UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 11 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 11 BY SHATU

Seda akai sadakar bakwai sannan washegari Baba yazo Dan daukata tareda Ammi da Gwoggo da zata Kara musu gaisuwa, Tunda garin ya waye Mama ke kuka, Baffa kamar yadda suke Kiran mahaifin su Yana ta lallashin ta da ni kaina da nake ganin zuciyata ta gaza, Ina ganin kamar rayuwata karewa zatai, ban taba kawowa cewa haka zamu rabu ba, ban taba kawowa zai tafi ya barni a duniya ba so early, Allah ya kaddara hakan ce zata kasance, Amma ban kawo hakan ba. Da kyar aka banbare ni daga jikin ta na nufi mota, inata kuka Wanda har yau idan na tuna dacin da naji lokacin da nake kukan se naji idanuna sun ciko da kwalla, se naji wani Abu more of a lump ya tsaya min a makoshi. Kuka nayi na rashin abinda zuciya take so, I just longed for him, his voice and everything about him, lokuta da dama se naji kamar echo din muryar shi,  ko kuma Ina zaune se naji kamar ya shigo na Jima ban daina kukan rasuwar shi ba, ta girgiza ni tazo min a bazata, ta Kara sakawa na Kara Zama

reserved. Seda muka tsaya a asibiti aka duba hannuna sannan doctor ya bawa Baba shawarar ya nema min psychotherapist saboda yadda yake gani I’m already in a state of depression. Gaba daya a kwanakin Baba hankalin shi a tashe yake, karku manta Anty Rumasa’u tana can asylum bawai ta warke bane, dukda jikin da sauki matsalar da ta fara samun sauki se hallucinations su dawo shikenan se ta koma gidan jiya.+

Se yamma muka karasa Gumel, Ammi ta hada min ruwa wanka, Rayha ta taimaka min nayi wanka sannan na dawo na shirya na kwanta kan gado, Ayaan na dauke da Little tana Mata Wasa yarinyar nata bangala bakin da Babu ko hakori daya tana dariya, kawai se na shagala Ina kallonta, har a lokacin na manta da damuwa ta, ganin hakan yasa Ayaan daura min ita akan cinya ta, na rike ta Ina jin soyayya ta cikin zuciyata,ita Kuma tayi tunanin Rayha ce se ta kwantar da kanta a jikina, Amma tana jin sallamar Rayha ta dago ta kalleni sannan ta kalli Maman ta se ta gangara zata tafi, Rayha ta dubeni tana murmushi jin dadin ganin Ina murmushi tace

” Wai ta gane bani ba ce”

Dan shafa kanta nayi na gyada Kai bance komai ba, Zama tayi tana Dan min hirar can Qatar din Amma ko kadan ba gane abinda take fada nake ba. Can na dubeta nace

” Anyi retrieving wayata a gurin kuwa?”

Ta gyada Kai ta dakko min wayar da taci screen Amma Baba ya sake min wani sabo, cikin sauri na shigo scrolling pictures Dina, hotunan shi na samu tsiraru saboda da mukai fada na riga na goge, I felt heartbroken da bamuyi fada ba da may be bazan rasa hotunan sa da conversation dinmu ba. A hankali labari ya bazu aka ta min taaziyya, Yaya Ismail yazo shida Hanifa dake da karamin ciki. Ina zaune a kofar parlon Ammi ta shimfida min sallayya, hannuna rike da wani sabon book da Baba ya kawo min dukda kokarin focussing da nake amma dukda haka wani lokacin se na gagara gane abinda na karanta. Sallamar da naji yasa na dago idanuna, Yaya Ismail ne a gaba se bayan shi Hanifa, nayi mamakin zuwan ta Dan ko Anty jidda Bata je maska ba haka ba ta Kira ba, dukda mutane da dama da banyi expecting ba sun kirani sun duba ni sun Kuma min gaisuwa. Na rufe littafin hannuna Ina Dan sakin fuska ta, suka karaso har zata zauna gefena nace

” A’a mu Shiga ciki”

Mikewa nayi na Shiga ciki Ina jin kaifin idanun Ismail akai na, seda suka zauna sannan na Kira Ammi, Rayha already sun koma Kano, su Kuma su Anisah sunje gidan Gwoggo. Ammi ta fito Suka gaisa tana tambayar su yadda suke, suka Mata gaisuwa sannan na zauna Nima Suka min gaisuwa, Hanifa tace

” Kina cin abinci kuwa? Kin rame da yawa”

Na danyi murmushi na shafa wuyana nace

” I’m fine”

Amma nayi mamakin yadda take min magana a hankali with concern, Ashe ita bani ce target dinta ba, sun Jima sannan suka tafi Bayan sun kawo kayan duniya da yawa, se books da ya siyo min yace na dinga karantawa zai dauke min hankali. Bayan rasuwar shi da wata daya na Dan ware ba kamar ko yaushe ba, Ina Hira na Dan saki jikina, hannuna an cire cast din Kuma cikin aminci Allah ya nufa gyara yayi, a wañnan lokacin Kuma se wata matsala ta kunno Kai wadda daya nayi expecting hakan daya Kuma ban taba kawowa ba.

STORY CONTINUES BELOW

Ina zaune akan kujera da wayata a hannu muna Hira da Widad, lokaci lokaci Ina Kara bibiyar chat dinmu da ya riga ya shude, na duba last seen dinsa a month and days offline, se naji idanuna sun Kara taho min, da sauri na maida su Dan munyi da Ammi na daina kuka, saboda idan Ina kukan tayar Mata da hankali nake, shiyasa yanzun ko abun ya ciyo ni sede naje dakin mu na kwanta nayi me isata. Wayata ce ta fara ringing se ta katse min tunanin da nake, hakan yasa na girgiza kaina Ina duba caller ID din, Anty yusra na fada a hankali sannan na Kara a kunnena.

” Sofyn Ammi”

Haka ta koma fada min, na danyi murmushi na gaisheta ta amsa tana fadin

” Bakida kirki yanzun anyi Miki irin wannan rasuwar sede Hussy ta fada min ko?”

Na Dan girgiza Kai nace

” Anty yusra bazaki gane ba, gaba daya ban Jima da dawowa nutsuwata ba, wallahi Babu Wanda na fadawa kowa a gari yaji. Amma kiyi hakuri”

Se ta sassauta muryarta tace

” Allah ya jikan shi ya Masa rahma, ke Kuma ya zaba Miki mafi alkhairi”

Bana son wannan adduar da ake min, to Amma ya zanyi tunda har ni din ban mutu ba Dole ne ayaimin, mundan taba Hira tace min zata zo har Gumel tayi min gaisuwa, nace ba se tazo ba wayar ma ya Isa. Da haka mukai sallama tana ta insisting, se na kyaleta kawai.

Washegari na manta munyi maganar da ita se nabi Ammi shagon ta, tana bude shagon naji kawai bana son Shiga Dan haka na tafi gidan Gwoggo. Anan na samu Anty jidda tazo itada Anty Ikhilima . Na gaishe su na wuce dakin Gwoggo se naji ta kwala min Kira, na fito tace min

” Sofy ya jikin?”

Na amsa da da sauki kawai na koma ciki, Ina ji suna magana kasakasa Amma banma bi takan su ba. Ban Jima da kwanciya ba se naji sallamar Ammi, na sakko Ina jinta suna gaisawa da Gwoggo tana fada Mata nayi baki ne, fitowa nayi nace Mata

” Su waye?”

Ta dubi su Anty jidda da Suka kasa kunne se Taki amsa ni haka na ma Gwoggo sallama muka tafi. A kofar gida na ganshi a tsaye hankalin shi dukka akan wayar dake hannun shi, tundaga nesa nasan ko tantama Babu shi ne, Muna zuwa daf dashi ya dago Yana kallona, se kuma ya maida wayar aljihu ya leka motar yayi magana Sega Anty yusra ta fito, zuwa lokacin muka karasa inda yake tsaye, ya tsugunna har kasa ya gaida Ammi sannan ta shige ciki itada Anty Yusra ni Kuma na tsaya a gefen shi, tubda na tsaya yake kallona ni Kuma uffan Bayan gaisuwa bakina ya kasa furtawa se takura da naji nayi.

” Kiyi hakuri! Allah ya jikan shi yayi Masa rahama”

Na gyada kaina Ina jin hawaye na bin kuncina a hankali, yayi shiru ganin Ina kuka yace

” Kiyi shiru ki daina kuka kinji ko? Allah Yana sane dake, better things will come your way.”

Na Dan dago nace

” What better thing Kuma Bayan ya tafi ya barni”

Ya girgiza kan shi yace

” Ki daina fada Allah yasan gobe shiyasa yayi hakan. Kinga duk kin rame I’m sure kin kusa kowa makaranta, hakan zakije duk a rame”

Dan bakina na turo Ina share hawayenta yace

” Ko Afaf yanzun ta fiki kiba fa”

Na Dan Harare shi ina murmushi Kuma at the same time hawaye na zuba daga idanuna, karshe har seda yasa nayi dariya se na ji I’m brand new. Muka Shiga ciki suka ci abinci dukda yaki sakin jiki. A hakan Baba ya same su ganina inata dariya ya bashi mamaki sannan yaji dadi.

Washegari na tashi da karfina, saboda Usman ya fada min wannan abin da nake kamar Ina jayayya da will din Allah ne, kamar Ina nuna Allah Bai Isa hukunci a rayuwata ba, ya Jima Yana min nasiha wadda kusan kowa yayi min irinta Amma bansan dalili ba tashin se tafi tasiri a cikin kaina har washegari na shiga Taya Ammi aiki a kitchen. Bayan munyi breakfast Baba Yana zaune na kwashe kayan na Kai kitchen na dauraye sannan na dawo na tarar suna magana se na nufi daki, Baba ya tsayar Dani akan na dawo Yana nemana, na samu guri na zauna yana ta kallona kafin can yace

” Bai dace Ina fada Miki wannan maganar ba a halin da kike ciki, Amma Babu yadda zanyi Dole Zan fada Miki. Daga gidan su marigayi Jaafar sun min maganar akan kada mu maida kudin auren da suka kawo brother din shi Junaid zai aureki!”

Idanuna kamar zasu fado kasa na fara kuka nace

” Baba Dan Allah a’a, Dan Allah a’a Baba…”

Se na sunkuyar da kaina Ina kuka, ya Dan dago kaina ya riko hannuna yace

” Uwata bazan taba Miki auren Dole ba, bear this in mind. Amma abinda nake so ki sani Jaafar ya rasu, bazai dawo ba ya tafi har abada, Dole ki bawa wani chance Koda ba Junaid din bane.”

Tabbas abinda Baba ya fada gaskiya ne Amma bansan yadda Zan fara accomodating Junaid din ba, haka Baba ya lallashe ni akan na yadda na bashi chance muyi magana. Wannan shi ne abinda banyi expecting ba.

Wanda nayi expecting shi ne dawowar Yaya Ismail filin daga, wannan Karan bashi bane ya dawo mahaifiyar shi ce ta kawo nata barar saboda mu bamu sani ba tsakanin ta da Anty jidda komai ya lalace. Har gida tazo ranar Ina Shirin komawa Zaria Kuma har lokacin ban tsaya na saurari Junaid ba, tana shigowa Dani muka fara haduwa bayanta ramlah ce da Bata jima da dawowa daga UK ba. Tazo ta rungume ni tana fadin

” Uwata ta kaina sannunku fa.”

Na Dan janye jikina na gaishe ta fuskata Babu yabo Babu fallasa, ta tambayi Ammi nace tana parlor. Sun jima itada Ammi ba tareda masaniyar me suke tattaunawa ba seda ta tafi sannan Ammi ta Kira Baba ta fada Masa, a take yace Bai yadda ba. Bansan yadda akai Hanifa taji labari ba, Babu jimawa Sega kiranta a wayata, nayi mamakin Kiran Amma duba da kwana biyu tana yawan Kirana se ban kawo komai a raina ba. Ina picking tace

” Sofy! Dan Allah tun Ina ganin guntun mutuncin ki ki fita harkar mijina…”

Cikin sauri na katse ta da fadin

” Wanne magana Kuma Hanifa, Dan Allah spare me all these talks, akwai abubuwan da suka fi haka muhimmancin a gurina.”

Har Zan kashe se nace

” By the way Dan Allah ki sani Yaya Ismail is the last person da Zan aura, saboda tun farko nace a’a I can’t revoke my words!”Ganin Hanifa ba zata fahimci abinda nake fada ba se kawai na kashe wayar sannan na fara neman number Yaya Ismail, bugu daya ya katse ya kirani, cikin sassanyan muryar shi yace+

” Sofy how are you?”

Na amsa Masa da I’m fine sanann kuma nayi shiru Ina tunanin ta inda Zan fara magana dashi, me Zan fara ce Masa, sai yayi saving Dina da fadin

” Akwai wani abunne?”

Na Dan sauke ajiyar zuciya nace

” Hanifa called, Amma ban fahimci abinda take fada ba”

Ya danyi shiru kafin yace

” Me tace Miki?”

Na mishi bayanin yadda mukai da ita se yace

” Kin koma Zaria ne?”

Kaina na gyada nace

” I’ve left tun shekaran jiya”

Ya gyada Kai yace

” Zanzo se muyi magana kawai”

Daga haka mukai sallama, na zauna saman gadona Ina rike kaina dake min ciwo, haka rayuwar take ne? Ko kuma tawa rayuwar ce cikin Lokaci daya gaba daya ta hautsune ta rasa setin ta, komai ya rikice. Na aje wayar a gefe Ina auna yadda komai Babu dadi.

Bangaren Hanifa ta Kira Anty jidda ta fada Mata halin da ake ciki,

” Wallahi Hanifa Koda Zan karar da komai ba Zaki zauna da kishiya ba, yadda na zauna ni daya kema haka Zaki zauna”

Hanifa tayi dariya tace

” Mom kenan! Har rantsuwa kikeyi? Ai ki daina rantsuwa wallahi Babu Wanda ya Isa ya aura Masa yarinyar nan.”

Anty jidda taji dadin alwashin Hanifa tace

” To kawai Dan saurayinta ya mutu se a nemi lakawa mijin ki”

Hanifa ta Kara dariya tace

” Kuma Mom Bata son shi fa, wannan Ummaah ce ke son hadawa, I know Sofy tun farko da tace Bata son shi wallahi Babu wani Abu da zai saka ta kula shi yanzun”

Sun jima suna magana kafin sukai sallama, Anty jidda cikin hanzari ta Shiga wanka ta fito ta shirya cikin atamfa ta dauki key din motar tayi waje se gidan Ummaah. Tana parking shi Kuma Ismail ya fito, seda ya jira ta kashe motar sannan ya gaishe ta, kadaran kadahan ta amsa shi ba kamar lokacin da zata dinga kirkiro musu topic din magana ba, to ta samu abinda take so, ya aura yarta Kuma Bayan hakan yarinyar is so powerful yanzun, tunda har tana tunanin ja da Ummaah.

A parlon ta samu Ummaah wadda ke zaune tana lissafin kudi da aka kawo Mata na kudaden gidan haya. Anty jidda ta zauna tana duban Ummaah dake dubanta itama, se can ta gaida ta sannan Ummaah tace

” Da tsakar Rana haka, baki jin ranar man”

Anty jidda ta gyara Zama tace

” Wani labari naji shiyasa nace Bari nazo naji gaskiyar abinda ya faru”

Ummaah ta ture kudin zuwa karkashin carpet tace

” Ina jinki, dukda jikina ya bani ba komai bane se zancen auren yarima da Sofyn Babandi”

Anty jidda ta tsira Mata idanu da mamaki tace

” Ke Kika kawo maganar kenan? Taya Zaki min haka Bayan kinsan ‘Yata yake aura”

Ummaah tayi Dan dariya tace

” Kin cika burin yarki ta aura Wanda take so, kema kin cika burin ki na hada zuria da masarautar Kano. Karki Manta munyi auren su Dan Musa ya manta da ita Sofy, nu Kuma na Masa alkawarin idan ya yarda ya aura Hanifa Zan aura Masa Sofy daga baya”

STORY CONTINUES BELOW

” Wannan me bazan taba Bari ya faru ba wallahi, ko me zanyi bazan Bari wata ya ta shiga wannan gidan ba”

Gaban Ummaah ya Fadi saboda tasan wacece Anty jidda, tunda tare suka hada baki aka ma Baba asiri da Anty Rumasa’u, Amma se ta dake tace

” Allah ya baki saa, se mu zuba mu gani”

Ranar haka suka rabu Babu dadi, ni Kuma a bangarena very early ranar Saturday Sega Yaya Ismail yazo, tunda na fito se nake jin kamar zanje Naga Likita ne, Dan sabon shi ne zuwa da wuri ko da yamma, a hankali naji idanuna sun cicciko da kwalla bansan se yaushe ne Zan tuna shi ba tareda kuka ya taho min ba, mun Saba mun shaku Amma mutuwa tazo ta Mana yankan kauna. Na share hawayena da hijab din dake jikina, wayata dake hannuna ta fara ringing, na Ciro seda naji faduwar gaba saboda caller ID Dana gani.

” Hamma”

Na fada a hankali saboda yadda nayi rauni

” Are you still crying?”

Kaina na girgiza kamar Yana ganina, Amma se hawayen ya kubce min na fara shesheka. Ni kaina mamakin kaina nake yadda da bana saurin karaya Amma wannan rasuwar ta min shigar sauri tasa

” Safiyya! Kina jina? Ki daina kukannan haka. Akwai wani abunne dake faruwa Kuma”

Na girgiza Kai na a hankali nace

” I’m missing him!”

Ya sauke ajiyar zuciya yace

” Duk lokacin da Kika ji haka ki Masa addua, ki Kira ni I’ll make sure baki Kara kuka ba kinji?”

Na gyada kaina na Masa godiya sannan nace brother na yazo zanje gurin shi, haka mukai sallama na danji sanyi a raina sannan na karasa inda Yaya Ismail yake, muka gaisa Ina tsaye ban shiga motar ba, ya dubeni yace

” Haka zamu Yi maganar kina tsaye?”

Na gyada Kai se ya daga kafadar shi irin ni naji dinnan, na dalla Masa harara se ya fara dariya ya fito ya samu gefena ya tsaya sannan muka samu kasan shade me tarin concrete seat muka zauna, ya dubeni yace

” Kin fasa tambayata ne?”

” Yaya Ismail please Dan Allah why are you doing this, I thought da kanka kace ka hakura, you’ve found Hanifa worth of been your wife, then me yasa yanzun ka canja magana”

Ya danyi murmushi yace

” Bakiyi mamakin da na aura Hanifa ba? Ok Ummaah tace idan na yarda in return zata aura min ke, Lokacin da Naga zakiyi aure se na hakura, to yanzun ke ba mallakin kowa bace shi ne na tunawa Ummaah maganar da tayi alkawari”

Na kalleshi wani irin kallo nace

” Kasan wannan abin da Kai kamar fada kake son hadawa ko? Ni yanzun problem Dina kawai ya isheni bana bukatar Kari, na fada maka ni bazan aureka ba”

Se Naga yanayin shi ya canja, yace

” Ki fada min me yasa Zan hakura dukda kinsan Ina sonki”

” Saboda Ummaah!”

” What did she did to you?”

Na Masa wani kallo na ni zaka rainawa hankali nace

“Batai min ba, Amma ta yiwa Ammi nasan ka sani…”

Cikeda damuwa yace

” Sofy what does that have to do with me? Dama dalilin ki kenan all this while?”

Na gyada kaina nace

” A gurinka zaka ga kamar ba laifi tayi ba, a gurina ta taba bottom line Dina, tayi crossing limit dinta, I’m sorry su suka lalata zaman gidan mu Dan haka bazan taba auren ka ba”

Cikin damuwar da tafi ta dazun yace

” Sofiyya, to ta Yaya kin aurena zai hukunta Ummaah, why will you be so cruel”

Na dage kafadata nace

” Zaka sani a hankali. Just leave me live peacefully”

Duk yadda yake kokarin ganin ha fahimta naki, da hakan muka rabu Babu wani dadi. Yana Isa kano gidan Ummaah ya wuce, tasan zaije Zaria Dan haka tarba ya tarar na jin labari me dadi, sede ko Zama baiyi ba yace

” Ummaah abinda na dinga fada Miki for years kenan, kinsan saboda abinda Kika ma Anty Hajara yasa ba zata aureni ba”

Da sauri ta mike ya juya bayan shi ji yake kamar yayi ihu, ya Sha fada Mata yadda take treating matan Yan uwanta Bai dace ba Amma Taki ji. Ina komawa daki na Kira Rayha na fada Mata komai nace

” Rayha ki bani shawara, ban ma Yi magana da Junaid din ba, Kuma Sumayya ta kirani dazun akan zai kirani shima”

Rayha ta jinjina Kai tace

” Ki fitar da miji! Shi ne kadai abinda zaiyi bailing dinki”

Tabbas maganar Rayha gaskiya ce sede a ciki wa Zan fitar, Ammi na Kira na fada Mata komai itama haka tace min. Ina aje wayar na fara ambaton Allah cikin Raina kafin can nace

” Allah kasa decision Dina daidai ne”

Daga haka na dauki wayata na fara Kiran Wanda ya fara cewa Yana Sona, mutumin da ya dinga kokarin ganin ya malllake ni Amma naki amincewa. Lokuta da dama da kasan me zai faru da baka Bata lokacinka ba, shiyasa idan zaka ka ki Abu kaki shi kadan kadan!

” Hamma!”

Ya amsa ni sannan na gaishe shi kafin a hankali nace

” Har yanzun kana Sona?”

Ya danyi dariya sannan yace

” Bakin da ya furta so ai bazai furta ki ba. Ina sonki har gobe indai inada Rai, na baki lokaci ne saboda ki danyi satisfying ego dinki, kada na Miki shigar sauri”

Na lumshe idanuna nace

” Kaje ka gaida Baba!”Bayan na kashe wayar na aje a gefena, se naji hawaye ya fara dripping mini kan farar fuskata, mutuwa me tonon asiri, na tuna ni na Kira Usman nace Yana Sona ko ya daina? Duk shunning dinsa da nayi, duk kin amincewa dashi da nayi, duk ikirarin da nayi bazan aura me Mata ba, bazan ma kula Wanda yake da Mata ba, Amma Wai yau nice na kirashi da hannuna har nake kamar rokon shi ya aureni , na sauke duk wani pride Dina nace ya tura. Na kwanta a hankali Ina sakin kuka me karamin sauti, wani irin kunci nake ji cikin Raina, ji nake kamar na fito da zuciyata na dauraye ta a cikin ruwan sanyi ko zanji dadi. Na Dan Jima inayi sannan na Mike Ina ganin to meye tunda shi bai ma Gama saurarata ba ya kashe saboda tsabar farin cikin da yake ciki. Wannan yanayin da naji shi a ciki ya kwantar min da hankali, wasu lokutan na kanyi tunanin Anya idan ban aura Ismail ba , banyi failing ba kuwa? Anya ban rasa babban masoyi ba? Sede ko Babu komai Hanifa Yar uwata ce, auren Yaya Ismail kamar I’m ripping the family apart, tamkar na Kara hada wasu yakin ne, shi Kam Junaid bansan shi ba, ban taba ganin shi ba Amma kawai naji bazan iya ma magana dashi ba, Usman din ne dai kadai right choice Dina, kullum Ina adduar Allah ya zaba min mafi alkhairi Dan haka na dauka cewar auren Usman shi ne zabi mafi alkhairi.+

Bai Kara Kirana ba har dare yayi na Gama Shirin baccina Amma haushin rashin Kiran na nan dankare a cikin Raina duk da kokarin kawadda abin nake a raina. Wayata na janyo na Shiga Wattpad a kokarin ganin bacci ya zo min sannan Kuma na fitar da rashin Kiran da baimin ba daga Raina. Amma ooops bana fahimtar komai hakan yasa na shiga kokarin yin kallo, Wanda ni kaina seda nayi dariya Dan ni bana kallo, it takes ages kafin ka ganni Wai Ina kallo, so film ne Rayha ta tura min ban masan wanne kasar bane nadai karba Amma har yau na gagara Gama single episode. Na aje wayar tareda juyawa na kulle idanuna se naji vib dinta, da sauri na juyo and I found him calling, murmushi na saki w hankali, se Kuma na Bata Rai lokacin da nake Kara wayar a kunnena

” I’m sorry ban Kira ki ba se yanzun, I was very busy Amma kinsan ko sau daya Baki taba barin Raina ba, in fact tun ranar Dana ganki wajen quiz dinnan zuciyata se yau taji sanyi”

Se nayi murmushi Wanda nasan yaji saboda sautin da ya fita,

” Dariya na baki ko? You’ve no idea yadda kikai torturing dina. Duk haduwar mu se kice Wai ke Baki yadda ba saboda wani so called reason dinki”

Na Dan harara wayar kace da gaske zaiga hararar, Nima maganganun da yake se Suka saka ni cikin nishadi.

” So called reason? Haka kake gani”..

Yayi Yar dariya yace

” So tell me what happened you decided to just give me a chance out of nowhere”

Na danyi Shiru shima se yayi shiru alamar Yana saurara ta, nasan Zan Yi hurting dinsa idan nace saboda Ina tsoron auren wasu, Dan haka nace

” Kawai ji nayi na gwada ka”

” Amma kinsan inada Mata ko? Kin hakura kenan”

Na danyi Murmushin takaici nace

” Ko daya, akwai lokutan da kake hakura da wants dinka saboda circumstances. Abu daya Zan fada maka Kuma Zan cigaba da maimaita maka, I’m peaceful person bana son tashin hankali sede cikin zuciyata na yiwa kishiya babban tanadi, inada kullinta a raina”1

Se naji alamar canjawar yanayin shi daga tone din muryar shi

” Why did you have so much hatred akan kishiya? Is not good kwata kwata”

Na danyi dariya nace

” Ba zaka gane ba, Ina fata zaka fahimta a hankali and mind you bawai tsanar ta nayi ba kawai dai I need peace”

STORY CONTINUES BELOW

” Se cewa kike Zaki aureni Amma baki ce kina Sona ba”

Ya fada saboda ya dauke wancan topic din, na danyi dariya nace

” Shekara nawa kayi kana trailing na aure ka naki, kaga yanzun ma a hankali zaka ga na fara sonka”

” Ni ban yarda ba Dan I always believed cewar kina Sona, shiyasa Baki taba mantawa Dani ba, duk lokacin da muka hadu Baki son mu rabu”

Mukai ta musu akan hakan daga karshe yayi convincing Dina Akan ina Sonshi, haka muka Yi sallama Ina tariyyo dukkan wata Hira da mukai. Kafin sati ya rufa min shaku sosae ni dashi har na kanyi mamakin hakan, to da tuntuni me yasa Bai rike min kafa ba ya barni na dinga denying dinshi. A wañnan halin semester ya Kare na shirya tafiya Gumel, tun ana saura kwanaki uku Ummaah ta kirani akan na sameta a gida idan na shigo kano, na Kira Ammi da Baba na fada musu Suka ce naje, tuntuni na fadawa Baba ni na tsayar da Wanda Zan aura he’s nowhere near to Ismail ko Junaid, Baba yasa albarka yace idan ya shirya ya sameshi. Tunda na Gama hada kayana nake jin jikina a sanyaye, se nake tuna wancan tafiyar da nayi, so koda Albi yace zai zo ya kaini se naki yadda Dan gani nake kamar it will happen again, Ina ganin shi idan na rasa shi I’m gonna go insane. Har seda ya fahimci hakan yace

” Tsoro me kike ji?”

Na girgiza kaina nace

” Ba wai tsoro nake ji ba, kawai dai abin ke dawo min”

Ya gyada Kai yace

” Nothing will happen inshallah, Zan ta Miki addua kije lafiya. Zaki tsaya a Kano din?”

Na gyada kaina ina Kara rike wayan a kunnena nace

” Eh zanje idan na sauka zamuyi waya”

Daga haka mukai sallama ,Widad dake gefena ta mike tace

” Har kin sake dashi kenan, gaskiya kinyi kokari banyi tunanin zakiyi accepting wani da wuri haka ba”

Tsaki na Mata bance komai ba saboda wani lokacin she’s very annoying. Tare muka tafi tun da muka tashi na Masa message akan min dauka hanya, se ya tura min kalamai masu sanyi da kwantar da zuciya Wanda suka Sa naji duk wani tsoro ya tafi. A Kano muka sauka, gidan Rayha na fara zuwa, ta Gama shiryawa tana jirana muje. Ko abinci ban ci ba muka dauka hanya gidan Ummaah, munata Hira tana ta zolayata Wai a karshe dai mutumin da naki shi din na dawo na yarda dashi. Nidai Babu bakin magana se murmushi kawai, Albi yayi hakuri da ya dinga jirana all this while. Tun kafin mu karasa Rayha ta Kira Na’ila ta fada Mata ai na yadda Zan aura sir Usman. Dukda ba speaker take ba Amma Ina iya juyo ihunta, Rayha ta dubeni tana dariya daidai parking a gate din gidan Ummaah tace

” Karki dauki Kiran Na’ila dan seta tsuye ki”

Nayi dariya hannuna rike da little na fito nace

” Ke Kika sani, ai ke Kika siya min, bazaku burgeni ba se kunyi broadcasting a Bakori girls”

Tayi dariya itama tace

” Meye abin gatse, karki damu ai main group ma kuwa”

Ban Kara kulata ba muka shiga gidan, Yana nan yadda yake kusan duk zuwan da zakai zaka tarar an kalkale can a canja face din can, haka suke gidan masu kudi. A parlor muka sameta, ta Dan rame Kuma alamu sun nuna kwana biyu kafar tata damun ta take. Zama mukai muka gaishe ta ta karba little da fir Taki zuwa, ta dubi Rayha tace

” Kiga ‘ ya har tasan uwarta”

Rayha tace

” Saboda Baki zo kin ganta ba shiyasa Taki yadda dake”

Tasan magana Rayha ta fada Mata Amma se ta fuske, aka cika Mana gaba da abinci dasu lemuka muka ce min koshi, seta dubi Rayha tace

” Rayhana hau sama inason magana da uwata”

Cikin sauri nace

” A’a Ummaah kawai fada shiyasa muka zo tare”

Maganar ce dai ta kullum wato auren Ismail, tunda na Gama secondary School ake magana daya, Ina tunanin ya kamata su hakura

” Ummaah kinganni gaskiya bazan aure shi ba, ni yanzun na bawa wani izinin turawa, aure zanyi nan Babu jimawa”

Se tayi Dan murmushi tace

” Idan ni ce ke zanso na dauki fansar akan abinda Babar Hanifa ta yiwa uwata…”

Rayha ta girgiza Kai se yanzun muka fahimci inda ta dosa wato so take ta toxarta Anty jidda da Hanifa ta hanya ta.

” Ummaah mu komai da akai ya wuce, mun fara ganin sakayyar komai, mu Babu Wanda zaiyi amfani damu wajen toxarta wani. Kiyi hakuri zamu tafi”

Na taba fada muku Rayha Bata tsoro ko? To haka take baro baro, har muka fita a parlon Ummaah ba tayi kwakwaran motsi ba, seda Rayha ta tada motar sannan wata daga cikin maaikatan gidan ta kawo Mana paper bags guda uku inji Ummaah. Mukai godiya muka wuce. Duk yadda Rayha taso na kwana naki Dana fadawa Albi yace in kwana kawai shima washegari zai shigo Kano se kawai ya kaini Gumel din.

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng  Taken mu a kullum shi ne ” …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *