SIYASA TAAH CHAPTER 4 BY MAMAN TEDDY?

SIYASA TAAH CHAPTER 4 BY MAMAN TEDDY?

Nan take ya hau gudu,gudu kam irin na kwatan kai,wanda a haka dai Allah ya taimaki Meemah ta tsere mawa wannan sojojin ta hanyar shigewa wata adaidaita dake tafya a tsakiyar kwalta,amma a haka ta shige,nan ko me Adaidaitan da yake ta hadu da dan arxiki ba tare da yaji inda zai kaita ba,da kuma inda take yajah hadi da figarta da karfi kaman zai kifah…ita dai Meemah Salati take,wanda sam Hankalinta bai natsu ba sai da taga tayi nesa da inda Sojojin suke,sannan tafara maida numfashi.

Sukan Wannan sojojin babu wanda basuyi nasarar kamawa ba sai Meemah,Wanda a haka suka tarkatasu suka nufi dasu gidan gonan da Major yabasu umarni,tun kan su isa suke azabtar dasu,suka fara shan duka,niko nace wannan inaga kuma Ankai su wannan wuri?….

Bayan ankaisu ne M Abdurrahman ya tambaya ciki kam da akwai wannan yarinyar? Wato meemah,anan ne suke shaida masa da cewa”Ai ta boye masu,sam basu ganta ba. Shiru Major yy na sakanni kamin yace”Ohk tom zanyi tunani akan wannan yarinyar,yanxu ko horamun wanda kk kamesu……Yana fadin haka baijira jin mai sojan zai fadi ba ya datse kirar tasa.

Ako can bangaren Honorable dasa’a,kaman yanda yasaba,koda.aka kawo masa yaran gidan marayun  nan sun kai mutum 12,bai saka an basu komai ba,a haka sai da suka kwana biyu,kamin nan tuni suka galabaita…babu yaron dake iya sarrafa kanshi saboda yunwa.

Sawa yayi aka fara fito maasa da yaran,kamin ya umarci wani babban sargent ya fara aikin shi,da ido yaran ke bin shi da kallo,nan take ganin wannan katon mutumi mai kama da super D yana tunkarosu hannun sa rike da wata irin makami,wanda fasalta irin shi zai wuya,babu tausayi bb imani,yafara cafko Yarannan yana daga su da hannu daya,kawai sai ya jefah a wani daki,wanda daga wajen shi wani irin duhu xaka gani,sai wurin da zaka hanga kaman rijiya….ihu yarannan suke,wanda a haka yake daukar daya bayan daya yana antayawa,shikam Honorble sai mirmushi yake yana fadin lallai siyasata zai kyau…Sukam makafi da basa gani sai dai suji kawai anyi sama dasu an wurgasu wannan daki,wanda shikenan sai kuma a Lahira. A haka ne y zamana saura mutane uku ciki kam harda Ahyan,hannu wannan mutumin yasaka yana kokarin dago Ahyan,amma sai yaji tayi masa nauyi kaman dutse,sam ya kasa Daukarta,wanda sao a sannan ya bude yan ficificin idon sa,wanda daka gani kasan babu imani a cikin su…. Firgigit yy ganin yanda kamannin ta ya sauya,kwarmin idon ta na fidda ruwa,amma bana hawaye ba,a wannan karon farin ruwa yake xuba daga idon ta kaman Nono ko madara. Kamin yy mata mgna ne cikin wata murya mai fitar da sautin Amo take cewa”karda ku taba ni,kada kuyi yunkurin cutar dani,mun dade muna rangwama maka ,tayi mgnar tana kallon Alh Dasa’a da shima abun ya dan firgita shi,duk kyaun yarinyar lokaci daya ta koma kaman Aljana. Kai yanka mun ita gunduwa gunduwa kamin ka jefah fah ta cikin dakin dodon. Cike da himma Wannan mutumin ya nufi Ahyan,wanda da isan sa ne suka yajah ya tsaya da wuka a gaban ta,sai kuma suka ga yafara kasa,kan sa yafara faduwa sai gangan jiki da kafafuwa duka suka xube sukayi gunduwa gunduwa……jah baya sukayi wanda kamin suyi Aune kawai sai sukaji zafin wuta ta koina na tashi,waigawar da zasuyi ne nan sukaga Wuta ya kama gidan baki daya,wanda allah ne kadai zai tsiratar da mutum…ai ba shiri harta Honorable guduwa yy,kowa na son ceto rayuwarsa…Gigif tayi kaman wanda ta farka daga barci,kamin ta hau ware² tana duba inda mutanen sukayi tana Mamaki ganin bb kowa. Ahyan…!! Tajiyo an kirata da muryar da tafi kama dana Wani mugun halittan…juyowa tayi nan taga Matan tsaye tana sakar mata murmushi,kamin tace kina so na koma dake gidan Marayu n ki,ko na tafi dake inda muke rayuwa? Hannun matan Ahyan ta rike,wanda yanda ta saki jikin ta zai nuna maka alaman da tasan matan ne… A’a ki maidani gida,tayi maganar cikin zazzkar muryar ta mai dadin sauraro…murmushi matan tayi kamin takai hannu tana rufe idon Ahyan,sai kuma taji ta bude mata,a cikin gidan Marayun ta tsinci kanta,wanda ware² tayi a wannan karon babu wannan matan,cike da ko inkula tafara tafiyarta tana nufar sasan su,wanda a filin gidanne ta tadda Mama Batula….

Kam balai Ahyan Anya ke ko mutum ce,dama kina cikin gidannN ake ta nemar ki babu ke bb lbrn ki? Ehh Mama ina nan,tana fada mata haka ta juya tana rabawa hadi da barin wurin da batasan meye Mama Batula takeyi va,ita da wasu mutane wanda daalama suna mata tambayoyi ne…..

Aiko da giftawan Ahyan suka cigaba da tmbyar Mama Batula tmbyoyin da suke mata,ciki kam harda tambayar ta wannan yarinya da ta gifta su…? Wato Ahyan…

Nan take Mama Batula kam da Baki babu tsarki ta fara koro mawa yan jaridun nan labarn Ahyan,da komanta,da yanda bb mai rabarta kai har yanda Ahyan ta shigo gidan marayun nan sai da ta sanar mata,wanda nan ta karke zancen ta da cewa’ duk da ta kasance a haka babu mao nuna mata hantara kowa na kookarin jan ta jiki. Topah kuji karya don Allah…!

Nidai kam ganin yanda Mama batula ta sauka a layi yasani saurin rabasu,ina Nufar Gidan Vice presedent,wato V_P muhd Areef.

Komai na gidan tsaruwar sa tadabamce,acan inner room na tadda Rahinart waya na makale a kunnenta,sai aikin kaiwa da komowa takeyi,Can kuma sai naji tana cewa” Mommy Muhammad na Gabda Hauka akan wannan mahaukaciyar,a kullum baida Aiki sai nata,baya sukuni sai ya ganta cikin kwanciyar hankali,ko Break fast xaiyi,tom bayayi sai yaje yaga Tayi nata sannan,baya bacci Mom sai yaje ya duba Lafiyarta,kuma ko yaga tana lfy baya fitowa sai ya tabbatar da ta kwanta sannan,wayyo Mom wlh nagaji,na tsani wannan Matan bana sonta,ji nake kaman tabar mun duniyar na huta…..

Nisawa Hjy Saratu tayi tana daga kinshigede,takaicin duniya duk ya isheta,Rahinart tsanar da nayi mawa Zainaba wlh bakiyi mata rabiin shi ba, na tsaneta a rayuwata,nikaina tun da lfyarta Alhji Aruwa da Muhammad duka sun fifita son Ta akaina,kinga ko ni na haifi Areef,nikuma nice matan Daddy. Hmm tom Mom don Allah ki sanarmun wai wata irin alaka ce tsakanin ku da wannan matan,ko nace tsakanin  Muhammad da Ita?

Murmushi Mom tayi kaman Rahinart na gaban ta,kamin tace yanda Halakata yake da Umman ki,tom haka Hakalar Zainaba yake da Mahaifin su Areef. Mom Bangane ba,wai kina nufin da Ammie Zainaba da Daddy Mahaifansu guda ne? Rahinart tayi mgnar cike da kurewar mamaki. Kwarai kam da gske Rahy,Hajiya Zainaba da Alh Aruwa uwa daya uba daya suke. A takaitaccen labarin Zainaba shine Ada baya Itadin Cikakkiyar  jonarlist ce,wanda har ayau idan kikace Jonalist zainab Aruwa,tom duk nigeria bb wanda baisan ta ba…kasancewar ta ada baya bata da tsoro sam,duk girman ka a kasa indai ana zargi ko tuhumarka da wani Abu tom sai ta tunkare ka ta maka tambayoyi,wannan ne yasa mutane da yawa suke son Ta kuma tayi suna a kankanin lokaci,Gskiyarta ne ya fara hadata da Honorable Dasa’a,wanda ta taba kuresa a cikin dubbannin jama’a ahakan ne takara samun daukaka a idon duniya,dama aikin ta baki daya….shi kuma Honorable tun daga wannan lokaci ya lashi takobin ramuwa ga Hjy Zainaba,wanda ganin baya da hanyar ramawa,don ko a lokacin Daddy mukaminshi a soja shine Marshal,kinga ko shine mai sarrafa komai na gida nigeria indai a harkar tsaro ne, don yawuce mukamin general, hakan yasa Honorable yanke shawarar neman Auren Hjy Zainab wato Ammie,hakan yy mun dadi matuka,saboda a gidana dama take zaune,kuma yanda kkga Areef na nuna mata so,haka yake mata tun yana jariri take masa son duniya,Har wajen aikin ta dashi take xuwa kamin yy wayo yafara xuwa School. Kasancewar ta ko a wannan lokacin xatw kai shekaru 26,27. Dafari sam bataso Auren Honorable ba,amma ganin hantarar da nake mata da habaice habaice yasata don dole amincewa da Auren Honorble da Shikam Daddy baiso ba sam,kuma kina mgnar soyayyar su,tabbas dole ne Daddy yaso Zainaba musamman yanayin ta,hakuri da kauda kai,itace kadai masa kannin sa biyu ne,daya tana Auren wani dan kasuwa,wanda ayanxu yasamu karayar arxiki,suna cikin matsanancin talauci,ko sun zo bana barin su shigo mun gida,kuma banyarda ko daya daga cikin yaya na sun san inda suke ba,itama tana can da iyalinta. Itace gaba da Zainaba,Alh Aruwa shine babba,Kuma sun taso mahaifin su ya rasu,don Zainaba batasan mahaifin su ba,itama mahaifiyarta su batayi tsawon raiba don Zainabs na Secondary ta rasu,duk daa wannan lokacin ita yayar zainaban tayi Aure,kuma nima na Auri Alh Aruwa,ganin yarintan zainaba da kuma rashun iyaye duka,hakan yasa  Daddy yake mugun tausayin Kanwarta sa,kuma duk wani soyayyar iyayen su yakoma kanta.

A haka dai akayi Auren Honorable da Hjy Zainaba,wanda nigeria tadauki dumi matuka,wanda kowa ke cewa da manufarsa nayin  hakan,komai na zainaba abun kallo ne,don bb abu daya daaka siya anan gida nigeria,Tun daga ranar da Zainaba tavar gida,bata kara waiwayo ba sai bayan shekaru kusan 4,wanda da kyer Honorable yabarta,don bakaramun azabtar da ita yake yi ba,da xata koma ne Daddy ya dauki Muhammad Areef yabata halak malak,ganin har a lokacin bata haihu ba.

Zuwan Areef ne yaga irin mugun tar da Honorable keyi mawa Ammien shi,wanda anan ne kiyayyar honorable ya kuma nikkuwa a zuciyar sa,Kuma sam yaki rabuwa da Ammie,kullum suna tare,ashe duk idan tasamu ciki,sai ya xubar da cikin tahanyar baimawa Dodon tsafin sa,don Akwai lokacin da tayi barin bakwaini anata murna,amma yarinyar bata kwana ba ya bada ita ga  tsafin sa. A haka Areef yakai kusan shekara 15 ,wanda tun tafiyar su bai taba zuwa dubamu ba,sai sau biyu,shima sai da Zainaba tayi da gske honorable ya yarda yabar gidan…..anyi hakq baifi da shekara Uku ba Ammie ta samu ciki,wanda awannan karon cikin ta yakai har wata 9,akuma nan ne Areef ya dauki son duniya ya dora mawa cikin nan nata,wanda da wayo da dabara dakyer suka yi dabaran barin gidan hinorable don.a wannan Karon Areef yasamata rigima bafa xata bada babyn suba,hakan yasata bi tanasa,salsilan dare suka gudu daga gidan honorable,wanda anan ne suka fara cin karo dq bala’u dabam dabam….. Sunan suna titi ne,amma a daji suke ganin kansu. Wanda shidai Areef dake makale da Ammie,cintar kanshi yy a gidan Daddy baiga ammie ba,ayanda yake cewa shi tabbas yaji  kukan jariri,amma babu ita babu labarinta,wannan ne ya firgita Ammie ganin babu cikin.wata tara jikin ta,wanda tun da ta yanka ihu hadi salati,bata kara dawowa hayyacin ta ba,har aka kwana buyu ana nemanta babu Ammie bb labarin ta,wanda abun da yabamu Mmki shine shikanshi Honorable yazo mana yana sababi abashi yar sa idan baxa’a bashi matarshi ba…anan ne muka fahimci Shima baisan inda take ba…Daddy ne yabisa da tijara,don kinsan soja da iya sababi,don.a lokacinnan cemawa Dasa’a yy ya basa kwana uku ya taho masa da kanwa idan ba hakq ba kuma sai ya kashe shi har lahira.

Haka daiko ina yadau tajim tajim,wanda gidan tv radio,jaridu koina nemar J Zainaba akeyi,wanda a wata ranar  Larabace Areef ya fito daga wajen gidan daddy,don baida aiki a kullum sai kuka da tunani bb ci babu sha,babu mgn da kowa,anan ne yy ido biyu da Ammie  a halin na kama dq mahaukata,Kai a wannan rana tashin hankalin da wannan familyn suka shiga Allah yy yawa dashi,tun daga nan Areef yasa tsanar Honorable aranshi,kumq yq lashi takobin ramuwa ga Ammien shi. Wannan ne yasa tun zuwan ki kiga zainaba cikin wannan lallurar ta hauka.wanda sam bamu san maiya kawo mata shiba. Kuma abun mmkin shine babu cikin sai dai daalama ta haifeshi. Kin san meye? Tun daga wannan rana Muhammad ya sauya,ba mgn babu wannan har dama abunka ga miskili sai abun ya kara tsanan ta….

Akan Zainaba bakye ba,inajin koni nayi mata abu,sai ya nuna a fuska ko bai fadi mun ba. Don haka ki cigaba da lallabawa,don idan ya fahumci bakyeson Ta zai iya yin komai,duk da dama ni na tilasta masa Auren ki.

Hmm wlh ni Mom tausayi ma ta bani,Rahinart tace cike da sanyin jiki,da kuma jin tausayin Ammien Areef lokaci daya. Kujimun sakarya,ashe har yanxu da yarinta a kwakwalwarki?  Tom na fada maki da a yanxu tana da hankali,kuma tanada diya,sam Areef baxai Aure ki ba,idon shi ma baxaki gani ba,Aure kam sai dai ya Auri diyarta,Arxiki kam sai wanda aka sammana,kinji ma ban tsarkake kaina ba ni da na haifesa,don haka ina baki umarni ki cigaba da Azabtar da ita fiye da ta da baya…cike da gamsuwa da yarda da mgnar Hajiya Saratu na tabbas hakane,da duk son da take mawa Areef A banxa kenan…..tom Mom Inshallh,xan kokarin ganin yanda Areef baxai taba fahimta ba,har tagaji ciwon zuciya yq kamata ta mutu mu huta. Yadai fi Hjy Saratu tace kana suyi sallama ta datse kirar.

Kaman wacce aka tsikara Rahinart ta fara nufar Falon gidan nata,middle falo wanda a nan ne ta tadda Hauwa tana Aikin ta,sannu da gida Hajiya! Hauwa tayi mgnar tana risinawa na girmamawa. Zama tayi tana cika hadi da batsewa,kamin ta ce da Hauwa” ki kiranyo wa’ancan sakararrun yan aikin masu kula da wancen tsohuwar mutum mutumin…. Tom Hajiya,hauwa tayi mgnar jiki na rawa…hadi da nufar sasan ma’aikatan gidan,don ta kirawosu,ta lura da akwai masifa a cikin Rahinart. Itakam Rahinart ta kudurci sanar masu da karta kara ganin wata shegiyar maaikaciya a bangaren Ammie…Kuma banda bata abincin rana…na safe da dare ma albarkacin Vp ne. Wannan kenan!

Itakam bangaren Laila tun da Major Abdulrahman yabar gidan take tsula tsiyarta,wannan kawaliya ta shigo wancen tafita kowa da gayyar abun da take kawota.

Hajiya Laila ga wa’annan tabbas nasan su xasuyi maki zakiji dadin su inshallh. Hee Ba maganan jin dadi bane,banason ki kawomun wanda suke sababbin hannu,ba koyan aiki nakeso ayi akaina ba…Wata ce Mai fekakken murya da shegen iyayi,dagani kasan kwararroyar er lezbian ce…Hjy inshaallh zaki ji dadin kasancewa dani. Hmmm tom shikenan ke sahura shiga mun dasu daga ciki,tayi mgnar tana zanzare kudi tana mika baimawa Kawaliyar da takawo mata yammatan uku.

Mikewa tayi tana bin bayan Yammatan,wanda dai dai Sahura na fitowa,bata re da Laila ta kalleta ba ta wuce dakin da takaisu…..A natse tafara takawa hadi da shigewa Falon inner room ta nufah,wanda kamin tayi wata mgn da shigarta sukayo kanta,kowa da irin salon sa……..Masu shafan jikin dabam,masu Kokarin sauke Abayar jikin ta dabam,don dama ita irin shigarta kenan!  Kamin ta nufi bed tuni suka cire komanta…..wanda a haka ta fada gadon,su kuma kowa tana cigaba da sarrafata yyn da kowacce kye kokarin ganin ya samu karbuwa a wurin Lailah….nan take suka fara kwakulanta tana aikin lumshe ido,hadi da son tsayar da wanda tafi iyawa…niko maman teddy ganin haka yaasani fitowa da sauri ina Fadin Allah yaganar da waanan Yammata,itama Laila Allah ya tona asirin ta….idan kuma na shiryowane Tom Allah ya shiryeta.

************************

_ALBISHIRIN KU MASOYA MAKARANTA LITTAFAN MARUBUCIYA MAMAN TEDDY,INA MASU TAMBAYAR CIGABAN LITTAFAN TA,KAMAN SU BAFULLATANAN RUGA,GIDAN KWARATA,KWARYAR SAMA,DA DAI SAURAN SU:_ _A YAU NE TA SAUKAR MAKU DA BONANZAN DUKA LITTAFAN TA,SABODA ZUWAN TAURARI UKU✨_

Hjiyata mai kk jira bonon zan ya fara ne daga 29 nov 2021,zata rufe aranar data kammala free page wato 02 dec 2021,Taurarin littafan nata sune:

BAFULLATANAN RUGA

DIJAMA YAR FULANI

YAR AIKI NA

GIDAN KWARATA

YAR WAYE

KWARYAR SAMA

YAR MAULA

ZUMA DA MADACI

KAWALIYA

Ko wani guda daya akan farashi mai sauki 100?,guda duka kuma 800 sai ki magana ta wannan numbern domun samun dukan su 08081202932.

” Hajiya Atika inason naga kaina yanda kk dinnan,komai kinayin shi bb fargaba bb zullumi,wannan kune ake cewa anyarda daku,ni ina zan iya haka asirina bai tonuba,ai da Tuni Aure na ya mutu,kinga ko da girman ka ina dadin shi….Hjy Aina ce mai wannan mgnar,tana kallon Atika da take kurban Lemu ,kana ta ajiye cup din tana sauke trnsperent glass din da ya mamaye mata rabin fuska,Hmm Tom Aina,idan banyi hulda da maza ba da wazanyi?, nifah ba dutse bace,kina sane Honorable akan son siyasa da duniya har gabansa ya bada,bai da wani mamara,tom kinga don ina matanshi sai nayi ta zama bb jin dadi kaman na sauran mata? Aa ina hakan bazai yuwuba…cewar Aina ,kamin ta cigaba da fadin” ni ina mmkin xafin son dukiya da siyasa irin na Honorable da sa’a ace kan wani sayayya insaida jin dadin rayuwa ta?? Aa ina?? Wani dariya suka sheke dashi a tare suna tafawa irin na gogaggun hajiyoyinan da girman na jiki.

**********************

Ke karda ki kalleshi da’allh,cewan zubaida tana juyo da fuskar Meemah gyefe,Dariya Meemah tayi,kamin tace” Aini har Abada baxan taba mantawa da wannan mutumin ba,ya fake da malamin islamiya ya dinga feshe mutane da yawu,wai shi ga Ustaz,komai ya wani ce Dayyib fuzzzz…..ya tafeka da yawo,wlh ban yafe….Meemah tace tana bin wani dan ustaz da kallo da ya rabasu ya wuce a kan hanyan…Dariya zubaida tayi tana fadin kinmanta na gauta ne,duk idan mun sayo sai yace sai yy mana Addua shima duk a tofe mana yalo da Miyau,kai wannan mutumi ya azabtar damu,musamman ke Meemah da shegen tsaginagini…..hmm Ai wlh yy wa kansa,Meema tayi.mgnar a kufule….a haka suna tafiya suna fira da zagin wannan malamin nasu har suka isa gida……….Gaban Mermah ne ya yanke ya bada damm!!   Ganin sojoji kulullube a jikin gidan su,tabbas ni ake nema,abun da ta iya cewa kenan,kamin tacigaba da cewa”idan kin shiga kice mawa su Baba da Mama Suyi takansu,nima guduwa zanyi,idan kuma suka tsaya soja ba hankaline dasu kashe su zasuyi murus har lahira…..

Ke Meemah ban ganeba,vadai ke kk jawo waanan sojin ba?  Ehh to nice kuma bani ba,don duk abun da nayi akan Siyasa ne,don na ci kudi dole nayi campe,Wannan majorn da nake baki labari nayi masa rashin kunya,tom shi yaa aiko waanan mutanen….innalillahi wainna ilai….abun da Zubaida ta hau cewa kenan,wanda kamin ta karake ne meemah ta katse ta da cewa” Ai zubaida gomma ki saitq mawa kanki hanya nima nayi nan. Wayyo ni Zubaida yanxu ina xanga zanga Namadi? Lallai kam zubaida da sauranki,Au namadi kk nema,tom tsaya neman namadi zaizo ai…

Tana mgnar hadi da tarar adaidaita ta shige da sauri tabar Zubaida da hannu akai?……….

Wannan labarin yana daya daga cikin jerin taurari uku na karshen shekara….wanda zamu rufe maku Karshen shekarar 2021.⁷ ⁸

About AIS

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *