SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 2 BY Xayyeesherthul-humaerath

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 2 BY Xayyeesherthul-humaerath

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

Karasowar Da Mammah za tai nan take Nafeesa ta Fada kasa sumammiya.

Ba karamin tashi hankalin Mammah da na sauran malaman ya yi ba, kokarin daukatar suke domin kai ta cikin gida.

Dakinta sukaje sannan aka shimfideta kan gadonta.

Cike da Mamaki Mammah ke kallon ‘Yar ta ta gata nan dai domin ba suma tai ba alamu sun nuna cewa barcine ya kwasheta lokaci guda.

Mammah ta ce, “Ikon Allah daga isowa gida sai wani kalan barci mai ban mamaki.”

Ta kalli Malaman tare da fadin, “Mun gode Allah ya saka da alkairi.”

Da “Ameen.” suka amsa sannan sukai mata sallama.

Kara gyara mata kwanciyar tai sannan ta fice daga dakin.

Kamar wasa karfe biyar tayi ko alamar tashi Nafeesa ba tai ba, Mammah ta dubata gata dai lafiya Amman bata tashi ba.

Ko da Abhi ya kira waya abaiwa Nafeesa, kawai

 Mammah cewa tai tana barci domin ta San da zaran ta Fada mai hankalinsa tashi zai mussaman yadda yake matukar kaunar ‘yartasa.

WACECE NAFEESA? SANNAN WANENE NAFSEEN? NA SAN MA SU KARUTU DA DAMA SUN ZAKU DA SU SAN ASALIN NAFEESA DA NAFSEEN TO GA BAYANANNE NA NAN TAFE.

WACECE NAFEESA?

Nafeesa ‘Yace ga Malam Aminu Direba (Abhi) tare da Mahaifiyarta Dr Salima wadda suke kira da Mammah,itace yar SU ta fari sannan kaninta Sabeer mai shekara goma su biyu  kadai Allah ya baiwa Iyayensu,baza asa su sahun masu arziki ba sai dai ace masu rufin asiri,domin kuwa Abhi Direba ne dake tuki gari gari wani lokacin ma sai ya yi sati baya gida,Mammah kuwa malamar asibitice da yake tayi karatu da haka suke rayuwarsu cikin farinciki da annashuwa ba tare da sun Sa son duniya aransu ba,gidan su Dan karamine iyaka arzikinsu daki biyar biyu na Mammah daya na Abhi sauram kuwa na Nafeesa da Sabeer.

Daga ita har iyayenta acikin garin Yola suke da zama.

NAFEESA Yarinyace mai ilimin addini da na boko tana da hankali matukar gaske ba za ace da ita kyakkayawa sannan bata sahun munana daidai gwargwado take,tun Nafeesa na da shekara goma aduniya ta fara karatun Hausa Novel kamar wasa malamin hausansu na Boko ya fara karanta musu littafin  *YAR AUTA* na Jameel Nafseen tun daga lokacin Nafeesa ta fara karatu domin gabadaya ji take marubucin na birgeta, alokacin bata San miye so ba Amman ta San cewa tana son littafansa kuma a kullum bata da burin da ya wuce karantasu, YA kasance a kullum Nafeesa ta kwanta barci bata da aikinyi sai mafarkin Nafseen aduk ranar da ba tai mafarkinsa ba to ba zaman lafiya domin ba mai gane kanta in ko tayi tana tashi zata fara sabga uban kuka sai tayi mai isarta kan ta bari,har ta San menene so kuma ta fahimci cewa son Sa take tare da kudurin cewa sai ta AURI MARUBUCI, duk da Iyayenta sun sani Amman ba Yarda suka Iya domin gani suke basu da arzikin nemawa Yar su shi bare ya aura, tsantsar so mai ban mamaki bata taba ganinsa ba Amman tana Iya zana kamanninsa sak kuma akan Sa ta fara Zane sannan bata taba Zane Indai ba shi za ta zana ba,bangon dakinta ko ina ban da zanen Nafseen ba komai har zanawa tai aka maida mata shi tamkar photo, ta Sa agefen gadonta.

Ko da wasa Ba ta son jin an zagi wani mai suna Jameel bare kuma Nafseen dinta kacokan ta kan iya komai kan hakan domin ficewa take ahankalinta nan take.

Shin me kuke tunani zai faru ranar da Nafeesa ta ga Nafseen kuma sak ga kalan zanen da ta saba??

Wannan ke nan kadan daga tarihin Nafeesa.

WANENE NAFSEEN?

Wani Hamshakin Matashin marubucine,kuma mawaki sannan director,kuma producer, waanda ke zaune cikin garin Kaduna, Ya rubuta littafai da dama na Hausa da kuma wakoki kuma ya jogaranci fina finai daban daban, yana da matukar basirar rubutu mussaman na Hausa, salon Sa na matukar tafiya da mai karatu hakan ya Sa a kullum masoyansa daduwa suke duk da kasancewar yana da mata ko kadan hakan baya damun al’umma, kowacce burinta kawai ta samu Shiga azuciyar matashin saurayin nan mai tashe da zamani,baya da wulakanci ko kadan kullum kokarinsa bai huce yaga ya faranta ran masoyansa ba,hakan ke kara masa kima da daraja a idanun mutane da dama.

Wannan ke nan.

Cigaban labarin…..

******Afirgice ta farka abarcin ganin cewa  ba kowa dakin,leka falon ma tai ba kowa hakan ya bata damar fita agidan.

Tafiya kawai take batare da tasan inda take nufa ba,wani haskene ya bayyana agabanta tsintar kan ta da bin wannan hasken tai, tafiya take adaji babu ko alamar mutane bare mutum illa ita daya, ta na cikin tafiya wannan hasken ya tsaya cak,tare da fara komawa wani irin launi, me za ta gani???

Nafseen ne ke bayyana gareta….

Karasawa tai aguje domin riskarsa.

Mik’a hannunta tai domin rungumarsa anan ta Kara wata zazzafar firgita nan take ta bude idonta kwance take adakinta Wanda tun jiya da aka dawo da ita daga makaranta bata farka ba.

Sautin Kukanta shi ya fahimtar da Mammah cewa ta farka,cikin sauri ta karaso gareta tare da fadin, “Nafeesa Lafiyanki kalau ko? Ki dai na kuka kinji? Ina kina son Nafseen?”

Ta girgiza kai.

Mammah ta kara da , “To kina so in miki addu’ah tare da tayaki nemansa ko?”

Nafeesa ta ce, “Eh, Mammah ina glass dina bana gani sosai.”

Cike da tausayin ‘Yartata ta mika mata glass din tare da taimakonta wajen sawa.

Tsabar karatun littafin Jameel da kukan rashin ganinsa yasa Nafeesa bata gani sosai sai da glass, ko da ta karanta littafinsa sau dari hakan ba zai hanata kara karantawa anjima ba,har ta kai ga takusa daina gani,da kyar aka samu damar ceton idonta tare da bata glass kuma hakan bai sa ta daina karatun ba.

Bayan ta sa glass din ta tashi, “Mammah zan yi sallah.”

Mammah ta ce, “OK to muje in raka ki toilet din ko.”

Murmushi Nafeesa tai, “Tab ni dai bazaki lek’ani ba,  zan Iya fa.”

Murmushi ita ma tai , “Shi ke nan Ummana Jekiyi ba zan lek’aki ba.” Cewar Mammah.

Sai da tayi wanka sannan  ta dauro alwala  sallarta tai cikin nutsuwa har ta idar.

 Kayanta tasa tare da dauko Jakarta domin tafiya makaranta.

Mammah da ke shirin tafiya office ta kalleta, “Nafeesa ko karya baki ba miye na saurin haka,kuma naga ma ba lafiya gareki ba?”

Ta ce, “Mammah yau fa munada lectures da safene kuma inna bari malamin ya zo ba zai bari in Shiga ba, ni jikina bana jin komai.”

Mammah ta mika Mata Dari biyar tare da fadin, “Ga shi nan ki sai wani abun kice sauran ki yi kudin mashin Dan kinga Abhi baya gari kudin hannuna ya kare gashi ba albashi.”

Murmushi Nafeesa tai, “Allah amfana Mammah.”

Tana fita ta samu Nafe nan kuwa ta Dane cikin sauri domin ta zaku ta shiga Skul, cikin sa’a kuwa  tana isa ta fara hango yan  Department dinsu da alama ba ashiga aji ba, Hamdallah tai azuciyarta, ta cigaba da tafiya.

Wata Yar budurwa da bata wuce sa’arta ba ne ta tawo da sauri, “Oyoyo Habibbty har na cire ran zuwanki wallahi.”

Nafeesa ta galla mata harara “mai zai hanani zuwa makaranta da lafiyata.”

Karaf wani saurayi ya cafe da , “Ai ko da baki zo ba ma ni zan zo gidan da kai na in daukoki.”

Tsaki Nafeesa tai tana, “Kin ga Habibbty zo mu tafi.”

Har sun fara tafiya ya ja gabansu tare da fadin, “Wai ke me na miki ne ki ka tsaneni? Dan kawai nace ina sonki? In ban da Soyayya ma da kwashe kwashe me zanyi da Makauniya wadda bata gani sai da glass, ko da yake naji labarin cewa wai wani banza da bai ma San kina nan ba kike so.”

Nafeesa ta dago tare da fadin, “Mutansir kar ka kara ce masa banza kuma maganar makauniya da ka ke dadinta ba ni nai kai na ba ko? Kuma bance ka soni dole ba,Dan Allah ka kyalleni.”

“Ke dakata, ki tsaya wai akan Banza mara aikinyi Wanda ya rasa sana’a sai ta rubutu ki ke Neman min rashin kunya? To na Fada banza.”cewar Mutansir yana wuce kamar an saukewa jaki kaya.

Jin Zuciyata tai na bugawa zafin hakan take ji har cikin ranta yanayinta ya fara chanjawa.

Maryam da ta fahimci hakan ta fara Jan ta da niyar su tafi.

Har sun fara Tafiya Kawai Nafeesa ta juyo tare da bin bayan Mutansir ta sha mai gaba alokaci guda ta kai mai wasu zazzafan marika biyu afuskarta, shi ta mari Amman ita take kwalla domin jin zafin abun da ya fada kan Nafseen dinta.

Kamewa Mutansir yayi awajen ya kasa motsi domin tunda yake bai tabajin mari mai dauke da radadi irin na yau ba, zufa ya farayi ta ko ina, ga fitsari na zuba, sauran abokansane suka taso suna dariya.

Ita kuwa Nafeesa ko ajikinta ta cigaba da tafiya batare da ta kara waiwayo garesa ba.

Sai da Mutansir ya dauki minti goma kan ya dawo haiyyacinsa, “Wallahi,wallahi kunji na rantse sai na illata yarinyarnan,illar da har ta mutu ba zata manta ba.”cewar Mutansir.

Sauran abokansa kuwa yan Neman ayi da suka gama shan dariyar kara zugasa sukai.⁷

About AIS

Check Also

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath                 …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *