UMM ADIYYAH CHAPTER 51 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 51 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


Tsayawa ya yi a cikin
zauren gidan, wanda Kwan wutan ya mutu, wani numfashi ya zuKa, kansa ya sara.
Yayin da ya maida numfashin, yau ya amince da duk abinda ya faru kawai Kaddara
ce mai Karfi. Tsakaninsa da Umm Adiiyya komai ya Kare kenan? Wasu hawaye masu Zafi ne ya ji sun zubo masa. Wayarsa ce ya ji tana Kara, yana kallon sunan “Mama’ akai ya ji wani diri ya ratsa
shi, ai tuni ya manta da ciwon kansa, hannu ya sa ya share fuskarsa. Da sauri ya
kanga wayar a kunnensa, ya amsa cike da ladabi

“Na ji hukuncin da ka yanke. Allah ya ba ka sa’a. Hakan ya yi maka daidai kenan.”
“Mama…” Ya fara, amma ta riga ta tsinke layin, wannan ya sa dole ya koma cikin
gidan ya wuce kai tsaye har dakinta.
Cikin tsanaki ya yi ta ba ta baki, ganin ta kafe ne, ya sa ya wuce wurin Anti don ya fi sakewa da ita akan Maman. “Anti don Allah, ki yiwa Mama Magana, sam ta Ki ta fahimci inda na fuskanta.”
Idanunta ta dago daga kan littafin addu’ar da ya samu tana karantawa, “Zaid. Wane


bayani za ka yiwa Hajiya, baya ga ka bar inda take, sai ta huce, sai dai ina son na Www.bankinhausanovels.com.ng
san me ya sa ka aikata abinda ka aikata ma tukuna?’
Kallon da ya yi na sadda kai ne, ya sa ta ce, “Duk daga abinda kayi mata ku na cikin
rikicin naku zuwa sakin, me ya yi zafi Yaya Zaid? Ka san da cewa babu wanda ya
taba Kure Baffanku irin yau ko? Har ma bai shirya sauraren uzuri ba, mutumin da yafi yi wa kowa uzuri.” “Ba ni da dalilin yin hakan, an samu kuskure, kuskuren da ya ci ace na kange kaina
daga aikatawa, tunda na san komai.” Hawaye ta ga ya zubo daga idanunsa.
“Subhanallah! Ai ka ga irin abin, sai ku yi abu, ku zo ku na da-na sani. Wannan ai shi ne fargar Jaji.”
“Mu bar wannan Anti, na zo ne ki roKar min Mama ta yi hakuri, ki yi ta lallaba min ita
don Allah. Ban yanke hukuncin ba, sai da na yi tunani, domin duk yadda na ke son
Umm Adiyya, haka duk yadda ta kai ga sona, ta fadi gaskiya daya a cikin wannan tsuku, zai yi wuya rayuwar aurenmu ta koma yadda take a da.”
“Sai na ke ga kamar ku, ku ke kambama wannan al’amari Yaya Zaid. Ai koda Www.bankinhausanovels.com.ng
aurenka a kanta, kai me barinta gaban su Abba ne, har sai kun sasanta, sai ta koma
dakinka, amma yanzu kowa ya yi fushi da kai, yanzu me gari ya waya?”
“Ta fada miki komai ne dazun?” Ya tambaya cikin rauni.Anti ta gyada masa kai, sai riKe labbansa ya yi cikin hakoransa, cikin KoKarin danne abinda yake ji.
“Sai da safe Anti, ina da ayyuka, amma ban yi tsammanin ina da sukunin yinsu ba
har sai na samu daidaito. Zan yi doguwar tafiya, zan shiga na yiwa su Umma
Sallama, amma don Allah ko bayan na tafi, ki ci-gaba da bawa Mama hakuri, ta yi fushi sosai.” “Indiyan za ka koma?” ‘Eh, wani Course ne dama zan je na yi, to sai kuma ga wannan abin, yanzu haka dai
zan sake komawa na kammala da wannan. Zuwa lokacin sai mu ga abinda hali zai yi.
“Yaushe za ka dawo?” ‘Zan rinka zuwa a tsakani, lokaci zuwa lokaci.”
“Allah ya bada sa’a, ya kuma kareku daga sharrin duk wata halitta. Zan yi KoKari na
yi nawa iyawar. Amma lokaci-lokaci ka rinka
magana da su Maamin.”
Murmushi ya yi mai zafi ya ce, “Anti, Maami ai uwata ce, koda Umm Adiiyya ko babu,
ba abinda zai shiga tsakaninmu.” “To, wodi. Allah barkidi.” Ameen Na gode, mun gode duka da taimakonku.” Ya fadla, sannan ya mike,
“Ina dai so ka san da cewa yafiya, ita kadai ce hanyar da ke sa zuciya ta samu
natsuwa.” Kai ya gyadla mata.
Ita kuwa Anti ba komai ya kashe mata jiki ba, sai irin yadda ta hango nadama a tare Www.bankinhausanovels.com.ng
da shi, sannan kuma ga halin daya jefa su. Na kafiyarsa kan batun barin sarari a tsakanin su biyun.

***********

Tunda aka watse a falon Baffa Abdu. Nazeef ya mayar da Hajja Kubitto gida tana ta
koke-koke. Zubaida na tare da ita, tana ta kwantar mata da hankalli.
Wannan ya sa aka yi tafiyar kurame daga gidan Baffa Abdu zuwa gidan Abba,
saboda Umm Adiyya tana motar, a ganin Abba kuma yau a dalilinta, ya rasa abu
mafi muhimmanci a rayuwa, watau zumuncinsa.
Tagumi kawai ta yi a motar, tana kallon gilmawar lantarkin titi, har suka isa gida.
Washegari da sassafe suka wuce Abuja.
Kafin su wuce. Zaid da kansa ya samu Abba ya facta masa batun tafiyarsa, duk da
ya kasa hada idanu da shi, amma ya ga ya cancanci su sani, tunda su Baffa sun ce
gidansa za ta zauna.
“Allah ya kiyaye hanya, ya dawo da ku lafiya, za ta zauna nan gida zuwa dawowarka.”” Abba ya ba shi amsa a takaice, don baya son ana zuwa ana komawa a kan wanann batun. Tunda suka iso gida, nan ta wuce su Faruk ko amsa sannunsu ma ba ta yi ba, duk
da a sanyaye su ma su kai mata maganar.
Ko kade gadonta ba ta yi ba, ta jibgu a kai tana kallon sama, ta shafe kusan minti talatin a haka, kafin ta zabura ta tashi zaune. A hankali ta turo Kofar dakin ta shigo, tana ganin yadda Maami ta kawar da kanta tamkar ba ta ganta ba, ta ci-gaba da duba Jakarta, tana neman wani abu. “Maami…”
Ba ta kula ta ba, bare ta juyo gareta, “Maami don Allah na roKeki, Maami kar ki juya min baya, Maami don Allah ki yi hakuri. Na yi kuskure da na saka ku fuskantar wannan ranar.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kuskure Ummu?” Maami ta juyo tana Kankance mata idanu. “Kuskure? Har ma ki
na da bakin fadin wannan kalmar daga harshenki? Kin san me ake kira tozarci? Jiya Umm Adiyya kin tozartamu a idanun duniya. Har za ki iya budfar baki ki nemi mijinki ya sakeki?
Me ki ka yiwa kanki? Akan wane dalili ne da har zuciyarki za ta KeKashe, ki je ki ki
kashe aurenki? Yau koda ba Zaid bane mijinki, ban san inda zan sa kaina ba, bare kuma ace shi. Wanda ya tashi a gaba na tamkar dana, wanda mutane suka sa idanu su ga yaya taron zai waste.” Maami abinda ya sa na aikata hakan, kuma abinda ya kai ni ga yin hakan, na so na fada maku tun ba yau ba, na so na fada, amma ba zan iya facla ba, shi ya sa na bar
shi a raina, amma haka nan kuma ba zan iya zama da shi, ina kallonsa ba. Maami na fada miki. Wallahi tsoronsa na ke ji. Wallahi ba Karya na ke yi ba, ki tambayi…” Maami hannu ta sa ta goge hawayen da yake son fito mata ta ce, “Ummu, ba sai kin ba ni dalili ko wani kare kanki wurin nuna dalilin da ya sa ki ka aikata abinda ki ka aikata ba, tunda har ba ki bar ni da zabin fita daga jin kunyar duniya ba, ba abinda zance miki, ko madubi na kalla, ina jin fargaba.” Maami ta sa hannu tana nuna Kofar cakinta, “Kin taba tunanin yadda zan fuskanci
dimbin zuri’ar gidanku? Yadda zan dubi Hajiya Mama? Kin yi tunanin me zai je ma ya dawo kuwa? Kin dauka ke za a zaga idan an ji ki na neman saki wurin miji? Bayan laifin da ki ka yiwa Allah, har ni da na haifeki zuwa duniya da mahaifinki da bai ji ba bai gani ba, sai an zaga. Jiyan ai akan idanunki, ba a gushe ba, kin ji me Hajja Kubitto ta fada? Ku duk tarbiyyarmu ce ya kamata mun san halin kowannnen
ku. Ni dai Ummu na san Wallahi ba tarbiyyata ki ka nuna a gidan mijinki ba. Ba haka ki ka ga ina rashin da’a wa mahaifinku ba. Na yi kuka da hawayena a kan
wannan lamarin, domin koda mijin Zubaida ya yi aurensa, ya Hoye mata ya saci kudinta ya gudu da matarsa, ban ji ciwon da na ji ba irin jiya.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Umm Adiyya kam hannu ta saka akai, tana rawa kamar mai jin fitsari tana kuka. “Maami, wayyo Maami. Ya-Salaam don Allah, don Annabi ki yafe min. Wallahi na tuba, ku yafe min. Zan je na roKe shi, ya mayar da auren namu, amma don Allah
Maami kar ki yi fushi da ni, ban san yadda zan rayu ba cikin fushinki, albarka kullum ki ke sanya min, randa ki ka daina. Allah ba zai bar ni ba, da fushinki a kaina. Wallahi na yarda zan roKe shi, zan koma na zauna, zan danne zuciyata, na daina jin tsoro, zan miki duk abinda ki ke so Maami, don Allah ki daina fushin, kin ji?” Justice tana Caga idanu ta ga fuskar ‘yarta, nan da nan zuciyarta ta burge daga-daga.
Kauda kanta ta yi gefe tana kallon kafet cinta, “Ba za ki roKe shi ba Umm Adiyya, ba za ki roKe shi ba. Ki bar shi shi ma ya huce. Na amince ba za a Hata goma, Claya ba ta gyaru ba. Ku na buKatar hutu, ku sarara tukuna, ku fahimci kanku kafin ku fara aiki kan fahimtar juna. Dole a samu wadannan ababen kan aure ya yi Karko. Auren da ku ka yi zaman tare kawai ku ka yi, ban yi tsammanin ku na da sanin me
aure ma ya Kunsa ba, ku ka shiga abin kai tsaye. Na amince kun yi Islamiyya. Amma
sai yanzu na ke jin cewa ya kamata ‘yan mata da samari kan ma su yi aure, a horar da su me auren kansa ya Kunsa. Ba wai a tsaya a soyayyar zamanin nan kawai ba. Na sanki da naci kan wasu abubuwan, zuciyarki za ki fara gyarawa ki sassauto. Sai Www.bankinhausanovels.com.ng
ki mori rayuwar duniya da lahira.” “Zan fara Maami, na ma fara . Kin yafe min?” “Ki je ki kwanta, sai da safe.” Jikinta ne ya mutu murus! Da jin wadannan kalaman na Maami. Haka ta juya sakwako, tana jan jikinta tamkar ta yi dambe, an doketa.

********

Ta zo tsakiyar kwararon da ya hada dlakinta da na Maami ne, ta ji idanunta sun yi uu! Take ta fara ganin digo-digon baKki a idanun, Daga nan ji ta yi kamar tana sulalewa, ba ta sake sanin inda kanta yake ba.

*********

A hankali Kofar ta yi Kara, alamun an budeta, hannunta rike da madaidaicin filas din
ruwan zafi wanda Malam Bala ya miko mata,
bayan ya gama shigo da sauran kayan abincin wurinsu. Ta Karasa cikin dakin. “Har yanzu?”
“Dazu dai ta dan motsa, amma tun daga nan ba ta Kara motsi ba, ina ga sun mata
allurai masu Karfi ne, take ta wannan barcin.” Ajiyar zuciya Maami ta yi, sannan ta ajiye filas cin da ta shigo da shi, ta sa hannu za ta karOi Maama da ta gama shan nono a hannun Asma’. “Ke kuma kullum ba kya gajiya da jelen titi. Ba za ku zauna a gidajenku ba. Son yawonku da yawa. ” “A’a kawai dai ya ce mana zai shigo Abuja ne, saboda wasu ayyuka, shi ne na nemi mu taho tare, ban ma san ma tana asibiti ba. Jiyan dai Adda Zubaida ta ce kun dawo.” “Eh, mun dawo.” Asma’ ta kula da yadda fuskar Maami ta canja. Nan take ta ce, “Maami hakuri fa za
ku yi daga ke har Abban, abinda ya riga ya faru, ya riga ya faru, idan lokacin abu ya yi ko na menene sai ya faru. Saboda haka duk ba dabarar mu bace.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Maami kam gyada kanta ta yi, sannan ta ce, “Tunda ki na nan, bari na leKa wurin aiki, zan shiga kotu.” “To ki dawo lafiya,” “Innayo tana zuwa, da Anti A’isha kasancewar gidanta take tun tafiyarmu Gombe.” “To ba damuwa.’ Asma’ na shafa kan fuskar wayarta ne, ta ji kamar magana, wannan ya sa ta dago idanu ta kalli santan gadon da Umm Adfiyya take kwance clauke da claurin ruwa a hannunta.
Da sauri ta ja kujerar kusa da gadon Umm Adiyyan. “Me ki ka ce?” “Adda shi ne ko ki kirani ko?” Asma’ ta kauda kanta, ta ce, “Kar ki dauko wata maganar da za ta haustsina miki lafiyar jiki, bayan an samu kin farfado da

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *