UMM ADIYYAH CHAPTER 49 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 49 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya
amma wannan abin bai yi dacfi ba, bari Malam din ya dawo ya zo Www.bankinhausanovels.com.ng
ya tarkata ta su koma kawai, su je su yi ta hakuri, haka duk muka yi muka girma. Iyi ai shi ne girman.”
Da dare suka wuce gidan Abba suka kimtsa. Adiyya kam duniya ta yi mata zafi, don Kiri-Kiri daga Abba har Maami ba mai kula sabgarta, a tunaninta wurin Abban ne ma

za ta samu Can sassauci, sai kuwa bai gwada mata fad ba, amma baya janta
kamar yadda yake mata a baya.
Zuwansu gidan Baffa washegari ne, suka ji yana ta facfa, “Yaro banda ya rainawa
mutane hankali, yaya za ka aikata irin wannan ta’asar, sannan ka sa Rafafu ka tafi
ka bar jama’a cike da tambayoyi, sannan kuma ka ki waya ka sanar da inda ka ke?
Zai ga Hacin raina muddin ya iso nan kuwa.” Su Yaya Nazeef ke ba shi baki da Yaya Saadik.
“Wani aiki ne mai muhimmanci ya taso masu, abokan aikin nasa kuma ba sa nan,

Www.bankinhausanovels.com.ng
kuma idan bai je ba, za a samu babbar matsala, wata Kila kamfaninsun ma ya durKushe.” Yaya Saadik ya fada, duk don ya kare Can-uwan nasa.
Kamfani? Ba a sake gina kamfani ne? Matarsa ce fa, ‘yar-uwarsa ya saki, ya kuma tafi ya bar ta, bai yi bayani ba. Ai ba daga sama ta fado ba, sai ya yi wa iyayenta bayani ko? Ba ta da waliyyi ne? Ya tafi ya bar mu haka nan. Wannan ya nuna bai Caukemu da daraja ba bare ya mutunta mu.” Haka dai su Saadik suka sadda kai su kai shiru har Baffa ya ida kai aya.
“Ina Ummun take?” Nan ne Anti da take zaune a falon ta ce, “Bari a yi mata magana.”
Umm Adiyya ta shigo falon Baffa cikin hijabinta, don haka ya kalli bangaren da su
Saadik suke zaune ya ce, “Bari na yi magana da ita.” Nan aka watse gaba dlaya aka
bar ta daga ita sai Baffa. Abba da Aunty, don Maami kam ba ta biyosu ba. Shiru ta yi
abin ta, tana kallon hannunta. Wanda hakan ya tunzura Abban.
“Ke ba ke muke saurare bane, za ki bar mu muna jira, mu clin sa’anninki ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
A firgice, ta gyara durkusonta kan gwiwowinta, “To… to Abba… Abba zan fad.”
Ganin yadda ta birkice, ya sa Baffa ya ce, “Tashi ki shiga ciki, a jira shi Sarkin yakin
randa ya samu isowa, sai aji koma menene lokaci guda.”
Abba kam tagumi kawai ya zuba, saboda sha’anin yaran nan sai Allah. Hakan kuwa
aka yi sai washegari sannan Zaid ya isa Gombe, bayan ya yi ta sauka daga Jirgi
Caya zuwa wani jirgin, har ya isa Gombe.
A gajiye likis! Ya isa, kasancewar isar sa Indiya da kwana guda ya kira wayar
Saadik, abin da ya faran ma bai kai ga yin nisa ba, bare ya kai ga Karasa shi, dole
ya taho. Ya san Baffa sosai, baya kuma so ya shiga hannun hagunsa. Hatta su
Abban ma bai so ya tafi, bai ce da su komai ba, domin girmansu da kimarsu sun wuce komai a gare shi.
Lokacin da muryar Umm Adiyya ta sauka a cikin kunnensa, tana ce masa ya saketa,
tunani kusan dubunnai sun gitta a Kwakwalwarsa har ma ya Sa ya ji wani saran kai
da jiri sun kwashe shi, ya san ba za ta huce ba, ya san tana da kafiya, amma bai
taba tunanin abin ta ya kai ga ta nemi hakan ba, sai kuma ga shi ta nema.
Bayan ya natsu, cikin dare ya dade yana auna maganganunta, da farko Kudirinsa
shi ne, ba zai taba biye mata ba, ko ba komai albarkacin iyayensu bai cancanci ya
sanya su a wannan halin ba, amma da ya natsu ya auna, ya duba, abinda yake faruwa.
Sai ya ga muddin bai bar ta ba, muddin bai ba ta abin da take ganin take so ba. To
har abada ba za su taba daina zama matsalolin iyayensu ba, domin kullum aikin
kenan zai zamo ba su da sirri, zai zamo kullum matsalarsu ce a bakin jama’a. Wasu su bi gaskiya, wasu su Ki bi, wasu su take gaskiya, saboda su bayan wannan suke bi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Har yaushe za su yi wannan rayuwar? Musamman abin da ya shafi
zamantakewarsu. Wataran Umm Adiyya za ta iya Kure shi ya yi abinda zai zo ya yi
da-na sani akai, wacce aka ce Keya ce. Da ace ana hakan kawai, ya ji gwamma sun
hakura na can lokaci kadan. MiKewa ya yi ya
yi nafila, yana idarwa, ya shirya
kayansa, ya yi wayoyi kashi uku, sannan ya zauna ya tsara saKon da zai tura mata,
bayan ya gama karantawa ne, ya goge ya sake rubuta wani, sai da ya yi hakan kusan sau shida. Sannan ya samu Karfin halin turawa.
A nan ya zauna ya yi karatun AlKur’ ani, kafin gari ya waye. Karfe shida ya bar gidan, bai duba halin da take ciki ba, saboda yana gudun kar ma ya canza shawararsa, ko
kuwa ganinsa da za ta yi, ya Kara tado abubuwa da dama. Tun tafiyarsa dai,
hankalinsa yana baya, don ya san ya baro Kura tirim!

*********

“Yanzu ina son ku fada mana meye matsalar da har zai sa kai ka dauki tsattsaurar
mataki haka akan Ummu? Ko ka fadla ko kuma Wallahi za ka ga me ake kira fushina.” “Baffa, ni na ce ya sakeni.” Baffa, ni na ce ba na son haihuwa yanzu.”
Dukansu biyu suka fadfa a tare, nan fa aka bar Baffa Mai-kano, Abba da Baffa Abdu da kallon-kallo.
“Ban gane ba ka son haihuwa ba?”
“Ban gane kin nemi saki ba?” Iyayensun kowa da abinda yake fadla a wannan lokacin.
“Kuma don ta ce ka aikata, sai ka aikata din saboda hankalinku daya ko mene? Ko giyar wake ku ke sha ne? Me ma ku ka dauki auren ne wai?” Baffa ya fadla cikin takaici. Hajja Kubitto tana zaune daga gefe, ita tsabar girman lamarinma ya Sa ta gaza cewa
uffam. Umm Adiyya na zaune a ganganta. “Baffa ku yi hakuri.”
“Hakuri za ka ba mu kan dalilin me? Ai ba abinda ya yi saura illa ka gyara abinda ka Hata.”
Ganin Zaid bai motsa bane, ya sa ya Kara da “Yanzu.” Baffa ban yi abinda ba daidai ba, domin na ba ta ‘yancinta ne, zaman mu akwai tarin matsalolin da idan har muna tare, to ba za mu taba iya fuskantarsu ba, wannan ya sa na toshe duka koma meye, na yanke wannan hukuncin. Na san ya bata maku rai matuKka. Amma abinda ya faru, shi ya fi mana gaba Claya.” Wani dogon salati suka ji daga inda tsohuwa take zaune, ba yadda ba ayi ba kar ta shiga wurin shari’ar, ta ce ba abinda zai hana ta zama a wurin, saboda ta ji me Tokenta ta yi har akai mata wannan danyen hukuncin. Lallai Malam yau ka ba ni kunya, haka muka tada kai? Wannan za ka facdla mana dama ka dawo daga can Kasar wajen? To ai da ka yi zamanka, ba ka Hatawa kanka
lokaci ba. Me ‘yar nan tayi maka za ka saka mata da hakan? Me ta nema a wurinka?Www.bankinhausanovels.com.ng
Ku maza wato saki ba komai bane a wurinku ko? Ba ku clauke shi a bakin komai ba, amma a wurin mace za ta jure komai, don ta
kare aurenta da martabar ta. Ban ji dadin wannan kalaman daga wurinka ba.” Zaid ya langwabe kai, cikin tsananin tashin hankali ya ce, “Hajja, zamanta da ni, ta fi cutuwa a kan rabuwarmu.”Girgiza kai ta yi, hannayenta a riKe da kafactun Umm Adiyya. “Ina za ka fahimta? Ina za ka fahimta? Amma ina so ka san daga yau kar ka sake zuwa inda take, ba mu
buKatarka mu ma, za mu riketa riko na amana har yanzu muna son ‘yar mu. Duk inda ka ke so, ka je ka Karashe yawonka ka je ka Karashe.” “Hajja da dai za a ji bayaninsa dai kan a mayar masa da laifin.” Maami ta fadfa cikin tsantsar kukan zuci, ita wannan al’amari ta gaji da shi, yaya za ayi ga mutum a nan,
Sannan za ayi ta yanke hukunci, ba za a ba shi damar bayani ba? Ta san ba yadda
za ayi Zaid ya ce baya son haihuwa.
“Ke Nahuce, aikinki ba na shari’a bane? Don me zai sa ba za ki Kwatarwa ‘yarki
‘yanci ba, ki na gani tana cutuwa? Duk matar da za ta bude baki ta ce namiji ya sake
ta, ita ta san Kololuwar racadin da take ji, mai fa daki, shi ya san inda cdlakin yake
masa yoyo. Kodayake me zance ma, tunda dukansu biyu tarbiyyarki ne, kin fi ni
sanin su ciki da bai. Ina so ki facla min, haka halin wannan yarinyar Ummu yake?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Maami kam ita ma ji ta yi idan ta budfi baki za ta saka kuka, hakan ne ma ya sa
hawaye ya dan cika mata idanu. Yau Ummu ta sa an zargi tarbiyyar da ta ba su.
Baffa Abdu ne da ya kula abin ya fara zafi ya sa baki, “Hajja ku yi haKuri, bari mu ji
dai komai dalla-dalla. Hauwa ku shiga da Hajja ciki, bari mu Karasa maganar.” Baffa
ya fada yana kallon bangaren da Mama take zaune, ta buga wani uban tagumi.
Haka matan kaf! Suka watse daga falon, aka bar daga Baffa, sai Zaid sai Adiyya da
Baffa Mai-Kano. Abba ma fita ya yi, don ya ga alama zai iya kwade Umm Adiyya kan
a gama shari’ar, ya fara shinshino rashin gaskiyarta akan al’amarin, kamar yadda matarsa ta facla.
Ya gaza yarda wai ita ta nemi sakin. Sannan Zaid kuma wai baya son haihuwa, to
wace ma irin magana ce baya son haihuwa?
Baffa Mai-Kano ne ya juyo ya dubi Baffa Abdu, “Yaya kai ma ka yi hakuri, ka bari mu
tattauna, don ganin idanunka zai sa su gaza fadin abinda ke ransu.”
Baffa kam ko ya kula Kanin nasa, juyawa ya yi kan Zaid. “Kai yanzu ba a haihuwa za
a haife ka?” Baffa ya fada yana kallon Zaid. Kai ya girgiza masa.
Umm Adiyya ce ta yi saurin cewa, “Baffa asibiti ya kai ni. Likitan ta ce tunda ba ni da
lafiya… Hakan za mu yi na samu lafiya.”
Zaid ya Mago idanunsa cikin dlacin rai ya sauke a kan Umm Adiyya, me yarinyar nan
take nufi, tona komai take so ta yi? Ko kuma so take yi ace ita ce mai gaskiya, mai
kirki tana kare shi? Ajiyar zuciya ya yi, sannan ya ci-gaba da sauraren Baffa.
Kwafa kawai Baffa ya yi, ya bugawa garensa iska ya tattare shi wuri guda ya kadla
kai, sannan ya yi waje Kofar gida, inda Abba ya samu kujerar zaman waje Caya ya
kame. Baffa ma ya samu dungun kan tabarma ya zauna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Baffa Mai-Kano ne ya dawo da hankalinsa kan su. “Ah’ah to. To me ya kawo batun
saki kuma a duk wannan bayanin Zaid? Ka manta kai ne jagorar gidanka, idan
abubuwa sun yi zafi, kai ne mai sanyayawa, idan rai ya Haci, kai ne mai kawar da
kai, idan an yi abu ba daidai ba, kai ne mai tsawatarwa? Idan ya kama ka zage ka yi
lallami da kalamai masu kyautatawa duka sai ka yi, amma Saki?
Cikinmu nan duka iyayenka ne, ga Abbanku a waje ga Baffa Abdunku, ga can
Baffanku Rilwanu a Legas, waye ka taba ji a cikinmu ya kori mace? Don kawai ta ce
maka ta gaji, sai ka biye mata, ku afka shiririta da yaranta? Don gama yaranta zan
kira wannan zancen naku. Ina iliminkun ya tafi?”
Nan kuma aka bar su da raba idanu. Ganin yadda habar Umm Adiyya ke rawa, ya
san ko zai kwana tambayarta, ba za ta yi magana bane, ya sa ya ce, “Ke tashi ki
shiga ciki, ki samu Antinku Muniratu, ki facia mata abinda ya hacfaku, ba za ku tsaya
mana wasa da hankali a nan ba, kwana guda da yini ana kan abu guda. Sai ka ce
cin Kwan makauniya.”
Jikinta na Hari, hanci majina, ido hawaye ta fito tana gauraye hanya zuwa cikin gida,
ta dai gaza hadfa idanu da Mama kam, don ba ta taba tsammanin ta taba jin kunyar
mutum ba, tunda take irin yadda yau da take jin kunyar Mama. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ganin ta shiga akin Antin, ya sa ta bi ta ciki.
“Kin ga Ummu, na san yanzu abin nan yana cikin zafi, duk lokacin da aka ce
zukatan mutane sun sare da al’amuranku, zai iya yiwuwa ayi gyara, amma fa kar ki
manta har abada wannan abin ba zai taba goguwa a idanun kowa ba. Ina wayonki

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *