SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 1 BY Xayyeesherthul-humaerath

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 1 BY Xayyeesherthul-humaerath

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wata Yar matashiyar yarinya na hango da bazata huce shekara goma sha bakwai ba aduniya, kwance take tana barci cikin nishadi da walwala domin da zaran an kalli yadda yanayin murmushi ke bayyana afuskarta wannan ka dai ya isa laburta cewa tana cikin yanayi na farinciki,ta kankame littafin Hausa akirji tamkar tana gundu a kwace mata, mafarkine Wanda ta sabayi kamar kullum Amman ko wanne da salonsa ko na yau din ya yake?  Bara mu lekye cikin mafarkin Nafeesa.

“Nafeesa kin San cewa ba jin cewa akwai Wata ‘ya Mace da zan so kamarki? Kina jin cewa zan iya furta Kalmar so ga Wata ‘ya Mace bayan ke?, Hmm babu tantama cewa ke ce zabina sannan kuma kece burina,ina miki so fiye da yadda majnun ke son laila,ina kaunarki fiye da yadda kifi ke bukatar ruwa domin rayuwa.” Cewar Nafseen da ke zaune gaban Nafeesa.

Gyara zama tai tare da kara kura mai kallo tai murmushi kan ta fara da, “Da ace ana Iya kidaye adadin soyayya a sikeli na tabbata cewa wadda nake yi maka bazata taba kidayuwa ba,kamar yadda Dan Adam ba zai Iya rayuwa batare da ruwa haka Nima nake jin cewa ba zan iya rayuwa batare da kai ba, ka zamemin jinin jikina,numfashina da walwalata, ada nakan ji cewa ka fi karfina ba zan taba samunka arayuwata Amman wai yau nice tare da kai har kake furtamin Kalmar so? Dan Allah Nafseen ka rayu da ni karka barni karkacemin wannan mafarkine nake yi.”

Rik’o hannunta ya yi,yana kokarin yin magana.

Karaf Mama ta shigo tare da bugawa Nafeesa dundu abaya.

Sambatu take,”Ka kara cewa kana so na ko da sau dayane Dan Allah kar ka tafi.”

Dukan da Mama ta kara kai mata ne ya sa ta saurin razana tare da dawowa hayyacinta, “Mama kin kuran min shi, Mama kice ya dawo yau ya fadamin cewa yana sona mama Dan Allah kice ya dawo.”

Tsaki Mama tayi, “Ki bar min wannan shirmen tun kan na kai miki mari maza tashi kije kiyi sallah wawiya kawai.”

Kara kallon dakin tai da kyau ta ga da alamar gaske dai daga itane sai Mama, kuka kawai ta fara tana, “Mama wallahi in ban gan shi na aure shi ba mutuwa zan yi, ni kan sai na AURI MARUBUCI.” ta kara fashewa da kuka.

Wani irin bakin cikine ya kara tirnik’e mahaifiyarta ta, ta fice batare da tace komai ba illa azuciyarta da take fadin, “Ban San wannan wani irin bala’in so bane ga mutumin ba ba a taba gani ba, daga karatun littafi kawai, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikin Nafeesa ba kuwa? Ya Zama dole in sanar da Abhee abin da ke faruwa adaren yau.”

Ta shige daki.

Ita kuwa Nafeesa kara kyankyame littafin tai tana kuka sai da tai mai isanta kan ta dauro alwala tai sallah, tana idarwa ba abun da ta fara  rok’a illa Allah ya nuna mata marubucinta Nafseen Sanan kuma Allah ya bata ikon auransa.

Bayan ta kammala addu’ar tashi tai ta fita waje da littafinta ahannu, zama tai afilin tsakar gidan na su tare da chok a hannunta Zane ta farayi tana waka Wanda da farkon zanen duk Wanda ya kalla zai dauka cewa shirme take zanawa,Amman ahankali kyahun zanen na fitowa,da mamaki duk da kasancewar Nafeesa ba ta San Nafseen ba Amman tsaf yanayinsa da kamaninsa take zanawa,ba musu duk Wanda ya San Nafseen kuma ya ga zanen Nafeesa zai dauka cewa ta San shi kuma kyakkyawan sani ma, azahirin gaskiya ko bata taba ganinsa ba bin abun da zuciyarta ke rada mata kawai take ya yin zanen tundaga farko har karshe.

Kallonsa ta tsayayi tana mai farinciki ji take tamkar na gasken ne agabanta, cikin littafan da ta fito da su ta dau daya mai suna YAR AUTA NA JAMEEL NAFSEEN, Karatu ta fara cikin nutsuwa da zakuwa akowanni feji ganin ta riski gaba, labari Indai na shi ne ko wani irin salo na tafiya da zuciyar Nafeesa.

Gabadaya hankalinta ya tafi ga karatun kaninta da ba zai huce shekara Takwas bane ya fito yana buga boll ta gabanta ya huce ba tare da sanin Sa ba har ya goge mata zanen Nafseen.

Ji tayi ajikinta hakan ya Sa ta saurin kallon kasanta gani tai tamkar na gasken ne ya yi hatsari hakan ya sa ta Jan dogon numfashi tare da suma awajen nan take.

Sabeer bai San lokacin da kurma uban ihu ba, “Mammah kizo Anti Nafeesa ta mutu,Mammah.”

A rikice Mammah ta fito tana, “Sabeer wai meyafaru ne ba yanzu ta fito karatu kalau ba?”

Sabeer na kuka ya ce, “Ban San tayi zane bane na goge mata tana kallo shine ta fadi.”

Dafa kai Mammah tai tare da fadin, “Yah Allah! 

Kokarin daga Nafeesa daga wajen tai domin maidata cikin gida, da yake Mammah malamar asibitice kokari tai domin dawo ‘Yartata cikin haiyacinta  a Dan kankanin lokaci.

Bude Idon da Nafeesa za tayi ta fara, ” Mammah Nafseen dina Sabeer ya gogemin, sai ta kara fashewa da kuka.”

Mammah bata da zabin da ya wuce ta rarrashi ‘Yartata awannan lokacin hakan ya sa ta Jan Nafeesa jiki tana shafa mata baya, “Ki yi hakuri kinji Nafeesa bai sani bane, kuma ai zanene na San zaki Iya zana Wanda ya fi wannan kyau ko?”

Wani Dadi Nafeesa taji aranta nan take ta mik’e “Sabeer Bani Littafina  zan tafi madarasa.”

Mammah ta ce, “Madarasa da littafin Hausa? Haba Maman Abhi kibari in kika dawo kyayi karatun.”

Nafeesa ta fara buga kafa, “Ni dai da abuna zan tafi wallahi.”

Tashi Mammah tai kawai tana fadin, “Allah ya kyauta.”

Nafeesa kuwa Hijabinta ta Sa har kasa tare da nikabinta ta yafa jakar makarantarta agefenta na hagu sannan littafin hausanta na marubucinta NAFSEEN a hannun dama wato Yar Auta.

Ko da ta isa makaranta  anfara karatu Neman waje kawai tai ta zauna tare da bude littafinta domin cigaba da karatu.

Karatu ake yi masu Amman gabadaya hankalinta na kan littafin da take karanta, murmushi ne kawai ke bayyana afuskarta, kara gyara zama tai tare da Jan dogon numfashi ta cigaba da karatun, Malamin ne ya lura da yanayinta ganin cewa hankalinta baya tattare da shi duk da kasancewar bai hango me take kallo ba.

“Ke Nafeesa, ta shi ki karantomin hadisin farkon nan da na kawo.”

Cikin Sauri ta ta shi arikice take maganar, “Mallam, ai Nafseen bai fadamin ba aciki.”

Sake baki ya yi yana kallonta kawai cen ya daka mata tsawa, “Waye Nafseen? Karatu muke ko maganar wani anan, Iye ba tambayarki na ke ba?”

Sunkuyar da kai Nafeesa tai batare da ta kara kallon malamin ba.

Cikin tsawa ya kara fadin, “Nace waye Nafseen?”

Karaf wata yarinya ta ce, “Malam wani marubucin littafan hausane.”

Kara fusata malamin ya yi, “Ah ya yi kyau aiko yau zakiga Nafseen a makarantar nan ganin idonki bani littafin.”

Jiki asanyaye Nafeesa ta mik’a masa littafin .

Yana karba ya karema littafin kallo kamar yadda aka Fada sunan marubucin Nafseen,tsaki ya yi Sannan ya fara fata-fata da littafin yana yankawa.

Kuka Nafeesa ta fara yi bilhakki da gaskiya,tun tanayi ahankali har ta fara shidewa daga karshe ma ta k’ame awajen  nan take.

Ganin yadda tai, abun ya matukar ba malam mamaki daga yaga littafi, tsaki ya yi yana fadin, “kar in ga kowa ya fita kuzo mu cigaba da karatun mu in  iskancine nawa yafi nata.

Kwance take awajen cen kuma ta mik’e tare da wani irin gawartaccen kara,Malam ta nufa kawai tare da damkosa tana wani irin numfashi.

Ihu ya fara yana, ” Dan Allah Ku kwaceni Nafeesa za ta kasheni,wayyo Allah na.”

Dalibai kuwa sai dariya.

Nafeesa kuwa bata fasa jibgar malam ba.

Dalibanne suka kira sauran malaman dakyar aka karba Malam a hannun Nafeesa sai numfarfashi take tana kara kokarin cacumosa.

Malam na samun hanya ya fice adari yana, “Wallahi Yarinyarnan ba mutum bace Ku bincika.” maganar yake cikin Sauri da hakki domin ji yake tamkar zata kara damkar shi.

Suko dalibai ba abin da suke  ban da dariya yau Mallam yaji a jikinsa Dama ba baya ba wajen jibgar dalibai.

Ita ko Nafeesa ban da kuka ba abin da take Dan arayuwanta bata  taba  shiga tashin hankali irin wannan ba Wai Lttafin Nafseen din ta aka yaga a gabanta sai ma  take ga kamar har shi din aka taba  ba Iya Littafin ba D ji take Zata Iya fada da kowa a yau dai kam.

Wani Malamine yazo kusa da ita ya ce, “Nafeesa me ke damunki ne ?” aiko sai ta  Kara sanya  wani irin kuka cike da sauti ta ce, ”  Malam Nafseen  dina ya yaga min ya taba  min rayuwa ta yamin kacakaca da Nafseen dina Wallahi bazan bar shi ba dole sai ya ji abin da na ke ji ,” kowa sai ya tsaya tsaro tsaro yana kallon Nafeesa yayin da wasu ke ganin ta haukace kuma ta hadu da bakak’e aljanu.

Da kyar akasamu Nafeesa tabar wajen,biyu daga cikin Malamamsu mata aka nada domin yi mata rakiya gida ganin cewa lamarin yafi karfinsu har suka bar makarantar bata  dai na maganganu ba kaman wata sabuwar kamu ,”wallahi daka  rabani da Nafseen gara ka yanki naman jikina  wayyo Nafseen Dina sai hakuri ake  bata amma bata  San ma anayi ba sai kara bankarewa da take.

Da Haka har suka  kai gida Mamma na daki  taji sumbatu Irin na Nafeesa  sai ko ta daura hannu aka tare da fadin, ” innalillahi Wa’inna ilaihir rajiun me kuma yake  faruwa da Nafeesa lafiya Fa muka  rabu .”nan da nan hankalin Mamma  ya ta shi abinka da uwa a gigice ta kara so garesu.³ ⁴

About AIS

Check Also

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath                 …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *