UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 15 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 15 BY SHATU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Anty jidda ta fito hannunta rike da mayafi da makullin mota. Parlonta bayan Hanifa dake zaune ta Dan fada se Kuma hannunta dauke da jaririyar ta nannade cikin layette, gaban ta abinci cikin plate an rufa wani plate din Dan Kar ya huce, dayan hannunta na rike da katon mug cike da kakkauran tea. Mutanen dake parlon akwai Amira, yayar su se Kuma kawayen Anty jidda guda biyu da cousins din su Hanifa guda biyu. Hajiya hanne ta fara duban Anty jidda tace+

” Ya na ganki da key din motar, se Ina kenan?”

Ta tsaya ba tareda ta zauna ba tace

“Zanje gidan surukan Hanifa ne, bazan iya jira ba Kuma yarinyar yaushe ya aureta zaa saka ya Kara aure?..”

Hanifa tayi saurin aje mug din hannunta tareda fadin

” Dan Allah Mom karki je, ki bar maganar nan kawai.

Ismail threatened me Akan abinda nama Ummaah, karki je ki Kara ballo wani abun”

Wani harara ta Mata tace

” Ke ai na lura Baki San kanki ba, bansani ba ko har yanzun zafin haihuwar ne Bai sake ki ba, tunda ba Zaki iya komai ba ni zanje na kwato Miki yancin ki”

Hajiya hanne da hajja kalsi Suka Mike tareda bin bayan Anty jidda da Bata saurari kowa ba ta fita, duka parlon kowa shiru yayi se Hanifa dake kuka kasakasa. Sister su ta taso tace Mata

” Ki daina kuka Kinga jinin ki already ya hau in Baso kike ya Kara Hawa ba Kuma”

Ta share hawayen da ya Mata kacakaca a fuska tace

” Adda kina gani dai nace Mata Kar taje, shi bashi yace zaiyi aurennan ba, ita komai mum ba zata bi a hankali ba”

Haka Suka lallashe ta har ta Dan kwanta bacci ya dauketa Amma tana hango irin tijarar da zata yiwa Anty jidda matsawar ta ballo Mata ruwa. A bangaren Ismail gaba daya kanshi ya dauki caji ya rasa abinda yake Masa Dadi, yasan Allah ne ya tsara Masa rayuwa haka he doesn’t have Whatsoever Right yayi questioning Allah, Amma tunda Hanifa ta haihu komai Kara lalacewa yake, abin ya masa nauyi ji take shi yasan baa raba bawa da kananan kurakurai, Amma a waƱnan extent din Yana jin abin ya masa nauyi, Yana jin kanshi tamkar zai fashe ne, he’s ok living with Hanifa, tun ranar da ya amince auren ta ya riga ya shirya karban ta, ya Kuma bude zuciyar shi Dan ya Bata dama, dukda tsakanin ta da mahaifiyar shi Basu jituwa Amma shi yasan bama lallai Sofy tayi Masa abinda Hanifa ta Masa ba. Se Kuma yanzun ya riga yayi settling Sofy ta riga tayi aure Bayan ya rasata gaba daya sannan Ummaah zata kawo maganar aure, she’s trying to use him ta kuntatawa Anty jidda da Hanifa, shi Baida wani niyyar aje Mata biyu, not when gaba daya Babu zabin shi a ciki, shi kullum mother’s son ne sede ace mahaifiyar shi ta zabar Masa Mata? Shi fa idan zai iya tunawa San Sofy kadai yayi willingly, bawai Ummaah tace Masa yayi ba Amma komai ita take fada Masa yayi, Bata taba barin shi ya zaba ko yayi deciding Abu, she’s the chief decision maker of his life! Wayar shi ta katse Masa tunanin da yayi zurfi a ciki, cikin rashin kuzari ya janyo wayar se yaga mahaifin shi ke Kira,dauka yayi Yana sassauta murya ya gaida shi cikin girmamawa, sannan yayi shiru yana sauraron abinda Wambai zai fada Masa

” Baa kawo min kawata na gani ba, ance min Kuma matar taka tazo har nan, shi ne nace Nanda mintina talatin zanje na ga kawata”

Sosae yaji kunya ta Kama shi Amma ya zaiyi itama Hanifa data je ba zuwan Dadi ya kaita ba. Mikewa yayi yace

” Zanzo na kaika ayimin hakuri”

Wambai yayi murmushi yace

” Ina jiranka”

Daga haka ya katse wayar, Ismail ya fara neman layin Hanifa wadda ke bacci har lokacin, dukda bama jimawa baccin yayi ba, idanunta ta bude ta dauki wayar tana mitar an katse Mata bacci Amma ganin me Kiran se tayi shiru ta Kara a kunnenta, Bai amsa gaisuwar ta ba yace

STORY CONTINUES BELOW

” In less than thirty minutes zamu zo da Wambai, ki fadawa Mom”

Ya katse wayar ya dauki mukullin motar shi me hade Dana parlon ya fice, tashi tayi ta kwallawa Yaya Kira, se gata ta fito dauke da sucker baby da alama sterilizing dinsu take, kallon Hanifa tayi da ta mike tace

” Ki Kira Mom kice ta dawo Baba Wambai zai zo ganin jikar shi”

Cikin hanzari suka Kira Anty jidda wadda saura kiris ta karasa jin bakon da zaizo Dole ta juya kan motar ta koma gida, komai kafin ta karasa ya kammalla se abinda baa rasa ba, kamar yadda yace minti talatin Yan mintina kadan suka Kara akai se gashi ya iso, mahaifin Hanifa ya shigo dashi parlon da yake saukar manyan bakin shi, sunata Hira da dariya har suka karasa parlon seda ya zauna sannan Dad dinsu Hanifa ya zauna Yana gaisawa da Ismail.

” Ka buya yanzun bama haduwa, coming in contact with you is really getting hard these days”

Daddy ya fadawa Wambai dake kurbar ruwan da aka serving Masa, ya girgiza Kai yace

” A’a fa Kaine baka nema na, rabona da Kai tun ranar auren yarannan, you’re really busy into politics”

Daddy ya watsa hannun shi yace

” Gaskiya kam! Kusan shekara da wani Abu. Politics Babu dadi muna tabawa ne saboda shi ne abinda muka iya”

Daga haka hirar tasu me cikeda ilimi ta koma kan matsalolin da Nigeria ke facing da yadda ya kamata ayi fixing abun, shigowar jidda da Hanifa yasa hirar ta tsaya, Anty jidda fuskarta a sake ta karaso ta gaida Wambai, Hanifa dake rike da baby ta karaso ta tsugunna har kasa ta gaishe shi cikeda girmamawa, shima fuskar shi a sake ya amsa sannan ya karba yarinyar dake bacci Babu ruwanta da matsalolin duniya dake. Ya Jima Yana kallonta sannan ya Mata addua ya dubi Ismail yace

” Na Mata huduba da Safiyya, sunan Gwoggo ta Gumel dukda Hanifa kema haka sunan ki yake’

Jikin Ismail yayi sanyi Dan ya riga ya Mata huduba da Furaira, Hanifa taji wani sanyi a ranta yayinda Anty jidda ta Masa godiyar karar da yayi musu. Bai Kara jimawa ba ya musu sallama suka fito Hanifa ta biyo Ismail fuskata da damuwa ganin ko kulata baiyi ba, seda suka ga tafiyr su sannan ta fara murnar canja suna da akai.

Cikin mota ya kalli Ismail dake zaune gefen shi  yace

” Kira min giwa a waya”

Haka yakan Kiran  Ummaah lokaci zuwa lokaci, yayi yadda akace tana picking Ismail ya fada Mata Wambai ke son magana da ita, ya Mika masa ita ta fara korafin ya fita Bai sanar Mata ba , ta aika bangaren shi ance ya fita

” Naga kamar ana min rowa be shiyasa na fita Naga sabuwar kawata, na Mata huduba da sunan marigayiya Gwoggo, Allah yasa tayi halinta na arziki”

Zatayi complain yace

” Na zata zakiyi murna ai shiyasa banyi shawara da kowa ba, Ina hanya zamuyi magana idan na karaso”

Ya kashe wayar tareda mikawa Ismail yace

” I’ve saved you! Ya kamata ka sassauta fushin da kake da Hanifa hakan, tayi nadama I can see it a idanunta”

Baiyi mamakin yadda Wambai yasan komai dake faruwa ba, shi mutum ne da baya stepping har se yayi tsamari, Yana Kuma tunanin Ummaah ta kaishi bango wannan karon, saboda mostly yana supporting dinta. Ummaah ta cika ta batse ganin yadda Wambai ya Bata Mata plan dinta, Dan haka da kyar ta lallaba kafarta ta nufi part din shi ta zauna ta jira shi, Babu jimawa ya karaso kamar yadda yayi expecting tana zaune tana jiran shi. Da murmushi ya zauna Yana Mata kirari Amma Bata murmushi kamar yadda takeyi. Ya kalleta yace

” Ko dai akwai sunan da kike son a sakawa babyn ne?”

Rainin hankali ta ayyana a ranta Amma se tace Masa

” Zancen auren Ismail ya kamata kayi magana ayi gaggawar hadawa”

Ya kalleta ya daidaita fuskar shi me cikeda kwarjini da ilhama, se ta danji tsoron cigaba da magana

” Shi Ismail yace zaiyi aure ko Kuma kece Kika ce yayi aure? Se yaushe Zaki barshi yayi zabi akan rayuwar shi? Ya girma Amma kinki bashi dama yayi abinda zuciyar shi take so? Me yasa kike haka ne?”

” Shi yace yana son ta fa”

Girgiza Kai yayi yace

” Nayi magana da galadima idan Baki sani ba shi ya riga  ya Jima da bawa wani Yar shi, ke da Hajiya izzatu kuke abinku, idan Banda ke a Ina Kika taba ganin mace ta bada aure sannan mace ta karba aure. Matsalar ki kullum Kara yawa take me yasa kike son kuntatawa wasu ki faranta ranki…”

Seda yayi Mata wankin babban bargo sannan yace an fasa auren ya shige dakin shi ya barta a gurin.Duk abinda ake banma sani ba, na dai San Ammi tace min Hanifa ta haihu Kuma itama da kanta tayi min text din ta haihu sede ni ce ban samu na kirata ba, Dan haka Ina kwance a bedroom da Rana gidan yayi shiru dukda dama ba wani hayaniya bace a gidan suma yaran ba kiriniya suke sosae ba, Kuma yau din banji ko daya ya shigo gurina ba, se na Bari akan ko basa nan ne. Albi Kuma ya tafi office,  Nima Ina zaman jiran letter of deployment Dan anyi posting Dina Anambra na nema Suka dawo Dani Kaduna, ya kaini naje camp a ranar na fito muka koma Gombe, yanzun kokari ake su dawo Dani Gombe kawai nayi anan.+

Wayata na dakko na fara Kiran Hanifa, bugu daya ta dauka muryar ta kadai naji nasan tana cikin farin ciki

” Me jego irin albarka”

Na fada Ina murmushi,

” Daga ni har ita munyi fushi, se yau zaki Kira kiji yadda ‘yarki take? Ni ko gombawa sun washe ki ne”

Nayi dariya tuna da yadda muke fada da ita tana ganin kamar zan aura mijinta Amma kalla yadda ta saki fuska tana min Hira

” Dan Allah kiyi hakuri, nasan banida uzuri Amma acewa babyna Ina gaishe ta and I’ll come soon and cuddle her in my arms”

Tayi murmushi da naji sautin shi tace

” Inshallah, Muna kiranki but guess sunan babyn?”

” Sunan Anty ko Ummaah”

Se tayi tsaki tace

” Kiji wannan sunayen, sunan mu ne sunan Gwoggo. Me kike ganin zaa dinga ce Mata”

Na sauke ajiyar zuciya cikeda Jin Dadi nace

” Let’s call her Safiyya, tunda min an boye namu sunan”

Ta amince da idea ta mukai sallama, mikewa nayi na fito parlor na zauna, nayi shiru Ina jin kamar I’m a prisoner, wani lokacin se naji inama Zan iya dawo da rayuwata ta yanmatanci Koda sati daya ne, naje inda nake so nayi magana da Wanda nake so Amma kalleni trapped in a place kullum cikin maimaita Abu guda, gyaran gida, girki da sauran su. Amma hakan shi ne ibadar, dashi zaka taka ka shiga aljanna. Wata Hamma ta kubce min lokaci daya naji cikina ya hautsuna min se naji amai ya taho min, da sauri na nufi daki da kyar na Kai se amai, nayi sosae Dan breakfast din da nake takama nayi duka ya fito yabi sink, na dafe kaina tareda kallon madubin dake saman sink din, na Kara haske fuskata tayi Yar kuyas da ita, na girgiza Kai na no wonder Albi kecewa bani da lafiya, yau da zai fita yace Yana dawowa zai kaini asibiti Dan shi gani take ma kamar banida jini a jikina. Wanke fuskata nayi da ruwan Dana kunna daga sink din, gaba daya tsikar jikina ta tashi, na fito tareda kashe fankar dake yi na kundundune cikin blanket,a hankali zazzabin ya mamaye jikina.

Cikin kunnuwana naji Kiran sallar azahar,da kyar na tashi nayi alwala da ruwan dumi, sallar ma a zaune nayi saboda jiri da yake dibata, na Jima a zaune sannan na koma na kwanta, inata addua Allah ya kawo min dauki, Allah ya sa Albi ya Kira ko ya dawo, at least someone should know that I’m sick, kada na mutu ni daya a daki. Amma shiru har akai laasar, wanann lokacin kasa sallar nayi ko daga hannuna na kasa se ayyanawa da nayi Ina yin sallah. Kamar daga sama naji tafiya a parlor, na sauke wani huci me zafi Ina hamdala cikin Raina, Babu jimawa se naji an turo kofar bedroom din da nake, Kubra ce ta shigo itada Amna, Ina daga kwance ta karaso ciki ta nufi bargon tana fadin

” No wonder naji shiru Babu motsinki”

Ta zauna tareda yaye bargon ta taba jikina se ta dauke hannunta ta dubeni tace

” Bakida lafiya Amma ba Zaki fada min ba, meye amfanin zaman taren”

Na cije lebe na Dan bazan ma iya maganar ba, ita ta taimaka min na saka hijab sannan ta riko hannuna muka fito zuwa tsakar gida, anan muka Shiga mota hannuna na rikeda kaina muka wuce asibiti, tunda naji kamshin car freshener nake amai, Dole se bude duka glasses akai Dan iska ta shigo. Wani private clinic ta kaini take aka fara bani taimakon gaggawa, anan Usman ya dawo ya samu bama gida akace Masa ni ce banida lafiya, Hajiya babba ta kaini asibiti, yaji dadi sosae, ya nufo asibitin lokacin nayi bacci ita Kuma suna Mata bayanin ciki ne dani, ba komai bane ai laulayi nake.

STORY CONTINUES BELOW

Lokacin Dana farka tana kan sallayya ta idar da sallar Isha, na dubeta tareda mikewa na zauna, Jin motsina ta kalleni tace

” Sannu Allah ya Kara lafiya”

Nace

” Amin nagode Allah ya saka da alkhairi”

Ta gyada Kai Sega shi ya shigo, kamar jira take Yana Zama ta mike

” Zan tafi nikam, Allah ya Kara sauki”

Ya kalleta yace

” Itama da wannan ya Kare tafiya zamuyi gida, ba se mu tafi gida duka ba”

Se ta firgice Kai tana yatsina fuska tace

” Na bar yarana a gida, Safiyya Allah ya Kara lafiya”

Na amsa da Amin ta fita yabi bayanta, nayi shiru da mamaki a raina, me ya Bata Mata Rai hakan? To banida amsa se na watsar da wannan tunanin, na ayyana dukkan yadda mutum yake da Hali marar kyau ko Kuma nace duk yadda kuke zaman rashin jituwa da mutum Dole akwai ranar da zai maka amfani, ban taba kawowa Kubra will notice cewar Bata ji motsina ba, ban kawo Dan Ina rashin lafiya zata kalli inda nake ma ba, se gashi ta bani mamaki, tabbas ya kamata mu fito da kyawawan abubuwa game da kishiya, duk yadda take da sharri to fa itama akwai alkhairin ta. Bai Jima ba ya dawo ya sameni nayi shiru inata tunani, Yana zuwa ya rungumeni a jikin shi tareda shanshano wuyana Wanda yasa ya lumshe idanuna shi saboda turaren dake gurin, ya shafa fuskata sannan ya dawo ya zauna a gabana ya riko hannuna me cannula yace

” I’m sorry I didn’t notice this early. Ashe baby ke wahalar min dake”

Nayi murmushi na kwantar da kaina a kafadar Shi bance komai ba, se ya fara tambayata abinda nake so, na zauna na dinga mishi lissafi, shi Kuma yana jina da bakinshi da yayi curving saboda murmushi yace

” Duk ke kadai Zakici wannan abubuwan?”

Na cuno Baki tareda dauke kaina daga kafadar shi nace

” Ba zaka siyo min ba kenan”

Ya girgiza Kai da sauri yace

” Na Isa! Tare zamu siyo ma ai, we’re in this together”

Ya fada Yana shafa min cikina. Nayi murmushi na daura hannuna akai Ina kallon cikin idanun shi, my love is there kwance a ciki, ya rungume ni Yana rada min Abu cikin kunne na. Tare muka siyo duk abinda nace Ina so, tun a mota nake ci har mukaje gida, da karfina na Shiga bakace ni ce na fita dazun ba kamar bazan Kai ba.

” Albi lemme thank Maman Afaf first kafin na kwanta”

Ya  girgiza Kan shi yace

” No! Ki Bari da safe”

Na marairaice nace

” Dan Allah, kaga ai jikin da sauki”

Se ya kyaleni na tafi, shi Kuma ya bude parlon ya shigar da sauran ledoji na, Ina shiga parlon naji

” Ciki ne fa da ita, kinji yadda nake ji kamar zuciyata zata fito Dan kishi..”

Jin sallama ta yasa fadila saurin karasawa ta Mata magana, ita Bata magana a hankali, normally idan tana magana ma zakai tunanin fada take, na lura halitta ta ce a hakan. Ta karaso fuskar ta a hade, Dan hakan na shiga nutsuwa ta tareda dauke Murmushin dake fuskata nace

” Kin dawo lafiya? Nagode sosae Allah ya saka da alkhairi”

Tace Amin sanann ta tambayeni ko akwai abinda zanci, na girgiza na Kara Mata godiya na fita Ina ayyana meye matsalar ta da cikin jikina, Banda abinta itada ta riga ta haihu meye damuwar ta.

Bayan kwana biyu na warke sosae Dan hakan na shirya tafiya Gumel saboda yayimin alkawarin zanje sunan Safiyya Hanifa Kuma lokacin yazo banida lafiya, har parlor naje na Mata sallama ta amsa faran faran tareda bada sakon gaisuwar ta gurin Ammi. Da safe a gurinta yake, seda na jira ya fito da shirinsa, ya fito da kayana sannan na fito na shiga mota har ya tada Sega Maman Afaf ta fito, shi baima ganta ba ni na tsayar dashi da reverse din da yake kokarin yi, handle din motar shi ta Kama ta bude tace cikin gadara

” Kasan kwanana ne Kuka zaka fita da ita ko?”

Ya kalleta yace

” Me kike Yi haka, inace tun jiya na Miki bayani Kuma kin amince da hakan”

Ta juyar da kanta gefe har lokacin Bata saki murfin motar ba tace

” Wallahi ba zaka fita da ita ba saboda ba ranar ta bane, ita me yasa ba zata je Tasha ta hau mota ba, ni idan zanje bauchi ai ba ko yaushe kake kaini ba”

Yayi shiru yana jin abinda take fada , Nima na lumshe idanuna Ina bawa zuciyata hakurin kada na tanka ta tunda ita dashi suke abinsu

” …ai Bata fi kowa ba, Dan haka wallahi ka fita da ita ka Shiga hakkina se Allah ya saka min”

Wannan furucin da tayi yasa nace

” Lokaci Yana tafiya, Bari naje Tasha na samu mota”

Fita yayi Bai ce komai ba, ita Kuma se Kara jijjiga jiki take alamun nasara tace

” Ah to dai!”

Raina idan yayi dubu to ya baci, ji nake kamar zuciyata zata fito Amma hakan na dauke kaina ban ko kalleta ba Amma zata San ni tayiwa haka, lokacin da na shirya tafiyar seda nace Masa ba girkina bane yace Babu komai yayi magana da ita ta amince. Shine se da za ayi tafiyar ta min hakan. Ganin ya wuce part dinta ta bishi a baya yasa na fito a motar na koma parlor na, idanuna sun ciko da kwalla Amma haka na daure na maida kukan Dan Banga amfanin yinshi ba. Na Jima se naji sallamar shi a hankali na amsa yace

” Fito ku tafi”

Bance komai ba na biyo bayan shi ya kullen ko Ina, Faisal na gani Yana min murmushi yace

” Anty Amarya Ina kwana?”

Na amsa duk yadda nake kokarin nayi Masa murmushi na kasa, Albi ya karaso ya bude min kofar baya, na wuce ban Shiga ba na bude ta gaba na shiga, ya kalleni a marairaice na dauke kaina, Faisal ya Shiga gaba ya tada motar, Albi ya leko ta window ya Kama hannuna yace

” I’m sorry, take care of yourself. Allah ya kiyaye Hanya”

Bance komai ba Amma a raina na amsa Amin din adduar, Naja hijab Dina na rufe fuskata hakan ya tabbatar Masa kuka nake, yaja baya Yana jin tashin hankali ya fara ma Faisal fadan ya tafi Dani a hankali, daga nan muka dauki hanya, nayi ta kuka saboda Ina ganin Kubra ta cimin mutunci, baa taba min abinda tayimin ba. Tun Faisal Bai gane kuka nake ba har ya fahimta, ya Kira Albi yace

” Anty kuka take fa”

Banji me yace Masa ba se kawai Naga ya Miko min wayar,na karba na kashe na aje Masa wayar shi.Har muka bar garin Gombe ban daina kuka ba, naji ciwon abinda ya faru, saboda nasan ni idan nice hankalina bazai taba kawowa Wai nace bazan Bari ya fita da ita ranar girkina ba, nasan inada fitina Amma fiti nata se an taba ni, ni kamar su sulphur nake se na samu wani element din sannan nake reacting, Dole se anyi triggering Dina nake Zama into action. Daga kukan bacci ya daukeni, lokacin Dana farka munyi nisa sosae, wayata na janyo Ina kallon Faisal da ya maida hankalin shi dukka akan titi nace+

” Sannu Faisal”

Yayi murmushi yace

” Sannu Anty, kinsha Zama”

Nayi murmushi na fara Kiran Ammi, ba jimawa ta dauka Bayan mun gaisa tace

” Kun taho kenan?”

Nace

” Mun taho tun dazun, ki dafa min danwake Dan Allah Ammi”

Seda tayi murmushi tace

” Ba Kano Zaki tsaya ba?”

Na Dan Bata fuska kafin nayi magana tace

” Ki tsaya a Kano kiyi kwana uku, gidan Hajiya maimuna. Idan yaso se kije barka da komai, idan kin gama ki taho nan ki karasa kwanakin ki”

Na gyada Kai ba dai haka naso ba Amma hakan zanyi tunda haka tace, sallama mukai na fara Kiran Mama sede Bata dauka ba, tabbas ya kamata ace naje gidan tunda mukai aure sau biyu na taba zuwa gidan. Faisal na kalla nace

” Mu wuce Kano kawai, ai kasan gidan Mama ko?”

Yace

” Maman Hamma? Nasan gidan”

Nace yawwa daga nan na lura da message daga gurin Albi, tsaki Naja na Shiga Wattpad Neman abinda Zan karanta, hankalina kacokan na maida gurin karanta Once upon a Muslim. Na tsunduma sosae Ina jin how I wish I can meet the writer in person, I would have given her a hug saboda tayi portraying abubuwa da dama cikin littafin. Kamar yadda Ammi tace min hakan nayi, gidan Mama ya kaini, na gaji ga cikina dake hargitsawa kamar zanyi amai, ga jikina duk ciwo yake. Da ya bude min se na kasa fitowa na rike kaina Wanda yake kamar zai fado Dan ciwo, yace

” Anty ya dai?”

Na daga mishi hannu kawai bance komai ba, can ya Dan tsirga na Mike a hankali na dauki handbag dita na nufi cikin gidan, tana tsaye gaban kofar parlor tana magana da wata dattijuwa, seda ta kalleni sosae sannan ta fahimci ni ce, fuskar ta ta saki tana fadin

” Safiyya kece? Sannu da zuwa”

Na danyi faint smile nace

” Mamaa sannu da gida”

Dana karaso gabanta se Naga tana Bina da kallo, kamar me neman wani abu, se ta Kama hannuna mukai ciki ba tareda ta koma ta kan dattijuwar dake tambayar ta bakuwa tayi ba. Har bedroom dinta na sama ta kaini, se ya tuna min ranar da aka kawo ni, nan dakin aka kawo ni haka da na Kara zuwa ma nan din ta kawo ni. Seda na zauna kan carpet na Mike kafata Ina jin tamkar an sauke min dukka abinda nake ji na gaishe ta nace Mata nida Faisal ne, aikuwa ta fara fada Wai me yasa bazai katse komai yake ba ya kawo ni, fita tayi na samu na Shiga toilet lokacin ta dawo da tray hannunta na Yi yunkurin mikewa ta hanani, tace

” Yama tafi, an shigo da kayan kina toilet”

Na gyada kaina ta cigaba da fadin

” Nasan Baki ci komai ba, me kike so?”

Nayi shiru Ina tunanin ta zuba min idanu se can nace

” Dan wake”

Tayi murmushi tace min to nasha tea kafin a Gama, tana fita na janyo mug na hada tea da kauri Dan Madara yanzun idan ya siyo karamin gwangwani kwana biyar take ta Kare, nasha tea aka kawo danwake naci aikuwa se bacci. Da yamma ni da ita da Aysha muka fita zuwa gidan Anty jidda, da Amira naci Karo tana zaune da Abu a hannunta, tana ganina ta aje abin ta taho tana min murmushi, hannunta na rike muka shiga ciki, tana fada min wai yarinyar na Kama Dani, nayi dariya nace

STORY CONTINUES BELOW

” Se na tafi da ita Kinga shikenan”

Tayi dariya tace

” Kinsan yadda Hanifa ke sonta tab!”

Muna shiga Hanifa na fitowa a daki, ta tareni da faraa na mayar Mata, muka zauna na Mata introducing su Mama da Aysha aka kawo Mana baby su suka fara dauka se ni ta karshe, Anty jidda ta fita se Suka tafi akan zasu zo su daukeni idan sun gama. Tunda Suka tafi muke Hira se dare Anty jidda ta dawo, taji dadin zuwana mukai Hira sosae. Ina kwanciya bacci Kiran Albi na shigowa wayata, kamar bazan dauka ba se na gagara saboda nidin ma so nake naji muryar shi, I’m badly missing him.

” Baby fushi kike dani? Naga nace miki kiyi hakuri. Kinga ba laifina bane ai”

A hankali naji hawaye ya fara sakko min Amma dukda haka nace Masa

” Ba laifinka bane ka dai nunamin matarka ta fini, ka nuna min maganar ta ita ce magana, ai ni bansan baa fita da wata ranar da ba girkinta ba, a nawa kwanan sau nawa kuka fita, ka kasa tsaya min ka nuna Mata ni ba komai bace. Ka kyauta nagode sosae”

Tunda yaji Ina kuka yayi shiru ga Kuma maganar da nayi wadda Dole se ta taba shi,

” Ba hakan bane ai kinsan Ina son ki?”

” Wa yace baka Sona Albi? Ko shafawa akai an sani, but Ina son ka sani da matar da aka aura yau da wadda aka aura shekara dari duka daya suke, Nima matarka ce I’ve every right over you and your proprties, tunda ka kawo ni gidanka you have to treat us equal no matter the circumstances”

” Nayi laifi kiyi hakuri,ki daina kuka Kinga bana kusa balle na lallashe ki Kuma bana son Mamaa ta fahimci akwai wani Abu. Dan Allah ki yafe min kinji”

Na gyada Kai na Ina sniffing a hankali, haka ya dan yimin hira Amma ganin I’m not in the mood yasa ya kyaleni kawai mukai sallama nayi bacci. Washegari naje gidan Ummaah, Rayha ta dakko ni daga gidan Ummaah muka dawo gidan Mamaa anan ta yini, washegari da yamma muka tafi Gumel da ita da Yaya Nasir Dani. Wani farin ciki naji Dana Isa gida. Kwana na takwas sannan na fara Shirin tafiya, tun Albi na korafin naki dawowa har ya hakura kawai ya kyaleni, ni kuma Ina son na huce gaba daya ne se na koma a Dora daga inda aka tsaya, Kuma Ina son na nuna Masa ni ba wacce zaa cuta bace nayi nayi shiru.

Ranar da Zan tafi ban fada Masa ba, duk yadda ya damu na fada masa yazo ya daukeni nace a’a ya Bari zan taho da kaina, gaba daya na rikuta shi yace

” Ya kike so nayi nace kiyi hakuri Safiyya, why are you making things hard ne? Yanzun ba zaki…”

Kafin ya karasa Ammi ta leko tana Kirana Dole na Masa sallama Dan zuwa Kiran Baba, Ina zuwa yace min

” Rumasa’u ta samu sauki”

Gabana naji ya Fadi , da gaske na manta da wata Anty Rumasa’u Kuma koda Naga Ayaan still bana tunata. Na danyi yake na Mata addua, Rayha tace

” Zata dawo kenan?”

Ya girgiza kanshi yace

” Not after duk abinda suka faru, Nima bazan Yi taking wani risk din ba Kuma”

A hankali na sauke ajiyar zuciya nace

” To Baba Allah yasa haka ne mafi alkhairi”

Suka amsa da Amin, baba ya Miko min envelope yace

” Kin Gama school inata hidima ban baki komai ba, gashi Allah ya kawo babban rabo”

Nayi murmushi tareda budewa dukda shafal naji ta ga mamakina key din mota ya fado, na dauka na kalli Baba dake murmushi, na juya gurin Ammi dake kallona cikin farin ciki nace

” Baba nagode Allah ya saka maka da alkhairi”

Ya amsa Amin sannan muka danyi Hira naje na kwanta Ina jin kick din da ake min a cikina, na shafa Ina fadin

STORY CONTINUES BELOW

” Baby please sleep mummy wants to rest also”

Rayha dake changing pillow case tayi dariya tace

” Ashe kema kina haka, kinsan time din Little babanta se yace Wai I’m going crazy”

Na gutsiri ayabar hannuna nace

” Bazasu gane ba”

Washegari a mota ta muka tafi, fara Kiran 206 the car i always admired, tunda ban iya ba se Baba yasa a kaini. Wajen azahar muka Isa. Seda yayi min parking motar daidai sannan ya bani key zai tafi nace

” Tsaya Mana na girka maka abinci”

Yayi dariya yace

” Idan na zauna cin abinci yaushe Zan koma kenan”

Haka ya tafi na bude parlona na Shiga,an dawo gidan jiya na ayyana a raina. Gyaran da nayi bashi da yawa na Sha tea me kauri sannan na kwanta bacci ya daukeni, se laasar na tashi shima Amna ce ta shigo tana min gwauranci,na Bata alawa ta tafi. Wanka nayi na shirya cikin shadda maroon nayi kyau, cikina ya fara fitowa, nayi kyau sosae saboda kibar da nayi kwana biyu. Bai dawo ba se bayan maghrib, sallamar shi naji Ina dakin shi Ina maida kayan guga da aka kawo ya bar min su Akan gado, juyowa nayi Ina amsa sallamar na kalleshi fuskar shi dauke da murmushi Amma akwai gajiya a tare dashi. Hannunshi ya ware min na noke kafada Ina murmushi, ganin bazan zo ba ya karaso ya rungume ni Yana fadin

” I missed both of you”

Ya fada Yana shafa cikina, nayi chuckling nace

” What if we’re three?”

Ya Kara matseni yace

” The three of you”

Na Dan raba jikina da nashi nace

” Idan mu hudu ne fa?”

Se ya harareni yace

” See this silly girl, kece Zaki iya da Yara uku?”

Na tura bakina kamar Zan bige wardrobe din gabana nace

” Seriously? Am I that lazy”

Kaina ya shafa ya zauna ya fara tambayata kowa da kowa, Nima na bashi sakon kowa sannan nace banyi abinci ba Ina son mu fita waje mu ci daga nan zanje na gaida Baffa, saluting Dina yayi yace

” Anything for my Queen”

Haka ya shirya muka fita se lokacin ya dubeni yace

” Wannan motar fa?”

Nace Masa idan mun dawo na Masa bayani, a wani eatery mukaci abinci sannan naje na gaida Baffa da Ummaah muka dawo tun a hanya na fada Masa yadda akai yace

” Na zata saboda abinda ya faru Kika ce wa baba ya siya Miki”

Bance Masa komai ba se murmushi da nayi yanata tsokanata Wai hantar Baba da Ammi, shi Kuma ni ce zuciyar shi. Faisal Albi yasa ya fara koya min mota Babu dadewa na koya, matar gidan ko ta kanta banbi ba, banma je nace Mata na dawo ba dukda ya kamata Amma banje ba. Seda mukai sati biyu a hakan, da wuri Albi ya fita ranar, na fito da khaki na nysc a jikina na daura abaya me Fadi akai nayi rolling, na bawa motar wuta ita Kuma ta fito da shirin fita ita da fadila, duka suka tsaya suna kallona,fadila har da nuna ni da yatsa, nayi kamar ban gansu ba aka bude min gate na fita. Bayan na dawo da yamma ya shigo Yana ta dariya, na kalleshi nace

” Me ya faru”

Ya harareni Yana shafa gemun fuskar shi yace

” Son gulma”

Na gimtse na cigaba da duba littafin hannuna, ya janye littafin yace

” Hey! Bakice ma Kubra kin saya mota ba?”

Na kalleshi wani irin nace

” Saboda me? Does she owns me explanation? Bata Isa ba”

Ya girgiza Kai ya janyo ni jikin shi yace

” Haeee! Lokacin dana aureki I never knew you’re stubborn, what’s there in telling her kin Yi mota”

Na tabe baki na kwace jikina bance Masa komai ba, se yayi shrugging shoulders din shi yace

” It’s ok, ku dai zauna lafiya Dan Allah”

Na juyo nace

” Abinda maza kuka kasa ganewa, matsawa da kuke se anyi muamula shi ke saka matsala, yanzun tunda na dawo kaji wani Abu? Saboda nida ita bamu hadu ba. Dan Allah Albi ka barmu muyi rayuwar mu haka”

Baice komai ba yace na kawo Masa abinci. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya na cigaba da rainon cikina har ya fara kokarin tarban Baby. Anisah Ammi ta kawo min se Mamaa da tazo tunda sukai waya da Ammi tace Mata ita ba zata zo ba shi ne ita ta shirya ta taho. Nanma seda ran Kubra ya baci ai Mamaa Bata taba zuwa ba, har ta fadawa Maman se Mama tace Mata ita sau nawa ta taba zuwa ta gaishe ta.

Daren Friday na fara labor Wanda na kusa sati Ina ciwo a tsatsaye, a Daren na kasa kwanciya Dole na tashi Mamaa, muka dauki kayan haihuwa se asibiti Bayan ta taso Albi, muna zuwa ana ve akace 4cm, nayi shiru na rasa me yake min dadi, duk azabar da nake Sha a 4cm nake? Fitowa nayi na fara ambulating idan na gaji na dawo na zauna Mama nata min addua. Wajen bakwai ciwon ya dauke Baki daya naci abinci na fara bacci, kamar an tsira min Abu na Kara mikewa a gigice saboda azaba ana Kara dubani na Kai seven se kawai aka daura min ruwan nakuda, Babu jimawa ta taho ganga ganga, nasha wuya ba Haifa baby boy!!!

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng  Taken mu a kullum shi ne ” …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *