ZABI NA CHAPTER 4 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 4 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Days later!

HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE

MARAFA ESTATE+

Zaune suke a tangamemen falon gidan shi suna ta hira. Yawancin hirar tasu duk ta ‘yan mata ce da kuma rayuwarsu ta sharholiya da suka dulmiya a ciki.

“abokina wallahi ta matsa mun akan lallai Abbanta yace inyi introducing kaina kuma gaskiya I am scared.. ya kake gani ne???”

Yusuf wanda yake kwance kan doguwar kujera 3-seater ne yace “gaskiya kar ka kuskura ka je don kuwa duk ranar da ka samu Layla kamar yadda kake so sannan daga baya abubuwa suka dan birkice za’a yi tracing dinka. Ni na rasa meyasa ka kasa exploring dinta har yanzu.. yau fa sama da wata daya kenan da haduwar ku. Haba Habib.. ni da na san ka at most 3 days ka aiwatar da komai amma ace ka kasa yin komai har yanzu”

Habib ya dan sosa kan shi yace “ai baka gane ba, yarinyar tana da dan taurin kai ne.. dukda she is a bit loose ina gani kamar upbringing din da aka yi mata was kind of strict.. a hankali nake bin ta don bana so in nuna yunwa ta a fili.. initially idan na taba hannunta, jikinta har rawa yake yi but ka ga da nake bin ta ahankali yanzu har kiss ina yi mata a kumatu kuma bata damuwa..”

Ya saki ajiyar zuciya yace “oboy, akwai ranar da na shafa boobs dinta..”

Ya lumshe idanuwa ya bude tare da hadiye wani miyau na tsaban maita sannan ya cigaba da fadin “…wallahi laushin bala’i kamar pillow.. Na rantse maka da Allah duk ranar da na samu Layla sossai zan gurje ta..”3

Yusuf yana murmushi yace “I think I will be on queue.. idan ka gama da ita nima a bani in dana”

Habib ya fashe da dariya yace “Wallahi idan Leema ta ji labari babu ruwana..”

“bazata ji ba abokina.. afterall itama ai ina kyautata zaton tana holewa da wasu mazan ba ni kadai ba..”3

“toh koma dai meye Layla tawa ce ni kadai.. saboda ina tunanin nan gaba auren ta zanyi” cewar Habib.

“what??? wallahi inaaa.. ai babu yadda za’ayi in auri macen da na gama sanin ta a kan titi. Sabuwa gal zan auro..”

“kuma fa da gaskiyarka abokina.. toh amma kuma ina son Layla”

Yusuf ya ja tsaki tace “soyayyar banza?? ni dai ina qara jaddada maka kar ka kuskura ka je wurin mahaifinta don wallahi zaka daure kanka.. if things should go haywire babu ruwana”

Haka dai suka cigaba da hirar su.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Wuraren qarfe takwas na dare Layla tana kwance a kan gadon dakin su tana chatting da qawayen ta yayinda call din Zayd ya dinga shigowa tana rejecting.

A lokacin Ameera tana zaune a kan nata gadon tana karatu na wani test din da zasu yi jibi.

“Allah ya sani ka cika naci Zayd.. ni wallahi na gaji da kai. wai ana soyayya dole ne??? dagaske blocking din layin shi zanyi kawai..” ta fadi tare da jan wani mugun tsaki.

Ameera wadda zuciyarta take ta tafasa ce ta kalle ta cike da takaici tace “Haba Ya Layla.. meye laifin Ya Zayd ne?? don kawai yana son ki??? shin hakan laifi ne?? don Allah kar kiyi blocking dinshi.. kiyi haquri”

STORY CONTINUES BELOW

“abeg spare me this stupid talk.. ni fa dama tun farko ba son shi nake ba kuma kin sani haka shima ya sani.. toh ya qyale ni mana yadda daga ni har shi duk zamu huta ke ma ki huta” cewar Layla.

Ameera ta sauka daga kan gadonta ta matsa kusa da gadon Layla ta zauna tace “don Allah Ya Layla kar kiyi mishi haka.. wallahi yana bala’in son ki”

Cike da mamaki Layla tace “toh ni kuma Habib nake so.. sai ya kenan??”

Kafin Ameera tayi magana ne aka qwanqwaso qofar dakin.

Suleiman ne ya shigo cikin sallama wadda Ameera ta amsa.

“Ya Layla dama Ya Zayd ne yake jiran ki a waje”

tsaki ta ja sannan tace “ka je kace mishi ina zuwa”

Suleiman yayi mamakin jin tace tana zuwa don kuwa yau tsawon sati Uku kenan Zayd yana zuwa amma bata fita.

Ita kanta Ameera tayi mamaki sossai jin tace ace mishi tana zuwa…

Bayan ya fita ne ta miqe tana fadin “I think zanyi ending komai yau, kaca-kaca zan yi mishi don na gaji wallahi… haka kawai bazan dinga fita cikin sanyi ina zaman banza ba a kan dakali sannan in tashi babu ko sisi…”

A gigice Ameera ta miqe tsaye ta nufi wurinta tare da hada hannayenta biyu alamar roqo tace “please Ya Layla dont.. don Allah kar ki kore shi ta hakan.. you will break his heart”

“so what if I do??? ya je ya samo daidai da shi mana, ko ni ce autar mata a duniya??? wallahi rabuwa zanyi da Zayd”3

Ameera wadda idanuwanta suka ciko da ruwa ji take yi kamar ta kwashe Layla da mari… ya za’ayi ta dinga wulaqanta mutumin da take bala’in so a duniyar nan??? bawan Allah wanda bai yi mata laifin komai ba sai bala’in sonta da yake yi… Allah ya sani da akwai yadda zata yi ta cire soyayyar Layla daga zuciyar Zayd ta musanya da nata da tayi.. she just cant bear seeing Layla hurt him like this..5

“Okay please listen to me, bazan hana ki rabuwa da Ya Zayd ba amma don Allah kar kiyi mishi kaca-kaca.. ki fadi mishi kalamai masu sanyaya zuciya as you are ending things with him..”

Ta duqa har qasa tace “please Ya Layla..”

Layla wadda ta cika da mamaki sai fashewa tayi da dariya tace “lallai ma Ameera dagaske dai son Zayd kike yi.. toh why not ki zo mu je as I am ending things with him ke kuma sai kuyi starting afresh??”3

Ameera wadda ta miqe tsaye tana kallon Layla cikin ido tace “Ya Layla dagaske ne ina son Ya Zayd amma kuma ke yake so, Ya Zayd shine ZABI NA amma kuma ke ya zaba.. Zan so ace ni yace yana so don kuwa ina bala’in son shi.. Abinda nake so ki gane shine duk yadda na kai ga son namiji bazan taba zubar da mutunci na ba in tunkare shi da kalmar so don haka….”

Layla ce ta daga mata hannu tare da fadin “ya isa haka nan hajiya.. Ni dai rabuwa da Zayd zanyi.. duk yadda zakiyi da shi kiyi, na bar miki.. and yes, kar ki damu zan bi shi ahankali amma tabbas daga yau zan rufe babin shi har abada insha Allah”4

Ta raba ta gefen Ameera tace “bari ma ki gani in sa kaya mai tsada don ya tabbatar ni din ba ajin shi bace a yanzu..”

Haka Ameera ta bi Layla da idanuwa cikin tsananin tashin hankali har ta nufi wadrobe dinta.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune yake a kan dakalin da yake qofar gidan yayinda yake jiran fitowar Layla.

A yau dai ya ji dadi sossai da ya ji saqon tace tana zuwa.

Layla ce ta fito fuskar ta dauke da murmushin mugunta.. Zayd wanda ya qura mata idanuwa sai da ya qyafta su sau uku don ya tabbatar da abinda yake gani.

STORY CONTINUES BELOW

Layla tana murmushi???1

“Baby nayi kewar ki sossai…” Ya fada cike da murnar ganin ta.

Ko da ta qaraso zama tayi a gefen shi tace “Ko Malam Zayd sarkin naci?? ni kuma gashi ban yi kewar ka ba ko kadan.. ina ta yi maka signal ka qi ka fahimta. Da alama dai so kake in fito maka baro-baro”

Maganar Layla ba ita ta bashi mamaki ba.. Yanayin shigar ta da kuma wayar da ya gani a hannun ta su suka bashi mamaki a yanzu da take zaune kusa da shi.

Sanye take cikin wani leshi mai laushi da bala’in kyau.. dinkin doguwar riga ce, da ganin Leshin ka san ya ja kudi.. sai baza qamshi take yi na designer turare. Wayar hannunta ya kalla ya ga Samsung galaxy S10..3

“Na ji kayi shiru.. kai ma ka kula levels don change ko??? A gaskiya tun farko ka sani cewar ni bana son ka amma dukda haka ka nace mun.. tabbas kai kyakyawa ne, ka iya soyayya amma kuma bakada kudi.. A duniyan nan kudi suna da matuqar amfani a rayuwar dan Adam domin kuwa da su ake yin komai.. A yau ka duba ka gani, idan ka aure ni a wane irin gida zaka ajiye ni?? Ciki da falo??? me zan ci??? tuwon masara da miyan kuka??? me zan sa?? atamfar roba-roba??? a me zaka kai ni unguwa??? tsohon mashin dinka??? me zaka bani??? SOYAYAYA cikin TALAUCI?? a’a wallahi bazan iya ba.. bazan tashi a maneji in fada ma talauci ba don haka kayi haquri ka nemi daidai da kai don wallahi na fi qarfin ka ta ko’ina…”4

Tunda Layla ta fara magana kan Zayd yake a duqe yayinda idanuwan shi suke a runtse.. Kalaman ta ne suke dukan qwalwar shi yayinda zuciyar shi take bugawa da qarfin gaske har tana yi mishi barazanar faso qirjinshi.. ji yake yi kamar an watsa mishi ruwan zafi..

“Please stop.. kar kiyi mun haka, Arziki ai na Allah ne. I love you Layla.. ke ce ZABI NA” ya fada yayinda ya dago kanshi ya kalle ta cikin ido.

Girgiza kai tayi tana dariya yayinda tace “I love someone else, he has what I want and you dont… ba kai bane ZABI NA Zayd, so???”

Miqewa tayi tsaye tace “ni dai ka ga tafiya ta kuma don Allah ina roqon ka kar ka qara zuwa gidan nan da sunan ka zo wurina don bazan fito ba.. again dont call me. Ina fata kamar yadda Allah ya hada ni da daidai da ni kai ma Allah ya baka wadda zaku ci soyayya tare”

Daga nan ta juya tayi tafiyarta.

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, kenan I have been wasting my time with her all this while??”3

Gaba daya ya zama confused.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Ameera tsaye a dakin su sanye cikin hijabi tana ta kai da komowa, Hankalinta a matuqar tashe..

Qarar qofa ta ji wanda ya sanya ta juyo da sauri don ganin ko waye.

Layla ce.

“Ya Layla kin fadi mishi?? me yace??? is he alright???” Ameera ta tambaye ta yayinda ta nufi wurinta da sauri.

“Me zai hana ni fadi mishi?? I did.. ban tuna abinda yace ba kuma babu abinda ya dame ni if he is alright or not.. na dai bar shi a waje idan kina so ki je ki tambaye shi.. Ni kam yau I am happy na yar da qwallon mangwaro na huta da..”3

Kafin ta qarasa maganarta kuwa Ameera ta fice daga dakin da gudu.

Layla ta bi ta da ido tace “mahaukaciyar banza.. ki rasa wanda kike so sai matsiyaci.. Allah ya hada ku kuma ya bar ku tare cikin talaucin da yake fama da shi har abada”

☆☆☆☆☆☆☆

Zayd yana zaune a kan dakalin qofar gidan yana ta birkita gashin kan shi da hannuwan shi biyu a lokacin da Ameera ta fito.

A guje ta qaraso kusa da shi ta tsugunna a gaban shi tace “Ya Zayd are you okay?? don Allah kayi haquri da abinda Ya Layla tayi maka.. na tabbatar idan Allah ya nufa matar ka ce zaka ga komai ya wuce kuma kun auri juna and if otherwise I am sure you will find someone better, someone who will love you with all her heart.. Don Allah kar ka sa damuwa a ranka, You need to be strong please…”

Dago kanshi yayi ya qura mata idanuwanshi wadanda suka yi ja.. hakan ne ya sanya ta yin shiru yayinda take kallon shi cikin tausayawa.

A hargitse yake amma dukda haka yayi masifar kyau.. wata muguwar soyayyar shi ce take ta yawo a jinin jikinta gaba daya..

Murmushi ya sakar mata sannan ya miqe tsaye yace “nagode sossai Ameera..”

Gani tayi ya juya zai tafi yayinda ya dafa kanshi.. Da alama he is not okay!

Da sauri ta miqe tsaye tace “Ya Zayd wait.. will you be okay??”

Juyowa yayi ya girgiza mata kai alamar ‘eh’ sannan yace “shiga gida abinki.. thank you for everything”

“please take care of yourself” ta fada yayinda ta juya itama zata shiga gida.

Ko da ya juya ya cigaba da tafiya juyowa tayi da sauri tana kallon shi yayinda zuciyarta take ta zafi… Bata san lokacin da hawaye suka fara bin fuskarta ba.

“If only you see me thesame way you see Her, I would have made you the happiest man on earth.. I love you so much Ya Zayd and I pray you find peace a duk inda zaka tsinci kan ka” ta fada yayinda ta shiga gida tana ta zubar da hawaye.5

♤♤♤♤♤♤♤

Washegari!!!+

KADUNA STATE UNIVERSITY

Zaune suke a Cafeteria lokacin break yayinda Zarah take cin abinci. Ita kuwa Ameera tayi nisa a tunani.

Zarah dai ta kula tun da safe Ameera bata cikin hayyacin ta.. Gaba daya lectures din da aka yi yau for the first time batayi contributing komai ba a ciki… Gaba daya ‘yan ajin sunyi mamaki a yau because its unlike her.

Akwai lecturer din da sai da ya tambaye ta why she is dull today and she said babu komai.

Zarah ta tambaye ta countless times tace babu komai.. In between kuma takan duqar da kanta a kan table ta dade.. idan ta dago kuma sai fuskarta ta nuna alamun tayi kuka.

Zarah dai qyale ta tayi har sai da suka gama lectures… Da qyar ta ja ta suka je Cafeteria shima din ba wai don ta sa ma ranta zata ci abincin ba.

“amma dai kin san baki yi mun adalci ba idan baki fadi mun abinda yake damun ki ba ko???” Zara ta fada yayinda ta ajiye kwalin yoghurt din da take sha.

Ameera wadda take wasa da yatsun hannun ta ce ta dago kai ta kalli Zarah sannan tace “she broke his heart..”

“Who??? ban gane ba..”

“Ya Layla finally succeeded in breaking his heart.. ta kori Ya Zayd jiya, Ya tafi cikin tsananin damuwa.. Hankalin shi a matuqar tashe, I dont even know ko ya isa gida lafiya, ban san halin da yake ciki ba a yanzu. He told me he will be okay amma wallahi ina ji a jikina he is not okay. Soyayyar da yake yi ma Ya Layla is so intense and i am sure after receiving the bad news from her yesterday he is not okay…” daga nan ta fashe da kuka har students din da suke kusa da su suka juyo suna kallon su.3

Da sauri Zarah ta mayar da kujerar ta kusa da ta Ameera ta janyo ta tayi hugging dinta.

“Bestie please calm down.. I never knew cewar son da kike yi mishi yayi zurfin haka ai.. Don Allah ki daina sa damuwa a ranki.. Na tabbatar duk inda yake he is fine..”

“Zarah meyasa Ya Zayd yake sonta ba ni ba?? Na sani cewar ni baqa ce kuma bani da kyau amma kuma I have a good heart kuma ina son shi for who he is unlike Ya Layla da ta wulaqanta shi.. I swear I…”

“sssssshhhhh, Bestie stop talking nonsense. Na fadi miki ba tun yau ba ke kyakyawa ce.. ki daina ganin kanki a matsayin wadda bata da kyau.. Saboda kina baqa doesn’t mean baki da kyau.. You have a good heart and it’s exactly what he has missed. Abinda nake so da ke shine kiyi qoqari ki cire tunanin shi daga ran ki sannan ki manta da shi.. na tabbatar he will move on in life tunda ba Layla bace kadai mace a duniya.. Zan so ace hankalin shi ya karkata zuwa gareki amma kuma what will be will be and what will never be will surely never be. Insha Allah zaki hadu da wanda yake son ki tsakani da Allah.. please kin ji”4

Girgiza kai Ameera tayi sannan ta share hawayen ta tace “nagode Zarah”

Zarah tace “it’s okay, now please cheer up”

Daga nan kuwa Ameera ta dan saki ranta yayinda suka shiga hira dukda dai Zarah ce take ta magana..

Wayar Zarah ce tayi ringing… Da sauri tayi answering ganin ‘sweetheart’ dinta ne yake kira.

“Hello sweetheart.. kar dai kana missing dina ne?? hala kana gida baka fita ba??”

Shiru tayi tana sauraron shi yayinda na ga ta zaro idanuwa tace “subhanalillah.. yaushe?? yana ina???”

STORY CONTINUES BELOW

Miqewa tayi tsaye tace “okay, gani nan dawowa..”

Ameera wadda tuni ta miqe tsaye ce tace “Zarah lafiya???”

“ZAF abokin sweetheart ne babu lafiya an kwantar da shi a asibiti.. yanzu haka yana jira na zamu tafi Abuja mu duba shi”

“Subhanalillah.. ciwon yayi tsanani kenan??”

“Hmm, ai tunda ya kwanta ciwo har kowa ya sani lallai abin ya kai inda ya kai” Zara ta fada yayinda suka fito daga Cafeteria din.

“an ce idan baya da lafiya boyewa yake yi don kar a ce za’a je asibiti. Baya son magani baya son allura.. ke gaba daya ma baya son asibiti. A haka yake kwanciya ciwo har Allah ya bashi lafiya ya tashi ba’a sani ba.”

Cike da mamaki Ameera tace “ikon Allah, wane irin mutum ne wannan kuwa? Toh Allah dai ya bashi lafiya”

Zarah tace “Ameen..

A haka ta raka Zarah har wurin motarta ta tafi sannan ta juyo ta nufi hanyar Lecture theatre dinsu.. Haka kawai sai ta tsinci kanta da yi ma ZAF addu’an samun sauqi yayinda ta damu sossai.5

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALLAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Kwance take a kan gadon Ummanta tana ta bacci. A yau dai da ciwon kai Ameera ta dawo daga makaranta.. tunda ta sha magani ta kwanta ta fara bacci.

Wuraren qarfe shidda na yamma ne Umma ta shigo dakin ta qaraso wurinta ta taba kanta.. babu laifi ya sauka compared to lokacin da ta dawo daga makaranta.

Ameera ta dan motsa yayinda ta bude idanuwanta ahankali ta ga Ummanta..

Matsawa tayi tare da dora kanta bisa cinyarta ta rufe idanuwa ba tare da tace komai ba.

Umma tana shafa kanta tace “ya kike jin kan naki yanzu???”

“Alhamdulillah Umma”

“me ke damun ki?? na kula tun da safe da na gan ki ba daidai kike ba… “

“Umma babu komai..”

“Qarya kike yi Ameera.. kar ki manta ni mahaifiyarki ce kuma na san ki sarai.. ki fadi mun abinda ke damunki.. Mama ce ko Layla???”

Ita dai Ameera bata so Umma tayi mata wannan tambayar ba… bata so ta fadi mata halin da take ciki.. bata so ta fadi mata dalilin da ya sanya ta shiga damuwa… ta ya zata fadi mata cewar saurayin ‘yar uwarta take so??? wanne irin kallo Umman ta zata yi mata???3

“toh shikenan.. idan bazaki fadi mun ba..”

“don Allah Umma kiyi haquri” Ameera ta fada tare da tashi zaune ta riqe hannun Umma.

“zan fadi miki amma don Allah kar kiyi mun fada.. wallahi nima ban san ya akayi haka ta faru ba”

A yanzu dai Umma ta zama confused yayinda ta zuba ma ‘yarta ido.. Daga nan Ameera ta fara bata labarin tun farkon haduwar su da Zayd da yadda yake zuwa gidan nan wurin Layla da yadda take bala’in son shi da kuma yadda ita Layla bata son shi har zuwa jiya da ta samu damar korar shi…

Umma dai shiru tayi cike da mamaki tana kallon Ameera yayinda take ta share hawayen fuskarta.

“Dama akwai wanda kike so shine baki taba fadi mun ba??”

“Umma don Allah kiyi haquri”

“wane laifi kika yi da kike bani haquri Ameera??”

Umma ta janyota ta rungume ta sannan tace “bakiyi laifin komai ba Ameera.. Shi dama so haka yake, Zuciya bata yin shawara da mai ita kafin ta So wani abu. Ban ji dadin yadda zuciyarki ta afka son mutumin da bai san kina yi ba.. Ameera Ina so kiyi qoqari ki manta da shi a rayuwarki, kiyi haquri ki cigaba da addu’a Allah ya kawo miki namiji wanda zai so ki tsakani da Allah. Ina nan ina yi miki addu’a dare da rana akan Allah ya baki miji nagari.. Ina so ki mayar da hankalin ki sossai akan karatun ki a yanzu don haka ki cire tunanin yaron nan a ran ki kin ji??”2

STORY CONTINUES BELOW

Shawarar da Umma ta ba Ameera dai a yanzu iri daya ce da wadda qawarta Zarah ta bata.. truth be told abinda kadai zata yi kenan.

Ameera tace “insha Allah Umma”

Kafin Umma tayi magana ne wayar Ameera tayi ringing. Sunan Zarah ta gani don haka ne tayi answering da sauri.

“Zarah don Allah kiyi haquri ban kira na ji ko kun isa lafiya ba”

A dayan bangaren Zarah tace “babu komai bestie.. Ya kike??”

“Lafiya lau.. ya mai jikin???”

“Qawata sai dai ace da sauqi.. har yanzu bamu samu ganin shi ba, hatta familyn shi an hana su ganin shi, gashi twin sister dinshi har suma tayi saboda tashin hankalin da ta shiga.. so sad wallahi”

“Subhanalillah.. wane irin ciwo ne haka???”

“Likitan dai yace jinin shi ya hau sannan sunyi mishi tests wanda har yanzu ana jiran results..”

“Allah sarki… Allah ya bashi lafiya”

“Ameen qawa ta.. please ki gaida mun Umma”

“Insha Allah, bye”

Bayan ta kashe wayar ne ta ba Umma labarin rashin lafiyar ZAF yayinda tayi mishi addu’an samun sauqi.

Da aka kira Sallah ne suka yi haramar dauro alwala.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune take a kan gadon dakin Mama bayan sallan isha’i yayinda suke ta hira.

Layla ce take ba Mama labarin ta kori Zayd jiya.. Dayake girkin Mama ne jiya tana dakin Abba don haka basu samu sun kebe ba balle ta gaya Mata.

“aikuwa dai kin kyauta ma kanki.. ko banza kin rabu da matsiyacin nan kin huta” cewar Mama.2

“ai baki sani ba Mama, Ameera ita ta bani mamaki yadda ta shiga damuwa, ashe dagaske son shi take yi… har kuka ta dinga yi fa jiya don na kore shi. Yau ma a class gaba daya bata cikin hayyacin ta don kuwa hatta malaman mu sai da suka gane tana da matsala..”

“Sakaryar banza dangin talakawa.. dayake mummuna ce batada zabi.. sai ta lallabe shi ya dawo Mata su je can su qarata”3

Layla ta fashe da dariya.

“Ya maganar da Abban ki yayi miki a game da Habib?? kin fadi mishi ya zo ya gan shi???”2

Layla ta dan bata rai tace “Nayi mishi magana amma bai ce komai ba.. Yace gobe zai zo makaranta ya gan ni.. idan ya zo zan qara yi mishi maganar”

“ki tabbatar kin qara fadi mishi ya zo ya gan shi don na ga alama Abban ku bai amince da shi ba.. kin san ko lokacin da matsiyacin can zai fara zuwa wurinki sai da ya nemi izini a wurin shi don haka shima yakamata ya zo din”

Layla tace “Zan fadi mishi Mama.. ni kam ina da ‘yar matsala da Habib wallahi.. dama fa ina so in fadi miki”

Da sauri Mama ta gyara zaman ta tace “me ya faru?? ba dai rabuwa yake shirin yi da ke ba??”

“kin ga fa yana yawan son riqe mun hannu ne sannan har kiss yake yi mun a kumatu kuma fa ni bana so..”

Kafin ta rufe bakinta Mama tace “Sumba kike nufi ko me???”

“eh Mama, idan nayi mishi magana akan ya bari sai yace mun shi tsakani da Allah yake sona kuma aure zamuyi.. wai haka ake yi. Ni kam wani lokaci sai in ga kamar dan iska ne”2

Mama dai shiru tayi tana juya zancen Layla..

Muryar Layla ta ji tana fadin “wani lokaci sai in ji kamar in rabu da shi wallahi..”

“Ke rufe mun baki sakaryar yarinya… ki rabu da shi ki koma ma wa?? wa kike da shi da ya wuce Habib din a yanzu??? wa zai baki kudade irin wadanda yake baki??? wa zai cigaba da gyara miki rayuwa kamar yadda yake yi miki?? ke kanki baki ga yadda kika canza ba daga haduwa da shi?? ni kaina baki ga yadda qawaye na suke kallo na da mutunci ba a yanzu?? baki so idan auren ki ya tashi kowa ya shaida cewar mun shiga sahun masu arziki??”10

Layla ta turo baki yayinda Mama ta cigaba da fadin “ki saurare ni da kyau, haquri zaki yi da ‘yan abubuwan da yake yi miki din tunda dai ba neman ki yayi a shimfida ba.. kar ki kuskura ki janye daga gareshi don wallahi idan kika rabu da shi bamu da hanyar samun kudade”

Layla tace “toh Mama kina nufin in qyale shi ya cigaba da taba jikina yana sumbata na yadda yake so???”

“Toh meye??? danne ki yayi ya biya buqatar shi ko me??? wai ke meyasa kike nema ki watsa mun qasa a ido ne?? meyasa kike neman ki bata ma kanki tsarin rayuwa da kike ciki a yanzu? A yanzu qoqari kawai zaki yi ki gabato mishi da maganar aure in yaso ayi a huta tunda dai muna samun abinda zamu rufa miki asiri daga wurin shi muyi miki kayan daki na gani na fada”3

Ita dai Layla jin Mama ta gwada abinda Habib din yake yi mata ba komai bane sai ta sa a ranta bazata qara damuwa ba..3

A haka dai suka cigaba da hira yayinda Mama ta dinga lallashin ta akan kar ta sake tayi tunanin rabuwa da Habib domin kuwa shine gatan ta a yanzu..!!

Really????3

KADUNA STATE UNIVERSITY

Zaune take a cikin motar shi suna ta hirar soyayya.

A yanzu haka ana lecture a class amma Layla ta qi shiga- a wurinta Habib ya fi lecture din muhimmanci.+

Habib dai tunda ta fara matsa mishi akan Abba yace ya je ya gan shi ya daina zuwa gidan gaba daya.. A kullum makaranta yake zuwa ya ganta.

“Sweetheart ya maganar zuwan ka gida ganin Abba… baka ce komai ba har yanzu”

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya gyara zama yace “uhm Pretty ba haka bane.. kin ga akwai wani dan shirin da nake yi ne kafin in je.. na tabbatar serious magana ce ta sa Abba ya neme ni..”

“kana nufin you are not serious about our relationship kenan???” ta fada yayinda hankalinta ya tashi.

“haba haba dai Pretty.. ni da nake sa ran auren ki nan da ‘yan watanni.. uhm, I am very serious about US.. Kin ga presently ban fara aiki ba kuma na tabbatar Abban ki zai so ya ji cewar ina da aikin yi. Bana so ya ga kamar dukiyar mahaifi na kawai nake facaka da ita and I am not capable of standing on my own.. ko alama bana so inyi losing dinki don haka kar ki damu zan zo da zarar na karbi appointment letter na wani aiki da na samu a Abuja” ya fada yayinda yake fatan Allah yasa ta gamsu da bayanin shi.

Shiru ta dan yi sannan tace “na fahimce ka sweetheart toh amma me zan ce ma Abba idan ya tambaye ni kai?”

“Just tell him na dan yi tafiya idan na dawo zan je”

“Kenan bazaka qara zuwa gida ba sai a nan zamu dinga haduwa??”

“kiyi haquri Pretty.. for now yes amma it wont be for long”

Bata rai tayi alamun tana fushi.

Hannun shi yayi stretching ya tallabo fuskarta yana shafawa… Hakan ya sa ta lumshe idanuwa.. Aikuwa bata ankara ba ta ji lips dinshi a kan nata inda ya sakar mata wani dan qaramin kiss..

A firgice ta bude idanuwa tana kallon shi cikin tsananin mamaki… Zuciyarta ce take ta harbawa yayinda gaba daya jikinta yayi mugun sanyi.1

Layla dai kasa magana tayi, haka kuma ta kasa daina kallon shi.

Habib wanda ya kula ta daburce sai yayi seizing opportunity din ya matsa tare da cafko lips dinta da nashi..2

Layla dai qoqarin qwacewa take yi amma Habib ya qi bari..

Wani irin intense kiss ya shiga yi mata cikin wani salo mai haukatarwa.. Gaba daya ya birkita mata lissafi… abubuwa ne suke ta yawo a cikinta.. tuni tayi nisa!!

Tun tana qoqarin qwacewa har ta sakar mishi bakinta.. Abin mamaki sai ta tsinci kanta cikin jin dadin abinda yake wakana.. Tuni ta shiga mayar mishi da martani.1

Subhanalillah!!4

Babu abinda kake ji sai nishin su.. Dayake motar Habib Tint ce babu wanda ya san abinda suke yi a cikin motar. Hannun shi ya jefa cikin rigarta ya damqo boob dinta.. Da qarfin tsiya ta ture shi yayinda ta firgita sossai.. Sauke numfashi ta shiga yi kamar wadda tayi gudun tsere kilometer dari.1

“meye haka sweetheart??”

Habib dai kwantar da kan shi yayi a kujera yayinda idanuwan shi suke a rufe… har yanzu bai fito daga duniyar dadin da Layla ta afka shi ba a cikin qanqanin lokacin nan.

STORY CONTINUES BELOW

Bai taba jin dadin kiss ba a rayuwar shi irin wannan.. Duk yawan ‘yan matan da yayi mu’amala da su a nan gida Nigeria da kuma qasashen waje babu wadda kiss dinta yayi rabin dadin na Layla..3

Hannun shi yake murzawa yayinda ya tuno abinda ya ji lokacin da ya damqo boob dinta.. gaba daya ta tayar mishi da duk wata sha’awa da ke kowanne lungu na jikin shi.

“Sweetheart gaskiya bana son abinda kake yi mun.. ka bari idan muka yi aure sai mu yi duk wani abinda masu aure suke yi”

Aure??? tana nufin zai jira ta har sai sunyi aure?? a inaaa… Ya zai yi da bala’in sha’awarta da take damun shi??? ai wallahi qarya take yi.4

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dago kan shi. Idanuwan shi sunyi jajawur yayinda suke dauke da wani shauki na sha’awa.

Ita kanta Layla tayi mamakin yanayin shi..

“Pretty kin dai san baki da mijin da ya wuce ni ko?? ki kwantar da hankalin ki.. ban taba son wata mace ba banda ke kuma ke kadai zan aura.. Ki saki jikin ki mu fahimci juna sossai kafin muyi aure. Baki ga yadda Yusuf da Leema suke yi ba?? don’t you see how free they are with eachother??” ya fada cikin muryar lallashi.

“But sweetheart…”

“but nothing Pretty, bazan cuce ki ba… Ina da tambaya..” ya fada yayinda ya gyara zama.

“ki rantse da Allah abinda ya faru tsakanin mu yanzu bai yi miki dadi ba.. ki rantse a rayuwar ki kin taba jin dadi irin wannan??”

Shiru tayi tana kallon shi… tabbas duk duniya bata taba shiga yanayi mai dadin wanda ta shiga ba a lokacin da suke kiss din toh amma ai it’s not right..2

“saidai idan baki sona ne toh gwara kawai ki fadi mun in qyale ki..”

Hankalinta ne ya tashi jin yayi maganar rabuwa.. ita kuwa idan ta rabu da shi a yanzu tayi ya??? ina zata dinga samun kudi a yadda ta riga ta saba?? ta sani cewar Mama sai ta kusa kashe ta ma..2

“Sweetheart ba haka bane.. yes I won’t deny the fact that it was sweet toh amm..”

Hannun shi ya sa ya toshe mata baki sannan yace “kar ki damu Pretty zaki Saba kuma ma akwai abubuwa dayawa da zan koya miki.. I love you so much and bani da mata a duniyan nan sai ke”

Murmushin jin dadi tayi tace “I love you too”

Hango ‘yan class dinsu tayi suna fitowa, da alama an gama lecture.

“Ka ga yau ma ka sa nayi missing lecture ko??? don Allah kayi qoqari ka cigaba da zuwa gida.. ai ya fi”

“Yi haquri Pretty.. zuwa next two weeks zan gama documentation dina. Kin ga that way, I will be able to face your Dad”

Miqar da hannun shi yayi seat din baya ya bude wata jaka ya zaro kudi bundle na dubu dari ya dora mata akan cinya sannan yace “ga wannan ki sha ice cream”1

Murmushin jin dadi tayi yayinda ta dauka ta sa a cikin Jakarta tace “nagode sweetheart”

Qawayenta ta hango sun fito daga lecture theatre don haka ne tace “bari in je”

“toh Pretty, amma ina son goodbye kiss” ya fada cikin shagwaba.

Turo baki tayi wanda ya sanya tayi kyau sossai sannan tace “toh go ahead”

Da sauri ya cafko lips dinta ya tsotsa cikin qwarewa sannan yace “I love you”1

Murmushi kawai tayi sannan ta bude qofa tace “bye” jikinta duk a sanyaye.

Habib dai tana fita ya buga steering wheel dinshi yace “damn.. this is fire. Wallahi sai na gurji yarinyar nan” yana kallonta ta qarasa wurin qawayenta.. As usual mazaunan ta yake kallo wadanda yake imagining duk ranar da ya damqe su zasu sha murza a wurin shi..2

STORY CONTINUES BELOW

A haka yana ta saqe-saqe shi ya tayar da mota yayi tafiyarshi.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Haleema, Yusrah da Maryam ne suke ta kallonta cike da mamaki kamar wadanda suka ga ghost.

Layla wadda ta tsargu ce tace “wai lafiya kuke kallo na haka???”

“Me kuka yi a cikin mota??” Yusrah ta tambaya

Cike da tsarguwa tace “nothing, what??”

“nothing??? ga lips dinki a kumbure plus your lipstick is gone, gashi nan ma yayi staining miki gefen baki.. you guys kissed???” Maryam ta fada cikin bacin rai.

Aikiwa da sauri Layla ta fara qoqarin goge gefen bakinta..

“toh wai meye da har zaku sa ta a gaba haka? so what if they kissed?? aren’t they a couple??” Haleema ta fada yayinda take qoqarin goge ma Layla Jan bakin ta da ya dan yi staining gefen bakinta.3

“but you know it’s not right ko?? kin manta cewar babu aure a tsakanin ku?? baki san cewar sakar ma namiji jiki akwai hatsari ba? especially..”

Haleema ce tayi saurin daga ma Yusrah hannu tace “madam preacher don Allah ki qyaleta.. shiyasa har yau kika qi sauraron kowa?? don Allah ki barta tayi rayuwarta yadda take so.. besides Habib is a good guy kuma yana son Layla sossai.. bazai taba cutar da ita ba. Kissing, hugging and touching is not a big deal in relationships these days.. bambancin mu kenan da ‘yan zamani da- wayewa”

shin haka ne???6

Maryam wadda ta cika da takaici tace “is that so?? okay ooo.. Allah ya baku sa’a. Dama fa a wannan bangaren ne mukayi disagreeing da juna.. do what you feel is right for you.. afterall it’s a free world”

Ita dai Layla sossai ta zama confused.. ta sani  cewar maganar Maryam da Yusrah gaskiya ne toh amma kamar yadda Haleema ta fada tabbas ta hango soyayyarta a cikin idanuwan Habib.. ta sani cewar he really loves her again bazata yi qarya ba sossai ta ji dadin kiss dinnan kuma ko yanzu ya dawo ya nemi su qara yi a guje zatayi.. toh ma me zai sa ta wani damu tunda Mama tace ba wani abu bane..1

Ya salaam!!

“Ni kam don Allah mu je mu ci abinci kafin lecture din Mr. Isaac..” Yusrah ta fada.

Haleema tace “ai wallahi I am done for today… na gaji. akwai ma inda nake son zuwa.. wani sabon boutique aka bude a NNDC mall zan je in gani”

Ta kalli Layla tace “babes ko zaki je ne??”

Dayake Layla ta ji an ce boutique sai tace “mu je Leema.. nima kam bana son shiga lecture dinnan na Mr. Isaac, wallahi bana gane maganar shi balle in gane me yake nufi”

“ke ma kenan da kike struggling son jin abinda yake fadi…” cewar Haleema yayinda ta riqo hannun Layla.

Maryam tace “toh shikenan babes… sai kun dawo.. mu dai bari mu qarasa Cafeteria”

A haka suka yi sallama da juna…

Dama dai haka abin yake.. Haleema, Layla, Maryam da Yusrah qawayen juna ne amma kuma suna da bambancin ra’ayi… Haleema da Layla halin su daya don haka sun fi kusa.. Haka Yusrah da Maryam.2

☆☆☆☆☆☆☆☆

Tun daga wannan ranar kuwa Layla ta fara sakin jiki da Habib… A kullum yana zuwa ganinta a makaranta su kebe a cikin motar shi ya shashafa ta son ranshi sannan ya tsotsi bakinta iya tsotsa.. Kudi kuwa tana kwasar su a wurinshi kamar ba wahalar neman su ake yi ba.. Dama dai burinta kenan.. the more yana sakar mata kudi, the more take qara sakar mishi jikinta… Ta kai har ya fara zura hannun shi a cikin bra dinta yana shafa boobs dinta. Tun tana noqewa har ta daina.. Layla dai a yanzu har ta fi Haleema missing lectures.. Ameera bata jin dadin yadda Layla kullum bata class… Assignments idan an basu ita take yi mata tunda ta san ba yi take yi ba.. Tun abin na damunta tana sanya mata ido har ta kasa haquri tayi confronting dinta.. aikuwa ta sha zagi da masifa, kaca-kaca Layla tayi mata don haka ne ma ta qyale ta.

STORY CONTINUES BELOW

Ameera dai dukda Zayd ya fita daga rayuwar Layla sannan tayi qoqarin mantawa da shi kamar yadda Qawarta Zarah da Ummanta suka bata shawara, daidai da rana daya bata manta da shi ba.. Zayd yana nan maqale a zuciyarta… Gaba daya a duk qarshen sallolin ta biyar da nafilfilin da take yi a kowacce rana sai tayi ma Zayd addu’a. Ta sani cewa ko aure tayi a rayuwarta Zayd will hold a special and important place in her heart.. Ta tabbatar ko mutuwa tayi da son shi maqale a cikin zuciyarta zata tafi..1

Wannan kenan!!

☆☆☆☆☆☆☆

Weeks later!!

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

A yau zaune suke gaba dayan su a falo wuraren qarfe tara na dare.

Gasashiyar Kaza ce a gaban su suna ta ci. Asali dai Abba yakan siyo musu gasassar Kaza irin haka su zauna gaba dayan su a falo suna ci suna hira dukda kuwa hirar dai yin ta ake yi don dole amma kowa ta ciki na ciki.

Over the years kam babu laifi Abba yayi iya qoqarin shi na ganin kawuwan yaran shi sun hadu tunda dai Mama has always made things difficult. Ameera da qannen ta maza gaba dayan su kuwa kan su a hade yake domin kuwa Ibrahim, suleiman da Munnir yaran Mama sossai suke sonta.. suna sonta fiye da yayar su Layla, haka kuma suna son Aliyu Haider sossai. Ita kuwa Layla ganin idanuwan Abba ne take jan su a jiki amma da zarar babu shi a kusa toh fa daga kyara sai hantara..

“Layla har yanzu ban ga shi saurayin naki ya zo ba.. kin fadi mishi saqona ko kuwa???” Abba ya tambayeta.

“Uhm Abba dama yayi tafiya ne.. amma idan ya dawo yace zai zo”

Ameera ta kalli Layla cike da mamaki.. Habib din ne yayi tafiya bayan ko yau ya zo makaranta har yasa tayi missing din test?? meyasa tayi ma Abba qarya??

“shi wancan saurayin naki Zayd lafiya kwana biyu bana ganin shi har a masallaci???”

Layla ta dan turo baki tace “nima ban sani ba Abba, na kira wayar shi ma bata shiga”

Mama ce tayi caraf tace “toh wa ya sani qila ya gane cewar ta fi qarfin shi ne ya dauke qafa.. ni dama ba son wannan yaron nake yi ba.. Mutum babu aikin fari balle na baqi.. sai buga-buga ta iska. Ta ina zai iya riqe Mata idan ba rigima ba”

Maganganun Mama sun soki zuciyar Ameera sossai… Ji tayi kamar ta mutu don baqin ciki na yadda ake zagin Zayd amma bata iya rama mishi.. Allah sarki marassa qarfi ya shiga uku a rayuwa!!1

“Ki daina irin wannan maganar Maman Layla, abinda Manzon Allah (SAW) yace, a auri namiji mai halaye guda biyu, na farko mai addini, na biyu kuma kyawun halaye… shi wannan arzikin da kike kira ai na Allah ne.. kuma idan har yaron nan ba sata yake yi ba.. yana aiki da gumin shi don neman halaliyar shi sannan zai iya ciyar da kanshi ya ciyar da iyalin shi ai ina ganin ba abin kushewa bane.. ita rayuwa da kike gani idan ka bi ta a sannu bazaka rasa samun nasara a al’amuran ka ba..”3

Tunda ya fara magana Mama da Layla suka canza fuska. Gaba daya ma zaman falon ya gundire su musamman Mama wadda ta kasa haquri tace “toh wai Abban yara a ina ka san yaron yana da abubuwa biyun da ka lissafa? na ga dai ba sanin shi kayi ba balle..”

Murmushi Abba yayi yace “Maman Layla kenan.. An ce juma’a mai kyau tun daga laraba ake gane ta. tun daga ranar da yaron nan ya zo ya gabatar da kanshi a matsayin Masoyin Layla Halayyar shi suka bayyana a maganganun shi… Ban taba fadi muku ba, duk ranar da yaron nan ya shigo unguwar nan idan limamin mu Malam Idris yana da uzuri shine yake ja mana sallah a masallaci sannan bayan mun idar ya tunatar da mu abubuwa dangane da addinin mu a cikin dan qanqanin lokaci.. Bayan kowa ya fita kuma ya share masallaci tas sannan ya mayar da komai inda yakamata wanda bayan nan ne yake qarasowa nan gidan wurin Layla.. Hafizi ne na Al-qur’ani mai girma.. Dukkannin mutane- Yara da dattijai da muke sallah tare da su a masallaci sun shaida cewar Zayd yaro ne mai hankali da Addini.. kar ki manta Hausawa sun ce Hali zanen dutse… Allah yasani nayi ma Layla kwadayin Zayd a matsayin miji amma kuma idan hakan shine ya fi zama alkhairi ai shikenan.. Allah kuma ya sa duk inda yake yana cikin qoshin lafiya”5

“Ameen” suka jiyo muryar Ameera.

Ameera dai jin wadannan kyawawan kalaman daga bakin Abba akan Zayd sossai suka sa ta ji dadi… Gaba daya ya wanke mata baqin cikin da Mama ta cusa mata a zuciya game da Zayd.. Irin mijin da take da burin aure- mai hankali da Addini. A yanzu sai dai tayi fatan samun mai irin halin shi tunda dai ta san bazata taba samun shi ba.1

Ita dai Umma dama idan magana ta shafi Mama da ‘yarta bata tsoma bakinta a ciki domin kuwa ta sani sarai ita baqin hali gareta a idanuwan su.

A haka dai suka cigaba da random hirarraki.. yawanci duk na makaranta ne. Kamar kullum Abban su yana basu shawara tare da yi musu nasiha na yadda zasuyi zaman rayuwa sannan su riqe addinin su da muhimmanci sossai..

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *