UMM ADIYYAH CHAPTER 55 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 55 BY AZIZA IDRIS GOMBE

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

matar nan, ina ga ba ta san me muke zo yi ba.”
“Me muka zo yi?” Mami ta mayar mata da tambayarta.
“Neman lafiya?” “To, waye kuma Likitar?” “Tta.”
“To kar ki damu, a sannu a hankali komai zai tafi daidai.” Yanzun da Maami ta zauna
ta ji komai da kunnenta, abin ya Kara kashe mata jiki, amma abin mamaki kullum Www.bankinhausanovels.com.ng
aka zo wannan zaman labarin. Adiiyya sai ta tuno wani abin sabo. Har ya zamana ba
ta Car-dlar idan ta zo ambaton sunan mijin Hajiya. Sai da aka shafe watanni suna zuwa wurin
Doctor Astha, tana sabunta masu
hanyoyi da dabaru, har ya zamana Umm Adiyya da kanta ta san cewa tana jin canji

a jikinta, game da yadda take kallon kanta. Don abu kadan mutum zai mata, ta ji
haushi ko ta yi tunanin don ba a sonta ne aka mata akan, ko kuma ba ta son shiga
mutane, amma yanzu ba ta jin kamar kowa ita kadai yake kallo idan tana cikin taro.
Sai da Likita da kanta ta bawa Abban shaidar cewa an samu Canji a al’amarin,


sannan ta rage mata lokacin zuwa. Zuwa wannan lokacin ita kacfai ma ake bari take
zuwa wurin Dr. Astha, wannan lokacin ne kuma suka gangaro kan matsalar aurenta.
Wata rana, Umm Adiyya tana rike da abin danne fefofin kan teburin Likitan ne, ta
gama ba ta labarin yadda ta yi aure, da ma duk sauran ababen da suka faru bayan auren.
Likitan ta yi murmushi ta ce, “Labarinku akwai Kayatarwa. Kun sake hadtuwa bayan
lokacin? Da tsohon mijinki, nake nufi…” Umm Adiyya ta fara girgiza kanta ne ta tuna, Likitan ta fi so ta bada amsa baki da Www.bankinhausanovels.com.ng
baki. Don haka ta ce, “A’a. Baya nan a Rasar yanzu.”
“Ya facia miki baya nan ne, ko a ina ki ka ji?’ “A bakin ‘yan gidanmu na ji.” “Kin shirya ganinsa a karo na biyu?”
Umm Adiyya ta yi shiru tana kallon Likitan. A hankali kalaman suka fito daga bakinta.
“I think, I’ll like to go for my Masters, Mechatronics Engineering.”
“Hmm! That sounds good.” Likitan ta fadla tana kallon Kyallin da ke idanunta, ba ta
mance yadda Umm Adiyya ta Ki ta ce wani abu game da sake ganin tsohon mijinta
ba. Engr. Zaid Abdur-Rahman. Wannan ya sa ta zana alamar tambaya a gaban dan rubutun da ta yi a takardar hannunta.

*********

Yanzu watanni shida da faruwar hakan, ga shi har ta gama Semester clin farko tana cikin na biyu.
Karatu take yi ba kama hannun yaro, ba ta kula kowa, ba ta shiga sabgar kowa, ko
shigarta makaranta, ta shiga ne a matsayin matar aure, ba ta san wane gulmawiyan
bane ya fada a makarantar da har mutum irin Malam Yusuf zai kalli cikin idanunta, ya ce yana sonta.

++++++++++

“Ummu A. Don Allah kar ki bi wani wuri, ba na son frosting din ya fara narkewa, kin
ga dai ana ruwa, amma zafi ba kama hannun yaro.”
“Ho! Maman Walid, kin min kashedi ya kai sha biyar, idan ki na yawan magana ne Www.bankinhausanovels.com.ng
sai subul da hannu ya yi Kamari ki ga tsautsayi ya auku.” “To Wallahi ki bari, idan na rage ayyuka na, na kai masu da kaina.” Dariya Umm Adiyya ta yi ta dauki kwali daya ta kai mota har ma ta bar motar a bude, don samun saukin sanya sauran. Ta koma ta Clauko na biyun ne, tana isowa falo ta ji abu ya
murKushe. “Hnnn!” Wani sauti ya kubce daga bakinta a razane, zaro idanunta ta yi ta kalli gabanta, yau ta ga ta kanta, me take kallo za ta buge ket clin da aka gama mata… Idanunta ne suka Kara wangalewa. “Uhm… sorry.” Juyawa ta yi ta runtse idanunta, babu tantama yau kam za a manna mata kalmar
ballagaza, mai tafiya da gudu tana kwara abubuwa a jikin jama’a. Hannu ya sa ya lakaci man bota mai zakin jikin rigar ta sa yana kallo, “Hmm! Na ga alama ba ki canza ba ko? Koda yake akwai canji, this is sweet.” ya fada yana dandana sauran na hannunsa.
Huh? Kara bulluKowa idanunta suka yi kafin ta fahimci me ya fadfa. “Oh, ba haka na ke ba da gaske, kai ma ka sani, kawai ina sauri kuma na bar Kofa a
bude, ban zaci zan samu mutum a hanya ba, kuma Adda Zubaida ta ce na yi sau…” “Cake dina!” Suka ji muryar Adda Zubaida ta fito a razane daga bayansu.
Sorry.” Umm Adiyya ta fada cikin yanKwane fuska, ai yau nata ta same ta. Ba wani sorry din nan, tun dazu na ke ta miki hucluba ki yi hankali da abin nan, kina san minti kadfan ya rage su buKace shi. Kun zo kun zubar min.” “Sorry za mu gyara.” Ya fadla hade da karbar kwalin daga hannun Umm Adiyya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Adda Zubaida ta sa hannu ta karbe abin ta. “Ba za ku iya ba. Argghh! Me ya sa ma na tsaya ina maku bayani? Uncle TJ. Ina su Minaal?” Lafiya Kalau.” Adda Zubaida tana wucewa da kwalin ket cinta. TJ. Ya yi murmushi ya ce, “Idan ki ka ci-gaba da bata min kayana, za ki saya min wardrobe cike tim da kayan sakawa.” Baki ta bude za ta yi Magana, sai kuma ta rufe, sannan ta sake budlewa. “Ka na
nan?” Abin da ya iya fitowa daga bakinta kenan. Hannu ta sa ta make goshinta, Sannu da aiki. Uhm! Ina wuni na ke son cewa.” Lafiya dai lau, kafin a zuba min pink butter a
jiki na.” “I’m very sorry about that.” Juyawa ta yi kan teburin cin abincin falon ta dauko kwalin Tissue ta miKa masa, tana ba shi dukansu biyu suka tuntsure da dariya. “Na ga alama dai wata ta girma.”
Kunya ta ji kamar ta nutse cikin Rasa, cikin tuno randa ta zuba masa miyar kuka, ita
ta shiga goge masa, ashe bai manta ba. Wannan ya sa tana karbar kwalin, ta juya
da sauri ta bi bayan Adda Zubaida, ta je ta samu ta kumbura tim! Sai masifa take yi.
“Na ga alama kwashe komai da komai zan na yi, idan na ga ku biyun nan, kullum ku
na cikin bari, idan kun ga juna sai ka ce wasu Kananan yara ku na tafiya ba kwa
ganin gabanku. Kin sa yanzu komai ya lalace, yanzu ta ina ki ke tunanin na fara
gyara wannan abin?…” Haka dai Adda Zubaida ta ci-gaba da mita, kafin ta ankara
Umm Adiyya ta jona mixer, ta sake kwaba mata wani sabo, taba hannunta ta yi ta
ce, “Adda ga wani, kwashe wancan na gyara
miki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ajiye kitchen roll din hannunta ta yi da Karfen sumulmula ket clin nata, ta yi ajiyar
numfashi, sannan ta bawa Umm Adiyya wuri.
“Bari kawai na yi, je ki ji da bakonku. Kuma ba ni bace mai tafiya ido a sama, wa
yake shiga gidan mutane ta gefe-gefe, kuma ba tare da babban sallama ba?”
Adda Zubaida na hada kayan tabe-tabe a Tray tana cewa, “Ku dai ku ka sani da
bare barenku na fama.”
Tana fita ta ji muryar su Walid a falon, jin zuwan Baffansu ya sa suka bar wasan da
suke yi, suka nufe shi da muma. “Aunty Zubaida na ga alama zan daina sa fararen
kaya a gidan nan.”
Sai lokacin abin ya ba ta dariya ta ce, “Yaya wurin su Hajiya ko ba ka leKa ba?”
“Tun safe ma muna can, lafiyarsu Kalau. Na ga Ummu ta zo maku hutu.” Ya fada
yana kallon bangaren Adda Zubaidan.
Murmushi ta yi ta kau da kanta, sannan ta ce,
“Uncle TJ. Kenan, mu fa ba ma son PDP.”
“Wallahi da dai ba ma ‘yar haka da ke, to amma bari na Kara ladabi ko za a fada min yadda abin yake.”
“Ai ka ji koma menene, ba za ka zo ka sani a gaba da tambaya ba.”
“Da gaske ne kenan?” Kai ta gyada masa, amma ta Kara da cewa. “Hakan ne amma dai nan din da ta zo kamar yadda ka ce ne, hutu ta zo yi.” Ta fada zancenta cike da harshen damo. “Yau kuma. To na gode, ayi hutu lafiya.” Ya fada yana murmushi.
Haka nan ya kau da maganar bai sake dagowa ba, suka shiga wasu hirarrakin, Www.bankinhausanovels.com.ng
sannan ya yi masu sallama, bayan ya shigowa yaran da wata Katuwar leda cike da tsaraba.
Lokacin da ta fito da gyarraren cakes din ta samu suna sallama, don haka ta kai su
mota ta leKo ta ce, “Sai anjima.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *