SADAUKIN SADAUKAI BOOK 2 by Nura Muhammad

SADAUKIN SADAUKAI BOOK 2 by Nura Muhammad

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

alokacimda taga MARKAHULNAR kuwa nantake taji bugun zuciyarta yacanja domin tinda take aduniya bata ta6a gani kyakkyawan jarumin aljani irin saba. nanfa tabude baki tana kallansa domin takamu da tsantsar kaunarsa da sansa. 

aljani markahulnar ne yakatseta tahanyar daka mata tsawa sanadiyyar da saida dajin yayi girgixa qasa ta tsatstsage sannan duk bishiyun dajin suka kama dawuta. cikin tsananin firgici gimbiya safrah tafadi akan gwiwowinta jikinta narawa amma su aljani durfan da boka kiryan kuwa tunisuka fadi sumammu. 

Da aljani markahulnar yalurada duk abindake faruwa saiya canja sifa zuwa wani qaramim aljani kamarsu sannan sannan yamatsa kusa da gimbiya yacemata ‘yake gimbiya safrah kisani tinkafin kizonan nasan daxuwanki kuma nasan bukatarki domin nima itace bukatata inje wajan uban gidana wanda kona samu farinciki domin yaushekaruna hamsin da uku inacikin kurkukunnan wadda yau nasamu encin kaina inamai fari ciki sannan inamai godiya agarekuu. 

 ita kuwa gimbiya kallansa kawai takeyi domintakamu da tarkon kaunarsa. 

Bayan lokaci mai tsayi saisu boka Kiryan da aljani Durfan suna farfado.

Nandanan MARKAHULNAR yace kushirya zamu tafi can garin irami inda sadauki SHAHYAT take. 

Tafiya daga dajin waqqas zuwa garin IRAMI tafiyace ta kwana alba’in ga aljanu kamar su Boak Kiryan da gimbiya SAFRAH amma MARKAHULNAR yashaida musu cewa zai kaisu akwana hudu.

Nqndanan yabasu umarni suhau bayansa domin tafiya BIRNIN IRAMI.

Tabbas aljani markahulnar yacika gwansamemen kato aljani domin daya rikida saida yaninkasu sau goma. Dukkansu aljanun uku wato aljani durfan, boka kiryan sannan Gimbiya Safrah sukahau bayansa sannan yatashi dasu tamkar bedau koda tsinkeba abayansa.

Fuka fukan aljani MarkahulNar guda dari da sittin dukansu yana kadasune cikin tsananin gudu domin adakika daya yakan kadasu sau dari da sittin.

Bayan sunyi tafiya hargari yayi duhu sai gimbiya safrah taroki markahulNar daya sauka domin suyada zango.

Kotankamata beyiba yasauka sannan yabace bat tamkar bewanzu a dajinba.

bayan sunkafa tantina wa’inda zasu zauna hargari yawaye sai gimbiya sarfah takira Boka Kiryan dominyabata labarin waye Markahul nar. Cikin biyayya yazo sannan yazauna.

 Daboka kiryan yaxauna sannan yafara bawa gimbiya SAFRAH labarin kamar haka: 

shekara 100 dasuka wuce acan birnin IRAMI anyi wani mashahurin sarki metsananin karfin mulki. domin akwaishi da xaratan askarawa daga jinsin mutane harmada aljanu iri iri. sarkin nan sunansa “JAUDAR” sarki jaudar yakasance yanada wani hatsabibin sarkin yaki. sarkin yakinsa bil’adama ne sunansa kuwa RIZIYAL. Jarumi riziyal yakasance mutumne mekirki gaduk sauran al’umar sarki. atariyi tinyana dan shekara12 yafara jagorantar yaki domin sarautar yaki gadone agidansu. 

tinda RIZIYAL yake beta6a jagorantar yakiba ba’a samu nasaraba. sarki jaudar abokine ga sadauki riziyal tinsuna yara tinkafin kowannensu yasamu sarauta, sunkasance abokai haryanxu domin ayanxu duksun fara tsufa domin shekarunsu yakai 130. 

suna matukar mutunta junansu amma abu dayane kedamun sadauki riziyal domin inyatina lamarinnan hankalinsa tashi yakeyi domin wani lokacin har hawaye kan fita ta idonsa. bakomai bane ke damunsa illa rashin magaji domin beda da beda jika.

 sarki yakasance yanada yaya uku. tafarko mace se nabiyu yan biyu namiji da mace. atakaicedai yanada ‘ya’ya uku namiji daya mata biyu. yayan sarki sunkasance jarumai agarin wanda sadauki riziyal ne yake horar dasu.

 abindake  damun sadauki riziyal kenan domin bayaso yaxama meyankakken baya. cikin dalilin haka seya yanke shawarar zaifita neman magani domin yayanke shawarar bazaitaba dawowaba face burinsa yacika kokuwa yamutu yana nema. 

Wata rana yaje wajan sarki yafadamai zeshiga duniya neman magani domin yana bukatar haihuwa. sarki ya rarrasheshi amma yaga bayada shirin amsar shawararsa. se sarki yacemai toba matsala nayadda kaje kanemi magani domin rashin haihuwa baqaramin lamari bane kuma yanada ciwo. ayanxu wane gari zakayi domin neman maganin? se riziyal yace duniya xanshiga domin ayanxu bansan inda xanjeba.

 nandanan yayi sallama da sarki domin yagama shirinsa natafiya tintini.

 nanfa se riziyal yafita kofar gari yayi gabas shikamsa besan inda yanufaba. da sadauki riziyal yafita betsaya ako inaba sai a wani kauye inda yafara neman maganin matsalar haihuwa. 

wani yabashi shawarar cewa yanufi birnin baitil~mukaddis inda kecan kusada kogin nil domin acanne akwai wani hatsabivin tsohon boka Wanda babu abinda yakeyi sai maganin matsalar haihuwa. 

tafiya daganam xuwacan kuwa tafiyar wata biyuce. nandanan RIZIYAL yayi shiri sai yanufa birnin baitil~mukaddis. bekwana agarinba yakama hanyar garin. yayi kwana uku yana tafiya saiya gamu da wani jibgegen katon aljani ahanya yatareshi.

Aljanin yakasance katon gaske, ga hakora sunfiffito wake tamkar na giwa.

aljanin yacemai ‘yakai wannan bil’adama kayi sanida yau kaxo hannuna kaxama bawana kuma yau gunkina zesha jininka’.

 nandanan se RIZIYAL yace ‘qarya kakeyi, kayi sanida yau zaluncika yaxo qarshe domin baxan barkaba’ cikin fusata aljaninnan yakawowa sadauki riziyal wata sara danufin kasheshi amma cikin bakin zafin nama yakauce sannan shima yayi wani siddabaru se wata wuqa xabgegiya tabayyana ahannunsa wanda nantake yafara kaiwa aljanin sara cikin zafin nama.

 abukamar wasa wajan dukya turniqe da qura domin sadauki riziyal yatada hankalin aljanin matuqa. cikin qwarewa sadauki riziyal yake farmakar aljanin.

 shikuma aljaninnan abinda yabashi mamaki shine yaga wannan qaramin tsohon bil’adaman ne yake shirin kaishi qasa. nantake saiyayi kururuwa yaja baya yayi wani tsafi yawullowa sadauki riziyal wuta nantake wuta tatawo kamar xata koneshi amma saiya goce. 

haka yadinga wullomasa mugayan abubuwa yana kaucewa. kusan dakika 200 besamu nasara akansaba. shikuwa sadauki riziyal yayi tsalle sekace tsuntsu yada6awa aljaninnan wuqa ahannu. nantake enyatsunsa suka cire silar dayaja aljanin yayi wata qarakenan sbd tsananin radadi, shikansa sadauki riziyal saida yaji kamar ze kurumce domin tsananin qarar ihun. hatta tsuntsayen dake dajin da dabbobin dajin duk sedasuka razana.

 cikin zafin nama sadauki riziyal yaqara da6amai sara sanadin dayasa yafadi kan gwiwarsa keman. 

Bayan aljanin ya tabbatarda dole saiya bakunci lahira saiya dago kansa sanna yacewa sadauki riziyal “kasani koda kabarni koka kasheni to baxan ta6a barinkaba domin seka mutu” 

Kafin sadauki Riziyal yayi wani motsi tini aljanin yayi wani tsafi wanda wata takarda me daukeda tadu rubu tatashi sama tabace sannan shikuwa aljanin yafadi kasa matacce.

ganin wannan aljanin yafadi amacene kawai sai sadauki riziyal yakada kai yanufi hanyarsa taneman maganin damuwarsa wato rashin haihuwa. 

amma abinda sadauki riziyal besaniba shine dayasan wannan aljanin dabeyi fada dashiba. tabbas dayasan matsalar dawannan ran aljani xata haifar tabbas dabe kasheshiba. 

bayan sa’a biyu da tafiyarsane se wani maye daga cikin jinsin aljanu yabiyo tawajan gawar yatarar da ita.

 ganin gawarnan yayi matukar tayar masa da hankali domin bakowa bane wannan aljanim face SARKI SHARDUS wato sarkin mayun aljanu. Nandanan aljanin yayi wata qara wadda duk ilahirim dajin seda hankalinsa yatashi sannan yakada fiffike yayi sama cikin tsananin gudu da zafin nama. 

Betsaya ako inaba se awani gari can kusada Bahrulmuhid awani qungurmin daji inda nanne masarautar mayun aljanun take. 

Cikin tsananin gudu da tashin hankali yafada fadar wanda kowa hankalinsa yatashi sannn suka mammatdo domin sauraron meke faruwa.. 

alokacin wazirin garunne yake riqe da fadar sbd sarki yafita. se aljanin yadurkusa kasa yafara…

 cikin hanxari aljanin yadurqusa sannan yafara dacewa “ya shugabana yanxu haka daga can garin sin nake. to ahanyata taxuwa nabiyo tawani daji inda naga wani abu dayayi matukar tayanmin da hankali, bakomai bane wannan abin face gawar shugabanmu wato sarki ABU~DURHAM” 

Cikin tsananin fishi da tashin hankali wazirin masarautar mayu yadakawa wannan aljanin tsawa wanda yasa fadar girgidi sannan yace “karya kake domin aduniyarnan babu aljanin dayakai abu~durham karfin damtse dahar xe kara dashi” 

aljanin yakara durkusawa yace “yaa shugabana inada bukatar kahadani dawasu daga cikin dakaru muje aduba agani sannan atawo dashi” 

Nandanan waziri yatara dakaru dubu goma domin aje aduba sannan ingaskene adauko gawar atawo da ita inkuma ba gaske bane kuyi kacakaca da aljanin daya kawo wannan zancen kudawo. 

Nandanan duk aljanun suka kada fiffike suka nufi birnin Sin domin tabbatarwa. aljanun sunkasance manya manya domin inkagansu asama sekace yakin duniya Akeyi..

ABANGAREN GIMBIYA SAFRAH YAYINDA BOKA KIRYAN YAKE BATA LABARI SADAUKI RIZAL WATO MAHAIFIN SHAHYAT. 

sadauki rixiyal kuwa, be xame ako’inaba sai’a baitul~mukaddis. tabbas garin baitulmukaddis babban garine domin yaqawatu matuqa awajan fannin gineginesu. garin babban garine sosai kuma da dukkan alamu ana xaman lafiya sosai agarin. 

Da shigarsa garin seya fara tambaya inane gidan babban memagani agarinnan. Besha wata wahalaba  akanunamai wani tanqamemen gida wanda yasha ado matuqa akacemasa nanne gidan Malam ZURU megani harhanji. 

Da isarsa kofar gidan sewani dan karamin yaro me katoton kai yafito yacemai “ance kashigo” ahaka sadauki riziyal yabi bayan yaron nan domin yakaishi zuwaga boka zuru. 

Saida sukadau tsawon lokaci suna tafiya sannan yaron yakaishi kofar wani daki yacemasa yashiga. 

Cikin sanyin jiki tsoho sadauki riziyal yaqarasa dakin. da shigarsa seyaji ajikinsa tamkar ba’a duniya yakeba domin yatarar da abubuwan al’ajabi iri iri. {koni nagani da idona. amma nasan innafara lissafo mukusu Hmmm sekunce qarya nakeyi Gwara Nayi Shiru Ko}…….        . 

alokacin da Riziyal yashiga dakin da Boka Zuru yake duk saijikinsa yayi sanyi. yana daga kansa yaga dakin zagaye yake da wutar tsafi. agefe guda kuwa saiyaqa qoqunan kan mutane kamar guda uku akowata kusurwa ta dakin amma duk yagama duba dakin amma bega mutumba. 

yayi niyyar juyawa kenan saiyaga wani hayaqi yabayyana agabansa nantake hayaqin yadunqule yaxama wani tsohon bil’adama. cikin wata murya mara dadin sauraro tsohon nan yace “sannunka jarumi Riziyal” Riziyal na shirin amsawakenan sai Boka Zuru yace “karka damu bukatarka zata biya kuma zaka haifi jarumi wanda zaixama gagarabadau gadukkan jarumai amma kasani cewa katafka babban kuskuren da dakasan abinda xefaru akansa toda tabbas bakayiba.

 bakomai bane face yaqar wannan aljanin dakayi domin ransa daya salwanta zejawo sular rasa rayuka dadama Amasarautarku harda na mahaifiyar danka Wato Matarka inba’a kulaba harda na danka Wanda xa’a Haifa sannan har danaka. 

Riziyal yace “towanene wannan aljanin?” Boka Zuru yafara dacewa_____       #Sadaukin Sadaukai Page43.                  

Boka Zuru Yafara Dacewaacan Nahiyar Bahrul’imuhid Akwai Wani Qunqurmin Daji To Acikin Dajin Nanne Masarautar Mayun Aljanu Take. Su Wa’innan Aljanun Sunkasance Manyamanya Azzalumai Kuma Gwanaye Tafannin Tsafi.

 Kasani To Wannan Aljanin Dakakashe Bakowa Bane Face Sarkin Mayun Aljanu Wato Abu~durham. Kasani Yanxu Haka Ankaimusu Labarin Cewa Ankashe Sarkinsu. Kuma Sunhada Dakaru Dubu Goma Domin Sujesu Dauko Gawar. Kasani Cewa Daga Ranar Da Gawar Sarki Abu~durham Tashiga Bahrulmuhid To Tabbas Rayuwarka Data Matarka Da Jama’arka Duka ta Shiga Matsala Domin Zasuxo Suyakeku Kuma Tabbas Zasu Iyayin Galaba Akanku Domin Yawansu Yaninka Naku Sau GomaShabiyar. Abu Dayane Mafita Shine Kushiryawa Zuwansu Domin Inbakuyi Babban Shiriba To Tabbas Zasumuku Finqarfi Sannan Suhalaku. 

Kasani Yakai Sadauki Riziyal Tabbas Zaku Tafka Yakin Dabaku Ta6ayin Irinsaba. Yanxu Zangayama Wasu Matakai Dayakamata Kubi Dan Kutsiratar Da Rayukanku.

    Boka Zuru Yafara Dacewa. “sarkin Mayu Abu~durham Yanada Wani Hatsabibi Kuma Matsatsubin ‘Dan’da Domin Ayanxu Haka Yanacan cikin Kogon BAHRULMUHID dake tsakiyar dajin bahrul’imuhid yana halwar tsafinsa. tabbas nayi bincike kafin kaxo cewa baxaita6a fitaba sainanda shekara uku. kenan yakai shekara saba’in acikin kogon. yakai sadauki riziyal kasani nanda watanni tara matarka zata haifa wani kyakkyawan yaro kuma koda bakazoba zata haifesa domin ko ayanxu tana dauke da cikinsa. 

Kuma data haifi yarone wanda babu kamarsa. tabbas rayuwar yaronnan xata zamto acikin hatsari domin DURHAM baxaibarsaba saboda inhar yaronka yagirma to tabbas shine zezamto sadaukin sadaukai” jinhakanne yasa Riziyal Farinciki matuqa domin yaji burinsa nasamu ‘Da zecika. 

Sannan yadau alkawarin cewa zedau nauyi kare rayuwar yaransa domin baxaibar komai yasameshiba muddin yana numfashi aduniya. sae boka zuru yayi murmushi yaciro madubin tsafinsa yace “yakai wannan jarumi me dakakkiyar zuciya kaduba cikin wannan madubin kagani” sai sadauki riziyal yakalla besan lokacin daya bude bakiba sbd tsananin mamaki.

 bakomai RIZIYAL yagani aciki madubin tsafin boka zuba face wani yaro matashi mekamadashi atsaye hadida wasu zaratan aljanu guda biyu dams da hagunsa.  Agefe guda kuma gawani kyakkyawan matashi sadauki atsaye amma abinda riziyal yakasa ganewa shine shin wannan matashin aljanine ko bil’adam. afiskadai dasurar jikinsa kamar bil’adama abinda ya bambantashi da mutane shine kawai yanada fiffike sannan kuma yaninninka bil’adama Girma.

yana cikin kallane seyaga matashi jaruminnan yayi girgiza yaqama wani surgumemen katon aljani kuma kyakkyawan gaske.  duk sauran aljanun bawanda yakai kaso daya bisa biyunsa. aljaninnan seyatsaya abayan wannan yaronyayinda wata kyakkyawar aljana tazo tatsaya akusa dashi.

 nanfa se Rizyal yatambayi boka zuru cewa suwaye wa’innan aljanun kuma wanene wannan yaron dake matuqar kama dani domin tabbas banibane dan bansan kodaya daga cikin aljanunnanba.  boka ZURU yaqarayin murmushi sannan yakalli RIZYAL yace…………

tsayawar da BOKA KIRYAN yayi dabawa gimbiya SAFRAH labarinne yasa SAFRAH cikin tsananin bukatarjin labarin tace “yakai boka kiryan ina umartarka daka qarashemin labarinnan yanxu domin inada bukatar jin qarshensa” 

Amma sai Booka kiryan yayi shiru nayan dakiku sannan yace yake shugabata kiyi sanicewa banida ikon qaracewa komai domin gari ya waye yanxu haka. gimbiya SAFRAH bata ankara gariya wayeba sai alokacin, a6angare guda kuwa saita hango aljani Markahul~nar atsaye yana kallanta cikin mamaki. gimbiya safrah tayi murmushi sannan tamiqe tsaye taqarasa gun Markahul~nar Tacemai Yakai Wannan Jarumin Aljani Shinyaushe Zamu Tafine Zuwa Garinnan Da Jarumi RIZWAN yake. Markahul~nar Yayi Murmushi Wanda Duksaida Dajin Yayi Haske SBD Hasken Bakinsa Sannan Yace. “kiyi Sani Cewa Yanxunnan Zamu Kama Hanya Amma Kafinnan Yakamata Ki6oye Abindake Zuciyarki Domin Kowa Na’iya Gani” 

yana gama fadin hakan yajuya yabarta awajan tana mamaki domin takasa gane abinda yake nufi.

 cikin tsananin mamaki gimbiya safrah taqaso wajen aljani boka kiryan tacemai “yakai wannan boka ina fatan kaji abinda Markahul~nar yacemin to amma banfahimta meyake nufiba” 

Sai boka kiryan yayi murmushi yace yake gimbiya kiyi sani cewa Markahul~nar Shine Wanda Yadakatar Dani Daga Baki Labarin Nan Domin Dana Cikagaba Dakinji Abin Mamaki Agareki Tare Dashi Kuma Kisani Tin Lokacin Da Aljani Markahul~nar Yaganki Yalura Dakinkamu Da Tsananin Sansa Shima Haka Amma Benuna Mikiba. Gimbiya SAFRAH tace “yimaxa kaqarashemin labarin kafin yadawo yakai bokan bokaye” gama fadin hakan keda wuya saiga MARKAHUL~NAR yadiro daga sama cikin wata shiga taban tsoro. nanduk jikinsu yayi sanyi. 

Markahul~nar Yakallesu Seyakau Dakai Sannan Yace Kutawonan Mutafi. Se Alokacinne Suka Tina Da Aljani Durfan Wanda Tin Lokacin Da Akafito Daga Dajin Bakaken Aljanun Nan Baya Cikin Hayyacinsa Domin Yazubda Jini Sosai Sannan Yagalabaita… 

 Alokacinne Boka Kiryan Yaje Yata6ashi Saiya Juyo Atsananin Takaici Domin Yagacewa Daqyar Aljani Durfan Yarayu. Saiyacewa Gimbiya. Yake Gimbiya Ayadda Nake Gani Tabbas Aljani Durfan Yana Gargarar Mutuwa Gwara Mutafi Domin Daukarsa Zexamanmana Kaya. Markahul~nar Neyaqarasa Wajan Durfan Yace Yakai Boka Kiryan Kasani Yarasa Jini Dayawa Amma Xan taimakamai Saidai Inharna Taimakamai To Kasani Cewa Daga Ranar Yatashi A Durfan Din Dakasani Domin Xenika Akarfinsa Kuma Daga Ranar Umarnina Zairinqabi sannan kuma karfin damtsenku Dana tsafinku zaizamto daya koma yaninkaka.

 Kawai Sai Markahul~nar Yaciro Wata Wuqa Abayansa Sannan Yayanka Tafin Hannunsa. Nanfa Jini Mekamada Wuta Yafara Tafarfasa  Ahannunsa. Saiyaje Dabda Aljani Durfan Sannan Yadigamai Jinin Abaki. Nandanan Aljani Durfan Yafara Shure Shure Tamkar Za’a Zare Rayuwarsa. 

Cikin Dakika Biyar Seyadena Motsi Tamkar BAbu rai Ajikinsa. bayan kusan dakiqa goma aljani durfan bemotsaba. boka kiryan cikin tsananin fishi zeyi magana kenan domin tinaninsa Markahul~nar yakashe durfan zeyi magana kenan seganin aljani durfan akayi yamiqe tsaye nandanan duk jikinsa yafara rikida ahankali ahankali yana qara girma. 

fiffikensa yaqara girma. duk jikinsa yacanja yadawo kamar wuta. agirma kuwa yakai boka kiryan girma da firgitarwa. alokacinne yayi wata qara wadda tsantsar wutace ke feshi abakinsa. daya daga fiffikensa yakada seda iska tayi tamar zata tafi da gimbiya da boka kiryan dan tsananin qarfi. 

seyatawo har xuwa gaban Markahul~nar Yadurqusa Yace ‘Amsawarka Ya Shugabana’ Kokallansa Markahul~nar Beyiba Yace Kutashi Mukama Hanya Domin Akwai Tafiyar Kwana Uku Agabanmu. Se Markahul~nar Yacanja Siffa Zuwa Sifarsa Ta Ainiyi Wanda Yaninka Boka Kiryan Sau Biyar. Tabbas Yacika Narkeken Katon Aljani Domin Dukansu Su Ukun Sukahau Bayansa Kamar bedau Komaiba Sannan Ya6ace 6AT Tamkar Bewanxu Awajanba.  

ADAYAN BANGAREN KUWA 

wato bangaren sankin aljanu wato sarki dawwam bayan yakashe wannan katuwar macijiyar dake dajin farko ahanyar garin darul~ahbab bayan sunyada xangone harna tsawon sa’a uku samnan suka tashi da nufin shiga daji nabiyu domin tinkarar dodo WasWas. Dukkan Aljanun Zuciyarsu Nadukan Taratara Domin Kowanne Tinaninsa Shine: Shin Ya Dodo Waswas Zekasance.  

Amma Ganin Sarki Dawwam Natafiya Cikin Kwarjini Hakanne Yaqara Musu Qarfin Gwiwa. Al’amarin Yabasu Matuqar Mamaki Domin Sunashiga Cikin Dajin Sukaji Wata Iska Mani’imciya Meratsa 6argo Ga Bishiyu Iri Iri Daukeda Kayan Marmari Mabanbanta. 

Acan Daga Qarshen Dajin Saisuka Hango Wani Irin Katon Jan Dutse Domin Tindaga Inda Suke Basa Hamgo Saman Dutse Saida Suka Matso Kusa Sannan Suka Fara Hango Samansa. Sunyi Kusan Rabin Sa’a Suna Tafiya Sai Daya Daga Cikin Tsuntsayen Takai Bakinta Xata Cira Wani ‘ya’yan Itatuwa Domin Taci. Cikin Dakika Daya Tak Sukaji Dajin Yayi Girgiza Silar Dayasa Dukansu Suka Fadi Qasa Kenan.

 adaidai lokacin da tsuntsuwar tacira ‘ya’yan itatuwar dajin yafara girgidi kamar qasa xata bude duka sufada ciki. wani gurnani mara dadin saurarone duk ya cika kunnuwansu. 

daga can qarshen dajin saisukaga wannan dutsen yana motsi. alokacinne suka tabbatar dacewa wannan ba dutse bane face dodo waswas. alokacin daya qara matsowa kusa dasune yagansu tankar ‘ya’yan kaji. saifa yayi wata kururuwa wadda duk dajin saida yadauka. 

Duk aljanun saida suka toshe kunnuwansu hard a shikansa sarki Dawwam sbd jisukayi  tamkar xasu kurumta. cikin tsananin sauri dodo waswas yayafuto aljanu guda biyar hadi da tsuntsaye biyu yawatsa su cikin baki nantake yahadiyesu amma tamkar beci komaiba. 

Ganin hakane se sarki dawwam ya ayyana azuciyarsa cewa tabbas yaxo wajan mutuwarsa begama tinaniba se dodo yakawo mai hannu danufin yatalitseshi amma cikin wani azababben zafin nama yajanye jikinsa. al’amarin dayabaiwa dodo waswas mamaki matuqa kena domin beta6a kai farmaki besamu Abinda Ya Farmakaba.

Mamakin Da Dodo Kiryan Keyine Hakanne Yabaiwa Sarki DAWWAM Dama Yabugawa Dodo WasWas Wuqa. Alokacin Dawuqar Tasari Dodo WasWas Nantake Wukar Tanarke Tatsiyaye Akasa tamkar an sakata a tukunyar narka large. 

Cikin Tsananin Fishi Dodo Waswas Yashuri Sarki Dawwam Dakafarsa sanadiyyar dayajanyo Sarki Dawwam Yatafi Tamkar Anbuga Kwallo kenan. 

Saidayayi Dakika Biyar Sannan Yadaka Wata Bishiya Yafadi Sumamme. Shikuwa Dodo Waswas Yadinga Ragargaxar Jibgajibgan Tsuntsayen Nan Da Sauran Aljanun. Seda Akadau Daqiqu Dari Da Ishirin Sannan Sarki Dawwam Yafarka Daga Doguwar Sumar Da Dodo Waswas Yasashi.

 Alokacin Daya Farka Seya Tarar Tamkar Anshare Dajin. Domin Duk Yahango Aljanun Da Tsintsayen Duk A Kwance Tamkar Matattu. Cikin Tsananin Fishi Da Tashin Hankali hadida karfin gwiwa Sarki Dawwam Yayi Kururuwa Nantake Wata Walkiyar Wuta Tafara Qona Bishiyun Dajin. 

Shikansa Dodo Waswas Saida Yadakata. Sannan Sarki Dawwam Yatinkari Dodo Cikin Tsananin Gudu Tinkafin Yakarasa Yadaka Tsalle Xuwaga Dodo WASWAS.

Alokacin Da Sarkin Aljanu wato sarki  DAWWAM Yayi Tsalle Domin Tinkarar Shu’umin Dodo Wato Dodo WasWas Seyaxamto Tamkar Anharbawa Dodo Waswas Kibiya Saboda Tsananin Gudu. 

Amma Seya Dira A Kan Cinyarsa. Cikin Wani Sihirtaccen Gudu Yake Tafiya Yana Kaucekauce Mazgar Da Dodon Kekawo Masa. Seda Yashafe Sa’a Biyu Sannan Yakawo Kafadarsa. Nanfa Akafara Sabon Tsere Domin Yana Gudune Tamkar Walqiya Danufin Yaje Kan Idonsa. 

A yayindaa Dodo Waswas Yagane Nufin Sarki DAWWAM Seyabude Bakinsa Yahuro Sarki Dawwam Da Iskar Bakinsa Me Warin Gaske. Cikin Tsananin Kasala Sarki DAWWAM Yafado Agalabaice. Dodon Yakawo Qafa Domin Yatalitseshi Amma Yayi Wuff Yaqoce Dukda Haka Seda Yata6ashi. Sarki DAWWAM Yayunqura Yaqara Binjiki Dodon Domin Zuwa Fuskarsa Seda Yashafe Sa’a Biyu Dakusan Rabi Sannan Yaqarasa Kafadarsa.

Domin Tsananin Kaucewa Dukan Dodon Dayakeyi Dukya Galabaita Kuma Yafara Gajiya Ananne Yadaka Tsalle Xuwa Idan Dodo Yadaga Wuqarsa Danufin Burmawa Amma Nantake Wuqar Tatsiyaye Alokacin Data Ta6a Idansa. cikin tsananin fishi dodon yamako sarki DAWWAM daga kansa sannan yayi wata kururuwa me qarfin gaske. alokacin da sarki DAWWAM yaje qasa yayunqura yatashi yayi nufin yaciro makami seyaji bakomai amma seyaji wani dan qaramin abu abayansa. yana cirowa seyaga ashe wata sandace wadda boka Balbalinbala’i Yabashi Sannan Yacemai Itace Xataxamarmai Haske Alokacin Daya Shiga Duhu. 

Seya Daukota Danufin Makami. Alokacin Da DODO WASWAS Yaga Haka Seya Bushe Dawata Mahaukaciyar Dariya “HAAHAAAHAAA” {kunji dariyar manyar arna} bakomai bane yaba dodon dariya face yasan cewa wuqama bata tasiri ajikinsa ballema wata ‘yar quntuwar sanda. al’amarin yabaiwa sarki DAWWAM mamaki domin seda yaji tamkar yawullarda sandar yashigeshi da karfin hannu amma seya kanne yafasa sannan yaqara tashi cikin sihiri kamar tsuntsu xuwaga dodon. cikin dakika uku yaqarasa jikinsa. yaduqufa cikin azababben gudu sannan yawanxu akafarsa bajira kawai yalabtamasa sandar awuya.

Alokacin da sarki DAWWAM yabugawa Dodo Waswas Wannan Sihirtacciyar Sandar Kwatsam Sejiyayi Dodon Yayi Wata Qara Ta Radadi Merikitarwa. 

Nan Sarki DAWWAM Yayi Murmushi Akaran Farko Sannan Yabada Himma Wajan Bugamai Sandar. Shikuwa Dodo WasWas Yawanxu Yana Ihu Tareda Kaimai Mazga Amma Shikuwa Sarki Dawwam Yana Kaucewa Yana Qaramai Bugu Da Sandar Iyaka Karfinsa.

Kusan Dakika Ashirin Sannan Dodo WasWas Yafara Tangadi Tamkar Zefadi. Alokacinne Sarki Dawwam Yaqarajin Farin Ciki Aransa Sannan Yaqara Tabbatarwa Da Kansa Cewa Tabbas Zaicika Hatsabibin Da Seya Shiga Birnin Darul Ahbab  Inda Akace Ba Bil’adama Ko Aljanin Dayata6a Shiga. Harya Qarasa Babul Ahbab Yadauko Takobin Mutuwa Wanda Zekashe ‘Yarsa Wato Gimbiya Safrah Sannan Yafara Shirin Mulkar Dukkan Shu’umai Da Hatsabiban Duniya Wato Yaxama Sarkin Aljanun Duniya… 

Begama Tinaninba Seji Yayi Anhadashi Da Bishiya Bakowa Bane Face DODO WASWAS dayasamu damar mangareshi daga kafadarsa.

Alokacin da sarki DAWWAM yafado daga jikin bishiyar saiya yunqura cikin qarfin hali yatashi yamiqe. nandanan yafara ambatar wasu dalasiman tsafi na tsawon lokaci sannan yayi wata kururuwa me rikitarwa, akaro nabiyu yayi tsalle cikin iska Cansama zuwakan DODO WASWAS… 

WANNAN SHINE ARTABUN DAKE FARYWA A HANYAR DARUL AHBAB INDA SARKI DAWWAM KE FAFATAWA DA DODO WASWAS

 A6angaren Gimbiya SAFRAH da boka kiryan hade da aljani durfan kuwa bayan suntashi hanyar birnin sin abayan Markahulnar.

 Markahulnar Yakasance Yanagudu Merikitarda Tinani Domin Adakika Daya Tak Yakanyi Gudun Da Se Wasu Zaratan Aljanun Masujidakansu Tafannin Gudu Zasuyi A Sa’a Daya. Gimbiya Safrah Ce Takatse Shurun Daya Wanxu Garesu Tahanyar Ta6o Aljani Boka Kiryan Sannan Tabashi Umarni Daya Cigaba Da Bata Labarin Sadaukin Sadaukai SHAHYAT dan RIZYAL. 

Aljani BOKA KIRYAN yasunkuyar dakai domi alabarin daxebata tabbas yanajin kunyar gimbiya be ankaraba sejiyayi gimbiyar aljanun tadakamasa tsawa tace yacigaba. boka kiryan yayi gyaran murya kenan zecigaba seji sukayi Aljani Markahulnar yace.

Adaidai lokacin da boka kiryan keshirin cigaba da bawa gimbiya labarin sesukaji aljani markahulnar yatsaya cak asama sannan yace, kuyi kallo ixuwa gabanku. seyayi musu nuni da wani katon dutse wanda saboda girmansa har sararin samaniya yatokare. 

Cikin mamaki dukansu suka bude baki suna kallan wannan dutsen, boka kiryan besan lokacin dayace menene wannanba. jin hakanne yasa aljani durfan wanda duk halittarsa ke canjawa lokaci bayan lokaci yatintsire da wata munafikar dariya. 

Bakomai bane yabashi dariyaba face waiyau bokan duniya wandake alfahari yasan komai waishine ke tambaya. ciki fishi boka kiryan yatur6une fuska kamar wanda yaga mutuwa amakwancinsa sannan yanuna aljani durfan dadanyatsansa nantake wata walqiya tabaiyana izuwa jikin aljani durfan amma bisa mamaki hasken nata6ashi seya baje tamkar bewanxuba. 

Itakuwa gimbiya SAFRAH Kallansu Kawai Take Amma Babban Burinta Shine Asauka Akan Turba Domin Tagaji Daxama Abayan Markahulnar saboda yakasance me tsananin jin kunya gareshi domin tabbas takamu da annobar kaunarsa amma itace abayansa.

Ta ayyana aranta inda ba tafiyaba da tabbas hakan bazata taba faruwa garetaba.

Gimbiyace tacewa markahulnar daya sauka kan turba dansu huta domin ayanxu haka sunyi tafiyar sa’a bakwai kenan batareda tsayawaba. ba musu markahulnar yayi qasa danufin sauka. tinkafin yaje kasa gimbiya tabude fukafikanta tayi gefe danufin sauka shima boka kiryan yabita. amma shikuwa aljani durfan kokadan benuna alamaar yunwa ko gajiyaba. 

Cikin qanqanin lokaci suka yada xango shikuwa aljani markahulnar ya6ace bat tamkar bewanxu awajanba. gimbiya takira boka kiryan dan yaqarashemata labarin. boka kiryan yacigaba dacewa… “aljanunnan ta tsakiyar takasance ke na gefe ni dayan gefen kuma aljani durfan. wannan aljanin dayayi sifar bil’adama bakowa bane face wanda xexamto mijinki. nanfa gimbiya SAFRAH taxaro ido domin tanasauraran taji waye amma se boka kiryan yayi shiru domin iyakan hakan yasani alabarin sadaukin sadaukai Shahyat.

gimbiyace tacemai yacigaba amma seya durqusa yacemata iyakananne saninsa. kafin gimbiya tayi magana seji sukayi anbushe dawata dariya, cikin hanzari suka waigo dan ganin waye….

Cikin sauri suka waigo danganin waye meyin wannan dariyar mara dadin sauraro da amo. suna waigawa  basuga kowaba amma sesuka farajin wani gurnani me karfin gaske. 

nantake sewani jibgegen maridi yabayyana agabansu yana daukeda wata kotar qarfe me girma dawasu qayoyi ajikinta. alokacin seya fara dariya yana lashelashen baki. bakomai bane yabashi dariya face kimanin shekara dubu saba’in ba aljani ko mutum daya sauka akan wannan dajin.

 maridinnan yakasance daya daga cikin wasu dodannin maridai masu cin nama su basacin naman dabbabi sena aljanu damutane. yakasance meban tsoran gaske. take gimbiya safrah da boka kiryan suka bude fukafukai zasu tashi subar dajin sesuka waiga wajan aljani durfan sukaganshi azaune yana kallansu yana murmushi. 

al’amarin dayaba gimbiya safrah mamaki kenan tatashi cikin fishi taqasa gun aljani durfan. shikuwa boka kiryan tuni yayi mutuwar tsaye domin tsananin tsoro. 

Dukda hakan maridin nan yanatsaye yana lashelashen baki domin yaga abinci memaiko.

 Alokacin Da Safrah Taqarasa Gun Durfan Tacemai “yakai Wannan Mahaukacin Aljani, Katashi Maxamaxa Mutafi Mubar Dajinnan” Aljani Durfan Yace “Gimbiya Kiyisani Cewa Tinda Munriga Munxo To Tabbas Muyi Artabu Dasu Domin Daxarar Kince Xakitashi Sama To Sunanki Matatta. Yanxuma Jira Yake Mutashi Ya Fyadomu Da Wancan Kulkin Nahannunsa” Alokacinne Gimbiya Hankalinta Yatashi Aynun Tsawon Sa’a Sannan Tadake Tace 

“tabbas Bala’i Ba’a Kiramasa Rana, Yanxu Tayaya Zamu Fuskanta Wannan Maridin Meban Tsoro?” Aljani Durfan Yace Kiyi Sani Yawansu Yakai Kimanin Miliyan Biyar Kuma Baxasu Tinkaremuba Facesunga Muncutar Da Dan Uwansu. 

Nantake Cikin Gimbiya Safrah Yadura Ruwa, Zatai Magana Kenan Segani Tayi Aljani Durfan Yafita Dagudu Tamkar Walkiya Zuwakan Maridin Aljanin Nan.

WANNAN SHINE ABINDAKE FARUWA GASU GIMBIYA SAFRAH

Shikuwa Sarki Dawwam Daga Dayan 6angare Alokacin Dayatafi Zuwakan DODO WASWAS cikin azababben zafin nama kwatsam seyafada hancin dodon mekamada shirgegen kogon dutse mematuqar duhun gaske.

Adaidai wannan lokacin da dodo waswas yaji shigar sarki dawwam cikin hancinsa sai yafara juye juye yana tsalletsalle dan yafyato sarki dawwam daga hancinsa. shikuwa sarki dawwam daya lura dahaka saiya daga sandarnan ixuwa sama nantake wani haske yabayyana ajikinta. ahaka yadage iyaka karfinsa yacokawa dodon ita.

 jikake BURUM talume yasake sokamai ita….

 hmmmm nanfa dodon yayi wani ihu nikaiba baxan iya misalta qararba. 

cikin dakika uku dodon yafadi rubda ciki matacce. koda sarki dawwam yayunqura xefita amma kash  seyarasa hanyar fita domin babu wata koda dazai iya rakubawa yafita.

 nanfa hankalinsa yadugunxuma ainun domin yasan cewa qarfin tsafinsa baxai iya daga gawar dodon ba balle yasamu damar fita. gashi hancinsa nakan qasa qofar tatoshe ba hanyar fita. kuma inyace xetsaya hargawar taru6e to tabbas kafin tafara narkewa yunwa takasheshi, inma be mutuba halan kafinnan ersa gimbiya safrah tasamu haduwa da sadauki Shahyat harsuxo sucimmai anan shikuma besamu damar dauko takobin mutuwaba. 

Nanfa yafara sake saken hanyar daxaifita. kwatsam sewata dabara tafadomasa.

Adaidai lokacinda yagama yanke shawarane dabarar daxaiyine seyamiqe tsaye acikin hancin dodo waswas sannan yafara ambatan wasu kalmomi marasa kan gado masu rikitarda lissafi, nantake seqasa tatsage wani guntun aljani {wato GAFTAR} yafito waje. koda aljaninnan yayi tozali da gawar dodo waswas domin atinaninsa barci yake. Seya Razana Ainun. 

Natareda yasan inda Aljani sarki dawwam yakeba yadurqusa Sannan yayi qasa da murya domin a tinaninsa kar Dodon yatashi sannan yace “ya shugaba kayisani cewa irina guda dubu saba’in baxasu iya tinkarar wannan shu’umin dodon ba” yadada dacewa “yashugaba yakamata munema hanyar tafiya daganan kafin yafarka yayi kalacensa damu” 

Dukda sarki dawwam nacikin tashi hankali amma besan lokacin daya bushe dawata mahaukaciyar dariyaba. sannan yace “yakai wannan matsoracin aljani kayi sani cewa nakirakane domin kasamarmin hanyar fita waje daga cikin hancin dodon nan” 

Alokacin Se Aljani Gaftar Yayi Murtmushi Sannan Yadaka Qasa Dakafarsa. Nantake Se Wani Tafkeken Rami Yabayyana Agabansa Mekamada Kogo.  Haka Yakutsakai Ciki Kusan Rabin Sa’a Sannan Yabayyana Agaban Sarki Dawwam Yana Nishi Tamkar Wanda Ake Finciko Ruhinsa. 

Shikuwa Sarki Dawwam Yahade Fuska Tamkar Wanda Aka Turo Masa Sakon Mutuwa. Kusan Dakika60 Sannan Gaftar Yadawo Hayyacinsa Sannan Yagayawa Sarki Cewa Tinda Yake Aduniya Beta6a Ratsa Gasarda Tabashi Wahalaba Kamar Wannan. 

Batareda Bata Lokaciba Yaqara Dakan Kasa Sannan Suka Shiga Domin Suratsa Kasa Sufita Daga Hancin Gawar Dodo Waswas.

ABINDA YAFARU KENAN BAYAN SARKI DAWWAM YASAMU DAMAR KASHE DODO WASWAS

 Acan 6angarensu Gimbiya Safrah Kuwa Lokacinda Aljani Durfan Yatinkari Wannan Maridin Aljanin Kamar Guguwa Yatafi. 

Yanaxuwa Acikin Dakika Uku Yaxubarda Maridinnan Kafin Yafadi Saiyayi Wata Qara Dukda Aljani Durfan Yayi Kokarin Rufe bakinsa Amma Hakam Yagagara. Nandanan Sukafarajin Wani Gurnani Kafin Sufarga Wasu Jibgajibgan Maridai Sukafa Fitowa Dago Kowani Sashe Na Dajin.

Nandanan dodannin maridan nan suka cika dajin. kimaninsu yakai miliyan ishirin da dubu saba’in da dari takwas. sbd tsananin yawansune duk dajin yayi bakikkirin tamkar duhun dare. nantake suka afkomusu. tunkafin sukaraso aljani durfan jikinsa yafara cida huta tamkar wanda keshirin konewa amma wuta itace take bashi kariya domin basa yin wajensa saidai suyunqura wajansu gimbiya safrah da boka kiryan amma yahanasu. 

Aljani durfan yakashe kimanin miliyan2 adakika60 yayinda sukamai yawa harsuka samu damar qarasawa wajansu gimbiya. itakuma gimbiya kociro takobi bataiba saboda tsananin mamaki abinda yafado mata raishine “shin markahulnar ya’ajiyesu ananne dan sumutu kokuwa yasan dajin nada hatsarine shiyasa yagudu yabarsu ko…..?” 

Bata gama tinaninba saiganin wani jibgegen maridi tayi mummunan gaske agaban yana lasar baki jini na dalala. ba 6ata lokaci tazare takubba cikin zafin nama da datse kansa yafadi matacce.

 Alokacin Da Gimbiya Tafara Sheqar Dodannin Maridannan Tamkar An’aikotane Danta Kasheshu. sai boka kiryan shima yasamu kwarin gwiwa sannan yazaro wasu sihirtattun takubba yafara daddatsa dodannin maridan nan Amma Sedai Tamkar Qara Yawansu Akeyi Domin Haryanxu Basugama Fitowaba. Kwatsam Sewani Maridi Yamake Gimbiya Safrah, Itakuwa Tafado Atsakiyar Dubun Dodannin Maridan. Duk Sesukayi Kanta Danufin Sukasheta. Baxato Ba Tsammani Seji Akayi Wata Iska Me Tsananin Ratsajiki Ta Bayyana Ga Jikkunan Kowa. 

Al’amarin Dayaba Kowa Mamaki Kenan Duk Suka Tsaya Cak. 

Gimbiya Safrah Ce Tafara Arba Damene Sannan Tasaki Wani Gamsashshe Murmushi Me Dauke Da Cikakkiyar Kauna. 

Duka Dodannin Maridannan Suka Daga Kansu Domin Ganin Menene Yawanxar Da Wannan Iskar Ta Musamman? Nantake Sukai Arba Dawani Qasurgumemen Katon Aljani Wanda Duk Hankulansu Seda Yadugunxuma Ainun..

 bakomaibane yabayyana face aljani markahulnar wanda ke tsaye asararin samaniya yana kada fiffikensa cikin nutsuwa. koda yakalla gimbiya safrah akwance akasa sannan yaga maridannan azagaye da ita. 

Seransa ya6aci matuka. Acikin fusata sannan yadaga hannunsa sama nantake wata shar6e6iyar wuqar haske da walqiya tabayyana ahannunsa. koda maridannan sukaga haka kowannensu yakama kansa cikin tsananin gudu suka fara afkawa dajin dan 6o66oyewa. bakomai bane yasasu gudu face markahulnar yakasance duk lokacin dayake cikin bacinrai dajin yake zuwa suyi artabu kuma baya amfani da makami yayin farmakarsu amma seya kashe kusan dukansu sannan yake tafiya, yanxu kuwa bakomai bane yasa ransa ya6aci yayi niyyar kashesu duka face sunta6a gimbiya safrah wadda yake baiwa kariya tintana yarkaramar yarinya batareda kowa yasaniba sbd yayi bincike cewa itace zata zamo………. {Madaiji a can gaban labarin}

   yayinda markahulnar yaga gimbiya agalabaice atsakiyar dodannin maridannan saiyayi matuqar fusata amma sakamakon duk sun gudu saiya qarasa ahankali wajan gimbiya safrah {itakuwa kallansa kawai take cikin tsananin mamaki} sannan yadurkusa gabanta yace mata “yake sarauniyar sarauniyin gobe, inafatan basuyi miki wani rauniba domin idona baxai juri ganin hakanba” gimbiya safrah batasan lokacin data saki wani kyakkyawan murmushiba sannan tagyada kai alamar eh. 

Markahulnar yayunqura zetashi yanemo maridannan se gimbiya tadafashi sannan tacemai “yakai sadaukin sadaukai tinda munada tafiya sosai agabanmu yakamata ka kyalesu tinda sungudu” tadandole yakyalesu. 

Sannan yamatso dabda gimbiya yace zenunamata wani abu. nantake yayi girgiza yaxama wani tsohon aljani. sbd tsananin mamaki gimbiya batasan lokacin data miqe tsayeba. bakomai bane yabata mamaki face wannan tsohon aljanin yakasance wani dattijo wanda tasani tin ayarintarta domin tasaba dashi fiyeda mahaifinta. 

Akoda yaushe tana ganinshi yana mata wasa amma sauran aljanun basa ganinsa. saudadama tasha gayama babanta harboka balbalin~bala’i yana bincike dan gano meye amma shuru. harbabanta wato sarki dawwam yake tinani kokawai wasantane na yarinta. gimbiya safrah tayi nisa acikin tinanin mamakin datakeyi seji tayi markahulnar yace “shekaru dari takwas baya nasan xaki iya tinani tokarkiyi mamaki bisa ganina domin wannan bakomai bane kuma xancigaba dakasancewa mebaki kariya iya tsawan rayuwata” maganganun markahulnar bakaramin dadi sukaiwa gimbiyaba. 

Jitayi tamkar ta rungumeshi amma se markahulnar yaqara dacewa “naji kina tambayar labarin uban gidana{cikin mamaki tace eh} to kigyara xama kiji cikakken labarin. markahulnar yafara…

  

   A Bangaren Sarki DAWWAM Kuwa.

bayan qanqanin lokaci sai gasu sun fito taqarqashin qasa. alokacin yayi daidai da faduwar rana. sannan sarki dawwam yayiwa GAFTAR Godiya sannan ya6ace. acikin qanqanin lokaci DAWWAM yahada katafaren makwanci saboda kasancewarsa shu’umin matsafi. sannanne yafara neman hanya yana bincike ya fafatarwasa da zakinnan zata kasance kuma ya birnin darul’ahbab zaikasance. har gari yawaye yana cikin wannan halin. bayan gari yawayene sannan yanemo wasu gayayyaki na mabanbantan bishiyu. 

“nikaina bansan kowani iribane” sannan yayi wani hayaki kafin hayakin yagushe ya ambaci wasu kalmomi. sanadiyyar dayasa dajin yacanja launi kenan. bayan kimanin dakika biyar saidajin yafara girgixa tamkar ana shirin fincikeshi daga qasa. nandanan sararin samaniya yakoma bakikkirin, wata walqiya tafara bayyana tana qoqqona bishiyun dake dajin, sedai kuga bishiya ta kwanjame adakika. nantake wata iska metsananin qarfi tafara yawo daga kowani bangaren dajin…….      

  Iskar qara qarfi take domin duk bishiyun dajin sedai kaga tamkar ana wulli dasu Suna Yawo Cikin Iska, cikin tsananin kwarjini da jarumta sarkin aljanu DAWWAM yatsaya. duhu qaruwa yake asararin samaniya. adaidai lokacin daya daga kansane Sama sannan yahango wani duhu naqara tinkaro dajin, bakomai bane face wasu hatsabiban bakaken ifritan aljanu aljanu wa’inda suke zaune abangaren dajijjikan dake gefen duniya. saboda tsananin yawansu gabakidaya daga nesa sundunqule tamkar duhun hadarine ke tinkaro dajin. 

Yayinda suka matso kusa setakasance shikansa sarki dawwam seda yayi amfani da tsafi Sannan ya’iya tsayuwa Daqafarsa Adajin saboda tsananin qarfin iskar dake tinkarosa. <nikaina seda nasuma sau7 dana gansu>. cikin qanqanin lokaci dajin yazama dun’Dum Tamkar Duhun Dare. Saukar Shugaban Aljanun Acikin Dajinne Yasanya Girgizar Qasa Me Girman Gaske Yayinda Kimanin Sauran Aljanun Miliyan Hamshn Ke Tsaye Cak Asararin Samaniya. 

Shugabana Aljanin yakasance shirgegen katon gaske, jikinsa yakasance amummude nagaban kwatance. idanunsa sunkasance jajaye jajur tankar garwashin wuta, tsawansa yakai kamu dubu, yanada fukafukai kimanin ishirin da tara29, kowani fiffikensa yakasance fari, jikinsa dukkansa bakikkirin, mummunane nagaban kwatance.

bakinsa kuwa aduk lokacin dayamotsashi wani launine ke fita mara misaltuwa. alokacin daya qarasa gaban sarki dawwam seyakance tamkar guntu agabansa domin yaninkasa sau uku xuwa hudu amma ahaka yarussuna gaban dawwam sannan yace YA SHUGABANA UMARTANI, MEKAKE BUKATA? WAKAKESO AKASHE? WANI GARI ZA’A RUGUJEMA? WA KAKEO AKAWOMA? YA SHUGABANA UMARTANI. 

Sarki dawwan yayi murmushi na karfin hali sannan yabude baki yace ……………

END OF BOOK TWO

About AIS

Check Also

SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 1 by Nura Muhammad

SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 1 by Nura Muhammad                 …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *