UMM ADIYYAH CHAPTER 53 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 53 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya

Adda Asma’ ba fa yawo na ke yi yanzu ba, ni da na ke idda?” “Ina dai jira ki gama idan lokacin yawon ya yi, a zo min, idan ba haka ba zan san matsayina a wurinki, wai tsaya ban gane bama. Umm Adiyya ta rufe zif din Karamin kit cinta inda ta gama saka kayan gyaran

gashinta, da su man shafawa. “Ki na nufin wai kin ajiye aikinki ne, ko me?”

“Kayya! Wane aiki ne yanzu, ni ba abinda yake ban sha’awa fa, kin ganni yanzun nan.
Ki dai je ki huce, ba za ki tsayar da rayuwarki ba ai haka nan, don wannan abin ya faru. Inshaa-Allah komai zai wuce, batun wancan maganar kuma ki kwantar da hankalinki, ki cire a ranki, da wuya, amma lokaci ya yi da za ki daina bari yana jan
ragamar rayuwarki, abin zai miki yawa.” Daga kanta sama ta yi tana Kokarin hadliye hawayen idanunta. “Adda Asma’ ina na taba tunanin bayan duka wannan shekarun abin nan zai dawo ya zame min matsala


a rayuwata. Kullum tunanina, tunda ba wanda ya sani shi kenan. Zan tsira, hankalina bai sake tashi ba, sai bayan da na ga wanda na aura, bayan na gama masa tanadi kan abinda na kama shi da shi, ya zo ya ga ga halin da na ke ciki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Abinda ki ka kama shi da shi?” It’s not important. (baida muhimmanci) Abinda kawai na ji tsoro shi ne yaya zan yi?” Wani murmushi ta yi mai sauti, wanda yake cike da ciwo, sannan ta ce. “Cikin ikon Allah, muka daidaita, ban Boye masa duk yadda abin ya kasance ba, na fadia masa, a lokacin idan da zai gan shi, ina da yakinin yanzu muna zaman taraddadi, domin za a iya kama shi da laifin kisan kai. Haka ya ajiye fushinsa a gefe ya nuna min babu macen da ta kai ni daraja a idanunsa. Adda Asma’ Yaya Zaid yayi min soyayyar da cikin watannin da muka yi zaman
lafiya, zan iya cewa, ya ci ya shafe duk wani Kuncin rayuwata. In fact, ya sa na fara mancewa da abinda ya faru, ya sa na sake fara yarda da kaina, ki auna ki ga halin da zan kasance, idan lokaci daya ya rikidle, ya zame min ina kallon fuskar Mijin Hajiya a madadin fuskarsa.” Adda Asma’ ce ta yi saurin dafa hannunta, Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ummu A.” “Na’am?” Ta fad tana kallon ‘yar-uwarta.
“Kin san cewa yanzu ki ka ambaci sunansa?” Wani irin abu ne Umm Adiyya ta ji yana yawo a kanta.
Runtse idanunta ta yi kawai ta kwanta a kan gadon nata, wasu irin hawaye suka fara bin fuskarta, masu dlacin gaske. Don Allah kar ki yi wa kanki haka, kin wuce wurin, kuma daga yau ki Gauki ragamar rayuwarki a hannunki, babu wanda zai nuna miki akasin hakan. Saboda kin san me? Ki na da juriyar da mata da yawa ba za su iya cauka ba. Ke mace ce mai jarumta, duk wanda zai fuskan ce ki sai ya shirya, da shirin fyade ko babu kusancin fyade (rape attempt or no rape attempt), tuni kin wuce wurin fintiKau.”
Hanunta ta Cauka ta riKe cikin nata. Motsin da suka ji ne a bakin Kofa ya sa duka hankulansu ya kai wurin. Juyawan da za su yi ne, suka ga Maami a
jingine da Kofar, jikinta ya yi lakwaf! Kamar za ta tafi ta facil. Da sauri Asma ta ajiyewa Umm Adiyya Maama, ta nufi inda Maami take ta rike ta.

*********

“Subhanallah! Maami!” Justice Khadija ta yi kusan minti goma ba ta furta komai ba, bayan Asma ta taimaka mata ta zauna. Domin a take a wannan lokacin ji ta yi kamar an zare mata dabara da basirar iya magana. Zuwa lokacin Asma’ ta san ba tantama Maami ta gama jin batunsu kaf! “Maami kin yi shiru. Allah ba mu san yadda za mu yi bane, kuma mun tsorata, shi ya sa muka Ri mu fadfa a gida.”
Har lokacin Maami bata Claga idanu ta dubi Asma’ ba. Kan gwiwowinta ta durKushe tana fadin, “Inna-Lillahi wa-Inna-IlaihirRaji’un! Allahummu ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minhaa.” Dakin ya yi tsit! Umm Adiyya ko sai hawaye kawai masu zogi ke fita daga idanunta, makoshinta ya yi Www.bankinhausanovels.com.ng
zafi. “Tun yaushe?” Ta tambaya bakinta na rawa.
“Ya dade Maami.” Asma’ ta facfa ita ma cikin kuka sosai. Laa haula wala Kuwwata, illa Billahil Aliyul Azeem.” Asma’ ba ta taba ganin irin tashin hankalin da ta gani ba a wannan lokacin a fuskar Maami. “Shekaru tara kenan Maami, ina ajin Karshe a Secondary School. Ummu A. tana aji hud.” Maami tana girgiza kai, tana runtse idanu hawaye na bin fuskarta. “Wace irin uwa ce ni? Wace irin uwa ce ni?” Abinda ke fitowa kawai a bakin Maami kenan.
“Maami, ki daina kuka don Allah, ba laifinki bane, ba laifin kowa bane baya ga Allah ya sakowa Ummu A. wannan jarabawar a ranar. “Na shafe shekaru ashirin da bakwai ina warware matsalolin mutane a waje, ina Kwatowa jama’a hakKokinsu, amma ga gagarumin rashin adalci an yi shi a cikin
iyalina ban sani ba, dole na yi kuka Asma’. Ya-Salaam! Na gaza zama uwa ta-gari.”
Shiru suka yi ba abinda ke tashi a dakin sai rushin kukansu, su duka. “Waye?” Suna shiru ta dago a zafafe ta dubesu. “Ku fada min wani marar imanin ne ya aikata?” Ranar da ba ni da lafiya ban je makaranta ba, muna (Extra Lesson) lokacin Ummu
ta rigani dawowa makarantar, Philippe direba ya ajiyeta a gida. Cikin barci na ji kamar hayaniya, wannan ya sa na sauko Kasa. Mijin Hajiya na zo na samu yana ta kokuwa da ita a falonki na Kasa…”
Umm Adiyya kam sai girgiza take yi da kukan da ya sake cin Karfinta. Ya dauki minti
daya kafin Maami ta fahimci waye suke nufi, sai lokacin ta gane mijin Hajiya wani
mutumi da suka taba dauka mai wanki da guga ne da share share. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ganin zai shake ta ne, ya sa na dauki vase din kan tebur din na kwada masa a bayan kansa.”
Umm Adiyya ba za ta taba mance wannan hoton a Kwakwalwarta ba. Tana shiga cikin gida ta cire hijabin uniform dinta ta wuce kitchen don shan ruwa. Tana tsaye gaban firij kenan, ta ji motsi. Wannan ya sa ta tambayar ko waye. Don shigowarta ba
ta samu Asma a kasa’ ba. Ta leKa falon ne ta ji hannu ya kamota ta baya ya toshe mata baki.
Ba Karamin mugun riko akayi mata ba, don da Kyar ta iya juya wuyanta. Tana ihu da
kokawar Kwacewa, tunaninta daya, an zo saceta ne. Ko ‘Yan fashin tsakar rana ne suka shigo gidan nasu.
“Ki yi shiru, ‘yar wulaKanci, yanzu ki yi yangar mu gani mana. Yau sai mu ga wa zai
ceceki, ana miki magana ki na kallon mutane Kasa-Kasa. Don kin ga ana sonki. Yau
zan gwada miki wa yake da iko a kanki.” Jelar
gashinta ya ja ta baya, sai da wuyanta
ya laKwashe, kallonta ya koma sama. Cizo ta gantsara masa a hannunsa, ya yi
saurin sake mata baki, ta sa gudu za ta bar wurin, ya sa Kafa ya tadiyeta.
Sun yi kusan minti uku a nan, ba abinda ba su fasa ba, sai Kalilan. Karar gilas da
Adiyya ta ji ya sa ta daskare. Jini ta ji yana shiga bakinta, saboda buge fuskarta da ta yi a hannun kujera. Zare idanu ta yi, da ta ga jini na malala daga wuyan Mijin Hajiya.
Da gudu ta koma Kusurwan falon ta kanannade jikinta, a nan tana bari, tana girgiza.
Asma’ kuwa tana huci da guntun wuyan tulun fulawan da ya rage a hannunta, ta yi
kan ‘yar-uwarta ta ruangume saboda tsoro.
“Ka fita a gidan nan, ko kuma yau Abba idan ya dawo sai ya kasheka. Mugu, mugu,
dan iska kawai.” Hannunsa na rike da gun da ta ji masa ciwo, ya fita a falon. Asma’ na rungume da Umm Adiyya. Adda, Adda Maami…” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ki yi shiru, ki yi haKuri kuma, ki daina kuka, ba abinda ya sameki, ki yi shiru, kin ji?” “Adda, Maami ta ce kar mu bari kowa ya taba mu. Adda ya taba ko ina na. Adda…” Wani kuka ta Kara fashewa da shi. “Ni ba ‘yar iska bace Adda. Wallahi ban san ya shigo ba… Adda ya taba ni…” “Ba wanda ya ce ke ce, yanzu za mu fadfa, idan sun dawo.” Za su kasheni, idan sun ji za su kasheni.” Asma’ na kuka. Umm Adiyya na kuka. Asma’ ta ce, “Zo mu je ki zauna a can, ba wanda zan faclawa, kin ji?” Umm Adiyya ba ta ma jinta, ta yi shiru kawai tana kallon sararin gabanta, ta koma
kukan zuci. Wasu abbuwa kamar Kwari ne ta ji suna bin jikinta, ga wani warin gumi da yake bugawa, ga na rana ga na tsana, wari kala-kala take ji a hancinta. Tunda ta girma ta yi wayo, tun tasowarsu, idan akwai abinda Maami ta fi jaddada masu, to yana bayan su rina sallah mai kyau kuma kar su yarda wani namiji ya taba su. Yau ga shi har cikin gidansu an shigo ana neman Karasata. Can cikin dishi-dishi ta hango Asma na share falon, ta bi ta gyara ko ina. Sannan ta zo ta riKe hannunta ta ja ta wani wuri, sai can ta fahimci Cakinsu ta kawota.
“Shiga ki yi wanka, ki sa kayan gida. Idan Maami ta dawo ki ce kin facfi ne kin zame
a falo.” Hakan kuwa aka yi. Ranar hankalin Maami ba Karamin tashi ya yi ba, ganin
kumburin fuskar Umm Adiyya da yadda ta canza launi.
Tun daga ranar shirun Umm Adiyya ya Kara Karuwa, ta koma zaman dlaki, kullum
sai sun yi kuka da Asma’ da dare. Duk da ba cikakken fyade Mijin Hajiya ya yiwa
Umm Adiyya ba, razanata da ya yi da raunuka da kokawar da ya yi da ita na KoKarin
ganin ya cusa mata tsoronsa a ranta, ya gama illata mata tunani, har ta ji duk duniya
ba wanda ta tsana irin maza. Sun yi kusan kwanaki hudu, sai ta farka a Www.bankinhausanovels.com.ng
razane cikin gumi. Kullum Asma’ na ba ta baki, har ta daina razanar, amma daga nan Kofar ciye-ciye ta bude mata. Ko za ku yi yaya da ita da ta ci abinci, sai dai ta sha cornflakes. Mijin Hajiya kuwa tun ranar da abin ya faru, an neme shi, an rasa, sai Philippes ne ya ce ai babu kayansa a dakinsu na BQ. Abin ya bawa su Abba mamaki. Maami da ta matsa da tambayar Umm Adiyya abinda ke damunta, sai ta ce, “Ciwon jikin faduwarta ne bai bar ta ba.” Da wannan magana ta wuce. Asma’ ba ta taba facia ba, haka nan Umm Adiyya ba ta taba fada ba. Tun lokacin duk namijin da zai zo yace yana son Umm Adiyya, ji take
yi kamar ta shake shi. Cikin ikon Allah, har ta kai shekarar gama Sakandirenta, lokacin da Yaya Zaid ya
dawo daga UK, lokacin da ta bawa kanta mamaki, ta yadda har ta faye son ganin sa, ko jin labarinsa, ko jin dariyarsa, lokacin da ta fahimci ashe akwai namijin da za ta
iya so a rayuwarta haka.Akan Yaya Zaid ta sake fara son namiji, bayan tayi masu tsana Karfaffa na shekaru biyu. Duk sauran manemanta kallonsu kawai take yi. Ta yi fama ta yi jinya, ta yi kuka, ta yi dariya duk akan soyayyar Yaya Zaid. Kafin kwatsam! Ta gan shi da matar can a Ofis dinsa.
Shi ma ya zo ya sa ta a kwana, ya toshe mata baki. Ba abinda take tunowa sai
faruwar makamancin hakan da Mijin Hajiya, wannan ya Kara haustina mata lissafi, taga ashe dama duka maza ma haka suke. Www.bankinhausanovels.com.ng
A hankali bayan aurensu ya shagaltar da ita da nasa salon soyayyar har ma ta saki jikinta da shi.
Wannan ya sa lokacin da ya zo mata bagatatan, ta razana har ma kwakwalwarta ta
koma ta kafe akan cutar da ita kawai zai yi, yana tariyo mata ranar da ta tsira da
Kyar a hannun Mijin Hajiya, a taKaice a take idanunta suka koma ganin mijin Hajiya,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *