UMM ADIYYAH CHAPTER 52 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 52 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

A’isha kasancewar gidanta take tun tafiyarmu Gombe.” “To ba damuwa.’ Asma’ na shafa kan fuskar wayarta ne, ta ji kamar magana, wannan ya sa ta dago idanu ta kalli santan gadon da Umm Adfiyya take kwance clauke da claurin ruwa a hannunta.
Da sauri ta ja kujerar kusa da gadon Umm Adiyyan. “Me ki ka ce?” “Adda shi ne ko ki kirani ko?” Asma’ ta kauda kanta, ta ce, “Kar ki dauko wata maganar da za ta haustsina miki lafiyar jiki, bayan an samu kin farfado da

Kyar.” Murmushi Umm Adiyya tayi mata sannan ta ce, “Ba laifi, wa zai yi kewata ma idan ba na nan?”
Adda Asma’ ce ta harareta. “Ki na Kwaya ne za ki faci hakan?”
“Ayyi, sha’ani na mutum da rai kuma? Adda fa ko ki kira ki ce kin ji abinda ya faru.”
“So ki ke yi na fara miki a nan kan mu je gida ko? Ba lallai bane ki dauka, amma
haba Umm Adiyya, me ki ka maida kanki? Adda Zubaida ke fada min komai, har ma
ki budi baki ki ce ya sake ki, bayan ki na sane da yadda yake sonki. Bai ma…”


“Komai ya wuce yanzu, ba na son mu dawo da abinda ba mu da iko akai.”
“Kin dai san ba zan yi shiru ba, ba zan kuma bar asibitin nan ba, sai kin fadia min wane irin abu ne ya faru.” “Ai na fada maku dukanku.” Umm Adiyya ta fada tana daga kwance. Idanunta a lumshe kadan.
Kallo kawai Adda Asma’ tayi mata, ya sa ta
kau da kanta gefe. “Gwamma kin fara
shirya zancenki, domin kin san zan gane, ba tun yau na ke ganewa ba.”
Jikin rigar filo Umm Adiyya ta sa hannu tana bin zanen kai da yatsarta. “Duka haka
suke Adda Asma’.” Shiru ta yi tana duban Asman, wacce idanunta suka budtu kacfan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin ta tuno zancen da ta yi da Adda Zubaida a waya. Addinin mutum, rayuwa da mutuwa.
Musamman Adda Zubaidan ta kirata tana tambayar ko ta fahimci meye manufar wannan kalamai, tunda ta bincika ba ta gane ba. “Ummu A…” “Kin gaji da ni ko Adda Asma’?” Wace irin magana ce hakan kuma? Yaya za ayi na gaji da ke? Ke ma kin san dukanmu muna sonki, rai dai ya yi ba dadii saboda abinda ya faru. Sannan dole laifinki za a fi gani. Na zaci kan na tafi mun gama magana na baki baki, kin kuma
amince za ki yi yadda na ce, sai kawai bayan na koma kuma na ji mummunar labari, ai kuwa dole na ji wani iri, amma hakan ba wai yana nufin mun tsaneki bane ai.” Umm Adiyya ta shiga kada kanta, tana hawaye, tace, “Na gode, Adda, kullum ke ki ke yarda da ni. Na gode.” “Me ki ke nufi amma da ki ka cewa Adda abin zai shafi rayuwarki?” “Kin tuna ranar? Ranar Talata.” Kallo daya Asma’ ta yi wa Kwayar idanun Umm Adiyya ta fahimci tsantsar tsoron da ke wurin, nan take kuwa ta tuno. Ba yadda ma za ayi ta taba mantawa. Ranar da dukansu biyu suka Cauki wani nauyi na girma da kuma amana suka dorawa kansu, ranar da suka Kara kasancewa kusa da juna fiye da koyaushe. Take gaban Asma’ ya fadi. “Me ya hada ranar da matsalarku? Kar dai tunda ki kaje… Amma ai kin yi miscarriages, yaya aka yi?” Komai lafiya fa Adda. Komai lafiya har sai da ya dawo daga Turkey, daga nan ne…
Adda he raped me. Bayan ya sani, na fada masa Wallahi na fada masa tun farko kuma shi ma…” “Ya Subhanallah!” Asma’ tuni ta mike zuwa ga ‘yar-uwanta ta riKota cikin jikinta, ta mance ma da
Maama a hannunta, sai da yarinyar ta sa Kara.

******

Nan hankalinta ya koma kan jijjiga yarinyar. Duk da haka ba ta saki Umm Adiyya ba,
nan ta ji wani rushin kukanta, har gadon da take kai yana girgiza, don kukan da take yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ya isa, Ummu A. Don Allah ki yi shiru, ki yi haKuri. Me muka yi da ke? Komai ya wuce, kuma ba zai sake dawowa ba. Kin min alKawari fa ba zai taba miki rayuwarki ba daga baya. Kin min alKawari ba za ki taba bari ya dameki ba, za ki cire a ranki. Wannan ya sa ba mu fadawa Maami ba kin tuna?” Na sani, na sani.” “Ummu A. Zurfin ciki ba shi da kyau. Bai da amfani ko kadan. Wataran kar ya kashe ki. Abinda ke cikin cikinki ya fi Karfinki. Kullum ina ganin wautata da na biye miki, na Cauki alKawarin yin shiru.”
“Ni na yafe masa fa Adda Wallahi, na dade da yafe masa. Saboda duk sun fada min, kuma ni ma na sani bai kamata na Kaurace masa ba. Amma zaman gaba na ke dubawa. Wallahil Azeem ranar tsoronsa ya Clarsu a raina na Kin Karawa. Daga ya zo kusa da ni, na ke ji kamar abubuwa suna yawo a jiki na. Sai na tuno ranar da Ph…” “Mijinki ne shi, dan-uwanki ne, kar ki sake hacdfa shi da wancan azzalumin.”
Ban hacfa su ba, kuma da farko da gaske idan na ce Yaya yayi min ba daidai ba, nayi masa Karya, kuma Allah zai saka masa. Ba wanda ya kai shi lallami da tattali da kalamai masu dadii ta kowane fanni.
Ba wanda ya kai shi nuna min so. Da farko na facia masa na ce ban shirya ba, ya fahimci hakan, daga baya da ya ce ba zai iya jira ba. Adda na mance komai. Na mance alKawarinmu da ke na yin shiru.
Na fada masa abinda ya faru. Wallahi Adda kuka ya yi, da idanunsa yana tausaya min. Ki duba ki ga, shin kin ga laifina, idan bayan ya sa na yarda da shi, na
sakankance da shi, bayan na yaki kaina da tsorona, na ba shi kaina, ya zo ya aikata min abinda ya san ya fi komai tayar min da hankali?” “Kin san ba ki da Www.bankinhausanovels.com.ng girma ko?” “Na’am?” Umm Adiyya ta tambaya tana goge idanunta da Tissue. Kin san kin yi Karama ki zuke dukkan wadannan matsalolin a cikin Rirjinki ko? Right now, ina jin kamar na nemo duk inda yaya Zaid yake, na ce masa bai kyauta ba. Amma ya wuce, duk abinda ya faru da mu a rayuwa, dole Kwakwalwa ba za ta manta ba. Amma kuma idan ba zai mayar da mu abinda ya wuce na da ba, ya kawo mana cigaba a rayuwa, to dole mu goge shi daga raywuarmu. Don muddin muka bari ya cigaba da hanamu samun ci-gaba, to tamkar bayan duka yaKin da muka sha da fafatawarmu ya tashi a iska ne. Tamkar sun yi mana babban tabo ne a rayuwa.” “Haka ne.” Yanzu ina so ki dauki lokaci, ki cire komai a ranki, ki mance abinda ya faru, ki mance abinda Yaya Zaid ya yi, idan zai yiwu ki samu abinda zai Cauke miki hankali daga tunaninsa ma. Zan yi magana da su Abba, bayan abubuwa sun lafa ko makaranta ko wani abin ki koma ki yi. A bar ki, ki huta tukuna. Saboda Ummu A. Ki
na buKatar hutu. You’ve gone through enough to last you a life time. (kin fuskanci kalubalen da zai isheki iya rayuwarki.)“

**************

BABI NA TALATIN DA BIYAR

Dago idanu ta yi bayan ta jinginu a jikin filon asibitin, ta murza yatsunta. “Ki na ga
zan iya manta shi?”
Shiru Adda Asma’ ta yi, domin ta san amsar ma ba buKatar fayyace ta. “Ki canza muhallinki, a hankali komai zai tafi. Ba zance zafin zai tafi ba, amma za ki samu sassauci, radadfin zai ragu. Fushin zai Kare.
Ni dai na san akwai abu guda, idan da wani abu da duk wannan ya kamata ya koya mana shi ne aure tarayya ne, na mutane masu yawan afuwa ga abokan Www.bankinhausanovels.com.ng zamansu.” Umm Adiyya ta gyadla kanta. “Haka ne. Na gode Adda Asma”. Hannu ta mika mata akan ta ba ta Khadija Maama, “A’a kwanta ki huta, ki na jirin za
ki karbeta, ai sai ta kada ku daga zaune, yadda taken nan.” Murmushi ne ya ziyarci labOansu, wanda ya Hoye tarzoman cikin zuKatansu a zahirance.

************

Washegari aka sallameta daga asibitin, tare da kashedin ta kula da cin abinci mai
kyau akai-akai da yawaita shan ruwa. Tunda kuwa aka ce sun bar asibiti. Abba da Maami suka Kara koma mata kusan kamar da, marabar dai shi ne idan tana wurin, ba sa daina magana, hirarsu suke yi ba tare da an tsomata a ciki ba. Wannan ya sa ta yanke shawara, ta gama hada Katoton akwatinta, ta wuce kai tsaye dakin Maamin ta sameta, ta gaisheta, duk da dai a ciki ta dan amsa ba tare da ta dago kai daga littafin da take karantawa ba. Abu ya kulle a wuyan Umm Adiyya, sannan ta Karasa cikin dlakin sosai.
Maami daman ina so nayi miki magana ne.” “Ina jinki.” Ta facla a daKile. “Ina son na tafi.” Lokacin ne Maami ta dago kanta tana duban ‘yar tata. Maami, idan ba ki yafe min ba, yaya na iya? Gwamma na tafi kawai na yi nisa da ku ko idan ba ku ganni ba, Www.bankinhausanovels.com.ng zuciyarku za ta fi sanyi.” Ba na son zancen shiririta. Ina ki ke da shi da ya wuce nan?” Ba ni da shi, amma Maman Walid ta ce gidansu akwai fili, za su ba ni kacdlan na zauna kafin aga me zai faru da ni nan gaba.” Idanun Maami ne suka dan yi rau-rau! Tana matuKar tausayin ‘yar tata, amma dama abinda take son gani a tare da ita kenan, ta ga nadama, ta shiga hayyacinta ta san cewa ba komai bane ka ke so a rayuwa, ka ke nema ka samu, ta san cewa girma ya
kamata, kuma ba ita kadai al’amuran da ta yanke a rayuwarta yake shafa ba. Ta san kuma muhimmancin yafiya. “Yanzu kin ji abinda mijinki ya ji lokacin da ya nemi gafararki, ki ka Ki amincewa?” Kai kawai ta shiga gyacfa mata. Na ji Wallahi Maami har ma fiye da shi. Yaya Zaid ban san ma inda yake ba. Abba
gaisuwa kawai ke hada ni da shi, su Faruk kawai suke kulani duk gidan nan sai Adda Asma. Maami kwanana uku ban yi barci
ba. Da na kwanta na ke jin surutai a kaina. Da na san haka baKin-ciki yake da ban tada hankalina a lokacin da na ke da komai ba, har ma na zo na rasa koman.”
Murmushi Maami ta yi sannan ta ce, “Uwa tana fushi da yaranta ne, har Kasan zuciyarta? Sai dai ta nuna Hacin ranta, domin su gyara halayensu. Allah ya yi maku albarka, ba zance zan miki mummunar fata ba, duk yadda ki ka kai ga laifi, bare ma kin fadfa ai, ba za ki iya bane ko? To tunda shi ma ga yadda ya fadla kuna buKatar lokacin. Allah Ya sa hakan ya fi zama alkhairi gareku, ni dai ina jiye miki ne, shin za ki iya samun mijin da zai so ki yadda Zaid yake sonki?”
“Maami ba na son kowane namiji ma ni kam, ni dai ki yafe min kawai.” “Sai Zaid ko?” Maami ta fadla tana murmushi. Umm Adiyya kuka ta Kara fashewa da shi. Justice dai yau tana ganin wani sabon al’amari mai cike da nuna ikon Allah. Wannan
wace irin rayuwa ce?

*********

Asma na dawowa daga gidansu Zunnurain da yake Garki, inda ta je su ma ta kwana masu biyu ne, ta samu Umm Adiyya ta gama hacia kaya. Hajiya sai ina?” Murmushi tayi mata sannan ta ce, “Inda na fi wayo.” “Ke su Abba sun yarda? Shi ne ko ki facia min ko?” Na fi so nayi miki bazata ai.” Ni ba za a zo min ba? Ban san me gidana yayi miki ba, kin mana yaji gaba daya abinki, tunda ku ka je bayan biki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Adda Asma’ ba fa yawo na ke yi yanzu ba, ni da na ke idda?” “Ina dai jira ki gama idan lokacin yawon ya yi, a zo min, idan ba haka ba zan san matsayina a wurinki, wai tsaya ban gane bama. Umm Adiyya ta rufe zif din Karamin kit cinta inda ta gama saka kayan gyaran

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *