ZABI NA CHAPTER 3 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 3 BY FADEELARH

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

KADUNA STATE UNIVERSITY+

A yau ne wani saurayin Haleema mai suna Yusuf Suleiman Mayana zai zo ganin ta. Asali yakamata ya je gidan su ne amma kuma tafiya ta taso mishi zuwa Russia wanda mahaifin shi ne ya aike shi don haka ne zai zo school don suyi sallama.

Yusuf dai yana cikin samarin Haleema da take ji da shi domin kuwa gayen yayi ne ta ko’ina. He is handsome, rich and sophisticated.

Tana zaune a garden tare da qawayen ta ne ya kira ta a waya tayi mishi kwatancen inda take.

“Yau dai Layla zata ga Yusuf dina.. ” cewar Haleema.

Layla tace “tabbas yau zan gan shi.. na kula kina ji da shi ai..”

Yusrah ta tabe fuska tace “hmm.. ni kam duk gani nake yi bata lokaci ne tsayawa sauraren samari idan ba wai na shirya auren bane”

Maryam tana dariya tace “Yussy kenan.. Allah dai ya kai mu ranar da wani zai sace zuciyar ki, I swear we wont hear word”

Suna nan zaune suka hango shi a parking lot inda ya faka motar shi. Wata dalleliyar Lexus jeep mai kyan gaske, sai walqiya take yi.

Gani nayi Haleema ta miqe tace “babes let’s go”

Zaune suke cikin motar tare da abokin shi mai suna Habib Aliyu Nasidi. Habib Aliyu Nasidi yaro ne a gidan Alhaji Aliyu Nasidi, tsohon senator. Habib ba fari bane sannan ba baqi bane, yana da kyau sossai sannan da ka gan shi ka ga hutu.. Ya masifar iya gayu shiyasa mata suke bala’in son shi.

Habib da Yusuf suna daya daga cikin manyan yara a cikin garin Kaduna.. A yanzu haka tunda suka kammala karatun su babu abinda suke yi sai kashe kudin iyayen su… babu aikin fari bare na baki. Iyakan su suyi ta kashe ma ‘yan mata kudi sannan su ziyarci night clubs suyi sharholiyar su da ‘yan mata.

“Abokina nayi gamo..” yayinda ya qura ma Layla idanuwa wadda suke dosowa wurin su tare da su Haleema.

“a ina??” Yusuf ya tambaye shi in a confused tone.

Yayi pointing at Layla yace “waccan farar, wallahi ina son ta kuma I dont care ko wacece, I dont care whether she is married.. I just like her and she has to be mine”

Yusuf ya fashe da dariya yace “Shege Romeo.. you’ve got all it takes to woo her ai.. I trust you. let’s find out who she is”

A lokacin da suka qaraso ne Yusuf ya bude qofar shi ya fito..

Abinda ya faru next shine ya masifar ba su Layla mamaki..

Gani sukayi ya bude hannuwan shi yayinda Haleema ta qaraso da sauri ta shige tare da hugging dinshi..

“Babe how are you doing?”

cikin shagwaba tace “I am fine.. yanzu daga dawowa jiya kuma sai yau kace mun zaka tafi Russia?? Gaskiya Daddy baya kyauta mun”

Kafin yayi magana ne ya ji muryoyin su Maryam suna gaishe shi..

Yusuf ya riqe Haleema ta gefen shi yayinda ya jingina da motar sannan ya amsa gaisuwar su.

“Ya school??”

Maryam ce tace “lafiya lau”

Haleema tace “sweetheart these are my friends.. wannan itace Maryam, ga kuma Yusrah sai Layla..”

STORY CONTINUES BELOW

“Nice to meet you all, hope dai ta baku labari na kuma da fatan ni nake mulki a birnin zuciyarta?”

Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Layla tace “ofcourse she did.. and guess what, labarin ka kawai muke ji a bakinta don haka it means kai kadai kake mulki a birnin zuciyarta”

Maryam da Yusrah dai da sauri suka kalli Layla cike da mamaki domin kuwa it’s a big fat lie.. Samarin Haleema sunyi yawa har baza’a iya qirga su ba.

Ita kuwa Haleema sossai ta ji dadin abinda Layla tayi.

“Aikuwa na ji dadi Layla..” ya kalli Haleema yace “thanks babe..”

Haleema wadda take murmushi ta ga alamun mutum zaune a cikin motar tace “tare da wa kake ne yayi zaman shi a cikin mota??”

Yusuf yayi murmushi yace “Habib..”

“ooh Habib ne ya qi fitowa mu gaisa?? ana jin mulkin kenan yau..”

Yayi knocking glass din window dinshi yayinda Habib ya bude qofar ya fito.

Kallo daya Layla tayi mishi ta zurma… Bata san tayi nisa a kallon shi ba sai da ta ji muryar shi a kusa da ita yana fadin “hello pretty”

Zuciyarta ce ta buga yayinda ta bi ta rude…

“Layla ina tunanin ki ya tafi ne?? Habib yana ta magana baki ji ba” cewar Haleema

murmushi tayi sannan tace “uhm.. sorry I was just”

“Never mind pretty.. ya kike???”

Kafin ta amsa ne Maryam tace “toh mu dai bari mu koma class..” yayinda ta kamo hannun Yusrah suka yi musu sallama.

Bayan su Maryam sun tafi ne Habib yace “Ni suna na Habib Aliyu Nasidi.. tunda na hango ki kika sace mun zuciya kuma in taqaice miki zancen nan wallahi son ki nake… don Allah ki so ni”

Ba Layla kadai ba hatta Haleema da Yusuf sai da suka yi dariya.

What is wrong with this guy???

“Layla wallahi ko aure gareki dole mijin ya sakar mun ke in aura… I have fallen deeply in love with you and there is no going back”

Cike da murna Layla tace “hey relax.. i am single”

Sossai ya ji dadi yayinda ya miqa ma abokin shi hannu suka tafa yace “today is my lucky day for sure..”

Ya kalli Layla yace “Pretty nagode sossai dukda baki ce kina so na ba tukun..”

Dariya kawai Layla tayi don kuwa ta tabbatar yau tayi kamu, ta tabbatar ta samu irin namijin da take nema, kyakyawa, wanda ya iya gayu, mai arziki… Lallai tabbas yau ta hadu da saurayi ba irin su Zayd ba… shin ta ma isa ta bude baki tace bata son shi???2

“Pretty mu dan matsa mu samu wuri mu zauna yadda zamu fahimci juna saboda akwai ‘yan sa ido a kusa” ya kalli su Haleema cikin tsokana yayinda suke ta dariya.

“wallahi ka bata mun rai zan tafi in bar ka” cewar Yusuf

Habib yayi dariya yace “idan dai tare da wannan sarauniyar zaka bar ni ai babu matsala.. I die here”

Haleema dai sai kwasar dariya take yi yayinda Layla take cike da tsananin farin ciki.. Allah ya hada ta da abinda take nema!!4

☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Kwance take a kan gadon mamanta yayinda take bata labarin Habib Aliyu Nasidi.

“wallahi mama sai kin gan shi.. kyakyawa, ga iya gayu sannan kuma uwa uba ga ‘ya’yan banki da suka zauna mishi”

Mama wadda take zaune a qasa tana cin tuwo tana ta washe baki yayinda tace “da kyau Layla ta.. ai tunda na haifo ki na sani cewar kina da qashin arziki.. na sani cewar ke matar manya ce. shiyasa nace miki ki dinga shiga cikin yaran masu kudi, a ta dalilin su ne zaki samu samari masu kudi. So nake ki riqe shi gam ki ci arziki ki mori rayuwa”3

STORY CONTINUES BELOW

Layla tana dariya tace “ai baki sani ba, yace gobe zai kawo mun sabuwar waya don mu dinga chatting.. wallahi har na qagara…”

Wayar ta ce da tayi ringing ta hana ta qarasa maganarta.

Ko da ta duba gani nayi ta bata rai harda buga uban tsaki tace “ai wallahi baka isa ba.. ni bazan ma qara fita in saurare ka ba.. talakan banza kawai”1

“ke da wa kuma??” Mama ta tambayeta.

Tsaki Layla ta ja tare da jefar da wayar tace “wannan Zayd din ne mana.. mutum babu ko sisi sai kazo ka ishi mutum da hirar soyayya ta banza..”

Mama tace “Allah dai ya riga ya kawo mu qarshen tarayyar ki da shi.. zaki rabu da shi ki huta.. ya je can ya nemi daidai da shi”

Haka Zayd ya dinga kiran Layla a waya amma sam ta qi picking. Da ta ji shiru tayi tunanin ya haqura ne.

Hirar Habib ta cigaba da ba Mama yayinda take cike da farin ciki.

Suna cikin hirar ne suka ji sallamar Munnir a bakin qofar dakin.

Mama ce ta amsa sallamar.

“Ya Layla dama Ya Zayd ne yake jiran ki a waje… wai ya kira wayar ki bakya picking” cewar Munnir.

Danna mishi harara tayi tace “je kace mishi nace bazan fito ba kuma kar ya qara zuwa gidan nan..”

Cike da mamaki Munnir yake kallon ta yayinda ya kasa motsi..

Mama ce ta dago ta kalle shi tace “baka ji abinda ta ce bane??”

“amma Mama ya za’a yi in fadi mishi wannan magan..”

“ka ci uwaka Munnir.. dan ubanka ni zaka fadi ma magana???” Mama ta fadi cikin masifa.

Da sauri yace “Yi haquri Mama..” daga nan ya juya ya bar dakin.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Munnir ya fito daga dakin mama jiki a sanyaye ne ya tarar da Ameera a falo zata shiga dakin su.

Ganin yanayin shi ne ta dakatar da shi.

“Munnir ya na gan ka haka?? wani abu ya faru ne???”

A nan ya bata labarin abinda ya faru wanda bata yi mamaki ba.

Hannun shi ta riqo tace “Munnir ka daina yin abubuwan da zasu bata ma Mama rai.. ka ga mahaifiyarka ce..”

“toh Ya Ameera ya za’a yi in je in fadi ma Ya Zayd saqon Ya Layla.. wallahi bazan iya ba. Ina jin kunyar shi sossai”

Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “jeka abinka.. ni zan je in fadi mishi”

“dagaske Ya Ameera??” ya tambayeta cike da relief.

“yeah bro.. bari in je in dauko hijab dina”

☆☆☆☆☆☆☆☆

Zayd ne zaune a kan dakalin qofar gidan yayinda yake riqe da torchlight phone dinshi yana jujuya ta kamar wanda yake analyzing dinta. Sanye yake cikin wata T-shirt da wandon jeans wadanda suka kode amma so neat…

Wata leda ce ajiye a gefen shi.

Ameera ce ta fito daga gidan yayinda ta tsaya tana qare mishi kallo. A yau ganin ta da shi ma biyu kenan..

Dukda babu wani wadataccen haske na wuta a qofar gidan bai hana ta ganin kyakyawar fuskar shi ba da gashin kanshi wanda yake a kwance luf-luf tamkar na balarabe.. ta tabbatar Zayd yana da dangantaka da larabawa domin kuwa features dinshi duk irin nasu ne… ta tabbatar da yana cikin kwanciyar hankali zai fi haka haske da masifar kyau.

“Assalamu’alaikum” ta fada cikin muryarta mai sanyi.

Da sauri ya dago kanshi ya ganta tsaye a gefen shi.

STORY CONTINUES BELOW

“wa’alaikis Salam..” ya fada cikin tashi muryar wadda take masifar so.

Ita kam har accent na larabawa take ji a muryar shi.. bata sani ba ko qila saboda tana daganta shi da su ne oho!!

“Ina wuni Ya Zayd”

“lafiya lau Ameera..” tare da yi mata murmushi.4

Sossai ta zama shocked da ta ji ya kira sunan ta..

Dama ya san ta ne???

“Ya Zayd dama ka san sunana??”

“uhm.. eh mana. ke ba qanwar Layla bace???” ya tambayeta tare da miqewa tsaye.

Ameera dai sossai zuciyarta take harbawa.. gaba daya ma ya dagula mata lissafi. Wutar soyayyar shi ce take ruruwa a cikin zuciyar ta.. Ji take yi kamar ta bude idanuwanta ta gan ta a gidan shi a matsayin matar shi.3

“Layla tana bani labarin ki ai.. ” ya fada yayinda ya qura mata idanuwa.

Ameera ta cika da mamakin wannan maganar.. Layla take bada labarin ta?? ai bazai taba yiwuwa ba… saidai idan zaginta take yi..

“she told me how very nice you are and…”

Ameera dai bata san lokacin da ta fashe da dariya ba.. hakan ya sanya shi yin shiru yana kallonta.

“meyasa kike dariya?? did I say something funny???”

Girgiza kai tayi alamar ‘eh’ sannan tace “uhm dama na zo in fadi maka cewar Ya Layla tana bacci.. kan ta ne yake dan ciwo shine ta sha panadol ta kwanta”

Murmushi yayi yace “ki fadi mun gaskiya Ameera.. tace bazata fito bane ko???”4

Shiru Ameera tayi tana kallon shi cike da tausayawa yayinda tace “don Allah kayi haquri”

Girgiza kai yayi yace “its okay” Ya miqa mata ledar hannun shi yace “ga wannan ki bata.. ki ce ina gaishe ta.. sai da safe”

Ameera ta karbi ledar yayinda tayi tsaye ta kasa motsi har ya juya yayi tafiyar shi.. Sossai ta hango disappointment a fuskar shi, da alama ya so ganin ta..

Ajiyar zuciya ta saki tace “if only you know how very much I love and care about you Ya Zayd”

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Ameera ce tsaye a qofar dakin Mama tana ta sallama amma sun qi amsa ta. Tana jin su suna ta hirar su harda dariya..

Cikin sallama ta shiga dakin wanda ya sanya su duka suka juyo suna kallon ta.

Cike da bacin rai Layla tace “lafiya zaki fado mana cikin daki babu sallama?”

“Yi haquri wallahi ina ta sallama amma baku ji ba…” ta qarasa wurin Layla tace “dama Ya Zayd ne ya kawo miki wannan”

Ta miqa mata ledar hannunta..

Layla tana karba ta zazzage ledar sai ta ga atamfar Chiganvy na ankon da tace ya siyo mata wadda sai da ya fara kawo mata roba-roba tayi mishi wulaqanci kuma ta amshe..

“Iyyeh.. dan halak ya cika alqawari. kenan ya samo ‘yan kudade. Ai da na sani na fita qila ko na katin waya in samu”

Wannan maganar sossai ta qona ma Ameera rai.

Juyawa tayi zata bar dakin yayinda ta duqa ta kwashe kwanon da Mama ta ci abinci sannan ta fita da sauri don sam bata so ta ji wasu baqaqen magnaganun daga bakin Layla.

Aikuwa tana fita Layla tace “baki ga ta ji haushi ba saboda maganar da nayi??? Ni kam idan son shi take na bar mata don wallahi babu abinda zanyi da talaka”

Mama tayi murmushi tace “zasu fi dacewa kuma.. Ni kam kiyi qoqari kiyi ta karbar ‘ya’yan banki a hannun wannan Habibun don mu samu mu hada na kayan daki. Kin dai san mahaifinki ba wani abin arziki zai hada miki ba… gwara mu hada kaya na gani na fada tunda gidan masu arziki zaki”

“kar ki damu Mama.. a yadda nake gani na tabbatar zan tara dukiya mai yawa daga wurin Habib.. da ganin shi yana da sakin hannu. Bari dai in fara karbar wayar tukun”

♤♤♤♤♤♤♤♤Cikin dan qanqanin lokaci Habib Aliyu Nasidi ya canza ma Layla rayuwa.+

Tuni ya bata sabuwar waya.. qirar Samsung Galaxy S10. Habib ya kula cewar Layla is from a poor family.. ya sani cewar idan har yana so tayi matching social class dinshi dole ne sai yayi polishing dinta..

Sossai ya dinga sakar mata kudi.. kudaden da yake bata kuwa tun tana lissafa yawan su har ta daina.

Da zarar ya bata kudi sai ta kawo ma Mamanta.. A nan dakin Mama suka samu wadrobe suna ta zubawa cikin Ghana-must-go.. sai dai kawai idan hidima ta taso su bude su cire.

Tuni ta siyo manyan atamfofi Super wax, manyan lesussuka, manyan shaddoji getzner da materials masu tsada kala-kala ta bayar dinki.

Jakkuna da takalma ta siyo su dayawa su ma.. Ga jewelries masu kyau da tsada

A yanzu haka Layla ta zama first class babe.. sossai ta dace da clique dinta- Maryam, Haleema da Yusrah.

Tunda ta hadu da Habib ta daina bin Ameera makaranta a Napep.. kullum shi yake zuwa ya dauke ta ya kai ta sannan ya dawo da ita. Akwai lokacin da baya nan ma driver ya aiko ya dauke ta ya kai ta.

Duk wannan hidimar da ake yi Abban su baya da labari saboda a bayan idanuwan shi ake yi. Bai ma san Habib ba sannan bai san yana zuwa ba… dayake lokutta da dama a makaranta suke haduwa.

Umman Ameera batayi mamakin abinda yake faruwa ba tunda dai dama Ameera ta bata labarin komai. A kullum dai tana cikin yi ma ‘yarta nasiha akan lallai ta tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ta.. kar ta sake ta bari halayen Layla su rude ta. Banda kwadayi da son abin duniya… Duk mai kwadayi babu inda mota take sauke shi sai tashar wulaqanci.6

Gaba daya Layla ta daina sauraron Zayd.. tun ranar da ta hadu da Habib ta fita batun shi gaba daya.. Sai ya zo sau biyar amma da qyar take fitowa sau daya.. shima din idan ta fito ba wata maganar arziki ke fita daga bakin ta ba.. banda cin mutunci da wulaqanci babu abinda take yi mishi.

Lokutta da dama haka zai dauki jiki ya je har gidan su ya aika a kirata amma sai ta qi fitowa. Hakan kuma bai hana shi dawowa gobe.2

ikon Allah!!

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

One month later..

A yau ne ake bikin kamun qawar Layla mai suna Bilkisu.

Layla dai a dalilin tana so ta nuna ma qawayenta ta zama babbar yarinya sai bata dinka Chiganvy wax din da Zayd ya kawo mata ba.. instead sai ta siyo irin atamfar sak amma Super wax tayi mata wani shegen dinki mai kyau da tsada.

Chiganvy din ma wata qawar su ta ba kyauta don tana ta complain akan bata samu kudin siyan anko din ba.

Layla ta so ta gayyaci qawayen ta su Haleema amma ta sani sarai bazasu so irin bikin ba tunda dai tana ganin hotunan irin bukukuwa na manyan mutane da suke zuwa.

A Arewa house za’ayi bikin kamun.. dayake tayi planning tare da Habib zata je sai ta sanar da qawayen ta (Su Ramlatu..) kar su jira ta kawai zasu hadu a event hall din.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

AREWA HOUSE

RABAH ROAD

Mutane ne tsaye a waje yayinda ake jiran isowar amarya don a tsara yadda za’a shiga hall din..

STORY CONTINUES BELOW

A daidai wannan lokacin ne Motar Habib Baqa wuluk sannan sabuwa dal qirar latest BMW X-series ta danno kai..

Gaba daya kuwa kallo ya koma kan motar yayinda aka sa ido don ganin fitowar amarya..

a tunanin su ita amaryar ce a ciki..

Layla ce zaune a cikin motar yayinda take kallon shi tana murmushi..

“Sweetheart kallon nan fa yayi yawa… tunda ka dauko ni daga make-up studio kake kallo na.. kusan sau uku kana kusa bige mutane a kan hanya…” ta fada cikin shagwaba.

Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “kin dai san ba laifi na bane ko?? toh laifin ki ne..”

“kamar ya Laifi na??”

“Your beauty is the cause of all these my dear.. kin fi kowacce mace kyau a duniyan nan..”

Ya kamo hannun ta yayi kissing sannan yace “I just cant wait to have a taste of you pretty”

Layla dai a farkon haduwar su bata bari Habib ya taba ta saboda bata saba ba amma ganin yadda Haleema take yi da Yusuf sai ta fahimci harka ce ta wayewa..4

A yanzu haka tuni Habib yana riqe hannun ta har ma yana shafa fuskar ta ba tare da ta damu ba..

Yau ce rana ta farko da ya fara yi mata kiss.. dukda a hannu ne sai da ta ji wani iri..

Ganin ta kasa motsi ne yace “pretty why are you cold?? baki son kiss din da nayi miki ne???”

Murmushi tayi tace “no Sweetheart ba haka bane.. kasan kawai ban saba bane”

Matsowa yayi daf da ita yace “kar ki damu zaki saba.. Yanzu dai ya za’a yi?? in je in dawo ne ko kuwa in jira ki??”

Gani nayi ta waiga ta kalli qawayen ta da yadda ake ta kallon motar..

Da sauri ta juyo ta kalle shi sannan tace “I think bari in kira qawaye na ku gaisa sannan sai ka tafi in ya so anjima idan an gama sai in kira ka zo ka dauke ni ko???”

Ya girgiza kai tare da fadin “okay pretty.. your wish is my command”

Murmushi tayi sannan ta bude qofa ta fita.

Aikuwa tana fita na ga qawayen ta sun zaro idanuwa cike da mamaki suna kallonta.

Tana murmushi ta fara tafiyarta cikin salo mai rikitarwa..

Habib wanda yake cikin mota kuwa qura mata idanuwa yayi musamman mazaunan ta da yadda hips dinta ke motsi cikin salo na birgewa. Gaba daya ta tafi da tunani da hankalin shi..

Dinkin fitted gown Layla tayi wanda ya fitar da shape dinta sossai.. ta sanya wani dogon takalmi a qafar ta yayinda tayi adorning kanta da wasu jewelries masu tsada..

Kallo daya zaka yi mata ka san cewar babbar yarinya ce sannan da ka kalle ta ka san ba qananan kudade ta kashe ma jikinta ba.

Qawayen ta guda hudu suka rugo wurinta a guje cike da mamaki.

“Layla??? ashe dai dagaske ne kin canza rayuwa???” cewar Ramlatu.

Murmushi kawai tayi yayinda Maimunatu tace “babu shakka ke ce na gani ranar a Daraja kuna fitowa tare da wani kyakyawa kunyi shopping..”

Layla tana dariya tace “I am sure ni ce Maimunatu.. toh ya kuke?? amaryar tamu bata iso ba ne??”

Safiya ce tace “hmm.. mu da muka hango motar da kika fito ma we thought ita ce.. Hala ke da ogan naki ne?”

Layla tace “eh wallahi, mu je ku gaisa”

Safara’u tace “Lallai ma Layla.. wallahi ke kam kina da sa’a a rayuwa. Dama fa ni na san ke ta manya ce don wallahi kyan ki ba a banza ba”

STORY CONTINUES BELOW

Gaba dayan su suka yi dariya yayinda suke ta hira har suka iso wurin motar Habib.

Cike da fara’a ya fito suka gaisa har suka dan yi ‘yar hira. Da zasu tafi ne ya basu bundle na sabbin naira dubu daya har na dubu dari.

Aikuwa suka dinga washe baki suna godiya yayinda suke ta mamakin yawan kudaden da ya basu da kuma wadanda Layla take samu a hannun shi.

Ko da suka yi mishi sallama sai ya hana Layla tafiya don haka ne suka tafi suka barta.

Komawa suka yi cikin mota suka zauna.

“thank you very much for..”

“don Allah ki daina.. babu abinda bazan yi ba a dalilin ki”

Murmushin jin dadi tayi yayinda tace “nagode sossai”

Bata ankara ba ta ji ya kamo hannunta wanda ya sanya ta dan rude amma kuma ta matse.

Murza hannun ta ya shiga yi yayinda take ta jin wasu abubuwa suna yawo a cikin jikinta. Gaba daya duk ta bi ta rude..

Habib dai idanuwan shi suna bisa qirjinta yayinda yake kallon cleavage dinta da kuma tudun boobs dinta da suke a bayyane..

“Pretty jikin ki akwai laushi sossai.. I swear I love every part of you”

tana murmushi tace “nagode”

Abinda ya faru next ne ya firgita ta.. Hannun Habib ta ji a kan Cleavage dinta.

Da sauri ta zabura tace “Sweetheart what are you doing?”

Fashewa yayi da dariya yace “hey relax, babu abinda nake yi.. kawai ina qoqarin gyara miki wuyan rigar ki ne.. ta dan sauko har tana revealing cute boobs dinki”

Da sauri ta kalli qirjinta ta ga lallai maganar da yayi gaskiya ne.. Yanayin dinkin da aka yi mata irin wanda ke bayyanar da saman qirji ne (deep neck) wanda ‘yan mata suke yayi a yanzu.

Gyara zaman ta tayi ta dan gyara rigar sannan tace “nagode”

Murmushi kawai yayi yayinda hankalin shi yayi nisa wurin tunanin laushin abinda ya taba… Tabbas yana buqatar kasancewa da Layla.2

Haka suka cigaba da hirar soyayya har motar amarya ta shigo. A nan ne suka yi sallama wanda kafin ta tafi sai da ya bata naira dubu dari biyu. Layla kuwa mamaki ta dinga yi irin kudaden da Habib yake kashewa a kanta.. bata taba tunanin zata dinga riqe manyan kudade ba irin wadannan.. Godiya tayi mishi sannan sukayi sallama akan zai dawo ya dauke ta idan an gama.

Haka Habib ya sa mata idanuwa har ta isa wurin motar amarya yayinda ya saki ajiyar zuciya.. Gaba daya Layla ta tafi da hankali da tunanin shi. Duk ‘yan matan da yake mu’amala da su babu wadda ta kai Layla kyau da diri… Harkar shi na zuwa night club da bin ‘yan mata da yake yi duk ya daina tun daga ranar da ya hadu da ita. Ya tabbatar duk ranan da ya same ta sai ya gurza ta fiye da yadda ya taba gurza wata mace domin kuwa sha’awar shi ta qare akan Layla.

Ya kula Layla bata waye ba sossai shiyasa yake qoqarin bin ta ahankali yadda zata saki jiki da shi su more rayuwa.. Ya kula cewar KUDI sune abinda Layla take so kuma yayi alqawarin zai bata ko nawa take so idan dai har zai same ta kamar yadda yake mafarki. Habib bayada burin aure ko alama amma kuma haduwar shi da Layla sai yana ji kaman he is finally ready to settle down but not until he tastes her.4

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Wuraren qarfe tara na dare suna zaune a cikin motar shi a qofar gidan..

Bai dade da ya dauko ta daga gidan su Bilkisu ba.. Dayake bayan an gama bikin Kamun ta bi qawayenta suka tafi gidan su Bilkisun sannan.. Sai bayan sallar Isha’I ta kira shi don ya je ya dauko ta.

STORY CONTINUES BELOW

Riqe da hannunta yake yayinda ya qura ma qirjinta idanuwa yana ta hadiye miyau.. Dukda babu wadattacen haske mayatattun idanuwan Habib suna ganin abinda suke gani.

“Ina son ki sossai Sweetheart.. Allah ya nuna mun ranar da zan mallaki wannan kyakyawan jikin naki.. i really cant wait to rock you”

Ita dai Layla bata so idan Habib yana mata irin wannan maganganun. Tun haduwar su ta kula bayada wata magana idan ba ta jikinta ba.. ta sha ayyanawa a ranta Habib dan iska ne amma kuma kudaden da yake shaqa mata suke sa idanuwan ta su rufe ta manta zancen.3

Yanzu haka fuskarta a murtuke tace “ni kam sai in ga kamar ba so na kake yi ba.. kamar jikina kake so and I am….”3

“what???? nooo pretty. Wallahi ko kadan, ina son ki sossai sannan a tunani na don na yaba kyan tsarin jikin ki banyi laifi ba ko kuwa???” ya fada yayinda ya qura mata idanuwa.

Kafin tayi magana ne ta hango Abban su tare da makwabcin su Malam Zakari suna tattaunawa.

Dawowan su kenan daga meeting na ‘yan committee na Masallaci.2

Tunda suka tsaya Abba ya kalli motar Habib ya kauda kanshi… fuskar shi ta bayyana bacin rai!

Da sauri Layla ta fizge hannunta daga na Habib yayinda ta bi ta rude.

“Ga Abba na ya dawo, yakamata ku gaisa saboda ya san ka..” cewar Layla.

Sosa kai Habib yayi yace “gaskiya ba yau ba Sweetheart.. ban shirya facing dinshi ba, maybe next time”3

Layla dai bata ji dadin response dinshi ba musamman sanin cewar Abba baya so samari na tsayawa qofar gidan shi anyhow ba tare da izinin shi ba but babu yadda zata yi don haka ne ta haqura.

Suna kallon Abba yayi sallama da Malam Zakari sannan ya juya zai shiga gida..

Gani nayi ya qara kallon motar cike da disappointment sannan ya shige gidan.

Layla dai ganin yanayin Abba ta tabbatar akwai matsala.. dayake duk ta bi ta rude sai kawai ta nemi suyi sallama da Habib.

Kafin ta tafi kuwa sai da ya qara danna mata wata dubu dari biyun a hannu yayinda ta cika da murna..5

Yana nan zaune ya qura mata idanuwa har ta shige gida.. Mazaunan ta ya bi da kallo da yadda take juyasu cikin qwarewa.. Bayan ta shige ne ya daki steering yayinda yace “wallahi sai na dandana ki kwanan nan”

☆☆☆☆☆☆☆☆

Layla tana shiga gate din su tayi sauri ta bude Jakarta ta zaro gyale ta yafa..

Dama dai haka take yi a kullum.. idan zata fita daga gidan tana yafa gyale saboda Abban ta amma tana fita take sanya shi cikin jaka.. A cewar ta wayayyun ‘yan mata na zamani sun daina yafa gyale saboda yana rufe gayun da suka yi.

shin haka ne???3

Tana shiga falon gidan tayi arba da Abba zaune a kan kujera tare da Mama da Umma.. Da ganin fuskokin su ka san babu lafiya musamman fuskar Abba wadda take a murtuke.

“Daga ina kika fito??” ta jiyo muryar Abba cikin fushi.

A tsorace tace “Abba dama bikin Bilkisu ne…”

Dayake ya san da zuwanta bikin sai bai yi dragging wannan din ba..

“waye na gan ku tare a mota??” ta qara jiyo wata tambayar daga wurin shi.

A yanzu kuwa duk ta rude yayinda ta kasa magana.

Mama ce tayi caraf tace “hala Habib ne?”

“eh Mama, shine..”

“ka gani ko, ai na fadi maka babu wanda yake zuwa wurinta a irin motar da ka kwatanta sai shi” Mama ta fadi.

Ita dai Umma tana ta sauraron ikon Allah yayinda take mamakin dabi’a irin ta mama da ‘yar ta.

Wani irin kallo Abba yayi ma Mama wanda ya sanya ta sha jinin jikinta.

Ya kalli Layla yace “ki fadi mishi ya samu lokaci cikin ‘yan kwanakin nan ya zo ya gan ni.. bazan lamunci yawan tara samari kala-kala ba daga gareki Layla.. yakamata ki kula da irin mutanen da zasu dinga zuwa wurin ki domin kuwa bana son shashanci..”

“toh Abba.. ” Layla ta fada cike da tsoro.

Daga nan ya miqe ya bar falon yayinda Umma ta bi bayan shi… dayake yau din ranar girkinta ne.

Mama kuwa ta bi ta da harara tana fadin “mai baqin hali”

Umma kuwa ta ji ta sarai amma ko juyowa batayi ba balle tayi magana.. Baiwar Allah ta riga ta saba!!

Layla kuwa da sauri ta matsa kusa da Mama cikin rada tace “Mama ya bani kudi masu yawan gaske.. zo mu je daki ki gani”

Mama ta washe baki yayinda ta miqe da sauri tace “da kyau Layla ta… Yarinya mai qashin arziki”GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI+

A yau asabar babu makaranta.. gaba dayan su suna gida.

Tun da safe da Ameera ta tashi daga bacci ta shiga yin ayyukanta na gida da ta saba. A yau din tana qoqarin yi da wuri saboda tayi ma qawarta Zarah alqawarin zata taya ta gyaran gidan ta a dalilin mijinta da zai dawo.

Tun jiya ta nemi permission a wurin iyayenta suka bata izini.

Asali dai tunda Ameera ta hadu da Zarah bata taba zuwa gidanta ba.. Ita dai Ameera dama haka take, a rayuwarta batada shishigi.. musamman idan ta kula social class dinku ba daya ba.

Tunda ta fara ganin Zarah ta sani sarai da iyayenta da Mijinta masu kudi ne domin kuwa daga irin motocin da take hawa da wayoyin da take riqewa zaka gane hakan.. Ba lallai bane ka gane ta daga dressing dinta domin kuwa Hijabi take sanyawa.

Ameera ta so ta ja baya da qawancen nasu a dalilin hakan domin kuwa bata son kai kanta inda batayi fitting into ba.. she prefers living her simple life with simple people.

Zarah ta fahimci hakan amma ta nace mata.. abun har ya kai kamar Ameera tana mata wulaqanci wanda da ace wata ce da tuni ta qyale ta amma inaaa, Zarah dai qara matse mata tayi.

Akan dole suka zama best of friends..

Dukda hakan kuwa Ameera bata taba tambayan ta komai ba dangane da rayuwarta.. abinda kadai ta sani shine Zarah matar aure ce.

A bangaren Zarah itama bata taba fadi mata komai about herself ba because ta kula Ameera bata son mingling da mutanen da ba class dinsu daya ba and she so much like her as a friend so she doesnt want to scare her away.

Zarah ta zo gidan su Ameera har sau uku. Akwai ranar da ta zo ma har wurin Abba ta je ta gaishe shi.

A yau din sun shirya akan ita zata zo ta dauke ta su je gidan nata sannan ita zata dawo da ita.

Wuraren qarfe goma sha daya Zarah ta zo gidan.. Kamar ko da yaushe idan ta zo har dakin Umma take zuwa ta gaishe ta. Umma dai tana son Zarah saboda tana da hankali da natsuwa, Sossai take son qawancen da ke tsakaninta da ‘yar ta… atleast she is certain ‘yarta is not amidst bad company…3

☆☆☆☆☆☆

Zarah tana zaune a dakin su Ameera tana jiran Ameera wadda take wanka ne Layla ta shigo.

Wani irin kallo na wulaqanci Layla tayi ma Zarah sannan ta kawar da kanta.. ita dai Zarah dama can bata son Layla don haka itama yi tayi kamar ma bata ganta ba yayinda ta cigaba da latsa wayarta qirar Samsung Galaxy S20.

Dukda Layla ta san cewar Zarah tana da dagantaka da arziki daga kalolin motocin da take hawa da kuma wayoyin da take riqewa, a dalilin kullum tana ganin ta cikin hijabi sai tana yi mata kallon bagidajiya don haka ne ta raina level of wayewar ta.3

Layla ta haye kan gadonta ta kwanta yayinda ta cigaba da chatting a wayarta.. Hira suke yi da clique dinta a group dinsu da suka hada a watsapp.

Ameera ce ta fito daure da towel wanda ya sauka har qasan gwiwarta.

“Zarah don Allah kiyi haquri na bata miki lokaci..” ta fada yayinda ta nufi gaban madubi ta zauna kan stool.

Zarah tana murmushi tace “take your time bestie.. ni kam tunda kika amince yau din zaki zo gidana ai nayi murna sossai”

STORY CONTINUES BELOW

Ameera dai girgiza kai kawai tayi tana murmushi.

Bayan ta kammala shafa mai ta fesa Deodorant sai ta bi jikinta da spray kuma.. Daga nan ta miqe ta nufi wadrobe din dakin ta bude side dinta ta ciro inner wears dinta da wata atamfa dinkin doguwar riga. Corridor na bathroom dinsu ta koma don ta shirya… Asali dai sun killace corridor din sun mayar da shi dressing room dinsu.

Bayan ta shirya ta fito ne Zarah ta qare mata kallo tace “kinyi kyau sossai bestie..”

Basu ankara ba suka ji Layla ta fashe da dariya har tana fadin “a haka?? saidai inda babu kyawawa..”3

Ameera wadda ta cika da bacin rai ce ta bude baki zata yi magana yayinda Zarah ta daga mata hannu alamar tayi shiru.

Ran ta a bace ta juya ta nufi wadrobe ta dauko Hijab dinta.

Bayan ta sanya ne ta fesa turare sannan tace “mu je..”

Zarah ta miqe suka fita.

Sossai Layla ta ji haushin yadda suka yi watsi da ita basu kula ta ba amma dai dukda haka ta sani cewar ta bata mata rai…

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

MUSTAPHA ISAH YUGUDA RESIDENCE

GWAMNA ROAD-KADUNA

Tunda suka tsaya gaban gate din gidan hankalin Ameera yayi mugun tashi… Ta sani cewar Mijin Zarah mai kudi ne amma bata taba sa ran kudin ya kai haka ba.

Bata qarasa mamaki ba sai da ta ga gate din gidan a wangale yayinda suka shiga.

Ameera ta kalli Zarah da sauri tace “Zarah ina ne nan??”

Zarah tayi murmushi tace “Kin dai san ba kidnapping dinki nayi ba ko? please feel free…”

A gaban porch tayi parking sannan suka fito. Daya daga cikin drivers din gidan ne ya rugo a guje cikin ladabi ya duqa har qasa yace “sannu da zuwa Hajiya”

Cikin fara’a Zarah tace “Yauwa Nuhu” ta miqa mishi makulli sannan ta zagaya gefen Ameera tace “Hajiya bisimillah”

Ita dai Ameera babu abinda take yi sai kalle-kalle. She is speechless ganin danqareren gida irin wannan a gaban ta.. bata taba ganin gida mai kyan wannan ba duk tsawon rayuwarta.. gashi kuma da ta gani har shiga zata yi!2

Tunda suka shiga ciki kuwa Ameera gaba daya ta zama baqauya.. duk wani abun jin dadi na more rayuwar dan Adam akwai shi a cikin gidan nan… Wasu abubuwan ma kallon su take yi bata san ko meye su ba balle ta san amfanin su.

A lokacin da suka shiga kicin kuwa gani nayi Ameera ta tsaya cak cike da mamaki… Kicin din gidan Zarah ya kusa girman rabin gidan su. Gashi komai na cikin kicin din fari da baqi.

Ita dai Ameera ta rasa wane irin aiki ne zata taimaka ma Zarah da shi domin kuwa tunda ta shiga gidan ko ina tsab-tsab ta gan shi.. Ga wani qamshi mai masifar dadi da yake ta tashi ta ko’ina.

Masu aiki ne har guda uku suna ta faman goge-goge.

Suna ganin su kuwa suka duqa har qasa suka gaishe su. Ita dai Ameera tana ta faman kalle-kalle bata bi ta kansu ba.

“Bestie qaraso mana.. akwai abubuwa dayawa da zamu yi fa”

Ameera wadda hankalinta ya dawo jikinta ne tace “toh wai da kike fadin akwai aiki dayawa yana ina?? na ga fa gidan nan is very neat.. Ga masu aikin ki nan kuma duk suna ta qoqarin kammalawa…”

“ai dama ba wannan aikin bane bestie.. abinci ne fa zamu dafa” Zarah ta fada tana murmushi.

“yanzu dama abinci ne zamu dafa shine kike ta fadin aiki dayawa??? abincin ma cin mutum daya fa..”

STORY CONTINUES BELOW

Zarah ta fashe da dariya tace “ba na mutum daya bane.. shi da abokin shi ne ZAF. if it were upto my Sweetheart abinci kala daya kawai ya ishe shi but abokin nashi ya fi son variety and guess what? each in a very small quantity”

Ameera ta riqe baki tace “ashe kuwa ki ce matar shi zata sha wahala”2

“ai dadin abun he is a great cook.. duk yawan masu aikin da ya tara a gidan shi bayada chef ko daya… haka duk yadda yake very busy a koda yaushe, da kanshi yake shiga kicin ya dafa abincin shi…” Zarah ta fadi yayinda ta nufi wani bangare da ya sada ta da wata danqararrar freezer.

Ameera wadda take biye da ita ce tace “kenan hutawa matar zata yi.. its hard to find a man who is a great cook”

“aikuwa matar ZAF ba qaramar ‘yar gata zata zama ba…”

Haka dai suka cigaba da hira yayinda suka fara shirya abinci kala-kala. Tuni sun sallami masu aikin dayake suna da nasu kicin din a quarters dinsu a can suke dafa ma duka ‘yan aikin gidan.. ita kuma ta dafa nata da na mijinta idan yana nan.

Suna cikin girke-girken su ne lokacin sallah azahar tayi suka nufi dakin Zarah suka yi sannan suka dawo suka cigaba.

Ameera dai har suka dawo kicin din dakin Zarah bai gama yi mata gizo ba a idanuwa.. Ya za’ayi mutum yana zama a irin wannan danqareren gida sannan ace yana da mugun sauqin kai kamar Zarah?? tabbas a yau ta amince ba duka masu kudi suka taru suka zama daya ba..

Abinci kala-kala suka shirya amma fa duk kadan-kadan, yawancin kalolin abincin ma Ameera bata san su ba.. Bayan sun gama ne suka zuba nasu suka nufi dinning room suka zauna.

Ameera dai tun tana mamakin komai na gidan har ta wartsake ta daina..

“Gaskiya Zarah gidan ki yana da masifar kyau.. wadanda suka qera shi sunyi qoqari sossai” cewar Ameera.

“thanks bestie… kin san City-shelters???”

“ina dai jin sunan kamfanin.. like yana da offices a Lagos, Abuja sai kuma a nan Kaduna ko??”

“Yeah… toh ai abokin shi ZAF da nake baki labarin shi shine mamallakin kamfanin”

“wow haba??!! kai amma kuwa aikin su yana kyau wallahi.. ji gidan nan for example. I swear idan ni ce a ciki sai inyi sati daya ma ban fita ba”

Zarah ta fashe da dariya tace “makarantar fa??”

“Zan haqura inyi zaman bautar aure”

Zarah ta fashe da dariya tace “you are not serious”

“amma ta ya kike kwana ke daya a cikin wannan qaton gidan?”

“tare da Sister na Fareeda.. dazu da safe kafin in zo gidan ku na sauke ta a gida.. tace wai ta san yau bani da lokacin ta tunda sweetheart zai dawo”

Ameera tayi dariya tace “aikuwa dai ta kyauta ma kanta don na tabbatar baza’a samu time dinta ba”

A haka dai suka cigaba da cin abincin su suna ta hira…

A cikin hirar ne Zarah ta ba Ameera taqaitaccen labarinta kamar haka:

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ZARAH AMINU??

Mahaifinta Babban likita ne a asibitin 44 army reference Hospital. Mahaifiyarta full house wife ce.. Fatima Zarah tana da qanne guda uku, maza biyu da mace daya. Faisal, Fareed, Fareedah. Mahaifin Zarah yana da arziki daidai gwargwado domin kuwa yana da gidan kanshi da motocin hawa..

Yaran shi kuma tunda suka taso basu nemi wani abu sun rasa ba.. Iyayen su sun tashi tsaye wurin tabbatar da yaran nasu sun samu ingantaccen ilimi na addini da boko. Sossai yaran suke da hankali da natsuwa. Zarah dai ba fara bace sannan ba baqa ba, tana da kyau amma ba irin mai daukar hankali dinnan ba. Tunda ta taso take sanya hijabi a duk lokacin da zata fita.

STORY CONTINUES BELOW

A yanzu haka shekarunta Goma sha takwas kuma duka wata biyar kenan da tayi aure. Zarah tana auren Mustapha Isa Yuguda the famous young pilot dinnan da ake alfahari da shi a qasar nan. he is one of the richest young pilots a qasar nan..

Haduwar su dai a Dalema supermarket ne watarana da suka je tare da Mummyn ta da kuma qannen ta. A lokacin yana tare da abokin shi..

Tunda ya ga Zarah ya ji kawai ta kwanta mishi a rai.. Gaba daya ya rikice ma abokin shi wanda ya kawo plan akan su bi bayan su kawai don su ga gidan su.. aikuwa haka aka yi. Ko da suka dawo ba Zarah suka nema ba, Mahaifinta suka fara gani..

Shi kam yana ganin su ya gane su. Babu wanda bai san Mustapha Isa Yuguda da Zayd Ahmad Fadoul a qasar Nigeria ba. Mustapha Isah Yuguda shahararren international pilot wanda qasar Nigeria take alfahari da shi, dan gidan Alhaji Isa Yuguda, former minister of petroleum. Zayd Ahmad Fadoul mamallakin shahararren kamfanin nan masu qera gine-gine masu kyan gaske wato City-Shelters, Yaron Ambassador A.M Fadoul wanda yayi shekara Goma yana representing qasar Saudiya a nan Royal Embassy a Abuja.

Daddyn Zarah yayi mamaki matuqa na yadda suka hadu da ‘yar shi sannan suka biyo ta har gida. A wannan lokacin kuwa sam bai yi niyyar aurar da ‘yar shi ba saboda duka shekarunta Goma sha bakwai.. Again, baya da burin hada zuri’a da Rich and powerful families irin na su Mustapha don kuwa mutane zasuyi ta magana akan sun kai ‘yar su gidan masu kudi saboda kwadayi da sauran su don haka ne ya ba Mustapha haquri.

Mustapha dai ji yayi kamar ya mutu.. shi kam idan ba Zarah ya aura ba tabbas zai samu matsala a rayuwar shi.

Abokin shi Zayd ne ya bashi shawarar kawai su turo manya don ayi ma Daddyn Zarah magana.. that way zai tabbatar lallai he is serious.

Aikuwa hakan aka yi.. Daddyn Zarah dai kwatsam sai ganin Alhaji Isa Yuguda yayi a gidan shi.. Ya zo tare da abokanen shi har guda uku. Wannan kadai ya tabbatar mishi da lallai yaron ba wasa yake yi ba.. Babu yadda zai yi dole ya haqura yayi ma Mustapha izini akan ya fara zuwa wurin Zarah amma da sharadin idan har tace bata son shi shikenan sai ya haqura.

Da farko kam Mustapha ya sha wahala da Zarah don kuwa bata son shi. Da taimakon Zayd ne suka dinga lallashin ta har ta dan fara sauraron shi.. ahankali kuwa ya fara dasa mata soyayyar shi a cikin zuciyarta.

A lokacin Mustapha ya dauki hutu mai tsawo just to win Zarah’s Love and he succeeded. Cikin qanqanin lokaci Zarah ta fada tarkon son Mustapha.. Soyayya mai qarfin gaske.

Ganin komai yana tafiya daidai ne Mustapha ya nemi izinin turo magabatan shi don ayi maganar aure.. tunda dai shi da Zarah suna son juna why wait?? he needed to have her as a wife badly. Dayake daidai ta kammala secondary school dinta ne lokacin sai kawai aka sa bikin su.

Mustapha da ‘yan uwan shi sun so ayi bikin in a grand way amma family din Zarah wanted it on a low key don haka ne aka yi bikin very simple.. Dukda haka kuwa an shaida don kuwa an batar da kudade kamar ba neman su ake yi ba. Ranar daurin aure manyan mutane a cikin qasar mu har da qasashen waje sun halarta.

Zarah bata san ko waye Mustapha ba sai da aka kai ta gidan shi.. Mustapha yana da masifar kudi. A lokacin ta gane asalin ko shi waye da irin dukiyar da ya mallaka.. Iyayen ta sun sani but still kept her in the dark.. suna so ta so shi tsakani da Allah ba don abin hannun shi ba..

Bayan bikin da kwana biyu suka bar kasar for their Honeymoon.

Tsawon watanni uku suna yawo a qasashen duniya.. Mustapha ya nuna ma Zarah soyayya. Duk abinda take so shi yake yi mata.. a dalilin zata cigaba da school shiyasa ya hana ta daukan ciki da wuri, yana so tayi adapting to school life da rayuwar aure.. tayi balancing dinsu tukun!!

Ya so tayi karatun jami’ar ta a London tunda yana yawan zuwa can din.. he flies to London more than any other country amma ta qi.. ta fi son gida kusa da iyayenta don haka ne tayi deciding ta je KASU.

Suna nan zaune a daya daga cikin gidajen shi na nan garin Kaduna wanda yake Gwamna Road

wannan kenan!!

♤♤♤♤♤♤

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *