UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 2 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 2 BY SHATU

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kafin mu baro Gumel Ammi tayi bakuwa, ba kowa bace Banda kishiyar Anty Hadiyya, sunanta Anty zeenatu. Kusan Saar Ammi ce sede ita Bata fi shekaru uku da auren kawu Salman ba, saboda ita tayi karatu shiyasa batayi aure da wuri har haka ba. Ammi tayi mamakin ganin ta,Dan ita she’s very wary of dangin Baba, ita fa idan aka dauke Anty Azeeyza da Anty Safara’u Bata mutunci da kowa, idan an hadu a gaisa, Amma wani special relationship Babu ita a ciki. Anty zeenatu suna gaisawa idan sun hadu Amma they’re not acquainted much. Ta shigo da ita parlo tareda kawo Mata ruwa Suka gaisa, se tace Mata dama tazo gaida Gwoggo shi ne ta leko su gaisa tayi Mata godiya sannan Suka danyi Jim se tace da Ammi+

” Nikam maman Sofy kinata zaune ba Zaki kwaci kanki a gurin su Furaira ba, duk sun bi sun Raina ki, kin ganni nan wallahi Babu shegiyar da ta Isa ta juya ni, yadda take ji gidan ta gidan ta ne haka Nima nake jin nawa gidan. Har yaushe ma Zaki zauna a rinka Miki abinda aka ga dama, wallahi ki Kara taku”

Har seda ta gama sannan Ammi tace Mata ta gode, tasan fa kansu hade yake dasu Ummaah, shi ne Dan gulma zata zo tana wani Mata famfo, sallama sukai  ta tafi tunda ta Fadi abinda ya kawo ta, Kuma Bata ga alamar fuska ba. Baba na dawowa ya cewa Ammi Bai santa da kwashe kwashe ba tayi hankali da mutanen dake shige da fice a gidan.

Bayan mun koma makaranta Baba ya biya ma Ammi aikin hajji, zata tafi itada Gwoggo da Anty Safara’u, tayi ta murna tana farin ciki, tayi mishi godiya har seda yace

” Hajara godiyar nan tayi yawa, nikam meye bazan Miki ba a rayuwata”

Cikin jin dadi tace

” Banyi expecting hakan ba, kaga Dole nayi murna!”

Se yayi murmushi kawai, Yana ayyana yafi shekara biyar Yana son biya Mata Makkah Amma Ummaah na hanawa, wannan ma kawai kyaleta yayi Bai biye Mata ba, ya rasa meye aibun Ammi, me yasa su Basu ganin abubuwa masu kyau da yake gani a tattare da ita. A wañnan Lokacin idan na kalla Ammi da Baba naga shakuwa da kuma yadda suka Zama bangaren junansu se abin Yana bani shaawa, naji Ina cikin shauki, little did I know cewar zaa tarwatsa gidan!

Ammi tana ta Shirin tafiya saudiyya dama ta riga data yaye Anisah, Baba yayi suggesting a kaita gidan Ummaah ta zauna, Ammi tace Masa Bata yadda ba, ta riga ta fadawa Baba cewar Dan ladin gumel zata kaita, se baice komai ba kawai ya amince da hakan dama Ummaah ce ta kitsa mishi hakan, ita niyyar ta idan Ammi ta dawo  ba zata maida Mata Anisah din ba. Da taji shiru Baba baice komai ba ta Kira shi, se yace Mata ai kafin yazo har ta Kai ta Dan ladin gumel, se kuwa ta fara fadan

” Ni Kam Babandi wai wannan yarinyar shanye ka tayi ne ko me? Ni wallahi se naje har Dan ladin gumel din na dakko ta, Naga shegiyar Mata kawai!”

Kawai ya girgiza kan shi yace

” A’a Kar ki je, ai Zan dinga zuwa Ina kawo su”

Ta tabe baki tace

” Ai kai Kam ka Zama mijin tace..”

” Ki daina fadar haka Dan Allah”

” Idan ba shaye ka tayi ba say nawa nace kada ka biya Mata wani Makkah, bakauyiyar Hajaran ko addinin kirki ta sani ne? Amma saboda baka dauek ni a komai ba seda ka biya Mata, kaje ya rage naka”

Shidai ya lallaba ta suka gama waya, Ammi taje Mana visiting anan taji labarin zamu kammalla BECE Kuma gida zamu dawo, Dan haka idan min dawo Bata nan Dole se ta samo wadda zata zauna damu, da farko tace min

” Sofy ko kawai kuje Gumel har na dawo”

Kafin na Bata amsa Rayha tace

” Gumel kuma? Naga kince harda Gwoggo zaku tafi”

STORY CONTINUES BELOW

Ammi tace eh, aikuwa take Rayha tace ba zamu je ba sede mu tafi Dan ladin gumel, nan ni kuma nace

” A’a Ammi gwara a Nemo wata mu zauna da ita, Kinga zamu dinga zuwa islamiyya Kar mu rasa abubuwa da yawa, plus Zama mu iya Zama mu kadai tunda Baba nan”

Ammi ta girgiza Kai tace

” Sofy kinyi tunani, to Amma ba lallae Babanku ya yadda ba, zai iya cewa kuje Kano ko gidan jidda”

Rayha ta Bata Rai tace

” Wallahi Babu inda zanje”

Hararta Ammi tayi tareda Mata kashedi, Ammi Bata taba bamu fuskar Raina dangin Baba ba, dukda Bata son su Amma tasan sune gatan mu Koda Babu ran Baba, Kuma su Basu taba nuna Basu sonmu ba, Basu taba Mana wani Abu na cutarwa ba, sudai ita din ce kawai ba taso.

Bayan ta dawo ta samu Baba da maganar se yace Mata Shima baya son muje ko ina, Amma zai Nemo Mana wadda zata zauna damu, da farko niyyar ta tayi suggesting kanwar ta Rahma da mijinta ya rasu watanni uku Bayan anyi auren, dukda ba wani shiri take da Hajja Babar rahmar ba Amma yanzun tunda sunga a daular da take ciki Dole suka kawar da akai aka rungumu juna, itama Kuma se ta kauda duk grudges ta karbe su, tunda Yan uwanta ne, Babu yadda zaa Yi ta canja hakan.

Har muka dawo a makaranta hutu Baba baiyi deciding me Zama damu ba, itama Ammi Bata Kara ce Masa komai ba saboda Kar yaga ta takura Masa, ana sauran kwana biyu tafiyar zai fita aiki tace

” Baban Sofy baka ce komai akan wadda zata zo ta zauna da yarannan ba”

Se yace Mata

” Karki damu munyi magana da Ummaah, zamu dakko ta Bayan Kun tashi”

Cikin rashin fahimta Ammi tace

” Ummaah Kuma? Ita meye nata a ciki”

Se ya mata wani kallo yace

” Kamar Yaya? Yayata ce fa karki manta”

Ta tabe baki tace

” Masu Yaya, Nima ai inada su”

Se yayi dariya yace

” Ni ba Gori na Miki ba”

Daga haka ya fice Amma ran Ammi ya baci akan wai Ummaah ce zata turo wadda zamu zauna da ita. Bayan kwana biyu muka tafi Kano, a gidan Ummaah muka sauka kamar yadda muka Saba, Gwoggo itama da Anty Safara’u sun riga da sun karaso, su kaita Hira mukuwa munata bawa Ammi sakon abubuwan da zata siyo Mana. Karfe Tara muka raka su airport se karfe daya na dare sannan Suka tashi, Babu Wanda yayi kuka a cikin mu, muka dawo gida washegari Sega Anty Rumasa’u tazo daga Kaduna, tunda tazo muka gaishe ta Muna cin abinci ta amsa sannan ta shige ciki wajen Ummaah, Bata Kara fitowa ba se laasar da Baba yazo zamu tafi, nayi ta mamakin abinda suke fada, da katon trolley dinta aka saka a booth, mu dai munata kallon ikon Allah ni da Rayha, ta bude gefen Baba a gaban mota ta zauna tana taunar chewing gum a hankali cikeda Jan hankali, Baba ya kalleta se yace

” Sofy daughter dawo gaba, Rumasa’u koma baya ki zauna da Rayha”

Ranta a bace ta bude motar Nima na bude, ta bangaje ni Allah yasa Yaya amir din Ummaah ya rikeni da se naje har kasa, ta shiga ta zauna sannan Nima na shiga naji Rayha na cewa

” Anty Rumasa’u kin buge Twin Kuma baki Bata hakuri ba”

Ko kulata batayi ba, Baba ya dauka hanya Bayan ya saka mu duk munyi addua, saboda gajiya se na fara bacci har seda muka je malumfashi sannan na farka, Baba yace

” Kuna jin Yunwa?”

Rayha ta fara amsa shi ya tsaya ya siyo Mana mama da lemo sannan muka Kara daukar Hanya. Bayan mun iso gida muka Taya Anty Rumasa’u ta shigo da kayanta, tuntuni mun tashi daga quarters din asibiti, Baba ya Mana gini a cikin makera anan muke zaune, gidanmu dakuna uku ne, daya Ammi daya Baba se namu, se study room dinmu daga gefe akwai guess room, tun kafin Ammi ta tafi dama tayimin kashedi akan Koda Wasa kada na sake na bar wadda zata zauna damu ta shigar Mata daki, na tabbatar an kulle Mata dakin. A parlor ta zauna har muka gama gyara gidan ni da Rayhana Bata Taya mu ba, seda muka Gama muka dauka trolley dinta dan mukai dakin dake na baki tace

” Ke Sofy Ina Zaki Kai kayan?”

Nace

” Zan Kai Miki guess room ne, har na shimfida Miki bedsheets na Kai maki duvet”

” A dakin Ammin ku Zan zauna”

Na kalleta da mamaki nace

” Ammi kuma? Ai ta kulle dakin ta ta tafi dashi”

Ta Jima a zaune ni kuwa na bar Mata kayan anan, Dan rainin hankali wai dakin Ammi ma, itakam Rayha dariya ta dinga Yi, Baba ya dawo ya same ta a zaune, se ya zauna yace

” Rumasa’u ya kike a zaune har yanzun”

Se ta shagwabe fuska wai bamu nuna Mata dakin da zata zauna ba, Rayha ya Kira Dan daga parlon yana jiyo ni a study room Ina tilawa, tana zuwa yace ta dauka kayan Anty Rumasa’u ta Kai dakin baki, ta kalla Rumasa’u ta kalla tace

” A’a Baba tace wai a dakin Ammi zata zauna, seda muka gyara Mata can”

Inaga ba Anty Rumasa’u ba, hatta Nima seda nayi mamaki da Rayha ta fadawa Baba, Ina jin shi yace

” Shirme kenan, Kai Mata dakin ku to”

Ta Kai Mata dakin mu, se ta biyo bayan Rayha tace duk lokacin da ta Kara Mata haka se ta dake ta, Kuma ta wuce ta je ta daura abinci tunda ita ba baiwar uwarmu bace. Rayha Bata ce komai ba, taje ta kirani muka shiga kitchen Dan dafa abinci, Allah yasa ma Ammi na koya Mana Amma Bata barin mu muyi mu kadai se on supervision!Munyi nisa a girkin, Anty Rumasa’u ta shigo ta dube mu, Rayha ce ta tambayeta ko tana son Abu, Amma nikam barar Maggi kawai nake ban ko kalla inda take ba, ba tace komai ba ta Kara fita daf da zamu Gama ruwan zafin da muka rage ya barowa Rayha a kafarta, ta tsalla ihun da ni kaina seda na yadda laddle din hannuna saboda tsoratar da nayi, abinka da fara gurin yayi ja, kusan Anty Rumasa’u ta fara zuwa tana fadin+

” Uban meye Zaki dinga yiwa mutane ihu ? Bakida hankali ne ko yaya?”

Muryar Baba mukaji yace

” Ruma what’s this? Kin tambayeta me ya sameta tayi karar? This is nonsense!”

Se taja gefe tana kunkuni, ya kaarso ya Kama kafar ya Mata addua sannan suka fita, ranar Babu Wanda yaci abincin se ita daya, Bayan mun dawo daga asibiti da takeaway dinmu, Baba yace ta kwashe kayanta ta koma guest room, tunda ta shiga dakin Bata ma duba time ba kawai ta Kira Ummaah, tana kuka wai Baba yaci Mata mutunci, mun Rai na ta waye ya mutu waye ya dawo!

” Banda abinki keda kwanaki kadan ya rage mulkin gidan ya koma hannunki, meye matsalar ki? Shi dadin humiliation bazai Bari ki manta goal din daya kamata kiyi achieving ba, kada ki manta cin mutuncin dashi da yayan shi Suka Miki, seki Rama akan Hajara, idan har baki kwace wa Hajara farin cikin ta ba, to ki tabbatar Zan canja ki!”

Anty Rumasa’u ta sauke ajiyar zuciya, taji wani karfin gwiwa ya mamaye ta, duk duniya Babu matar data tsana kamar Ammi, tun ranar data fara ganinta matsayin matar Baba taji ta tsane ta haka kurum, ko Dan lemme not put it this way, dama can tana son Baba tunda Ammi ko ta girme ta ba zata Bata shekara biyar ba, dukda ba haduwa suke sosae ba Amma duk lokacin da Suka hadu se Anty Rumasa’u ta jangano wani abin. Baba yasan da hakan Kuma ya kawota ta zauna a gidan mu, shiyasa da abubuwa Suka lalace se naso na Masa uzuri se naji Bai canci uzurina ba.

Bamu da wayon da zamu gane lokacin da table yayi turning, daga disgusting look din da Baba ke yiwa Anty Rumasa’u zuwa wani adoring smile da yake Mata, dukka abin ya faru cikin sauri, kafin mu ankare ta karba ragamar gidan gaba daya, dake ta gama KASU ta je camp, tunda tasan da maganar Zama damu se akai relocating dinta katsina malumfashi, da kyar ta samu da naci da bin connections aka dawo da ita funtua, duk lokacin da zata fita Baba zai kaita, Muna zaune zata Kira tace ta gama yaje ya dakko ta, haka zai fita Koda dawowar shi kenan ya tafi dakko ta. Tun muna ganin normalcy abun har na fara jin tsoro cikin raina. Itama ganin ya fara shigowa hannunta se ta fara amfani da damar ta wajen cuzguna Mana idan baya nan,abinci a dafa Dan kadan Wanda bazai taba Isa ba, ko kuma my dawo daga islamiyya mu tarar Bata dafa ba, Kuma ta Hana mu mu dafa. Kudin da Baba ke bamu ta hannunta yake biyowa se ta siyo sabon piggy bank take zubawa a ciki. Ban taba damuwa ba Koda Rayha ta mini complain akan Anty Rumasa’u da abubuwan da take nace

” Nifa Twin wallahi ban damu ba, saboda nasan komai na duniya lokaci ne, duk abinda akeyi watarana zaa daina”

Cikin damuwa tace

” Amma twin role din Ammi take karbewa fa..”

Na rufe littafin dake gabana nace

” Don’t think too much, bawa bazai iya canja kaddarar shi ba, kawai muyi musu addua”

Shikenan se muka hakura da maganar muka cigaba da Zama Muna kwasar takaici, ni se na daina zaman parlon yawancin rayuwata idan Babu islamiyya to Zaki sameni a study room din mu Ina karatu, ita Kuma Rayha tana kallo ko tana games din ta, yawancin Sudoku ko kuma puzzle, abinda da dai zatayi racking Brain din ta.

Wata ranar Friday, Baba yayi call so a asibiti ya kwana Bai dawo ba, tunda muka tashi wajen seven mukai tilawa se nayi wanka na tafi study room Ina son na gwada solving wani equation da zamuyi a ss1, Ina Yi Ina tsoma Pringles cikin mayonnaise Ina ci, Anty Rumasa’u ta tafi mo monthly clearance dinta, har wajen 10am sannan na fito na tashi Rayha nace

” Twin ke Kika kulle kitchen ne?”

Cikin rashin fahimta tace

” Kitchen Kuma? A’a ni fa tunda nayi wanka nake bacci period pains ke damuna”

Nayi Mata sannu sannan na fita, nasan ko da na tashi kafin Anty Rumasa’u ta fita na debo mayonnaise daga fridge din kitchen, Amma waye zai kulle? Ina nan zaune Ina tunanin yadda Zan bawa cikina hakurin yunwar da nake ji, Rayha ta fito sanye da skirt da riga, ta zauna da fuskar ta da tadan kumbura kadan saboda hormones.

” Ko Anty Rumasa’u ce ta kulle?”

Nayi tsaki nace

” Kai shiyasa Ammi tace miui hankali da ita, to meye abin rufe kitchen tunda abincin ba nata bane”

Haka mukai jugum jugum har wajen daya Baba ya dawo, freezer da zamu dauka drink itama ta Dade da kulleta da cire key din, mukam duk mun Zama marayu, lemo daya idan zaka dauka se ka amsa series of questions kafin ka dauka, ni kuwa bana jurar wannan na kwammata na daina Shan lemon. Duk wannan abubuwan Baba Bai sani ba tunda shi aikin shi ne a gaban shi. Ganin mu zaune yasan Yunwa muke ji, ya zauna Yana tambayar mu ko munci abinci, Rayha idanunta taf da kwalla tace

” Yunwa muke ji Kuma kitchen din a rufe”

Ya maimaita a rufe sannan kuma ya dakko waya ya Kira Anty Rumasa’u, tana dauka yace Mata Ina key, banji me tace ba Amma daga amsar shi na gane abinda ta fada

” Kuma makulli a jakar ki, kafa ce dashi da zai shiga ciki? How can you lock the kitchen and leave this kids starving?!”

Yayi ta fada karshe ta kashe wayar shi se kawai ya dauke mu muka fita ya siya Mana abinci. Bayan ta dawo ta dinga bacin Rai ko Baba Bata yiwa magana ba, Shima Bai kulata ba se ta shiga dakinta, ta fada gado ta Kira Ummaah tareda fada Mata abinda ya faru

” Na gaji Ummaah, kinji tsawar da yayi min Akan kawai na tafi da key din kitchen..”

Tsawa Ummaah ta daka Mata tace

” Rufe min baki shashasha kawai! Hajara ce kawai Target dinki, auren shi zakiyi ki suppressing Hajara. Kinsan yaran nan yadda nake son su, to bashi ba Nima Zan iya mantawa da alamar mu na ci muku mutunci akan su Sofy!”

Duk abubuwa sun faru so quick, kafin mu Gama tunani abubuwa sunyi lalacewar da baza su gyaru ba. Kwata kwata kwanakin Basu wuce arbain zuwa hamsin ba Amma komai ya lalace. Bayan ta gama waya da Ummaah tayi tsaki tareda Kiran mahaifiyar ta wadda ita ce take matsayin cousin din su Baba. Ta gama fada Mata komai itama se tace ta bimu a hankali mission dinta Bai zo ban ba.+

Bayan wani lokaci muka fara shiryar taryar Ammi, Baba dama tuntuni sun Kara komawa ruwa shida Anty Rumasa’u, tunda ta daina takura Mana shikenan. Ranar da Ammi zata dawo mun Gama duk Shirin daya kamata na tarbar ta, Baba zai tafi dakko ta yace muzo muje  mu dakko ta, da farko munata murna zamuje se Kuma muka ji ai da Anty Rumasa’u zamu tafi, se nace Masa suje kawai mu bamu karasa Abu ba. Bai damu ba ta bishi Suka tafi, muka Kara gyara gidan sannan na shiga wanka na fito na shirya cikin blue din atamfa skirt da riga, Zama mukai Muna Dan Hira, Bayan wajen awa hudu zuwa biyar naji tsayuwar mota, da gudu muna rige rigen fita a parlon, daidai lokacin Ammi ke fitowa daga motar ranta a matukar hade, ta danyi kiba kadan Amma tayi duhu Wanda ke da nasaba da ranar da ake kwallawa a can. Da gudu cikin doki na fada jikinta Babu Bata lokaci ta rungume ni jikinta, se ta bude dayan hannunta ma Rayha itama tazo ta rungume ta, ruwa naji ya zubo a wuyana hakan yasa na dakko, se Naga Ammi ke kuka, hakan se ta karyar min da zuciyata Nima na fara kuka tareda kankame ta, Baba ya fito fuskar shi Shima ba wani abin kirki akai se faking murmushi da yake kokarin plastering. Muka shiga ciki shi Kuma ya kwaso kayan daya bayan daya, a parlor ta zauna muka sakata tsakiyar, Anty Rumasa’u ta shigo ta samu guri ta zauna, seda Baba ya shigo da kayan tas sannan Ammi ta tashi ta nufi daki, tana Shiga Baba ya bi bayanta, Anty Rumasa’u dake zaune ranta a hade ta Mike ta koma dakinta. Muka tare kayan gefe sannan muka Shiga shirya Mata abinci, data fito daga ita har Baba mood dinsu ya Dan canja, Zama tayi tana ta shafa kanmu tace

” Sofy kin rame, bakida lafiya ne?”

Na girgiza Kai Ina kokarin Bata amsa Baba yayi beating dina da fadin

” Kinsan dama ita yadda jikinta yake”

Na maida hankalina Ina serving mana abinci cikin tray, se hirar ta koma take bamu labarin saudiyya, har mun fara cin abincin Ammi ta kalleni tace

” Ya baki zubawa Rumasa’u abincin ba? Ko Dan kirata taci anan kawai”

Baba ya aje spoon din shi yace

” No Sofy, zuba Mata kawai ki Kai Mata daki”

Na dauka plate na zuba Mata komai a wadace na nufi dakinta, tana kwance da waya kunnen ta Bata ma ji shigowa ta ba ta cigaba da kuka tana fadin

” Kinga tunda muka hada Ido da ita a airport ta Bata Rai, shi Kuma se rawar Kai yake, jikin shi har mazari yake Mami. Wallahi tunda muka shiga mota ko kulani batayi ba Shima haka se ya dinga Mata shishiggi tana share shi. Baki ji zuciyata ba Mami kamar zata fashe haka nake ji…”

Abincin na aje Mata na fita a dakin with many thoughts running through my mind. To meye tsakanin Baba da Anty Rumasa’u da take wannan maganar ne, na koma parlor muka ci abinci. Har dare ranar tana daki, mu kuwan muna parlor Ammi ta bude Kaya tana ta warewa itada Baba, se bayan maghrib sannan muka kammalla. Da kanta tayi Mana dinner.

Washegari Anty Rumasa’u tana tashi ta shigo parlor ta cewa Ammi tana son magana da Baba, Ammi ta wuce daki ta Kira shi sannan ta dawo dakin mu tana kallon yadda muke gwada kayan da ta kawo Mana, baa Jima ba taji Baba na kiranta hakan yasa ta fito,hannun shi rike da key din motar yace

” Zan Dan ajje Rumasa’u a gurin aiki”

Ammi ta kalleshi se kasa take da kanshi, se tace Allah ya kiyaye ta koma ciki abinta,da ta dawo take tambayar mu tare da Anty Rumasa’u Baba yake fita, muka ce ai wani lokacin har office take raka Shi. Tundaga nan yanayin Ammi ya canja. Bayan ya dawo ta sameshi Yana zaune a daki itama ta zauna tace

STORY CONTINUES BELOW

” Har ka dawo”

Ya shafa kanshi yace

” Na Jima da shigowa”

Ta gyada Kai sannan tace

” Baban Sofy meye tsakanin ka da Rumasa’u ne?”

Ta fada tana tsare shi da idanun ta, da sauri ya dago yace

” Me su Rayha suka fada Miki?”

” Ba fada min sukai ba ni na tambaye su, sunce tare kuke zuwa office, shiyasa nake tambayar ka meye tsakanin ku?”

” Ba abinda kike tunani bane Hajara..!”

” Me nake tunani nace maka? Tambaya ce me sauki kawai amsa nake so”

Yayi Shiru hankalin shi yakai kololuwa a tashi, se gumi take, abinda yake gudu kenan tunda ta dawo ya kasa fada Mata zaiyi aure ba da jimawa ba, ganin yayi shiru Ammi ta mike ta fita, duk tunanin shi ta hakura kenan,inaga Baba bai San wacece mace ba, indai zata iya given up so easily akan abu to ba mace bace. Dakin mu ta shigo tace muzo zata aike mu, Bayan ta gama bamu Aiken tace mu zauna can se ta Kira tace mu dawo. Muka shirya muka dauka sako muka tafi. Bayan tafiyar mu Babu jimawa Baba ya fita, Yana fita Ammi ta dawo parlor ta zauna tana tunanin yadda zatayi, Amma tsoro da fargaba ya hanata tunani da kyau. Tana zaune taji dariyar Rumasa’u tana cewa

” Ayya kwana nawa ya rage, kayi abinda make so…”

Ganin Ammi a zaune a tsakar gida Dan zaman parlon ya rigada ya gundure ta, shiyasa ta fito. Kallon su kawai takeyi, Baba ya fara kame kame Amma ko kalma daya ta gagara fitowa a bakin shi. Anty Rumasa’u tayi wani murmushi Dan dama a hanya tace Masa ya kamata ya Fadi matsayin ta kowa ya sani, Dan kuwan indai Ammi taje Gumel kamar yadda ta tsara karshen sati to zata ji komai. Se yake ce Mata shi tsoron Ammin yake ji ne, se tayi ta dariya Amma a ranta ta kudura se ta tarwatsa wannan understanding dake tsakanin su.

Ammi ta kallesu Amma uffan Bata ce ba, ta gama kwashe kayan da ko Gama bushewa ba suyi ba akan igiya ta Shiga ciki, seda ta musu masauki kan carpet kafin taji duk Basu bushe ba, kofar baya ta bude taje ta fara sabuwar shanya tana makala pegs. Seda ta gama ta jiyo se tayi kicibis da Baba, gefen shi ta rabe zata wuce ya ruko hannunta, ta kalleshi sannan ta kalli hannun kafin ta Kuma kallon shi, cikin dasashiyyar murya da bacin Rai ya gama lalata tace

“Ina aiki, saki hannuna”

Bai saki hannun ba se yace

” Haba Hajara, wai meke damun ki ne?”

Seda ya tsorata da ihun data Masa , Babu shiri ya saki hannun tareda Bata Hanya ta wuce, daki ta koma ta kwanta akan gado ta fara kuka, yanzun duk irin wulakancin da cin kashin data shanye na dangin Baba,da abinda ya tashi saka Mata kenan? Idan dai she’s calculative tasan cewar aure zasuyi tunda a kunnen ta taji Rumasa’u tana fadin kwana nawa ya rage. Jiki a sanyaye Baba ya shigo ya zauna gefenta, yaji wani irin rashin hankali ya mamaye shi jin irin kukan da Ammi keyi

” Wallahi Hajara Ummaah ce tace se na aureta, wallahi bani nace ba”

Ta tashi ta zauna fuskarta tayi jawur abinka da fara, hawaye na zarya kan kuncin ta tace

” Abinda zaka fada min kenan? Kai azzalumi ne bazan taba manta wannan abin ba, Ina lefin idan zaka aureta ka aureta, se ka kawo ta gidana ta kalla sirrina?…”

Ya Kai hannunshi zai riko ta ta kwace da fadin

” Karka taba ni, ka tashi kaje ka fita da ita daga gidannan!”

Ya kalleta irin bakida hankali dinnan, ta Mike tareda nufar kofa tace

” Na fahimci tsoro kakeji ko? Ni Bari naje na koreta”

Da sauri ya karaso ya rike ta yake fadin

” Hajara meke damun ki ne? Have you lost your mind, this is unlike you”

Ta kwace hannunta tace

” I’ve lost my mind? Bari ka gani”

Yayi saurin blocking hanyar tareda dawo da ita gadon ya fara fadin

” Hajara Dan Allah ki saurareni, wallahi gobe Rumasa’u zata bar gidannan Amma yanzun dare yayi. Kuma ko Babu komai she’s my cousin “

” Wallahi kaji na rantse yau zata bar gidannan, ba zata kwana ba, idan Kuma Bata Bari ba, ni Zan bar Mata gidan.kuma zancen cousin da kake Kai wannan ya dama”

Baba Basu taba irin wannan fito na fito shida Ammi ba, she always show him the good side of her, yayi amfani da hakurin ta ya taka ta. Shi duk tunanin shi aljanu ne Suka hau kanta, Dan Bai taba tunanin a right senses dinta zata iya yin Abu makamancin haka ba.

Mata da yawa bawai suna kin auren bane but yadda ake treating Mata idan zaayi auren shine matsala,  approach din shi ne babbar damuwa, matan da ake nuna musu auren bazai Zama wani obstacle da zai raba su ba, suna kwantar da hankalin su.Bayan ya tabbatar zaman Anty Rumasa’u gidan mu Kara lalata komai zaiyi, se ya fita ya sameta a dakin tana zaune tana Shan wani abu cikin cup, Zama yayi tareda fadin+

” Rumasa’u”

Tunda ya shigo take kallon shi, Bai taba shigowa dakin ta ba se wannan lokacin, farin cikin da take ciki yasa Bata lura da Yanayin da yake ciki ba, seda taji yanayin yadda ya Kira sunanta se ta aje cup din tareda kallon shi Amma Bata amsa ba, kudi ya Ciro ya Mika Mata, kafin yayi magana tace

” Kudin meye wannan?”

Ya Sosa kanshi yace

” Kiyi hakuri, Zaki koma gidan Baffanki kafin lokacin da Zan shawo kan Hajara”

Da mamaki ta kalleshi, ranta ba karamin baci yayi ba ta bude baki zatayi magana yace

” Dan Allah Kar kice komai, kiyi packing lokaci na tafiya, dare zaiyi”

A wañnan lokacin tasan idan har tayi fada bazai taimaka ba sede ya Kara hasala shi hakan yasa ta fara kuka tace

” Yanzun doctor a gidanka zaka koreni?…”

” Ba wai korar ki nayi ba, kawai kije idan komai ya lafa seki dawo, keda Zaki dawo dindin gidan ma”

Maganar shi Banda Kara Bata Mata Rai Babu abinda take, ta Mike a fusace tace

” Kana nufin ka zabi matarka a kaina kenan?”

Bai ce Mata komai ba Amma a ranshi Yana ayyana me yasa Mata suna da matsala ne, idan ba haka ba meye na hada kanta da matar shi, shi akan Ammi Babu abinda ba zaiyi ba. Yana tsaye haka ta dauka necessary ta fita a gidan tareda Shan alwashin ranar da zata dawo gidannan mazauna gidan se tayi musu abinda har duniya ta nade ba zasu manta ba.

Bayan ta tafi ya koma gurin Ammi dake kitchen tana hada abinci, ko kallon shi batayi ba, Shima se ya fita kawai Dan yasan ya Bata Mata Rai. Bayan sallar Isha ya dakko mu muka dawo, gidan shiru Babu dadi, Ammi ta gimtse fuska shi Kuma komai daridari yake. Haka gidan ya kasance har karshen sati muka tafi Gumel. Anty Rumasa’u na gidan wani baffanta anan wajen jabiri suke. Ta Kira mamin ta ta fada Mata, hakan yasa matar ta dauki alwashi. A Dan ladin Gumel muka fara sauka ta aje musu tsaraba ta dauka Anisah muka wuni anan, da suka kebe itada Baba ta zauna ta fada Mata halin da take ciki, iyayen mu ne nada se ta Bata hakuri tace Mata watarana komai zai wuce, tayi kokari ta kyautatawa mijin ta ta Kuma rikemu ta kula damu. Se dare muka koma Gumel. Seda mukaje mukaji wai an matso da bikin zuwa sati uku, bayan Gwoggo ta gama tausar Ammi wadda tayi daurewar duniya batayi kuka ba, Amma gaba daya haushin Baba takeji ko gaba suke ya kamata ya fada Mata cewar zaiyi aure. Bayan ta dawo gida ta same mu mun dawo daga gidajen da ta lissafa Mana muje, gidan Yan uwan baban mu. Ta shiga daki ta rufe tayi kuka kamar ranta zai fita, mukam kwana biyu munsan Bata jin dadi kamar yadda ta fada Mana, se bamu dame ta ba, Amma nidai Ina tabbatar wa kaina cewar something somewhere is definitely wrong. Duk lokacin da Naga Ammi tana cikin bacin Rai se naji nawa ran ya baci, idan da akwai abinda Zan bayar Naga ta dawwamma a farin ciki da tabbas zanyi shi.

Washegari muka koma Funtua, Baba Yana asibiti kamar yadda ya fadawa Ammi, se muka maida hankali muka gyara gidan sannan muka Yi girki, se dare Baba ya dawo , lokacin dukka munyi bacci se Ammi dake parlo tana jiran shi. Can Ina bacci nake jin kuka a hankali da maganganu, se na sakko daga gadon da nake kwance na zo kofar parlon na tsaya, daga inda nake Ina hango Ammi da Baba na zaune opposite each other.

” Zakai aure kwanaki kadan Suka rage ba zaka fada min ba, wanne irin Zama muke? Kana ganin ni na isa na hanaka ka aureta? Kasaani tunda na dawo Babu abinda nake tsinta cikin gidannan se bakin ciki da takaici. Ka darsa min abinda bazai taba goguwa a raina ba”

A hankali na sake lafewa jikin curtain din tareda rufe bakina, Baba zaiyi aure? Maganar da yayi ta katse min tunanin da nake

” Ni dai kullum hakuri kawai Zan baki”

Daga haka bai Kara cewa komai ba Ammi ta mike se nayi saurin komawa na kwanta, Amma bacci ko daya ya gagara a idanuna, se juyi nake inajin wani nauyi a zuciyata. Da safe na tashi jikina a mugun sanyaye, ko shara da kyar nayi, nayi wanka sannan na tafi study room, kilan acan I’ll find something pleasurable na karanta. Ina fata karatun se na manta da abubuwan da Suka faru. Wannan kwanakin sun zamo mabudin fara lalacewar abubuwa a gidan mu, Zan iya cewa bayan korar Anty Rumasa’u da Ammi tayi Bata Kara kokarin kwatar kanta ba, daga baya ma se ta tattara komai ta watsar ta Kara rungumar Baban se zaman gidan ya koma lafiya.

Baa dauka lokaci ba akai biki na gani na fada a Gumel, Baba ya cewa Ammi Yana son taje tace Masa ba zata je ba, muma Kuma ba zamu je ba. Se kawai ya tafi shi daya, Bayan ya tafi Ammi ta fada Mana cewar Anty Rumasa’u zata aura Baba, tana son duka muyi hakuri da wasu abubuwan da zamu gani sun canja, kada mu sake muyi Mata rashin kunya sannan duk abinda ta samu na aiki ko aike to muyi Mata.

A Gumel ta fara Zama seda sukai kwanaki bakwai dinsu cif sannan ya dakko ta suka dawo Funtua, ya riga ya saya gidan dake gefen mu ya hada da namu, so part dinta Yana gefenmu, Ammi tayi girki ta Kara gyara gidan, Dan ya canja Mana dukka furniture dinmu. Yayi Mana sabbin paint so se muma gidan ya koma kamar sabo. Basu dawo ba se yamma, ta gate dinta ya shigo shiyasa bamu ji Kara ba. Seda sukai settling sannan ya shigo part dinmu, muna zaune Ina cike form din da zaa Kai Anisah makaranta, Rayha na Shan cornflakes.

” Baba sannu da zuwa!”

Muka hada baki muka Masa sannu da zuwa, ya dauki Anisah ya Mata Wasa Yana amsawa sannan Ammi ta fito tayi kyau cikin wani coffee din material, fuskar ta dauke da murmushi tace

” Sannu da zuwa ya Hanya? Ya amarya Allah ya Sanya alkhairi!”

Yayi murmushi bayan ya zauna yace

” Nagode sosae, Allah ya muku albarka!”

Ta amsa da Amin sannan ta tambaye shi ko a kawo abinci yace Mata Yunwa yake ji, ta zuba Masa sannan ta zuba wani a cikin warmer tace Rayha ta Kai mata. Tasan halin mu duka shiyasa ba tayi gigin aika ni ba. Kafin Rayha ta fito a kitchen din mukaji sallamar Anty Rumasa’u, Ammi ta amsa Mata se gata ta shigo looking elegantly cikin wata atamfa, tayi kyau Babu karya. Tana Murmushin nasara ta shigo ta zauna, Ammi ta Mata tayin Zama, ta zauna kan kujera sannan ta gaida Ammi, muma muka gaishe ta ta amsa tana daukar Anisah wadda ke Wasa da Teddy dinta. Anan taci abinci sannan ta tafi. Gidan ya koma normal, Babu wata matsala, kullum Anty Rumasa’u na part din Ammi anan take yini se dare take tafiya, idan ranar girkinta ne kuwa tun kafin ya dawo zata koma can.Bamu Kara sati daya a gida ba muka koma makaranta, yanzun min Zama manyan Yara min shiga SS classes. Ni na dauki sciences ita Kuma Rayha ta dauka commerce. A lokacin aka raba Mana class Amma dukda haka hostel dinmu daya haka Kuma dakin mu, Ammi tayi wannan kokarin, saboda Bata son a rabamu tafi son yadda take treating dinmu kamar Yan biyu to haka take so mu dore. A wañnan term din na fara period, jikina kamar abinda yake jira kenan se development ya fara. Kafin muyi hutu Nima na fara jin kaina a sahun Yan mata. Visiting din farko da akai Ammi kadai ce tazo se Anisah, abun ya bani mamaki Dan Baba Bai taba missing visiting ba, Koda Yana da aiki zai samu wani ya rike Masa ballantana yanzun ya fara kokarin Zama consultant. Na kasa hakuri nace+

” Ammi ya Baba Bai zo ba?”

Se tayi murmushi tace

” Yaje Zaria”

Se na gyada Kai, lokacin da ta cire hijab dinta zatayi alwala Naga yadda ta rame sosae, Bayan ta idar da sallah nace

” Ammi kinyi rashin lafiya ne?”

Ta girgiza Kai batace koami ba Nima se na Yi shiru Amma duk na damu. Har seda aka fara cewa mutane su tafi sannan ta tashi tafiya, muka hada kayan ta bamu pocket money dinmu dama tuni mun Kai shopping din da akai Mana hostel. Ta tambaye mu ko akwai abinda muke so idan ta koma ta fada Masa nace Babu, Rayha ma haka. Seda ta shiga mota sannan muka juya zuwa hostel, Rayha tace min

” Sofy bakiga changes a tattare da Ammi ba?”

Nace

” Rayhana I’ve noticed, na tambaye ta tace Babu komai”

Rayha ta girgiza Kai tace

” Kodai Anty Rumasa’u ce”

Nayi shiru ban ce komai ba Dan bansan me zance din ba. Muka karasa hostel duk jikina a sanyaye. Tun daga ranar ko me nakeyi se Ammi ta fado min and I’ll be wondering me takeyi, ko wani abin ya sameta, ga karatu tunda ni me naci ce se duk na bi na Kara lalacewa, at a very young age na saka damuwa a cikin raina. A haka a daddafe satittika Suka wuce se gashi wani visiting din yazo, lokacin Ina wani mugun zazzabi da amai. Tun safe da muka tashi Rayha ta debo min ruwa nayi wanka na dawo gado na kwanta, ta shiga tayi wanka ta shirya itama, Babu jimawa aka ce mu zo, a hankali na saka Kaya sannan muka fito Ina rike da hannun Rayha, tunda Ammi ta hango mu tasan Babu lafiya, hakan yasa tayi saurin mikewa tsaye ta nufo inda muke, Ina ganinta se na fada jikinta na fara kuka, ta riko ni ta karaso kan tabarmar da ke shimfide ta zauna Baba da karasowar shi kenan yaje ganin guardian dinmu yace

” Sofy Ashe bakida lafiya?”

Inata kuka ban amsa su ba se Rayha ke musu bayani. Anty Rumasa’u tace

” To meye abin kuka, kiyi hakuri Mana”

Dan kwanciya nayi jikin Ammi, Baba yace da Ammi kawai permission zai karbo su tafi dani gida hankalin shi bazai kwanta ba. Aikuwa visiting din ko awa basuyi ba suka bawa Rayha hakuri muka tafi gida.  Bamu je gida ba asibiti muka wuce, akai running test kafin aka rubuta min drugs muka tafi gida. Baba na parking muka nufi part din mu da taimakon Ammi data rike ni. Ina zuwa nayi wanka se naji Dan dadi a jikina,Nasha tea sannan Nasha magani, Baba ya min allurai se bacci ya daukeni me nauyin gaske. Ban farka ba se daf da sallar maghrib, nayi sallah na Dan ci abinci sannan na Kara kwanciya. Saboda rashin lafiyar da nake se banma lura da Yanayin gidan ba, da yadda suke tafiyar da alamuran su. Se da nayi kwana biyar sannan na ware gaba daya se anan na fahimci gaba daya Baba baya ta Ammi ko da ranar girkin Ammi ne ba zakaga ya zauna part dinmu ba sede ya tattara ya koma can se dare ya dawo idan zaiyi bacci, ko kuma yaki Zama a gidan gaba daya se dare yayi ya dawo ko abinci ta kawo zaice Mata shi ya koshi. Tabbas ko ni abin se ya sakeni. Ranar da Zan koma school ya shigo da safe, ni har na shirya Ina zaune kan sofa a parlor Ina taya Anisah da assignment dinta, Baba ya shigo na gaishe shi ya Dan tsaya yace

” Zaki iya komawa ko?”

Na gyada Kai na Ina murmushi nace

” Eh Baba”

Se ya Dan yiwa Anisah Wasa sannan ya nufi dakin shi, dakin Ammi na leka nace Mata Baba ya shigo fa Yana dakin shi, ta amsa ni sannan Kuma ta fito ta nufi dakin nashi, Bai Jima ba suka fito tana fadin

” Tun yaushe nake fada maka Amma kullum sede kace to”

” Banida kudi!”

Ya fada ba tareda ya kalleta ba, se ta girgiza Kai tace

” Allah ya kawo!”

Ya dubeni yace na tashi mu tafi, nayi ma Ammi sallama sannan muka tafi ko rakani ba tayi ba, a bangaren Anty Rumasa’u ya tsaya ya Ciro kudi daga aljihun shi ya Bata , Ina tsaye Ina kallon su yace

” Wannan zai Isa?”

Tace

” Zaayi manage”

Se ya gyada Kai yace

” Ni Zan wuce Bakori, daga nan Zan wuce Zaria kilan na kwana acan”

Tace

” To Allah ya tsare ya kiyaye Hanya, Sofy Allah ya kiyaye ki gaida Rayha”

Na amsa da Amin sannan muka fito, seda muka bar gidan sannan ta koma part dinta, wani Abu naji ya tokare min makoshi na saboda yadda Baba ke treating Ammi ya banbanta da yadda yake treating Anty Rumasa’u. Tunda muka fara tafiya banyi magana ba Shima Bai ce komai ba seda muka Shiga school ya Yi signing ya dawo Dani ya Kara Mana kudi yace na gaida Rayhana sauri yake shiyasa bazai tsaya su gaisa ba, na Bata hakuri. Daga haka ya tafi na wuce class, Yan class dinmu se daga min hannu suke na zauna can baya Dan an zauna min a seat dina, seda aka gama class din sannan muka gaisa anata tambayata jiki Ina amsawa da sauki. Class din su Rayha na wuce, tana ganina ta rungume ni, Nima haka na zauna gefenta Ina fada Mata sakon gaisuwa daga gurin Baba da Ammi.

Ban fadawa Rayha komai ba muka cigaba da rayuwa a school. Ending term din aka kawo sababbin corpers. Dake ba lesson muke ba yasa bamu sansu ba seda akai hutu muka dawo sannan akai introducing dinsu a gaban assembly. Ni hankalina gaba daya baya kansu Yana kan kuskus din da mukeyi Dani da Na’ila. Seda muka koma hostel naji anata zuzuta daya daga cikin corpers din. Senior samiha tace

” Ni fa wallahi kinsan me ya burgeni dashi? Bakin shi. Zaiyi dadin kiss wallahi”

Ta fada tana dariya tareda rufe fuskar ta, senior Ummiey tace

” Kiji iskanci, wai kiss?”

Tayi dariya tace

” I’m already crushing Usman wallahi”

Ranar duk inda kaje to hirar Usman ake, ni har wata Yar js3 naji tana zancen shi. Na dawo daki nace da Rayha

” Rays wai Dan Allah waye wannan Usman din? Se maganar shi akeyi”

Na’ila dake gefe tace

” Help me ask oooo! An ishe mu da maganar shi fa”

Rayha tace

” Dazun akai introducing dinsa wai sunzo service, Dan Gombe ne ko bauchi, I’m not sure”

Nayi tsaki nace

” Allah na tuba meye a wani namiji duka makaranta sun zuzuce akan shi, kamar ba Bakori girls ba”

Wata Christian dake gefe tace

” Sofy stop saying that, if you see him, you definitely gonna crush on him”

Abin mamaki ban hadu dashi ba duk yadda nake son haduwa dashi Dan Naga meye dashi da ya saka Bakori girls suna drooling. Se karshen term din aka hada programme da zaayi Mana akan career guide Wanda corpers dinmu Suka hada. Gaba daya muka hadu a school theater, Ina zaune a gaban theater gefe na Na’ila ce se Rayha acan Dan nesa damu itama da nata kawayen. Aka fara program din smoothly, can ana tsaka dayi naji theater tayi tsit, na dago kaina daga kan presenter din na mayar kan gentleman din dake shigowa cikin theater, sanye da khaki din corpers, idanuna na dauke daga kanshi na mayar kan presenter dake cewa Yana welcoming Usman Dikko Wanda yazo latti saboda abin Hawa daya bashi matsala. A raina na ayyana dama wannan shi ne infamous Usman Dikko daya tada hankalin Bakori girls, if I must say tabbas Yana da kyau, he’s Charming and cute Amma take naji Bai burgeni ba saboda bana son abinda attention din kowa yake kai, nafi son abinda ni kadai idanuna yake Kai!

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng  Taken mu a kullum shi ne ” …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *