YAR NAJERIYA CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR 

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Hasna’u na shiga gida kai tsaye bangaren su ta nufa da sassarfar ta, Hajjo matar Kawu na zaune kofar dakin ta tana kallon ta ta shige bata ce mata komai ba, kayan ta da aka shigo da su duk Hajjo ta sa an tule mata a kofar dakin Innar ta. Don ma kada a fara cewa a dakin ta zata zauna.

Tun daga kofar sassan take kwada sallama tana fadin.

“Inna kina kusa? Inna gani na dawo!”

Ta sa kai a rumfar, duhu dudum, ya bakunci idanun ta, Inna bata kunna aci-bal-bal da ta saba kunnawa ba, ko mai yasa?.

“Inna lafiya kike zaune cikin duhu haka? Wai kina ina ne ko gyaran murya bazaki min ba in sallah kike yi?”

Ta fada tana lalube a cikin dakin. Sai ta jiyo gyaran muryar Kawu daga bayan ta, yana haska tocilan yana tahowa. Yace “Hansai dakko kayan ki ki biyo ni” cikin damuwa tace “Kawu ina Inna ne? Ko bayi ta zaga?” Kawu yayi gaba bai kula ta ba, sai ta bishi da gudu-gudu cikin alamu na fara shiga rudu, har ta riga shi shiga dakin nasa. Saura kadan ta bangaje shi.

Ya zauna yana haska ‘light blue eyes’ din ta wadanda sai sheki suke yi kamar idon mussa (mage) yace. “Zauna Hansai ki bani hankalin ki kin ji? Hakika Ubangiji baya dorawa rai abinda ya san bazata iya dauka ba. Ya san ZAKI IYA! Shi yasa ya dora miki”.

Hasna’u ta fiddo iyakacin ‘yan kananun idanun ta da iyakacin girman su tana kallon Kawu Sama’ila. Ya cigaba dacewa “Kullu nafsin za’ikatul maut, daga ni har ke bamu tsira ba, jiran ta muke yanzu ne? Gobe ne? Anjima ne? Tana tafe bazamu taba iya guje mata ba sai fa in lokaci bai buga ba”.

Hasna’u dai kallon sa take tana jiran ta ji karshen wannan wa’azi da bata ga dalilin sa ba. Daga tambayar sa ina Inna? Kawu yacigaba da jawo aya da hadisi yana fassarawa akan muhimmancin yarda da hukuncin Ubangiji mai dadi ko mara dadi wajibi ne ga dukkan musulmi. Wanda ya yarda Allah shine mai bayarwa kuma mai karba a duk sanda ya so. Ya kasa fitowa fili ya fadi maganar dake kunshe a bakin sa, sai dawurwura yake, a ran sa yana fadin “da na sani na shigo tare da Sahabi, na ga ya fini kaifin harshe”, ita kuma bata katse hanzarin sa ba sai da ya rasa sauran hadisin fade sannan ya nisa….

Ya ce “Hansai Zulai ta sha jinya ta wata biyu, masassara ta kwantar da ita, ba irin maganin da ban sayo mata ba, an yi jike-jike har ba adadi a karshe na kaita asibiti a birni.

Kwanan mu biyu da dawowa daga asibiti jikin ya dan yi kyau, kuma likita ya ce tayifot ce ta kama mata hanji, an dora ta akan gwaje-gwajen da suka dace, kafin akai ga yi, da safe na shiga don in kai mata koko, sai gani na yi rai ya yi halin sa…”.

Hasna’u ta runtse idanun ta kafin ta ce.

“Kawu menene rai yayi halin sa?”

Yace “halin sa na bakon kan hanya mana! Ya tafi inda aka turo shi, ta rasu!”

Zai cigaba da wa’azi sai gani yayi Hasna’u ta mike ta fita da gudun gaske, dakin su ta koma tana lalube tana kiran sunan Inna! Da iyakacin muryar ta. Da iyakcin makogaron ta. Wanda hakan ya janyo hankalin al’ummar gidan duka aka taho sassan. Kawu ya zo ya kamata  ganin tana buga kanta da bango har goshin ta ya fashe. Yace “Hansai kice “Innalillahi wainna ilaihi rajioun…. Kada Allah yayi fushi da ke”. Ina! Hasna bata ji me yake cewa ba, jinni ke fita daga goshin ta a lokacin.  Duk da cewa fatar zabiya tana da karfi amma ta buga kan sosai da bango hoping itama Allah ya dauki ranta kafin abinda Kawu ke fada ya zama tabbatacce. Kawu ya rike ta tamau yana ta ambata mata.

“Ina lillahi wainna ilaihi rajioun…. ” Bai gushe yana yi ba sai da ya ji ta kama. Kuma bai saketa ba, sai da ta sulale da kanta ta yi kasa.

Koda ya duba sai gane bata numfashi, Hajjo tace “Hassan maza kawo ruwa kada ‘yar ma ta mace mu shiga uku” Hassan yace “Hajjo don Allah ku bar ta ta karasa, kowa ya huta, in ta rayu me zata yi mana banda karawa Baba nauyi? A bar shi ya ji da mu,  mu lafiyayyu da muka zame masa dole, ku barta tabi Uwar ta”. Kawu ya saki Hasna’u yayi kan Hassan da mugun duka Hassan ya gudu, Kawu ya fadi, sabida babbar rigar sa da ta tadiye shi, ya bugu sosai, Hajjo ta ce.

“Oh ni Hajjo! Duk akan zabiya zaka hallaka kan ka? To wallahi ‘ya’ya na basu shirya zama marayu ba, in ka mutu kuma ka san inda zaka kai zabiyar ka”.

Kawu bai san sanda ya fashe da kuka ba ya dawo kan Hasna’u yana dingishi. Atika ce ji tausayin Kawu ta kawo ruwa a kofi wato autar Hajjo ya hau shafa mata a fuska yana kiran sunan ta.

“Hansai, Hansai, Hansai diya ta!”

STORY CONTINUES BELOW

An dauki lokaci kafin Hasna’u ta yi ajiyar zuciya, shima Kawun yayi, ya kwance dankwalin dake kanta ya daure goshin ta. Daga nan ta  mike zaune, sai kuma ta ja gefe ta sanya kai a tsakanin cinyoyin ta ta soma kuka….

Hakika kuka rahma ne ga dan adam a lokacin da zuciyar sa ba ta da sassauci. Hasna’u tayi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita, kuka irin wanda bata taba yi a rayuwar ta ba. Kukan sabo da kewa… kukan kauna da soyayya, kukan da ba zai dawo da UWA ba, balle UWA irin tata da ta sadaukar da rayuwar ta domin inganta tata. Hajjo da ‘ya’yan ta suka yi tafiyar su, amma Kawu  akan Hasna’u ya kwana, don ya kasa tafiya ya bar ta cikin wannan mawuyacin halin, shima sai a lokacin mutuwar ‘yar uwar sa ta doke shi ta dawo masa sabuwa. Suka hadu su ka yi ta kuka shi da Hasna’u.

Bai fita ba saida aka kira sallahr asubahi, bayan ya zuba mata ruwa a buta, ya roke ta tayi sallah ta yi wa uwar ta addu’a. itace kadai tsakanin su yanzu.

Hasna’u tayi alwala ta tada sallah amma koda tayi sujjada bata iya addu’ar ba sai kuka. Kullum Inna ce ke tada ita sallah suyi tare. In ta tuna wai bazata sake ganin Inna ba ko yin Magana da ita sai taji zuciyar ta kamar zata fito ta bakin ta.

Koda gari ya waye ba wanda ya bi ta kanta a gidan. Kowa harkar gaban sa ya shiga yi yadda ya saba. Ko gaisuwa babu wanda yayi mata. Tana can takure akan gadon bonon Inna ta dauki zanin atamfar Innar ta lulluba ta rungume rigar ta, hawaye na bulbula. Hawayen da basa dawo da UWA a lokacin da DA ya rasa ta. Koda Kawu ya fito don tafiya kasuwa yace da Hajjo dake rabon dumame da koko.

“Hajjo in ce ko kin mikawa Hansai nata?”

Hajjo ta aje ludayin da take damun kokon da shi ta jefa masa harara ta ce “da can ni nake basu?” Yace “ai yanzu ba mai batan, dole duk abinda kika baiwa ‘ya’yan ki ki bata”.

Hajjo tace “tabdijam! Dole fa ka ce! Hakan kuwa ai ba mai yiwuwa bane tunda kuwa su talla suke da sayar da Rake su kawo min, ita ko ‘yar makaranta ce bazai yiwu ‘ya’ya na su sha rana su nemo abincin su in dauka in bata ba, sai dai in itama in dinga dafa mata Rogo tana kaiwa kasuwa kamar yadda Atika ke yi”.

Kawu ya ce “amma kin san Zabiya baya son rana ko? Uwar ta ko surfen data ke wuni yi kina gani bata bata ko sau daya ta ce ta taya ta ba, wane talla wannan halittar Allah zata iya yi miki?” Hajjo tayi mirsisi tace bata bada dumame saidai yaje ya sayo mata a waje.

Kawu yace “sai aka yi rashin sa’a sunana Samaila amma ba sauna bane, da za’a gindaya min yada zan yi da gida na, dole kullum kika dafa ki bata ko ni a cire min kwano a gidan a dinga bata nawa, ai nima ina fita in nemo in kawo to a bata wanda na kawo.

Hajjo tace nayi rantsuwa kuwa daga yau na cire ma kwano a gidan nan har sai ta koma inda ta fito”.

Duk abinda suke yi din nan a kunnen Hasna’u. yanzune ta tabbatar ta zama marainiya ta kowacce fuska amma a baya babu wanda ya kai ta gata. Yanzu ne ta tabbatar wanda ya rasa uwa shi ke da kuka kuma mutuwa TONON ASIRI GARETA.

Kawu ya shigo da kwanon dumamen yana kiran sunan ta “Hansai kin tashi?” Ta daga masa kai “ga nan dumame to ki ci” ta girgiza kai alamar bata ci. Yace “kada ki soma cewa zaki hora kan ki da yunwa, hakan bazai dawo da Zulai ba, saidai ya sanyata cikin damuwa. Maza karbi ki ci in je in nemo miki ruwan shayi mai zafi ki warware hanjin cikin ki”.

Ta karba ta ajiye a gefe ba don zata iya ci ba, sai don so take ya fita ya bata waje, she want to be alone tayi tunanin makoma ga rayuwar ta.

Zai fita kenan yaci tuntube da manyan bagco guda biyu, ya tsaya ya bude yana dubawa, sai ya ga duk wani kayan bukatar dan adam yana cikin wadannan jakunkuna daga na ci har na amfani. Cikin mamaki yace.

“Hansai, wannan kuma daga ina?”

A hankali ta kai idon ta ga kayan amma bata ce komai ba. Domin ta gane daga inda suka fito. Jakar farko sayayyar da kai mata unity ce ya ce inji Inna, ta biyun kuma wadda yayi a Albasu ce a hanyar su ta dawowa bata san ko wa ya yi wa ba.

Ajiyar zuciya ta kwace mata, amma bata ce komai ba.

Shima Kawun sai ya gane daga inda kayan suke ba tare da ta bude baki ta gaya masa ba. Ya jinjina kai yana mamaki yace.

“Sahabi ko?”

Kai ta gyada masa. Sai ya dawo ya zauna akan karaunin dakin yana fuskantar ta yace “Hansai, me ke tsakanin ki da wannan yaron ne?”

Kai ta girgiza masa da sauri alamar babu komai. Yace “a’ah Hansai, in kin ga kare na sunsunar takalmi dauka zai yi. Ni na gaya miki akwai wani abu a kasan ran sa game dake, amma lokaci zai fada miki idan ni baki yarda da ni ba.

Saidai kuma hakan ba mai yiwuwa bane domin bazan kai ki inda zaki wulakanta ba, ke ba uwa ba ke ba uba ba, don haka na riga na yanke hukuncin da zai fishshe ki, in ya so ni ayi ta haifomin jikoki zabiyan ina kula da abuna, dama Kakar mahaifinmu ma Zabiya ce, nafi kyautata zaton wajen ta kika gado”.

Yana fita Hasna’u ta lula a tunani? Ko me Kawu yake nufi da cewa ya riga ya yanke hukuncin da zai fishshe ta? Ta ji dadin abinda yace da yace ba zai kai ta inda zata wulakanta ba, wanda ke nufin ba abinda zai rude shi ya sarayar da martabar ta, koda abinda yake hasashe din ya zama gaskiya akan Uncle Saheeb.

Wunin ranar zungur Hasna banda sallah ba abinda ke tada ta daga gadon bonon Inna. Bata tashi jin sababbin hawaye sai ta yi sujjadah.  Bata ci komai ba tun safe har dare, tana ji Hajjo da Kawu na fada kamar zasu yi dambe da yamma da ya dawo wai tunda ya ce Hasna’u bazata yi talla da rana ba, to dole tayi mata tallan gyada a kofar gida da daddare ko a dandali.

Kawu yace “Kinsan Allah Hajjo? In kin ga Hansai ta yi talla, to ki tabbata bana numfashi”.

Tace “da ranka da lafiyar ka, da idon ka da jin ka, sai Zabiya tayi tallan Rogo da gyada”.

Ya riga ya san halin Hajjo, bata sa kanta abu ta fasa, shi yasa yau litinin ya ki fita kasuwa ya zauna a soro yayi shimfida, ya kunna radio ya aje tum-tum din auduga ya kishingida a kai, shi bai yarda ba gadin ‘yar sa yake kada a dora mata tallan Rogo. Kawu ya ce.

“Kasuwar ma na daina zuwa kowa ya ci uban sa. Rigima uban wa ta kashe? Nima rigimamme ne”.

STORY CONTINUES BELOW

Motsi kadan Hajjo ta leko soro ta ga ko ya gaji ya tafi? Sai ta gan shi daram-dakam ya kunno jakar magori ko taskar labarai. Hussaini wanda shi kadai ke zuwa makaranta a gidan ya dawo da azahar ya gan shi  a soro. Yace.

“A’Ah Kawu yau baka fita bane?” Yace ban fita ba din, kun bani ajiya ne? Ko kuna bi na bashi? Ko a kan ku nake zaune?” Hussaini yace “Allah ya bada hakuri daga tambaya? Ai ba ni nakar zomon ba, kuma ba nina kashe uwar Zabiya ba. Na lura tunda Zabiya ta dawo hutu kake cikin bala’i da kowa a gidan nan”.

Kawu ya rarumi takalmin sa ya maka masa yana cewa “uban ku zaku ci daga ku har uwar take mai zuga ku ku min rashin kunya”. Hussaini yayi ciki da gudu yana kiran Hajjo. Hajjo tace “rabu dashi, mutuwar kanwar sa ta sa ya zama kansa da motsi. Ni kuma ba mai aje min zabiya a gida, Atika tazo haihuwa ta haifo min jika Zabiya saboda yawan ganin Zabiya. Dole yasan yadda zai yi da ita.

Wajejen karfe sha biyu na rana wata mota kanknuwa ‘dark-blue’ ta yi fakin a kofar gidan Kawu Samaila. Kawu yaji hucin motar (don sam bata kara) amma bai kawo gidan sa aka zo ba. An dauki mintuna kafin mai motar ya fito yana rufe kofar ta da keys din hannun sa, wadanda ke makale jikin wani kyakkyawan key-holder.

Ya isa soron yana sallama da wata lallausar murya. Kawu ya amsa yana zuqar turare mai dadi a kofofin hancin sa kafin ya ce.

“Wa nake gani kamar SAHABI!”

Ya rage tsawo yadda bazai buge da gajeriyar kofar zauren ba ya shigo yana fadin “ni ne Kawu, ba fa Sahabi bane sunan, har yau ka kasa fada dai-dai, SAA-HEEB”. Kawu yace “koma menene duk abokin Manzo yake nufi, shigo daga nan kusa gare ni ka zauna, ka sha hanya”.

Ya tsugunna har kasa ya gaida Kawu sannan ya zauna a gefen sa yace. “Yaya Karin hakuri Kawu? Kuma yaya Hasna’u ta kara ji?” Kawu yace “Ai na ga boni! Kai dai akwai ka da wayo, shine ka zame ka barni da jidalin Hansai, wallahi har goshi ta fasa. Yau kwana biyun nan bana jin ta ci abinci ko loma daya ne. ban taba ganin mai son Uwa irin Hansai ba”.

Da Kawu ya san yadda maganar ta doke shi da bai fada masa ba. Kwana biyu ba cin abinci? Ta fasa goshi? That delicate and fragile skin? Murya can kasa yace.

“Zan iya ganin ta Kawu? Ni in na bata abinci zata ci, idan na bata baki zata saurare ni”. Kawu “ya ce da na ga ta fara borin nan kamar na mai iskokai sai da na tuno ka ai, na ce da na sani kai ka gaya mata”.  Ya kwalawa Atika  kira ta fito da sauri, idon ta a kan Saheeb, yace “maza kirawo min Hansai, ki ce tazo in ji Sahabi”.

Kafin ta kira Hasna’un sai da ta fara gayawa Hajjo ga wani dan gayemai mota ya zo wajen Zabiya. Hajjo tace “dadi na da ke Atika dabbanci, waye zai zo wajen zabiya?” Ta ce “Hajjo toh? Fito da kan ki ki gan shi”. Ai kuwa Hajjo sai ta yi lullubi ta je soron kamar zata leka waje neman yaro, ta gansu suna cin rogo da soyayyar gyada shi da Kawu. Ta ce.

“Gafara dai!” Kawu ya zabga mata harara shi kuwa Saheeb sai yayi kasa yana gaishe ta.

“Samari me kake nema? Ko ka yi batan kai ne?”

Kawu ya ce “a’ah makuwa yayi, kinsan kowa makakke ne irin ki, da auren ki Hajjo? Ki fito cikin maza ba iznin mijin ki?” Ta wuce ciki tana cewa “meye laifi na don na zo in gaya masa gaskiya? Ka san Zabiya abinda yasa ake haifar su a haka, an sadu da uwar su tana jinin al’ada”.

Ba Saheeb kadai ba hatta Kawu kunya ce ba ‘yar kadan ba ta kama shi mai tattare da bakin-ciki da takaici. Yana so ya baiwa Hajjo amsa daidai da wacce ta fada yana tsoron kada su raba abin fade a gaban bako mai daraja a gareshi irin Saheeb. Duk sukayi mata shiru, sai ta wuce ciki tana fadin.

“Ni dai na gaya maka gaskiya”.

Kawu yayi ajiyar zuciya Saheeb kuma ya sunkuyar da kai, Kawu yace “wato su mata duk girman su da shekarun su tumaki ne Sahabi. Banda haka da tuni na rabu da Hajjo domin zaman nan daka ga na yi gadin Hansai nake kada ta dora mata tallan rogo, yarinya gata nan kamar ta-kitse-ta-kitse in je ta narke a rana”.

Saheeb ji yayi nan duniya ba wanda ya tsana irin Hajjo, da yana da iko yau duka zai yi mata ko ya daureta har sai igiya tai rara kafin ta dorawa Hasna’u tallah.

“A tambayeta ko nawa ne cinikin rogon zan dinga bata kullum, amma don Allah don Annabi Kawu kada a daura mata tallan nan, fuskarta zata yi dabbare dabbare in ta sha rana ko kwaro ya cije ta, sannan basa jure zafin rana ko kankani”.

Kawu yace “ai na gaya mata ‘sai bayan rai na’ sai dai in daina fita neman abinci in yi ta gadin Hansai har zuwa ranar da zan daina numfashi”.

“Balle ma baza a yi haka ba, a kira ta muyi lissafi, duk sati sai in din ga kawo mata kudin tallan amma dole kaje harkokin ka kuma Hasna’u bazata yi mata talla ba, in ta dage wallahi Allah zan kai ta HUMAN RIGHT”.

Atika ta shigo tana zumbura baki tace “Kawu nayi-nayi ta zo ta yi min banza, na gaya mata saurayin tane ya zo amma ko kallo na bata yi ba, ina jin fa ta zama kurma”. Kawu ya rasa abinda zai raruma ya maka mata sai ya dauki rediyon sa ya saita bakin Atika da ita…Saheeb yayi maza ya rike rediyon, Atika ta gudu”.

“Ni dai na haifi jarraba, yara duk sun biyo halin uwar su na rashin iya magana, Hussainin dana ke dan jin dadin sa shima kwanan nan ya fara daukan halin su, dazu sai da ya gwaba min magana” ya soma matsar kwallah. Saheeb yana cewa.

“Kayi hakuri Kawu addu’a zaka yi musu ba kuka ba”.

Kawu ya tashi ya shiga gidan da kansa domin ya turo Hasna’u.

“Hansai na turo kizo kika ki zuwa ko?”

Ta sake rushewa da kuka bata ce komai ba. A wurin ta ta riga ta gama yanke alaqa da SAHEEB WAMAKKO, bata bukatar komai daga gare shi tunda yayi ZARAR BUNU….. ya haura limit din da yake kai na Yayan ta. Dama alakar tasu ta Yaya da kanwa ce, tunda kuma yanzu yace ba ita bace ai shikenan, itada shi haihata-haihata….

Masu iya magana sun ce “tsuntsun da ya ja ruwa… shi ruwa kan doka, ba zata jawowa rayuwar ta tozarci ba. Wanda ta fara gani a wurin uwar sa da kanwar sa kadai ya ishe ta misali”.

Shima Kawun yayi maganar duniya bata tanka masa ba, yayi lallashin ya gaji, gashi bai iya zuwa ya ce da Saheeb ta ce bazata zo ba, a karshe yace.

“Ko dai gaskiyar Atika ne  kin kurumce?” Ta motsa bakin ta a hankali tace “da kunne na!” Yace “to alhmdulillahi, sakarci ne abin kenan!”. Sai ya juya ya fita.

A zaure ya tadda Saheeb yana safah yana marwa yana naushin hannun daman sa cikin na hagu, Hasna’u kawai yake son gani da halin da take ciki. Wannan wane irin damalmalallen gida ne wadanne irin mutane zata rayu da su haka? Abu daya ya rage masa damuwa da ya fahimci Kawu Samaila tsayayyen mutumne akan ra’ayinsa matar sa bata juya shi amma a yadda ya fahimta gabadaya ‘ya’yan basu da tarbiyya.

Kawu y ace “biyo ni Sahabi”.

Ya bi bayan Kawu zuwa cikin gida ta kofar shiga sassan su Hasna’u.

About AIS

Check Also

YAR NAJERIYA CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR  Www.bankinhausanovels.com.ng  BAKIN  KANON-DABO (MAGANA ZARAR BUNU….) Kwanaki goman …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *