsa qawata.. Yanzu kina nufin you had a chance of becoming one of the richest women in this country and you blew it up? ” Haleema ta fada tana girgiza kai.2

Maryam tace “gaskiya Layla na ji miki wallahi.. kin ga samu kin ga rashi.. we shouldn’t blame him gaskiya, dama dai matan yanzu ba soyayyar gaskiya suke yi ma samari ba, it’s always about money and its obvious shi wannan din soyayyar gaskiya ya nema shiyasa ya bullo miki ta hakan gashi yanzu kuma you fell for it.. “

Yusrah tace “Kar ku manta abinda ya faru da shi last 2 years.. ko don wannan ma ai ya ci yayi shinning idanuwan shi kar ya qara yin zaben tumun dare dukda ma an ce she wasn’t even his choice..”

Maryam tace “hmmmm… Ai fa shikenan Ameera ta haye.. ta zama sarauniya”

Layla ce ta tashi da sauri cikin masifa tace “wallahi bazai yiwu ba.. bazan taba bari ta aure shi ba don ni yake so ba ita ba”4

Daga nan ta dauki jakarta ta fita a guje yayinda qawayen nata suka bi ta suna ta kiran ta.. Hatta Maryam da ba isassar lafiya gareta ba sai da ta bi bayan su…

☆☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Ameera ce tsaye a gaban wadrobe dinta tana qoqarin ware kayan ta masu kyau wadanda zata tafi da su gidan mijinta yayinda take fitar da wadanda zata bayar.

Kusan awa biyu kenan da Mai gyaran jiki ta gama mata session dinta na yau.. Zarah ma bata dade da tafiya gida ba domin kuwa tana nan mai gyaran jikin ta gama aikinta ta tafi.

Bata ankara ba ta ji an shaqota ta baya wanda tana juyowa kumatun ta suka ji saukan mari masu zafin gaske har kala biyu.

Ameera dai sai da ta ga walqiya na wasu seconds yayinda kunnuwan ta suka mutu sannan wani mugun zafi ya dirar mata a fuska..

“dan uwarki wallahi baki isa ba.. Zayd nawa ne kuma ni zai aura..” Layla ta fada cike da tsanar Ameera yayinda take ta huci. Gaba daya idanuwanta sun kumbura- alamar ta ci kuka.

Ameera wadda hawaye suka wanke ma fuska tana dafe da kumatunta tace “kamar ya zaki ce Ya Zayd zaki aura.. ba ke kika ce baki son shi..”

Kafin ta qarasa magana kuwa Laya ta qara kwasa mata wani mari tace “Yanzu ina son shi kuma wallahi baya da matar da ta wuce ni a duniyan nan.. Wato dama kin san ko waye Zayd shine kika maqale mishi ko, kin san cewar mai kudi ne na fitar hankali shine baki fadi mun ba har kika yi nasarar raba mu kika cusa mishi kanki ko??”1

“Don Allah Ya Layla kiyi haquri.. wallahi Ya Zayd baya da komai.. you are mistaking him for someone else.. kin fi ni sanin ko waye Ya Zayd” Ameera ta fada yayinda take ta kuka.

Wayarta ta fitar ta shiga Instagram.. ko kafin tayi searching Handle din Maheera tuni ta ci karo da same picture a pages din Bellanaija, Hausa fulani, Africansweethearts da alot more public pages- da alama hoton da yake trending kenan at the moment..

Jikinta har kyarma yake saboda bala’i ta miqa mata wayar tace “don uwar ki wannan ne baya da komai?? ba hoton ki bane aka hada da nashi?? ba labarin auren ku ake yi ba???”

Ameera wadda take kuka ta karbi wayar tana kallo.. Zuciyarta ce ta buga ganin fuskar wani mai kama da Zayd.. Tabbas suna kama amma wannan din ya fi Zayd dinta haske nesa ba kusa ba dukda kuwa shi din shima da hasken shi.. again wancan bayada tabo a goshi kamar Zayd dinta.. most importantly, Zayd dinta talaka ne sabanin na hoton and from all indication wannan din ba ma dan Nigeria bane.

“don Allah Ya Layla kiyi haquri.. na tabbatar kama ce kawai suka yi..”

“Ni zaki raina ma hankali?? hoton ki da aka hada da nashi kuma fa???”

Bata jira Ameera ta amsa ba ta rufe ta da duka ta ko’ina..

Ameera tana qoqarin qwace kanta daga Layla wadda ta matse ta jikin wadrobe din amma ta kasa.. Duqewa tayi a qasa tana ta kuka yayinda take ta ihu..

Umma da Mama ne suka jiyo ihun Ameera daga dakunan su wanda ya sanya su fitowa tare.. Jin kukan daga dakin yaran nasu ne suka ruga a guje zasu shiga dakin.

Ameera wadda ta qwace kanta da qyar ta fito daga dakin a guje.. Ganin Ummanta ta ruga ta rungumeta tana ta kuka.. Mama ce tayi saurin riqe Layla wadda ta biyo Ameeran tana ta zage-zage.

“Lafiya?? me ya faru??” Umma ta tambayi Ameera wadda har gefen bakinta yana jini a dalilin marin da ta sha a wurin Layla.

Muryar Layla suka ji tana fadin “Wallahi baku isa ba.. Zayd nawa ne kuma bazan taba bari ya aure ta ba”

“Zayd??? wanne Zayd din? wannan baqauyen talakan? me ya hada ki da shi kuma??” Mama ta tambayeta cike da mamaki yayinda itama Umma ta cika da mamakin jin kalaman Layla.3

“Wallahi Mama ba talaka bane.. Zayd yana daya daga cikin yaran manyan masu kudin qasar nan.. yana da qaton kamfani don haka ni wallahi shi zan aura…”

“Umma wallahi qarya take yi.. kawai fa wani ta gani mai kama da Ya Zayd shine kawai ta zo ta hau ni da duka.. ba Ya Zayd dina bane”

“Kin san idan kika qara fadin Zayd din ki zan iya kashe ki?? Wallahi kin ji nayi rantsuwa I can go to any extent in order to have what is rightfully mine… Zayd baya da mata a duniyan nan sai ni tunda ni ya fara so ba ke…”

Saukar marin da ta ji a kumatunta ne ya sa ta saurin zabga ihu yayinda ta daga kai don ganin ko waye…

Gaba dayan su suka dago suka gan shi a tsaye..

ABBA!!

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *