UKU BALA’I CHAPTER 14

UKU BALA’I CHAPTER 14

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

A hankali take tafiya kanta akasa ga wani zundumemen Hijabi da ta saka a jikinta har yana sharar kasa hannayenta cikin hijabin sai wasa da su take yi.+

Kallo daya zaka yi mata ka gano yanayin rashin kwanciyar hankali a tattare da ita fuskarta tayi fari sosai ga wata rama da ta zabga kamar wacce tayi ciwon shekara guda.

Ratso layin take yi tana bin gefe mutane sai binta da kallo suke yi kamar sun ga watan ramadana sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗin wannan fitowar da tayi bata taba zaton zata tsani kanta ba sai a cikin wannan kwanakin da fita ma

gagararta take yi in kuwa ta fito an dinga zundenta kenan ana nuna ta da baki wasu har tararta suke suna gaya mata magana son ransu sai dai ba yarda zatayi ita ta jawo wa kanta.

Cikin wannan yanayin ba zato ba tsammani taji an janyo mata hijabi ta baya wata irin dokawa taji gabanta yayi zuciyarta harba da sauri ta dago kanta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici dubansa take yi tun daga kasa har sama bata san shi ba bata san daga ina yake ba.

“Ke ba kya ganin mutane ana yi maki magana kin yi banza da mutane iye wacece ke dan kan…”.

Ya lailayo ashar ya dire gami da daga hannunsa daya yana kokari kife ta da mari mai ya gani kuma sai ya sauke yana mai da numfashi.

Sosai tsoro ya bayyana a fuskarta a hankali ta shiga ja da baya tana raɓashi zata wuce don ta lura dan iskan gari ne dan kwaya in ba don haka ba ai bai isa yayi mata wannan cin mutuncin ba ta kyaleshi da sai ta keta masa rashin mutunci amma

halin da take yanzu ba zata iya ba duk da zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke yi akan zagin kare dangin da yayi mata.

Sake fizgo mata hijabin yayi ganin tana kokarin raɓashi ta wuce ya tsaya dab da ita har suna shakar numfashin juna ba abin da ke tashi a jikinsa sai warin solisho da sukuɗaye kau da kai tayi da sauri gami da toshe hanci wani yinkuri taji zuciyarta ta nayi tana kokarin yin amai.

Ganin abin da take yi masa yasanya shi duban fuskarta da take yatsine masa tana toshe hanci wata irin ashariya ya danna mata gami da cafko hijabin jikinta ya cikuikuye.

“Ke dan kan uban ki ni kike toshewa hanci to ubanki ne ke wari ba ni ba matsiyaciya karuwan banza da wofi”.

Yana fadin haka ya fizge hibajin gabadaya daga jikinta daga ita sai zani da ves ga katon cikinta da ya fito sosai wanda haihuwarsa nan kurkusa runtse idanu tayi gami da toshe

kunnuwanta wani kuka ne ya zo mata da sauri ta durkushe tana mai sakin sa shi kuwa sai faman danna mata ashar yake yi.

Lokaci kankani mutanan layin duk suka taru aka rasa wanda zai zo ya kwace ta domin kuwa suna tsoron TANGA ba wanda bai sanshi ba a fadin garin nan tattarin dan jagaliya ne kashe mutum a wajansa ba komai bane yayi zaman gidan kaso yafi a lissafa a fitowa dashi.

“In kana yiwa Allah da Annabi ka bani hijabi na”.

Ta fadi cikin muryar kuka jikinta sai rawa yake yi wani takaici take ji a zuciya ji take kamar ta hadiye zuciyar ta mace.

Cilli yayi da hijabin da sauri ta rarrafa za ta dauka ya danne mata yatsun hannu ta kurma uban ihu a daidai lokacin motar Dr.Karami ta sanyo kai ganin abin dake faruwa a layin ya sanya shi taka burki ya fito da sauri yana duban mutanan da sukayi cirko-cirko suna kallon rigimar Hafsat da Tanga da sauri ya isa wajan sam bai san wacece ba amma ganin irin cin zarafin da ake yi mata ya sanya shi zuwa ya hankaɗe tanga a daidai lokacin ita kuma Hafsat ta dago kai.

STORY CONTINUES BELOW

‘Innalillahi’ abin da Dr.Karami ya furta kenan yana ja da baya duban ta yayi kafin cikin hanzari ya isa ya dauko mata hijabin nata ya yafa mata a jikinta cikin sauri duban mamaki yake mata da al’ajabai ganin yarda ta koma kamar ba ita ba.

“Hafsat me ya hadaki da wannan mutumin har yayi miki wannan cin zarafin?”.

Girgiza kai kawai take yi zuciyarta na suya hawaye sai ambaliya suke yi mata a fuska numfashi taja mai cike da takaici ta mike kan kafafuwanta ta dubi Tanga sannan ta dubi Dr.Karami a hankali ta raɓashi zata wuce gabanta ya sha yana mai sake

tambayarta amma ta kasa bashi ansa kuka kawai take yi abin duniya ya yi mata yawa abin da bata so a gane yau gashi a bainar jama’a kowa ya gani kuma ya san halin da take ciki dama an dade ana zarginta yau dai gashi zargin ya tabbata kowa zai tsine mata da kazamar rayuwar da ta zaɓawa kanta wanda take ciwa mutunci take yi wa kallon banza ta sani yau sai sun zuba ruwa aka sun sha.

Ihun da taji ne ya katse mata dogon tunanin da take yi cikin razana ta juya Dr.Karami ta hanga ya cakumi Tanga sai jibgarsa yake yi gabadaya ya kumbura masa fuska bakinsa har ya fashe yana zubda jini ware idanu tayi mamaki ya sake cikata da sauri ta ja jiki ganin hankalin mutane ya bar kanta ya koma wajan su Dr.Karami.

Tafiya take yi cikin sauri-sauri kamar zata kifa hijabin sai harɗe ta yake yi tattareshi tayi sosai ta rike a hannu ta shiga jefa kafarta a duk in da taji ta dira idanuwanta sun kara kaɗawa sun yi jajir tana kokarin karya

kwanar da zata shigar da ita gida suka yi arba da Abulle kallo ta bita dashi daga sama har kasa kafun ta dauke kanta cike da takaici da bakin cikin wannan rayuwar da ‘yarta ta tsinci kanta a ciki Allah na gani tayi bakin ciki tayi takaici tayi kuka sosai a kan wannan lamarin zuciyarta ji take yi kamar za ta soye don raɗaɗin da take ji tun da abin nan ya faru ta kasa kwanciyar hankali kullum cikin fargaba take akan abin da zai je ya dawo.

“Daga ina kike?”.

Ta fadi fuskarta a daure tamau kamar bata taba yin dariya ba ba alamun tausayi amma in da zaka fasa zuciyarta tausayin ‘yar ta ta ne makil a cikinta.

Girgiza kai Hafsat tayi hawaye na sake balle mata sautin kukan da take boyewa ya bayyana sosai hakan ya kara tayar da hankalin Abulle da sauri ta riko mata hannu tana mai

tambayar ta cikin yanayi na firgici amma ta kasa magana sai girgiza mata kai take yi tana kai hannayenta saman bakinta tana toshewa.

Riko ta tayi sosai ta sanyata gaba suka nufi gida tafiya suke yi gabadayan su zuciyoyinsu na suya musamman Hafsat in ta tuna cin zarafin da akayi mata a bainar jama’a sai ta sake rushewa da kuka kamar numfashinta zai dauke a soro suka ya da zango Abulle sai mai da numfashi take yi ita kuwa Hafsat zubewa kan

gwuiwowinta tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana hadiyar zuciya sai shassheka take yi idanuwan nan nata sunyi luhu-luhu jikinta na faman k’yarma.

“Ya isa haka Hafsat dai na kukan fada min abin dake faruwa?”.

Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke su kan Abulle cikin wani irin yanayi muryarta na rawa ta shiga bata labarin abin da ya faru da ita a yanzu…

Wani kuka ne ya sake kufce mata ta rarrafo ta riko mata kafa.

“Don Allah Umma ki yafe mani na tuba wallahi ba zan sake ba ina cikin bala’in rayuwa ita cikin kazamar rayuwa wacce ni ne na zama silar faɗawa cikin ta don Allah ku yafe mani abin da nayi muku na san ban kyauta muku ba a matsayin ku na iyaye na…”.

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri Abulle ta toshe mata baki tana mai duba kofar gidan da soron gidan ganin ba kowa ya sanyata duban Hafsat wacce gabadaya ta fice daga hayyacinta.

“Hafsat kukan ya isa haka nan kiyi shiru karki haifarwa kanki da wata matsalar ciki ne a jikinki wannan kukan kuma da kike yi kina ta da hankalin ki sai ki fuskanci matsala…”.

“Nafi kaunar in shiga matsalar da zan mutu akan wannan rayuwar da nake yi na tsani wannan rayuwa na tsani wannan duniyar na tsani kaina…”.

Da sauri ta rufe mata baki ita kanta ‘yarta ta tausayi take bata kwalla ne suk cika mata idanu da sauri ta kau da kai ta dauke su ta janyo Hafsat jikinta.

“Ya isa haka ki daina fadin haka komai da kika ga yana samun bawa a duniyar nan ƙaddararsa ce haka…”.

“A,a Umma wallahi ba ruwan kaddara ni ne sila komai da yake faruwa dani ni ce sila kiyi hakuri Umma ku yafe mani na gaji da rayuwar nan nafi kaunar mutuwa da wannan rayuwar na san ko a wajan

Allah ni mai laifi ce nayi abun da yake fushi dani nayi abin da ya kauce hanyar addini na kaico! Umma nasan na aikata kuskure Umma duk abin da kika ga yana faruwa Goggo ce sila ita take sanya ni”.

Da sauri ta sake rufe bakinta tana mai girgiza mata kai.

“Nace kiyi shiru ko bana son jin komai daga gareki…”.

“Umma ki bari na fadi domin ni dai na san rayuwata ta kare gwanda na fadi komai domin ki rokar min afuwa wajan mahaifina da wanda ya zama ina da hannu cikin faɗawarsu hukubar rayuwa”.

Nisawa tayi tana mai da numfashi kafin ta gyara zaman da tayi dirshan akasa ɗan cikinta take ji yana ta faman juyawa yana tokare mata kirji laɓɓanta ta ciza gami da runtse idanu hakan da Abulle ta gani ya sanyata ware idanu tana tambayarta ko lafiya amma ta kasa bata ansa sai da ta dauki lokaci a haka kafun ta nisa wasu zafafan hawaye suka zubo mata.

“Duk halin da su Mariya suka shiga da Ummanta Goggo ce sila haka bacewar Abban su Mariya Goggo ce sila ita taja ni muka je wajan wani mutumi a dajin kauyen Sulalla akayi masa kurciya…”.

“Innalillahi wa inna ilair raji’un”.

Abin da Abulle ke maimaitawa kenan tana dafe kanta da take jin yana kokarin rabewa biyu lokaci guda idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir wata irin tsanar kanta take ji tana tsanar zaman ta a duniyar nan a

daidai wannan lokacin wani takaici ne da bakin ciki ya turnuke ta bata san tsanar da Goggo tayi ma su Bello har ta kai haka ba ta san kiyayyar da take masu takai haka ba.

Mikewa tayi kan kafafuwanta tana duban Hafsat kafin ta fidda hannu cikin zafin nama ta dauketa da Mariya hagu da dama har sai da ta tuntsira ta bugu da bango hancinta da bakinta duk sun fashe suka dinga zubda jini da sauri ta ja jiki zuciyarta na suya ta fice daga cikin soron zuciyarta take ji tana kara ya

mutsewa gabadaya taji ta tsani zaman ta a duniyar ina ma numfashinta zai dauke ta rabu da wannan takaicin da bakinciki da uwarta da ‘yarta suka cusa mata a zuciya.

Hafsat ganin yarda Abulle tayi mata ta sake rushewa da kuka tana hada kanta da bango kamar ba a jikinta yake ba sai da tayi kuka ma ishinta sannan ta mike tana faman hade hanya ta nufi cikin gidan.

********

Fizgo shi yayi suka isa kofar gidan sai faman cin magani yake yi Alhaji Abdurrazaq ya kwala sallama hannunsa rike da Huzaif da gabadaya ya gama kumbura ji yake yi kamar ya fashe don takaici da bakin ciki wai mahaifinsa ya yi masa irin wannan cin zarafin akan wata banza wacce bai ganin ta da wata kima ko daraja.

Abban su Mariya ne ya fito yana duban su daya bayan daya don bai san su ba Alhaji Abdurrazaq ne yayi masa sallama ya ansa shi cikin yanayi na son karin bayani.

“Kai ne mahaifin Hafsat?”.

Bello ya gyaɗa kai yana duban Huzaif ganin yarda aka riƙe shi kamar wanda yayi sata shi abin har dariya ya so ya bashi.

“Sunana Alhaji Abdurrazaq ni ne mahaifin Huzaif wanda ya ci zafin ‘yarku ya keta mata haddi”.

Zaro idanu yayi sosai yana duban su zuciyarsa yake ji tana bugawa da sauri-sauri wani takaici ya kume shi da sauri ya juya cikin gidan dakin Goggo Marka ya nufa ba ko sallama ya shiga tadda ita zaune yayi ta hada tagumi can gefe kuma Hafsat ce ta dukunkune sai faman numfashi take ja tana saukewa.

“Kunyi baki ku taho suna jiranku”..

Yana fadin haka ya fita daga cikin dakin zuciyarsa na raɗaɗi gami da zafi ya jima yana takaicin wannan lamarin tun lokacin da ya gane wa idanuwansa ya tambaya amma Goggo Marka ta so ci masa mutunci tun daga wannan lokacin bai sake magana ba sai dai yaje har gidan Abulle ya hadu da mahaifin Hafsat suka zauna sukayi magana a nan ya san komai yayi bakin ciki sosai yayi takaici.

Tabarma ya dauka yanufi soro da ita ya shimfiɗa sannan yayi musu iso har lokacin Huzaif na hannun mahaifinsa ya ki sakin sa zama sukayi amma shi Huzaif ya tsaya kerere a tsaye a daidai lokacin suka iso su kuma Hafsat tun da ta hango huzaif ta ji gabanta ya yanke ya fadi wani kallo ta ga ya watsa mata ita ma kallon ta watsa masa daga nan ta kau da kai.

Alhaji Abdurrazaq ne ya muskuta ya dubi Goggo Marka da tayi wiri-wiri da idanu sai hada gumi take yi abi duniya duk yabi ya addabeta.

“Maganar da mukayi kwana ki dake na cewa zan aurawa ɗana jikarki domin kuwa cin zarafin da yayi mata ba zan yarda dashi ba domin ba zan yarda ko ‘yata ayi wa haka ba don haka shine nake so ku bashi aurenta domin ba wanda zai aureta bayan shi in kuma ba ku yarda ba ni zan shigar da wannan maganar kotu kuma zan tsayawa Hafsat kai da fata har in ga an kwatar mata hakkinta”.

Bello ne ya dube shi sosai yanayin sa ya burgesa yarda ya nuna ba yarda ba akan cin zarafin da ɗansa yayi wa Hafsat ba ya ji dadin haka sosai ko ba komai ya nuna shi mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata duban Goggo Marka yayi kafun ya kau da kai.

“Ba sai maganar taje kotu ba ni ina bayanka nima a matsayin uba nake ga Hafsat in dai ta haihu ni na aminci ya aureta sai dai kuma magana daya akwai sharaɗi na lura kamar dole kayi wa ɗan naka don haka zan masa gargaɗi in har ya aureta ya ci zarafinta ko ya kuntata mata wallahi tallahi ni da kaina zan shigar da maganar nan kotu sannan a sake tada tsohon duk wani cin zarafi da yayi mata”.

Wani kuka ne ya zo wa Hafsat mikewa tayi ta dubi Huzaif da yayi tsiru-tsiru da idanu sosai take jin har yanzu tana son sa bata jin zata iya rabuwa dashi duk da abin da yayi mata son sa ya zama jinin jikinta wanda hakan har yanzu ya kasa sanyata ganin laifinsa duban su tayi dukkan su kafin ta ja kafafuwanta da sukayi mata nauyi ta shige cikin gida….Gumi ne kawai ke ta faman keto mata kamar wacce aka juyewa diron ruwa sai faman yamutse fuska take yi tana cizon laɓɓa gabadaya ta gama galabaita ta fice daga hayyacinta lokaci-lokaci take ajiyar zuciya ita kadai tasan bala’i da masifan da take ciki yau kusan kwana uku kenan tana jin ciwon a tsaitsaye amma na yau ya shafe na kwanakin da tayi.+

Jikinta har karkarwa yake yi buɗe idanuwanta tayi da suke runtse sun kaɗa sunyi jajir jijiyoyin goshinta sun fito sosai kamar shirya su akayi kan fatar goshinta hawaye ne suka

kwaranyo mata karo na ba a dadi duban dakin tayi gani take yi yana juya mata sama na dawo kasa kasa na dawo sama sake runtse idanun tayi gami da yin wani yinkuri da ya sanyata sakin wata kara mai razanarwa kafun lokaci guda tayi luf! kamar ba ita bace tayi ihun ba.

Goggo Marka ce ta fado dakin cikin hanzari tana dubanta ganin yanayin da take ciki ya sanyata saurin isa gareta rikota tayi tana faman

duddubata kafun lokaci guda ta gano abin da ke wakana da sauri ta gyara mata zaman dirshan da tayi tana mai rike mata kafadu da sauri ta fizge kanta daga hannun Goggo Marka tana faman sakin wani wahalallan numfashi hawaye sai ambaliya suke mata a fuska.

Sake kai hannu tayi zata rikota a daidai lokacin cikin nata ya sake juyawa wata irin zabura tayi gami da wancakalar da ita gefe guda kan ta ya hadu da gadon karfen dake gefen su  da sauri ta ja da baya tana riko goshinta don sosai ta bugu lokaci guda wajan ya kumbure sosai duban Hafsat ta shiga yi idanuwanta suna kawo kwalla gabadaya ta gama rikicewa kanta gabadaya ya gama shiga duhu tunda Hafsat ta fara

nakudar nan a tsaitsaye hankalinta ya kai kololuwa ba ta san lamarin zai kai ga haka ba wai yau Hafsat ce za ta haife musu abin kunya ɗan shege na gaba da fatiha ba ta taba dana sanin wannan lamarin da kaico ba kamar yau zuciyarta gabadaya ta gama karyewa da tashin hankali bata san yarda za tayi ba bata san wa za ta kai wa kukan ta a daidai wannan lokacin ba kowa ya juya musu baya

musamman Abulle da gabadaya ta dauke musu kafa ta daina bi ma ta kansu ga gidan yanzu ita kanta kunyarsu take yi ta rasa dalili ko da yake ita kadai ta san abin da ta aikata a garesu sosai take jin zuciyarta na kara karye da komai na duniyar ma.

Ihun da Hafsat ta kuma yi ne ya sanyata dawowa hayyacinta dubanta ta shiga yi a tsaye take sai faman ya kice kayan jikinta take yi tana jifa dasu laɓɓanta cikin baki sai faman cijesu take yi kamar ba a jikinta ba idanuwanta a rufe da sauri Goggo Marka ta ja gefe ganin al’amarin ya girmama waje tayi da hanzari tana faman hada hanya Umma ce ta fito ta dubeta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar mata ba lafiya isa tayi gareta tana riko hannayenta ba abin da jikinta ke yi sai karkarwa.

“Habeeba Ban san abin da ke faruwa da Hafsat ba ga ta can cikin dakin sai fizge-fizge take yi”.

Zaro idanu tayi tana ambaton innalillahi wa inna ilaihir raji’un da sauri ta saki Goggo ta nufi daki durkushe ta same ta sai faman nishi take yi ga wani mahaukacin gumi da ta hada gabadaya tayi jagaf! duban kasan ta tayi ganin ruwa na kwarara ya tabbatar mata haihuwa ce da sauri ta fice ba tare da ta taba ta ba can ta hango Goggo sai safa da marwa take yi hannu aka hakan yayi matukar bata mamaki yau kuma girgiza kai tayi gami da komawa daki mayafinta ta dauko ta yi hanyar waje.

Tana sanya kai kofar gida ta hango su da sauri ta yo baya tana mai da numfashi ita gabadaya ta manta ma Mariya na waje lekawa tayi a daidai lokacin ita kuma Mariya idanuwanta na kallon kofar gidan don ta ga lokacin da Umma ta fito ta koma da sauri ya fito ta tayi da hannu sannan ta koma cikin soron sai faman kai kawo take yi don yanayin da ta ga Hafsat a ciki yayi matukar tsorata ta ba abin da ta tuna sai lokacin

STORY CONTINUES BELOW

haihuwar Mu’azzam sosai zuciyarta ta karye lokaci guda hawaye su ka zubo mata a daidai lokacin Mariya ta iso ganin Umma da hawaye a fuska ya tsoratar da ita da sauri ta iso gareta tana tambayarta lafiya numfashi ta ja kafun ta runtse idanu jin yarda zuciyarta ke mikata wani yanayi.

“Mariya Hafsat na cikin wani yanayi matuka haihuwar ce na ke zaton lokaci yayi amma yanayin da take ciki yana bani tsoro”.

Gaban Mariya ya yanke ya fadi idanuwa a waje.

“Haihuwa!?”.

Ta fadi tana dafe kirjinta Umma ta gyaɗa mata kai da sauri ta juya tayi kofar gida wajan Dr.Karami ta koma kallo daya yayi mata ya gano tashin hankalin da take ciki da sauri ya iso daf! da ita kamar zai koma jikinta bakinsa har rawa yake yi wajan

tambayarta lafiya runtse idanu tayi kafun ta buɗe su da kwalla hakan ba karamin kara tayar masa da hankali yayi ba.

“Hafsat ce take wani mataki na haihuwa amma lamarin sai a hankal…”.

Tun kafin ta rufe baki yace da ita.

“Muje!”.

Da sauri ta juya yana biye da ita suna shiga cikin soro suka tadda Umma wata irin kunya ce ta lullubeta shima Dr.Karami sadda kai yayi kasa don ba su yi tsammanin tadda da juna ba da sauri Umma tayi cikin gida shikuwa

sai kokarin buɗe baki yake yi don gaishe Mariya ce tayi masa jagora zuwa cikin gidan dakin Goggo suka nufa wacce take bakin kofa lokaci-lokaci take daga labule tana duban Hafsat sai hawaye su zubo mata shar-shar.

Daga labulan yayi ya shiga da sauri ya isa gareta ya dago kanta da ke sunkuye yana kiran sunanta amma ina ta kasa ansawa da sauri ya kalli inda take durkushe shiru yayi na dan lokaci kafun ya mike ya leka waje Mariya ya yafito dake tsaye ita ma cikin yanayin fargaba da hanzari ta iso gareshe.

“Ku kamo ta kawai mu wuce asibiti ina ganin hakan zai fi dace wa don kin ga dai yanzu ko nace zan yi wani abu ba komai na aiki a wajena da zan taimaka mata domin ba a san yarda haihuwa zata kaya ba duk da dai gaf! take da yinta…”.

Wani ihu ne ya cika musu kunnuwa da sauri Dr.Karami da Mariya suka faɗa dakin a daidai lokacin kan jaririn ya sanyo kai ware idanu yayi kafun yayi waje da sauri cikin

sakanni ya dawo hannayensa da safa a ciki duban Mariya yayi wacce ta runtse idanu har da rufe fuska da mayafin jikinta girgiza kai yayi kafun ya isa wajan Hafsat wacce sai faman nishi take yi na wahala da taimakon Dr.Karami cikin ikon Allah Hafsat ta haihu bayan ta gama kururuwa jaririn na fadowa ta ta baje  a kasa numfashinta na fita kadan-kadan.

“Mariya anso mani reza wajan Umma”.

Da sauri tayi waje ta isa inda Umma ke tsaye sai faman Addu’a take yi idanuwanta sun kaɗa Mariya na isa ta dubeta jiki a sanyaye.

“Umma reza ake bukata”.

Da sauri ta faɗa daki ta binciko sabuwar reza ko buɗeta ba ayi ba ta mikata mata zuciyarta na rage fargaba tunda ta ga an anshi reza da alamun an haihu da sauri Mariya ta juya ta koma dakin tana mika masa ya buɗeta ya yanke cibi a daidai lokacin kuma mahaifa ta fado dauke jaririn yayi wanda ya kasance namiji kyankyawa dashi dube-dube ya shiga yi.

Mariya ta lura dashi kuma ta gane abinda yake nima don haka da sauri ta kara so ciki dakin can gefe ta nufa inda wata akwaku take budewa tayi ta zaro wani sabon zani da alamun ko daura shi ba a taba yi ba ta mika masa goge jaririn ya shiga yi dashi sai da yayi masa tsaf! Sannan ta sake dauko wani ta mika masa ya nannaɗe shi a ciki ya mika mata komawa yayi wajan

STORY CONTINUES BELOW

Hafsat ya dubata ganin yanayin da take ciki ya sanya shi yin waje da sauri Goggo Marka ya duba da ta gama firgicewa can gefe Umma ce ganinsa ya sanya ta yin kasa da kai.

“Alhamdulillah ta sauka”.

Yana fadin haka yayi waje da sauri su kuwa har rige-rige sukeyi wajan fadawa dakin duban juna suka shiga yi kafun Umma ta shiga tsaftace dakin ta gyarawa Hafsat jikinta sosai ta tsorata ganin yarda ta karu a kasan ta hakan ya fadar mata da gaba duban Mariya tayi wacce itama idanuwanta na kanta gyaɗa mata kai tayi ba tare da tace komai ba a daidai lokaci

Dr.Karami ya yi sallama suka ansa shi shigowa yayi hannunsa dauke da dan karamin kwanati (First Aid Box) cikin taimakon Allah yayi mata dinkin inda ta karu gami da allurai duban Umma yayi bayan ya ajje kunyar gefe.

“Jininta ya hau sosai kar ku saka mata ruwan zafi yanzu a dai samu mai dumi ta wanke jikinta dashi sannan ga wannan magangunan…”.

Ya mikawa Mariya ledar yana mai cigaba da fadin.

“In ta ci abinci sai ku bata ta sha tsarin na nan a ciki Mariya sai ki duba ki gani Allah ya raya ya ɗayyaba”.

Yana gama fadin haka ya mike yana duban Hafsat wacce ta dawo hayyacinta idanuwanta sai zubda hawaye suke yi ta kasa kallon kowa ma a cikin dakin yana kokarin fita yaji muryar Umma nayi masa godiya gami da Addu’a murmushi yayi gami da cewa ‘Ameen’ azuciyarsa sosai yaji dadin addu’ar a ransa.

*****

A wulakance ya anshi jaririn da ta mika masa sai faman cin magani yake yi yana hararar Hafsat da kanta ke kasa ita kadai ta san yanayin da take ciki tunda ta haihu yau kwana uku kenan gabadaya taji komai ya canza mata bata jin dadin komai rayuwar ta take ji gabadaya ta gaji da ita zuciyarsa sai zafi take yi ruhinta kamar zai kama da wuta.

“Meye haka Huzaif ya naga kana riƙe shi a wulakance ne kamar ba jininka ba ban son rashin hankali fa”.

Mahaifiyarsa dake zaune ta fadi dama tunda da ta mika masa jaririn ta ga rikon da yayi masa ranta ya ɓaci sosai ji take yi kamar ta mike ta kwada masa mari don sosai take jin haushin sa tun a gida don da kyar da dole sannan ya zo wajan ganin jaririn da Hafsat ta haifa masa.

Sake turbuɗe fuska yayi yana dubanshi ya wullawa Hafsat wani mugun kallo cikin tsana da takaici abin da ke kara bata masa rai yarda jaririn yayi kama da shi sak! kamar kak’i yayi ya ajje hakan na kara kona masa zuciya domin kuwa bashi da wata mafita ko yace ba shi yayi ba ina ma zai ce bashi yayi ba ba yarda  za ayi ba yarda ya  ga kowa na gidan su ya dau zafi dashi akan Hafsat har sun fi kaunar ta dashi a yanzu.

“Ka tafi ka kaiwa mahaifin naka shi ya ga jikansa”.

Ta sake fadi cikin ba da Umarni gabanshi yaji ya yanke ya fadi tunawa yayi da mutannan  da suke soro a zaune ga Abban su Mariya ga nasa ga kuma mahaifin Hafsat wani irin ihu yaji kwanyarsa tayi saura kadan jaririn ya suɓuce a hannunsa da sauri ta kai hannunta ta na cilla masa mugun kallo.

“Wai mai yasa Huzaif kake son bata min rai ne kai yanzus aboda rashin imani ɗan naka zaka yasar saboda wata banzar akiɗa taka da bata da madafa ko mafaka kasan Allah zan bata maka rai in baka yi wasa ba kuma ka rike shi ka mika musu shi tun kafin na bata maka rai”.

Da sauri ya juya ya fita ta bishi da mugun kallo kafun ta juya da idanuwanta ta dubi Hafsat dake ta faman zubda hawaye.

“Kin ga irinta ko Hafsat duk macen da bata kama kanta ba har namiji yayi galaba akanta tana cikin masifa duk son da namiji zai nuna miki duk kaunar da namiji zai ce zai miki karki sake ki saki jiki dashi har wani abu ya shiga tsakanin ku domin duk namijin da ya kasance da mace ba tare da aure ba har ta yarda to wallahi ya daina ganinta da daraja da kima kenan

STORY CONTINUES BELOW

yanzu dai kin ganewa idanunki wani uba ne zai dinga wulakatar da ɗansa har haka in da kunyi hakuri kunyi aure ba ku keta hakkin Allah ba duk haka ba zata faru gareku ba kuna da son zuciyarku so na rufe muku ido har kuyi sake Shaidan yayi tasiri akan ku kina dai kallon yarda Huzaif yake yi miki a yanzu wanda ni sam bana jindadin haka don ba zan goyi bayan sa ba ina so ki kwantar da hankali ki ajje komai a gefe ki fuskanci rayuwa ki raini ɗanki sannan ki dauki komai a matsayin ƙaddara a rayuwarki ta

duniya kuma nayi miki alkawari in har auren nan naku ya tabbata ni zan tsaya miki ba zan taba yarda Huzaif ya cutar dake ba ko yaci zarafin ki”.

Dago idanuwanta tayi ta dubi Mahaifiyar Huzaif idanuwanta na kara rikicewa da zubda kwalla zuciyarta take ji tana kara yamutsewa wai ita ce yau namiji ke wulakanta wa bayan shine ya yi mata cin zarafin da ya zama bala’in rayuwa a gareta

gaban kowa yake yi mata kallon tsana da k’yara ɗan cikinta da ya kasance jininsa shima bai tsira ba kaicon wannan rayuwa duban tsakar dakin tayi niki-nikin kayan da su kawo mata take bi da kallo kafun ta kau da kai ta cikin yanayi na zafin rai da kaicon wannan yanayi da ta tsinci kanta a ciki.

Huzaif sai da ya gama safa da marwa a tsakar gida domin kuwa kunya ce gabadaya ta gama baibaye shi ya kasa zuwa ya kai musu jaririn duk abin da yake yi Mariya na laɓe a labulan dakin su tana kallon shi ji take yi kamar ta fita ta rufe shi da duka don takaici yarda taga yana duban jaririn yana harararsa ya bata haushi da sauri ta dage labulan ta fito wani firgita yayi don ya dauka

mahaifiyarsa ce ta fito har zai kwasa da gudu jin gyarar muryar da Mariya tayi ya sanya shi tsayawa yana dubanta kallon sa ta shiga yi zuciyarta na zafi da raɗaɗi kafun ta dauke kanta ta koma cikin dakin fakare yayi da idanu yana kallonta kamar ya ga sabuwar halitta zuciyarsa yaji ta buga da wani irin yanayi kwanyarsa na ansawa runtse idanu yayi sannan ya buɗe a hankali ya taka kafafuwansa ya shiga cikin soron gabansa na

yankewa yana faduwa yana shiga gabadaya suka zubo masa idanu ji yayi kamar ya nutse cikin kasa don kunya kafafuwansa sai harɗewa suke yi ji yake yi in ya kara taku daya zai baje a kasa mahaifinsa ne ya dubeshu da mugun kallo kafun ya ce dashi cikin daga murya mai cike bacin rai.

“meye haka zaka zo ka tsayawa mutane a kai in ba zaka iso ba ka fita mana”.

Da hanzari ya iso gareshi gami da mika masa jaririn ansa yayi ya shiga dubansa kafun ya dago kai ya dubi Huzaif sak! kamar su ta bayyana a ransa ya dinga ina ma ina ma ace da aure ka samar masa wannan jikan da sai yafi kowa farinciki da jindadi a rayuwarsa amma ƙaddara ta rigayi fata.

“Ƙayi masa huɗuba ne?”.

Ya fadi yana kallon Huzaif da yayi kasa da kai abin duniya duk yabi ya dame shi dago idanuwansa yayi ya sauke a na mahaifinsa yana girgiza kai.

“Wa kake so to yayi maka wa ka mai da dan aikin ki haka za ka haifi ‘ya’yan baka yi musu huduba don baka san darajar su ba?”.

“Ayi hakuri Alhaji miko min shi nayi masa ni  zan wakilce shi”.

Abban Mariya ya fadi da murmushi a fuskarsa.

“Da kan sa zai yi masa ko nan gaba ya koya”.

“Ba za ayi haka ba”.

Ya sake tarar sa, shi dai Mahaifin Hafsat abin duniya ne duk ya addabe shi ya kasa cewa kala sai bin su yake yi da kallo yana wurgawa Huzaif mugun kallo ji yake yi kamar ya mike ya rufe shi da bugu.

“Wani suna za a saka masa?”.

“Tambayi shi rasa kunya din”.

“Hakuri za kayi”.

“Saka masa Muhammad Huzaifa”.

Dukkansu suka dube shi cike da mamaki Huzaif kuwa daskare wa yayi a kasa yanayin da suka ga Fuskar Alhaji Abdurrazaq ba wasa ba wanda ya tanka shi Abban Mariya yayi masa huduba sannan ya mika wa Mahaifin Hafsat amma sai ya kau da kai ya ki ansa ba yarda ya iya dashi ya mikawa Huzaif shi.

“In tayi arba’in za a daura musu aure in Allah ya kaimu”.

Alhaji Abdurrazaq ya fadi ya harara Huzaif da ya mike jiki a sanyaye ya koma cikin gidan.BAYAN SATI HUDU.

Kai kawo kawai take yi tsakar dakin gabadaya ta gama firgicewa yau sati guda kenan ta rasa gane kanta tunda Dr.Karami ya sanar da ita zai turo iyayensa ta dauka abun wasa ne sai taga ya tabbata hakan ba karamin kara rikita mata lissafi yayi ba+

musamman da Abba ya turke ta akan tsakaninta da Dr.Karami duk da ya san komai amma sai ya matse ta sosai domin ta tabbatar masa da cewa Dr.karamin ne zabin ta ita dai Umma yar kallo ce har sukayi kidin su sukayi rawar su fata alheri kawai  take yi don ta fi kowa farinciki da jindadin wannan lamari.

“Wai ke lafiyarki kalau kuwa cikin kwanakin nan gabadaya na rasa gane kan ki?”.

Umma ta fadi tana duban Mariya numfashi ta ja kafun ta daga laɓɓanta tana koƙarin yin magana wayar Umma dake yashe ta dau kara tsuke bakinta tayi tana duban wayar ganin su Baseera ya sanyata saurin daukar wayar jiki a sanyaye.

“Mariya kina ina ne?”.

Muryar Baseera ta karaɗe mata kunne ba tare da tayi sallama ba yanayin muryarta da ta yi maganar da alamun tsoro da fargaba numfashi Mariya ta ja kafun ta nisa.

“Ina gida ya akayi ne?”.

“Wai kin ji yau za a kawo lefe inji Dr.Aqeel jiya yake sanar dani da daddare kin san shekarar jiya iyayensa sun zo tambaya”.

‘Innalillahi wa inna ilahir raji’un’.

Mariya ta fadi a zuciyarta tana mai runtse idanuwanta kanta taji yayi mata wani gingirin gim! kamar an daura mata dutsen dala da goron dutse zuciyarta taji ta matse da wani irin yanayi komai take jin sa yana sauya mata ji take yi kamar ba ita ba komai take ji tamkar a mafarki yake faru.

“Meye kuma haka ya za ayi kiyi shiru kuma kina jin ana zuke mata kudaɗen wayar ta ta”.

Umma ta fadi ganin yarda Mariya tayi mutuwar tsaye wayar a hannunta amma ta kasa furta komai kwanyarta take ji tana hautsewa da tashin hankali lamarin ne take ganinsa kamar ba gaske ba kalmar ‘lefe’ ce kawai ke mata hayaniya aka.

“Nima haka take Baseera yanzu haka shirye shiryen da nake gidanku zan taho don bana son…”.

Shiru tayi tana duban Umma da ta kafe da idanu cike da zargi kau da kai tayi ta fara jan kafafu za ta fice daga cikin dakin Umma ita dai ido take watsa mata tun da aka fara maganar bikin nan na ta ta rasa gane kan ‘yar ta ta komai nata ya sauya ga wani

sanyin jiki da yake damunta ita dai ba ta ga abin damuwa a wannan lamarin ba abin farin ciki ya same ka amma gabadaya kuma sai ka sauya kamar mara lafiya.

“…Uhmm fa kin san mi nima fa yau za su kawo anya Dr.Karami ba hada baki sukayi da Dr.Aqeel ace daga fara magana sai su zage suna kokarin rusa mana rashin mutunci nifa Allah na gani ban shirya ba…”.

Fizge wayar taji anyi da sauri ta juya Umma ce a tsaye fuskarta a hade kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa kasa tayi da kanta ganin irin kallo da Umma take yi mata nuna ta tayi da dan yatsan hannunta tana kokarin yin magana Bello ya shigo bin su yayi da kallo kafun ya dubi Mariya da kanta ke kasa.

“Me kuma ke faruwa naga kun yi cirko-cirko da ku haka kamar zakaru?”.

Ba wacce tayi magana a cikin su Umma ta juya da sauri ta koma cikin dakinta duban Mariya yayi.

STORY CONTINUES BELOW

“Ke me kika yi mata na ga ranta a ɓace?”.

Girgiza kanta tayi idanuwanta na kawo kwalla.

“Ni ba kuka nace kiyi mani ba kin san natsani wannan hawayen naki ko don haka ki shafe su ki fada min abin da ke faruwa”.

“Ni ban yi mata komai ba Abba kawai dai…”.

Shiru tayi tana susar gefen kuncinta kafun ta dago kai ta dube shi shima ita yake duba kafun ya juya yayi cikin dakin Umma ya hango zaune ta zabga tagumi da sauri ya isa gareta zauna gefen ta gami da cire mata tagumi.

“Me kuma ya hadaki da ‘yar taki yau abin da ban taba gani ba?”.

Kallonsa tayi kafun ta dauke kai tana ajiyar numfashi.

“Mariya har yanzu hankalin ta bai gama zama daidai akanta ba in ban da rashin hankali da wauta bayan an gama magana meye kuma na son mai da hannu agogo baya wai maganar nan fa ta kawo lefen take tayi wa kunci alamun bata son wai yayi wuri kaji fa shiririta”.

Murmushi yayi kafun ya shafi haɓarsa.

“Da sauki in ba auren ne tace bata so ba duk labarin kanzon kurege take son biya miki ba wani abu ba”.

Ya fadi yana mikewa kan kafafuwansa dubansa tayi da mamaki.

“Au haka ma zaka ce Abban Mu’azzam kasan dai halin yaran nan abin da kake ganin ba komai ba sai ka ga su sun girmama shi”.

Tsayawa yayi da tafiyar da yake yi ya juyo ya dube ta yana gyaɗa kai.

“Bana so kina saka kokwanto a ranki don Allah ki daina in Allah ya yarda ba abin da zai faru sai alheri”.

Gyaɗa kai tayi gami da daga kafada tana mai da kallon kan Mu’azzam dake ta faman sheka barcin sa hankali kwance tashi tayi ta shiga kokarin gyara dakin domin ta san yau dai gidan sai abin da hali yayi ta san yanzu haka iyalan su Baffa da wasu tsirarun dangin Abban su Mariya na hanya domin su ne za su zo har da su za a anshi lefen.

Fita tayi can ta hango Mariya tana cigaba da gyaran gidan ba ta yi mata magana ba ta bi sahunta lokaci kankani duk suka kammala komai nan suka hau girke-girken tarar baƙi.

Sosai Mariya ta gaji domin ba su gama aikin ba sai wajan daya kuma karfe biyu yan kawo lefen za su zo so take yi ta bar gidan amma Umma ta kasa ta tsare ta hana ta sak! ji take yi kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu musamman yarda ta ga Umma ta tsare mata gida ko magana kuma ba tayi mata tun da safen.

Zaune take ta zabga tagumi sai faman tunanin yarda zata bar gidan take yi gidan su Baseera ta so zuwa to ita ma gashi an yi mata bazata an kwakuya mata rashin mutunci tana tunanin hadin bakin su ne Dr.Aqeel da mutumin nata.

*******

Horn taji anayi mata sam! bata dauka da ita ake ba sai da taji abin yaki ci yaki cinyewa sannan ta tsaya gami da waigowa motar da ta gani ne hakan ya sanyata tsuke fuska tana kokarin cigaba da tafiyarta.

Da sauri ya kashe motar ya fito da hanzari har da gudu gudu ya isa gareta gabanta ya sha yana kure ta da idanu ita mata kallonsa take yi kafun ta kau da kai tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri.

“Ina zaki je bayan kin san dai yau rana ce ta musamman”.

harararsa tayi kafun ta dauke kanta hakan da ya gani ya so bashi dariya don ya san laifin sa yayi mata abun da ba ta san dashi ba shi kasan kasa rike kan sa yayi tun da aka yarje masa an bashi ita gabadaya ya ji kamar nan da wani lokaci wani zai kwace masa ita musamman in ya tuna irin TAQADDAMA da aka kwasa.

STORY CONTINUES BELOW

“Ba laifi na bane laifin mutumin ƙawarki ne”.

Da sauri ta dube shi kafun ta motsa laɓɓanta kamar mai son yin magana amma ta fasa.

Gyaɗa kai yayi fuskarsa da murmushi.

“Har kun gama rigimar taku ne?”.

Ta tambaye shi idanuwanta cikin nashi dariya ya tuntsure da ita kafun ya sake dago kansa ya dube ta.

“Rigima ai dama kece sanadi tun da kuwa kika yi masa tukuici ƙawarki komai ya koma normal tun ranar da abin ya faru ya sanar dani komai kuma mun yafi juna SHARRIN SO ne kawai dama ba wani abu ba”.

Da mamaki take dubansa kafun ta saki murmushi tana mai rufe fuskarta da hannayenta.

“kin rufe fuska mana tunda kin hada zuciyoyi masu cike da ingantacciyar ABOTA suna rigima kamar mu abokai tun na makaranta amma ace a SANADIN ‘YA MACE mun samu matsala abinda ya bani mamaki sannan na kara yarda SO ba abin da bai zai  haifarwa zuciya ta aikata ba”.

ya fadi yana juya idanunsa da suke kara rikita mata lissafi.

“Ina kika nufa naga kin fito a daidai wannan lokacin?”.

Juyawa tayi ta dubi Kofar gidan sannan ta dube shi tana yatsine fuska.

“Ba zan iya zama bane su Baffa sun iso fa kuma hayaniya yayi yawa ni kuma bana so bayan haka kuma nasan yanzu…”.

Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa abin da tayi niyyar fadi tana mai sunne kai kasa murmushi yayi don ya gano in da zancen nata ya dosa.

“Zo muje ki raka ni tunda zaman gidan ne bakya so”.

Da sauri ta dube shi idanuwanta da wani irin yanayi kafun ta shiga girgiza kai alamun a,a shima mamaki ne ya cika shi ganin abin da take yi masa.

“Saboda me ba zaki ba, ba fa nisa za muyi ba?”.

“Ka bar shi kawai ai ba dadewa za suyi ba nima makota zan shi akwai abin da zan yi ne”.

Ta fadi tana mai kokarin wuce shi ta tafi shan gabanta ya sake yi yana dubanta cikin idanunsa da suke kokarin sanya mata gajiya a jiki.

“Baki yarda dani bane ko meye nufin ki?…ko da yake zo mu je to na kai ki gidan mutuniyar taki na san zaki fi sake wa a can din”.

Yana son takura mata ba ta son abin da zai dami zuciyarta so take yi ta tafi ta huta ko ta samu hutun kwakwalwarta don ta san tabbas in tabi Dr.karami surutunsa ya isa ya hanata sukuni ko kuma yayi ta yawo da ita ba su can shagon ba su can wajan shan Icea Cream ita kuma bata son yawa ce ya wacen nan.

“Ina yini Dr.Karami”.

Kamar daga sama suka juyo muryar daga bayan su da sauri suka ji ya macece sanye da nikaf a fuskarta bayan ta da goye kallo daya Mariya tayi mata ta gane wacece kau da kai tayi a daidai lokacin ita kuma ta dage nikaf din Hafsat ce gabadaya ta rame tayi zuru-zuru da ita ga wani baki da ta kara yi kamar wacce ta jima tana jinya duban ta sosai yayi kafun ya gane ta murmushin yake ya saki yana ansawa.

“A,a Hafsat daga ina haka da ranar nan”.

Murmushi tayi itama na yake duk ta sha jinin jikinta domin kuwa gabadaya kunyar Dr.Karami take a yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

“Wallahi Huzaif na kai asibiti ba shi da lafiya “.

‘Huzaif’ Ya fadi a ransa sunan nayi masa yawo kwanya kafun ya dawo tunaninsa ya sake yi mata magana har tayi gaba duban Mariya yayi wacce takure shi da mayun idanuwanta ta na jefa masa kallon mai dauke da yanayin bacin rai kau da kai yayi shima a zuciyarsa dariya yake yiwa Mariya ganin yanayin da ta nuna masa yaji dadin haka sosai ko ba komai ya hango kauna gami da kishinsa a tsakar idanuwanta.

“Kallon na meye haka?”.

Ya fadi yana murmushi hakan ya kara tura mata haushi sake tsuke fuska tayi tana kokarin wuce shi da sauri ya kai hannu zai riko mata hijab mai ya gani kuma yayi saurin janye hannunsa zuciyarsa na bugawa ba zai taba manta yarda suka kwashe da ita ba lokacin da ya rike ta bisa kuskure in kuwa ya sake maimaitawa a yau ya san zata dauka a gaske yayi Allah kadai ya san hukuncin da za tayi

masa numfashi yaja daidai lokacin da yaji tsayuwar motoci ita kanta Mariya tsayawa tayi da tafiyar da take yi ta juyo ganin motocin sunyi parking kure su tayi da idanu gabanta taji ya yanke ya fadi ta tabbata yan gidan su Dr.Karami ne masu kawo lefe don haka da sauri ta juya ta dube shi ganin yana yi mata dariya har da gwalo ya sanyata turo baki gaba tana harararsa kafun ta juya da sauri ta fada gidan makotansu.

Shi abin ma dariya ya bashi bai san wacce irin kunya bace Mariya gareta ko da yake jinin fulani in yayi duba da Umma sak! ita ma haka take da sauri ya shiga motarsa ya ja ya isa inda motocin suke mazaje ne ziryan ba Mace ko daya a cikin su sune yan kawo lefen.

Gaida su yayi bayan ya fito daga cikin mota wani kanin Hajiyarsa ce ya kalle shi cikin harara.

“Au wai ke dama kana nan unguwar ko biye damu kake?”.

So sa kai yayi kafun ya dubi sauran yan uwan mahaifin nasa da sukayi masa kuri da idanu suna dariya.

“Kawu Sako fa na kawo mata shi…”.

“Sako eh tabbas na ga sako ai sai ka zo muje Lefen ma mu kai da kai tare ko”.

Gabadayan su suka kwashe da dariya a hankali ya ja da baya kansa akasa ya fada cikin motarsa ya yi mata Key sannan ya leko da kai waje.

“Kawu sai kun dawo a dai yi duk abin da ya kamata surukar taka ta musamman ce”.

Ya fizgi motar da gudu yana faman sheka dariya suma dariyar suke yi kafun su bude  kofofin wata mota kirar Benz sabuwar dalla sai daukar idanu take yi suka shiga sauke tika-tikan akwatina masu kyau da tsari har set biyu kallo daya za ka yi musu ka kasa dauke idanuwanka domin sun hadu iya haduwa tsayawa masalta su wani cin lokaci ne da nuna kauyanci…

Abin fa ya zo shagalin da muke rawar kai akan sa ya zo gash har ya zo ya taddamu

Ina yan team din Dr.Karami da Mariya ku zo ku fidda mana da Anko tun wuri tsakani har ga allah duk wanda kuma bai yi ba Dole Dr.Karami ya bata dashi

Haka ma yan team Dr.Aqeel ku zo ku fidda mana da anko tun wuri

Bikin ya zo domin bikine za muyi na kece raini biki ne na manya

Ina jiran raayoyin ku akan wannan shagalin ku zo ku ba da shawarar yarda za a tsara abin

????Dubansa take yi zuciyarta na kara mikata wani mataki na son sa duk cin mutunci da wulakanci da yake yi mata sam bai damunta kamar yarda yake bayyana kiyayyarsa gareta sosai take jin zuciyarta na suya ruhinta da kwanyarta ja take kamar za su kama da wuta numfashi take ja a hankali idanuwanta sai zubda hawaye suke masu zafi ta duɓe shi a karo na ba a dadi hannunta rike da Huzaif.+

“Huzaif yau ni ce kake wulakanta wa Huzaif yau ni ce kake ciwa mutunci bayan kai ne silar faruwar komai gareni…”.

Wani banzan kallo yayi mata kafun ya mika mata Huzaif dake hannunsa dama duk ya gaji da rikonsa ji yake yi kamar an daura masa ƙaya a hannu in ba don Hajiyarsa tayi masa umarni da cewa ya dinga zuwa ba in ba haka ba zata bata masa ba abin da zai kawo

shi wajan banzar yarinyar nan da bai san ma ya akayi ya fara kulata ba a yarda yake na matashi mai jini a jika amma ace shine yake tsayawa da wannan kazamar har za ta zama matar auren sa nan da sati guda.

Wani kunci ne ya mamaye zuciyarsa ji yake yi kamar ya sheka ta ta mutu kowa ma ya huta.

“Karki sake daura min laifi don bani na kawo ki ba ke kika kawo kan ki gareni sannan ban yi miki dole ba balle kiyi tunanin ko na KETA HADDI a gareki”.

Runtse idanu tayi tana jin yarda maganganunsa ke ratsa zuciyarta da kwanyarta suna haifar mata da wani yanayi mai kokarin kona mata duk wani sassa na jikinta girgiza kai ta shiga yi numfashinta sai kai kawo yake yi kamar zai dauke.

“Ki rubuta ki ajje ko da kin aure ni wallahi ba zan taba son ki ba bana kaunar ki daidai da kwayar zarra a zuciyata domin ni ba zan auri jahila…”.

“Ya isa haka Huzaif ya isa nace maka!”.

Hafsat ta fadi cikin karaji tana toshe kunnuwanta da take jin maganganun kamar za su fasa mata su kuka ne ya sake kwace mata duban sa tayi.

“Ba sai ka gaya min baka kauna ta ba sannan ba sai ka gaya min ka tsane ni ba amma ka ajje wani abu a ranka wallahi tallahi Huzaif sai na aure ka kuma wallahi sai ka so ni a yarda nake don ba wanda ya bata min rayuwa sai kai ba wanda ya jefani cikin bala’i sai kai don haka wallahi tun da muka dama tare da kai sai mun shanye sai dai in an kai ni gidanka ka dinga yagar nama kana watsarwa”.

Ta fadi tana hadiye kukan Huzaif ta saba abaya ta goyashi sannan ta sanya hannu ta shafe fuskarta da hawaye suka ki tsayawa da zuba wani abu ta hadiye mai tauri kafun ta dubi Huzaif da yayi fakare yana kallonta wani kunci da takaicinta na kara turawa zuciyarsa bakin ciki murmushi ne mai ciwo ya wanzu a fuskarta.

“Kasan Allah Huzaif sai na aure ka a baya ina jin takaicin cin mutuncin da kayi mani bayan ka keta mani haddi amma tun da abin naka haka ne MU ZUBA MU GANI shege ka fasa”.

Da sauri ta juya zata tafi sai kuma ta tsaya zuciyarta na bijiro mata da wani tunanin juyowa tayi ta dube shi da mugun kallo a fuskarta goyon ta

kwance sannan ta iso in da yake tsaye mamaki duk ya gama cika shi ganin yarda lokaci guda Hafsat ta juye kamar ba ita ba gaban motarsa ta isa ta ajje jaririn kafun ta dube shi hawaye na kara balle mata.

“lokacin da muka hadu da kai ni kadai ka gani ba tare da wannan jaririn ba”.

Ta nuna Huzaif da yake ta faman wutsul-wutsul da kafa kafun lokaci guda ya balle da kuka.

“ka dauke shi don bani ni ne ya kamata na rike shi ba a halin yanzu ka je kai ma ka ɗanɗana abin da ake ji”.

Tana gama fadin haka ta juya da sauri ta shige cikin gida kunnuwanta sai faman ansa sautin kukan ɗanta suke yi wani irin yanayi take jin kanta a ciki gabadaya duniyar take ji ta sure mata ina ma ace za ta mutu da sai tafi kowa farin ciki.

STORY CONTINUES BELOW

Kwalla mata kira yake yi amma ina ko ta kan sa ba ta bi ba juyawa yayi ya dubi Huzaif ganin yarda yake rusar kuka gabadaya yaji ya firgice da sauri ya isa gareshi ya dauke shi yana jinjigashi amma ina kamar ana kara rura wutar kukan nashi waige-waige ya shiga yi amma ba kowa a layin da sauri ya isa kofar gidan ya tsaya

idanuwansa sunyi tsuru-tsuru gabadaya kwanyarsa yake ta rikice kafun ya ankara yaji saukar fitsari a jikinsa wani ihu ya saki yana daga shi daga jikinsa fitsari sai tsartuwa yake yi hakan ya kara bata masa rai ya shiga yatsine fuska ji yake yi kamar yayi cilli da jaririn amma ya kasa ya leka soron yana zundumawa Hafsat kira amma ina kamar yana kiran dutse tana jin sa amma tayi banza dashi zuciyarta kuwa sai zafi take yi in ta jiyo kukan ɗan nata ji take yi kamar ta tashi ta anso shi amma in ta tuna abin da Huzaif yayi mata sai ta komata zauna tana rusar kuka.

Mota ce kirar Benz tayi Parking a daidai kofar gidan su Mariya da Baseera suka fito daga can gefen direba kuma Dr.Karami ya fito fuskarsa da yalwataccen yanayin farin ciki duban su yake yi su duka kafun ya sauke akan Mariya da tayi kasa da kai Baseera kuwa sai zabga dariya take yi tana duban Dr.Karami da yake harararta.

“Malama ba ma son ranin sense ga ya za ayi za ki dinga mana dariya”.

Ya karashe shima dariya na kokarin kwace masa a daidai lokacin Mariya ta dago kai ta dube shi tana watsa masa harara.

“Malama zo mu wuce ciki in kun gama dariyar”.

Mariya ta fadi tana duban Baseera Dr.Karami ne ya miko musu jaka mai dauke da IV Baseera ta ansa tana dubawa kafun ta mikawa Mariya.

“Naki yafi nawa kyau gaskiya”.

“Ai sai ki sauya”.

Ta fadi tana harararta sake tuntsirewa da dariya Baseera tayi kafun ta ja hannun Mariya su fara tafiya.

“Au ko sallama babu da yake nayi muku abin da kuke so ko, ai ko ni direbarku ne sai haka inda na san haka Allah sai dai naki Dr. ya zo yayi wannan yawon dake amma saboda son kai ya tashi ya gudu ya barni da iyayinki”.

Dariya ta sake yi kafun ta dubi Mariya da gabadaya ta ki sakin jikinta  sai faman hade fuska take yi.

“Kai ka san in da ba abin da ya sanya shi gaba ba abin da ba zai mani ba kuma ko da ka tafi dani ai na taimaka maka ita mutuniyar taka mai tayi bayan zaman shiru komai ni nake yi”.

Tana gama fadin haka ta ja Mariya sukayi gaba bin su yayi da kallo zuciyarsa na mika shi wata duniya ta musamman sosai yake jin zuciyarsa na kara narkewa da wani irin yanayi game da Mariya ji yake yi kamar ya sake janyo lokacin bikin ya dawo nan da kwana biyu ba sati guda ba.

Sai da ya ga shigewarsu sun sha kwana sannan ya shige motarsa cike da farin ciki ya ja ya tafi.

Turus suka tsaya a kofar gidan ganin abin da ke faruwa Baseera ce ta dubi Mariya baki na rawa.

“Mugun abu Mariya me nake shirin gani?”.

Wani yaƙe Mariya ta saki kafun ta dubi Huzaif da yayi wujiga-wujiga dashi gabadaya jikinsa ya gama bacewa da fitsari da kashin ɗan nasa fuskarsa kawai zaka kalla ya baka tausayi don gabadaya yayi laushi ji yake yi kamar ya kurma ihu don takaici sam bai lura da su Mariya ba sai da suka iso kofar gidan za su shiga ya gansu ji yayi kamar ya nutse a kasa don kunya duk sai yayi wani wiƙi-wiƙi dashi kamar wanda yayi wa sarki karya Baseera kuwa abin dariya ya bata amma sai ta kanne dama ta dade tana jin haushin Huzaif tun

STORY CONTINUES BELOW

lokacin da ta samu labarin abin da ya faru tana kokarin yin magana taji Mariya ta fizgi hannunta sun faɗa soro da sauri ya bi bayan su yana kwalawa Mariya kira cikin wani irin yanayi na rawar murya tsayawa tayi cak! batare da ta juyo ta dube shi ba.

“Don Allah taimaka ki mikawa Hafsat ɗan nan tun dazu yake ihu na kirata amma ta ki zuwa ban san mai take nufi ba”.

Baseera ce ta juyo ta dube shi a wulakance.

“Meye nata ita da kake cewa ta anshe shi ta kai shi ai na dauka gidan ba bakon ka bane ko ai sai ka shiga ka kai shi ba ma wannan ba ai na dauka ɗan ka ne ka ga ai kaima zaka iya zama ka rarrashe shi ba dole sai uwarsa ba”.

Runtse idanu yayi domin sosai yaji maganganun Baseera sun taba masa zuciya amma sai yaki nuna haka a fili sai ma murmushi yaƙe da yake ta faman yi yana sanɗa kai domin ba abin da yafi bukata a yanzu illa a raba shi da yaron nan don ya gama firgitashi gabadaya musamman in ya dubi jikinsa yarda ya baci duk abin duniya ya bi ya dame shi.

“Don Allah na roke ki”.

Ya fadi da muryar tausayi ganin Baseera ta ja hannunta za su shige juyowa tayi ta dube shi.

“ka bari za a turo maka ita sai ta anshe shi da kanta ban san abin da ya hada ku ba har ta bar ɗan nata a nan ba zan asa taje taga baƙina ba”.

Tana fadin haka ta juya suka shige shi kuwa ji yayi kamar ya kurma ihu don takaici sai ya tafi kamar zai shiga cikin gidan sai kuma ya dawo da baya.

Suna isa cikin gidan suka hangota can kofar daki ta hada kai da gwuiwa sai shsashekar kuka take yi Baseera ta dube ta ta taɓe baki kafun ta saki hannun Mariya ta fada dakin Umma.

” Bai kamata ace kin zo nan kin zauna kin barshi rike da ɗanki ba ya kamata kisan darajar ɗa kuka yake yi fa amma kin zo nan kin zauna ai ko mai yayi miki shi Huzaif din bai kamata ki haɗa hukucin da zakiyi masa har da ɗan naki ba domin shi bai san komai ba bai ma san abin da kuke yi ba don haka ki je ki anso shi don ya ɓata masa jiki sosai”.

Tana gama fadin haka ta juya ta shigewarta dakin Umma zuciyarta na kara tausayawa yanayin da Hafsat take ciki gabadaya ta sauya kamar ba ita ba Mikewa tayi tana faman tankaɗi kamar wacce ta kwana ta wuni bata sakawa cikinta komai ba a hankali take tafiya har ta isa soron yanayin da ta ga Huzaif din a ciki sai da zuciyarta ta harba da sauri ta isa gareshi ta anshe shi tana wurga masa wani kallo kafun ta juya ta koma cikin gida ranta ba dadi gabadaya.

Umma ce ta dube su su duka kafun ta dubi ledar da Baseera ta ajje gefe guda.

“Wannan kuma na meye…ba ma wannan ba ina kuka tsaya tun dazu ku da kuka ce mani ba daɗewa za kuyi ba”.

Ta karashe tana duban Mariya da ta koma gefe ta takure kamar wacce bata da lafiya.

“Wallahi abin da muka je ansowa ne muka samu ba a karasa ba”.

Baseera ta fadi tana zaro Iv din tana mikawa Umma ansa tayi tana dubawa kafun ta dubi Baseera.

“Amma fa sunyi kyau sosai”.

Murmushi Baseera tayi kafun ta dubi Mariya wacce itama izuwa lokacin ta dago kai.

“AMAREN BANA”.

Baseera ta fadi cikin zolaya hararar ta Mariya tayi kafun ta dubi Umma.

“Ya kamata Umma ki yiwa Mariya magana gabadaya taki sakin jikinta shi kansa Dr. sai da ya tambaye ni ko akwai abin da ke damunta ne nace masa a,a gaskiya yanayin da take nunawa kamar akwai abin dake damunta”.

Numfashi Umma ta ajje kafun ta dubi Baseera.

“Ni ban san ta ina zan fara miki ba nima yanayin da Mariya take nunawa ya fara isa ta wani in ya ga haka sai ya dauka kamar auren dole za ayi mata…”

Bata karasa  maganar ba wayar Baseera ta dau kara da sauri ta zarota daga jaka ganin sunan Mami ya sanyata saurin mikewa.

“Umma bari na tafi kin ga har Mami ta kira ni nasan tana can tana jira na itama daɗewar da mukayi yayi yawa”.

Tana fadin haka ta dauki jakarta da ledar IV dinta ta fice bayan ta yiwa Umma Sallama Mariya ta mike jiki a sanyaye tayi mata rakiya.

MARIYA & DR.KARAMI

IV

BASEERA & DR.AQEEL

Runtse idanunta take yi zuciyarta na zafi ji take yi kamar ta haɗiyi zuciyarta ta mutu don bakin ciki kukan da take yi tana samun sauki a yanzu ya zama wahala a gareta HAWAYEN ZUCIYA da take jin zubar su suma tana samun sauki kadan suma sun dai na zuba idanuwanta gabadayan sun kekeshe ba alamun za su zubda hawaye zafin zuciya ne da na ruhi kawai take jin su kamar a wuta aka jefa ta.+

Dago kanta tayi ta dubi jikinta wani kunci ne ya sake mamaye zuciyarta in ta tuna yarda ta ga Mariya a wannan rana cikin yanayi na alfarma da shiga ta burgewa a matsayinta ta amaryar gobe har da ita amma ita ko wacce ta fi kowa rashin gata a duniyar nan sai ta fita jindadin irin wannan ranar wai ita ce yau kayan ma da zata saka ta fito a matsayinta na wacce za a daurawa aure amma sun gagareta kaicon wannan rana.

Sautin guɗar da taji ta karaɗe gidan ne ta daki kunnuwanta ya sanyata sake runtse idanunta gami da toshe kunnuwanta ji sautin take kamar ana zirara mata ruwan dalma cikin kunnuwanta mikewa tayi kan kafafuwanta tana faman haɗe hanya fuskarta kadai zaka kalla ka gane kuncin da take ciki duban Huzaif tayi dake kwance a yan kwane kamar wanda ya fado daga sama ba uwa ba uba kau da kai tayi tana taka

kafafuwanta tana kokarin fita a daidai lokacin Goggo Marka ta sanyo kanta cikin daki cikin yanayi na razana saura kadan su yi gware idanuwansu suka sarke da juna idanun Goggo Marka lokaci guda suka kawo hawaye da sauri ta kau da kai tana karasawa cikin dakin tayi zaman yan bori gami da dafe kanta wani irin kunci da takaici suke nukurkusar zuciyarta ga wani raɗaɗi da zafi da

take jin ruhinta na yi mata kwanyarta take ji na ta faman ihu da hayaniyar abin  da ya jefata cikin wannan halin bata taba zaton rayuwa zata juya mata haka ba bata taba zaton duniya zata yi mata gwatson mage ba sai yau.

Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke a fuskar Hafsat wani irin tausayinta take ji na kara narkar mata da zuciyarta tana kaico da wannan rayuwa da suke ciki wacce ita ce ta zamo sanadi garesu baki daya ita ce silar faruwar duk wani bala’i da masifa da suka tsinci kan su.

“Kiyi Hakuri Hafsat ki yafe mani NA YI NADAMA…”.

Wani banzan kallo ta wurgama mata dama cike take da ita tun jiya da ake ta shagalin baki tana kallonta ta kwashi jiki ta shiga tana farin ciki ita kuma ta barta da kayan takaici makale cikin daki sai dai in mutuwa za tayi tayi kenan haka a shekaran jiya Huzaif ya zo suka kai ruwa rana akan bikin nan nasu akan haka yayi fushi uban komai bai bata ba kuma

duk Goggo Marka ce sanadi dan kayan ma da ake yi  cewa yayi ba zai yi ba ita kuma bata so ta hadashi da iyayensa saboda yanayin da suka nuna mata ba ta so ta nuna masu yanayin da suke ciki da ɗansu domin ɗa da iyaye Allah ne kawai ya san tsakanin su tana tsoron su canza mata da ga kulawar da suke bata.

“Me zaki fada min Goggo ai kin rigaya kin gama cuta ta ba abin da zan ce da ke sai Allah yayi mani sakayya ba wanda ya jefani cikin bala’in rayuwa sai ke ba wanda ya zaɓa min wannan kazamar rayuwar sai ke bani ga karatu gani da dan shege ga shi mijin aure ma wulakantani yake yi tun kafin naje gidan sa wannan UKU BALA’In da mai yayi kama ni dai na san na gama ASARAR RAYUWA a filin duniyar nan”.

Wani kuka ne ya kwace mata da sauri ta zame bayanta na kartar bango ta zube kan kafafuwanta wani kuka ne mai cin rai take yin sa amma idanuwanta kemadagas ba alamun hawaye runtse idanuwanta take yi tana  buɗe su so take yi kawai ta buɗe su ta ganta a wata duniyar ba wannan ba…

Sallamar da ake kwaɗawa tsakar gidan ya sanya su duban junansu jin ana ambatar Hafsat da sauri ta fice ta leka ganin tsirarun mutane yan biki suna ta kai kawo sai wasu mata biyu da suke tsaye wanda kallo daya zaka yi musu ka gane cikakkun masu ji da kan sune  gaɓadayan su sai wani yatsine fuska suke yi suna taunar cingam gaban Hafsat ne ya yanke ya fadi kafun ta juyo ta dubi Goggo da tayi fakare da idanu.

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri ta fice daga cikin dakin gabanta na cigaba da buguwa ta isa garesu dubanta sukayi tun daga kasa har sama kafun su watsar dayan ta ja tsaki gami da tsartar da yawu hakan ya jawo hankalin yan bikin da suka fara taru har da na dakin Umma duk sun fito.

“Kece Hafsat?”.

Babbar ciki ta tambayeta tana nunata da hannun hagu daga kai Hafsat tayi gabanta na kara tsinkewa ganin irin kallo da suke watsa mata a sa’ilin da ta tabbatar musu ita ce Hafsat din.

“Da farko dai ni sunana Assama’u yayar Huzaif wanda kike fata ya zama mijin ki ta ko wani irin hali sannan ina so in sanar sake cewa ki shirya zaman kunci da takaici a gidan sa sannan ki sani mu zuri’armu ba ‘yar iska sannan babu wacce tayi yawon ta zubar har ta samu kyautar tukuicin ɗan shege na gaba da fatiha wanda kika likawa kanina kika ce shine sanadin sa”.

Gabadaya mutanan gidan idanuwansu yayo waje don wasun su da yawa ba su san abin da ke faruwa ba abin ka da mata nan aka fara

kuskus ana duban Hafsat wacce ta gama sankarewa a tsaye gabadaya ta ji duniyar na juya mata kafafuwanta take ji suna lauye suna kokarin zubda ita kasa numfashi taja mai tafe da zafin zuciya duban su ta shiga yi daya bayan daya kallon da suke mata mai cike da tsana da kiyayya ya kara tsinka mata zuciya.

“Na san ba komai ba ne ya sanyaki makale masa har kika kunsa masa wannan sharrin saboda an ga gidan dala an ga gidan da jar miya ke kai kawo ba a saba lasa ba mai dattin hula ba ya kawo shine za a makalewa ɗan mutane to ki rubuta ki ajje bar ganin hajiya da Alhaji na goya miki baya to kisa ni ba da su za ki zauna  ba da ɗan su za ki zauna har ɓarin jiki kike karen ki ya kamo zomo to wallahi zaki ya kawo miki wanda zai zaɓa miki UƘUBAR RAYUWA a gareki”.

Dayar ta fadi tana watsowa mata ledar dake hannunta gabadaya kayan suka zube a jikinta daidai nan wasu hawaye na takaici suka surnano mata a saman kunci gabadaya ta kasa motsi jin komai take kamar a mafarki ba

gaske ba dafa kafaɗar ta taji anyi a hankali ta juyo Goggo Marka ce  tsaye ita ma idanuwanta na zubda hawaye duban matan tayi cikin jin haushi kafun ta hadiye wani abu da ya tokare mata zuciya.

“Rashin arzukin har ya kai haka ai ba karya akayi ba shi Huzaif din ai ya san shi ya lalata mata rayuwa don haka ya kamata ku gyara kalamanku sannan ku sani  ba a ‘yar iska daya dole sai an  samu dan iska…”.

“Tsohuwar alagidigo tsohuwar banza gayyar kwadayayyu kisan dai ba yarda za ayi namiji ya tursasa mace akan wani ra’ayi ko dole sai ta aminta abu ke tabbata don haka karki sake karki sake dorawa Huzaif kalmar dan iska domin wannan karuwar ‘yar taki ita ce silar komai”.

Gabadaya gidan ya dau salallami Umma dake tsaye bakin kofa idanuwanta sun kawo hawaye da sauri ta iso garesu ta shiga ba su hakuri da su tafi amma ina kamar kara ingiza su ake yi nan suƙa shiga hayaniya suna tsinewa Hafsat da Goggo Marka a cikin wannan yanayin Abulle tayi sallama ta shigo

hankalinta yayi matuka wajan tashi  ganin abin da ke faruwa da sauri ta isa ga Goggo Marka dake ta faman rusar kuka kamar ranta zai fi janye ta tayi ta kai ta daki kafun ta fito

idanuwanta itama sun kaɗa sun yi jajir ta dubi Hafsat ta watsar domin kuncin da take ji a ranta akan Hafsat ji take yi kamar ta hauta da bugu domin komai ya faru duk ita ta jawo musu.

Rigima ce ta balle sosai gidan biki ya hautsi ne sai da akayi da gaske bayan Umma ta kira Abban su Mariya ganin abin ya ki ci yaki cinyewa sannan komai ya lafa yan uwan su Huzaif suka fice Hafsat ta koma daki cike da takaicin wannan rayuwa da ta faɗa nan gidan biki lamari ya sauya nan da nan batun Hafsat ya zagaye ba abin

STORY CONTINUES BELOW

da ake tattaunarwa akai sai maganar cikin shege da tayi Abulle ganin abin ya girmama kasa zama tayi ba tare da kowa ya sani ba ta fice daga cikin gidan cike da ɗacin rai.

****

Sosai wajan ya tsaru tun da ga Get din in ka kalla zaka gane ba karamin waje bane aka kama domin shagalin bikin kamu na yau da za ayi tsaruwar ciki kuwa ba a magana ko ta ina haske

kwayaye ne ke walwali kamar a kasar turai ga wani daddaɗar kamshi mai sanyaya zuciya kawai ke tashi ga wani CoolMusic dake ta faman tashi yana kara jefa al’ummar dake wajan kara faɗawa kogin nishadi sosai wajan ya ƙawatu da kayan alatu na more

rayuwa ga wasu lafiyayyun kujeru za gaye da wani hadadden Table mai shimfiɗe da wani kayataccen yadi mai kalar Pink sai a tsakiyarsa an ajje wata fulawa mai kyalli da daukar idanu.

A daidai lokacin da jama’a suka gama hallara ana jiran amare su ido Mc sai faman zubda zance take yi da yake mace ce Khadeeja S Muhammad yarda ka kusan taci  bakin aku kawai nishaɗantar da mutane take yi ana ta dariya a wannan lokacin aka fara sanar da cewa amare sun iso a

hankali Mc ta sanya Dj ya canza kiɗa wani lafiyayya sauti ya shiga tashi ga duka na faman ratsa jikin yan biki nan suka shiga gyaɗa kai suna rausayawa hankalin su gabadaya ya koma kan kofar Hall din wani turirin kamshi ya shiga fesowa kawayen amarya guda biyu daga gaba suƙa shigo hannayensu dauke da kaskon turaren wuta suka shiga zagaye wajan da shi kafun cikin sakanni AMAREN BANA Mariya da Baseera suka sanyo kai cikin Hall din da yake hada bikin akayi waje daya.

Sanye suke cikin wani tsarren material Mariya ta saka Yellow colour ita kuma Baseera ta saka Light-Blue fuskokin su kawai zaka kalla ka gane suna cikin farin ciki da nishaɗi ratsantsiyar kwalliyar da akayi musu ta kara bayyanar da kyan su.

Mariya

2

Baseera

Nan da nan waje ya hargitse shewa kawai ake yi sauti na cigaba da tashi a cikin wannam yanayi har suka iso mazaunin su suka zauna sannan Mc ta bada umarni a tsayar da kiɗa nan ta shiga jawabin da abin da ya tara su a wajan kafun ta nemi daya daga

cikin yan biki ta zo ta buɗe taro da Addu’a Anty Yusra ce ta fito yayar Baseera tayi addu’o’i na neman yin taro lafiya a tashi lafiya sannan ta goɗewa duƙ wanda ya samu damar zuwa wannan bikin daga nan kuma lamari ya sauya a ka shiga biki gadan-gadan

Malam SANAH S MATAZU aka gayyata ta gwangwaje amare da wa’azi da duk wasu karin haske na zaman gidan miji da nuna masu hanyoyin na salo salo na kula da miji da yi masa biyayya sannan da hakuri da juriya da boye sirrin miji sannan da

girmama iyayen miji da yan uwansa da duk wani majibancin sa wa’azi sosai tayi musu mai ratsa zuciya da jiki  tsayi lokacin mai  nisa kafun daga bisa lamari ya sauya sosai da sosai  kamu ya ƙawatu sai son barka nan ka shiga ciye ciye da shaye shaye kafun wani lokaci kuma komai ya zama

daidai misalin karfe shida da rabi a ka tashi na yamma domin mazajen sun ce ba su yarda su kai dare a wajan ba ita kanta Mariya bata so yin taron ba bayar da za tayi ne Baseera son bidi’a gareta sannan ta samu goyan bayan su Dr.Karami.

Haka ko waccen su ta koma gida a gajiya Mariya gabadaya ta gama yin la’asar musamman in ta tuna gobe kamar yanzu ta jima da zama matar wani abin sosai take jin sa wani iri banbarakwai a cikin wannan daren sai da Umma ta kara kwantar mata da hankali sannan ta kara nuna mata

darajar aure da martabobinsa ga ‘ya mace sanna ta tunatar da ita fa’idar hakuri da juriya a gidan aure da duk wasu tsarurruka da yakamata ta bi domin dacewa da gidan aurenta sosai ta tsoratar da ita akan raina miji da dangin sa sosai ta nuna mata illar kin biyayya ga miji da duk wasu abubuwa da za su bata mata gidan aure ta.

Gyaɗa kai kawai Mariya take yi tana jin yarda zuciyarta ke kara tsinkewa da lamarin a wannan daren barci sai dai barawo ne ya yi yawon gaba da ita.

Yawwa yawwa  gamu mun iso wajan kamu ya kuka ga yanayin abin da fatan dai ban baku kunya ba kusan tsarin abin ba sosai na san yarda ake yin sa ba.

Amma fa nayi kokari ko ba haka

ba..lolx

Ya kuka ga amaren bana din dafatan dai sun yi kyau

????

About AIS

Check Also

UKU BALA’I CHAPTER 11

UKU BALA’I CHAPTER 11                    Www.bankinhausanovels.com.ng  Sosai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *