ZABI NA CHAPTER 1 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 1 BY FADEELARH

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM

✍ZABI NA✍

☆☆☆☆☆☆

Babban abin da yake janyo wa wasu ‘yan matan rashin samun mazajen aure shine ruwan ido. Da yawan ‘yan mata yayinda suka kai wani mataki na girma, tauraruwar su na haskawa a wannan lokacin.. Hakan yana sanyawa samari su dinga tururruwar zuwa wajen yarinya don zama masoyinta na aure da wanda ba na aure ba….+

A wannan mataki ne ita budurwar take ganin ta zama tauraruwa wanda hakan ya kan sa ta ruwan ido wajen zabar masoyi na qwarai kuma na gaskiya wanda yake sonta tsakani da Allah.

‘Yan matan su kan zabi masoyi, Idan kuma suka samu wanda ya fi shi sai su canza… haka zasu yi ta canzawa har su rasa wanda za su zaba.

Rudin duniya ya kan saka idanuwansu rufewa su rasa gane ina suka dosa.

Ba wani abu bane yake janyo hakan…

illar KWADAYI da kuma SON ABIN DUNIYA shi yake kawo hakan

Wani lokacin ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu.1

Da yawa a yanzu sukan dauki buri mai girma su dorawa kansu wanda hakan ko kusa ba zai samu ba idan kuwa ya samu, toh sai an sha wuya ko kuma a same shi da sauqi qarshe a sha wahala.

Wasu sukan sakawa zuciyarsu cewa lallai sai kyakkyawan saurayi mai hanci dogo, shi ma dogo fari kamar zubin fulani irin saurayin cikin littafin Hausa.

Sai mace ta saka wa zuciyarta ita lallai sai irin wannan namijin za ta aura wanda yake ba shi da makusa kamar shi ya yi kansa.. ko kusa bazan ce ba za’a samu ba, amma kafin a samu za’a dade a ce an samu irin wanda ya hada komai ba shi da wani makusa kamar yanda na cikin littafin Hausa yake.

Wasu su kan saka wannan a ransu duk saurayin da ya zo sai su ce ba sa so saboda sun riga sun bar wa zuciyarsu wannan tsarin.

Ko kuma mace ta kudurta cewa lallai sai mai KUDI, saboda mijin qawarta ko saurayin qawarta mai kudi ne, don haka ita ma sai mai kudi ko kuma ajinta ya wuce ta auri talaka ko wanda sana’arsa ba mai girma bace irin wanda duniya za ta san da zaman sa…

Ire-iren wadannan da ma wasu ra’ayoyin nasu wadanda ban fado su ba… toh su kan sa wasu matan ruwan ido, domin ba duka ne aka taru aka zama daya ba, sai an amince wa saurayi amma da zaran wanda ya fi shi ya zo sai zance ya lalace.

Ki sani cewa yayinda kika tsaya ruwan ido za a kai ki a baro komai kyanki. Mata su kan rasa na zaba har lokacin da samarin za su daina zuwa, lokacin mace ta wuce wannan matakin da tauraruwarta take haskawa sai kuma ta dawo tana lissafa adadin samarin da ta yi tana da na sani tun a wancen lokacin ta zabi daya da ya fi mata, amma yanzu ga shi tana zaune ana aurar da qannanta tana gani.

A cikin ruwan idon wasu su kan qudurta cewa su ba za su auri mai mata ba, wani lokacin ma har iyayen su kan ba wa yaran nasu gudummowa wajen haifar da ruwan idon, yayinda aka rasa sai a dawo ana addu’ar Allah ya kawo ko da mai mata uku ne, saboda burinsu a lokacin a yi auren domin kar ‘yan unguwa su rinqa cigaba da zagi ko kuma saka ido a kowanne motsi na yarinyar.

A cewar wasu ‘yan matan zama da saurayi daya tsautsayi ne, gwara su raba qafa har Allah yasa a dace, sai dai kuma abin takaicin shi ne za ku ga wasu mazan na arziki wadanda suke da niyyar yin aure kuma sun je wajen yarinya da zuciya daya, amma ita sai ta qi amincewa da soyayyarsa ko da kuwa bashi da wani makusa a tare da shi, sai su dinga biye wa samari matasa wadanda ba su da niyyar yin aure a wannan lokacin.

STORY CONTINUES BELOW

Ina kira ga masoya musamman mata ku daina ruwan ido ku tsaya ku kula wajen zabar miji na gari, domin gudun da an sani wata rana.

Wasu mazan su kan zo wa ‘yan mata da abubuwa daban-daban don janye zuciyarta wanda a bayan auren mace za ta ga ba hakan yake ba, sai kuma ta yi da ta sani wane ta zaba. Sai a lokacin zata dinga hango halayyar wancan wanda ta bari ta yi da ta sani ta dauke shi..

DA NA SANI QEYA CE

Wata ma garin ruwan idon ta zabo wa kanta wanda kullum zai rinka jibgarta ko kuma wanda zai rinka hana ta abinci, don akwai masu kudin da ba sa iya fitarwa cikin gidansu, ba sa ba wa iyalansu komai sai dai a dinga gyara ginin gida ko shi ya yi dinki yana canjawa ana Alhaji wane mai kudi ne amma fa cikin gidansa iyalai na kuka..

‘yan mata sai a kiyaye.

Haka zalika, akwai namijin da za ki dade da shi don gayunsa, amma bayan an yi aure sai lamari ya canja wannan dan tsukewar da yake yi yana janyo zuciyarki sai ki ga duk ba hakan yake ba.. sai zai fita yake samun daman yin wanka ma in har ba zai fita ba, to ba shi ba wanka. Kin ga ba labari domin kuwa lamari ya baci, sai a kula don gudun da an sani an zabi mai shigar kamala wanda yake sako ta-zarce ana kushe shi ana cewa bai waye ba.

Ruwan ido ya kan korar wa da mace samari, a qarshe ta zo tana da ta sani.

Masoya sai a kula a dinga danne zuciya a nutsu a yi aiki da hankali wajen zabar mijin aure don kar a yi zaben tumun dare.

☆☆☆☆☆☆☆

☆☆☆☆☆☆

✍ZABI NA✍

Labari ne da ya qunshi abubuwa da dama.. Labarin LAYLA FAROUQ, AMEERA FAROUQ da Kuma ZAYD MUHAMMAD

********

LAYLA FAROUQ da AMEERA FAROUQ mahaifin su daya amma Uwa kowa da tata.. Mahaifin su ba mai arziki bane don kuwa zamu iya cewa talaka ne..

Gidan su gida ne da ake samun rashin zaman lafiya from time to time…

LAYLA FAROUQ: Kyakyawar gaske wadda kallo daya zaka yi mata ka tabbatar da hakan.. samun mace mai kyan ta sai an tona.. fara sol mai dogon gashi.. Qarya da kwadayin abin duniya su ta sa a gaba.. Burinta shine tayi qawance da yaran masu kudi sannan ta auri mai kudi…

ZAYD MUHAMMAD: Dan kyakyawan saurayi, fari sol tamkar balarabe wanda bashi da komai sai dan abin rufin asirin shi.. Allah ya jarabce shi da son Layla… Ji yake yi idan bai same ta ba lallai zai iya rasa ran shi… LAYLA itace Zabin shi..

AMEERA FAROUQ: Baqa ce sannan sai ka kalle ta da kyau zaka hango kyanta domin kuwa boyayyen kyau gare ta.. Yarinya mai haquri, hankali da natsuwa.. Yarinyar da ta ajiye kanta a matsayin da Allah ya ajiye ta.. A duk duniya babu wanda take so sama da ZAYD MUHAMMAD amma kash zuciyarshi tana wurin ‘yar uwarta

☆☆☆☆☆

Hausawa sun ce:

KWADAYI mabudin wahala

QARYA fure take bata ‘ya’ya

DA-NA-SANI qeya ce

Sannan dan hakkin da ka raina shi yake tsone maka ido..

☆☆☆☆☆☆☆

Lallai da ace kyau, hali nagari da Soyayyar Gaskiya LAYLA FAROUQ take nema toh tabbas zata zabi ZAYD MUHAMMAD amma inaaa… Abinda take so sune KUDI kuma baya da su, baya da hanyar samun su don haka bazata taba amince ma hopeless talaka ba kamar shi..

Tabbas duk yadda ka kai ga jure wulaqancin da ake yi maka akwai laifin da za’a yi maka wanda is unforgivable, wanda zai sa ka tsani wannan mutumin/abun ka haqura da wannan mutumin/abun har abada.. Hakan ne ya faru da ZAYD MUHAMMAD. Lokaci guda ya tsani LAYLA FAROUQ sannan ya karkata zuwa ga qanwarta wadda ta tsana a duk fadin duniyan nan AMEERA FAROUQ

A wannan lokacin ne abubuwa da yawa suka faru.. Abubuwa da dama suka bayyana sannan komai ya canza.

Lokaci guda aka wayi gari LAYLA ta shiga yaqi da AMEERA akan soyayyar ZAYD

“ihu bayan hari”

Shin tambaya anan:1

Meye dalilin ZAYD na koma ma AMEERA??

Don ya rama abinda LAYLA tayi mishi ne ko kuwa Soyayyar gaskiya yake yi ma AMEERA??2

Me yasa LALYA ta canza ra’ayinta a game da ZAYD??6

Shin Soyayyar da ta dawo tana yi mishi ta tsakani da Allah ce ko kuwa??2

Tsakanin AMEERA da LAYLA wacece zatayi nasarar zama gimbiyar ZAYD??4

Is this a game of LOVE???4

Shin ya kuka gani???

Labarin zai bada ma’ana ko kuwa???9

☆☆☆☆☆

Assalam my people!!

Dee is back… Yeeeey!!!

Actually UMMI was supposed to be my last but then, My loyal fans kept putting pressure on me and here I am with a short story…9

the question now is:

Will I ever be done writing on this platform???

Well, ZABI NA gajeren labari ne wanda ya qunshi abubuwa da dama…

Important Life lessons to be learnt in this story Insha Allah!!

☆☆☆☆☆

AUTHOR’S NOTE

Masu karatu ina roqon ku don Allah idan kun san bazaku yi VOTING ko COMMENTING ba don Allah kar ku karanta..

Gwara in ga 50reads, 50votes and 50comments instead of 500reads, 5votes and 0comments

Kar ku kasance cikin mugaye da munafukai.. YES….

Munafinci ne da mugunta ace mutum zai karanta labarin ka salin-alin sannan ya qi appreciating..4

I wont hesitate to drop this story idan ban samu support dinku ba..

Take it as a threat/warning..

whichever suits you but it’s the plain truth..

Remember I didn’t ask any one of you for a single dime in order to have access to reading my stories..

duk kyauta ne…

toh muguntar kuma daga ina???

Ina fatan zan samu hadin kan ku daga farko har zuwa qarshen wannan tafiyar!!GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI-KADUNA+

Kwance take a kan gadon ta wuraren qarfe takwas da rabi na dare riqe da wayarta qirar Tecno torchlight tana buga game.

Ibrahim qaninta ne ya shigo dakin da gudu ya fada kan gadonta yayinda yake sauke numfashi.

Fadowar da yayi mata kan gadon ya razana ta sossai wanda har sai da wayar hannunta ta kufce mata.

“wai kai wane irin mahaukaci ne Ibrahim?? sau nawa zan ce maka ka daina fado mun haka???” ta fada cike da tsananin bacin rai.

“Ya Layla don Allah kiyi haquri.. dama fa Ya Zayd ne ya zo shine yace in kira ki”

Tsaki ta ja sannan ta janyo wayarta ta koma ta kwanta tare da fadin “je kace mishi bana nan..”

“Ya Layla kin tabbata??? na ga wata leda fa a hannun shi”

Da sauri ta kalli Ibrahim tace “dagaske??? babba ce ko qarama?”1

Ibrahim yana murmushi yace “gaskiya ba qarama bace.. amma kuma tunda kince in ce mishi bakya nan..”

Duka ta kai mishi a kafada tace “qaniyar ka dan banzan yaro… kace ina zuwa”

Ibrahim yana dariya yace “Allah ya shirye ki Ya Layla..” yayinda ya sauka ya ruga a guje ya bar dakin don ya san halinta.

Layla kuwa bata bi ta kanshi ba ta sauka daga kan gadon tana fadin “finally yayi abun arziki.. ashe shiyasa yake ta kirana a waya. yau kusan kwana nawa kenan ina fama da kai ka kawo mun atamfar anko ka kasa.. mtseeew”

Gaban madubin dakin ta nufa ta tsaya tana kallon fuskarta…

“ace yadda nake da kyau da jiki mai kyau ina fama da qananan samari wadanda basu da ko sisi.. gaskiya dole in tashi tsaye. I need someone with money and class don wallahi ni Layla ba kalar talaka bace..”1

Tsaki ta ja sannan ta gyara fuskarta ta fesa turare. Ran ta a bace tace “haka kawai mutum yana asarar turaren shi a banza.. sai dai ka zo ka baza hanci ka shaqa amma baka iya kawo ma mutum”

Sanye take cikin doguwar rigar atamfa dinkin fitted gown wadda ta bala’in yi mata kyau.. gaba daya qirarta ta bayyana a cikin rigar. Sossai tayi kyau kamar ka sure ta ka arta a guje.

Wadrobe dinta ta bude ta zaro gyale kalan atamfar jikinta sannan ta yafa shi a kanta.

Layla bata son daura dan kwali a kanta.. abinda kadai take qoqarin sakawa shine hula. Idan zata fita kuwa gyale take yafawa a kai abinta.

Komawa tayi wurin gadonta ta dauki wayarta sannan ta fita.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune yake a kan dakalin qofar gidan su yana jiran fitowarta.

Sanye yake cikin doguwar Jallabiya fara sol wadda ta bala’in dacewa da kalar fatar shi.. Gashin shi baqi qirin mai laushin gaske ya kwanta luf-luf a saman kan shi da fuskar shi.. kyakyawan mutum tamkar balarabe.. Kamar shi yayi kanshi saboda tsananin kyau..

Zayd dai tun bayan sallar Isha’i ya iso qofar gidan. Yana ta kiran wayarta amma bata amsa ba. Gashi ya buga gate din gidan babu wanda ya ji tunda dai ba mai gadi keda akwai ba a gidan.

STORY CONTINUES BELOW

Yana nan zaune yana ta kiran ta a waya ne Ibrahim ya fito da niyyar zuwa aike don haka ne ya tura shi ya kira mishi ita.

Yana nan zaune ya ji qarar gate wanda ya sanya shi saurin dago kanshi..

Layla ce ta fito fuskarta a murtuke amma fa hakan bai hana ta yin kyau ba. Tunda ta fito kuwa ya sa mata idanuwa.. Allah ya sani Zayd yana masifar son Layla, baya jin ya taba son mallakar wani abu a duniya sama da ita.

“wannan kallon kuma ai sai ka sa in fadi..” ta fada yayinda ta samu wuri a gefen shi ta zauna.

Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba.

Ita dai Layla tana mamakin halin Zayd.. Talaka da shi amma sai isa da miskillanci.

“Kinyi kyau sossai shiyasa nake kallon ki.. Allah ya nuna mun ranar da zaki zama mata a gareni” ya fada cikin muryar shi mai dadin gaske.

Wani lokacin idan yana magana sai yayi tamkar ya hada jini da larabawa.. his looks even supports the fact!!

“aikuwa dai da saura.. don sai ka samo kudi”

Murmushi yayi yace “Allah zai kawo”

“kullum dai haka kake fadi..” ta kalli ledar da ke gefen shi tace “Ka siyo mun ankon nawa ne??? dan bani in gani”

Zayd ya janyo ledar ya miqa mata. Shi kam ya saba da halin Layla.. An ce so hana ganin laifi, duk wulaqancin da Layla take yi ma Zayd baya damuwa domin kuwa a dalilin bala’in son da yake yi mata zai iya jure duk wani bacin ran da zata sanya shi. Burin shi shine Layla ta so shi ko da rabin yadda yake sonta ne.. Shin hakan abu ne mai yiwuwa???

“ban gane ba.. wannan fa roba-roba ce. Haka muka yi da kai??? ba nace maka Chiganvy wax nake so ba??” ta fada yayinda take kallon shi a wulaqance.

“kiyi haquri don Allah.. kudin da na sa ran samu ne basu shigo ba shiyasa na siyo miki wannan din. Na ga kuma design din iri daya sannan kala daya ai babu wanda zai gane”

Tsaki tayi tace “wa ya fadi maka baza’a gane ba?? Wallahi babu wanda bai san roba-roba ba.. ni kam da ka sani ma da baka siya ba”

“toh ki kawo in mayar idan na samu kudi kafin bikin sai in..”

Kafin ya qarasa maganar shi tace “ka mayar kuma?? ai da babu gwara ba dadi..”

Girgiza kai kawai yayi ba tare da yace komai ba.

Shiru ya dan ratsa yayinda take ta latse-latse a waya.

“Yaushe zaki fara zuwa school din??”

Ba tare da ta kalle shi ba tace “next week ne..”

“Allah ya kai mu.. Allah ya bani ikon gyara mashin dina kafin lokacin sai in dinga kai ki ina dauko ki..”

Da sauri ta kalle shi cike da mamaki.

Lallai ma ta je KASU a kan mashin.. ai bazai taba faruwa ba.. ita kam tana shiga KASU zatayi mingling da yaran masu kudi ko Allah zai sa ta hadu da saurayi mai kudi..

“a’a wallahi na hutashe ka.. muna da mai adaidaita da yake kaimu school na ji Abba yace shine zai cigaba da kai mu cikin rufin asiri.. kai kam ka dai yi qoqari ko mota mai qofa daya ce ka siyo”

“Baby idan na samu irin wannan kudin ba gwara nayi hidimar bikin mu da su ba??”

Murmushin takaici tayi tace “tab.. wallahi Zayd baka shirya aurena ba kuwa”

“Baby na kusa shiryawa insha Allah.. idan dai akwai so da qauna a tsakanin mu ai ina ganin komai zai zo mana cikin sauqi”

“Hmm.. toh so da qauna shi zamu ci???”

Kafin ya amsa ne wayar shi ta fara ringing..

Gani nayi ya zaro Nokia torchlight daga aljihun jallabiyar shi yayinda ya kalli mai kiran nashi.. maimakon yayi answering sai yayi rejecting.

Layla ce tace “hala budurwar ka ce take kira shine zaka wani yi rejecting..”

Murmushi yayi yace “are you jealous??”

Hararar shi tayi tace “Ni?? Allah ya kiyaye.. akan me??”

Kafin yayi magana ne wayar ta qara ringing.. gani nayi ya runtse idanuwa ya bude sannan yayi answering.

“Ok ina zuwa..” abinda ya fada kenan sannan ya miqe tare da fadin “Baby bari in je ana nema na.. wani dan uwan mu ne ya samu matsala.. bari in je in ji”

Miqewa tayi tace “toh.. ka gaida gida”

Zayd ya girgiza kai yana mamakin halin Layla.. he expected her to sympathise with him jin cewar akwai matsala da ta samu dan uwan shi amma sam bata ko nuna damuwa ba.

“toh Good night.. I love you”

Ba tare da tace komai ba ta juya ta shiga gida abinta.. a ranta tana fadin “ka ji da shi dai..”

Zayd dai bai bar wurin ba har sai da ta shige gida.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “I pray you reciprocate my love soon Layla..”

☆☆☆☆☆☆☆☆

Duqe take a dakin su tana gyara gadonta cikin natsuwa yayinda take ta yin waqar India.

Wannan ita ce al’adar Ameera, a kullum idan tana aiki zaka ji tana waqar India.. Sossai take qaunar Indian films, Soyayyar su tana matuqar birge ta.

Layla ce ta shigo dakin cikin masifa tana fadin “Haka kawai ka zo ka bata ma mutum lokaci a banza.. Ni wallahi na gaji da irin wadannan samarin wadanda bazasu iya baka komai ba”

“Ledar hannun ki yanzu wa ya baki ita??” cewar Ameera wadda take ta kallonta tun lokacin da ta shigo.

Jefar da ledan tayi akan gado sannan tace “wata shegiyar roba-roba ce ya kawo mun..”

Ameera ta girgiza kai tace “haba Ya Layla, ai babu laifi yayi qoqari.. kar ki manta iyakan qarfin shi kenan.. wallahi na tabbatar da Ya Zayd yana da hali zaiyi miki fiye da hakan..”

Layla ta dalla mata harara tare da fadin “ke don Allah tafi can.. ke dama baki iya magana ba.. iyakan qarfin shi kenan ko kuma lalata?? ba yayi karatu ba??? ya fita ya nemi aiki mai kyau mana ya samu kudi.. ya tsaya yana ta buga-buga. Ni wallahi na kusa rabuwa da shi ma.. bari ki gani mu fara zuwa KASU.. I swear levels go change”

“Hmm.. ki dai bi ahankali Ya Layla… wallahi samun masoyi irin Ya Zayd sai an tona don haka ki..”

“Mtseeeew… Zancen banza. don Allah kiyi mun shiru kafin in bata miki rai… ban ma san uban da ya sa ni yi miki magana ba. Ni na rasa meyasa bai maqale miki ba wallahi.. Tunda ke baki gaji da harkar talauci ba kun yi daidai.. sai ki je kuyi ta gurzawa” cewar Layla yayinda ta dalla mata harara ta wuce kewaye su.

Ameera ta bi ta da idanuwa sannan tace “how I wish ni yace yana so.. da nayi treating dinshi tamkar sarki. Ya Zayd shine ZABI NA, Allah ma ya sani ina bala’in son shi..”3

♤♤♤♤♤

Mun ga LAYLA

Mun ga ZAYD

Mun ga AMEERA

hali kowa da irin nashi.. haka ZABI kowa da nashi!!

Ya kuke ganin tafiyar tasu zata kasance??WAIWAYE….+

Malam Farouq Abdallah ya kasance mutumin Kano ne. Mahaifin shi Malam Abdallah baya da qarfi sossai don kuwa sana’ar trader yayi a wata kasuwa ta kusa da su. Asali Iyayen Abdallah sun haifi yara guda hudu ne.. Farouq shine babba kuma shi kadai ne namiji. Sauran duk Mata ne: Aminatu, Khadeeja da Zainab.2

Farouq shi kadai ya samu zuwa makaranta domin kuwa Mahaifin su baya da halin biyan kudin makaranta.

Shi kanshi Farouq din sai da ya hada da aikin qarfi wanda anan yake samun ‘yan kudaden da yake hadawa ya biya kudin makarantar shi.

Yayi karatun primary da secondary dinshi a nan cikin garin Kano. Daga nan ya wuce BUK inda yayi karatun jami’ar shi.. Ya karanta Economics ne a bangaren Education.

A wannan lokacin kuwa tuni qannen shi sunyi aure.

Aminatu tana gidan mijinta a Sokoto sai Khadeeja da Zainab suna aure a nan cikin garin Kano.

Bayan Farouq ya kammala karatun jami’ar shi ne ya fara neman aiki.. Kamar dai yadda kuka sani samun aiki a qasar mu abu ne mai wahala musamman idan baka san kowa ba.. Ga mahaifin su ya tsufa.. sana’ar trader din ma Farouq ne yake dan taimaka mishi yana zama a shagon.

A haka ne har Allah ya taimake shi ya samu aikin teaching a wata makarantar private a nan cikin unguwan su.. Dukda dai albashin babu yawa…

Dayake Farouq yana da qoqarin neman na kan shi bai yi sanya ba wurin cigaba da neman aiki.. A hakan ma idan an tashi daga makarantar yana zuwa koyar da wasu yara lesson a gida da yamma.

Sai da yayi kusan shekara daya da rabi yana koyarwa a makarantar private din wata rana kwatsam sai aka aiko mishi da letter daga Garin Kaduna cewar an dauke shi aiki a State ministry of Education ta Kaduna.

Farouq yayi murna sossai da samun wannan aiki. Ai kuwa nan da nan ya tafi Kaduna yayi documentation dinshi gaba daya sannan ya dawo Kano yayi resigning a private school din da yake teaching.. Inda Allah ya taimake shi dama wata saura kwana biyu ya qare don haka suka yi mishi alqawarin zasu biya shi salary din dukda a qa’idance shi yakamata ya biya su albashin wata daya in lieu of notice kamar yadda yake a rubuce toh amma Farouq was a hardworking teacher and the least they could do was pay him as gratitude..

Bayan dan lokaci kuwa Farouq ya tattara tsab yayi sallama da iyayen shi ya koma garin Kaduna.

Dayake akwai sabbin gidaje da gwamnati ta gina tana raba ma ma’aikatan ta masu so sai kawai ya karbi daya wanda a cikin albashin shi za’a dinga cire wani percentage har tsawon shekarun da zai gama biya ya mallaki gidan.

A wannan lokacin kuwa Farouq ya so iyayen shi su dawo gidan nashi su zauna tare amma Sam suka qi. A cewar su tunda dai gidan da suke ciki nasu ne gwara suyi zaman su.. Shawara suka bashi akan lallai ya fitar da mata yayi aure… tunda dama muhalli shine babban matsala kuma ya samu.. Da wannan ne kuwa Farouq ya fitar da yarinyar da ya dade yana nema.

Hindatu yarinya kyakyawar gaske.. Asalin Mahaifinta dan Kano ne amma mahaifiyarta ‘yar Qasar Niger ce…

Hindatu Fara sol mai dogon gashi.. tana da jiki mai kyau… Gaba daya ta dauko Kamarnin mahaifiyarya. Tunda Hindatu ta taso ta ga tana da kyau ne take masifar ji da kanta.. Girman kai gareta na bala’i.

STORY CONTINUES BELOW

Tun lokacin da Farouq ya qyallara idanuwan shi a kanta kuwa ya ji yana masifar son ta. Ya sha wahala sossai kafin ta fara sauraron shi don kuwa ko alama bata so tayi tarayya da talaka.. A dalilin dan abin hannun da yake riqo mata ne ya sanya ta fara sauraron shi.

A lokacin da ta ji labarin Farouq ya samu aiki a Kaduna harda gida an bashi ne ta zama serious a kan shi.. Ko da yace zai fito tuni ta bashi go ahead. Ita dai murna take yi zata shiga birni kuma dai dama duk cikin samarinta babu wani na arziki har gwara shi din gashi dama ba makaranta take zuwa ba balle… zaman banza kawai take yi.

Nan da nan kuwa aka gabatar da juna sannan aka sanya ranar biki. A kwana a tashi babu wuya har aka sha biki aka kai amarya Hindatu gidan mijinta a Malali cikin garin Kaduna.

Hindatu dai tunda ta shigo unguwar babu gidan da bata leqa ba a layin su.. Tuni ta qulla zumunci da yawanci matan da suke zaune a layin.. yawanci duk masu hasken take shiri da su. Ita dama bata son talakan mutum. Babu abinda ta sa a gaba banda Qarya da son abin duniya.

Harda adashe ta shiga Wanda ake zubin naira dubu Uku sannan a kwashi dubu talatin a qarshen wata. Yawanci wadannan matan suna ‘yan sana’o’in su shiyasa basu da matsala.. ita kuwa Hindatu bata sana’ar komai.. rigima ce kawai.

Tunda suka yi aure Farouq ya dage mata akan ta fadi sana’ar da take son yi ya bata jari amma tace ita babu abinda zata yi… A kullum aikinta ‘bani-bani’

Adashen ma babu shiri duk qarshen wata Farouq ne yake bata dubu ukun da take yin zubi.

A watan su na biyu da yin aure ne ta samu ciki.. Sossai Farouq yayi murna. Haka can gida a garin Kano iyayen su sunyi murna tare da fatan Allah ya sauke ta lafiya.

Tunda ta samu cikin nan kuwa take wahalar da Farouq.. daga yau tace zata ci qwan zabi sai gobe tace zata ci kaza.. Haka dai yake iya qoqarin shi yana bata kulawan da ya dace.

A haka har cikinta ya shiga wata takwas.. hakan yayi daidai da watan da zata kwashi adashen ta..

Dama burin Hindatu ta kece raini cikin qawayen ta ranar suna idan ta haihu don haka bata yi sanya ba ta nufi kasuwa ta siyo atamfar super wax dinta tare da wata qaramar atamfa (a lokacin super no expensive like now… lol)3

Dayake Farouq ya siyo mata wani leshi mai kyau da wata qaramar atamfa aikuwa sai ta hada su ta bayar dinki.

A lokacin da cikinta ya kai wata tara daidai ne ta haihu ‘yarta mace fara sol mai kamar ta sak. murna wurin Farouq ba’a magana… tuni yayi ma yarinyar huduba da suna Layla. Farouq dai tun yana qarami yake son wannan sunan.. dama yayi alqawarin duk lokacin da ya samu ‘ya sai ya sanya mata sunan.

Iyayen Hindatu sun so ta koma gida wankan jego amma sam ta qi.. a cewarta ta fi so ta zauna a nan Kaduna saboda tana so tayi taron suna a gidan ta ba don komai ba sai don kwadayin abinda za’a kawo mata wanda idan ta tafi Kano ba lallai bane wasu su bata. Babu shiri kuwa mahaifiyarta ta zo Kaduna ta zauna da ita saboda kula da ita da ‘yarta.

Ana gobe suna ne qannen Farouq su ma suka iso.. Farouq dai ya siyo Ragon shi dan madaidaici wanda za’a yanka ma Layla. Haka duk wani abinda za’a buqata na hidimar suna duk ya tanada daidai qarfin shi.

Ranar suna kuwa mai jego ta fito ta kece raini.. tayi shiga kala hudu yayinda aka dinga yabawa.. dama dai abinda take so kenan. Haka aka dinga kawo mata atamfofi da kayan jarirai, sabulai, omo, Pampers da sauran su.

Sossai mahaifiyar ta da qannen Farouq suka yi mamakin yadda ta san jama’a dayawa a garin Kaduna a dan qanqanin lokaci..

Haka akayi taron suna aka watse yayinda mahaifiyarta da qannen Farouq suka koma gida. Akwai wata ungwozoman da take zuwa tana yi ma Layla wanka har zuwa lokacin da zata yi arba’in.

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin da Layla tayi arba’in ne suka tafi Kano ganin gida.. Sossai kakaninta suka yi murnar ganin jikan su.. dama tunda aka haife ta basu je ba.. wai saboda kara. Sai da suka yi sati daya sannan suka dawo Kaduna.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya.. Hindatu sai qara shigewa take yi cikin masu arziki. Layla kuwa tana ta wayau. Shi kuwa Farouq duk wata buqata tasu yana qoqarin biya musu ita.. Kudaden da yake samu har iyayen shi da qannen su da suke gidan mazajen su yakan aika musu su sa albarka.

☆☆☆☆☆☆

A lokacin da Layla take wata tara ne wani abokin aikin Farouq ya rasu.

Malam Abubakar dai ya kasance mutumin kirki a lokacin yana raye.. Tunda suka hadu suka qulla aminta da juna.. Duka shekara daya kenan da yayi aure.. Ya auri wata marainiyar Allah mai suna Sameera.

Sameera yarinya mai hankali da natsuwa. Ko bayan bikin su da Hindatu ta kula yarinyar ba wata wayayya bace sai bata qulla zumunci da ita ba.. Farouq yayi da ita su qulla zumunci amma Sam ta qi.. Ita dai Sameera takan je gidan Hindatu wanda har ta qarashi zamanta ta tashi ba wata maganar kirki suke yi ba. Ita ma Sameera a dalilin mijinta yana matsa mata ta je ne ya sanya take zuwa.

Malam Abubakar ya rasu a sandiyyar hatsarin mota da suka yi akan hanyar su ta dawowa daga Abuja inda yake daya daga cikin wadanda suka wakilci Kaduna state a wani taro da aka yi.

Sossai hankalin abokin shi Farouq da matar shi Sameera suka tashi.. Sameera har suma ta dinga yi domin kuwa batada kowa sama da Abubakar a duniyan nan.. she had no one because she was an orphan. Dama a hannun Limamin unguwan su ta girma wanda bayan wata biyu da yin bikinta ya rasu.

Malam Abubakar ya rasu ya bar iyayen shi da qanne shiyasa ko da aka zo rabon gado ba wani abun arziki Sameera ta samu ba.. Dayake bai yi nisa ba a biyan kudin gidan da yake ciki sai gwamnati ta mayar ma iyayen shi da kudin shi wanda aka hada aka raba gado.

Sameera kuma gwamnati ta bata wata uku har ta gama iddah kafin ta samu wuri ta koma. Farouq shine yayi shige da ficen da ya samar mata wannan alfarmar. sossai ta gode mishi.. tabbas shi kadai yake kula da ita tun bayan rasuwar mijinta. Farouq shi ya cigaba da ciyar da ita yana biya mata dukkanin buqatun ta.

A kwana a tashi babu wuya Sameera ta gama Iddah.. kwana daya da fitowarta kuwa Farouq ya je gidan musamman don yin muhimmiyar magana da ita.

Farouq ya sani sarai Sameera batada wurin zuwa sannan bazai taba so ya ga ta wulaqanta ba domin kuwa sunyi zama na amana da mijinta Allah ya jiqan shi. Abinda zai iya yi ma Sameera shine ya kula da ita.. hakan kuma zai yiwu ne idan ya aure ta.

Tabbas Farouq bayada burin auren mata biyu tunda ba wani qarfi gareshi ba toh amma ya zai yi da Sameera???

Ko da ya gabatar mata da maganar son aurenta qin amincewa tayi domin kuwa ta fahimci cewar Hindatu ba mutumiyar arziki bace.. A lokacin da take matar abokinshi ma ta wulaqanta ta balle idan ta zama kishiyarta..

Ita dai bata iya fada da tashin hankali ba don haka ne ta qi amincewa.

Farouq dai da magiya da wa’azi ya lallashe ta har ta amince.

Musamman ya tafi Kano ya sanar da iyayen shi buqatar shi na son qara aure.. Iyayen nashi sun amince a dalilin bayanin da yayi musu na halin da Sameera take ciki da wanda zata iya shiga a nan gaba.

A lokacin da wannan maganar ta shiga kunnuwan Hindatu kuwa ta tayar da bala’i. Sossai ta haukace yayinda ta dinga fada tana zage-zage. Farouq dai duka ne kawai bata yi mishi ba amma cin mutunci iri-iri ta dinga yi mishi.. A tunanin ta zai gaji ya fasa auren.. Ganin lokacin biki yana ta gabatowa ne ta tattara kayanta ta dauko Layla ta bar gidan.. Farouq dai a ranar sai dawowa yayi ya tarar tayi tafiyarta.

Farouq ya sani cewar Hindatu tana da masifa da kishi.. ya kuma sani cewar idan ta huce zata sauko don haka ne tunda ya kira waya aka sanar da shi tana Kano sai yayi watsi da al’amarinta.

A haka har aka daura auren Farouq da Sameera ta tare a gidan mijinta.

Dayake gidan daki biyu ne sai ya ba Sameera daya yayinda dayan ya kasance na Hindatu. Yayi planning qara dakuna biyu zuwa uku a gidan tunda akwai fili mai girma a tsakar gidan sannan yau da gobe dole ne zai hayayyafa wanda hakan yana nufin buqatar more rooms a gidan.

Amarya Sameera dai sossai take kyautata ma mijinta.. tana yi mishi biyayya sannan tana kaffa-kaffa da duk wani abu nashi.. Sossai Farouq yake alfahari da ita domin kuwa abubuwan da take yi mishi na kyautatawa ko rabin su Hindatu bata yi mishi.

Sameera dai ta kasance tana da ciwon asthma wanda yake tashi mata lokaci-lokaci.. tana shan wahala sossai a duk lokacin da ta tashi. tana amfani da inhaler a duk lokacin da ta taso mata wanda da taimakon Allah har take samu ta sauka.. ita kam ta sanya a ranta ciwon asthma nan shi zai kai ta lahira watarana domin kuwa ita kadai ta san yadda take ji idan ta taso mata.. Ko maqiyin ta bata fata ya gamu da wannan ciwon.

Tunda Sameera ta shigo gidan daidai da rana daya bata taba tambayar Farouq kudi ba.. haka idan ya bata sai tace ya ajiye ya qara a cefane.. hakan ba qaramin mamaki yake bashi ba.. She is so different from Hindatu. A kullum yana cikin sanya mata albarka.

Hindatu dai ganin Farouq ya fita batun ta sannan gidan nasu ba wani dadi ke da akwai ba kamar gidan Farouq din ne ta ga lallai gwara ta koma.. in ya so sai ta wulaqanta Sameera har ta gaji ta bar gidan.

Aikuwa nan da nan ta tattara kayanta ta koma Kaduna.

Tun daga ranar da ta dawo kuwa aka yi sallama da kwanciyar hankali a gidan. Kullum Hindatu tana cikin bala’i da masifa, Kullum tana cikin yi Mata gori akan ita ta fi ta komai- Kyau, jiki mai kyau, haske da sauran su.

Sameera dai ko kadan bata biye mata… ta sani cewar Allah da ya halicce su shi ya ga daman yin hakan kuma yake so ya gan su a haka, da alama Hindatu bata da cikakken sani na addinin mu.

A kullum aikin Sameera shine HAQURI.

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *