UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 10 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 10 BY SHATU

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Na goge dukkan digit dinsa dake cikin wayata, haka chats dinmu nabi nayi wiping dinsu,na Kuma bi messages da mukai exchanging ta inbox nayi deleting dinsu Baki daya, ni nufi na ai bazan samu wani Abu da Zan dinga tunawa dashi ba. Haka nabi pictures dinsa cikin wayata na goge, zuciyata na Gaya min cewar it’s over, kullum idan nayi shiru se nace is not as if shi ne karon farko daya fara ganina da Yaya Ismail ba, karewa a gaban shi na Mara Yaya Ismail, na dauka darajar shi akan ta Dan uwana shi Kuma se yaga sakayar da zai min kenan. Na rufe chapter shi Amma kuma chapter ban tabbatar ba ko ta rufu ko Bata rufu ba. A hakan lokaci yaja har muka fara Shirin karkare semester, gashi daga wannan na gama preclinical Dina se Kuma clinical.

Tun abun na damuna har nazo na Saba na fara kokarin mantawa dashi, saboda zuciya wata Mysterious hallittar Allah ce, idan kana son Abu yayi nesa da Kai se zuciya ta fara kokarin ganin ta samu abinda zai maye gurbin wannan abin a gurinta, it’s a concept da da yawan mu bamu fahimta ba, haka ma idan kana son mutum Yana treating dinka badly, kana yafe mishi duk lokacin da abin ya faru, to shi zuciyar shi na Kara sonka yayinda Taki zuciyar na fara fitar dashi daga cikin ta, a lokacin da zai daina komai yayi embracing dinka fully a waƱnan lokacin taka zuciyar ta riga ta hakura dashi.+

Nayi nisa sosae a karatu naji sallamar Widad, ta shigo hannunta rike da Leda, na dago Ina kallonta har ta gama shigowa ta cire hijab dinta ta aje akan gado ta zauna tana dubana yadda na baza books, tab dita a gefe ga wayata da Kuma journals Dan haka nake karatuna very wide and broad se na tabbatar na hada ideas da yawa kafin nake hakura. Zama tayi gefen gado ta bude ledar ta Ciro packaged abincin ta Miko min na karba a hannunta, tareda cewa

” Thank you, dama yanzun zanje na ci abinci na kona glucose Dina, har brain Dita ta fara daina ganewa”

Tayi murmushi tana bude handouts dinta ni Kuma naci in utmost silence,sede taste din abincin yasa Bature yayi crossing mind Dina, shi ne indai zaizo ke kawo min abinci me irin taste din, rubber spoon din na aje na dubeta hankalinta duka Yana kan karatun da take, nace

” Widad Likita yazo ne?”

Se tayi dariya tace

” Ya akai Kika gane?’

Ture abincin nayi daga gabana na dubeta nace

” Just tell me, Ina Kika hadu dashi”

” Ni na Kira shi yazo, shi ne ya kawo Miki abinci saboda yasan Baki ci ba.”

Na Dan ja tsaki nace

” Widad ba Wasa nake ba, don’t provoke me, me yasa yazo?”

Na fada Ina jin Raina ya fara baci, ta dage kafadar ta ta maida kanta kan littafin ta ba tareda ta Kara min magana ba, balle ta bani amsar tambayar Dana Mata. Se na ture abincin na maida hankalina kan tab dita, Amma se na daina gane komai,Babu abinda nake fahimta hakan yasa na Mike dauke da wayata a hannu na cira veil na fita, bansan Ashe trap suka min ba, can Bayan hostel dinmu naje Babu mutane sosae na zauna gefen wata katuwar bishuyar maina, na fara Kiran shi, zuciyata tamkar anyi ripping dinta haka nake ji, tamkar na Ciro ta na dauraye ta cikin ruwan sanyi haka nake ji,na Kira har say biyu Bai dauka ba, but na saka a raina cewar ko ba zai dauka ba wallahi sena karar Masa da caji. Ana wajen biyar ya dauka muryar shi can kasa yayi sallama, Banda muhimmancin sallamar da bazan amsa ba, Dan haka Ina amsawa nace

” Dama abinda kake nufi dani kenan, tun farko se ka fada min Widad make so ba se kayi putting mask ba, ba se ka kirkiri fadan da bashi da amfani ba, karka manta Yaya Ismail confessed before and I chose you over him, I left responsible and grateful mutane saboda kai Amma a karshe abinda ka bani kenan. Lemme warn you idan zakai abinka kaida ita kada ka Kara jawo ni ciki, sannan nayi regretting rashin bude maka halayena ka fahimci ni wacece, Babu damuwa ka cigaba yadda zaka rasani har abada!”

STORY CONTINUES BELOW

Ina kaiwa nan na kashe wayata, se naji wani sanyi ya mamaye zuciyata, naji dadin na amayar da dukkan abinda nake rukewa, Dama haka extrovert mutane ke ji? Amma mu muta rike Abu Yana Neman kashe mu da ranmu. Na zauna a gurin se naji a hankali hawaye ya fara saukar min, na saki kuka a hankali Dan nasan zai taimaka min na Yi fighting abin, Ina jin wayata a hannuna tana ringing Wanda nasan shi ke Kira Amma ko kula shi banyi ba se na maida wayar flight mode, na goge hawayena na koma daki Bayan nayi alwala, na sameta tana waya kamar bana jin abinda take fada na dauki books Dina na cigaba da abinda zai fishhe ni

” Nifa ba wani Abu nace Mata ba, abinci kawai na kawo Mata…to nasan zata ji haushi ne?… Inshallah bazan Kara shiga abunku ba.”

Ta Gama fada sannan ta kashe wayar ta cemin zata koma dakinsu na sake fuska na Rakata bakin kofa ta tafi na dawo na janyo abincin na karasa ci abin dariya.

Washegari da yamma Sega Kiran Ammi, na dauka ta fara tambayata me ya faru tsakanina da Bature nayi shiru Ina assessing tambayar cikin kaina, aikuwa ta rufe ni da fada, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, har ta cemin I’m an ungrateful person, in Banda haka me ye Hadi na da Ismail, ban taba ganin ranta ya baci haka ba. Seda ta gama nace

” Ammi kiyi hakuri, inshallah Zan Kira shi na bashi hakuri. Amma Ina son idan akai irin haka ki dinga tambayata my side of story”

Se Kuma ta sassauta tace

” Ke ya kamata ki fada min, ba se kin jira har shi ya kawo karar ki ba. Me yasa zaki bi Ismail Kuma yayi Miki magana Kika fishi fushi ?”

Na zauna gefe nace

” Kinsan ba halina bane na fada Miki munyi fada saboda na dauka zamu shirya, Bai fada Miki bayan ya tafi na fahimci bai dace na fada Masa abinda na fada ba Amma Bai picking ba Bai Kuma Kira ba. Ammi ya zanyi? kawai saboda nabi  Yaya Ismail, shi yasan I chose him over Yaya Ismail din, me yasa shi bazaiyi reasoning Yaya Ismail is still my cousin ba.”

Se Kuma ta koma lallashina, tareda nuna min maza haka suke, kishi ne dasu nace

” Ammi nifa ki fada Masa idan yasan abu kadan zai dinga fushi Dani Zan fasa ne, ni bazanyi aure nazo Ina jin kuncin da Kika ji ba, ni bazan dauka ba.”

Se Kuma ta fara min nasiha akan na cire hakan daga Raina ma, zamuyi zaman mu lafiya, sannan mukai sallama. Washegari Banda exams se gashi yazo na fita nida Widad da da Taki nace wallahi se ta bini, Yana tsaye bakin motar shi Yana waya na jira ya gama sannan ya karaso Yana murmushi yace

” Sofy dear! Ya exams”

Na Dan saki fuska na amsa masa, suka gaisa da Widad tace zata je ta dawo, ya zauna Nima ba zauna bayan mun je wani Dan eatery a VIP section yadda Babu hayaniya sosae.

” I’m sorry da duk abubuwan da suka faru”

Na dauke kaina daga kallon shi nace

” Ya wuce Amma duk lokacin da ka Kara haka just know it will be over tsakanin mu, ni bazan dauka hakan ba, ba zaka dinga fushi ba over a silly thing”

Ya Kara bani hakuri shi kenan se muka cigaba da Hira abinmu, min Jima tare sannan ya tafi na koma hostel, ranar da daddare kusan raba dare mukai Muna waya saying all abinda bamu fada ba na wajen sati uku, sede akwai lokutan da bashida amfani yin fada ko kadan, baka San me zai faru ba. A satin daya rage min a Zaria we were so close muka bude sabon chapter soyayya, har yafi na da, ranar Dana Gama exams yazo daukata, ranar Widad Kuma nada sauran biyu tace na jira ta Gama mu tafi naki saboda washegari Rayha zasu dawo itada Fahad da babyn ta, nasan nayi laifi bance ta haihu ba, ta Haifa yarinyar ta Hannatu ana Kiran ta Little. Tun safe dana tashi bana jin dadi kaina ya dinga min ciwo kamar zai tsage, seda Nasha pcm sannan na danji dama dama. Da wurwuri muka dauka hanya saboda yace Yana son dawowa Zaria a ranar yaga ginin da ake mishi. Tun a hanya muke Hira Yana fada min plan din rayuwar shi.

” We will have Yara biyar, idan suka fara girma nasan lokacin inshallah nayi kudi kowa a turai zaiyi Alevel din shi”

Nayi dariya nace

” To haka ka tsara, to Allah yasa muna da Rai da lafiya”

Yayi murmushi yace

” Zan soku na Baku kwanciyar hankali da kuke bukata, Zan zame muku shield din da Babu wani Abu da zai tunkare ku keda yaran”

Nayi dariya nace

” Muma zamu so ka yadda kake son mu”

Wayar shi ce tasa Bai bani amsa ba, ya dauke kan shi daga titin Dan dakko wayar, kamar ance na kalla gefe wata mota ta taho a highest speed ta nufo mu, hannuna da bakina na rawa na dafa hannun shi dake kan steer wheel tareda fadin

” Gefenka!”

Bansan ko ya amsa ni ba shikenan everything went blank! Baka gane rayuwar is too short se wani bangare na jikin ka ya rabu da kai, bayan komai ya lafa se Naga dukka rayuwar is just an empty shell. Fada, masifa da tashin hankali duk na menene? Gaba daya rayuwar idan ka dunkule ta is too short wallahi.+

Motar da ta buga tamu da muke ciki, irin Wanda suke hording kayan abinci ne, sun taho custom Kuma sun biyo su, suna neman tsira Dan haka kowacce mota ce a gabansu zasu iya shigar mata Dan su tsira, tana tahowa mu Kuma zamu wuce ta buga mu tareda hada mu da wata motar, Bayan furta masa wannan “Gefenka” nasan na runtse idanuna daga wannan ban Kara bude shi ba se a gadon asibiti, ko kuma nace a kwance a kasa Shima bawai na dawo consciousness Dina bane duka na dai ji hayaniya da koke koke gefena, ban Kara Kuma gane komai ba na Kara dozing a gurin. Lokacin Dana Kara dawowa hayyacina I was fully aware of inda nake, me ya faru dani da Kuma su waye a gefena. Ko Ina na jikina ciwo yake haka yayi min nauyi tamkar an daura min Abu a kirjina. Na bude idanuna Amma hasken da ya nemi lalata min pupils dina yasa cikin sauri na mayar na kulle idon, se Kuma a hankali na Shiga bude idon nawa, har nayi adjusting da hasken dakin, hannuna na hagu na daga Dan taba kaina da nake jin tamkar an daura min Abu me nauyi Amma se hakan ya gagara, Shima hannun yayi nauyi se na Kai idanuna kan shi, take na gane na karye ne saboda yadda akai casting hannun. Na runtse idanuna sannan na fara kokarin tashi, cikin saa na tashi na zauna Ina bin dakin da kallo, ni kadai ce a ciki Babu kowa se can gefe na hanga Gwoggo akan sallayya tana Jan casbaha hannunta. Na bude baki nace

” Gwoggo”

Amma ko ni kaina banji abinda na fada ba balle ita, se kawai na sakko daga kan gadon na nufeta, sede duk jikina ciwo yakeake min,na karasa gefenta na kwanta a kafadar ta, cikin hanzari ta dubeni tareda rungume ni a jikinta, fuskar ta na fitar da tsananin annuri na farin ciki, Nima nayi Mata murmushi se Kuma naga ta rike hannuna me lafiya tana sakin kuka me ban tausayi, a tuanina duk tausayin na ne.

Ammi ta shigo bayanta Baba suna rike da carton a hannun su, Ammi na ganina a tsaye ta karaso gurina ta rungume ni, tana kuka a hankali, Nima se na fara Taya ta, Baba ya karaso Yana tambayar Gwoggo yaushe na tashi, tace Masa ban Jima ba se ya juya Dan ya sanar dasu na tashi, suka karaso in a team, har lokacin Ammi na gefena tana kuka, Wanda yasa na fara jin kamar akwai wani Abin dake faruwa, idan Dan nayi accident ne to ai yanzun na tashi. Suka zo se Baba ya fita da ita Gwoggo tabi bayansu, Dr ya tambayeni ko Ina jin ciwo na Masa bayanin jikina ne ke ciwo yace buguwa ce a hanakli zai daina, zasu sallameni se muna zuwa follow up tunda gyaran yayi kyau, Bayan 3 weeks se a cire. Na musu godiya da muryata da ta fara fita a hankali. Gwoggo tasa nayi wanka, Anty Safara’u ta hada kayanmu Amma har lokacin Banga Ammi ta Kara dawowa ba. Dukkansu sunyi jugum su day suke tare dani, seda na gyara jikina sannan muka fito Dan tafiya se lokacin kwakwalwa ta ta tuna min ai ni da Likita mukai accident din, shi Yana Ina, tsayawa nayi cak Ina duban Baba dake rike da hannuna na dama nace cikin dasashiyyar murya

” Baba Likita fa?”

Yayi min shiru kamar Bai jini ba se nayi tunanin Bai ji din bane da gaske, Amma hannunsa dake cikin nawa se naji sunyi gumi sosae har seda na kalla fuskar shi, naga gaba daya ya fita hayyacin shi, fuskar shi tayi zuru zuru. A take naji gabana ya fadi. Ban Kara magana ba har muka dauka hanya seda mukaje Dayi sannan na fahimci Muna katsina, tun da muka bar Dayi nake jin wata faduwar gaba na riskata, Ammi dake gaba kusa da Baba lokaci zuwa lokaci se naga ta share hawayenta, haka Gwoggo ma se ya zamana Anty Safara’u da Baba ne kadai Wanda Basu kuka, itama Anty Safara’u rungumeni tayi jikinta nayi lamo. Daf da zamu bar funtua na kasa hakuri na dubi Anty nace

” Ummiey Ina Likita yake, tare dashi mukai accident din ko baa fada muku ba”

Ai Ammi na jin abinda na fada ta Kara fashewa da kuka, haka Gwoggo ma duk se naji hankalina ya tashi, na dubi Anty Safara’u idanunta sun kawo kwalla nace

” Ummiey ki fada min me ya same shi? Shima karyewa yayi?”

Ta rungume ni a jikinta tana shesheka, har Raina ban kawo zai mutu ba, a kwana kusa ban taba kawo Masa mutuwa ba Ashe shi his days were only a mere count down, Ashe a karar kwana muke. Baba ne ya fada min daf da min shiga maska, a cewar shi gwara na sani ba se anje can ba. Yana fada min naji gaba daya hawayen idanuna sun kafe, na kwantar da kaina a jikin kujerar motar, tareda runtse idanuna a hankali Ina jin wani Abu na taso min tundaga cikina har zuwa makogaro na, duk wasu tunani were blocked, na kasa fahimtar abinda kaina ke ciki. Ammi ta dubi Baba a tsiarce tana fadin

” Baban Sofy kaga Bata kuka, Gwoggo kina kallonta Taki kuka”

Na bude idanuna nace

” Gwoggo Wasa Baba yake ko, Bai mutu ba ko? Ina laifin ace Shima ya karye kamar yadda nayi. How am I supposed to believe cewar Likita ya rasu”

Kowa yaji abinda na fada yasan hankalina ya fara gushewa, tundaga wannan maganar da nayi ban Kara cewa uffan ba Kuma na kasa kukan sede zuciyata kamar ana soya ta haka nake ji, tunda muka shiga nake bin kowa da idanu, Ammi ta rungume ni, ganina da plastered hand yasa suka San ni ce wadda mukai accident tare se kuka ya dawo sabo, na hango Yan uwana kacakaca a gidan saboda umarnin Gwoggo ne kowa yaje. Dakin mahaifiyar shi aka kaini, tunda na shiga gaba daya fuskokin dake ciki tamkar an cire fuskar Likita an sassaka musu a tasu, se naji labarin mutuwar shi ya dawo min, a hankali na shiga ciki, tunda taga Ammi a bayana ta saki kuka tana zaune can kuryar daki sanye da hijab. Hannunta ta Miko min tana fadin

” Alhamdulillah bamuyi gawa biyu ba, taho yata Babu rabon naga auren ku”

Na karasa inda take zaune tana rikon hannu na saki kuka kamar Zan fitar da idanuna saboda kuka, dukka ‘Yan uwanshi suka dinga kuka. Na Jima Ina kuka a jikin matar har aka samu nayi shiru, anan gurin nayi sallah amma abinci duk yadda aka taru akan lallashina naki ci, da suka ishe ni se na rike hannun Mama, Maman Bature na dinga kuka se tace su barni kawai. Ban taba jin bakin ciki a iya rayuwata ba, ban taba jin zuciyata tayi kuncin da tayi ba. Da dare yayi duka aka kwanta, Mama ta matsa min akan lallae lallae naci abinci naki se Naga tana kuka kawai se na dauki cup din tea na kafa a bakina, daci naji Amma hakan na daure nasha. Can cikin dare Ina takure na lulluba da hijab din da sister din shi ta bani da zanyi sallah, tunda aka kwanta nake kwance Amma ko dison bacci Babu idanuna, maganganun mu da shi kanshi ke dawo min, na tuna Yara biyar da yace zamu Haifa, I remembered yadda yake planning rayuwa hundred years to come, shi kan shi Bai kawo wa Kansa mutuwa ba, mikewa nayi na fita daga dakin mutane nata bacci abinsu, se Naga basuda matsala kenan, can gefe na samu na rakube na dinga kuka inajin dama Ina da damar zabar rayuwa ko mutuwa Allah na tuba da Zan zaba gwara nabi Bature Nima. Dafa ni naji anyi da sauri na goge hawayena na dago idanuna, Rayha ce alama sun nuna daga toilet take, ta zauna gefena idanunta sunyi ja, tunda na dawo na ganta amma I wasn’t in the mood muyi magana, duk yadda nake daukin ganinta, dawowar tata yazo min baa dadin Rai ba. Mun Jima da ita tana ta rarrashina sannan tasa nayi alwala nayi sallah amma Shima a sujaddar se na Jima Ina kuka, kafin safe na zabge ga jinya ga Kuma tashin hankali. Ashe kwana na biyu asibiti, bayan motar ta buge mu ya samu fractured rib Wanda ya Huda lungs dinsa, tun kafin akai mu asibiti ya rasu, nikam mild head injury ne saboda buguwa se karaya a hannu.  Nayi kuka nayi kukan rashin shi, na tuna dukkan wahala da sadaukar da yayi min, ya bar aikin shi Dan dakko ni ko kaini makaranta, Ashe our time is limited, na tuna fadan mu. Nayi kuka har idanuna seda suka fara ciwo, bana tunanin akwai ranar da Zan Kara irin wannan kukan a rayuwata.

Full-width

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng  Taken mu a kullum shi ne ” …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *