NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 5

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 5

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

To” Umar ya fad’a yana mai mi’ke wa jikin sa babu ‘kwari

Khadija sai sannu take ma Jiddah da bakin ta ya kumbura yayi suntum sai zubar jini yake

Umar bai wani jima ba ya dawo “Aunty Khadeeja na fad’a masa bari na haura sama na d’auko muku mayafin”

“To” Umar khadija ta fad’a tana rungume ‘yar uwar ta a ‘kirji

A haka Umar yadawo ya iske ta ya mi’ka mata ta ansa ta yafa sannan ta yafa ma Jiddah “zaka bimu ne?”. “Eh zani”. “To muje ko”. Tafad’a tana d’aga Jiddah daga jikin ta “sannu sister daure ki tashi na kama ki sai mutafi asbiti ayi miki dressing kada abinda kike rainawa yazama babba da ‘kyar Jiddah ta iya kama hannun Khadeeja tana waiyo waiyo ta samu ta mi’ke kallo d’aya zaka yi mata ta baka tausayi saboda yadda bakin ta ya kumbura da taimakon Allah da na Khadija suka fito falon a lokacin Idi driver ya tada mota Habu mai gadi ne ya hango su cikin sauri ya ‘kara so inda suke ya bud’a masu ‘kofa yana yiwa Jiddah sannu Umar kuma ya zagaya ta d’ayan bangaren ahankali Jiddah ta shiga khadija ta mara mata baya Habu mai gadi ya wangyale musu get suka fice+

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Tsaye Siddeeqah take ri’ke da kugun ta sai zum ‘bure zum ‘buren baki take yi a cikin ran ta take fad’in “kai kuwa matar ka ta bani ayi mutum dun kum ba za ayi fira da shi ba sai kace wani boss kullum fuska daure” “ke mai ki ka ce ina wasa dake?”. Abinda Siddeeqah bata sani ba ba acikin zuciyar ta tayi maganar ba sarai sadeeq yaji mai tafad’a

‘ko’korin tashi yake yazo ya cim mata sai wayar sa ta shiga naiman dauki da kamar bazai duba ba saboda wannan yarinyar ta ‘bata masa rai amma sai wata zuciyar tace “ya duba dai yaga wake neman sa”. Haka kuwa akayi dauko wayar yayi daga kan hannun kujera My Baby shine sunan da yake yawo akan screen din nan take ya saki murmushi  harda d’an cije leban sa na ‘kasa ya gyara kwanciyar sa da kyau

Baki bud’e Siddeeqah ke kallon sa a tunanin ta aljanin sa ne ya motsa

Amma sai taga ya d’aga wayar ya kara a kunne baiyi magana ba daga can ‘ban garan aka ce

_”Amincin Allah ya tabbata a gare ka ina fatan wanda nafi so da kauna a duk duniya ya wayi gari lafiya koda yike naji a jiki na kana cikin koshin lafiya saboda inajin duk wani yanayi da ka ke ciki a jiki na_”.

Sadeeq kusan suman kwance yayi saboda shi a rayuwar sa yana son kula wa musamman a bangaren soyayya zai iya ‘bata lokaci mai yawa wajen tsara kalaman soyayya saboda shi a yadda yake gani idan bai ba ma soyayya hakkin ta ba bai more rayuwar sa ba

Bakin sa washe kamar tana ganin sa yace _”gimbiya sarautar mata ina fatan amincin tare dake”_

“Na gode My”. Jiya na gaji ban san sanda bacci ya dauke ni ba dan Allah kaya kuri ban kira naji yadda ka iso gida ba”.

“Kada ki damu baby Allah ya kare miki ni da kariyar sa na zo gida lafiya kema fatan dana baro ki babu abinda ya taba min ke”.

Zuby na dariya tace “kana nufin har na kai a bani irin wannan kulawar sai kace wata gimbiya?”.

“Haba ke kuwa ai kin wuce gimbiya a gurina ko kin mata da auren ki nike so nayi? Nan da kika ganni akan abinda nike so bani da sakaci ina basa kulawa ta musamman”.

Cikin kissa da kisi sina Zuby tace “yanayin muryan ka ya nuna min baka karya ba kana jin yunwa”.

Sai alokacin Sadeeq ya tuna ashe bai karya ba

Siddeeqah kuwa duk sona da gulma dole na kyale ta saboda na kasa fahimtar yanayin ta har yanzun a tsaye take idon ta akan Sadeeq kyam shi kuwa bai san tana yi ba ya tafi duniyar masoya

Ya cigaba da ce wa “wallahi Baby na manta”.

“My kaman ta fa kace yanzu fa 12:00 gaskiya ka daina barin mun kanka da yunwa saboda ba kan ka ke bari ba ni kake bari idan kuma kanason na cutu ai shikenan”.

“Haba Baby na na daina insha Allah zan dunga kula miki da kaina kamar kina gani na dazun ma har zan karya sai wasu ‘kannai na suka kama rigama har sukayi doke doken juna to shine duk naji raina babu dadi”.

“Ayyah my sorry kasan sha’anin yara sai ana hakuri da su amma gaskiya ka tashi ka je ka ci abinci idan ka gama bayan sallar azahar saika kirani mu daura daga inda muka tsaya”.

“To ranki shidade na gode da kulawa I love you”. ?

“I love you too”

“By”

“okay by take care for me”.

zuwa yanzu Siddeeqah ta nemi guri ta zauna amma wannan karan ba shi take kallo ba da yatsun hannun ta take wasa saboda yadda take jin ranta babu dadi.

Shi kuwa Sadeeq har cikin zuciyar sa ya manta da wata Siddeeqah a d’akin sa shiyasa ya saki baki ya yi ta suru tu

Kallon sa tayi tace “yaya zanyi fitsari” banza yayi da ita kamar bai ji mai tace ba

Can da taga fitsarin zai iya zubo mata tace “yaya yafa matse ni zai zubo”.

Sai a alokacin ya dago kai suka had’a ido sai yanzu ya tuna ashe tana  d’akin nasa, bai kula ta ba ya tashi ya shiga bedroom din sa bai jima ba ya fito hannun sa rike da mukkullin mota ya nufi ‘kofar fita  batare da yace mata komi ba  ganin haka tayi sauri ta mike kafar ta a matse ta soma tafiya alokacin shi har ya bude kofar ya fice

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Kwance take akan gadon da ake kwantar da marasa lafiya anyi mata dressing din bakin ta kuma an sa mata ledar ‘karin ruwa ga dukkan alamu ma batasan wa ke kanta ba saboda allurar baccin da aka mata Khadija na gefe tayi tagumi Umar ma haka kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa _____Ringing din wayar Khadija ne ya katse shirun nasu bayan ta fiddo wayar Sunan Momy ya bayyana akan screen d’in wayar da han zari Khadija ta d’auka ta kara a kunne tace “Aslm Momy”. Daga can ‘ban garen Momy ta amsawa Khadeeja da “W/slm Khadija naji ku shiru ne shine nace bari na kira naji ya ake ciki”. “wallahi Momy lafiya lau anyi mata dressing din bakin ta ne sai karin ruwa da aka sa mata”.

“sai yaushe kenan zaku dawo?”.

“dazaran ruwan da ake ‘kara mata ya ‘kare saboda nurse d’in tace zamu iya tafiya ba wani ciwo bane kawai buguwan da tayi ne, saboda ce mata nayi fad’uwa tayi abayi ta bige”.

“yayi kyau”. Momy ta bawa Khadija amsa daga haka suka yi sallama+

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Da bibbiyu Sadeeq yake tsallake steps soboda yana son yaje wurin cin abinci kafin a kira sallar azahar kici’bus yayi da Momy a dai dai lokacin da ya gama sauko wa daga steps din cikin sakin fuska Momy tace “ah Sadeeq ga fa abin karya wan ka can fuskar ka tayi zuru zuru nasan kuma yunwa ce kake ji”.

“eh wallahi Momy yanzu haka saurin da ki ka ga inayi restaurant zani”.

Kafin Momy ta ba Sadeeq amsa Siddeeqah ta sauko daga sama d’an kwalin ta rike a hannun ta tana susur kanta d’ayan hannun ta kuma rike take da bakin zanin ta daya kwance tayi wani iri da ita yayanayin ta ya nuna alamar tana cikin damuwa

Kallon ta Momy tayi na wasu ‘yan da’kiku bayan ta gama nazarin ta tace “Mai gaskiya lafiyan ki ki kayi zuru zuru dake ko kema yunwar ce”.

“wallahi Momy nima haka kawai naji ni wani iri ina Ummi take?”.

“Ummi tana sama tun da kuka haura tabi bayan ku kin san ta da bacci idan babu makaran ta tana can tana sana’ar”.

D’an ta’ba baki nayi nace to ina Khadeeja?”.

“ta raka Jiddah asbiti ayi mata dressing d’in gurin da taji ciwo”.

“To Momy nima bari naje na huta”.

“ba dai ki huta ba kije ki shirya Sadeeq ya kaiki gurin gyaran kai saboda jibi ne tafiya makarantar ki in Allah ya kaimu”.

Jiki na ne yayi sanyi ni wallahi da zasuji ta tawa su ‘kyale ni na cigaba da rayuwa ta a haka saboda banga aibin ta ba

“Maza mana kije ki shirya Siddeeqah tunanin me kike yi haka”. Momy ta tambaye ni “babu komai”. na fad’a ina haurawa sama

Maida duban ta tayi ga Sadeeq da yayi kicin kicin da rai kamar wanda akece ga ranar mutuwar sa “ba sai kaje restaurant ba ga kayan da mukayi breakfast can na hana suwaiba ta kwashe kaje ka karya saboda ka kai Siddeeqah wajen gyaran gashi kanta yayi wani iri”.

“Haba Momy asa idi driver ya kai ta mana ni inada uzurin da zanyi”. ya ‘karasa fad’a kamar zai rushe da kuka

Saida Momy ta ‘kare mai kallo sannan tace “lallai Sadeeq kana da aiki tana matsayin matar ka ace sai wani driver ya kai ta gurin gyaran gyashi to kai maye amfanin ka da bazaka kula da iyalin ka ba?”.

Yana sosa ‘keye ya ce “uhm Momy baza ki gane bane amma wallahi ba wani son yarinyar nike ba kawai dai zan hakura ne saboda nayi muku biyayya”.

Tabe baki Momy tayi kana tace “ina tausayin ka Sadeeq amma kaje kayi duniya ce”

Ba tare da yaji komai aran sa ba ya nufi dinning tebur

Momy ma d’akin ta wuce abin ta saboda Daddy yana gida

Zuciyar Sadeeq a cun kushe ya bud’e kular farfesun hanta ya zuba a filet kana yaja kujera ya zauna ya d’auki cokali ya fara cin farfesun amma sai yaji kamar yana cin magani saboda magan ganun da Momy tayi masa basu yi masa dadi ba saboda haka ya bar cin abincin ya ciro wayar sa yad’an shafa screen d’in wayar ya danna number Farooq saida Wayan ta fara ringing sanan ya kara a kunne ringing d’in farko Farooq d’in ya daga yace “officer officer”. Muyan Sadeeq a murtuke yace “kayi maganar makarantar yarinyar nan kuwa?”.

“d’an iska wai saurin me kake yi haka yaushe garin ya waye”.

Sadeeq na jin amsar da Farooq ya bashi yayi saurin katse kiran yana Jan wani dogon tsaki “mtssss”.

Adai dai lokacin Siddeeqah ta sauko daga sama tayi fes da ita sanye take cikin shigar doguwar riga ‘yar dubai mai ruwan hanta ta yafe kanta da mayafin rigar duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi kyau abinka da farar mace mai siririyar fuskar da ke d’auke da dogon hanci gaskiya tayi kyau ko ma’kiyi dole yace masha Allah saboda kama take da larabawa

Gaban sa ta tsaya tace “yaya na shirya”. Wani mugun kallo ya watsa mata gami da cewa “dan uban ki ni sa’an ki ne zaki ‘bace min dagani ko saina tashi na yi ball da ke”. Kafin Siddeeqah tayi wani yun ‘kuri Momy ta fito daga part din ta. Tana Murmushi ta ‘karso gurin Siddeeqah ta kama hannun ta ta kalli fiskar ta tayi fayau da ita masha Allah “gaskiya irin wannan kyau haka kamar zaki gasar kyau”. Rufe fuskar ta tayi da d’anyan hannun ta ce “Allah Momy banyi kyau ba ko hoda da kwalli ban shafa ba”.

“ai gwara da kika bar fuskar ki ahaka sai ainihin kyanki ya dad’a fitowa masha Allah”.

Tana Murmushi tace “Momy da gaske ina da kyau?”.

“wata ta ta’ba kiran ki da mummuna ne?”.

Waiga wa tayi inda yaya Sadeeq yake suka had’a ido ya balla mata harara Momy na lura dasu idan ta fahimci Siddeeqah Sadeeq ne ke ce mata mummuna. Kafadar Siddeeqah ta dafa tace “rabu dashi mai sunan manya kinfi shi kyau nesa ba kusa ba kishi yake dake amma ko makaho ya shafa yasan kin fita daban kama da larabawa kike yi wallahi da za a kwana yana fad’a ma wani ke hausa fulani ce bazai yadda ba har sai kinyi magana yaji muryan ki”.

Murmushi ne kwance akan fiskar Siddeeqah tace “Allah yabar mana ke Momyn mu ta bata fek kiss a kumatu”.

Kallan sa Momy tayi tace “tashi mana Sadeeq ka kai ta ta shirya kai take jira”.

Kamar zaiyi kuka ya ce “yanzu sai a ganni da wannan abar rigi rigi zan kaita gurin gyaran gashi ai abin kunya ne”.

Momy na dariya tace “Sadeeq kenan wani lokaci idan kayi wani abu kamar sai ka dawo kamar karamin yaro Siddeeqah ce zaka ce wannar abar? Allah ya shirya ka amma aga ni na ganin ka tare da ita zai ‘kara maka girma saboda iyalin ka ce”.______”haba Momy ‘yar wannan abar ce zan fita da ita a matsayin iyali na?”.

“Eh Ita d’in fa wallahi Sadeeq ka kiyaye ni ka raina ni ko? Duk abinda nike fad’a maka abanza nike fad’i saboda baka d’auka”.

“Momy dan Allah kiyakuri na daina ki ce mata ta wuce mu tafi”.

“Au bakin ka ciwo yake da bazaka  fad’a mata ba kai? Ko kafi ‘karfi ne? Sadeeq ina raba ka da kiwan kyalla kana shige wa kyallah ta haihu”. Momy ta fad’i haka cikin dakiya da tsitstsire sa da ido

Kame kame ya fara

+

Siddeeqah da taji haka tace “Momy sai mun dawo”.

“to adawo lafiya ‘yar albarka”.

Harabar gidan ta fito  taja ta d’an tsaya kamin yayan nata ya fito su wuce,

adai dai lokacin mlm Habu ya wangele get motar su Jiddah ta silalo ciki idi driver ya samu guri yayi faking kana ya fito ya bude musu murfin motar Khadeeja ce ta fara fitowa sai Umar ya fito saida Khadeeja ta zura kan ta da hannayen ta a cikin motar ta kamo Jiddah da kyar Jiddahn ta iya fito wa tana cicci za le’be saboda yadda take cin zuciyar ta na mata daci da radadi akan dukan da Siddeeqah ta mata ita kadai tasan kalan tana jin cin mutuncin da tayiwa Siddeeqah

kallo daya Siddeeqah ta musu ta kawar da kan ta gefe tana dariya ciki ciki saboda yadda taga bakin Jiddah ya yi sun tumeme

Sadeeq ne ya fito shima ganin Siddeeqah na dariya ita kad’ai abin ya bashi mamaki yana shirin daka mata tsawa sai ya hangi Khadija rike da hannunan Jiddah Umar na biye da su suna taho wa

Kallo na yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya yi gaba abin sa cikin sauri nima na mara masa baya ba tare da na lura ba naji na ci karo da mutum a tsorace na ja da baya ina yarfe hannu na, ganin Jiddah ce na bige “mttsssss” na ja wani dogon tsaki naga sanda Khadija ta yi mata magana da alamar dai mantuwa tayi a mota saboda naga cikin motar ta koma  Idan jidda yayi ‘kwala ‘kwala murayan ta na rawa tace “wallahi zaki san kin ta’ba ni yarinya zan nuna miki kalar nawa rashin mutuncin banziya d’iyar shegu ke idan….”.

“Tas tas”. shine ‘karan marin da Sadeeq ya wanke Jiddah da shi yana wuci yace “kada na kara jin kin ce mata shegiya duk lalacewar naka naka ne saboda hannun ka bai ru’bewa ka yan ke ka wurgar ita d’in jinjin ki ce nasan kin San da haka. ‘bace min dagani kafin na ‘ba’b’ballaki”.

Jiddah kusan suman tsaye tayi saboda yadda taji saukar marin batayi zata ba lura Sadeeq yayi da Jiddahn bata cikin hayyacin ta d’an ta’be baki yayi ala mun ko a jinkin sa, kana ya kallo ni nayi sauri nayi ‘kasa da kai na zaki wuce mu tafi ko sai na had’a dake munafuka kidinga yin abu sumi sumi to ki kaddara aure na dake… “.

Bai ‘karasa maganar ba kira ya shigo a wayar sa laluba aljihun sa yayi ya fiddo batare da ya kalli sunan mai kiran sa ba yayi picking call d’in gami da karawa a kunnen sa sannan yayafito ni da hannu ya yi gaba. Sai a lokacin Khadeeja ta iso kallo na take yi nima da kallon na bita yaya Sadeeq har ya shiga mota nima bu’de gidan baya nayi na shiga na zauna sai Sadeeq d’in ya waigo fuskar sa a murtuke yace “ke uban waye diraiban ki zaki dawo gaba ki zauna ko saina miki tsinannan duka”.

“uhm” ta fad’a kana ta dawo gaban motar. Habu mai gadi ya buɗe masa get ya fice daga gidan

Khadija na taba Jiddah tayi luuuuu zata zube a ‘kasa cikin hanzari Khadeeja ta mai do ta kirjin ta ta run gume ta mamaki kwance akan fuskar Umar yace “wai aunty Khadija mai yasa meta ni ma yan zu na dawo kina tafiya nima naje gurin Habu mai gadi”. Cikin kuka Khadija tace “Umar wannan wace kalar rayuwa ce daga wannan sai wannan gaskiya ni na gaji Zan roki Daddy ya barni na koma kaduna da zama wallahi bana son tashin hankali, nasan ita da Siddeeqah ne ko yaya tunda ina zuwa suka bar gurin”. Ta ‘karasa fad’a tana rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

STORY CONTINUES BELOW

Tana kokarin kama Jiddah sai ga Daddy ya fito da alamar masallaci zai je soboda ankira sallar Azahar, hannun sa d’auke da gorar ruwa ta faro, hango ‘ya’yan sa daya yi cikin wani hali yasa shi karasa wa gurin su da sauri

Allah sarki mahaifan mu  ko mai zamuyi musu bazamu taba biyan su ba saidai muyi musu adduar Allah ya yafe musu yayi musu sakaiya da gidan aljanna fiddausi ?

“Khadija mai yasa meta ne haka na gan ku cikin tashin hankali”. Daddy ya tamabaye ta

Murayan Khadeeja na rawa cikin kuka tace “Daddy wallahi nima ban sani ba bayan mun dawo daga asbiti shine na barta anan na koma mota saboda na manta magun gunan da aka bamu nan dai Khadija ta kwashe labarin abin da ta sani ta fad’awa Daddy gorar ruwar  hanun sa ya bude murfin ta ya zuba rawa a tafin hannun sa ya watsa wa Jiddah a fuskar ta nan take taja dogon numfashi ta sauke ‘kirjin ta na bugawa da sauri da sauri kara rungume ‘yar  uwar ta tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin ta farfado yasa daddy cewa “ku shiga daga ciki Umar zo mu tafi masallaci”. “To Daddy”.

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Aban garen Sadeeq kuwa wani ‘katon plaza ya kai ni mai kyau da tsari bakin Siddeeqah a sake take kallon gurin saboda ita tun da take bata ta’ba ganin kasuwa mai kyau irin wannan ba badan taga basuyi tafiya mai nisa ba da sai tace kasar ya bari da ita yana gaba tana bin sa a baya har suka isa daidai bakin wani ‘katon shago mai dauke da kofar gilas tafke ke irin wacce na ciki yake ganin na waje amma shi na waje baya ganin na ciki

Wani abun Sadeeq ya danna a jikin bangon shagon can sai ga wata mata ta fito da ganin ta ba bahaushiya bace saboda a kwai ‘karin gashi a kanta kuma babu mayafi a jikin ta rigar ta irin mara hanu ce sai wani d’an gajeren siket da take sanya dashi da turan ci Sadeeq yayi mata magana itama ta mayar masa bayan sun gama naga ya ciro kudade masu yawa ya mika mata ta amsa tana godiya yace “bita mana kika saki baki da hanci kina kollo na kamar yau kika taba gani na”.

Bayan sun shiga daga ciki Siddeeqah ta ga Mata a zazzaune akan kujeru masu kyau da burge wa wasu kuma an saka musu kan su a cikin wani inji yana kara wuuuu haka dai Siddeeqah tai tabin gurin da kallo kamin ta zauna a kan wata kujera da babu kowa a kusa da ita  tsoro ne fal a cikin ranta saboda yadda taga ana sa mutum cikin inji gaskiya ita baza ta yarda a sata ba aje a fille mata kai ana zaune ‘kalau da ido matan gurin suke kallon ta ganin ta suke kamar balarabiya wata a cikin su ce tayi karambani tace “sannu baiwar Allah”.

Kallon ta Siddeeqah tayi sai taga babbar maca ce saboda a kalla zata kai shekara 30 a duniya

Adan dakile tace “yauwa sannu Aunty”. Saida gaba daya matan gurin suka kalli junan su saboda yadda suka ji muryan ta sanyi ga dadi haruffa suna fita dai dai kamar koyan hausar tayi masha Allah

Saida aka gama ma wasu mata sannan layi yazo kaina mai saloon din ta dube ni “kanwar oga taso ki zo layi yazo kanki”.

A tsorace Siddeeqah ta tashi tace “amma ni dan Allah kada ku sani a cikin wancen injin ku wanke mun kaina kawai haka”.

“To bazamu saki ba tashi muje” mai saloon tace

Bayan wasu mintocin da basu haura talatin ba saiga shi Siddeeqah ta fito das da ita an gyara mata kanta har kyalli yake bayan kamshin da yake tashi asalin kyanta ya kara baiyayana masha Allah a gaban katon madubi ta saya tana kallon yadda aka gyara mata gashin  duk tsayin sa da cikar sa anmayar dashi guri daya anyi mata faking a tsikayar kai sai shafa kan take tana mur mushi saboda ita kanta tasan tayi kyau. Mai kula da gurin ce tazo tace “kan war oga ya dawo yace kizo ku tafi”.

“to”. Na ce na yafa mayafi na ta zuge min glass na futo

A jikin motar sa na hango sa hannayen sa dore akan kirjin sa ya zuba min idanu kamar wani maye? da ni ke kallon sa haka da yace “uban me nike kallo”. ahankali na karaso inda yake bai ce min komai ba ya zagaya yashiga nima na shiga ahanya ya kunna mana karatun alkur’ani mai girma muna saurara naji na kara samun natsuwa sosai kuma hankali na ya kwanta gaskiya alkur’ani rahama ne a tare damu saboda yadda ye samar ma da bawa nutsuwa da kwanciyar hankali

Cikin wata unguwa ya shiga damu mai gidaje iri daya A bakin get din wani gida naga yayi faking sannan ya dauko wayar sa ya dade yana danne danne yana dariya harda yin kiss a wayar ni dai ban ga ya kira kowa ba sai na ga ya aje wayar

Can sai ga Zuby ta fito sanya da d’ikin atamfa riga da siket amma irin dinkin nan ne da ake cema jahannama ga fasinja saboda komai na jikin ta ya bayyana mayafin ta a kafada ta doro shi bakin ta dauke da cingom tana taunawa yana kas

Tabe baki Siddeeqah tayi kana Ta cigaba da da kallon ikon Allah

Bangaren da nike tazo ta bud’e gani na da tayi a ciki yasa tayi turus harara ta buga min taja dogon tsaki ta maida murfin ta rufe cikin masifa ta dawo bangaren da Sadeeq yake tana jijjiga kafa

Tace “wace ce wannan ka kwaso Sadeeq? kamar aljana ko gamo nayi ni Nike ganin ta kai baka ganin ta?”.

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Ina mai baku hakuri akan rashin jina da ba kwayi akai kai

Ina godiya da yadda kuke nuna min kauna Allah yabar mu tare ya hada fuskokin mu a cikin aljanna fiddausi

About AIS

Check Also

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 8

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 8 Www.bankinhausanovels.com.ng  Momy ta ce “amma sai ka kai Siddeeqah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *