TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 2 BY AUFANA

TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 2 BY AUFANA

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tana isa tak’ara murtuk’e fuska cikin tsintsar masifa tace “hallooo gyaizz ina buk’atar kubani aron hankulanku α nan”  dasauri suka juyo suna kallonta tacigaba da tauna cwingom d’inta sannan tace “wane d’an rainin wayou ne yai parking yagaggiyar motarsa a inda nake parking motana” shuru sukai suna kallon juna hakan kuwa bak’aramin k’ara b’ata mata rai yaiya tak’ara jin haushi da takaici tasake cewa,,….+

“Waiko bakuji abunda nace bane” wanine can daga nesa yace “bawanda yai parking motarsa anan danma yau ko mota bamuzo da’ita ba watakil dai awaje ne” rantane yak’ara baci kamar tai kuka sai kawai tawuce fuuu kamar zata tashi sama,,,….

Tana fita sai yafito daga mab’oyarsa  suka tafa da wanda yai maganar ashe friend d’insane cosmate d’insane sannan suka kyalkyale da dariya ashe dik plan ne suka had’amata, MUJAHID yace “tin yanzu harkinfara b’ata rai kina damuwa tin wasan batai nisaba hhh don’t worry smolle baby wasan yanzu aka fara” abokinsa yai dariya sannan yace “nidai friend inajimaku tsoron kada wannan game d’in naku yajuye yakoma love saboda irin haka tasha faruwa wallahi daga k’arshe saikaga abun yasauya”  wani mugun kallo yamasa cikin b’acin rai yace,,,….

“haba Rayyan meyasa kakeman wannan muguwar fatar kai a tinaninka zan iya auren wannan yarinyar to idan ma kana tinanin haka kai gaggawar cire wannan tinanin daga zuciyarka dan ni wallahi ko soyayya bazan iyayi da itaba bare har na aureta” cikin b’acin rai yake maganar yana gama fad’ar haka yajuya cikin b’ata fuska yawuce, Rayyan kuwa dariya yai sannan yabi bayansa,,,….

Tana fita kai tsaye gunda suka saba had’uwa da k’awayenta tawuce, tinda tatinkarosu suka fahimci akwai damuwa a fuskarta tana isowa Nusy tai murmushi tabata hanu suka gaisa sannan tace “yadai feedom naga fuskarki kamar ba walwala what’s happened” glass d’in dake idanunta tacire sannan tace “nazo zanyi parking kawai sainatarar wani banza yazo yai parking a gunda nake parking d’in motana kuma inada tabbacin wannan sha sha shanne” cikin mamaki Amira tace “lallai kuwa akwai wata a k’asa kodai yana nufin yanzune yafara nasa game” Nusy tace “of course hakane yanzu yafara”  wani murmushin gefen lebe tai sannan tace “ku kwantarda hankalinku ladies idan yasan wata ai bai san wataba just follow me” tasaka glass d’inta tawuce suma sukabi bayanta,,,…

Gun masu aikin restaurant d’in school d’in taje tace su’aramata wuk’a ko karamace, dafarko k’in bata sukai saboda tsoro dakuma rashin sanin mezata aikata da’ita saida tamasu barazana sannan suka bata takarb’a tana murmushin gefen lebe, bayan takarb’o tafito tacimmasu a waje,,,….

Gun motar takoma saita durk’usa ahankali sannan tacafka wuk’ar a tayar motar nantake iskan tayar yadinga fita,, tana ganin haka tai murmushi suma k’awayen nata sukai dariya, saida iskan yakusa fita gaba d’aya sannan tamik’e tsaye tamayarda glass d’inta tace “so now ladies tinda mungama aikin saimuje class ko” tajuya sukabi bayanta suna takon k’asaita mai d’aukan hankalin mai kallo,,….

Har suka shiga class tanajin zuciyarta cike famm da farinciki sai wasa take jan su Nusy suna dariya, suna zaune har lecturer d’insu yashigo sunfara d’aukan lecture sai aka aiko kiran MUFIDA, gabantane yafad’i rass kan taji wanda ya’aiko kiran nata wani lecturer d’insu ne daya manne mata shi adole santa yake itakuma sai wasashi take kamar wuk’a tana jansa kamar rak’umi da akala,,….

Wannan farinjinin nata shine yakesakata take k’ara jin girmankai saboda har PC d’in school d’in sonta yake kasancewar musulmi ne kuma Allah yajarabceshi da son mata idan yaga mace kamar yadamkota yakeji, hakama sauran lecturers da dama sun nuna suna sonta dakuma wasu students saboda MUFIDA macece mai sha’awa tanada k’irar mata sosai bayan kyanda take dashi gakuma farinjini wanda shine yakemata rumfa,,….

Wannan damarce take amfani da’ita wajen yin abunda takeso kuma taga dama acikin school d’in saboda taga tanada opportunity, saidai MUFIDA tanada kamun kai bata yarda ta sakemasu fuskaba hakan yasa wasunsu dole suke cemata aurenta sukeso suyi kad’an ne suke nunamata life kawai sukeso suyi da’ita daka fad’a mata kuwa anan take zata cimaka mutunci ta yayyagamaka rigar arziki sannan tahad’aka da PC ko hamma faruk suci ubanka kuma akoreka daga School,,,….

Ahankali tamik’e tsaye tafita cikin tsintsar b’acin rai tasha kunu ta tamke fuska, kai tsaye tashiga office d’insa tana shiga ta taddashi zaune akan kujerarsa cikin masifa tafara masa magana “haba Mr adam wannan wane irin wulak’anci ne nagayamaka kada ka k’ara kirana idan muna lecture wallahi banasan haka natsani haka karatunnan fa danshine nazo k’asar nan dan nayisane nazo School dinnan so why kake takurawa rayuwata plss and plss narok’eka ka kyaleni kafita daga harkana if not kuma wallahi yanda nasa akayiwa mr abbas kaima zansaka amaka haka” kallonta yake harta gama abunda takeyi, tana gamawa batajira komaiba tafita abunta fuu kamar zata tashi sama,,,…

Class takoma tacigaba da d’aukan lecture, yau 4pm suka tashi koda suka fito tanajin yunwa sosai danhaka suka wuce wani restaurant dake cikin School d’in domin suci abinci,,,….

Bayan sungama ci suka wuce wajen shan iska dake kusa da restaurant d’in, suna zaune sai Nusy tahango MUJAHID yanata fama da motarsa yana k’ok’arin yatadata, dasauri ta tabo MUFIDA tanunamata shi tana dariya itama dariyar ta kyalkyale da’ita har tana rik’e cikinta,,,…

Tashi sukai sukaje kusa dashi MUFIDA na kyalkyala dariya tacemasa “eyyah Allah sarki sannu mr man Nusy kozaki taimakasa da k’udi ne kokuma ki aramasa motanki yaje gida kar amasa fad’a baikoma da wuriba” itakuma Nusy tace “a,a nikam feedom miye had’in kifi da kaska kumama ni ai kinsan bancikasan bama kowa aron motana ba bankuma cika d’aukan kowa a motana ba barekuma kazamin talaka kamar wannan” tana fad’ar haka suka kyalkyale da dariya suka tafa shidai kallonsu kawai yake yana murmushi saboda yama rasa mezai cemasu,,…

Juyawa sukai suka wuce sunata dariya, suna wucewa yafiddo wayarsa yai dialing nmbr na mubashir ringing d’aya yad’aga cikin sauri tareda fad’in “Allah yak’ara maka nasara ur Highness”  cikin isa da k’asaita yace “kad’akko man wata mota ka kawoman sannan kazo da mai gyaran mota a d’auki wannan ta lallace” cikin girmamawa yace “angama ur Highness”,,,….

Baifi 30mnts dayin wayarba saikuwa gashi yazo dawata dank’areriyar mota sabuwa gall yakarb’i key yashiga yabarshi atare da masu gyaran motar idan an gyara shi zaitafi da’ita,,,…

Kai tsaye gidansa yanufa yana isa yai parking yafito sannan yawuce ciki, wani dank’areren parlor ne naga yashiga ciki yakunna fitilu sannan yazauna akan kujera 2seater ya kwantarda kansa akan hanun kujerar, ransa yakejin yana masa suya yarasa wane hukunci zaiyiwa yarinyar nan saboda shifa a ganinsa batafa isheshi fad’a ba amma yaga tana k’ok’arin ta rainasa saboda haka dolene yad’auki mataki akanta dolene yamata hukuncinda ko sunansa taji saita tsorata bare kuma taga fuskarsa,,,….

Haka yaita tinanin irin hukuncinda zai mata daga k’arshe yatashi yashiga kitchen yad’akko girkinda mubashir yamasa sannan yadawo parlor yazauna,,,….

Zama yai yafara cin abincin yanaci yana tinanin MUFIDA rashin tsoro irin nata da tsiwa irin tata, mamakinta yake sosai saboda baitab’a ganin mace k’aramar yarinya mai irin shekarunta tana irin abunda takeba, yamatuk’ar mamaki rana ta farko data d’aga hanu tamaresa abunda ko amafarki baitab’a tinanin wata y’a mace zata iya masaba,,….

Shi yakasance namiji miskili sosai bamai yawan magana ba hatta k’anensa tsoronsa suke mahaifiyarsa kullum cikin yimasa fad’a take akan miskilancinsa wasu har cewa suke wai mugun raine dashi ko dariya bayayi gashi kuma baya d’aukan raini agun kowa k’anensa dasun masa laifi yake bulalesu hakan yasa suke mugun tsoronsa amma wai yau shine wannan k’aramar yarinyar takeyiwa haka kuma batareda ya hukuntataba to wai meyasa haka ne why….? yatambayi kansa,,,…

Da wannan tinanin yagama cin abincin sannan yawuce bedroom d’insa, kayansa yacire yawuce bathroom yai wanka sannan yafito yasauya kaya,,,….

A b’angarenta kuwa suna wucewa suka shiga motocinsu suka wuce izuwa gida saboda yau agajiye suke bazasu fita yawoba gakuma exam data matso saboda haka yanzu dole surage yawo sufara karatu……

Daisarsu kai tsaye tawuce bedroom tacire kayanta tawuce bathroom domin yin wanka, bayan tai wanka sannan tadaura alwala tad’auro towel tafito,,,…+
Mai tashafa sannan tasaka tirarukanta masu dad’in k’amshi, bayana tagama sannan tasaka wata doguwar jallabiya bak’a tareda hijab tashimfid’a sallaya takabbarta sallar magrib, bayan tagama bata tashiba tad’akko Qur’an tafara karanta suratul kwasas,,…
Saida lokacin sallar isha yai sannan tarufe Qur’an ta tashi takabbara sallar isha, bayan tai sallar isha sannan tai shafa’i da witiri tasallame, bayan tagama sannan ta tashi tacire kayan jikinta tad’akko kayan bacci tasaka tafita parlor,,,….
Koda tafita ta tadda mubina da munira suna kallon TV kitchen tawuce tadibo abinci sannan tadawo parlor tazuna tafara ci, sunjima sosai a parlor suna kallo daga bisani itadai MUFIDA tawuce d’aki tad’akko littafanta tafara karatu kasancewar dama al’adartace matuk’ar zasu fara exam tofa batawani baccin kirki, sai kusan 4am sannan ta kwanta,,,….
Washe gari tin 6am suka farka nan sukai sallar asuba sannan suka fara shirin zuwa school, yauma kamar jiya tariga kowa fita kasancewar mubina ce zata had’a break kuma tasan halinta sarai agun cin break d’in idan batai a hankaliba saisubata lokaci suna masifa shiyasa kawai tafice abunta,,….
Tana isa school kai tsaye tawuce gunda take parking taje tai parking tayi zaton yauma zata cimma motarsa amma saitaga akasin hakan aikwa nan taita dariya, bayan tai parking sannan tafito tareda saka glass d’inta cikin wani irin salo tarufe motarta sannan tafara tafiya cikin salo da kwarewa tamkar maijin tausayi k’asa tana tafiya ahankali,,….
Kai tsaye restaurant tawuce tai break sannan tawuce gunda suke had’uwa dasu Nusy, tana isa suka gaisa sannan suka wuce gun shan iska saboda zasufijin dad’in karatu acan,,….
Zaune suke akan wata bishiya dake cikin wajen shan iskar kamar nacewa Nusy tajuya tana juyawa kuwa saitahango MUJAHID yai parking motarsa yafito yana tafiya izuwa cikin School, dasauri ta tabo MUFIDA tanunamatashi tana dariya itama dariyar ta kyalkyale da’ita suna dariya suna tsokanarsa,,,….
Itadai Amira kallonsu kawai take saboda dama dik abunda suke batasaka kanta sosai aciki, murmushi tai takalli MUFIDA tace “hmm wallahi MUFIDA inajiyemaki tsoron wani abu akan wannan abun dakike aikatawa mutuminnan”  wani mugun kallo tamata hakama Nusy,MUFIDA tace “mekike nufi kenan Amira…?” tai maganar cikin tambaya sai Amira tai murmushi sannan tace,,…
“wallahi ina jiyemaki tsoron kar wannan game d’in dakukeyi tajuye wato reshe yajuye da mujiya ma’ana wasar tasauya salo” wani kallo tamata na kinma rainani wallahi ashekeke Nusy tace “wannan yana d’aya daga cikin abunda yasa bancika fad’amaki damuwata ba saboda wallahi Amira kinada matsala to bakinki yasari d’anyen kashi wallahi me MUFIDA zatayi da wannan k’azamin yaron itada manyan gyaiz kebinta bata kulasuba taya zata b’ata lokacinta ga wannan yaron”,,,….
MUFIDA kuwa nantake yanayin fuskarta yasauya idanuwanta sukai ja saboda b’acin ran abunda Amira tafad’a, cikin tsintsar bacin rai tace “haba Amira wannan wace irin muguwar fatace kikeman amatsayinki na aminiyata, bantab’a tinanin haka daga garekiba amma bakomai nagode sosai saidai ina rok’on Allah daya tsareni yakuma kareni daga sharrin mugun bakinki”  tana gama fad’ar haka tamik’e tsaye tawuce abunta fuuu nan itama Nusy ta tashi tana hararan Amira tabi bayan MUFIDA,, murmushi Amira tai afili tace “insha Allah wata rana saikin tina da abunda nafad’a maki kince tabbas nafad’i gaskiya” anan tacigaba da zama tana karatunta tasharesu,,,…..
STORY CONTINUES BELOW
         Yau kimanin kwana biyu kenan MUFIDA bata sake ganin MUJAHID ba acikin School, yaudai tace bara ta zaga school d’in kozata gansa amma hartai iya yawonta batagansaba nantake saitaji ba dad’i kwana biyun nan dabasuyi rigimaba, haka tawuce class tacimmasu Nusy acan,,,…..
Shikuwa ashe sunfara exam ne nakammala degree shiyasa yanzu bashida zama bashida hutu any time yana karatu saboda yanda sukeshan wuya sosai agun malaman dama hausawa sunce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi to hakane,, yaso yaso yasami lokaci d’aya yaladabtarda MUFIDA amma ina bahali karatu yahana, haka dole yahak’ura yacigaba da karatunsa yanzuma bakoda yaushe yake shigowa school d’inba sai lokacin shiga exam yayi sannan yake shigowa kuma dasun gama bayawani dad’ewa yake wucewa to wannan dalilinne yasaka MUFIDA tadaina ganinsa suka daina rigima,, su kansu y’an school d’in harsunsansu kwana biyun nan dabasugansu suna rigimaba diksai sukaji wani iri,,,…..
Yau takasance Wednesday bayan sunfito daga exam saitabisu Amira gidansu gaba d’aya saisuka wuce gidan Amira, wanka suka sannan sukai sallar magrib suna gamawa suka haye gado saboda dik jikinsu ciwo yake, MUFIDA ce tadubesu tace “friends wai 2 day’s nadaina ganin mr man a school bansan meyasa yadaina zuwaba gashi kuma suma sunfara exam sunma rigamu farawa saboda su sune y’an final year” Nusy tace “eh wallahi nima 2 day’s nadaina ganinsa aikuwa munyi missing game d’inku wallahi sosai har y’an class naji suna fad’in 2days baku buga game ba” murmushi tai batareda tasake cewa komaiba,,,….
Amira dariya tai sannan tace “hmm mudaije zuwa ai garin ba nisa hausawa sukace iya gani iya kyalewa” tana fad’ar haka tamik’e tafita tana y’ar waka,, tsaki Nusy tai saboda tafahinci abunda take nufi itakuwa gogar sam batama fahimci inda zancemta yadosa ba,,,….
Girki Amira tamasu mai shegen dad’i suna zaune a parlor sunaci MUFIDA takalli Nusy tace “inama mr man zai samu irin wannan garar natabbta dasai taune harshensa saboda nasan baitab’a cin irin saba watakil daga kuka sai kwabe akasaba ci agida” Nusy kyakyalewa tai da dariya tace “kai feedom wallahi bakida dama” tabata hanu suka tafa itada Amira kallonsu kawai take batace dasu k’ala ba har suka gama takwashe kayan takai kitchen tawanke sannan tadawo tad’auki notebook d’inta tafara karatu,,,….
Suma karatun suke amma time by time dik sun tsokani MUJAHID suyita kyalkyala dariya, dahaka har lokacin baccinsu yai suka wuce bedroom suka kwanta,,,….
Zaune suka acikin wani d’aki akan wani gado mai haske sosai, da gadon da d’akin dik haskene dasu sosai tamkar hasken farinwata acikin sararin samaniya, suma kayan dake jikinsu fararene sosai, kwance take akan cinyoyinsa yana shafa kanta cikin fara’ah,,,….
D’agowa tai tana murmushi tace “mr man dan inaso kaman wani alk’awari” murmushi yai tareda shafa fuskarta cikin k’auna yace “wanne alk’awarine smolle baby fad’a yanzu namaki shi” matsowa tai dab dashi tad’ora kanta akan shoulder d’insa sannan tace cikin wata iriyar murya mai taushi,,….
“inaso dan Allah kaman alk’awarin bazaka tab’a barinaba har abada”  murmushi yai harya bud’e baki zaiyi magana saigawasu mutane sunzo cikin fararen kaya suka janyeta daga jikinsa sannan suka daukesa suka wuce, kiran sunanta yake MUFIDA MUFIDA yana mik’o hanunsa alamar tazo itama tana kiran sunansa MUJAHID MUJAHID cikin murya mai karfi tana mik’a hanunta alamar kar yabarta, dahaka akacigaba da tafiya dashi har suka bace tabar hangosu,,….
Tana waigawa bayanta saikuma taga fuskarsa tadak’arfi tafarka tareda kiran sunansa cikin murya mai sauti, “MUJAHIIIIIID…..!!!” dak’arfi suma suka farka a firgice saisuka ganta a zaune tai zufa jikinta sai rawa yake, tana ganin sun farka saita rungume Amira tareda fashewa da kuka,,,….
Addu’oi Amira tadinga tofamata har tad’an yi shuru jikinta yadaina karkarwa sannan tajanyota tasharemata zufanda yake zuba a fuskarta sannan tarik’ata suka koma suka kwanta saidai bacci k’auracemasu yai kowannensu da abunda yake sakawa acikin zuciyarsa,,,….
Azuciyar Nusy cike take da mamaki to me hakan yake nufi MUFIDA tai mafarkin MUJAHID lallai kuwa akwai jan aiki agabansu,, Amira kuwa batawani yi mamakiba saboda dama tasan hakan zata iya faruwa saboda Amira tafisu shekaru hakan yasa dole tafisu sanin me duniya take ciki,,,…
MUFIDA kuwa har safiya ta waye batasake yin bacci ba zuciyarta sai sake sake take mata akan abunda tagani acikin mafarkinta kaddai abunda Amira tafad’a ne yake nema yazama gaskiya kai ina hakan bazai tab’a yiwuwaba wallahi dole tai gaggawar kawarda wannan zancen daga zuciyarta, dahaka har asuba tai suka tashi domin yin sallah suyi shirin fita school,,,….
Sallah sukayi sannan suka shiga kitchen suka had’a breakfast sannan suka fito, bayan sunyi break sannan suka koma ciki sukai wanka suka shirya sannan suka fito izuwa school,, har suka fito ba wanda yayi maganar abunda yafaru jiya saboda daga Amira har Nusy tsoron suke suyi maganar kada MUFIDA tanemi ta had’iyesu saboda sunsan halinta,,,….
Har suka iso School tai parking bawani mai mostin kirki acikinsu musamman ita gogar datakejin jikinta dik ba dad’i kasala ga danga diksun mata yawa aciki,,,….
Yauma haka tawuni tana raba idanu kozata hango MUJAHID amma shuru ko motarsa bata hangoba bare shi, harsukagama zana exam suka fito suka wuce bata gansaba saitaji dik ba dad’i a kwana biyun nan dabata gansa sukayi rigima ba, haka suka wuce gida batada wani kuzari sosai………
Zaune yake ak’asa cikin makeken parlon sa ga tarin litattafai agabansa yad’aga kansa sama yad’ora hanunsa d’aya akansa d’aya kuma akan hanun kujera,,…+
Rigimarda suke da MUFIDA ce yake tinawa itace take dawomasa tana masa yawo acikin kwakwalwa, d’ank’aramin bakinta yake hangowa yanda take tujayasa tana masa masifa,, wani k’ayataccen murmushi yai yace “hmm smole baby kenan”,,….
Cigaba yake da tino dik irin rigimarda sukai tin ranarda ta maresa har ranar k’arshe data fasa masa taya tad’auka baisan itace tayiba, yai zurfi sosai acikin tinanin har yakaiga baisan shigowar Rayyan da mubashir ba saida Rayyan yadafasa sannan yai firgigit yadawo hayyacinsa,,,….
Rayyan yace “haba Prince mekake tinani haka sai zuba sallama muke tin a k’ofar shigowa har muka iso kusa dakai amma dik bakajiba ka lula cikin tinani kai zurfi”  murmushi kawai yai yashafa lallausar sumarsa”  zama sukai sannan suka gaisa MUJAHID yakalli mubashir yace “muby inafatar ka kammala aikinka gaba d’aya”  cikin girmamawa yace “eh nakammala ur Highness ga komai a rubuce cikin wannan file d’in cikakken sunanta dakuma address d’insu da garinsu” karb’an file d’in yai yaduba sannan yad’ago yace “good aikinka yayi kyau zaka iya tafiya” nan yatashi yafita,,,….
Fira suka fara a hankali shi da Rayyan suna cikin firar sai rayyan yadubesa yace “wai Prince shuru nadaina ganin mutuniyarka kundaina buga game” murmushi yai yace “ai ita tagama nata wasan yanzu nawa time ne yafara saidai kasan yanayin karatunmu naso naso wallahi na ladabtarda yarinyar nan nakoya mata hankali sadai exam tahana saidai nayiwa kaina wani alk’awari wanda nikad’ai nabarwa kaina shi” murmushi kawai rayyan yai sanna yace “gaskiya nidai naso naga k’arshen wannan game d’in naku amma nasan bazan ganiba tinda dika dika kwana nawa yarage muyi bankwana da juna, sadai ina rok’on Allah yasa wannan game d’in naku tasauya salo takoma love dan wallahi kun matuk’ar dacewa da juna Prince har kamanninku ma d’aya yanda halayyarka take itama haka tata take miskilanci dakuma jiji da kai sadai ita tafika jiji da kan zaku matuk’ar yin marching idan kuka zama masoya”,,,….
Tinda yafara maganar MUJAHID kemasa wani mugun kallo har yagama, bayan yagama yakallesa yace “kagama” murmushi kawai yai sai yace “to malam plss idan kagama kafita kabarman gida tin kan nasaka afitar dakai yanzu yanzinnan”  yai maganar cikin tsintsar bacin rai fuskarsa ba alamun wasa, ganin haka kuma rayyan yasan halinsa sarai hakan yasa yatashi yana murmushi yace “Allah yabaka hak’uri yarima mai jiran gado nidai nasan gaskiya nafad’a kuma inarokon Allah yasa maganata ta tabbata tazama gaskiya” binsa yai da gudu shima yafita dagudu yana kyalkyala dariya yashiga motarsa yawuce shikuma yadawo ciki yana huci kamar kumurcin maciji yana zara idanuwansa,,,….
             *****  *****
Kwance take akan makeken gadonta tai shuu itakad’ai ga tarin littafai agabanta tarasa meke mata dad’i a duniya dik inda tajuya fuskarsa take gani tanamata gezau acikin idanu, tashi tai a zaune tai tagumi tana mamakin abunda ke shirin faruwa da’ita, acikin zuciyarta tace “to wai meke shirin faruwa danine ohh ni MUFIDA kardai maganar Amira ce keshirin zama gaskiya agareni son mr. Man kenan zuciyata keyi hmm tabbas inkuwa hakane ina cikin babbar matsala da tashin hankali”,,,…
Can kuma sai taji tsintsar tsanarda tamasa ta taso mata acikin zuciya sai tace cikin tsananin b’acin rai “kai noo wallahi bazai tab’a yiwuwaba hakan bazata tab’a kasancewa ba natsaneshi wallahi zuciyata k’arya kike bazan tab’a barin wannan abun ya zama gaskiya ba” haka taita surutai itakad’ai harta gaji takwanta bacci b’arawa batasan lokacinda yai awon gaba da’ita ba,,,….
Washe gari haka taje school jikinta dik ba walwala dik inda sukaje sai dube dube take kozata hango MUJAHID amma harsuka dawo ko walk’iyarsa bazata ganiba, hakan kuwa bak’arin k’ara sakata acikin damuwa yakeba gashi batada damar ta tambeyasa saboda aganinta hakan zubda girmanta ne da ajinta aji ita da kanta tana nemansa bayan irin cin mutunci da bala’i da musifarda tadinga masa kai ina hakan bazata tab’a kasancewa ba, hmm nikwa nace yo ina ruwan so dawani class hhh Lol,,…..
Haka tawuni a school d’in amma bataga walk’iyarsa ba har suka koma gida,, su kansu mubina da munira sunga sauyi sosai ga MUFIDA a yanzu takoma tamkar wacca batada lfy idan tana tafiya kamar wacca kwai yafashewa a ciki gashi dama tafiyar ta yanga ce bare kuma yanzu, a school ma idan sunje batayin kamar yanda takeyi a da yanda take hura hanci tana d’aga kai sama kamar wata y’ar shugaban k’asa dik tadaina yanzu daga class sai restaurant sai gun hutawa saikuma gida, saidai basuda halin tambayarta abunda ke damunta saboda sanin halinta,,,….
               *****  *****  *****
Kwance yake akan gadonsa yai shuu,kyakkywar fuskarta yake tinowa da d’an k’aramin bakinta yanda take juyasa idan tana rashin mutunci ji yai kamar ace tana kusa dashi yakame bakin yatsotse shi saima a yanzu yake mamakin kansa dakuma jin haushin kansa dabai damk’eta yamannata da k’irjinsa yatsotse bakin nata datake rashin mutunci da rashin kunyaba dashiba, afili yace “amma bakomai yanzuma bata b’aciba akwai sauran lokaci ai”,,,….
Rayyan ne yafito daga wanka saiyajiyosa yana magana kamar acikin mafarki, tsaye yai yana kallon ikon Allah a ransa yace “yarinyar nan tana nema tazautar man da friend sai maganarta yake shikad’ai kodai yatsunduma ne wai hhh” yai dariya yace “mujedai zuwa ai garin ba nisa sannu a hankali zaka gasgata maganata”,,,….
Matsowa yai kusa dashi yadafasa saiyai firgigit yadawo hayyacinsa sannan yasauke numfashi “hmm wai Prince meke damunkane kwana biyun nan nalura dik bakacikin hayyacinka nalura kwana biyun nan dik so so silent kake plss tell me what’s rong with u” shuru yamasa can kuma saiya tashi yashige toilet batareda yace dashi uffan ba, murmushi rayyan yai saboda inda sabo yasaba da halin MUJAHID wannan bazai damesaba nan yacigaba da abunda yake yakyalesa tinda bayasan yafad’a masa damuwarsa idan tai wari yaji,,,…
             
              *****  *****
Abun duniya yataru yayiwa MUFIDA yawa tarasa ina zata saka kanta taji sanyi, a yanzu kam ta yarda da abunda zuciyarta take fad’a mata ta tabbar da zuciyarta tagama cika da tsintsar k’aunar MUJAHID saidai ita kanta tasan wannan babban al’amarin da zuciyarta ta rarumomata bak’aramin al’amari bane kuma tasan dole tafuskanci k’alubale akansa,,,…
Zaune suke acikin wajen hutawa dake cikin school d’insu tai shuu talula acikin zurfin tinaninsa, Amira da Nusy sai shan firarsu suke amma itakam tai shuu tana ware dara daran idanuwanta tana kallo masu shigowa da masu fita acikin school d’in,,,….
Tinda suka zauna Amira takula da yanayinda MUFIDA take ciki saidai tashareta takyaleta,, tana cikin dube dube kamar ance ta waiga a gefenta na dama tana waigawa kuwa sai tai tozali da kyakkywar fuskarsa acikin wata dalleliyar mota dake shigowa cikin School d’in,,,…
Dasauri tamik’e tsaye tawashe fararan hak’oranta tana dariya fuskarta d’auke da tsintsar farinciki, mamakine ya bayyana tsintsarsa a fuskokinsu ganin yanda tai kamar zautatta, gunda take kallo suma suka juya domin ganin abunda take kallo…….
Ance ina shagwab’aku sosai ? saboda haka yanzukam nadaina maku 2pages kullum kuyi manage da wannan

About AIS

Check Also

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV Www.bankinhausanovels.com.ng  Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *