TAWA TA SAMENI CHAPTER 29 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 29 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

 Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya

Bamu shiga cikin gidan ba da yake su Baba suna can gidan mamana gidan babana muka koma a gurguje kafin motar daukar amarya tazo suka kuma min wani gyaran na dubi Amira da Mami nace ina wayata suka ce tana gurin Saudat suka kirata ta kawo min na kunna ta ina
budeta text ne ya fara shigowa na bude shi naga ansa “dama nace miki i am always lucky gashi kuma.. kaina

ya daure nace me kenan sai naja tsaki na soma del din text dinshi nace koma wanene ya karata can har yana cewa baga shi nan ba yana nufin shi aka aura min?me karya ina ma su Baba suka wani sanshi,su Mami suka ce ke da wa kike wannan fadan?na dan kishingida nace um Amira tace kinsan mijinki kuwa?da sauri na tashi zaune nace wanene Mami tace itama fa bata sani ba Amiran,nace um ni ko wanene ma na hakura zan zauna dashi tun da rufa mini asiri ma yayi bayan an kini kuma shima wanda ya kini din dama bashi zuciyata take so ba na rasa wanda nake son ma na hakura bare Adams? sai naga Amira da Mami sunyi dariya nace in ma kun sanshi baku son ku gaya min ai zan ganshi ne,suka ce har ma ku zauna har abada,muna cikin haka Anty Maijidda ta shigo tace Babana yana san ganina ina Www.bankinhausanovels.com.ng
zaune gabanshi yana mini nasiha gami da nuna min
nayi biyayya nayi koyi da hali irin na uwata sannan
yace yaji dadin mijin da Alhj ya zaba min domin shi
kansa lokacin da ya ganshi ya so ace ya kasance
mijina,na soma kuka yace na daina kuka duk abinda
nake bukata kar na zama mai rokon mijina na mishi
waya zai bani kamar na tambayeshi wanene mijin sai
naji kunya nayi shiru mamakin da naji shine ganin
abokan yaynmu sune dai suka zo daukar Amarya,a
motar Isma’il aka daukeni a raina nace to ni Iman me
ya kawo yaynmu kai amarya kuma?to ko dai Adams din ne tsokanata sukeyi?wa zan samu ya amsa min
wadannan tambayoyi?ina cikin tunani har muka iso
gidan,Anty Yagana ke rike dani fuskata rufe har cikin gidan ta umarceni dana shiga da kafar dama gami da yin Bissimila nayi yanda tace tafi tafi har dakina inda ta zaunar dani akan gado nan da nan mutane suka cika gidan yan ganin daki nan na bude idona tsayawa fadar kayan da aka zuba min a dakin ai kauyanci ne komai na dakin green ne bedroom din kenan falon dai ban fita ba hatta setin gadon dasu madubin duka green ne,ban taba ganin setin irin setin nan ba haka kowa yake cewa Mama,Mami ta shigo ta dubeni kai Iman kin more kaya kinga falonki da bayinki kuwa?Amira tace ai kallo yana
kicin nace uhm! ina bayin suka nuna min gashi nan
ashe ma a cikin bedroom din yake haka dai mutane
sukayi ta zuwa suna leka bayi da sauran wurare har
suka soma tfy Ya rage sauran kawayena,Nasir ma yayiwa Mami waya Www.bankinhausanovels.com.ng
wai ta fito su tafi ta dubeni matar yaya sai kinji ni a
waya da sauri nace wanne yayan?ta fita tana dariya
Amira ma ta fita tana dariya, tace to Iman sai kin ganni dan wannan mijin naki baya wasa da mutane bare muce zasu shigo da aboka ango na riketa nace sai ta gaya min ko wanene tace bansanshi ba na dai ganshi dazu ne naga kamar ba shi da fara’a,ta kwace nace dan Allah Amira kada ki tafi ko saurarona batayi ba sai da ta kai kofar fita daga bedroom din sannan tace Anty Yagana tace in ce maki sun wuce sai sunzo kawo maki akwatuna amma akwai kaya cikin wardrp nace shine suma suka gudu harda Saudatu,Amira tace eh na taso nace bari na rakaki da gudu ta fita kamar dama ta san
riketa na so nayi tace sai wata rana har falona na fita tausayin kaina ya kamani nan tsakiyar falon na tsaya ina duban dukiyar da iyayena suka narkar cikin katon falon komai na ciki tunda ga Carpet har zuwa Kujera Labule marun ne,wata yar kofa na gani koda na bude ashe kicin ne ya tsaru kayan aiki masu amfani da lantarki gasu nan,na dawo na daga labulen window na leka sai naga wani katon falone na alfarma falon da kamar naso na sanshi a hankali na bude kofar dakin na leko gabana yayi wani mugun faduwa ganin gidan yaynmu tabbas gidan yaynmu ne kenan shi na aura wata zuciyar tace min ko Kabir ne,shine zamu zauna anan kafin ya gama gida?na koma bedroom kaina daure na leka Toilet din da naji ana ta kwarzanta koda na ganshi sai da nace Allah yasa ka ma iyayena da albarka na shiga nayi alwala nazo nayi shafai Www.bankinhausanovels.com.ng
da wuturi da yake nayi isha a gida na idar na bude wardrof na ga kaya kala kala kusan cike na dauko rigar barcina mai hawa biyu nasa na kama gashina na tufke sai a lokacin na kula da wani show glass cike da kayan kwalba a cikin kwalban akwai turarukan wuta masu kamshi,na hau gado na kwanta zuciyata cike da tsoro da tunanin wa na aura ga tsoro ni kadai ce dan da na saba ni dasu Jamila muke kwana nace gobe zanyi wa su Jamila waya su dawo nan,can barci ya soma daukana naji
motsin kofa da sauri na juya don ganin mai shigowa
Yaynmu na gani tsaye cikin kayan barci riga da dogon wando kyanshi da annuri yana tashi a tare dashi ya taho a hankali har kusa da gadon nima na tashi zaune fuskarshi babu yabo ba fallasa yace ya jikin?a hankali yake magana,da sauki na fada ina dubansa farin ciki da dadi suka cikani sai dai na kanne,yace ina yake maki ciwo ynxu?nace babu yace shi kenan sai da safe nace Allah ya kaimu ya juya na bishi da kallo yana fita na
fada kan gadon don murna da farin ciki sai na nemi
ciwon ma na rasa kai a karshema durowa nayi na shiga bayi alwala nayo alwala nayi ta nafilfili ina ma Allah godiya daya sa iyayena suka zaba min abin sona,shiko daya koma dakinshi sai da ya gama komai na al’adar rayuwarshi sannan ya dauki waya ya kira layin Mimi ta dan jima tana ringin sannan ta dauka,lafiya? abinda ta soma tambaya kenan,ya baki kawo min lipton ba ne? tace Amarya ba sai ta kawo maka ba ta kashe wayar ya jima yana duban wayar shi mimi zata kashe ma waya?lallai ma, da kanshi ya shiga kicin din ya dafa ya fito bayan ya gama ya kwanta ya jawo filo ya Www.bankinhausanovels.com.ng
rungume tsam a kirjinshi idanuwanshi a lumshe ido surar Iman kawai yake gani,gsky ya girgiza da ganin halittar kirjinta bai taba tunanin haka take ba wato shi wannan abu baiwa ce daga Allah ba shekaru ne ba domin ko yanzu tafi Mimi kira duk da dai kirjin kawai ya gani ranar yayi baccin da ya jima baiyi ba tunda ya samu yarinyar daya jima yana so gashi tana da abin da yafi so a gurin ya mace duk biyun wato kasa da sama sai dai inda zaisamu matsala yaya zai yi ya tinkareta da wani batu na bukata?a ganin shi sai girmanshi ya zube a idonta da wannan tunani yayi barci. Da safe nayi wanka na gyara gado na share na goge inda yayi datti sannan na jona naurar saka turaren wuta na zuba nan da nan dakin ya gauraye da kamshi kwalliya na sha cikin atamfa yar Ghana dinkin riga da siket rigar fitet Breazier style gashi na na daure shi da ribon sannan na daura dankwali turare na fesa na koma falona na shiga kokarin hada TV,ban ji karar bude kofa ba sai dai naji sallama gabana ya fadi na juyo yana tsaye da Jeans baki da shirt,yayi kyau sosai na zauna kan kafet na ce ina kwana?ya amsa Ify ya jiki?nace naji
sauki ya juyo tare da fadin zo nabi bayanshi har falo ya zauna kan kujera sannan yace shiga dakin Mimi ki
gaisheta sannan kice tazo ina kiranta cikin tsoro na
shiga tana kwance a kan doguwar kujera cikin ta ya
tsufa girman falonta kamar nawa nace Anty Mimi ina
kwana da sauri ta tashi ke!! Ta daka min tsawa ni ba
antyn ki bace batun kwana kuma banganshi ba cikin
tsoro na ja baya nace yaynmu yace kizo ban jira amsa ba nayi waje da gudu ya dubeni menene?nace am….ba komai yace to zauna nan ya nuna min kujerar da take kalonshi kusan minti goma sannan ta fito kusa da shi ta zauna tana wani cin magani yace kinsan tun dazu nace ki zo shine kika ki zuwa ko?ta kauda kai taki magana yace to dama nayi kiranki ne dan na gabatar miki da Amina wato Iman a matsayin yar ta katse shi ni ba yaruwata bace ya ce to ya isa haka ni matata ce kamar yanda kike matata tace to kace dama can kana sonta munafunci ne kawai…..ya mike yanda uwata tace in aureki haka na aureki ke ma zabin mahaifiyata ce kin gane?wannan kuma ya nuna ni zabin
mahaifina ce dan haka ba zabina a cikinku sai ku kula
na san gaba kila na samo zabina. kuma kina cin
albarkacin cikinki ne,ya fita gsky naji haushin abinda
yayanmu yace ko da yake Anty Mimi ta fini jin haushin
tunda ya ba da ita gabana. Da rana bala dryva ya kawo mana abinci inji Www.bankinhausanovels.com.ng
Mama,yaynmu ya dawo lokacin ina kwance a kan kujera
a falona na sake wanka na sanya material baki me
zanen fararen fulawoyi ya zauna kan kujera na tashi
zaune sannan nace sannu da zuwa yace yauwa na
mike na shiga kicin na zubo mishi kayan ciki salat ma
kadan na zuba mashi na hado da coke da ruwan cway
na ajiye a gabansa nace mama ce ta aiko yace to kin
ba mimi ne?nace a’a yace bari na kai mata wannan
mamaki ya kamani a raina nace ita ba tayi ta bani ba
Sai ni na ce da saura bari na kai mata yace kawo dai
na kai mata nace to na shiga na dauko na kawo mishi
ya fita jim kadan ya dawo ina zaune shima ya zauna
yana cin abinci yace kunna min TV nan na dubeshi
nace ai ba’a hada area din ba sai dai kaset zan saka
maka yace barshi sai da ya gama na kwashe kayan ya
dan kishingida yace Iman kina jina?nace eh yace kar ki yarda na samu lbr kin ma Mimi rashin kunya sannan ki dinga yin abinci kullum kina bata saboda kinga Www.bankinhausanovels.com.ng tana da ciki sannan zansa Mama ta samo miki mai tayaki aiki kin gane ko?nace eh bama sai ka nemo mai aiki ba ni zanyi,yace shi kenan yanzu Babanki ya cika mana Store da kayan abinci gami da kayan cefane sai ki duba babban kicin duk abinda babu sai ki rubuta Kabir zai kawo nace to ya mike ya fita na bishi da kallo a raina nace dama nasan mai aiki zan zama a gidan nan.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  haka tukunna ina …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *