TAWA TA SAMENI CHAPTER 33 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 33 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

nawa duk suna gurin wanki, kuma ki daina kuka haka

bana son ganin fararen idanuwanki sun koma ja kinji?

nace to na dakko mishi sallaya sabuwa na tuno duk

juma’a in Allah zai je masallaci ya kan shigo dakin

mama ita kuma sai ta dauki turare ta fesa mishi gami

da mishi rakiya bakin kofa nan nima na dauki turare na

fesa mashi yace nagode na mika mashi sallayar ya amsa na biyo shi har bakin kofa ya juyo me

zan roka

maki?na juya baya don kunya nace ‘ya’ya na gari naji

yayi jim bai ce komai ba na juya sai ya kago murmushi

yace har da kishiya ko?na daure fuska nace a’a yay!

murmushi to sai na dawo.

Kafin ya dawo na hada mishi salat, nayi salla na sake

wata kwalliyar da pakistan irin na India sky blue sun

zauna tsam na zuba yan kunne da abin hannu tamkar

ba Indiya yan kudancinsu marasa fari sosai ina jin

tsayuwar mota na leka ta window dina su uku ne da

sauri na daure gashi na tsam da ribo mai kalar kayan

gashina ya sauka abaya ina isowa falona shima yana
shigowa ya dubeni a ranshi yace yarinyar nan zata

kasheni da salon gayunta ya jawoni jikinshi kin fi dazu Www.bankinhausanovels.com.ng

kyau nace na gode yace zamu samu abincin mutum

uku?nace sosai ma yace yauwa ‘yar albarka a kawo

mana ya fita na kai musu na koma na kawo masu

drinks sannan na gaidasu, dayan Bello ne biyun kuma

ban sansu ba yace shiga ciki ki kirawo Mimi kice tazo

da dady ga bakina nace to na shiga na zata Haj tana

nan ashe ta tafi na gaya mata na fito na koma daki,da

zasu tafi yai min text wai nazo zasu tafi amma na rufe

mishi gashina su daina ganin mashi, nayi murmushi

gyalen kayan na warware na rufo muka yi sallama,ya

tafi raka su,ya dawo ya sameni inna ma babana waya, Www.bankinhausanovels.com.ng

ya jawoni jikinshi nace ma babana baba ina son kudi

yace nawa?nace ko nawa ne ka bani na gode yace to
direbana zai kawo maki ina mijin naki na juya na

dubeshi da zan ce ga shi nan sai na ga ya sha mur sai

nace baya nan to in ya dawo ki gaishe shi nace to sai

anjima na gode cikin fargaba na dube shi ya mike zai

fita na ruko shi yaynmu menene?harara ya sakar min

da sauri na sakeshi ya fita na koma na zauna nace to

mena mishi haka na cigaba da zama sukuku .Karfe

hudu ina kicin, tuwon shinkafa da miyar agushi nayi sai

kaza dana gasa,kunun aya da dabino da na amfani na

sannan na kaima Anty Mimi da mai gadi nasu sauran

na kwashe na tafi dashi kicin din dakina sai da na yl
Www.bankinhausanovels.com.ng
wanka sannan na yi sallar magriba ina zaune har akayi

Isha’i na idar siket na sa na Jeans da yar riga mai

hannun singleti ta dameni sosai na canja salon fakin

din gashina na zauna a falona cikin fargaba, takwas da
rabi ya shigo da sallama ciki ciki ya zauna na dubeshi

har ynxu fuskarshi a daure take na daure nace sanu da

zuwa, bai amsa ba na shirya mishi abinci a gabanshi

yace in kwashe ya koshi na sa hannu na dafa kirjina na

tsura mishi ido a raina nace to wai shi wannan wane

irin mutumi ne? ya dubeni kwashe nace,na matsar da

kayan gefe naje na durkusa a gabanshi bisa gwiwoyina Www.bankinhausanovels.com.ng

nace yayanmu don Allah sanar dani abinda nayi maka

tun kafin ubangijina ya soma fushi dani wilh ba zan

sake ba pls!ya dubeni fuska tamke me yasa kika ce

babani ya baki kudi? me yasa ba zaki tambaye ni ba?

menene wanda kike so ba zan iya miki ba gaya min?

nace ok daman wannan ne? to dan Allah kayi hakuri

dama ba wai zanyi wani abu da kudin bane saboda

kawayenmu na makaranta da suke zuwa shi yasa ina

son na dan ringa basu na mota kuma Babana yace kar

na tambaye ka kudi na tambayeshi, to amma kayi

hakuri ba zan sake ba kaji?na kawo maka abincin?kaji

don Allah um ni ya zuba min ido yana kallona na kifta

idona na baka a baki?na fada ina dubanshi ya harareni

na runtse idona sai hawaye na tashi zan shige bedroom

ya jawoni jikinshi to na hakura yi shiru kinga zaki bata Www.bankinhausanovels.com.ng

min kwalliya baki bari nace kinyi kyau ba, nayi lamo

kan jikinsa yayi mani magana cikin kunne tashi ki bani

abinci my Dear tashi,na tashi nayi ina yar shgwaba ta

na soma bashi abinci yana ci bayan ya gama ne muka

tarkata sai master bedroom kai yaynmu karshene ya

iya soyayya mai ban mamaki daran ranar ya min

abubuwan da na san yes ni mace ce kauna zalla mai

tsayawa a ral. Washe gari sai ga Haj Yaya ta kuma zuwa

lokacin ma

baya gida tana ta masifa har ya dawo tace su tattara

su koma England tunda yace jira yake ta haihu ai ta

haihun yace Haj kinga dan bai yi kwari ba don Allah ki

bari ko wata yayi tace yayi acan dole suka bari akan

sati maizuwa zasu tafi wannan satin dai mun kwashe

shi ne cikin soyewa,bana manta ranar lahadi ana gobe

zasu tafi ba kowa sai ni kadai yaynmu ya tafi ya kai

Anty Mimi gidansu sallama ina zaune a falona abin duk
Www.bankinhausanovels.com.ng
yabi ya dameni yanzu in yaynmu ya tafi shikenan ko

sai yaushe zai dawo oho?banji shigowar mutum ba sai

ji nayi an kama min gashi ta baya zan yi ihu sai naji

yaynmu yace ke sarkin tsoro ni ne tunanin me kikeyi ne

ban rufe ba nace tunaninka mana in ka tafi ko sai

yaushe oho?ya zauna zanzo da zarar na samu sukuni

tunda na dade,nasan zan dan kwana biu dama
sun

dameni da waya karki damu mun gama magana da Alhj

gobe Haj Maska zata zo sai ki gyara mata dakin kusa

da kicin ko,nayi shiru duk ya damu na kula so yake

yaga na daina damuwa ya jawoni yana min wata

magana cikin kunne na mike nace a’a yace ni ko?nace

eh ya kai hannu zai kamo ni na ruga ya biyo ni muna ta

zagaya kujerun babban falon na gaji inata dariya na

fada kan doguwar kujera ya zauna a jikina nace wayyo

zaka kasheni yace to kin yarda?nace na yarda pls ya

dagani ya dorani a jikinshi hannuwanshi yasa ya balle

maballin gaban rigata ya sa baki yana aikin….kungane Www.bankinhausanovels.com.ng

dai,na kuma kwacewa zan gudu yace pls kinga daga

yau bana nan zanyi missing dinshi nace to sai ka

goyani yayi dariya yace to zo hau ya duka na dane ya

sulmiyoni ya kwantar kan kafet ya cire min
rigar gaba daya ya soma sarrafa albarkatun kirjina shi dai yana

son wannan abu daran ranar mun raya shi kan gobe

zasu tafi..

Washe gari sai da hankalinshi ya tashi ganin yanda duk

na tada hankalina ynxu iman in kina wannan kukan kike

son na tafi?ko ban fada miki ba kinsan kina da matsayi Www.bankinhausanovels.com.ng

mai girma a gurina karki damu wata rana dake zamu

tafi sannan ga waya ko yaushe zakijini ki dai kular min

da kanki shi ne nafi so ina share hawaye nace shi

kenan,ni na hada mishi kaya suka fito har gurin mota

na raka su,Anty Mimi sai wani jin kai takeyi,ta shiga

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  haka tukunna ina …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *