UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 6 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 6 BY SHATU

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kafin wani lokaci kowa yasan cewar Rayha aure zaayi Mata, hakan yasa Yaya Ismail yaga wannan dama ce gareshi Dan ya aureni, idan yaso zai tsiri karatu se kawai mu fita overseas muyi karatun mu dawo. Ummaah ya samu ya fada Mata abinda yake tunani se tace Masa+

” Ismail me yasa Sofy kawai kake so?”

Saboda Anty jidda ta fara zugata tana fada Mata me yasa zata Bari dan da take ji dashi Wanda akwai high tendency zai iya rike sarautar masarautar Kano ya Kare da auren Yar makiyiyar su, Ummaah ta fara tunanin Anya zata Bari auren yayi.

” Ni kawai Ummaah Ina sonta, Dan Allah kada ki Bari na rabu da ita. Bansan ya zanyi ba”

Da fuskarta a tamke take Dan haka Anty jidda tace Mata tayi, Amma ganin yadda rabin ran nata yake ta marairaice mata yasa ta sassauta tace

” Se kace ba namiji ba. Bari na Kira kawun ka naji”

A lokacin ta Kira Baba Wanda ke zaune gefen Anty Rumasa’u tana zuba mishi abinci, ya Kai hannu itama ta Kai hannu wajen daukar wayar Amma sede ita tayi nasarar dauka. Tana ganin Ummaah ce ta Mika masa tace

” Kace Mata zaka ci abinci!”

Yadda ta fada so authoritative, abin har da mamaki Yana dauka yace zai kirata he’s busy, Anty Rumasa’u tayi murmushi na nasara ta zauna tare da fadin

” Kuma ita Sofy din ba zaka Mata auren ba?”

Ya girgiza Kai yace

” Not now, ba tada wani tsayaye Kuma bayan haka tana son karatu bazan iya tauye ta ba”

Ta tabe baki ranta na masifar kuncin auren da Rayha zatayi, Kuma har ma wata kasar zataje ta zauna not anywhere in Nigeria. Tabbas tayi sake ta ayyana Amma alkawari tayi ni bazan tafi haka ba, me kudi sede Naga kawayena na aura. Bata San Babu lissafin kudi a rayuwata ba, babban abinda zatai min shi ne ta hanani karatu Ina tunanin wannan shi ne mafi munin Abu. Bayan Baba ya kammalla cin abinci ya Kira Ummaah wadda ta cika fam saboda a ganin ta Baba yayi kadan ta Kira yace Mata he’s busy. Tana dauka tace

” Har ni Babandi Zan Kira kace wai busy?”

Ya sassauta murya yace

” Ba hakan bane, kinsan baa son mutum na cin abinci Yana magana. Ai gashi na kiraki yanzun”

Tace

” Zancen auren Rayhana ne, sede kawai naji ka bawa Fahad aurenta? Me hakan ke nufi”

Ya kosa da maganar Amma hakan yace

” Kiyi hakuri ban samu shigowa bane ba. Kuma kinsan maganar abin yazo da gaggawa ne”

Yaya Ismail dake gefenta se ce mata yake Dan Allah tayi maganar da ya fada Mata ba zancen wata Rayha ba.

” Zancen Ismail ne yayi min maganar Yana son uwata Sofy”

A bazata abin yazo ma Baba Dan haka ya gyara zaman shi, ya tashi ya zauna, shi fa baya son auren zumunci itama Rayha abinda yasa ya amince abin yazo so sudden Kuma ya fahimci daga ita har Ammi duka sunyi naam, plus Yaya Fahad is aloof from the world, basa shiga matsalar family shiyasa ya yadda Kuma Baban su sunada wani kyakyawawan alaka da Baba Dan ko cikin Yan uwanka akwai Wanda taku tafi zuwa daya to shiyasa without hesitation ya amince. Amma maganata da Ismail ba Abu bane me yiwuwa ba, yasan takun sakar dake tsakanin Ammi da Ummaah ya Kuma San Ammi ba zata taba son wannan abin ba. Dan haka yace

” Ina ganinu bar maganar nan kawai, Kinga Sofy nawa take da har Zan Mata aure”

Ummaah ta cire wayar a kunnenta ta Kara mayarwa to be sure cewar dashi take magana tace

STORY CONTINUES BELOW

” Amma nasan dai Sofy ta girmi Rayha, kadai kawo wani dalilin ba wannan ba”

” Ba yanzun Zan Mata aure ba Amma na bawa Ismail damar take zuwa zance gurin ta idan har ta amince to lokaci nayi Zan bashi ita”

Se ta saki ajiyar zuciya da duk tunanin ta abinda take ganin tana da iko dashi ke son zame Mata wani abin daban. Sukai sallama ya aje wayar tareda dafa kanshi, lokuta da dama Yana jin kamar a daddaure yake, Yana jin tamkar rayuwar shi ba tashi ba ce wani ke jagorantar ta. A hankali ya Mike ya fito zuwa part din mu dake Babu kowa a ciki, ya tura kofar yaga yadda Yana ta cika gurin ga kura ko Ina yayi datti. Yayi shiru yana hango yadda muke Kai kawo cikin gurin, se ya fara tuhumar kanshi dalilin da yasa ya Kore mu, me yasa yace mu koma Gumel, shi dai yasan Rumasa’u tace Masa ita kadai take son Zama Funtua, ya dinga rokonta yace sede ya zaba ko mu ko ita shi ne dalilin sakin Ammi da yayi sannan ya dawo da ita ya maida mu Gumel. Zama yayi gefen da take yawan Zama he felt he missed her, ya tuna yau asbar ya kamata ace ya tafi Gumel kamar yadda ya dace Amma Bai San dalili ba Bai ma je ba, se ya Ciro wayar shi ya fara dialing number Ammi seda ta kusa katsewa kafin Ammi ta dauka

” Hajara!”

Ya ambata a hankali, Ammi se taji Baba ya koma Mata Baba na da kafin ta tafi aikin hajji, kafin komai ya lalace. Ta gaishe shi se yace

“Jiya ban zo ba, aiki yayi min yawa”

Dama Ammi ta gama fada a ranar Friday din da Bai zo ba, saboda mun gama girki da komai Amma bai Kira yace ba zai zo ba se hakura mukai da jiranshi muka kwanta, Dan Hala se ya Sosa Mata inda yake Mata kaikayi. Yace

” Kaji tsoron Allah, ka sani Nima inada iyaye Kuma aura ta kayi, abinda kake min Allah zai saka min. Kuma wallahi indai har ka cuceni Dan ka farantawa matar ka Rai Allah ya Isa bazan taba yafe muku ba!!!”

Gabana ya Fadi jin abinda ta fada, nayi saurin komawa da baya Ina jin gaba daya jikina yayi sanyi, abin ya Kai ga hakan kenan. Na koma dakin mu na samu Rayha ana Mata gyaran jiki Dan bikin sati uku kadai ya rage, idan na kalle ta se naji kamar kada ta tafi, to Amma hakan rayuwar take da mutuwa ce ma haka zata wuce. Ranar haka na wuni jikina a sanyaye nasan kullum Ina adduar Allah ya kawo ranar da Baba da Ammi zasu shirya kamar da to amma nasan Allah ya karba kawai anyi delaying effect dinta dan a jarrabi Imani na, as long as I live to I’ll hold on na cigaba da addua.

Shirye shirye sosae ya kankama Ammi kullum tana tafe a hakan ma Allah ya taimaka ba Zama Rayha zatayi ba da bansan wanne shiri Ammi zatayi ba, ana two weeks zuwa biki a kawo lefenta, Kaya sunyi kyau se San barka da Kuma fatan zaman lafiya.

Ranar alhamis shi ne ranar kamu Wanda zaayi a farfajiyar gidan Gwoggo, na gama shiryawa cikin wani dakakken lace peach me manyan holes a jiki, aka min fitted kimolly  ta zauna jikina cas, gidan shiru saboda duk yawancin an tafi wajen kamun, Nima nazo daukar ma Rayna Abu ne, dama friends dinmu da yawa daga Bakori sunzo saboda shi ne biki na farko da zaayi a set dinmu. Na fito Bayan na Gama na taho na hadu da Yaya Ismail na zaune saman mota rike da wayar shi, ganin Bai ganni ba se nayi saurin juyawa Dan nabi dayar a hanyar Amma Ina ya riga da ya ganni, ya sakko ya karaso inda nake Yana sakin murmushi yace

” Da tuni kema amarya ce yau”

Na danyi murmushi nace

” Amaryar wa?”

Yace

” Tawa Mana! Akwai Wanda yake son ki Bayan ni. Kawu ya bani izinin na dinga zuwa gurin ki”

Na Harare shi Ina tafiya a raina nace zakaga izini, har inda ake taron ya bini, Ina shiga ya cigaba da bina na Isa inda Ammi ke zaune na Dan Mata magana a kunne sannan na gaida bakinta, na barshi tsaye Yana gaida Ammi data amsa Babu walwala. Guri na samu na zauna cikin friends din mu Shima ya zauna Dan gefe na. Munata fira se naji tsaki a baya na, hakan yasa na juya idanuna Suka sauka akan Hanifan Anty jidda, na kalleta kamar yadda take kallona se nayi murmushi nace

” Hanifa kunzo Ashe?”

Ta kalleni ta Dan Bata fuska tace

” Yeah!”

Se na kyaleta dama na Mata magana saboda nasan duk Wanda yazo taron danmu yazo, mikewa Yaya Ismail yayi yace min

” I’m leaving, please idan na Kira ki ki dauka”

Nace

” I didn’t promise that”

Ya langwabar da kanshi yace

” Pleaseeeee Baby!”

Yadda yaja please din se da naji sanyi a jikina nayi saurin gyada Masa Kai ya tafi, hakan yasa na maida hankalina kacokan akan event din, ana Kama amarya aka tashi a bikin. Friends dinmu nasa a motocin friends Yaya Fahad dukda bamu da nisa Amma at least karamci ga bakin ka. Na Gama alwala a dakin Gwoggo naji an dafa ni, na juyo na dubi Hanifa nace

” What’s up?”

Ta zauna tace

” Ina son na Miki magana akan Yaya Ismail”

Na Dan daga girata nace

” Me ya faru da Yaya Ismail din?”

Cikin nutsuwa kamar yadda nake magana cikin nutsuwa haka take, wasu abubuwan namu suna yanayi dukda maganar da take min na fahimci she’s angry Amma ko Wanda ke dakin Basu fahimci fada muke ba, I remembered lokuta da dama idan na Gama fada na, ni Ina ganin na Gama fadan he’ll just kiss me and say bana game fada kike ko magana, wannan se ya Kara Bata min Rai.

” Yaya Ismail Naga Yana shishige Miki, baki da labarin shi din nawa ne ni daya?”

Na danyi murmushi nace

” Kamar yadda bakin ki ya fada shishige min yake bani ke shishigge masa ba. Macen data Isa da saurayin ta Bata fada da wata akan shi, saboda naturally zakiga idon shi akanta kawai yake”

Na fahimci maganata ta Bata Mata Rai, ta Dan kalleni sannan tace

” Wallahi kiyi nesa dashi I’m warning you..”

Banma batta ta karasa ba na wuce nayi sallah sannan na koma gida.Daidai yadda circle din ke juyawa alamar Yana Neman network din da zaiyi min loading result din Nima Hala zuciyata ke bugawa, hannuna suka yayi gumi Amma na kasa dauke hannun daga kan wayar, wajen minti uku Suka wuce se gashi an watso min result din, na goge hannuna Dan wayar Taki dannuwa na dauka sannan na fara scrolling kasa Ina bin courses guda tara da nayi waec dasu daya Bayan daya, kowanne na kalla sede na sauke ajiyar zuciya na furta Alhamdulillah. Ba karamin tallafi na samu daga Allah ba Dan na San ba kokarina ko nacin karatu na yasa na samu wannan kyakyawawan result din ba. Uku daga ciki including maths, physics da biology B2 ne Dani sauran shidan duka A1 ne. Nayi sujaddar godiya sannan na duba result din Rayha itama tayi kokari Babu wani matsala na fito inda Ammi ke zaune na Mika Mata screenshot din da nayi, ta rungume ni tana hamdala. Customers dinta na ta Mana murnar bayan ta fada musu. Komawa daki nayi na Kira Baba a waya na fada Masa ya nuna jin dadinshi sannan yace na fada Masa duk abinda nake so zaiyi min, nace Masa to zanyi tunani. Screenshot din na turawa Yaya Fahad da Rayha Wanda suka kusan wata daya a wata kasar, ta bar mu da kewar ta kullum na kalla empty space din daya kamata ace ita ke kwance senaji zuciyata ta karye, to yazanyi auren kenan.

+

Se Kuma aka nutsa fafutukar admission dina yau ace muyi kaza gobe muyi. Haka nan dai na samu har lokacin da zanyi post utme yazo da farko Ammi tace zata rakani Zaria saboda Baba na can wajen sarauniyar Mata, se Kuma yace Mata ai ba se taje ba zai turo Dr Bature yazo ya dauke ni. Na kalli Ammi nace

” Kuma shi doctor ne zai zo”

Se ta girgiza Kai tace

” A’a za akai ki Kano idan yaso se ku hadu acan”

Na Bata fuska bawai bana son ganin shi bane Ina son na ganshi har Raina I’m badly missing him, but kunyar shi nakeji sosae. Ganin yanayi yasa tace

” Bature ne fa ba wani ba, ya Naga fuskar ki haka?”

Na tura bakina nace

” Ammi fa yace Yana Sona ne wai dama ni yake jira se yayi aure”

Maimaikon Naga mamaki a fuskarta se kawai Naga kallona kawai take kafin ta dauke kanta kawai ta maida kan turaren wutar da take filling cikin buckets. Na dawo kusa da ita Ina fadin

” Ammi to kice wani Abu Mana”

Tayi murmushi tace

” To ke bakya son shi ne?”

Na girgiza kaina subconsciously nace

” Tsoro nake kada Baba yace Nima zaiyi min aure”

Se tayi murmushi tace

” Wayace Miki haka? Bazai Miki ba itama Rayha saboda Fahad zai tafi wata kasar yasa akai Mata aure if not da se tayi nisa a karatun ko kuma ma ta Kai karshe.”

Na sauke ajiyar zuciya sannan cikeda wauta nace

” To Ammi nace Masa na yadda”

Tayi dariya tace

” A’a ni bansani ba…”

Na rukunkume ta Ina fadin

” Ammi please naaa!”

Tayi dariya sosae kafin yace

” To sake ni na fada Miki”

Na saketa tareda Zama na Bata dukkan attention Dina, I so much want to be together with him, Amma Kuma I need guidance, tun lokacin da ya fada min cewar shi fa Yana Sona na nemi nutsuwata na rasa, I remembered ranar ko karasa wayar bamuyi ba na kashe wayar, Shima se ya kyaleni kawai sede kullum zai  turon message Yana tambayar yadda nake, I kind of reply with a single word shi kenan.

STORY CONTINUES BELOW

” Yanzun period kike ko?”

Na gyada kaina

” Idan kikai tsarki se kiyi istikhara kin iya ki?”

Nanma na Kara gyada kaina,

” That’s good, ki bashi lokaci kada ki zurfafa da yawa rayuwar nan is full of betrayals, kafin kayi aure kana da damar canja abubuwa da yawa, you have choice Amma Bayan ka Shiga choices din are limited, bana son daya daga cikin ku ya dandana zafin hakan, Ina son kuyi rayuwar aure me dadi wadda zata daure ba yadda BAHAUSHE yake yi ba”

Se na kalleta dukda tana kokarin danne abubuwan da takeji Amma akwai lokuta da dama da Zan same ta daki tana kuka, na fahimci har yanzun son Baba na ranta, ni Kuma Ina ayyana idan da ni ce da tuni na nemi saki ya sakeni na bar Masa gidan shi, se daga baya  na fahimci Ashe mune yasa Ammi ta dinga compromising Zama da Baba, ba zata iya tafiya ta barmu ba.

Da daddare na hada duk abinda nasan zanyi amfani dashi, hatta kayan da Zan saka seda na fito dashi,na yiwa Ammi sallama na tafi dakina, Ina shiga na tarar da wayata tana haske Dan a silent take, na karasa Ina kallon caller ID se Naga Dr Bature ne, kamar bazan dauka ba se Kuma kawai na dauka, Ina gaishe shi naji ya sauke ajiyar zuciya

” Kin gama gudun kenan?”

Na samu guri na zauna nace

” Ni fa ba gudu nayi ba, ya aiki?”

Maimaikon ya amsa tambayar se yace

” To idan ba guduwa kikai ba me kikayi”

Na danyi shiru holding on to my breath nace

” Nasan aiki sun maka yawa shiyasa Naga kawai na barka kayi focussing “

Yayi dariya a hankali yace

” Da kin kirani da kinyi relieving lot of stress”

Se nayi shiru Ina kokarin assimilating abinda ya fada, Yana nufin idan yaji muryata zata Kore Masa gajiyar da yake ciki, bansan na kwanta saman gadon ba Ina Kara rike wayar zuwa kunnena. Bamu Kara minti biyu ba yace nayi bacci yadda Zan samu nayi exams din cikin sauki. Dana kwanta Sena fara tunano hirar mu, na dauki wayarna Shiga Whatsapp akan profile din shi, na bude hoton shi nayi zooming, ni na dauke shi hoton ranar daurin auren Rayha, Yana sanye da coffee din yard me taushi, dake fari ne sosae tunda munsan katsinawa yadda suke, bashi da jiki siriri ne Amma saboda Yana cikin afuwar rayuwa yayi Dan Kumari kadan, he looks exactly like typical bakatsine. Hatta accent dinsa zaka San shi Dan can ne, duk da muma saboda tashin can yasa idan Ina magana ana ganin katsina in me Amma nashi is obvious daya na magana zakai placing din shi inda ya dace. Kyakyawa ne na gaske, kamar yadda kuka sani shi haifaffen Funtua ne Amma mahaifin  shi dan asalin Maska ne, mahaifiyar shi Kuma Yar Faskari ce. Asalin sunan shi Jaafar sunan kakan shi ne, Amma dake Bature yawancin suna ne da zaka samu a Funtua kamar yadda zakaji Babandi a Gumel, kaji Babawo a ringim kaji Babangid a hadejia, kaji Ambaby a kazaure.1

Washegari ana idar da sallar asuba cousin dina da zai kaini Kano yazo, Ina zaune parlor Ina jiran shi, Yana zuwa Ammi ta dauki basket din data hada min abinci muka fito, Dana gaishe shi se na kunna wayata Ina Kara duba PQ, shikam Yana ta driving din shi har muka Isa inda zamu hadu da doctor, nayi Masa godiya ya juya mu Kuma muka dauka hanya. Tunda na muka hada Ido na dauke kaina ko gaishe shi banyi ba se shi ne yace

” Good morning!”

Na rufe fuskata feeling embarrassed nace

” To bani Zan fara gaishe ka ba, shi ne zaka gaisheni”

Yayi chuckling yace

” Naga har yanzun kunyata kike ji ai, ni bansan Yan Gumel da kunya ba”

Na dago na harareshi nace

” Ni ba kunya nake ji ba fa”

Hankalin shi na kan titi yace

” To fada min idan ba kunya kike ji ba meye”

Na tura bakina gabana, Wanda har ya fara Kama jikina nace

” Ni Babu komai”

Yace

” To kin amince duk Wanda ba gani nace Masa ke budurwata ce Kuma Zan aureki?’

Nayi shiru Ina mamakin yadda yake zaro zance, se can nace

” A’a ba yanzun ba”

Ya zaro Ido da yasa nayi dariya yace

” Me kike nufi bakya Sona ?”

Na Bata Rai nace

” Kuma fa exams zanyi Amma kana ta mini zancen soyayya”

Se da yayi dariya me isar shi kafin yace nayi karatu tunda ni bana gajiya. Har mukaje Zaria I was avoiding Hira dashi na fake da exams. Bamu Jima ba aka fara test exercise din, tamkar Shan ruwa haka na tsarge ta. Dama ana raba Mana question paper kafin ace a fara na juya tawa na fara solving physics din dake first section, nayi wajen 10 questions naji an daka min tsawa a kaina, hannuna ya saki pencil din na dago jikina na rawa, wani dattijo ne sanye da glasses yace

” Who ask you to start? Stand up”

Nayi saurin na Mike Ina kokarin composing kaina, ya dauki paper ya fara bin abinda na rubuta, yasa hannu ya dauki plain paper da Akai Mana providing saboda rough work, ya kalla sannan ya kalleni yace Na biyo shi, Ina ta addua a raina Allah yasa ba korata zasuyi ba, bakina Kuma yaki budewa ya bada hakuri, wani secluded seat ya kaini yace na zauna Kar na Kara rubutu se an bani instructions, cikin sauri har bakina na hardewa nayi Masa godiya sannan na zauna, wani middle age man yazo Yana tambayar shi abinda ya faru ya dakko Masa rough paper yace

” Within this 2 mins tayi wannan, yarinyar is gifted gaskiya”

Na maida kaina kasa Ina fidgeting hannuna har aka ce a fara, kafin wani lokaci tuni na cigaba da attempting questions din zuwa awa daya na Gama, ko da Wasa mutumin Bai bar kaina ba, Dan na fahimci gani yake zanyi malpractice ne, Ina kammalla wa yace na Kara bi na duba akwai sauran time, haka na cigaba da dubawa har mutane Suka fara gamawa. Nayi submitting sannan na fita Ina jin I’m contented da abinda na rubuta. Ina fitowa na nufi motar shi,Yana zaune seat din driver da kafafun shi awaje yana waya, cup na dauka na hada tea me kauri sannan na fara gulping dinsa a makogaro na. Seda na shanye sannan na dakko chips din na fara ci, ya gama wayar ya tambayeni ya exams din nace alhamdulillah sannan Shima na hada Masa tea da sauran na bashi, Yana gamawa muka dauki hanya. Tunda muka fara tafiya yake min hira duk yadda nake nokewa seda na saki jiki dashi. Muka ta hira na Kara fahimtar abubuwa da dama a tattare dashi.Baba ya biyo Ammi daki, tana zaune ta maida kanta kan wani karamin littafi da take lissafi a ciki, dukda ba wai gane abinda take takeyi ba Amma kokari take wajen ganin ta nuna karfin zuciyar ta,Yana shigowa ya karbi pen din hannunta ya wulla tsakiyar gadon, ta dago idanunta ta zube cikin nashi da suke boiling da masifa, Shima kallonta ya tsaya Yi na wajen mintina uku seda tabbatar kallon yayi tasiri a kanshi kafin tace+

” Baban Sofy”

Se ya samu guri ya zauna, ya riko hannunta Wanda ba Zama ta iya tuna last da yake kallonta with admiration ba,

” Me yasa Kika koyi fada, kwana biyu ne kawai zatayi ta tafi”

Ta girgiza kanta tace

” A’a taje gidan Gwoggo ta zauna!”

Ta fada tana karbe hannunta daga nashi,ya Jima Yana lallashin ta cikin nutsuwa tace ita Bata yarda ba se kawai ya Mike ya fito, ita Anty Rumasa’u tunanin ta tunda ya Shiga dakin da masifa expectation dinta ya ciwa Ammi mutunci ko ya saketa, ko ma ya daketa ita dai burinta taga Ammi ta wulakanta, ganin shi ya fito a sanyaye Kuma tunda ya Shiga dakin duk yadda ta kasa kunne bata ji Koda tarin su ba yasa hankalinta yayi mummunan tashi ba dai aikin ya lalace ba? Sede Babu me Bata amsa, akwatin ta ya dauka yace

” Muje ki zauna gidan Gwoggo!”

Ta tattaro duk wani karfin gwiwa tace

” Wanne irin gidan Gwoggo ni nan gidan Zan kwana ai na riga na fada maka”

Tsaki yayi yace

” Rumasa’u why are you so naughty, nace ba anan Zaki zauna ba”

Ya fada Yana Dan daga Mata murya, ganin ya fara hasala se kawai ta bi bayan shi kamar zuciyar ta zata fito Dan bakin ciki.

Bansan Ina Ammi ta samu karfin gwiwa ba, Amma nasan dai me hakuri Bai iya fushi ba ko kadan, nasan Ammi tayi hakuri ko nace tana kan Yi ma, Amma wannan tsakuwa da ta tauna tabbas aya taji tsoro, se Baba ya Dan dawo hayyacin shi abubuwa da dama da yakeyi se ya daina, badai su koma kamar yadda suke da ba Amma Kuma an samu cigba. Ita kuwa Bata Kara zuwa gidan mu ba, ranar Monday na raka Baba gidan Gwoggo anan na sameta ta Gama shiryawa zasu koma Funtua, kamar nayi dariya yadda naga tana ta hararata amma na Dan daidaita na gaishe ta na shige wajen Gwoggo abuna. Seda zasu tafi sannan muka wuce tare zanje Registration, tun a hanya Hira kawai muke ni da Baba. Anan ya ke tambayata

” Sofy daughter, Ummaah ta min magana akan ke da Ismail”

Na danyi murmushi Ina jin kunya tareda kallon bangaren Anty Rumasa’u dake bacci Kain da nain, se da ya Kuma cemin

” Ina jinki, tace min wai tana son ki aura Ismail ne, kin yadda?’

Na girgiza kaina Dan kada na Bari wannan kunyan yasa na cuci kaina, nace

” A’a Baba ni ba komai tsakanin mu”

Ta rear mirror ya kalleni sannan ya maida kan shi kan titi yace

” Are you sure? Bature fa?”

Gabana seda ya Fadi na sunkuyar da kaina, abinda nake ta gudu kenan wannan tambayar hi nake kamar na nutse cikin seat din motar, yayi murmushi lovingly yace

” Kar kiji kunyata, Ina son nayi coming da decision, bana son nayi abinda zai Bata ranki ko na Ammin ki”

Hakan daya fada yasa naji dadi sosae, na sauke ajiyar zuciya nace

” Ni dai Baba I want Dr.”

Words din na fita a bakina ban Kara cewa komai ba, Baba ya nuna min dadin daya ji sannan yace min Bature tun Ina SS1 ya fada Masa kudurin shi Amma se ya dakatar dashi akan ya Bari se na Gama secondary Shima ba wai aure zamuyi ba Aa kawai dai ya dinga zuwa gurina mu shirya kanmu Kuma mu fuskanci juna. Sannan ya nuna min yau na riga na kulle duk wata kofar kula wani, baya son Kama ni da wani Ina dating Dole na tsaya akan magana daya. Idan ya dawo zai bawa Bature aurena officially.

STORY CONTINUES BELOW

A Funtua na kwana gidan ta, memories din zaman mu ya dinga dawo min, tunda muka Isa na Taya ta shara muka gyara gidan sannan nace Mata Ina son nayi wanka, na zata ba zata barni na zauna ba Ashe Gwoggo ce ta ja Mata kunne ta Kuma kwantar wa da Ammi hankali shi ne dalilin da yasa Ammi ta barni na biyo su. Washegari na tafi Zaria kwana na biyu Allah ya taimaka na kammalla komai so banma Kara kwana Funtua ba na wuce Gumel na barta tana ta bacin rai.

Bayan an gama wannan se Kuma Shirin tafiyata Zaria ya dakko Hanya,Ammi ta Gama shirya min komai, da kanta itada Kawu dake kaimu unguwa ta rakani Zaria,ana saura kwanaki uku Zan tafi Zaria Likita yazo,dama ya fada min zaizo Dan haka na fadawa Ammi ta fadawa Baba. Tun safe dana tashi nayi duk abinda ya kamata na nayi. Ammi ta hada abinci da zaici Wanda normal abinci da muke ci a gida. Wajen karfe daya na idar da sallar azahar Ina sanye da shadda blue black dinkin skirt da riga, nayi kyau saboda duhun kayan akan fatata me haske, wayata dake aje kan cetre table ta fara ringing, na Mika hannuna na dauka Ina Dan murmushi nace

” Ka karaso?”

Yace yanzun zai shigo, na Mike na nade praying mat din na fadawa Ammi sannan na wuce dakin mu na daura dankwali , Ina jin gaisawar shi shida Ammi sannan na fito Bayan ta koma daki, zama nayi Ina maida Masa martanin Murmushin da yake min nace

” Barka da zuwa! Ya Hanya?”

Ya kalleni yace

” Kinyi kyau sosae! Ya kike?”

Na langwabar da kaina nace

” I’m fine”

Ammi dama ta fada min Baba yace idan yazo na Kai shi ya gaida Gwoggo, se na shiga na fadawa Ammi muka fita dashi, dake Babu nisa a kafa muka karasa gidan, Muna tafiya iskar bazara na Dan kada mu, se naji weather tayi kala da romantic. Muna tafe Muna Hira har muka Isa gidan, Allah ya taimaka ban hadu da kowa ba balle ace banida kunya. Tana parlor an gama girkin shirya abincin Rana, tabbas Gwoggo mutumniyar arziki ce Bata yarda komai aka dafa gidan yayanta maza se an kawo Mata ba, ta taba cemin ci baya ne da saka Ido,gwara a dafa Mata abinda take so. Shi ne ta cigaba Kuma tasan yayanta sunyi arziki. Kullum bazan daina fadar cewa mu Mata mune matsalar kan mu, zakiga namiji yayi aure anyi insisting se ta Kai abinci gidan su mijin, wannan alada ce Amma alaadar bahaushe ce mummunan, kina amarya kilan mijin baya nan Kuma ke kadai a ranki baki son girki Amma se kinyi kin aika, Kuma ita tana da yaya ko an Kai abincin ba Isa zaiyi ba Amma Dole se an ga me Kika ci, me ya kawo Kika dafa, ya kamata wannan alaadar ta tsaya a hakan.

Tana cikin daki, na mishi tayin Zama sannan na wuce bedroom dinta, ta gama shiryawa cikin shadda irin ta jikina, Ammi ce ta dinka Mana farkon fara business dinta, ni da Gwoggo iri daya, Rayha da Baba ta Dan ladin Gumel. Tayi kyau ta fito bayan na fada Mata yazo Yana parlon ta. Ta kalleni taga Ina rufe fuskata feeling shy, ta Dan daki bayana tace

” Takwara ta tayi goshi”

Nayi murmushi muka tafi, cikin girmamawa Suka gaisa sannan Suka tsokani juna na kakkanni, na zauna se murmushi nake, abinci tasa na zubo dukda nace Mata an daga mishi abinci acan Amma tace wai kishi nake Shima ya biye ta Wai duk abuna gurin ta zaici, se kawai na zauna helplessly Ina karatu cikin wayata, seda ya gama ya saki jikin shi da yasa naji dadi sannan ya kammalla, na kwashe kayan. Muna Shirin fitowa naji sallamar Ummaah a bakin kofa, na kalli gurin da sauri tana tsaye itada Ismail da Yaya Nabiha. Na Dan hade fuska, Gwoggo tace

” Mutanen Kano, barkan ku da Hanya. Kaga Jaafar har kwa gaisa da Babarka”

Ummaah ta shigo, Ismail ma haka dake kallona kamar idanun shi zasu fado kasa, seda ta zauna sannan na gaishe ta, Bata amsa ba cikin daka min tsawa tace

” Waye wannan?”

Ta fada tana nuna Bature dake durkushe gefe kamar yadda yaga nayi Yana gaishe ta, na Bata Rai nace

” Saurayi na ne”

Wani Mari ta sakar min a kuncin dake kusa da ita tace

” Ke kin Isa! Yaushe aka haifeki da Zaki cemin saurayin ki ne?”

Gwoggo dama ta shiga ciki, karar Marin da Kuma fadan Ummaah ya dawo da ita ciki, ta tsaya fuskarta a hade tace

” Furaira menene haka? Me ya hau kanki!”

Ina gefe Dan na riga Dana Mike saboda bana tunanin tunda Ammi ta haifeni an taba Marina, na gigice idanuna sukai jawur Amma ko mhm bance ba. Ismail ya karaso ya riko min hannuna na kwace ya Kara kaiwa na Kara kwacewa cikin daga murya nace

” Don’t you ever touch me ever again!”

Muryata ta resounding cikin parlon baki daya, se yaja baya saboda ya firgita, Bature ya nufo ni Yana fadin

” Keep calm, kiyi shiru”

Ummaah da Bata amsa Gwoggo ba ta cigaba da hararata a karshe tace

” Kinsan Ismail na sonki ke wacece da Zaki kawo wani da sunan shi kike so? Dan kin samu ya taimaka Miki yace zai aureki, keda matsiyaciyar uwarki!”

Wannan kalmomi sune mafi muni da aka taba fada min, se kawai hawaye Suka fara min zarya, Bature na girgiza min Kai yayinda Nima battling nake kada nayi kuka a gaban su, kada na dizga kaina ko na Bata kofar ganin Lago na. Gwoggo ta girgiza Kai tace Mana mu tafi ta gode da ziyarar mu, Kuma zatayi magana da Bature Kar yaji komai. Ta gefen Ismail nazo fita yayinda Bature ke dayan barin nawa, har lokacin hawaye sunki daina gudu akan kuncina, Ismail ya matso tareda saka hannun shi kan fuskata Yana goge min hawayen da fadin

” Stop crying it’s melting my….”

Marin Dana sakar mishi a fuskar shi ta Hana shi karasa maganar, kowa a parlon seda numfashin shi ya dauke na wucin gadi kafin na nuna shi da yatsa na nace

” Wannan shi ne karshe da hannunka zai taba jikina!!”

Bayan Yan satittika result din post utme ya fita, Allah ya taimaka min na samu na haye. Abinda nake jira kawai shi ne admission list na samu na tafi makaranta Nima, Ina fata idan na danyi nesa da gida wasu abubuwan ba zasu dinga Bata min Rai ba, Zan dan manta cewar uwata a wulakance take wajen babana, duk da hakan ba me yiwuwa bane manta ba Amma dai bahaushe yace kazantar da baka gani ba to tsafta ce.+

A waƱnan lokacin shakuwata da Bature ta Kai wani level Wanda Ina jin ya Zama jinin jikina, dukda Ina kokarin ganin ban Bari sin shi yayi min illa sosae ba, saboda ni mutum ce paranoid ni nasan inada wannan disorder din. Ranar an tashi ana kwalla Rana kasancewar lokacin sanyi Bai shigo ba haka damuna ta riga ta Fadi, Ina zaune kan sofa din shagon Ammi, ita Kuma tana ta attending ma tsirarin customers da suke zuwa yawancin masu sari ne se Kuma masu fitar da anko. Hannuna rike da wani littafi 5 love languages by Gary Chapman, Yana daya daga cikin books din da Usman ya aiko min lokacin da na gama secondary, se wannan satin na fara karantawa, har na Gama da uku cikin goma. Tuna shi da nayi ko idan na dauka littafin se Ina samu kaina da tunanin ko Ina yake? Ki me yake? Kilan ya manta Dani yayi moving. To Amma wannan tunanin tamkar Ina downgrading abinda karfin kaddara zaiyi, lokuta da dama idan na tuna actions Dina se naga me yasa na Bata lokacina. To Amma kowanne mutum akwai path din da Allah ya tsara Masa ya bi.

Murmushi nayi Ina tuna lokutan da yake stalking dina da idanun shi ko ya biyo ni class very early kafin kowa ya fito,a lokacin gani nake ya takura min amma bayan ya tafi nakan Jima Ina kallon empty space din daya kamata ace shi yake zaune Yana min magana da gentle tone din shi Amma baya nan, I can’t deny the fact that I missed him. Maganar da Ammi tayi min akan na binciko Mata wata batik wax yasa na aje litaffin na je na dauko na dawo. Littafin na Kara dauka Amma wannan Karan na maida dukkan hankalina wajen fahimtar me Chapman yake son isar Mana. Love languages guda biyar ne Wanda idan Kai da partner ka bakuyi understanding love language da kake speaking ba to zaayi ta samun matsala. Na farko shi ne words of affirmation, abinda na fahimta shi ne mutanen da suke nuna soyayya ta hanyar zance, shi ne amfani da zallan kalmomi wajen nunawa abinda suke so soyayya, na biyu Kuma quality time, Ina ganin shi ne abinda muke lacking, yawancin mu shi ne language din da muke ji, bawai a bamu gift ba ko zancen baki a’a a bamu lokaci, duk lokacin da kake bukatar abinda kake so ya Zama he’s ko she’s at your disposal. Na uku shi ne gift giving, to yanzun idan kace wannan language din kake ganewa se ace Kai kwadayayye ne you building your relationship based on materialistic. Ba mayiwa kanmu uzuri, may be shi namijin language din da yake ganewa kenan, na hudu shi ne act of service, akwai Wanda zasu bauta maka, being there for you a kowanne lokaci wannan se aga kamar baka da hankali ace kenan namiji kake yiwa hakan ko kuma macen kake yiwa hakan. Na biyar shi ne Wanda I’m strongly against it shi ne physical touch is much common a westerners Amma yanzun muma hausawan mu sun dauka wannan rashin addinin da jahilcin.

Bayan na Kare littafin tas se Naga inda nake Ina cikin quality time shi ne abinda nake ganewa when it comes to love language, na fahimci Likita na a Ina yake Shima, Yana cikin act of service Dan haka min fahimci kanmu so bamuda matsala. A hankali na maida littafin na rufe sannan na janyo wayata Dan na duba WhatsApp Dina Ina budawa message din Rayhana ya fara shigowa, ciki ne da ita, na tabbatar aure na Kara modelling mutum Dan itakam ta Kara nutsuwa more matured than before. Mun Jima Muna Hira har mukai video call sannan mukai sallama bayan sunyi magana da Ammi itama.

Se yamma muka koma gida, Bayan nayi wanka na shiga kitchen Dan hada Mana dinner, Ina aikin Muna waya da likta dake fada min Yana nan isowa cikin weekend din Dan ya ganni

” Sure zaka zo? Kada ranar tazo kace min aiki ya maka yawa”

Na fada Ina juya Irish din dake cikin Mai, yayi dariya da yasa ni murmushi yace

STORY CONTINUES BELOW

” Me yasa baki da mantuwa ne, say daya be fa. Say daya!”

Nayi murmushi Ina sauke ajiyar zuciya nace

” Say dayan Mana, bana son a maimaita hakan”

Daga nan muka tsaya akan Saturday din zaizo, Ina aje wayar call din Baba na shigowa, na dauka na gaishe shi yace

” Ina Hajara inata Kiran ta wayar ta a kashe”

Nace

” Tana daki Bari na Kai Mata”

Na fada Ina aje leak spoon din hannuna nayi bedroom dinta, tana zaune ta shirya cikin wata sleeveless gown, fuskarta look serious saboda lissafin da take bugawa da wayatta, Ina shiga ta dubeni tace

” Nazo ne?”

Kaina na girgiza nace

” A’a dama Baba yace na kawo Miki waya”

Amsa tayi na fita na koma bakin aiki, bansan me sukai discussing ba, se dare Bayan mun Gama cin abinci tace min

” Babanku zai zo da Antyn ku gobe”

Ba tareda na kalleta ba nace

” Oh Allah ya kaimu, Amma ba nan zata sauka ba”

” Shi be ban tabbatar ba”

Se nace

” To Allah ya kaimu, Amma ai no need ya fada Miki indai bawai nan zatayi lodging ba”

Wayata da tayi ringing yasa Bata bani amsa ba, number Ismail ta fara bayyana, hakan yasa na Bata fuska tareda kallon Ammi helplessly nace

” Ammi kina kallo ko”

Se tace

” Ki dai tsayar da hankalin ki guri daya”

Tana Gama fadar haka ta wuce bedroom dinta ta barni zaune Ina tura baki, is not as if ni nace ya Kirani Amma yadda Ammi take nunawa kamar ma ni ke kula shi. Washegari Friday muka Gama shirya komai na taryar Baba, Ina zaune a parlor sanye da wando da riga kaina na daure shi cikin mayafi Dan karami, nayi kyau sosae saboda navy blue din mayafi Akan farar fuskata, hannuna rike da Quran Ina tilawa. Sallama naji hakan yasa na sauke Quran Ina amsawa, a hankali Anty Rumasa’u ta shigo janye da trolley se Ayaan dake biye da ita, Ina tunanin tunda muka bar Funtua bamu sake haduwa dasu ba, na bita da kallo Ina jin daci a bakina saboda tsanar da nayi Mata ba ta Wasa bace, ta karasa shigowa tana Bina da kallon ba hakan taso na kasance ba. Ko Babu komai matar Baba nace Dan haka nace

” Sannu da zuwa”

Ta tabe baki tace

” Ana nan kenan”

Ta fada tana karewa parlon kallo, Wanda yafi nata haduwa da komai, Ayaan ta zauna gefenta tunda Babu Wanda zata iya tunawa cikin mu, ni Kuma na fara kwallawa Ammi Kira Dan bazan iya bar Mata parlon ita daya ba balle tayi implanting wani abun. Kusan tare Suka shigo parlon Ammi daga bedroom Baba daga tsakar gida, na gaishe shi sannan na wuce dakina Ayaan ta biyo baya na kamar yadda Baba yace Mata. Ammi ta kalleta sannan ta kalli Baba tace

” Sannu da zuwa ya Hanya?”

Yace

” Lafiya Lau! Ga Rumasa’u zata zauna tazo bikin cousin dinta ne”

Ammi ta dubi Rumasa’u da ko magana batayi Mata ba tace

” A Ina kenan?”

Se ya Bata Rai yace

” A Ina nake nufi to, nan gidan”

Se Ammi ta Bata Rai tace

” Lokacin daka dawo Dani gidannan baka cemin zamuyi sharing da wata ba wannan gidan nawa ne ni kadai, sede taje wani gidan ta kwana!”

Baba mamaki sosae ya Kama shi Dan Bai taba fada tana fada ba, Dan haka ya Kara harzuka da fadin

” Se na sakeki ki bar gidan Naga karshen gidan ki ne”

” Bismillah! Amma wallahi bazata zauna a gidannan ba kaji na fada maka”

Aikuwa ta juya ta barshi tsaye shi da matar shi suna kallon kallo, ita Anty Rumasa’u ta zata ta gama gamawa da Ammi, dakina ta shigo ta sameni nayi shiru deep in thought hakan ya tabbatar Mata naji komai tace

” Fitar Mata da yarta”

Nace

” Ammi…”

” Zanci ubanki Dan ubanki”

Ai tuni na Mika Ayaan waje dan ban taba jin tayi zagi ba ban Kuma taba ganin ranta ya baci haka ba, a parlor Anty Rumasa’u tace ita Kuma wallahi gidannan tayi niyyar sauka Kuma anan zata zauna. An saka Baba a tsakiyar!

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng  Taken mu a kullum shi ne ” …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *