TAWA TA SAMENI CHAPTER 27 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 27 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

,can text din da aka saba yimin ya shigo Amira ce ta miko min waya gashi ango yayo text nace ba ango bane na duba sai naga ina miki murna amma har ynxu bancire rai da samun ki ba har sai na ga an daura miki aure abinda bana fata dan ban san ya zan kasance ba wannan ranar,nace kaini wannan mutumin
ya dameni Amira karanta ki gani wanda nake gaya maki din nan ne ta amsa tana kokarin dubawa tana cewa kila

ma Adams ne kin kasa ganewa kafin ta gama dubawa
sai ga call ganin sunan Adams ya sanya ta bani tace to ga ango ki ce mishi ya fa iso yau don gobe zamu soma shagali kuma muna so kowanne yaje,duk surutun da take yi ban saurare taba dan sai samu kaina da wata mummunar faduwar gaba na amshi wayar na daga sai naji muryar Adams cikin sanyi da sakewar murya yace Amina gabana ya fadi dan bai taba kiran sunan ba,na kwace kaina daga

hannun bose nace Adams menene yace dan Allah kiyi hakuri banyi niyar yaudarar ki ba amma am sorry ba zan aure ki ba na fasa sai dai still ba zan daina sonki ba,jikina ya soma rawa nace adams ka cuceni me nayi maka? A…A….Adam…ka,ban karasa ba sai kirjina ya tokare jikina yana ta Www.bankinhausanovels.com.ng
karkarwa,na dai ji su bose da yar borno suna tambayata Ify?Amira na salati daga nan sai na fadi
Tindaga nan bansan inda kaina yake ba sai a Rimi
Clinic lokacin ma bayan magriba ne na farfado,Dakin
dam da mutane, Babana shine kusa dani yana rike da
hannuna,ina farfadowa shina soma gani na shiga ‘yan
dube dube ina kokarin tuno me ya faru?Babana ya
dubeni sannu uwata ya jikin?duk yan dakin kowa ya
shiga yi min sannu,hannuna na daga zan share fuskata
sai naga lalle sai na tuna ashe fa ni Amarya ce nan
take na tuna mai ya faru da sauri na tashi zaune nace
Babana kaji abinda Adams yayi min ko?yace ya fasa
aurena, babana ya rungume ni kiyi hakuri kar ki
damu,sai a sannan na dubi mutanen dakin Alhajine da
yaya Kabir da yayanmu sai Mama da Aunty Yagana
nace ashe har su yayanmu sun iso dako Adams yace
min tare zasu zo sai kuka ya kwace min babana da
Alhj sai lallashina suke mama kam cewa tayi saiki yi
tayi tunda yace bai sonki dole ne?cikin kuka nace
mama yace har yanzu fa yana sona saidai ba zai aureni ba kila ma yana tsokanata ne,na dubi yaynmu nace dan Allah yayanmu tare kuka zo?harara ya sakar min sannan yace kiyi wa mutane shiru ynxu da kike magana Www.bankinhausanovels.com.ng
gobe ne daurin aurenshi a yola can garinsu kuma
iyayenshi sun. bada hakuri dan da yarinyar suka so ya aura yaki tashi daya yace yanajin inbai auri yarinyar ba mutuwa zai yi ina ganin shima ba laifinshi bane da akwai wani abu,mama tace ba komai Abdulrahim wulakancin shine kawai dan cin mutunci sai da ya bari ana saura kwana uku biki sannan zai ce ya fasa ga shi mun gayyaci mutane ya zamuyi kenan?ai gsky abinda Adamu yayi mana sai dai muce Allah ya saka mana,Babana yace ku dai ku yi hakuri ynxu mu samu kanta in yaso sai mu san abin yi,da sauri nace yawwa Babana don Allah ku taimaka min ku shawo kan Adams ina sonshi, Mama ta kawo min duka Alhj ya tare har suna hada baki shida babana suna cewa Habiba haba menene na duka?shi ko yaynmu fita yayi, jim kadan sai ga su Doctor yace ciwona bai tashi ba na dai firgita shi yasa amma a guji tashin hankali dan haka ynxu ya sallameni,mun fito kan titi gurin da suka ajiye motoci Alhj yace na shiga motar nace ni ba zani can gidan ba baba yace to muje nan ma nace a’’ah,mama haushi ya kamata tace to ko gidansu Adamun zakije?sai kin dawo nace ni Anty Yagana zan bi Alhj yace to kuje,ya dubi yayanmu yace kai su Abdulrahman,a mota ina jikin Anty
Yagana a kwance shi kuma yana tuki Anty tace
Abdulrahim yaya abokinka yayi mana haka?yace anty ni kaina na rasa gane kan abin jiya fa muna tare da shi bayan mun tashi daga wani wasa wanda dama ranar zamu gama yau mu taho gaba daya da abokanmu dan har na ma Kabir waya akan ya kama mana Hotel zamu sauki baki a jiyan da daddare sai ga shi wai shi Ghana yake son zuwa ya je yaga Aisha,nace wacece kuma Aisha?sai yace yarinyar nan da aka ce ya aura yaki Www.bankinhausanovels.com.ng
yanzu kuma ita yake so,da kyar ya kai safe, yau da
sassafe ya dau hanya babanshi ya min waya wai ko da
wata matsala ne tsakaninshi da Iman?nace ba komai
shine babanshi yace to ynxu yace yau ya ke son ya
auri Aisha ba sai gari ya waye ba koda suka ce a’ah su
ba zasu yi karanta ba sai ganinshi sukayi ya fadi
sumamme shine fa ba shiri suka dau hanyar Www.bankinhausanovels.com.ng
Yola,Babanshi din yace in sun dawo zasu zo nan su
bada hakuri.Jin wannan lIbr sai wani sabon kuka na saki dan lokacin sai naji wani son Adams din ma
nakeyi,yaynmu ya daka min tsawa yi mana shiru ko na
tsaya na bubbuge ki, wannan bakin ya yi tsit nayi shiru har mukaje gidan anty yagana.
Washe gari ina kwance anty yagana ta shigo ta

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  haka tukunna ina …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *