ZABI NA CHAPTER 5 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 5 BY FADEELARH

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI+

Layla ce kwance a kan gadon dakin su tana video call da Habib..

A lokacin Ameera tana tsaye gaban wadrobe dinta tana jera kayanta da ta wanke ta goge.. tana jera su yayinda take feshe su da turare daya bayan daya.

Ameera dai tana aikinta tana sauraron Layla da yadda take ta hira da Habib a waya..

“wane irin Birthday party ne all night long sweetheart??? Gaskiya fa Abba bazai bari in kwana a waje ba”

“Yanzu Pretty birthday party din nawa ne zaki kasa zuwa?? toh meye amfanin yin party din babu ke??? besides na fadi miki Leema zata zo and zan so inyi introducing dinki to my friends.. please dont say no”

“Sweetheart wallahi zan so zuwa.. kawai dai babu hanya ne..”

“Ke yanzu duk dabarun ku na mata kina nufin you can’t come up with something?? I swear sometimes sai in dinga gani kamar son da kike yi mun ragagge ne…”

“Haba sweetheart.. kar kace haka mana. Yakamata ka san cewar ina son ka sossai”

“then what’s love without sacrifice Pretty?? wallahi idan baki zo ba zan gane matsayi na a wurin ki.. kuma just so you know your presence will be the best birthday gift I will receive”

Ajiyar zuciya ta saki tana kallon yadda ya daure fuska wai shi alamar yayi fushi.. Murmushi tayi tace “toh saki fuskar ka.. I will find a way. Zan zo”

“Yeeesssss…” ya fada yayinda yake dariya.

“thank you pretty.. by the way kin yi kyau sossai cikin sleeping wear dinnan. Ina son yadda ta kwanta a jikin ki da yadda nipples dinki suka yi protruding which is just so cute.. cant wait to marry you and have you all to myself”2

Jin yayi maganar auren su sai ta ji dadi tace “nima haka Sweetheart.. Allah ya kai mu”

Ameera wadda ta gama jera kayan ta tuntuni tana nan tsaye tana kallon Layla yayinda take mamakin maganganun iskancin da Habib yake yi mata wanda da alama ita din bata yi finding fault a cikin maganganun ba… Abinda ya fi bata mamaki shine Layla tana planning zuwa birthday party dinshi wanda za’a yi all night long.. Is she okay???3

Bayan sunyi sallama ne ta tashi zaune tana kallon Ameera cikin bacin rai.

“ke kuma lafiya kike kallo na kamar mayya kina sauraron hirar mu.. ko baqin ciki kike yi don na samu mai kudi??”

Maganar ta so ta ba Ameera dariya amma ta matse.. ta sani sarai idan tayi har marinta zata iya yi.

“Yi haquri Ya Layla.. dama magana zanyi miki akan abinda na ji kina fadi a waya. Na farko dai bai dace ace kina sanye cikin irin wannan kayan kina waya da shi ba.. ba muharramin ki bane da har yake da ikon ganin ki a cikin wannan yanayin… A yayinda yake yaba kyan da kika yi Allah ne yake la’antar ku da ke da shi.. I am so sorry Ya Layla I mean no disrespect but..”

“kutuman Uba.. yanzu Ameera har wuyan ki yayi kauri zaki dinga gaya mun maganganun banza irin wadannan?? sannu alarammiyya ‘yar aljannah.. sai ki zo ki jefa mu wutar jahannama idan kina da iko.. Ko uwar ki ta fadi mun wannan maganar sai na taka ta balle ke don haka ki kiyaye ni”

“Bana nufin ki da sharri ko alama Ya Layla, tunatar da ke nake yi abinda aka koya mana a islamiyya amma idan na bata miki rai don Allah kiyi haquri. Yanzu dai kawai ina so ne in roqe ki wata alfarma please..”

STORY CONTINUES BELOW

Layla ta girgiza kai tana hararar ta tace “ina jin ki gimbiya..”

Ameera ta matsa kusa da ita ta duqa har qasa tace “don Allah don son Annabi (SAW) kar ki je birthday party dinnan.. wallahi akwai hatsari a zuwan ki… abubuwa da dama suna iya faruwa.. babu wani taron arziki da baza’a yi shi ido na ganin ido ba har sai cikin dare.. taro ne na maza, baki san kalan su ba.. duk wata ‘ya musluma ta qwarai…”

Bata rufe bakinta ba ta ji saukar mari a kumatun ta wanda yasa ta yin shiru bata shirya ba.

“idan kika qara shiga sabga ta sai nayi miki dukan tsiya a cikin gidan nan.. shekaru biyu na baki don haka you have no right to question my actions whatsoever. wato ni ‘yar iska ce kenan ko??? toh zan ga uban da zai hana ni zuwa.. shegiya baqar banza mai baqin hali.. haka zaki qare babu wanda zai ce yana son ki kullum kina fama da hijabi kamar tsohuwar bagidajiya..”4

Ameera wadda take share hawayen fuskarta ce ta miqe tsaye tare da dago ma Layla hannu tana kallon ta cikin ido tace “Ya isa haka Ya Layla.. kar ki qara zagi na.. I respect you alot don haka kar kiyi crossing limit dinki.. Insha Allah bazan qara yi miki magana akan rayuwar ki ba.. kiyi duk abinda zaki yi I dont care anymore.. just remember this ‘for every action, there is an equal and opposite reaction’ Allah ya baki sa’a”1

Tana gama magana ta fita daga dakin yayinda ta bar Layla sake da baki.. Jikinta ne ya dan yi sanyi yayinda take mamakin kalaman Ameera.. Tabbas a yadda ta ga yanayinta she is capable of slapping her back kuma kamar yadda tayi warning dinta ta tabbatar next time zata rama din don haka ne ta qudurta a ranta ta bi ta a hankali henceforth idan ba haka ba kuma girma ya zube.. for the first time ta gode ma Allah akan yadda Abba ya tsaya tsaye don tabbatar da raini bai shiga tsakanin yaran ba. Duk yadda yaran gidan basu son Layla da halinta suna respecting dinta for being the eldest.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!!

KADUNA STATE UNIVERSITY

Zaune suke a class suna hira yayinda suke jiran shigowar next lecturer.

Ameera ce ta ba Zarah labarin abinda ya faru tsakanin ta da Layla jiya da daddare.

Zarah wadda ta cika da mamaki tace “wai dama iskancin Layla ya kai haka ban sani ba??? kuma ta mare ki saboda kin fadi mata gaskiya?? wai me duniya ta zama ne?? abinda muke jin labari gashinan a gaban mu yana faruwa… subhanalillah”

“hmmm.. ni duk ba wannan ba. Wallahi ina jiye mata abinda zai iya faruwa a party dinnan.. dukda nayi ma kaina alqawarin bazan qara shiga sabgarta ba bazan bar maganar ba… zan fadi ma Umma abinda take planning in yaso sai ta fadi ma Mama akan tayi warning dinta.. ya kika ce??”

Zarah tana murmushi tace “Allah sarki Ameera.. da ace kowa yana da irin zuciyarki da an zauna lafiya.. I agree with you. Atleast you’ve tried, idan ta qi ji duk abinda zai biyo baya she should deal with it”

Wayar Zarah ce tayi ringing.. Ko da ta duba sunan ZAF ta gani. Da sauri tayi picking..3

“Assalam.. Yayana ina kwana” shiru tayi tana sauraron shi sannan tace “wallahi kuwa ina School.. I am fine kuma komai good”

Dariya tayi tace “Babu komai, na san you are a very busy person.. ai kai yakamata ka dinga rage stress don wallahi ka bamu tsoro weeks ago da ka kwanta ciwo”

Girgiza kai tayi tana murmushi tace “toh shikenan Yayana.. Nagode sossai. Allah ya bar zumunci”

Bayan ta kashe wayar ne tace “that was ZAF, ya kira ya bani haquri wai yana Lagos kuma bai samu shigowa Kaduna ba balle ya zo ya gan ni.. kin san a hannun shi Sweetheart ya bar amana ta”

Ameera tace “Allah sarki..”

Wayarta ce tayi qara alamar text message ya shigo.. Tana dubawa ta ga Credit alert na 2million naira from Zayd Ahmad Fadoul.

STORY CONTINUES BELOW

Gani nayi ta girgiza kai tace “na shiga uku da wannan mutumin..”

“Me ya faru??” Ameera ta tambaye ta.

“Kudi ya aiko mun har 2m. Kullum fa haka yake yi mun.. na fadi ma Sweetheart ya fadi mishi ya daina aiko mun kudi masu yawa.. idan har ya ji lafiya ta ma ya isa sai ce mun yayi wai they are like brothers and that’s how they look out for eachother.. he would’ve done thesame too in such situation..”

Ameera tana murmushi tace “sai kiyi haquri tunda shi haka yake…”

“Bari ki ga idan na kira shi inyi mishi godiya bazai yi picking ba”

Aikuwa ko da tayi dialling layin shi ‘busy’ aka ce mata.

Da ta gaji da trying ne ta rubuta text message ta aika mishi.

“Ni kam ina son ganin matar ZAF a rayuwar nan.. Na tabbatar matan da zasu fi ta jin dadi a duniyan nan basu da yawa.. mutum kamar father Christmas wurin kyauta?”

Ameera ta fashe da dariya tace “kar ki manta an ce wanda ka bayar shine naka”

“hmm.. haka ne fa. Nima tunda na samu zan bayar.. Don Allah Bestie for once ki turo mun account number dinki in tura miki wani abu… I swear babu yawa”

Ba tun yau ba Zarah take dragging da Ameera akan ta turo mata account number dinta don ta tura mata kudi kyauta amma sam ta qi.. she made it clear to her cewar batada account number kuma ma ko tana da shi bazata bata ba.. Ita dai Zarah bata amince cewar bata da shi din ba shiyasa kullum sai tayi mata magiya akan lallai sai ta bata..

Har cash Zarah ta sha ba Ameera kyauta amma ko Sisi bata taba karba ba.. Daga baya ma threatening dinta tayi akan zata bata friendship dinsu if she continue to insist.. da wannan ne ta haqura ta daina. Yanzu haka ko abu ta siyo mata sai tayi dagaske take karba shima idan babban abu ne bata karba…

A dalilin wannan ne Zarah take qara respecting Ameera yayinda take bala’in gode ma Allah da ya hada su a matsayin qawaye. A yanzu haka Zarah ta dauki Ameera a matsayin Aminiyarta don kuwa bata da qawa irinta..

“you already know the answer Zarah… dont push or…”

“Yi haquri Bestie.. ba sai kinyi threatening friendship dinmu ba.. idan kika daina yi mun magana ai sai hawan jini ya kama ni..”

Ameera ta fashe da dariya tace “rufa mun asiri kar Yaya Mustapha yasa a kulle ni a cell..”

Itama Zarah fashewa tayi da dariya.

Haka dai suka cigaba da hira har lecturer ya shigo. As usual Haleema da Layla basu class, da alama ma basu cikin makarantar amma dai Yusrah da Maryam suna nan.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALLAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Mama ce a kicin tana qoqarin kammala girkin dare.. dayake dai yau din ranar girkin ta ne kuma kamar kullum ita kadai ce take yi don kuwa Layla bata ko leqowa kicin din balle ta taimaka mata da wasu ayyukan..

Tun asali dai dama ba koya mata tayi ba balle.

Umma ce ta shigo kicin din cikin sallama wanda kamar kullum bata samu amsa ba.

Qarasowa tayi kusa da Mama tace “sannu da aiki”

A daqile tace “Yauwa” ba tare da ta kalle ta ba.

“Dama akwai ‘yar maganar da nake so inyi miki ne a game da Layla idan babu damuwa”

Jin ta ambaci sunan ‘yarta sai ta juyo ta kalle ta tare da fadin “ina jin ki… Allah yasa alkhairi ne”

Umma tayi murmushi tace “Insha Allah alkhairi ne.. Dama Ameera ce take fadi mun cewar ta ji Layla zata je taron birthday na Habib cikin dare.. tayi mata magana akan kar ta je saboda hatsarin da ke tattare da ziyartar irin wadannan taron amma ta qi sauraronta.. Shine ta ga ya dace ta fadi mun akan in fadi miki kiyi mata magana tunda ke mahaifiyarta ce idan kika…”

“Don Allah dakata, dakata anan. Wai meyasa kuke da sa ido da baqin ciki ne?? me Layla tayi muku da kuke sa mata ido haka ne?? kuna nufin Layla ‘yar iska ce ko me??? Ko haushinta kuke ji don ta samu saurayi mai arziki kamar Habib?? shin an gaya muku Habib din dan iska ne? meye a ciki don zata je bikin taya saurayinta murnar zagayowar shekarun shi?? Wallahi Sameera da ke da ‘yar ki ku fita daga idanuwa na in rufe. Kuna yi wa Allah ku sakar ma ‘yata mara tayi fitsari.. Layla dai ta fi ‘yar ki kyau da farin jini kuma yarinya ce mai qashin arziki don haka dan baqin ciki sai dai ya mutu…”6

“Kiyi haquri don Allah.. abun bai kai nan ba. Kawai dai gani nayi ya dace in sanar da ke ne amma insha Allahu daga ni har ‘ya ta mun fita batun Layla.. Allah ya huci zuciyar ki” Umma ta fada yayinda ta juya ta bar kicin din.

Aikuwa tana ta jiyo muryar Mama tana ta zage-zage tana masifa..

♤♤♤♤♤♤♤

Days later!!+

A yau Saturday, Yau ne birthday party din Habib.. Layla dai tayi ma Mama bayanin komai amma bata fadi Mata cewar ‘all night long’ bane.

Ta dai fadi mata cewar za’a kai qarfe Goma na dare don haka ne zata bi Haleema gidan su ta kwana a can saboda kar Abba yayi fada.

Aikuwa tuni suka tsara abinda zasu ce ma Abba.

Sun yi da Mama akan tayi ma Abba qaryar yayar qawarta zata yi aure don haka ne qawarta ta gayyace ta. Da farko Abba ya hana ta kwana tunda dai bikin na yayar qawa ce ba na qawa ba..

Sai da Mama ta sa baki suka dinga roqon shi sannan ya amince.. Ya ja mata kunne akan banda shashanci.

Umma da Ameera dai sun sani sarai cewar qarya suka yi.. Sun sani cewar birthday party din Habib zata je amma dayake ance baqin ciki suke yi sai suka ja bakunan su suka yi shiru..

Da yamma kuwa Layla ta shirya tsab tayi ma Mama sallama ta tafi..

Dama dai sunyi da Haleema zata je gidan su sai su wuce daga can..

Abin mamaki gaba daya qawayen nata basu taba zuwa gidan su ba amma ita tana zuwa gidajen su musamman gidan su Haleema tunda sun fi shiri.3

Sun riga sunyi shopping na kayan da zasu sa daga wani classy boutique wanda suka bari a gidan su Haleema tunda a can zasu shirya.

Maryam da Yusrah dai sun ji labarin Birthday party din kuma an gayyace su amma suka ce bazasu je ba… dama dai su ba ma’abota zuwa party bane.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI IDRIS BUNGUDU’S MANSION

UNGUWAN SARKI

Zaune suke a tangamemen dakin Haleema wanda yake cike da kayan jin dadi na zamani yayinda Lubabatu CEO ta blush beauty take yi ma Layla make up.3

Musamman suka gayyaci Lubabatu don ta tsantsara musu kwalliya.. Sossai suke so su fi kowace macen da zata halarci partyn kyau.

Dayake dama iyayen Haleema sunyi tafiya babu kowa a gidan sai masu aiki.. ko dama idan suna nan ba hana ta fita zasu yi ba tunda dai sun shagwaba ta.. duk abinda take so shi take yi.

Haleema wadda aka riga aka gama mata nata tana zaune a gefe ce tace “Layla yakamata idan mun tashi zuwa kar mu je da wuri saboda ina so kowa yayi acknowledging presence dinmu.. especially you- babe din Celebrant din. Ko ya kika ce??”

“Haka za’ayi Leema..”

Bayan an gama ma Layla ne ta juyo ta kalli Haleema tace “Leema ya kika gani???”

“wow.. Babe kin gan ki kuwa??? I swear ke kyakyawa ce ta bala’i.. dole Habib ya sukurkuce akan ki. You look absolutely beautiful”

Lubabatu wadda take qoqarin arranging kayan aikinta cikin kit tana murmushi tace “I agree with you ma’am.. she is super gorgeous.. I am so looking forward to having more sessions with you”

Layla tana murmushi tace “you got it Lubcy.. thanks”

Haleema ce tayi ma Lubabatu transfer na kudin aikinta zuwa bank account dinta.. tayi musu sallama ta tafi abinta.

Daga nan ne suka fiddo kayan da zasu sanya suka fara shiri.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE

MARAFA ESTATE

STORY CONTINUES BELOW

Wuraren qarfe Goma saura na dare ne suka iso gidan. Security dai ko da ya ga ‘yan mata ne a cikin motar bai tsaya tambayar su komai ba ya wangale musu gate.. Tunda dai a kullum sai mace ta ziyarci gidan ai ba sai ya tambaya ba..2

Ko da suka shiga harabar gidan sunyi mamakin ganin babu motoci dayawa parked inside the house sannan yanayin yadda gidan yake shiru babu alamar mutane a ciki..

“Leema ya na ga gidan shiru.. is a party not suppose to be going on??”

Haleema wadda ta zama suprised itama tace “nima haka na gani babe.. ko dai ba a nan za’a yi ba?? let me park the car and call Yusuf,  I think an canza venue kenan”

“amma ai da sun fadi mana.. hakan ba daidai bane gaskiya” Layla ta fada yayinda take qare ma gidan kallo.

Qaton gida mai bala’in kyau.. addu’a kawai take yi a ranta akan Allah ya kawo ta ranar da zata shigo gidan a matsayin matar Habib.

Ko da Haleema ta faka motarta ta dauki waya ta kira Yusuf sai ce mata yayi su shigo kawai don ba party bane na mutane da yawa.. it’s just close friends.

♤♤♤♤♤♤

Tsaye suke a gaban main entrance door na gidan yayinda Haleema tayi ringing door bell.

Habib da kan shi ne ya bude qofar…

Gani nayi ya tsaya cak yayinda yayi freezing gaba daya… Ko qyafta idanuwa ya kasa yi ganin Layla tsaye da yadda tayi bala’in kyau.

Sanye take cikin wata black floor length Sequin and velvet V-neck mermaid gown wadda ta bala’in dacewa da jikinta… Gaba daya ta fitar da shape din jikin ta.. in all wannan rigar dai tayi ma jikin Layla justice sossai. Ta daura wani black turban a kanta wanda tayi rolling dinshi hade da dogon gashinta ya bada wani style mai kyau.

“wow wow wow… Pretty you look immaculately beautiful”

Murmushi tayi sannan tace “thank you Sweetheart.. kai ma kayi kyau sossai. Happy birthday to you”

Gani nayi ya janyo ta jikin shi yayi hugging dinta very tight yayinda Haleema tayi murmushi ta ratsa ta gefen su ta shige..

“Ya na ga babu kowa ne a gidan?? ina ‘yan taya murnar suke??” cewar Haleema wadda ta nufi wurin Yusuf.

Ni kuwa nace an zo wurin!!4

Yusuf wanda ya sa mata idanuwa babu ko qyaftawa yace “it’s just us baby.. kin yi kyau sossai… Come here”

Ta qarasa wurin shi suka rungume juna..

Muryarta qasa-qasa tace “thank you dear…”

Tayi breaking hug din sannan tace “but wait, na ji kace it’s just us… why??? ba yau bane birthday din???”

Yusuf wanda ya daga kai ya hango Habib yana shigowa tare da Layla ne yace “I will tell you later.. for now dai let’s chill, hope kin shirya mun sossai don kwana biyu na ga kina ta yi mun rowa… ko dai kin samu wani ne??”

Hararar shi tayi tace “kai din ba wata ka samo ba??”

Hannun ta ya riqo suka nufi kujera ya zauna sannan ya janyo ta bisa cinyar shi yace “no one but you baby”

Muryar Layla ya ji tace “Ina wuni Yusuf”

“Lafiya lau ya gida??”

“Lafiya”

“kin yi kyau sossai”

Kafin tayi magana ne Haleema ta harare shi yayinda Habib yace “easy man.. ina nan zaka fadi wannan maganar??”

Dariya yayi yace “yi haquri mutumina”

Layla ce tace “toh wai ina sauran mutane?? na ga mu kadai”

STORY CONTINUES BELOW

“Yes my love.. its gonna be a private party  daga mu sai su Yusuf”

I am laughing out loud in igbo ooo?10

Bata rai Layla ta dan yi sannan tace “amma sweetheart..”

Qara matse ta yayi a jikin shi yace “amma nothing Pretty, kawai fa ke kadai nake buqata ki kasance tare da ni idan zan yanka cake dina.. why would I need people when I have a precious woman whom I want to spend the rest of my life with”

Dan murmushi ta saki yayinda tace “I love you”

“I love you too pretty” ya fada sannan ya kalli su Yusuf wadanda suke kallon shi yace “mu je mu yanka cake din ko??”

Wurin Dinning suka je inda suka yi mishi waqar happy birthday sannan ya yanka cake din.. Layla ce ta yanka ta sa mishi a baki sannan shima ya yanka ya sa mata… Haka Yusuf da Haleema.. a nan dinning din suka ci kayan ciye-ciye da drinks suna ta hira.

Bayan sun kammala ne suka dawo falo riqe da drinks suka zauna a kan kujera.. Haleema maqale a jikin Yusuf yayinda Layla take zaune a gefen Habib suna hira.

Layla wadda take kallon su Yusuf bata ankara ba ta ga sun hade bakunan su suna ta kissing juna.. bata yi mamakin ganin wannan al’amarin ba tunda it’s normal.. kuma suma suna yin hakan.

Habib wanda ya kafa ma qirjinta idanuwa ne ya kula tayi nisa a kallon su ya kamo hannunta… Da sauri ta juyo ta kalle shi..

“sun birge ki ne da kika sa musu idanuwa haka??”

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba..

“mu ma fa zamu iya yi tunda dai muna dan yi ko??”

Zaro idanuwa tayi tace “a’a Sweetheart… namu bai yi zurfin nasu ba…” bata rufe bakinta ba ta ji ya cafko lips dinta da nashi ya shiga kissing dinta kamar yadda ya saba.. tuni ta biye mishi don kuwa idan akwai abinda Layla take so bai wuce salon kisses din Habib ba..

Wasa-wasa dai kiss yayi nisa har Hannuwan Habib sun fara bin jikin Layla..

Abinda suka ji next ne ya sa su saurin sakin bakin juna suka juyo..

Haleema ce kwance a kan kujera half naked yayinda Yusuf yake bisa kanta.. Duk tsawon rayuwar Layla bata taba ganin Namiji da mace a wannan yanayin ba..2

A razane Layla ta miqe tsaye tace “meye haka Leema??? me kuke yi???”

Haleema da Yusuf suka dago kai suka kalle ta suna murmushi…

“Layla ba wani abu muke yi ba fa.. we are just cuddling ne and I swear akwai dadi… just try it”

Kafin Layla tayi magana Haleema tace “Ouch..” a dalilin sabon salon da Yusuf ya bijiro mata da shi.

Da sauri Layla ta juyo tana kallon Habib wanda shima ita yake kallo tace “bazaka hana su ba??”

Janyo ta yayi ta fado jikin shi yace “toh me suke yi da zan hana su?? haka fa ake soyayya Pretty.. hakan yana qara danqon soyayya.. wannan din shi zai tabbatar cewar baza su iya rabuwa da juna ba.. cant you see how happy she is?? ki amince in yi miki ki ji dadi, idan kuma baki so zan bari.. kin ji pretty??”

Juyawa tayi ta kalli Haleema wadda gaba daya tayi nisa… sai surutai take yi wadanda zasu tabbatar ma mutum cewar tabbas tana jin dadin abinda yake wakana….

Da sauri ta kauda kai yayinda ta miqe tsaye tace “ni fa tafiya zan yi gaskiya.. bazan iya ba”

Tuni ta dauko wayarta ta juya zata tafi yayinda Habib ya cafko ta da qarfin gaske ya hada ta da jikin shi… Ba tare da yayi magana ba ya qara hada bakin shi da nata ya shiga kissing dinta da qarfin gaske… Gaba daya Layla ta birkice.

STORY CONTINUES BELOW

Ni da nake tsaye ina jira in ga Layla ta qwace ta juya ta tafi amma inaaa… sai na ga sabanin hakan. Qara matse shi tayi itama suka cigaba…

Layla dai bata ankara ba ta ji yayi sama da ita.. har a wannan lokacin suna ta faman cinye juna da kisses..

Tana hannun shi ya wuce da ita dakin shi.. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan gado. Da sauri ta zare bakin ta daga nashi tace “Sweetheart ya haka?? me zamuyi anan??”2

Habib wanda idanuwan shi suka yi ja ko sauraronta baya yi… tuni ya fara cire kayan jikin shi yayinda ya qura ma qirjinta idanuwa.

Layla dai ganin Habib daga shi sai boxers ne ta firgice.. da sauri ta tashi zata sauka daga kan gadon amma ya riqo ta da qarfi..

“Kawai ki tsaya muyi abun nan cikin kwanciyar hankali.. Na fadi miki cewar ina son ki kuma zan aure ki.. shin baki yarda da ni bane?? ni din ba saboda na yarda da ke ne nake baki kudade masu yawa ba??? an gaya miki da bana son ki zan dinga daukan kudade na ina baki ne?? kuma dukda haka cant you do just this for me??”2

Layla wadda zuciyarta take ta bugawa gaba daya ta rude… Jikinta sai rawa yake yi yayinda hawaye suka fara bin fuskarta..

“toh shikenan.. dama ba sona kike yi ba kenan. I think we should just break up..”

Da sauri ta kalle shi tace “Sweetheart wallahi ina son ka.. ka ga abinda kake shirin yi mun ne fa bana so, babu kyau kuma..”

Gani tayi Habib ya juya da sauri zai sauka… da alama yayi fushi ne.

Gaba daya ta rude, idan ta bari suka yi breaking up sai Mama ta kusa kashe ta.. toh amma kuma abinda yake shirin yi mata ne bata so.. kenan idan ta hana shi bazai qara bata kudi ba? yadda ta saba da kashe manyan kudade yanzu shikenan??? Kalaman Mama ta tuno da tace mata idan dai don taba jikinta ne ta qyale shi tunda ba danne ta yayi ya nemi kwanciya da ita ba.. idan har irin abubuwan da su Haleema suke yi zai yi mata ai babu matsala kenan..

Habib wanda tuni ya fara sa wandon shi ne ya ji tace “yi haquri sweetheart, zo mu yi…”2

Aikuwa wani irin sanyi ya ji a zuciyarshi.. dama dai so yake yi ya gwada ta. Asalin Habib baya kwanciya da mace da qarfi.. Sam baya enjoying sex da macen da bata so, ya fi son yayi komai da amincewar ki.. Dukda hakan kuwa yayi niyyan idan har Layla bata amince din ba toh lallai zai yi mata da qarfi don kuwa ita daban ce, baya ji zai iya haqura da ita sannan bazai iya dealing da mugun sha’awarta ba da ta baibaiye shi.

Da sauri ya cire wandon nashi ya haye kan gadon yana murmushi..

“Yauwa Pretty.. kar ki damu idan baki so kawai ki fadi mun sai in daina. Yanzu dai tunda na cire kayan jiki na kema ki cire..”

Jikinta yana rawa ta fara qoqarin cire rigar ta.. Ganin tana yi cikin sanyi ne yasa hannu ya taimaka mata… Nan da nan ya raba Layla da kayan jikinta.. Ta rage daga ita sai inner wears..

“don Allah kar ka raba ni da budurci na.. ka taba inda kake so kawai amma please.. I dont want to lose my virginity until after marriage”

Habib dai surar ta kawai yake kallo. Da alama ma bai san tana magana ba don hankalin shi yayi nisa akan kayan marmarin da yake kallo a jikinta.. gaba daya ya bi ya rude ganin kyakyawar halitta ta Layla a gaban shi.

Ita kuwa sai zubar da hawaye take yi..

A hankali cikin siyasa da qwarewa ya fara sarrafa jikin Layla.. tun tana noqewa tana kuka yayinda bata son abinda yake yi mata har ta fara sakin jiki…

Daga baya kuma sai ga Layla ta fara amsar saqonnin Habib. Dayake Habib ya qware sossai a harkar tuni ya dulmiyar da ita..

Dama dai an ce duk inda mace da namiji suka kebe toh fa na ukun su shaidan ne…

A haka dai Habib ya jefa Layla cikin mummunan aiki, aikin alfasha.. aikin Zina.

A cikin qanqanin lokaci yayi mata dabarar da ya raba ta da budurcin ta..9

Subhanalillah…

♤♤♤♤♤

Iyaye suna da haqqi akan ‘ya’yan su.. haka suma ‘ya’ya suna da haqqi akan iyayen su

Abba yayi iya qoqarin shi wurin ba yaran shi tarbiyya amma kash! Mama (Hindatu) ta lalata tarbiyar ‘yar ta Layla.. Mama ita ce sanadin abinda ya samu ‘yarta..8

KWADAYI da SON ABUN DUNIYA sun kai Layla ga halaka…

Tabbas mahaifin Layla ba mai arziki bane amma kuma yana da na rufin asiri, daidai gwargwado yana biya musu dukkanin buqatun su amma hakan bai yi ma Mama da Layla ba..

Idanuwan su a rufe suka bi hanyar banza don samun KUDI.

Layla ta bi qawar banza HALEEMA da saurayin banza HABEEB sun lalata mata rayuwa!

It’s a life lesson my people..

this has become a reality in our modern life!2

‘Yan mata a ji tsoron Allah, a guji bin qawayen banza da samarin banza, a guji aikata munanan ayyuka irin wadannan.. Arziki da rashin shi duk yin Allah ne. Ka gode ma Allah a dukkanin yanayin da ka samu kanka. People of “ALHAMDULILLAH” dont have time to complain!1

Note that You cannot delete your history from ALLAH and remember that your interview with HIM is coming!!

Allah yasa mu fi qarfin zuciyoyin mu!4

*******

It is rightly said that ‘For every action, there is an equal and opposite reaction’3

What next for Layla???

HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE

MARAFA ESTATE

Wuraren qarfe tara na safe tana kwance a kan gadon dakin shi cikin Duvet tana ta rusa kuka yayinda Haleema take zaune a gefenta tana lallashinta.

Layla dai a jiya bayan sun gama gurzar juna ita da Habib ne hankalinta ya dawo jikinta… A lokacin tayi realizing abinda tayi.. ta aikata babban kuskure wanda bazata taba iya gyara shi ba.. ta bata rayuwarta har abada.. babu ita babu shiga gidan miji da budurcin ta intact.. For the first time tayi da ta sanin qin daukar shawarar Ameera da Umma..3

Aikuwa ta dinga rusa ma Habib kuka.. kuka sossai kamar ranta zai fita. Shi kuwa sai aikin lallashi yake ta yi mata tare da qara jaddada mata cewar auren ta zai yi kuma abinda ya faru tsakanin su zai zama sirrin su ne tunda babu wanda ya gani.. Har wani mugun zazzabi ya saukar mata.. jikinta yayi mugun zafi, babu shiri ya samo magani ya lallasheta ta sha.. A haka har bacci ya kwashe ta.

Habib dai sossai yake cikin farin ciki na abinda ya faru tsakanin shi da Layla.. Ko kadan kukan ta bai sa yayi regretting abinda suka yi ba.. ko tausayi ma bata bashi ba. Shi kam ya riga ya saba da wannan a wurin yawancin matan da yake mu’amala da su.. haka zasuyi ta borin kunya suna kukan banza sai daga baya ma su zo su fi shi jaraba.. Ya sani sarai su kansu matan suna jin dadin yadda yake tafiyar da su a kan shimfida.. Duk wani abinda zai haukatar da su ya sani.. Shiyasa tunda yake bai taba forcing yarinya ta kwanta da shi ba.. saidai yayi seducing dinta su aiwatar da komai.

“Don Allah Layla ki daina kuka ki tashi ki sha maganin nan… it’s very important. Kin ga a yanzu asirin mu a rufe komai ya faru amma kuma idan baki sha maganin nan ba ciki ya shiga asirin ki zai tonu”

A firgice Layla ta tashi zaune dafe da Duvet a qirjinta tace “na shiga uku.. Yanzu kina nufin zai iya yiwuwa ciki ya shiga??”

Daga nan ta qara fashewa da sabon kuka..

“wannan maganin shi kadai zai iya hana shi shiga idan ma har yayi niyya… shiyasa nake yawo da shi a kullum idan muka sha soyayyar mu da Yusuf sai in sha”1

Cike da mamaki Layla take kallon Haleema tace “wai dama kin san abinda Habib zaiyi mun kenan jiya shine baki fadi mun ba?? dama kuma abinda kuke yi kenan?? you told me cewar you were only cuddling ne..”

“Layla in tambaye ki mana.. yanzu don Allah ki fadi mun gaskiya baki ji dadin abinda kuka yi ba jiya???”

Shiru Layla tayi sannan tace “amma dai kin san babu aure a tsakanin mu ko?”

“So what idan babu aure?? ba asirin mu a boye muke yi ba?? ni din tunda kike gani na kin taba sanin ina yi ne??” ta gyara zama tare da dago contraceptive pill din da yake hannun ta tace “kin ga Layla.. idan dai kin riqe wannan toh ina mai tabbatar miki asirin ki a boye.. Ku sha soyayyar ku sannan ki kwashi kudade”2

“Leema idan har saboda kudi zanyi wannan ke ai bai kamata kiyi saboda kudi ba… you have everything”

Murmushi Haleema tayi sannan tace “ai ni ba don kudi nake yi ba.. ina yi ne to satisfy my needs.. ke ni fa zan iya da maza biyu a lokaci guda ma..”1

Layla ce ta zaro idanuwa cike da mamaki.. har ga Allah ta sani cewar Haleema is loose amma bata taba tunanin iskancin ta ya kai wannan matakin ba.

Haleema dai ganin yadda Layla take kallonta kamar Ghost ne ta fashe da dariya tace “kar ki damu ‘yar uwa zaki saba… ni dai yanzu ga magani nan ki sha sannan ki tashi kiyi wanka.. kin ga har sallar ma bakiyi ba.. ko zaki hada da azahar ne???”

STORY CONTINUES BELOW

Layla wadda gaba daya bata jin dadin jikinta ta share hawayenta sannan ta karbi maganin.. tabbas idan ciki ya bayyana a jikinta sai Abba ya kashe ta don haka she needs to take precaution.

hmmmm…

☆☆☆☆☆☆☆

Zaune suke a dinning suna breakfast yayinda yake cikin nishadi marar misaltuwa.

“Kai abokina.. wallahi ban taba cin mace kamar yadda na ci Layla ba.. na rantse maka da Allah ta hadu iya haduwa.. na haqura ne ba don na gaji ba sai don kar in illata ta wallahi”

Yusuf wanda ya fashe da dariya ya miqa mishi hannu suka tafa yace “amma dai ka san kayi na farko kayi na qarshe ko?? ka kuwa san daga dakin mu muna jiyo ihunta??”

Habib yana dariya yace “Wallahi mutumina kukan dadi ne.. idan ka ga yadda ta maqale mun zaka rantse ba sabuwar shiga bace.. Na tabbatar jarababba ce kuma muna nan da kai zata kawo kanta har gidan nan… ka manta ko ni waye??”

“Shegen sama… ban taba ganin dan iska irinka ba Habib.. duk ranar da Daddy zai ji abinda kake yi sunan ka sorry”

“Aikuwa bazan so ya gane ba don wallahi idan an raba ni da wannan harkar zan iya mutuwa..”

Yusuf ya fashe da dariya yace “gaskiya baka da kyau.. Nima dai a taimaka a bani in dana”

“inaaa mutumina… ai Layla specially tawa ce. idan dai kana son Fiddy zan baka ita aro..”

“Wa??? Allah ya tsare ni… ai Fiddy ta fi ni jaraba, wallahi bazan iya ba”

Habib ya fashe da dariya yace “ni zan baka labari abokina… Fiddy kam qarshe ce, gata shegiya bata gajiya, she is a real sex machine”

Motsin da suka ji ne ya sa su yin shiru yayinda suka bi direction din da kallo. Haleema ce ta fito riqe da Layla wadda take tafiya a hankali har tana dingyashi.. sanye suke cikin kayan da suka zo da su jiya.

Da sauri ya tashi tsaye ya qarasa wurinta ya riqo hannunta yace “Pretty how..”

Fizge hannunta tayi tace “kar ka sake taba ni… I hate you”

“Hey me nayi miki da zaki fadi mun these hurtful words… I love you very much”

“Just shut up and leave me alone” ta fada yayinda ta fashe da kuka..

Yusuf ne yace “Haba pretty din Habib.. Meyasa zaki yi mishi haka?? I thought you guys are inseparable..”

Ba tare da ta jira ya qarasa maganar shi bane ta kalli Haleema tace “mu tafi gida”

Haleema tace “ki bari muyi breakfast mana..”

“Fine.. idan bazaki tafi ba ni kin ga tafiya ta..”

Ta juya zata tafi ne Haleema tayi saurin riqe hannunta tace “tsaya Layla.. I am coming with you”

Ta kalli Yusuf tace “My love sai mun yi waya”

Habib dai shiru kawai yayi bai hana ta tafiya ba.. it’s not the first time da yake ganin haka daga wurin mace.. kamar yadda ya sani kuma ya fada ‘she will bring herself back’1

“Uhm ku dan tsaya please.. ina zuwa” ya fada yayinda ya juya ya nufi hanyar dakin shi.

Layla dai bata saurare shi ba ta wuce abinta ta fita yayinda Haleema ta kalli Yusuf tace “kace mishi muna jiran shi a mota”

Yusuf yana murmushi yace “okay but you need to calm her down please”

Itama murmushi tayi tace “dont worry I will”

☆☆☆☆☆☆☆

Habib dai fitowa yayi riqe da wata qatuwar envelope ya qaraso wurin motar Haleema ya tsaya ta window din Layla ya dora mata envelope din a kan cinyarta sannan yace “Pretty I am sorry please.. kar ki manta cewar I love you so much and I cant wait to have you as my wife”

STORY CONTINUES BELOW

Ko kallon shi bata yi ba yayinda hawaye suke ta bin fuskarta.. Haleema ce tayi mishi godiya sannan suka yi sallama suka bar gidan.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI IDRIS BUNGUDU RESIDENCE

UNGUWAN SARKI

Kwance take a kan gadon dakin Haleema tana ta rusa kuka kamar ranta zai fita.

Haleema wadda take ta lallashinta ce tace “Babes ki daina kuka don Allah.. Nima fa I could remember haka nayi first time dina.. Na dinga kuka ina tunanin duk wanda ya gan ni zai san abinda nayi but the truth is nobody knows idan ba ke ce kika fadi ba..”

Cikin kuka Layla tace “that is not my problem Leema.. Matsala na shine na aikata Zina ba tare da aure ba.. kin san me hakan yake nufi a addinin mu???”

“Na sani qawa ta.. amma ai wannan din is different”

“how different?”

“Kin yi ne da wanda zaki aura”1

“a tunanin ki Habib zai aure ni ne bayan ya riga ya gama sani na a matsayin ‘ya mace??? how sure am I ni kadai ce?? baki gani tunda yayi mun hakan ya saba yi da wasu??”

Haleema wadda ta sani sarai zancen Layla haka ne ta dan sosa kanta sannan tace “I doubt qawa ta.. Habib yana bala’in son ki kuma I assure you zai aure ki..”

“Ni kam bazan iya auren namiji irin shi ba… Habib dan iska ne, na tabbatar yayi planning komai ne.. na tabbatar ma birthday party din na qarya ne, it wasnt even his birthday. How I wish I listened to Ameera da Umma… all of these wouldn’t have happened”

“No please Layla ki daina fadin haka.. dagaske Habib ba dan iska bane.. soyayyar da yake yi miki ce tayi yawa.. ita ta tunzira shi yayi miki abinda kuka yi.. ko kuma in ce kuka yi ma juna abinda kuka yi. Kin ga fa idan muna yi da Yusuf yana yawan yi mana nasiha and we keep telling him its love.. idan ya samu wadda yake bala’in so bazai iya controlling ba.. I guess abinda ya faru kenan a kan ki. He couldn’t control it and it had to happen.. please calm down my friend”1

A haka dai Haleema ta cigaba da lallashin Layla.. ita kuwa ta gwada mata lallai babu ita babu Habib.. bazata qara sauraron shi ba.. ta rabu da shi!!

Shin is it not too late???4

♤♤♤♤♤♤

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Zaune suke a falo wuraren qarfe biyar na yamma yayinda suke kallon wani Indian film mai suna ‘Kabhi khushi kabhie gham’

Wannan film dai tsohon film ne wanda ko da aka yi shi ma ba’a haife su ba.. Sossai Ameera take son wannan film din.. ta haddace komai na film din, waqoqin ciki kuwa kamar ita ta rubuta lyrics din.

Best waqarta itace ‘suraj hua maddham’ wadda Shahruhk Khan da Kajol suka hau a cikin film din.1

A kullum idan tana kallon waqar babu abinda take picturing sai Ita da Zayd a gidan su a matsayin ma’aurata suna ma juna waqar.. sossai soyayyar indiyawa take birgeta.. tana son yadda suke expressing feelings dinsu through songs.1

Su Suleiman dai tun suna jin haushin yadda ta nace ma film din har suka haqura suka biye mata.. yanzu haka idan ta kwana biyu bata kalla ba da kansu suke sa shi su kalla wanda kuwa itama take zuwa tayi joining dinsu.

Sunyi nisa a kallon ne suka ga ta shigo falon babu ko sallama.. Gaba daya fuskarta a kumbure take yayinda take riqe da Qaramar travel bag dinta.. Ko kallon su bata yi ba ta wuce yayinda take dingyashi.. Su Suleiman dai basu kula da dingyashi da take yi ba amma ita Ameera ta kula.. Bata kawo komai a ranta ba tunda batasan komai ba.

STORY CONTINUES BELOW

Kamar dai yadda tayi watsi da su suma haka basu ce mata komai ba..

Bayan ta shige ne Ibrahim yace “kun ganta kamar wadda aka zane su a gidan bikin??”

Munnir, Suleiman da Aliyu ne suka fashe da dariya yayinda Ameera tace “what nonsense.. ba an hana ku rashin kunya ba?? yanzu idan ta ji ku fa?? please mind your business”

Ibrahim yace “Sorry Ya Ameera”

☆☆☆☆☆☆☆☆

Mama tana zaune a kan gadon dakinta ne Layla ta shigo. Ko da ta ga yanayin ta dan yi mamaki.

Fuskarta ta kumbura tayi ja alamar ta ci kuka sannan tana tafiya kamar tana dingyashi.

“Lafiyar ki kuwa Layla?? ya na ga kamar anyi miki duka???”

Jiki a sanyaye ta haye kan gadon Mama ta kwanta yayinda take tunanin ta fadi mata abinda ya faru ko kar ta fadi.

Maganar da Haleema tayi mata a qarshe ta tuno..

“whatever you decide babe.. kar ki kuskura ki fadi ma kowa abinda ya faru, hatta Maman ki kuwa.. idan kika sake kika fada toh wallahi sai duniya ta ji ki.. keep it a secret and no one should have to find out”

Ajiyar zuciya ta saki tace “wallahi gajiya ce Mama, kin san party.. Wani shahararren mawaqi aka kawo, mun sha rawa har mun gaji.. Ko da muka koma gidan su Haleema jiya duk mun gaji.. baccin ma ba wani mai kyau muka samu ba.. Yau ma na so in dawo tun da safe amma aka ce za’a kai mu lunch…”1

“Allah sarki.. ki ce dai kin shiga mutane kin qara ganin abinda duniya take ciki ‘ya ta… da kyau. Yanzu dai bari in hada miki ruwa kiyi wanka don ki ji dama-dama” Mama ta fada yayinda ta miqe ta shiga kewaye ta don hada mata ruwan wankan.2

Ko da Layla ta shiga bathroom qara gasa jikinta tayi sannan ta fito.. Sossai ta ji dama-dama.

Tuni Mama ta dauko mata rigar ta daga dakin ta don haka ne ta sanya.

Travel bag dinta ta janyo ta bude sanna ta ciro envelop din da Habib ya bata… Layla dai saboda tsananin tashin hankalin da ta shiga bata ko tsaya ganin abinda yake ciki ba.

Da ta zazzage envelope din kuwa na ga Mama ta zaro idanuwa…

Aikuwa da sauri ta nufi qofa ta sa key sannan ta dawo tace “ke Layla, wadannan kudaden masu yawa fa?? duk shi ya baki???”

Layla wadda itama take cike da mamakin ganin tulin kudaden ce tace “shine Mama” a ranta kuwa tace “dan iska kawai.. ai dole ka bani kudade masu yawa tunda ka samu jikina.. kayi na farko kayi na qarshe”

Muryar Mama ta jiyo tana fadin “wannan ai sun kai miliyan guda Layla” yayinda ta shiga qirga bundle na dubu dari..

Tabbas miliyan daya ne cur.2

Mama sai washe baki take yi tana fadin “Kin ga ‘yar albarka.. yarinya ‘yar arziki mai qashin arziki. Allah ya nuna mun ranar bikin ki in kece raini cikin qawaye”

Ita dai Layla murmushin yaqe kawai tayi ma Mama..

“Yanzu sai Ki debi yadda kike so in boye sauran ko??”

Layla tace “kar ki damu Mama, ina da sauran kudi a hannu na. Ki boye su duka kawai”

Gani nayi ta kwashe kudaden ta zuba su inda take tarawa cikin ‘Ghana must go’ da take cikin wadrobe dinta.

Hmmmmm…..

♤♤♤♤♤♤♤♤♤

Toh fa..

Hajiya Layla dai tace babu ruwanta da Habib dinta kuma.. Gashi shi kuma yace zata kawo kanta da kanta next time1

Ya kenan???1

Haleema is surely a bad friend.. Allah ya raba mu da qawaye irin ta!!5

I dont even know what to say about Mama.. a kullum qara bani mamaki take yi!5

Allah ya shirya mana zuri’a1

My people… Where is ZAYD???

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *