UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 8 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 8 BY SHATU

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ayaan! Ayaan!!”

Ta Shiga fada a firgice, Baba dake gefenta ya Mike tareda saka wayar shi ya haske fuskarta, gaba ta jike da gumi, kafafunta dake a kannanade se shura su take, haka hannunta da take ta mikawa alamar Ayaan din take son kamawa, wani takaici ya lullube Baba yaji tamkar ya dada Mata duka, ya girgiza kai tareda saka hannun shi ya bubbuga kafadar ta, tayi saurin bude idanunta a gigice, tasa hannunta ta dafe goshinta Jim yadda ruwa yake diga kawai se ta fara sharce gumi tareda kallon Baba dake gefenta, bakinta se rawa yake tace

” Mafarki nayi! Wai…”

Tsaki kawai yayi ya juya baya yayi kwanciyar shi, idanunta ta zaro cikeda mamaki tace

” Likita magana nake maka fa, na tsorata fa Amma ka juya min baya”

” Me kike so na Miki? Dare ne Dan Allah ki barni nayi bacci”

Daga haka ya kashe flash light din wayar shi ya juya Mata baya da niyyar komawa bacci,a wasu lokutan baka sanin komai ya lalace maka se ya Gama kwabewa kafin kake ankarewa, to Anty Rumasa’u is a victim, ta hadiyi yawu tareda kallon Baba dake kwance haka duhu ya mamaye dakin, take mafarkin ta ya fara dawo Mata, se take ganin kamar sarkar da aka sakale ta da ita, ita ce ake nufo ta da ita, wata Kara ta saki tana kankame Baba, mikewa yayi ya janye ta daga jikin shi sannan ya dauki wayar shi da pillow ya bar Mata dakin, wayatta ta laluba ta kunna se ta saki ajiyar zuciya Amma duk da hakan a firgice take, a haka ta kwanta tana tunanin me ya faru Baba yayi Mata hakan, bawai wannan shi ne Karo na farko da ta fara ihu cikin dare ba, idan zata tuna hakan ma ya zame Mata jiki kullum cikin mafarkai take masu ban tsoro, Kuma duk lokacin da hakan ta faru to shi zai zauna tare da ita, har zuwa lokacin da zata nutsu, to me ya faru yau Kuma.

Washegari saboda Bata Yi baccin kirki ba se ta kwanta tana ta bacci har Ayaan ta gama shiryawa haka Baba suka fita Amma tana bacci. Se can wajen daya sannan ta tashi, ta mike ta Dan gyara gidan itama mutum ce me tsafta, ta gyara gidan sannan ta shiga kitchen ta daura abinci, ta Jima zaune tana tunanin abinda ya faru cikin dare, har shinakafar dake kan wuta ta fara kamawa sannan tayi snapping daga tunanin da take, ta juye cikin warmer sannan ta koma parlor ta dauki wayar ta ta fara Kiran mahaifiyar ta, Mama Altinne tana dauka tace

” Mama Kinga ban daina mafarkan ba”

Ko gaisawa basuyi ba, Mama Altinne tace

” Kinje kin duba binnin da kikai?”

Ta girgiza Kai tace Mata zataje ta duba sannan zata kirata, tana aje wayar ta nufi can Bayan bangaren Ammi inda anan ne ta binne kayan Tsubbin nata, tana zuwa gurin taji gabanta ya Fadi saboda tsiron da komai sun bushe, ta dafe cikin ta ta zaro Ido ta Kai hannunta ta fara hako gurin Amma komai ya bushe se bibbige, juyawa tayi ta koma ta dauki wayatta ta Kira Mama

” Komai ya bushe, Kuma wallahi Mama duk bayan kwana biyu se na bawa abin ruwa, ko shekaran jiya ma haka!”

Maman tace

” Ikon Allah! To Amma ba ciki ya shiga jikin ki ba?”

Anty Rumasa’u ta shafa cikin ta tace

” Eh Mama ciki ne dani wata daya”

Wani ashar ta kunduma Mata tace

” Ke mahaukaciyar Ina ce da Zaki cire implant din, to ki sani kiyi hanzarin cire cikinnan!”

” Haba Mama kina kallo shekarar Ayaan bakwai ban Kara haihuwa ba, ni dai haihuwa nake so, gashi babanta ya canja min, dazun kamar zai mareni cikin dare!”

” Kadan Kika gani, matsawar baki cire cikin ba kin dinga ganin bakin ciki kenan. Ke kanki kinsan yace ciki da wannan aikin ba zasu hadu ba, kwana nawa ya rage ki Bari yace ki samu ciki Bayan yace a wañnan auspicious time din Zaki Haifa namiji”

” Nidai Mama kawai ki Nemo min mafita, wallahi idanun Likita dazun ba karamin tsorata ni yayi ba, kamar yasan abinda nake aikatawa Kuma cikin jikina bazan iya fitar dashi ba”

A bangaren Anty jidda ta Gama hada duk wani Abu da take ganin zai kaita ga ci ta Kuma kawar da duk abinda zai kawo Mata obstruction. Wata kawarta Hajiya Laila ita ke Kara zuga ta tana Kara Hira Kai. A bangaren Hanifa Bata San abinda uwarta ke shiryawa ba, ranar Friday ta shirya cikin fitted gown wadda hannunta da kirjin ta duka net ne, rigar tamkar a jikin ta aka dinka, ta dauki katon hijab ta saka sannan ta hada kayan da zatai amfani dashi cikin jakar ta ta fito ta dubi Amira dake zaune a parlor tace

” Idan Mom ta fito kice mata zanje get together”

Amira ta dubeta tace

” To meye Kika zumbula hijab, tsoron wancan tababben kike?”

Hanifa tayi dariya tace

” Baki ji me Kika ce ba tababbe, yanzun se yace zai dakeni Kuma Mom Babu yadda zatayi”

Daga Mata hijab tayi Suka kwashe da dariya, Amira tace

” Abasu kala Yar gidana”

Daga haka ta fice, Haruna shi ne babban yayan su da suke uba daya, mahaifiyar su ita ce matar baban su ta farko da ta rasu se ya auri Anty jidda, da tazo seda ta baza su, su uku uwar su ta Haifa, Haruna, Mubarak se autar su Asiya, wadda azabar Anty jidda ta sa  ta koma Danbatta dangin babanta, yanzun haka tayi aure harda yaranta, Mubarak shi Kuma kamar Anty jidda din ce ta haife shi yayi blending sosae da life style dinsu shiyasa Amira ke shiri dashi, shi kuwa Haruna makiyi kenan, tababbe suke ce Masa saboda Yana tsare su.

Driver na hango ta ya taso ta Shiga ba tareda ta yiwa Haruna magana ba Shima kokarin alwalar sallar maghrib yake se ya kyaleta ta gama ai zata dawo ta sameshi. Seda ya kaita zoo road tayi makeup ta cire hijab aka Mata dauri kamar amarya ta saka jewelry sannan ta fito Suka nufi Chicken republic inda akai reserving na yin get together, tana Shiga ta samu Wanda shigar su tafi tata rashin mutunci, Amma itama ba baya ba.

Se wajen Sha daya sannan ta dawo gida, tunda driver yayi parking tana fitowa wannan Karan da ainahin shigar data fita da ita, Dan Bata Yi tunanin zai jira har ta dawo ba, tana fitowa ya karaso Yana kallonta kasa da sama yace

” Daga Ina kike?”

Ta mishi banza ta nufi cikin gida har tana hardewa saboda kada ya kamo ta, kyaleta yayi har ta Shiga parlon Babu kowa Dan haka ta lallaba ta shiga dakin su, Amira na zaune tana waya, ganin ta ta kashe tace

” Kin dade, Abba yazo nemanki”

Tayi tsaki tace

” Rabu dashi, wallahi abubuwa sukai zafi bansan dare yayi ba”

Ta gyada Kai tareda karbar wayar tana kallon hotunan da sukai, tana ta squeeling na murnar kyau. Washegari Anty jidda ta shigo ta dubesu tace

” Haneey Ina Kika je Kika Kai dare har wancan mahaukacin ya fadawa Babanku?”

Hanifa ta mirtsika idanu tace

” Get together naje, shi ya fiya saka Ido. Tukun ma Mom se yaushe zaayi auren ne?”

Tayi murmushi a ranta tace aiki yayi kyau kenan, tunda Suka je gurin malamin Hajiya Laila tace sede wata ba Hanifa ba. A wañnan ranar ta saka kwalli ta tafi gidan Ummaah, tunda suka hada Ido Ummaah ta fara fadin

” Jidda sannu fa, meye labari?”

Anty jidda tayi murmushi tace

” A aurawa Hanifa Ismail”

Ummaah tace

” Hakan yayi, nagode sosae. Yaushe kike son ayi auren?”

Tace

” Ending next month”

Ummaah tace angama, kafin kace meye wannan Shirin biki ya kankama sosae, kowa yaji zancen bikin se yayi mamaki, Ismail ya kirani Ina makaranta yake fada min, naji tausayin shi sosae saboda na fahimta pains din da yake ciki, na lallashe shi na nuna Masa tasa kaddarar kenan!

Ban Bari abinda Ismail ya fada min ya dameni ba, tunda ni Babu ruwana a ciki, revenge ma da nace Zan daukar ma Ammi naji zuciyata tayi sanyi Babu wani amfanin Yi, na tabbatar akwai babban show that’s about to play a dangin mu.  Koda mukai magana da Rayha na fada Mata abinda take faruwa tayi dariya tace min+
” Allah Kaine abin godiya, ai wannan fadan cikin gida ne Sofy, se mu ja gefe mu ga ikon Allah”
Nayi murmushi Ina girgiza Kai nace
” Ke muguwa ce wallahi, bakijin tausayin Yaya Ismail dinne wai?”
Tace
” Saboda me? Mu ta ragawa tamu uwar, ni jikina na bani Anty jidda ma tanada wani ulterior motive din hada airennan”
” Sosae ma, so take ta kuntata mana, irin tunda naki gashi zai aure kinsan haka ta fadawa Baba, shi Kuma ya kirani wai Kar na damu,na kyalesu, ni dai dariya kawai nayi”
Ta tabe baki tace
” Naga Shima Baban kamar ya dawo hayyacin shi ko?”
Na gyada kaina nace
” Baki San last semester har visiting suka zo min shi da Ammi ba”
Tayi dariyar jin dadi se muka cigaba da hurar yadda gidan mu ya samu lafiya, a haka mukai sallama dan mijinta ya dawo, na aje wayar sannan na samu na Shiga tunanin kullum, yadda rayuwa ke canjawa kullum daga wannan se wancan, idan kana tunanin ka bar wannan case din to da ka fita daga shi wata sabuwar kaddarar na jiranka, rayuwa is never a smooth sailing, akwai thorns Wanda zasu dinga dragging dinka, Allah dai ya datar damu.
Kwanci tashi akace asarar me Rai, lokacin biki yazo, Anty jidda tayi gagarumar nasara, wannan yayi daidai da hutun session Dana fara na kammalla level 1 Dina, haka Gama school din Anty yusra. Ranar da zata Gama final exam dinta, Usman ne zai zo daukar ta, dukda tace min wai saboda ni zai zo tunda shi ba mutum bane me sakin aikin shi Dan irin wannan abun ba. Tun kafin ta Shiga exams yazo, Nima Kuma banida exams ranar, so da zata fita se muka fita tare Dan bazan iya ce Mata a’a bazanje gurin shi ba, hakan na bita. Yana zaune kan wata concrete chair Yana sanye da manyan kaya harda hula ranar, se Naga ya manyanta he looks much more responsible ba kamar da can Dana San shi ba, gefen shi yarinya ce tana ta tsalle tsalle. Tunda muka hada idanu ya fadada Murmushin fuskar shi, Nima na Dan saki tawa na karasa tareda gaishe shi, ya amsa Yana duban yusra dake Masa sallama zata tafi exams, Zama nayi na Kara gaishe shi
” Ya karatu?”
Ya tambaya Yana tsareni da idon shi
” Kararu alhamdulillah, Afaf ce?”
Ya gyada Kai, na Kai hannuna na rike nata, remembering ranar da ya kawo min ita cikin layette Amma gata har ta girma.
” Gata ta girma, Afaf greet your second Mum”
Ta kalleni sannan ta kalla baban ta se Kuma tace
” Ina kwana?”
Nayi murmushi nace
” Lafiya Lau Afaf!”
” Sofy ya ake ciki? Yanzun kin Kara girma Ina fata yanzun Zan samu matsugunni a gurin ki”
Na danyi Jim tareda kawar da kaina, yanayin fuskata ya canja se naji na Dan takura
Tasowar yayi daga inda yake zaune ya dawo gefe na ya zauna, making sure ya bada space tsakanin mu yace
” Kamar wancan time din bazan takura ki ba, it up to you ki yadda za Kuma ki iya samun reason to turn me down. Fada min na saka Rai ko kuwa”
Na cigaba da Wasa da kalbar dake kan Afaf wadda aka Mata ado da multicolored beads, na kasa cewa komai har ga Allah ban so na Kara haduwa dashi ba, saboda na fahimci he’s a righteous man Amma Kuma ya riga ya makara Bature ya Masa shigar sauri.
” Wannan Karan ma Babu nasara ko? Allah sarki ni Afaf Kinga Sofy ko, kice Mata babanki da gaske sonta yake”
Se na Dan kalleshi he looks pitiful, duk wannan charming Murmushin da yake duk ya dauke Amma Kuma Bai bata fuska ba,
” Kayi hakuri already an bada aurena…”
” Yaushe?”
Na Dan gyara zama na nace
” Baifi wata hudu da suka wuce ba, Kuma ni bana son na aure Wanda ke da Mata”
Se yayi murmushi yace1
” Haka Zaki ce min tun farko, don’t say you’re bethroted bazan yarda ba. By the way akwai dalilin da yasa baki son kishiya?”
Na girgiza Kai na bance Masa komai ba saboda bazan iya fada ba, se nace Masa
” Kayi hakuri I’m turning you down”
Yayi murmushi yace
” You don’t have to be sorry, hakan rayuwar take ni Ina sonki ke kina son wani. It’s normal phase ai”
Na gyada kaina but I’m truly hurt da ban amince Masa ba, to me yasa tun farko naki yarda dashi na ayyana da tuni yanzun banzo Ina jin kunyar shi ba. Ganin yadda yanayina yake se ya canja maganar ya fara tambayata akan course Dina na zauna mukai ta Hira har lokaci sosae ya tafi, Anty yusra ta dawo ta same mu so engrossed a hirar da muke, se tai tunanin ai mun yadda da kanmu. Anty yusra ta Gama komai ta fito zasu tafi, naji Babu dadi saboda yadda muka Saba, Muna zuwa bakin mota ya dakko min leda ya Miko min, na noke kafada alamar bazan karba ba, se ya Buda min anan naga books ne da sauri na amsa Ina murmushi a raina Ina Raya yasan weakness Dina, abinda duk zamana da Bature bazai Yi ba sede tarkacen alawa kamar yarinyar goye shikam shi da Ismail sun san abinda nake so yake saka ni nishadi, na kalleshi idanuna yayi sparking da haske nace
” Nagode sosae, Allah ya kiyaye Hamma”
Ya kalleni yace
” Kara fadar sunan naji, it’s good hearing Hamma from you”
Nayi dariya tareda rufe fuska ta nace
” Anty yusra na jiranka”
Ya Shiga ciki ya tada motar Yana kallo na zagaya bangaren Anty yusra nace
” Allah ya kiyaye Hanya, I’ll miss you”
Ta gyada Kai tace
” To amaryar Hamma se munji magana me dadi”
Rankwashi ya Kai Mata ni Kuma na daga musu hannu Suka tafi Ina dariya, na juya zuwa hostel se nake ganin kamar ban kyauta Masa ba, ita Kam Anty yusra tace ma Hamma
” Hamma make a move Mana Sofy na sonka”
Ya girgiza Kai yace
” Ko kadan, she just rejected me, na hakura kawai”
Se Bata ce komai ba, bayan kwana biyu na Gama exams Bature yazo dauka ta, akwai wata da Baba ya turon contact dinta akan zata biyo mu zamu sauke ta Kano, da safe tazo dakin mu sunan ta Widad tana level hundred itama.A Kano muka sauke Widad har gidan na Shiga na gaida maman su sannan na fito muka tafi nida Bature, tunda muka dauki hanya bayan na tsaya inda Ammi tace na karbo dinkunan mu ni da Anisah da nata na bikin Hanifa, Banda Hira Babu abinda muke Yi se wayata ta katse ni, na Kai duba Naga bakuwar number haka na dauka tareda yin sallama ko amsawa baayi ba, se cemin tayi+
” Ya Kika gani? Ina fata zuwa yanzun kin samu labarin Zan auri Ismail ko? Kinga ni ba tsararki bace”
Karshen maganar ta ya tabbatar min Hanifa ce, nayi murmushi nace
” Gaskiya kam! Ina Miki fatan alkhairi”
Tayi tsaki tace
” Kya santa dai da gulmar ki, idan ma tsiya kike min fata na riga nayi gaba na barki”
Ko kadan words dinta Basu Shiga kaina ba balle su dameni nace
” Allah sarki Amma Ina son kullum ki tuna maganata cewa Matar cushe ba Mata bace, da kin San how much Yaya Ismail ya tsaneki bana tunanin Zaki daga kafada balle har ki hura hanci, auren huce haushin? shi kike yiwa wannan kafafar, kada Kuma ki manta ni nace banayi shiyasa kikai standing chance, ko yanzun nace na dawo Ina Yi dashi, ko a Mai aikin gidan mu bazaki zo ba, ballantana kisa ran zai aureki, Dan haka kiyi ta kanki!”
Banma jira me zata ce ba na kashe wayata na aje akan cinyata, Bature dake driving ya dubeni yace
” So dama kina fada?”
Na danyi dariya nace
” Raina ni zatayi”
Ya girgiza Kai yace
” Ni kaina kullum se nayi addua wannan Ismail din yayi aure na samu hankalina ya kwanta”
Nayi dariya
” Ka tsorata ne?”
Ya wani kalleni sannan ya kashe idon shi daya yace
” Faduwar gaba asarar namiji”
Se muka bar maganar muka cigaba da hurar da zata amfane mu, har gida ya kaini nayi nayi ya shiga yace wai shi kunyar Ammi yake ji, haka na tsaya Ina kallon shi sororo nace
” yau Kuma? Ikon Allah”
Yayi dariya yabi bayana muka Shiga ciki, ita kadai ce gidan se Anisah da wata cousin dinmu da tazo ramlah, ya tsugunna ya gaida Ammi sannan ya Mata sallama tayi tayi yaci abinci yaki yace wai sauri take a ranar yake son komawa Funtua, bayan Shi nabi na Masa sallama sannan na dawo gidan. Zama nayi gefen Anisah nace
” Ammi Ina wuni? Ya gida?”
Tace
‘ lafiya Lau ya exams din?”
Na Dan shingida na amsa da alhamdulillah, Anisah ta kawo min kunun Aya na fara Sha se naji sallama kamar muryar Rayha, hakan yasa nayi saurin sauke jarkar hannuna, Ayaan ce ta shigo tareda Zama gefen Ammi, na dubeta tana ta kallona nace
” Ayaan! Yaushe Kika zo?”
Ta gaishe ni sannan Ammi tace Mata
” Takwara kin ci abincin?”
Ta gyada kanta tace
” Naci Ammi, wai Gwoggo tace wai yaushe zamu tafi Kano”
Ammi tace
” Se gobe inshallah”
Se Suka tafi daki nace
” Ammi me yasa take zaune anan?”
STORY CONTINUES BELOW
Ammi tayi murmushi tace
” Ya kaita majia ne primary boarding, da akai hutu wai maman Bata nan shi ne ya kawo ta nan”
Na gyada Kai na shige daki nayi wanka. Washegari da yamma muka tafi Kano, akan a ranar Hanifa zatayi Ladies Eve. A gidan Kawu Hafizu muka sauka, bashi da nisa da gidan Ummaah, brother Ammi ne. Matar shi Anty Nuzla shekarar su biyar Amma har yanzun bata haihu ba. Da duk ta damu Amma indai zasu hadu da Ammi to zata kwantar Mata da hankali dukda Yan uwan Ammin na Dan tsangwamar ta to ya zatayi haihuwa dai ba mutum ke bawa kanshi ba, wannan karatu ne da ya kamata tuntuni mu haddace shi akan mu. Bayan mun gama cin abinci Ammi ta dubeni tace
” Ba Zaki je can Ladies Eve din ba”
Na girgiza Kai Ina maida hankalina kan littafin Men are from Mars and women are from Venus!
” A’a Ammi, ayi lafiya”
Se ta gyada kanta tace
” To tashi ki rakani naje na musu Allah ya Sanya alkhairi!”
Na Mike na gyara zaman rigata, ta kalleni har kasa tace
” Kinga canja Kaya”
Babu yadda zanyi haka na nufi kayan namu na Ciro coffee din lace me adon milk na saka dinkin skirt da riga da ya zauna jikina, veil na yafa na dakko dannkunne na saka sannan tace
” To yanzun ba gashi nan kinyi kyau ba”
Nayi murmushi sannan muka fita, su Ayaan da Anisah na zaune tareda Anty Nuzla, Ammi tace
” Anty Nuzla zamu je gidan bikin, Anisah zaku zauna nan ko Yaya?’
Ayaan ta mike ta rike hannun Ammi, Dan zaman da sukai ba karamin sabo sukai da Ammi ba, ko Anisah Basu shaku da ita ba kamar Ammi. I wonder yadda uwarta zatayi idan ta ganta. Gidan Ummaah Babu mutane sosae se irin na jiki sosae, muka Shiga har parlonta dake sama tana zaune a Hakimce se mulki take zubawa, ni da sauran yaran muka zauna a kasa Ammi ta zauna kan cushion tace
” Ina wuni ya taro”
Ummaah ta amsa a hankali tana kallona, na gaishe ta sannan na gaida sauran matan parlon na musu Allah ya Sanya alkhairi. Ummaah ta dubeni tace
” Uwata ya baki je gurin Eve din ba?”
Na kauda kaina nace
” Zanje”
Ta gyada kanta Ammi ta mike Bayan ta aje mata kudi tace
” Zamu wuce Allah ya Sanya alkhairi”
Ummaah ta kalla kudin sannan ta dubi Ammi tace
” A’a tafiya kamar Yaya? A Ina kuka sauka”
Ammi ta Mata bayani a takaice se tace
” To ke idan bazaki zauna ba su ki barsu su zauna anan Mana!”
Na kalli Ammi Ina adduar Allah yasa kada tace mu zauna se Naga ta girgiza Kai tace
” A’a zasu zauna tare Dani”
Ummaah tayi wani kuri da idanu saboda mamakin abinda Ammi tace Mata, ta juya muka take Mata baya, se a lokacin ta lura da Ayaan se ta kwalla min Kira, na koma na dubeta
” Wancan karamar ba kanwar ku bace Hajara?”
Na gyada kaina nace
” Eh ita ce”
Ta kura min idanu fuskar ta ta nuna mamaki tace
” Kira min mamanku”
Nayi murmushi a raina nace lokaci me zuwa, gashi Ammi an daina Kiran ta Hajara sede maman ku. Ammi ta dawo ta dubi Ummaah da gaba daya yanayin ta ya canja tace Mata
STORY CONTINUES BELOW
” Me Yar Rumasa’u take a gurin ki? Ba dai Kun hade Kai bane keda ita? Matar da ta lalata Miki zaman lafiyar ki. Me yasa Zaki ruke Mata ‘ya?”
Ammi ta kalli Ummaah da mamaki sosae a fuskarta, ta kasa gane wanne dalilin ne yasa take Mata wannan tambayoyin, tayi murmushi tace
” Sede ki Kira Likita ki tambaye shi. Se anjima”
Daga haka muka wuce Ammi tana ta mamaki nace Mata
” Ba abun mamaki bane ba Ammi, Ummaah gani nake tata tazo karshe tunda ta hada sirikanta da Hanifa”
Ammi dai mamaki sosae tayi muka wuce gidan Anty jidda, nan ake biki Dan tun daga waje nake ganin shige da ficen mutane, muka Shiga Yan gayu iri iri da Yan gayun Billahillazi da Yan gayun Dole suna nan ana shige da fice. Shigar mu daidai fitowar Hanifa tayi kyau da friends dinta uku se Kuma cousins din mu biyu, tana ganina taja ta tsaya, muka karasa Ammi ta Mata Allah ya Sanya alkhairi ta amsa da murmushi, su duk iskancin su suna ganin gorman Ammi Babu ruwansu da tsamar dake tsakanin iyayenmu, na dubeta Ina murmushi nace
“Matar cushe, kinyi kyau”
Wani mugun kallo tayi min ta kasa fadar komai, nasan da ban rigata magana ba da se ta yaba min maganar da zata saka ni ciwon kai, Amma Dana fada Mata se ta kasa magana Dan haka na dubi Amra dake bayanta da Sofy nace
” Brides maid”
Nayi murmushi dukkan mu hudun sunan Gwoggo gare mu kuma kusan shekarun mu daya, Amra babanta kanin Baba ne, Sofy it’s Kuma mamanta ce take bin Anty jidda, na wuce ciki na barsu da Bina da kallon banza. Anan ma bamu zauna da yawa ba muka tafi. A ranar bamu hadu da Ismail ba se ranar kamu washegari kenan, nayi kyau sosae a cikin ankon da mukai, Rayha hadda kukan ta tana can tana fama da tsohon ciki ga makaranta, Yan gidan su sunzo daga maiduguri. Bamu je da wuri ba se da har amarya da ango suka zauna kan cushion dinsu, mutumina yayi kyau Amma fuskar nan ko annuri Babu ita Kuma se murmushi take kamar bakinta zai yage, haka uwar ta ta kasa Zama yadda kuka San Yar siyasa se daga hannu take. Nidai tunda na zauna ba tashi ba seda sister Yaya Ismail tazo ta Kama hannuna wai Yana Kirana , na gyara zaman veil Dina na nufi gurin su Bayan ta, muna hada Ido ya saki murmushi tare da Bina da kallo, Nima mayar masa Murmushin nayi na tsaya gefen Hanifa da ta Bata fuska, mukai hoto ni ce a tsakiyar su. Aka tashi taro se washegari tun safe muka tafi saboda ranar daurin auren ne. Ina zaune a dakin Hafsa se ga Kiran Usman ya shigo, na dauka Bayan mun gaisa yace min
” Kamar Baba na gani a wajen daurin aure a Kano ko?’
Nace
” It’s possible mun zo biki Kano ne”
Se yace min
” Nima Ina kanon can we meet?”
Nayi shiru Ina tunanin kashedin Baba kafin dai nace
” Amma kana zuwa zaka tafi?”
Yayi murmushi yace
” Eh!”
Na tura Masa address din Babu jimawa kuwa se gashi ya kirani, na fita ba tareda na Bari Ammi ta sani ba, wani kofar gida muka tsaya nesa da gidan, ya fito a mota Yana Bina da kallo with lots of admiration yace
” Kinyi kyau sosae! Ashe kina gayu haka”
Na danyi dariya nace
“Wai gayu ba hakan ake cewa bafa”
Yayi dariya yace
” To me ake cewa?”
Na noke kafadata nace
” Zuwa zakai ka Nemo Amma ba gayu bane”
Ya marairaice fuska yace
” To ya maganar mu, ki fada min gaskiya me yasa bakya Sona?”
Na girgiza Kai na nace
” Nifa ban taba cewa bana sonka ba, it’s just that ni bazan iya aurenka ba”
” Saboda me?”
Ya tambaya Yana tsareni da idon shi, na fara Wasa da hannuna nace
” Then lokacin da naki yadda saboda kana da aure ne…”
“Yanzun fa?”
Na kalleshi sannan na sunkuyar da kaina nace
” An bada ni wallahi inada Wanda zan aura”
Ya gyada kan shi fuskar shi looks disappointed yace
” Babu damuwa Allah ya Sanya alkhairi”
Na kasa cewa komai, se ya bude motar ya shiga tareda Miko min littafi yace
” I thought you might like it”
Na saka hannu na karba, wani American novel ne, na Masa godiya sannan yace min
” Akwai wani app radish da light reader akwai novels sosae se ki dinga karatu acan. Allah ya Sanya alkhairi, Ina Miki adduar farin ciki me dorewa!”
Yadda ya fada se naji kamar anyi ripping zuciyata haka na kalleshi cikin sanyin murya nace
” Shi kenan tafiya zakai?”
” To Zama kike so nayi Ina hira da matar wani? Ai Babu dadi”
Se naji Raina baimin Dadi idanuna suka ciko da hawaye, ya lura da hakan Amma se ya kyaleni yayi tafiyar shi, ban sani ba ko shi ne haduwar mu ta karshe? Ashe haduwar da zamuyi a gaba ita zata canja rayuwar mu baki daya!!!

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng  Taken mu a kullum shi ne ” …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *