ZABI NA CHAPTER 7 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 7 BY FADEELARH

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tun daga wannan ranar kuwa Ameera bata qara ganin Zayd ba.. bata qara jin labarin shi ba. Ta sa damuwa sossai a ranta don kuwa lokutta da dama takan zauna tayi ta kuka.. ta rasa wane irin so take yi ma Zayd.. takan yi tunanin anya akwai soyayya mai qarfin nata a duniya kuwa??? soyayyar ma wadda ita kadai take yin ta..+

Qawarta Zarah ta tausaya mata matuqa akan halin da ta shiga.. kamar dai yadda Umma tayi mata nasiha akan mayar da hankali kan karatu ita ma Zarah hakan tayi.. musamman ganin jarabawar su ta matso.

Da taimakon Allah Ameera ta samu natsuwa tayi facing upcoming examz dinta.

Har a wannan lokacin dai Layla bata zama class.. kullum tana maqale da Habib.. Gaba daya jikinta ya saki don tana gurzuwa a hannun shi.. ya lashe ta tas, tun abinda suke yi yana yi mata dadi har ta daina jin dadi. Gaba daya ta daina sha’awa kawai dai tana yi ne don ta samu kudi daga hannun shi. Shi kanshi Habib din ta zo ta kula ya rage rawan jiki a kanta..2

Ko da ta yi ma Haleema maganan abinda yake faruwa sai ta hada ta da wata mai sayar da kayan mata wadda ake kira ‘Lami gyara su tsab’ Lami dai kayan mata take sayarwa masu tsada wanda kuwa idan kika yi amfani da su tabbas zaki san baki kashe kudin ki a banza ba don kuwa biyan buqata 100%.2

Aikuwa dai dayake harka ce ta kudi kuma Layla ta sakar ma Lami su nan da nan ta hada ta da magunguna kala-kala ita kuma ta shiga amfani da su..

Tuni ta koma danya shar… Nan da nan Habib ya dawo kanta.. Saboda faranta mishi da take yi ma kudin da yake bata har doubling yayi wanda rabin su suke zuwa wurin Lami yayinda sauran suke shiga ma’ajiyar su ita da mama ‘Ghana must go’6

A lokacin da aka fara examz ne Layla ta fara zama a makaranta domin kuwa ta sani sarai idan bata ci jarabawa ba zata hadu da fushin Abba.

Kamar yadda ta qudurta a ranta kusa da Ameera ta dinga zama tana kwasar amsa.. Abin har mamaki ya dinga ba Zarah yadda take wulaqanta Ameera amma da jarabawa ta zo babu ko kunya ta maqale mata tana satar amsa.

A haka dai aka gama examz aka bayar da hutun wata daya.

♤♤♤♤♤♤♤♤

HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE

MARAFA ESTATE

Kwance take a kan gadon dakin shi cikin Duvet yayinda take kallon shi a tsaye gaban Vanity mirror yana shiryawa.

Tunda aka basu hutu a kullum Habib zai shigo unguwar su ya jirata su tafi gidan shi.. Har yau dai ya qi zuwa ganin Abba, kullum excuse dinshi daban.. tun tana yi mishi magana har ta haqura ta qyale shi.

A yanzu haka tsawon awa uku kenan suna gurzar juna.. bayan sun sarara ma juna ne ya shiga bathroom yayi wanka.

“Sweetheart wai ya maganar auren mu ne?” ta tambaye shi.

Zuciyar shi ce ta buga da jin wannan tambayar nata.. Ya ma za’a yi ya aure ta?? ko giyan wake ya sha ai bazai aureta ba. A yanzu kuwa ya amince da zancen Yusuf da yake fadin babu yadda za’a yi ya auri macen da ya gama sani a titi…2

Murmushi yayi ya juyo ya kalle ta yace “Very soon my pretty.. I really cant wait to have you everyday”

“Nima haka sweetheart.. na gaji da wannan harkar da muke yi babu aure a tsakanin mu kuma bana so yadda nake shan pills dinnan sossai domin kuwa ina tsoron kar suyi mun illa nan gaba”

STORY CONTINUES BELOW

A ran shi ne yace ‘like I care’

A fili kuwa yace “kar ki damu pretty babu abinda zasu yi miki.. yanzu dai je kiyi wanka ki zo mu ci abinci… Gashi can an kawo tuntuni. Ko ni zanyi miki??”

Murmushi tayi tace “a’a kayi zamanka.. na fa san yanzu idan mun shiga ba wankan kawai zaka yi mun ba.. qara zane ni zaka yi”

Fashewa yayi da dariya yace “ai ke din ce you are so sweet”

Ta sauka daga kan gadon itama tana dariya ta wuce bathroom.

Shi kuwa bayan ya gama shiri ne ya wuce falon shi ya zauna zaman jiran fitowarta.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Doorbell din gidan ake ta ringing babu sassauci.. Habib wanda yake zaune ne ya tashi ya je dubawa.. Ko da ya bude qofa gani nayi ya zaro idanuwa yayinda ya firgita sossai.. kai kace aljani ya gani.

“Fiddy???” ya kira sunan ta cikin wata irin murya ta marassa gaskiya.

Ratsawa tayi ta gefen shi ta shige ciki yayinda tace “hmmm su Habib kenan.. na ji qamshin mace a cikin gidan nan. Ashe dai labarin da nake ji a gari gaskiya ne.. ance ka samo wata hourglass shiyasa kayi watsi da ni ko??”

Habib wanda ya biyo bayanta muryar shi tana rawa yace “Fiddy please not now.. don Allah ki tafi kafin ta fito.. I promise you I will explain but for now…”

Kafin ya rufe bakin shi kuwa ta yi saurin hugging dinshi tare da cafko lips dinshi ta shiga tsotsa cikin qwarewa.. aikuwa nan da nan ya rude gaba daya. Dama ya kwana biyu bai dandana ta ba sai ya ji ta daban.. tuni ya biye mata..

Sai da ta tabbatar ta zura shi tukunna ta dan janye daga gare shi tace “for now what??? kana nufin baka son wannan??” ta zuge zip din rigarta ta cire.. ya rage daga ita sai inner wears.. Gaba daya hankalin Habib ne ya tashi.. tuni ya manta da wata Layla tana cikin daki.. aikuwa nan da nan ta raba shi da kayan jikin shi ta tura shi suka fada kan kujera suka fara sarrafa juna cikin qwarewa..

Babu abinda ke tashi a falon sai nishin su da kuma surutai kala-kala..

“Me nake gani??” muryar Layla suka jiyo cikin tsananin tashin hankali.

Habib yayi saurin sauka daga kan Fiddy yayinda ya rude gaba daya.. qoqarin janyo wandon boxers dinshi yake yi yayinda yace “pretty I can explain.. wallahi ba…”

Layla wadda hawaye suka wanke ma fuska ce ta daga hannu tace “just shut up Habib.. ashe dama kai dan iska ne ban sani ba?? dama kai mayaudari ne??? kace zaka aure ni ashe qarya ne??? kenan ka dauke ni a matsayin one of your prostitutes?”3

Fiddy ce ta fashe da dariya yayinda ta gyara kwanciyarta a kan kujera tace “wai dama don baki da hankali kina tunanin auren ki zai yi??? ai babu zancen aure anan ‘yan mata.. kuna dai taimakon juna ne kawai… and yes you are just one of his prostitutes don haka ki cire tunanin aure a ranki ki zo mu hadu mu haukatar da Sweetheart din mu” ta qarasa maganar yayinda ta kashe ma Layla ido.

Habib wanda ya kalli Fiddy ne yace “hey shut up”

Layla kuwa gaba daya jikinta yayi mugun sanyi.. Gani nayi ta zame qasa dafe da kanta tana rusa kuka.

A guje Habib ya qaraso wurinta ya riqe ta tare da fadin “Pretty please listen to..”

Wani wawan mari ta kwasa mishi sannan ta miqe tsaye tace “Allah ya isa tsakani na da kai kuma daga yau kar ka qara nema na… dan iska kawai”

A guje ta wuce tayi hanyar fita yayinda ta bar Shi dafe da kumatun shi… Tunda yake babu wanda ya taba marin shi sai gashi yau mace wadda bai dauka a bakin komai ba ta mare shi..

Gani nayi ya bi ta a guje yana fadin “Layla please wait… don Allah ki tsaya inyi miki bayani..” yana kai qofa ya ji tayi banging mishi ita wanda har sai da ta bugi goshin shi.

STORY CONTINUES BELOW

“ouch” ya fada tare da massaging din goshin nashi.

Fiddy ta miqe tsaye ta nufi wurin shi tare da dafa goshin shi sannan ta shafa kumatun shi tace “just leave her.. na tabbatar zata dawo ba da dadewa ba.. I know girls like her”

“are you sure???” ya tambaye ta with so much hope.

Janyo shi tayi suka nufi hanyar dakin shi yayinda tace “yes i am sure… mu je in gwada maka wani abu.. na zo da sabon salo wanda zai mantar da kai duk wata damuwa da kake ciki”

A haka dai ta janye shi suka wuce dakin shi.

♤♤♤♤♤♤♤

GIDAN MALLAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

A rude Layla ta shigo gidan.. Fuskarta duk tayi jajawur ta kumbura. Tayi sa’a gaba daya ‘yan gidan basu falo. Duk suna can bayan gida suna taya ma’aikatan Umma yin kunun aya..

Dakin Mama ta shiga hankali a tashe ta zube kan gado ta cigaba da rusa kuka.

Mama wadda ta fito daga kewaye ne ta tsaya turus ganin Layla tana ta kuka. Da sauri ta qaraso wurinta tana fadin “ke lafiya kike kuka haka?? me ya faru??”

“Mama na shiga uku na lalace… Habib ya ci amana na. Ashe dan iska ne ban sani ba” Layla ta fada tana kuka.

“ban gane dan iska ba.. me yayi??” Mama ta tambaye ta

“Kama shi nayi tsirara da mace suna iskanci”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Habib din?? kenan yaudarar ki yake yi kenan?? lallai ba namijin aure bane wannan.. toh ke me kika je yi gidan shi??? kar dai ki ce mun kema yana kwanciya da ke din ne???”3

Layla ta sha jinin jikinta yayinda ta rasa yadda zata amsa wannan tambayar ta Mama tunda dai bata taba fadi mata cewar tana kwana da Habib ba..

“Ya na ji kinyi shiru.. kina kwana da shi ne??” Mama tayi tambayar yayinda ta kafa mata idanuwa.

“a’a Mama..”

“toh meyasa kika je gidan shi???”

“tare da Haleema muka je.. zata ba Yusuf saqo shine muka tarar da su” ta qara fashewa da kuka yayinda take picturing Habib da Fiddy a lokacin da ta tarar da su suna gurzar juna cike da qwarewa.

Mama ta rungume ta tace “gaskiya ina gani lokaci yayi da zaki rabu da Habib dinnan.. tunda dai kin samu abin arziki a wurin shi ai ina ga kin ci riba.. Tabbas ba mijin aure bane, irin wannan ma ki je ki aure shi ya debo cuta ya watsa miki..”1

Zuciyar Layla ce ta buga jin kalaman Mama.. Abinda bata taba kawowa a ranta ba..

Cututukan zamani!!

Shin a yadda yake kwanciya da wata mace da kuma yadda yake kwanciya da ita babu protection how sure is she lafiyar shi qalau?? how sure is she bai riga ya zuba mata wata cutar ba?? she was only focused on emergency pills din da take sha don kar ta dauki ciki yayinda ta manta babban matsala irin wannan…

Nan da nan ta rude yayinda ta qara fashewa da sabon kuka..

“Ke kam ki daina kuka haka.. kiyi qoqari ki samu wani saurayin mai arzikin ki cigaba da cin arziki.. Habib kuma daga yau babu ke babu shi kin ji na fadi miki”

A haka dai Mama ta dinga aikin lallashi.. A taqaice dai wani mugun zazzabi ya rufe Layla.. Yinin ranar tana cikin bargo tana fama. Ko da ta sha magani bai sauka ba.. Da Abba ya dawo aka sanar da shi ne ya aika aka Kira wata Nos da take da chemist a qasan layin su ta zo tayi mata allura.. Da haka ne ta dan samu sauqi.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Bayan kwana uku!!

Zaune take a kan sallaya tana karatun Al-qur’ani mai girma.. Ameera dai al’adarta ce wannan a kullum idan ta idar da sallar Isha’I ta dora da Shafa’i da witr sai ta rufe da karatun Al-qur’ani.

Bayan ta gama ne ta rufe Qur’anin ta mayar da shi mazauni shi sannan ta dawo ta ninke sallayarta.

A daidai wannan lokacin ne Layla ta shigo dakin ta hau gado ta kwanta..

Wani ikon Allah tun kwana uku da suka wuce da wannan al’amari ya faru tsakanin ta da Habib duk ta bi tayi sanyi.. Gaba daya ta rage magana dukda dama yawanci masifa ce. ‘Yan gidan sunyi tunanin qila bata qarasa warwarewa daga zazzabin bane.. A cikin kwanakin nan uku Habib ya matsa Mata da waya da text messages.. daga baya ma blocking din shi tayi. Haleema ma ta bata haquri dukda ta San Habib ya kwafsa sannan zai yi wuya Layla ta haqura.. Kuma kamar yadda tayi zato ne… Sam ta qi sauraron ta.

Wayar Ameera ce tayi ringing. Da sauri ta ajiye sallayar da ta ninke ta nufi wurin gadonta ta dauki wayar.

Wata baquwa lamba ta gani, baquwar lambar ma special number.

Kallon fuskar wayar ta cigaba da yi tana tunanin ta amsa ko kar ta amsa.

A haka har wayar ta gama ringing.. babu bata lokaci aka sake kira.

Gani nayi tayi answering yayinda take fadin “Bismillahir-Rahmanir-Raheem” sannan ta kai kunnen ta.

“Assalam..” ta jiyo muryar shi, Muryar mutumin da take bala’in so a rayuwar nan, muryar da ta fi mata kowacce murya dadi a duniyan nan, Muryar da ko bata cikin hayyacinta idan ta jiyo zata fadi ko waye… Muryar Zayd.

A firgice na ga ta zare wayar daga kunnen ta sannan ta kalla tace “Ya Zayd??”

Zuciyar Layla ce ta buga jin Ameera ta kira sunan shi.. Haka kawai ta ji jikinta yayi sanyi..1

Da sauri Ameera ta mayar da wayar kunnen ta ta ji yana fadin “baki amsa sallamar ba Ameera..”

Gani nayi ta dafe qirjin ta daidai saitin da zuciyarta take yayinda ta zauna a gefen gadonta tace “Wa’alaikas Salam.. Ya Zayd kayi haquri.. uhm, nayi mamakin kiran naka ne.. ina ka samu lambar waya ta?? Uhm.. Sorry ya jikin ka?? ka warke?? meyasa ka bar asibiti ranan baka jira ba? Abba da Umma sun je duba ka amma aka ce ka tafi.. Ka sa ina ta tunanin halin da kake ciki..”

“Wacce tambaya zan amsa miki Ameera???” Ya fada cikin harshen shi da yake yi mata kama da na larabawa.

Da sauri tace “yi haquri Ya Zayd.. How are you?”

“why dont you come and find out yourself?? ina qofar gidan ku..”

Zabura tayi ta miqe tsaye yayinda tace “Kana waje?? wurin Ya Layla ka zo???”

“No Ameera.. wurin ki na zo. Ko bazaki fito mu gaisa bane?”

“Zan fito Ya Zayd.. Ina zuwa” ta fada da sauri yayinda ta cika da murna. Atleast she will get to see him again.1

Gani nayi ta nufi gaban madubin su ta dauki turare ta fesa sannan ta wuce ba tare da ta kalli fuskarta ba balle har ta shafa mata wani abu da ya danganci kwalliya.

Ameera tana fita na ga Layla ta tashi zaune dafe da qirjinta.. Bata san daga ina ba sannan bata san ya aka yi ba, wani mugun kishi ne ya taso mata, ya tokare qirjin ta da maqoshinta.. why is that???GIDAN MALLAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI+

Ameera dai ko da ta fito daga dakin su sai murmushi take yi tana mamaki.. The very first time in her life da zata fita wurin wani- ba a matsayin ‘yar aike ba sai don ita aka zo gani… Wanda ya zo ganin ta din ma wai ZAYD!

Ganin abun take yi kamar a mafarki..

A falo ta tarar da kowa banda Layla da ta baro a daki.

“Ya na gan ki sanye cikin Hijab.. ina zaki je da daren nan?? Umma ta tambaye ta cike da mamaki.

Gaba daya falon suka juyo suna kallon Ameera wadda ta sunkuyar da kanta ta nemi wuri kusa da Abba ta zauna a qasa.

“Uhm dama Ya Zayd ne yazo shine ya kira ni yace yana waje..” ta fada a sanyaye.

Mama ce ta fashe da dariya tace “au, ya dawo miki kenan.. ai dama ke ce daidai da shi… qwarya ta bi qwarya.. Allah ya sanya alkhairi”3

Abba wanda ran shi ya baci da maganan Mama ne ya kalli Ameera yace “tashi ki je”

Umma tace “kar ki dade kuma..”

“Bazan dade ba Umma..”

Ibrahim ne yace “In zo in raka ki Ya Ameera??”

Murmushi kawai Ameera tayi.. ta sani sarai neman magana yake yi saboda sun sani cewar yau din itace rana ta farko da zata fita ganin wani.

Aikuwa tana fita Abba ya sallami su Ibrahim yayinda ya shiga yi ma Mama fada tare da nuna mata rashin jin dadin shi akan maganar da tayi.. Mama kuwa sai da ta gwammace dama bata yi magana ba don kuwa sai da Abba ya wanke ta tas.

☆☆☆☆☆☆☆

Ameera dai tana tafe tana tunanin dalilin da ya sanya Zayd ya zo wurinta a yau..

Wata zuciya ce tace ‘Qila ya zo ne yayi miki godiya akan taimakon da kika yi mishi’ yayinda dayar tace ‘toh ina ma ya san ke ce kika taimake shi? mutumin da baya cikin hayyacin shi a lokacin’

“Ko ma dai menene I am about to find out.. Ni kam I am so very much happy that I am going to see him” ta fada yayinda take cike da murna.

Zaune yake a kan dakalin qofar gidan sanye cikin kodadden wandon Jeans dinshi da kodaddar shirt yayinda yake riqe da torchlight phone dinshi yana jujjuya ta kamar kullum.

Qarar gate da ya ji ne ya sanya shi dagowa da sauri ya kalle ta.

Ameera dai tunda ta fito kanta a sunkuye yayinda zuciyarta take ta bugawa… Gaba daya jikinta rawa yake yayinda yake a sanyaye.

Zayd wanda ya qura mata idanuwa ya kula da how nervous she is.. hakan kuwa ya so ya sa shi dariya!

“Assalamu alaikum” ta fada a lokacin da ta qaraso wurin shi.

Yana murmushi yace “wa’alaikis salam”

Ameera dai daskarewa tayi a tsaye yayinda take jin al’amarin kamar a mafarki..

Zayd wanda yake jira ta zauna sai gani yayi ta tsaya tsaye yayinda ta kasa dago kanta ma ta kalle shi.

“Ameera a haka zamu gaisa baza ki zauna ba??? ko sauri kike yi ne???”

STORY CONTINUES BELOW

Dago kanta tayi ta kalle shi wanda hakan ya haddasa mata wata muguwar faduwar gaba.. Ba wani abu ya janyo hakan ba illa bala’in kyan da ta ga ya qara yi mata.. Ya ma za’a yi ta qi son wannan mutumin??

“Ameera please sit” ta jiyo muryar shi yayinda tayi saurin kallon gefen shi a kan dakalin.. Jiki a sanyaye ta matsa ta zauna.

Har a wannan lokacin jikinta rawa yake yi.. duk ta bi ta takure. Ta dunqule yatsun hannuwan ta wuri daya yayinda Zuciyarta take ta bugawa..

“Uhm first of all ina so in baki haquri akan laifin da nayi miki na barin asibiti a ranar ba tare da na jira ki nayi miki godiya ba… bazan taba mantawa da taimakon da kika yi mun ba, thank you very much”

Zuciyar Ameera ce ta kusa narkewa a dalilin wannan kalaman nashi… sossai ta ji dadi da yace bazai taba mantawa ba.. atleast ta San hakan yana nufin bazai taba mantawa da ita ba.

“Babu komai Yaya.. amma..” sai kuma tayi shiru.

“Amma me?? you wanted to ask a question I guess”

“uhm.. amma ya akayi ka san ni ce na kai ka asibiti??? na ga fa har na tafi baka farfado ba”

Murmushi yayi yace “Ameera I only passed out for a while and I could hear voices around me..”

Da sauri ta dago kanta ta kalle shi tace “does that mean ka ji abinda na fada ranar..”

Bai bari ta qarasa ba yace “kamar me kenan? was I supposed to hear something??” yayinda yake kallonta cike da curiosity.3

Kawar da kanta tayi ta duqar tare da runtse idanuwanta ta bude..

“No… babu komai..” ta fada yayinda take fatan Allah yasa bai ji Confession dinta ba a ranar.

Shiru ne ya ratsa a tsakani.. Kowannen su da abinda yake tunani..

Ameera dai addu’a kawai take yi akan Allah yasa bai ji ba… wannan irin abun kunya. A matsayin ta na ‘ya mace tayi confessing soyayyarta zuwa gareshi.. qila ma bazai qara ganinta da mutunci ba…

“Will you marry me??” ta jiyo wannan tambayar kamar daga sama.6

Zabura tayi ta miqe tsaye… A yanzu dai ta tabbatar abinda yake faruwa ba gaske bane, ta tabbatar Zayd bazai zo yace yana sonta ba balle har yace zai aure ta.. shin soyayyarshi har ta fara gaya mata qarya kenan?? Lallai tana buqatar addu’a don kuwa ta amince ta samu matsala a qwalwa… shin ko dai mafarki take yi ne??

Gani nayi ta dan mintsili hannun ta wanda ya tabbatar mata da lallai ba mafarki take ba..

A rude tace “Ya Zayd me kace???”

“Zo ki zauna” ya fada tare da nuna mata gefen shi yana murmushi.

Jiki a sanyaye ta koma ta zauna domin kuwa a yadda qafafuwan ta suka yi sanyi idan ta dade a tsaye zata iya faduwa.. A yadda zuciyarta take bugawa kuwa tana kyautata zaton zata faso qirjinta any moment.. a tunaninta ma shi da yake zaune gefenta yana jiyo bugun zuciyar nata..

“Na tambaye ki baki bani amsa ba Ameera.. please will you marry me??”4

A yanzu kuwa dafe qirjinta tayi sannan ta runtse idanuwan ta..

“A simple Yes or No will do Ameera.. idan baki so ki aure ni it’s fine.. dama I just wanted to…”

“Yes Ya Zayd… Yes” ta fada yayinda idanuwanta suke a runtse.. “Yes I will marry you..” ta cigaba da fadi.5

Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Zan iya yi ma Abba maganar auren mu??”

Daga mishi kai tayi alamar ‘eh’

“Okay then.. zaki iya shiga gida. Good night” ya fada yana murmushi.

Ameera dai kasa tashi tayi, gaba daya ta rude.. abubuwa ne dayawa suke ta yawo a qwalwar ta..

STORY CONTINUES BELOW

what has she done??? did she just accept a marriage proposal from Zayd?? this is too good to be true.. Haka kawai rana guda Zayd zai zo qofar gidan su ya Kirata ta fito ya tambaye ko zata aure shi?? toh me zai sa ya fadi haka??? Yana sonta ne kamar yadda take son shi??? Ko dai ya ji abinda ta fadi mishi ne ranan shine ya tausaya mata?? Babban burin ta a duniya shine ta ga ta kasance matar shi.. toh kenan should she be happy about this???3

“Ameera zan tafi.. ki shiga gida. Kin dai san bazan tafi in bar ki anan ba ko??”

Gani nayi ta miqe jiki a sanyaye ta wuce ta shige gida ba tare da ta waiwaye shi ba. Shi kuwa Zayd haka ya bi ta da idanuwa har ta shige!

Sai da ya ji qarar gate din gidan sannan na ga yayi dialing torchlight phone dinshi yana jira ayi picking..

“Bilal zo mu tafi.. I need to see Musty right away”

☆☆☆☆☆☆☆

Ameera dai tana shiga gida straight dakin su ta wuce ta cire Hijab dinta ta haye gado ta shige bargo.. Ban ankara ba na ji ta fashe da kuka.2

Layla wadda ta kasa bacci tun dazu tana cikin nata bargon ta ji shigowar Ameera har zuwa lokacin da ta hau gado ta fara kuka..

A ranta ne tace “why is she crying??? Hala Zayd din ya kwafsa mata??? maganinta kenan.. ba dai tace baqauye talaka take so ba?? kadan ta gani..”2

Tsaki ta ja yayinda ta gyara kwanciya tace “Malama don Allah ki rage sautin kukan nan naki.. bacci zan yi”

Ameera dai sauka tayi daga kan gadon ta wuce kewaye ta cigaba da kukan.. Ta sani sarai yau ranar girkin Umma ne don haka tana can tana hidimar mijinta… she will have to keep this to herself har sai da safe kenan!!

☆☆☆☆☆☆☆☆

MUSTAPHA ISA YUGUDA RESIDENCE

GWAMNA ROAD

Wuraren qarfe goma saura yana zaune a falon qasa yana jiran abokin shi wanda ya kira shi a waya yace yana zuwa..

Zarah wadda ta fito sanye da Hijab dogo ce ta qaraso wurin shi ta zauna a kan cinyar shi tace “sweetheart wai bazaka zo mu kwanta bane?? tun dazu nayi shirin bacci ina jiran ka fa..”

Wasu soft kisses ya shiga sakar mata yayinda ya rungume ta very tight yace “yi haquri Baby.. wallahi ZAF ne ya kira ni wai gashi nan zuwa. I think something important came up”

“Ashe ya dawo daga Dubai din…” Zarah ta fada.

“Yeah.. jiya ya dawo. Ban ma san ya shigo Kaduna ba sai dazu yace mun zai zo..”

“Allah sarki.. shi kam yana fama da zirga-zirga”

“Ai Zayd mugun workaholic ne.. ni na qagara ya samo macen da zata so shi tsakani da Allah ya aure ta ko Allah zai taimaka tayi regulating wannan stress din da yake…”3

Bai qarasa magana bane suka jiyo qarar doorbell.

“I think its him.. let me check” Mustapha ya fada yayinda Zarah ta sauka daga kan cinyarshi sannam shi kuma ya miqe ya nufi main door na gidan.

Mustapha yana bude qofar na ga ya zaro idanuwa yayinda ya ja baya da sauri kamar wanda ya ga ghost..

“Hey, waye wannan?? ZAF is this you??? what happened??? ya na ga kayi baqi??? abokina accident kayi ko me??? meye wannan a goshin ka??? Your clothes??” ya dinga jero mishi tambayoyi non-stop yayinda fuskar shi tayi displaying tsananin mamaki.

Ni kaina da na leqa na hango wanda aka kira ZAF din sai da na ja baya da sauri…

Masu karatu Zayd na gani… Zayd dai na Layla da Ameera..10

Toh ban gane ba, wai dama ZAF shine Zayd?? ya aka yi haka??5

Hararar shi yayi yace “malam bani wuri in wuce don Allah.. tambayoyin naka sun yi yawa.. wanne zan amsa maka??” Zayd ya fada yayinda ya ratsa ta gefen shi ya shige ciki.

Mustapha wanda yayi saurin rufe qofa ya biyo bayan shi yace “duka tambayoyin zaka amsa mun.. how do you expect me to not ask…”

Salatin da suka ji Zarah tana ta yi ne ya sanya suka firgita..

Ganinta suka yi a tsaye yayinda ta rufe bakinta da dukkan hannuwanta tana kallon Zayd.

Da sauri Mustapha ya qarasa wurinta ya janyota jikinshi yace “Baby what is it??”

Zayd ta nuna da hannu tace “me ya same shi na ga yayi baqi haka??”

Zayd wanda ya zauna a kan daya daga cikin lafiyayyun kujerun falon yana shafa fuskar shi yace “ba fa wani abu bane.. its just paint, da zarar nayi wanka shikenan.. why are you guys exaggerating?? do I look that bad???”

Cike da mamaki Mustapha yace “Paint kuma?? you mean har kana da lokacin batawa a rayuwarka kayi ma kanka fenti haka nan?? wato tambayar mu kake yi if you look bad ko?? well the answer is YES, you look horrible”

Turo baki Zayd yayi yace “kai dama baka da kirki wallahi..”

Mustapha da Zarah suka fashe da dariya…

“Idan kin gama dariyar sai ki taimaka mun da tea Hajiya..” Zayd ya fada yayinda ya gyara zaman shi a kan kujerar da yake zaune.

Zarah tayi saurin matse dariyarta tace “toh Yayana.. matarka dai ta shiga uku da hada shayi” ta kalli Mustapha tace “Sweetheart kai ma zaka sha??”

“No thanks Baby, Ni dan Nigeria ne ban saba ba… shayi sai larabawa”

Zayd wanda yake murmushi yace “Allah dai ya sa my Ammi is a Nigerian balle ayi mun gori”

“Haka ne amma you are an Arab tunda Abbu balarabe ne.. Ni kam don Allah ka bani labari, ya aka yi ka zama baqi haka?? what are you up to???”

Zarah wadda ta kusa fita daga falon ce ta juyo tace “Yayana don Allah ka jira ni in dawo kafin ka fara bada labari.. I really want to hear”1

“Okay then.. I will wait for you” Zayd ya fada yayinda ya fiddo wayar shi qirar Samsung Galaxy S20 Ultra ya fara latse-latse.. Da alama yana replying wasu messages ne.

“Na tabbatar idan Ammi ta ganka bazata gane ka ba… Kai wallahi hatta twin dinka Zaheera bazata gane ka ba balle su Maheera” Mustapha ya fada yayinda yake qare mishi kallo cike da mamaki.

Zayd wanda ya dago kai ya kalle shi yana murmushi ne yace “i swear ni kaina idan na kalli kaina a madubi bana gane ni ne.. I still can’t believe I did all that I have done with this look abokina”

Hmmm…

♤♤♤♤MUSTAPHA ISA YUGUDA RESIDENCE

GWAMNA ROAD+

“Wai tsaya ZAF, yanzu kana nufin duk wadannan abubuwan kayi saboda ka samu soyayyar mace? ka dinga baro Lagos ko Abuja just to see her sannan ta wulaqanta ka? Yaushe ka zama Romeo ne haka bani da labari?? this is unbelievable..” Mustapha ya fada cike da tsananin mamaki.1

Shi kanshi Zayd he is finding it difficult believing what he did for Layla.. He never in his life thought mace zatayi stressing rayuwar shi kamar yadda Layla tayi.

“toh wai dama kai ne Zayd din Layla da Ameera take bani labari wanda take bala’in so???” Zarah ta fada confusedly..

“Baby kin san su ne??” Mustapha ya tambayeta yayinda Zayd yake kallonta yana jiran amsar da zata bayar.

“Na san su mana Sweetheart.. Ameera ce fa da sister dinta, friend dina ta school da nake baka labari.. the one that fell madly in love with your friend here amma shi kuma ya nace ma Yayarta saboda kawai kyakyawa ce mai unique eyes”

“oh really???” Mustapha ya fada yayinda ya kalli Zayd wanda yake kwasar dariya yace “ni fa ba don kyan ta nake sonta ba…”

Zarah tana kallon shi tace “idan ba don kyan ta bane toh tell me, don meye?? bazaka dai ce mun saboda halinta bane ko??? tunda dai kace ko da kayi bincike akan su baka samu feedback mai kyau ba akan ta even though you didn’t want to believe coz you were blinded by..”

“toh ko ma dai meye yanzu I have realized my mistake..” ya fada da sauri1

“ni dai wallahi ka kyauta ma kanka da ka rabu da Layla.. sossai ka bani haushi da na ji labarin abinda ya dinga faruwa tsakanin ku.. Yanzu duk ba wannan ba, dagaske kake yi zaka auri Ameera???”

Kai tsaye yace “yes..”

“Lallai ma Ameera, dama fa bala’in sonka take yi. Toh amma kuma idan ta gano ko kai waye zaku samu matsala don from what she told me bata son auren mai kudi… ta fi so ta auri daidai ita wanda bazai wulaqanta ta ba.. she just wants to be loved unconditionally and wants her husband’s time..”

“Toh kai zaka iya bata abinda take nema din?? don fa na san ka abokina.. You only have time for your company” cewar Mustapha.

“I’ll try..”

Mustapha yace “Gaskiya I am happy for you abokina, Ammi will be very happy to hear this news”

“I bet she will..”

Ya kalli Zarah yace “my plea right now is don Allah kar ki gwada mata kin san ni. Bana so ta san ko ni waye har sai bayan bikin.. I am scared zata iya qin aurena idan ta gane I am not the Zayd da ta sani..”

“Hmm.. wato yadda abokin ka yayi mun haka zaka yi mata ko??”

Yana murmushi yace “ba haka na so ba.. bana so in rasa ta ne after the saga with Na’eema and Layla”

“Na’eema kuma, wacece ita??” Zarah ta tambaya in a confused tone.

toh fa…

“Zan baki labari” Mustapha ya fada

Zayd ya miqe tsaye yana murmushi yace “bari in tafi gida.. ina da meeting gobe da safe kuma yakamata in sallami Bilal ya je ya huta.. he needs it”

Mustapha wanda ya tashi tsaye shima yace “Gaskiya Bilal yana qoqari sossai… you can never get a better P.A”

STORY CONTINUES BELOW

“I agree with you abokina.. I kinda consider Bilal a brother because he has always been loyal to me.. please kar ka manta gobe idan na gama meeting dina zamu je ofis din Abban Ameera kamar yadda na fadi maka.. its safer mu same shi a ofis dinshi, I need to explain everything to him.. Allah yasa afterwards ya amince ya bani auren ta”

Cike da murna Zarah tace “Insha Allah zai baka.. ni kam I am so happy wallahi.. Allah dai yasa kana son qawa ta dagaske ba wai kayi ne don ka rama wulaqancin da Layla tayi maka ba??”

“Sannu mai qawa… na san interrogating dina kike yi cikin siyasa toh bazan fadi miki ba. It’s for you to find out….” ya fada tare da yi mata gwalo.

Dariya Zarah tayi tace “toh shikenan.. sai da safe”

“Good night and thanks for the tea”

“You are welcome”

Tare suka fita da Mustapha wanda zai raka shi.

Ko da suka isa wurin motar Zayd qirar Range Rover evoque sabuwa gal tana ta qyalli Bilal ya fito daga motar suka gaisa da Mustapha.

Mustapha ya kalli motar da kyau yace “mutumina yaushe ka siya wannan?”

“Wannan ai tun last month aka kawo mun ita.. kawai ban taba hawan ta bane sai wannan zuwan”

“Kai ZAF.. anya a duniyan nan banda su Ammi da CITY-SHELTERS akwai abinda kake so irin mota kuwa???”

“AMEERA…” Zayd yayi saurin fada tare da kashe mishi ido daya yana murmushi.3

“Inaa abokina, idan dai kace kana so kayi using dinta don ka huce haushin abinda yayar ta tayi maka, I would believe you. Ni dai Allah yasa idan ka auro ta ba ajiye ta zaka yi a qaton gida kai kuma kayi ta hidima da kamfanin nan naka mai qera gidajen da basu qarewa ba..”

Zayd yana dariya yace “Zan baku mamaki Musty..”

“Toh Allah yasa positive one ne mamakin da zaka bamu”4

nikuwa nace ‘ai lallai kam’

Haka dai suka cigaba da ‘yan hirarrakin su daga nan suka yi sallama da juna.

Bayan Zayd ya tafi Mustapha ya koma cikin gida ya tarar Zarah tana jiran shi..

Sa shi gaba tayi sai da ya bata labarin Zayd da Na’eema.. Labarin da ya girgiza ta sossai, Lallai mata sai dai a ji tsoron su.. tabbas bata yi blaming dinshi ba for disguising himself all in the name of finding true love.. Abinda ta sani shine Ameera tana son Zayd tsakani da Allah kuma ta tabbatar bata cikin Mata irin LAYLA da NA’EEMA!! fatan ta dai Allah yasa shi din dagaske yana son Ameera..1

Wacece Na’eema??1

♤♤♤♤♤♤♤♤♤

Washegari

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Wuraren qarfe Goma na safe Ameera tana kwance cikin bargo yayinda take ta tunanin abinda ya faru tsakanin ta da Zayd a jiya.. Har garin Allah ya waye bata yi bacci ba, tana ta faman tunanin shi.

Ameera bata taba sa ran Zayd zai ce yana sonta ba balle har yace zai aure ta.. toh amma ai bai ce yana sonta ba, Kai tsaye auren ta ya buqata.. me kenan???

“Ameera wai lafiya yau baki fito kin taya ni aiki ba??? ko ba lafiya ne?” ta jiyo muryar Umma wadda tuni ta qaraso wurinta ta yaye bargon da ta rufa da shi.

Da sauri ta tashi zaune tace “lafiya na lau Umma, ina kwana”

Umma wadda take qare ma ‘yar ta kallo ce ta zauna a kan gadon tace “ya na ga kamar idanuwan ki sun kumbura.. kin yi bacci kuwa Ameera??”

STORY CONTINUES BELOW

“Umma na dan yi karatu ne.. kin san na fadi miki ina so in fara shirya ma abubuwan da za’a koya mana ne next semester”

“toh shikenan, amma dai ki dinga qoqari kina samun isashen bacci kar ciwo ya kama ki”

“toh Umma”

“Me Zayd din yace miki jiya da ya zo?”

Da sauri ta kalli Umma yayinda tayi shiru ta kasa magana… ita kam har ga Allah kunya take ji ta fadi ma Umma abinda ya faru.

“uhm.. ya zo yayi mun godiya ne akan taimakon da nayi mishi lokacin da ya suma a makarantar mu”

“Ayyah, ya jikin nashi?”

“Da sauqi sossai”

“toh maza ki tashi kiyi wanka ki zo ki karya..  kowa ya ci abinci ke kadai ce baki ci ba”

“toh Umma”

☆☆☆☆☆☆☆

Ameera dai yinin ranar tayi sanyi sossai.. dukda dama ba hayaniya gareta ba amma dai da ka ganta zaka gane akwai wani abu.. Umma ta kula da hakan amma ta qyale ta tunda dai ta tambaye ta tace babu komai.

Hatta su Munnir sun gane akwai wani abu don kuwa ‘Kabhie khushi kabie gham’ din da suke kallo yau bata zauna kallon shi ba.

Ta so ta kira qawarta Zarah ta fadi mata abinda ya faru tsakanin ta da Zayd amma ta kasa.. Gaba daya ma gani take yi kamar ba dagaske ba.. Ita kanta bata gama digesting abun ba balle har ta fara fadi ma mutane.

☆☆☆☆☆☆☆

KADUNA STATE MINISTRY OF EDUCATION

Zaune yake a ofis dinshi yayinda yayi shiru yana juya labarin da Zayd ya gama bashi.

Kamar yadda Zayd da Mustapha suka shirya zasu je su samu Abba suyi mishi bayani hakan suka yi.. Abba dai da farko bai gane Zayd din ba domin kuwa ya zo mishi a ainihin yadda yake ba kamar yadda ya san shi ba.. Zayd ya bashi labarin rayuwar shi tun daga farko har zuwa qarshe (zan baku wannan labari a gaba) sannan yayi mishi bayanin abinda yake tsakanin shi da yaran nashi guda biyu..

“Don Allah Abba kayi haquri akan abinda yayi, yayi ne ba don wani abu ba sai don ya tabbatar ya samu mace wadda zata so shi tsakani da Allah….” cewar Mustapha.

Abba wanda yayi shiru kallon Zayd yake yi yayinda ya kasa magana… Allah ya sani tunda ya fara ganin Zayd yake son shi musamman don halin shi da kuma yadda ya riqe addinin shi da muhimmanci.. Ya so ma Layla shi a matsayin miji amma ta qi, A yanzu da ya zo a matsayin masoyin Ameera ma ya ji dadi amma kuma baya ji zai iya bashi auren ta knowing who exactly he is.. Abba bai taba sha’awar bayar da auren yaran shi ga Rich and powerful people kamar Zayd ba.. Burin shi a rayuwa shine ya tsaya a matsayin da Allah ya ajiye shi, baya so ko alama mutane su ga kamar KWADAYI da SON ABUN DUNIYA ya sanya ya bayar da yaran shi ga masu arziki.

Gyaran murya yayi sannan yace “toh Alhamdulillah, Zayd na ji bayanin ka.. tunda na fara ganin ka na yaba da halayen ka sossai, Zan so ka zama siriki na domin kuwa nayi imani da Allah zaka riqe mun yarinya cikin amana toh amma gaskiya a yanzu bazan iya baka Ameera ba saboda kai da ita baku dace da juna ba, yanayin rayuwar ku ba daya bane, Bani da burin aura ma ‘ya ta mijin da mutane zasu kalle ni a matsayin mai kwadayi da son abin duniya.. Zan fi so in aura mata miji wanda yake da rufin asirin shi daidai gwargwado wanda ya san darajar ta…”

Basu ankara ba suka ga Zayd yayi kneel down a qasa yayinda ya hada hannuwan shi biyu yace “Don Allah Abba kar ka hana mun Ameera, nayi maka alqawari zan kula da ita fiye da yadda zan kula da kai na.. bazan taba wulaqanta ta ba, Zan fifita ta akan duk wata mace a fadin duniyan nan.. Don Allah Abba kar ka biye ma maganan mutane, you know it’s not true and we all know it’s not true.. don Allah Abba ka amince in turo a nema mun auren ta.. please I beg you”1

STORY CONTINUES BELOW

Mustapha wanda yake zaune yana kallon abokin shi sossai yayi mamakin actions dinshi. Bai taba ganin Zayd yana roqon wani abu a rayuwarshi ba. Tun da suka taso ya sani cewar duk abinda yake so komai tsadar shi sannan a duk inda yake idan har kudi zai siya wannan abun toh fa sai ya mallake shi.. idan kuwa ba abu bane da kudi zai siya he can go to any extent to get it amma banda ROQO.. he never begs for anything.. A yanzu ya sa ran lallai abokin nashi yana son Ameera domin kuwa da baya son ta bazai taba kai gwiwar shi qasa yana roqon a bashi aurenta ba.. shin dagaske yana sonta din??1

Ji suka yi Abba yace “Kai Zayd tashi tashi.. ya isa haka nan”

Zayd ya tashi ya koma kan kujera.

“Kar ka damu zan je inyi shawara sannan zan tambayi ita Ameera idan tace ta amince zata aure ka shikenan..”

Wata ajiyar zuciya ya saki wadda daga Abba har Mustapha sai da suka kula..

“Abba nagode sossai amma ina neman wata alfarma daga wurin ka..”

Abba yana murmushi yace “wacce alfarma ce wannan Zayd???”

☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Zaune suke a falo gaba dayan su wuraren qarfe tara na dare wanda Abba ne ya tara su.

Gaba daya yaran suna zaune a qasa yayinda iyayen nasu suke kan kujera..

“Na tara ku a nan falon ne don in sanar da ku wata magana..”

Gaba dayan su suka mayar da hankali don jin maganar da Abba zai yi..

“Magana ce akan yaron nan Zayd..”

Da sauri Ameera ta dago kai ta kalli Abba yayinda Layla ta cika da mamaki.

“Ya zo ya same ni a ofis yayi mun magana akan yana son auren daya daga cikin yaran nan”

Tun kafin Abba ya rufe baki ne Mama tace “wacce ‘yar? ba dai tawa ba ko??? don wallahi bazan dauki ‘ya ta in ba talakan banza ba”

Abba dai shiru ya dan yi yana takaicin hali irin na Mama.. Wato da ace yau Zayd ya fito musu a ainihin shi na mai arziki a guje zata amince ya auri ‘yar ta kenan?? Lallai duniya ta zama abinda ta zama.. A wannan lokacin ne ya tuno alfarmar da Zayd ya nema a wurin shi..1

“Kwantar da hankalin ki Maman Layla.. Zayd dai ya zo neman auren Ameera ne ba Layla ba”

Zuciyoyin Ameera da Layla ne suka buga.. A bangaren Ameera ta sani cewar yace zai yi ma Abba magana amma bata san cewar da wuri haka bane.. ita kuwa Layla mamaki take yi wai Zayd ya zo neman auren qanwarta, the last time she checked ko atamfar chiganvy da qyar ya siyo mata.. toh ina ya samu kudi da har yake niyyan yin aure??

“Ke Layla shin dagaske ne babu komai a tsakanin ki da shi a halin yanzu??”

Layla wadda ta dan yi shiru gaba daya kanta ya kulle.. Haka kawai wata zuciya take ayyana mata lallai something is not right..

“Babu komai a tsakanin su Abban yara.. ‘ya ta dai bazata auri talaka ba don kuwa ba kalar wahala bace” Mama ta fada cike da gadara.

“Ina so in ji daga bakin ta ne don kuwa bana son qananan maganganu daga baya.. Layla ke nake sauraro” Abba ya fada yayinda ya dakatar da Mama

“Eh Abba.. Babu abinda yake tsakani na da shi, dama tun farko ba son shi nake yi ba shine ya nace mun” Layla ta fada cike da mixed feelings din da bata san daga ina ba.

Ya kalli Ameera wadda ta bi ta daburce yace “Ameera kina son Zayd???”

“Eh Abba..” ta fada without thinking twice.1

Ya kalli Umma yace “Dama ya nemi izini akan zai turo sati mai zuwa a nema mishi auren Ameera.. Ya kika gani Umman yara?”

Ameera dai gaba daya jikinta yayi sanyi.. Zuciyarta kuwa sai bugawa take yi.. Wai maganar aurenta ake yi?? za’a zo neman aurenta sati mai zuwa??? Ko da wasa bata taba sa ran zata yi aure ba anan kusa tunda ba saurayi gareta ba ma.. toh wai is she even ready? Tabbas she is ready as long as ZAYD ne.. Allah ma ya sani ZAYD shine ZABIN TA.. ita kam ta gama samun komai a rayuwa tunda har zata zama matar Zayd..

Wata ajiyar zuciya ta saki yayinda ta dinga gode ma Allah.. burinta ya cika a rayuwa!

“Sati mai zuwa Abba?? bai yi kusa ba kuwa?? na ga yakamata a bi komai ahankali ko?? kuma na ga dukda ka yaba da halin shi ai kamar ba wani fahimtar juna suka yi da Ameera ba sannan mu kan mu muna buqatar lokaci da zamu shirya..” cewar Umma.

“Haka ne Umman Ameera, Zuwa neman auren ba wai yana nufin auren za’a yi yanzu yanzu ba.. wani abinda yakamata kiyi la’akari da shi shine Aure da mutuwa lokaci ne, idan har lokaci yayi babu mai tarewa don haka Addu’a zamu cigaba da yi akan Allah ya zaba mafi alkahiri”

“Toh Abban yara, Allah ya zaba mana mafi alkhairi”

Mama wadda take dariya tace “Allah ya sanya alkhairi.. dama dai kam shine daidai da ita. Mu dai namu kallo”

Ta kalli Layla tace “ke tashi mu tafi..”

Jiki a sanyaye Layla ta tashi ta bi bayan Mama suka wuce dakinta.

Abba ya kalli Umma yace “ki same ni a daki yanzu” Ya miqe ya tafi yayinda Umma ta bi bayan shi.

Suna barin falon su Ibrahim suka dawo kusa da Ameera cike da murna..

“Ya Ameera wallahi na ji dadi da zaki auri Ya Zayd.. Ina son shi sossai” cewar Ibrahim.

“Dama fa ko kadan bai dace da Ya Layla ba don halin su bai yi daidai ba.. shi he is cool kamar ki, ita kuma she is hot” cewar Munnir

Gaba dayan su suka fashe da dariya.

Aliyu yace “Yanzu shikenan idan kika yi aure kika tafi bazamu qara kallon film tare ba??”

Ameera tana murmushi tace “zaku dinga zuwa gidana mu kalla ai ko??”

Suleiman yace “da Ya Zayd zai bari ma har kwana zamu dinga yi.. zamuyi missing dinki Ya Ameera”

Haka dai suka dinga hira kala-kala akan auren Ameera yayinda take cike da tsananin farin ciki..

What a dream come true for her!!

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *