NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 4

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 4

Www.bankinhausanovels.com.ng 

_____A gaggau ce yayi faking motar sa ya fito ya shiga cikin gidan yayi sa’a babu kowa a falon sai TV da aka bar sa a kunne yana ‘kira’ar alQur’ani mai girma, darect sama ya haura bai zarce ko ina ba sai d’akin sa, yana shiga ya aje wayo yinsa ya cire a gogan hannun sa sannan ya fad’a bayi bai wani d’auki lakaci ba ya fito d’aure da towel a ‘kugun sa da wani a hannun sa yana tsane ruwan jikin sa gaban madubi ya zauna mayuka ne kala kala da tura ruka masu ‘kamshi da tsada ya shafa wannan ya mutstsuka wancen saida yabi yagama shafa ko wanne, sannan ya fesa body spray mai sanyin

‘kamshi wata dakakkiyar shadda fara ya d’auko wanda aka ‘kawata ta da ado da dinkin zamani hular zanna bukar ya ciro ya a je a gefe sannan ya d’auko agogon hannu da safa da ba’kin takalmi mai sheki, a tsana ke ya shirya abin sa tsaf sannan ya d’auki wayo yin shi ya fito. Da sauri sauri yake sauka akan step d’in tun kan ya ‘karasa saukar yake jin hayaniyar su Momy bai so haka ba, saboda yanzu saita tsare shi da tambayar ina zashi “Momy”. Sadeeq ya fad’a alokacin da ya ‘kara so cikin falon gaba d’aya yaran gidan sun sha jinin jikin su saboda basu san ya zo ba Siddi’ka kuwa batayi mamakin ganin sa ba, bakin ko waccen su na rawa suka fara gai dasa ya amsa fuska ba yabo babu fallasa “yau she kadawo gidan sadeeq? Kuma ina zaka haka kaci wannan kwalliyar sai kace sabon ango”. Yana sosa ‘keya yace “wallahi Momy ban jima da shigowa ba bikin wani aboki na zani anyi daurin auren jiya yau ake dinner shine nike ta sauri kada nayi latti”.

“A dawo lafiya”.+

Tun a hanyar sa ya kira gimbiyar ya shaida mata ya taho ‘kara ta kuma kwatan ta mishi unguwar da misalin ‘karfe 8:17 ya isa cikin unguwar daganin ta ma’aika ne a cikin ta saboda gidajen kusan duk iri d’aya ne kamar quarters haka unguwar take

Bayan yayi faking a gefen wani gida, ya d’auko wayar sa da ke ajiye a gefen sa yad’an shafa screen d’in sai ga number tafito da suna Baby a jiki call ya danna sai da ta fara ringing sannan ya kara a kunne

Ringing biyu ta d’auka ajiyar zuciya ya sauke yace “Baby na” daga can ‘bangaren cikin shagwaba tace “my heart kazo ne?”.

Ce wa yayi “akasi aka samu Baby na bayan na gama waya dake sai ga kira da ga office din mu wai ana son gani na to babu yadda na iya kin san aikin gwaumnati shine na juya a kalar tafiyar hanzu haka ina hanya ban isa ba ha’kuri na kira na baki”.

Zuby da ta gama shiryawa, zuwan Sadeeq d’in kawai take jira, batasan sanda kwalla ta fara zubo mata ba cikin shagwa’ba take fad’in “amma my kasan dai bazan ji dad’i ba wallahi har Abbah na sanar masa kuma yana gida inason ka gaisa da shi ga Momy da tun sanda ka shaida min zaka zo na fad’a mata tasa aka shirya maka abin ci yanzu mai kake so na ce musu?”. ta kara sa maganar tana fashe wa da kukun shagwa’ba

Tun Sadeeq yana dariya ciki ciki har saida ta fito fili saboda yadda Zuby ke shagwaba gunin ban dariya ga kuma kasala da ya rasa ta maye ta saukar masa duk a lokaci daya

“Haba my wai dariya naba ka?”. Niyar fashe wa da wani kukan take yi, yayi saurin cewa “gani a ‘kofar gidan ku kisa mai gadi ya bud’emin get ko ba shine mai ba’kin get ba?”.

Shuru tayi saboda bata yadda da abinda yace ba

Jin shurun yayi yawa Sadeeq yace “ko in koma ne?”.

“Wai da gaske My kana ‘kofar gidan mu?”.

“Na ta’ba yi miki ‘karya ne?”.

“A a”. Ta bashi amsa

“to kisa abud’e min get”.

Ihu ta saka ‘kamar ‘karamar yarinya ta cilla wayar kan gado

STORY CONTINUES BELOW

SADEEQ da kallo yabi screen din wayar yana mamakin Zuby d’in wani lokaci idan tayi abu saita koma kamar Baby amma duk da haka tana matu’kar burge sa saboda son ta a kullum ‘kara dad’uwa yake yi acikin zuciyar sa

A yanzu haka yanajin idan ba ita bazai iya rayuwa da wata ‘ya mace a matsayin matar sa ba

Mai gadi ne ya wangale get d’in Sadeeq ya sulala da motar sa ciki kana ya nemi guri yayi faking

Bai fito daka cikin motar ba wayar sa ta hau ‘kara a kasalan ce ya d’auka ya kara a kunne

Daga d’ayan ‘ban garen tace “My ga Rahmatu nan yar aki zata kaika falon baki”.

“Banga kowa ba ni”.

“to baby ka fito daga cikin motar mana zaka gan ta”.

Ta fad’a tana ‘kara gyara tsayiwar ta a jikin balakona saboda tun sanda Sadeeq ya shigo Zuby ke le’ken sa har kawo yanzu da take waya da shi tsaye take ko motsin kirki bata yi sai Murmushi da take yi zuwa zuwa mai wuyan fassaruwa

Da ya bud’e murfin motar saida ya d’auki 10 seconds sannan ya fito da ‘kafar sa guda bayan wasu seconds din ya fito da d’ayar Zuby dake la’be a balakona mamaki jan ajin Sadeeq tayi, saboda ko ita da take mace bata da kalan sa.

“Wow” shine abinda Zuby ta fad’a a lokacin da taga Sadeeq ya fito, “gaskiya gayen nan ‘karshan had’uwa ne kamar shi yayi kanshi Sadeeq ka riga ka shigo hannu bazan taba bari ka kubuce min ba ban taba jin ina son nayi aure ba sai akan ka zanyi iya bakin kokari na wajen jan hankalin ka kuma zan kiyaye duk abin da zai sa ka gane wace ce Zuby bazan bari wata kawa ta ta sanka yanzu ba ba gaskiya saboda gudun matsala inason asa bikin mu kusa saboda kada yan gulma su yimin cikas”. Zuby ce ta fadi haka bayan ta gama ‘karewa Sadeeq kallo

gaskiya Sadeeq namiji ne irin mazajen da suke da wahalar samu a wannan zamanin saboda ya had’a duk wani abu da ake san namiji ya mallaka Allah ya bashi yana da tsayi na misali ga kyau da hasken fata ga kudi da ilimi hankali ya iya daukan wanka ya iya soyayya mai daukan hankali duk shigar da yayi sai ta yi masa kyau shiba siriri ba shiba dan lukuti ba gaskiya masha Allah gayan ya hadu ajin karshe ne?

Wata matashiyar mace da bazata haura 35 years aduniya ba ta ‘kara so gurin sa cikin girmama sa tace “ranka shidade nice Zuby tace na kaika falon baki”.

Sadeeq da wani lokaci magana take masa wuya bai amsa mata ba sai nuni da yayi mata alamar babu damuwa ta kaisa, tana gaba yana bin ta a baya har suka isa cikin wani madai-daicin falon da yake d’auke da manyan kujeru masu ruwan orange da baki sai chanis kafet da aka shimfid’a a tsakiyar falon shima ba’ki ne da d’ishi d’ishin orange a jikin sa sai ‘katon TV da ya mamaye jikin bangon falon a gefe guda a kwai ‘yan ‘kana nun tebura zagaye da baba a tsakiyar su gaskiya d’akin ya had’u wani abun ma bazai fad’u ba

bayan Sadeeq ya shiga ya nemi kujera ya zauna a kan 1cter jim kad’an sai ga rahmatu ta shigo hannun ta rike da katon tirai da aka jera kulolin abinci masu kyau da ban sha’awa a kan babban teburin ta jera kulolin sannan ta fita ta kuma dawo wa da wani ‘katon turai din mai dauke da fruit da da kunin aya da zobo ta kuma jerawa ta fice

Can sai ga ta ta kuma dawo wa da jok din ruwa a turai da kofuna biyu bayan ta ajiye ta dauki kofi daya ta zuba mai

Ruwan sannan ta saka wani farin abu a ciki kamar ‘kankara nan take ruwan ya fara canza color daga fari ya koma ja haka dai yai tayi sannan ta mi’ka masa

Amma sai yaki amsa da taga bashi da niyar amsa sai ta ajiye ta fice acikin ranta take cewa “ko ina Zuby ta samo wannan kyakkyawan saurayin tunda Zuby ke kawo samarin ta bata taba kawo mai kyau da hankali da nutsuwar wannan ba”. Abinda ya daure wa rahmatu kai yadda Sadeeq din yayi shigar kamala yana kama da mutanen kirki a fuska to mai yakawo sa gurin Zuby, saboda Hajiyar ta ta san duk wani abu da Zuby ke aikata wa wani lokacin ma ita ke bata karfin gwuiwa sabanin Abban ta da bai san komi ba

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Gaba daya mutanen gidan zaune suke a falon sama amma kowa da abinda yake yi saboda Umar littafi ne a gaban sa yana homework yayin da khadija da Siddeeqah suke fira Momy kuwa laptop ce gaban ta tana danna wa sai Jiddah dake faman danna waya tana cika tana batsewa Ummi kuma Session flm take kalla sun dauki tsawan lokaci a haka

STORY CONTINUES BELOW

Bayan Momy ta gama abinda ta keyi ne ta dube ni “Siddee’ka”. saida naji ‘ya ‘yan hanjin cikina sun kad’a saboda fargabar abinda zata cemin da hanzari na dago kaina muka hada ido nace “na’am Momy”.

“dazun da rana nayi magana da Sadeeq akan maganar makarantar ki”. Yace “ya samami ki admission a makarantar kwana har ya gama komai ranar lahadi zai zo ya dauke ki ya kai ki

Ba Siddeeqah kadai ba har su Khadija sai da suka dago kai suka kalli Momyn domin su dad’a tabbatarwa basu ga alamar wasa afuskan ta ba duk da Momyn daman ba mai irin wasa da yarannan bace amma kuma tana jansu a jiki ta yadda duk wani abun da yashige musu duhu suke zuwa neman shawara gurin ta

“Momy makaranta kwana fa ki kace”. Siddeeqah ta fada murayan ta a sanyaye

“Eh”. Siddeeqah wallahi makaran tar kwana Sadeeq ya nemo miki naso na hana amma sai yace “ya kashe kuda de masu yawan gaske saboda sunan wata a ka cire aka sa naki”. Sannan yace “acan sai kin fi dagewa kiyi karatu idan kina gida wasa ba zai barki ba”.

“Momy Daddy fa shima ya yarda ko bai sani ba?”. Khadija ta tambayi Momy

Sai a lokacin Momy ta tuna ba tayi waya da Daddyn ba dan sanda ta kira sa ta nason suyi maganar yace “mata suna meting idan sun gama zai kira ta”.

“A a” Momy tace “zuwa anjima idan ya kira ni za muyi maganar”.

“Momy mai yasa yah Sadeeq zai mini haka gaskiya ni Momy ba zani ba gwara in koma ‘kyauye gurin Inna ta na hakura da karatun bazan wani yi kuku da ku ba”.

“Taso kizo kusa dani ‘yata”. Jiki na babu laka na tashi na koma kusa da ita na zauna na tsaida idanuwa na akan fuskar ta, hannun ta ta daura a kan kafad’a ta cikin lallashi tace “Siddeeqah ha’kuri zaki yi saboda ilimi gishirin rayuwa ne idan Sadeeq yayi haka ne don ya kunta ta miki to insha Allah aniyarsa ce zata bisa saboda ke gaba ta kai ki

Ki kwan tar da hankalin ki babu abinda zaj same ki sai alkairi”.

“Momy kuma wace makarantar?”. Ummi tayi tambayar

“Katsina” yace “zai kaita wai akwai kanwar Farooq a can” yace “makaran tar tana da koyar wa sosai kuma suna da kula da dalibai”.

Jikin Siddeeqah yayi mutakar sanyi duk da bata taba jin labarin makarantar kwana ba amma dai ba tason tayi nisa da gida ita da take so duk bayan 2 weeks tana zuwa Dande ganin Inna

Gashi yanzu za a kaita wani garin ba garin da take ba

Da kyar Momy ta sha kan ta ta amince ba dan ranta ya so ba sai dan ganin girman Momy da take yi Momy ta cigaba da bata baki da kal momi masu dadi da sanya ya rai har ta amince

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Zuby ce zaune a kan kujerar dake kallon ta sa kura mata ido yayi ko kiftawa ba ya yi

Cikin shagwaba tace “muni na ka ke kallo ko banyi maka ba ko?”.

“ko daya ina kallon irin baiwar da Allah yayi miki ne Kin kuwa san wani abu?”.

“A a”. Tace mai

“Ban taba ganin mace mai kyau irin kiba gaki tun da nike a rayuwa ta ban taba haduwa da wacce na ke so ba har naji ina mura din auren ta sai ke, gaskiya ki kara godewa Allah bai rage ki ta ko ina ba a lokacin da naga kina tafiya sai kikai mini kama da wahainiya hatta muryan ki abar so da kauna ce idan kina magana kamar ana busa sarewa, ga…”.

“Ya isa haka my kada kasa na kasa bacci yau amma ka zuga ni da yawa har ka da naji kaina yayi kato”.

Duk kuwa da ba karamin dadin kalaman shi taji ba wani d’a na miji bai taba yaban ta haka duk kuwa da ita mutum ce mai san ana kuran ta ta ana zuga ta shiyasa tace “Sadeeq din na musamman ne”.

“Ai kin wuce haka Baby na saboda kedin zara ce”.

Cikin zolaya tace “Allah My kafi kyau a fili ka dai na wahalar daukan picture’s saboda yana rage maka kyau”.

“Bawani nan kodai ban miki bane?”.

Zaro ido tayi waje gami da dafa kirji tace “wane mutum inji mutuwa”.

“amma kinsan labarin zuciya atambayi fuska ko”.

“fadamin nason daman dan sanda akwai ku da karantar yanayin mutum”.

Zai yi magana kenan wayarsa ta hau ruri Acp Taneem yagani yana yawo a kan screen d’in cikin girma-ma-wa ya kara a kunne ya gaida ogan na su

Ko mai yace masa daga can ban garen oho, Shi dai Sadeeq din yace “okay angama ranka shidade okay okay ahaka dai suka karasa wayar

Ya a je yana kallon Zuby da ta kura masa ido ko kiftawa batayi

“Ya dai” yace mata yayin da ya hura mata is kar bakin sa, sai a lokacin taga rashin dacewar hakan kunya ta kamata tayi sauri ta sadda kan ta kasa tace “kamar ana neman ka A gurin aki ko ne ko?”.

Gira yadaga mata alamar “eh”

“to bari na kira Hajiya ku gaisa sai na kaika gurin dady daga nan saka wuce”.

Bata jira amsar sa ba ta wuce bata wani dauki lokaci ba ta dawo tare da wata dattijuwar chocolate din mata ita ba doguwa ba ita ba Gajere ba tsaka tsakiya

Amma kuma kina ganin ta kin ga uwar Zuby saboda ba karamin kama suke ba duk da cewa Zubyn ta shafa mai tayi haske

Cikin mutunci Sadeeq ya russuna ya gaishe ta ta amsa mai cikin kula da jin dadi Sannan sukayi sallama ta wuce

“gaskiya Hajiya nada kirki”. Sadeeq yace wa Zuby

“Allah da gaske?”.

“Ehman ashe ita kika biyo”.

Zuby dan dadi har rufe fuska take yi wai yau ita ake yaba haka ?

“muje na kaika bangaren Abba ku gai sa”.

“Muje to” ya fada yana mike wa tsaye

Ta wata kofar suka bi sai gasu a cikin wani madai-daicin falon da babu tarkace a cikin sa da wani datti jo zaune a kan kujera hannun sa da jarida yana karan tawa fuskar sa sanye da siririn glass bayan sunyi sallama suka karasa ciki a kan kafet Sadeeq ya zauna ha gaida sirikin nasa Abban Zuby yaji dadi sosai da yaga sadeeq ne zai auri tilon gudan jinin sa bayan sun gaisa suka dan taba fira Zuby kuwa bakin ta ya ki rufawa farin cikin ta ya bayyana a fili, basu dade ba Sadeeq ya yi masa sallama

babu laifi Abban Zuby yana da haske fata wata kila agurin sa Zuby ta dauko hasken fatar

Har bakin motar sa Zuby ta rakosa tana yi masa shagwaba kala kala da kyar ya samu ya lallashi ta ta barshi ya tafi

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

“Ku tashi kowa yaje ya kwanta dare yayi sai kuma idan Allah ya kaimu gobe” Momy ce ta fadi haka yayin da take kallon ‘ya ‘yan ta “to” duk suka ce masu tarkace suka dauka Ummar da dakin sa yake a kasa ya shige haka Jidda ma nata a kasa yake itama ta ce “Momy good night” tuni mu uku muka dun guma zamu haura sama amma sai Momy ta kwala min kira “Siddeeqah na manta zo ki dauki abincin yayan ku ki kai masa ban garan sa tunda saman zaku haura gab yake da shigowa

*Ash wash kash*?

_Na gaji hhhmmmm idan ban ga ruwan comments ba za a dade banyi typing ba_ ?

*Kada ku manta*_____”To”. Nace wa Momy na nufi hanyar kitchen bayan na shiga na d’auko kular abinci da zobon da Momy ta hada mai akan wani madai dai cin tirai na d’oro su sanda na fito babu kowa a falon har Momy ta wuce d’akin ta saboda haka nima na haura sama sai da na fara zuwa daki na na sauya kaya na saboda izuwa yanzu nima na fara sabawa da kayan baccin idan ba dasu ba bana jin dadin baccin saboda haka na sauya izuwa wata farar doguwar riga mai kauri ta bacci akwai wata yar baza mai kamar leshi a gaban ta ina sau yawa na nufi bangaren ya Sadeeq da yake dan nesa da mu saboda saikin bi ta wata kofa sannan zai sada ki da bangyaran sa dake dauke da falo da d’akuna 2 sai bayi da kitchen, nayi sa’a saboda kofar shiga a bude take ina murmushi na karasa ciki saida na gama karewa falon kallo sannan naja dogon tsaki ina ta’ba baki na ce “shi ko kunya baya ji daki sai kace na mace”. A bude na bar kofar sannan na wuce bedroom din sa da shiga ta naga gado a gyare luf luf dashi ya lailaye zanin gadon sa ji nayi ina sha’awar hawa gadan saboda haka na ajiye kular abincin a kan wani teburi nayi sufa kan gadon? ina ‘yan tsalle tsalle na ina dariya ni kadai+

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Tafe yake a kan hanya tunani ne fal a cikin zuciyar sa ya sa’ka wannan ya warware wancen duk da tuki yake yi amma yayi zurfi a cikin tunanin sa ta yadda bai san mai yake yi ba Allah ne ya tsare sa da kuma kasan cewar ba akan babban titi yake ba ringing din wayar sa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula fir gigit Sadeeq yayi saida ya dafa kansa “ya Salam ni Sadeeq mai ke damu na haka wani irin tunani ne kuma akan me nike yin sa mtssss” .yaja dogon tsaki ba shida amsar tambar sa saboda haka ya lalubi wayar sa da yaji tana ringing bai wani tsaya ya kalli sunan wanda ke neman sa ba yana dauka ya kara a kunne.

Daga d’ayan bangar akace “wallahi aboki baka da mutunci daka zuwa Abuja ganin Princess sai ka manta damu, munafuki amma da anyi magana kace baka son yarinya ka tsane ta”.

“shege akace maka kowa mayen mata ne irin ka ka rasa dawa zaka hada ni sai da yar karamar yarinya wacce ko…”.

“haba malam kada kaci ka min baki daga karshe kazo ka fada tarkon karamar yarin ya”.

“Wa ni?!”. Ya fada yana nuna kan sa da yatsan sa “. Kamar Farooq din yana ganin sa “Allah ya kyauta ai na fada mata duk sanda taji nace ina son ta kada ta taba yadda dani saboda ba da gaske bane”.

Farooq baiji dadin yadda abokin sa yayi su’bul da baka ba saboda haka yace “uhm Sadeeq idan Allah ya tashi kama ka bazai maka kadan ba kuma gaskiya bazan ji tausayin ka ba koda zanji sai ka ji jiki, saboda duk abinda ka Shuka shi zaka girba dama na kira ne naji ya kake ya Momy tunda duk kuna lafiya sai da safe”.

“Kaga Farooq kada ka kashe a kwai maganar da nike so muyi”.

“Ina jin ka to”

“yanzu haka fa a hanya nike naje naga gimbiya ta, gaskiya babyn ta hadu tafi kyau a fili nike fad’a maka komai yaji zam-zam hhhmm nasan ba lallai ka yarda ba tunda kaki ko hotan ta ka gani amma tun na ganta na shiga wani yanayi”.

“Haba Sadeeq daman wannan ce maganar da kace za muyi?.

“Eh amma da akwai d’ayar nafi zumud’in wannan shiyasa na fara fada maka ita” kuma kasan nace “Momy ce take nema na ashe akan makarantar yarinyar nan ne to shine nike so ka nema mata admission a makarantar da Sadiya take saboda na cewa Momy na gama komai tafiya ta rage”.

Shuru Farooq yayi na wasu yan da’ki’ku alamar nazari can ya numfasa yace “haba Sadeeq wai meke damun ka meyisa kake son ka kuntatawa yarinyar mutane wani irin makarantar kwana ana zaune ‘kalau don Allah kajanye wannan maganar kaji tausayin ta

Har yanzu fa Siddy yarinya ce karama na tabbatar ma batasan maye aure ba da tasani wallahi da…”. Bai karasa maganar ba Sadeeq ya dakatar dashi da cewa “malam don Allah ba shawara na tambaye ka ba

Dan kaga na biyo ta hanyar ka shine zaka tozartani idan baza kaimin ba kawai ka fadamin”

STORY CONTINUES BELOW

“Allah ya huci zuciyar ka”. Farooq ya fada kana yace “aji nawa za a sata?”.

“Ko js1 ne asata ba matsala ta bace zan fi son haka saboda na more soyayya ta da Baby na kan tagama karatun”

Farooq nason yace wani abu amma gudun kar yakara laifi yace “babu damuwa zanyi kokari insha Allah ko js2 su kaita”.

Daga haka sukayi sallama

Bayan Sadeeq ya gama faking din motar sa ya fito jinsa yake wani iri saboda haka ya haura sama bai kai ga shiga dakin ba yaga kofar abude yayi mamaki bai gama tsinkewa ba sai da ya shiga bedroom din sa ran sa a mugun bace ya karasa kan gadon da niyar fusgo ta amma sai yaji kamar an soka masa kibiya a cikin sa bai san sanda ya zube a kan gadon ba numfashin sa nafita da sauri da sauri Siddeeqah garin juyi ta wurga wa Sadeeq kafa ransa bace ya wur ga mata harara tuna aikin banza yayi tunda bacci take yi ya shiga kwala mata kira “ke ke uban wa ya ce ki shigo nan?”

Siddeeqah da kamar a mafarki taji ana kiran ta a fir gice ta bude idanuwan ta suka sauka akan na Sadeeq dake mata kallon tuhuma fuskar sa a murtuke babu alamar wasa yace “dan uban ki uban wa yace ki shigo min daki?”.

Siddeeqah gaba daya ta rike ce bakin ta na rawa take fadin “lah yah…!”.

“Yayan uban ki zakiyi bayani wallahi bazaki sauka ba sai na yi ball da ke”.

‘Kokarin tashi yake amma cikin sa ya kara murde sa nan take ya rike cikin yana kiran sunan Allah a rude Siddeeqah ta ‘karasa gurin sa ta kama hannun sa “yaya yaya meke damun ka haka me yasa meka”.

A wahalce Sadeeq yace “cikina”. Kama hannun ta yayi ya dora a kan cikin sa ji tayi kamar akan shocking ya d’ora mata hannun saboda haka tayi sauri ta janye yaya bari naje na kira Momy saboda ni bansan mai zan maka ba zata sauka kenan Sadeeq ya kama hannun ta idon sa a rufe yake cewa “kar ki tafi ki banni kizo dan Allah kada ki tafi” cikin karfin hali ya janyo ta ya matse ta a jikin sa yana fitar da numfashi da sauri da sauri

Gaba d’aya jikin Siddeeqah rawa yake ta kasa fahimtar mai Sadeeq din yake nufi da haka kokarin saka mata hannu a riga yake Allah ya bata sa’a ta kwace daga rukon daya mata tace “karamin dan iska ashe daman kai dan iska ne to bari kaji ni ba yar iska bace inace daga waje kake to ba kaje gurin ‘yan iskan naka bane?”

Sadeeq jin maganganun yayi kamar ta watsa mai garwashin wuta saboda zafin su gashi baya jin zai iya tashi bare yayi maganin rashin kunyar ta

Saida ta rike ‘kugun ta ta dawo gaban sa ta dan jujjuya tayi fari da idanuwan ta tace “karamin d’an iska to duk abinda kayi min sai na fada wa Momy saboda tun muna yara ake jamana kunne akan mukula da maza shine a waje ba a lalata ni ba yanzu kai ka lalata ni” take ta fashe da kuka tana fadin “na shiga uku yaya Sadeeq yayi min ciki innalillahi wa innah ilaihi rajiun Allah kagani ni ba yar iska bace shine ya taba ni waiyo Allah Momy zata yanka ni yaya Sadeeq ka cuce ni azzalumi Allah sai ya saka min”. Ta kara rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi

Sadeeq bai fahimci mai Siddeeqah take nufi ba shidai yasan ana ce musu ko hannu suka bari namiji ya rike musu zasu dauki ciki to yana ga shiyasa yanzu take cewa yayi mata ciki? bai san sanda ya kwashe da dariya ba sai yanzu yake kara tabbatar da yarintar Siddeeqah kallan ta yayi suka hada ido tana rike da ‘kugu tana jijjiga ‘kirji

a yanzu yaji saukin murdawan da cikin sa ke mai saboda haka ya kamo ta cikin zafin nama tana ta zizzille wa saida ya daidai ta natsuwar sa ya koma mata Sadeeq din da tasani ada yace “ke dan uban ki ni kike cewa dan iska?” ta tsorata da yadda taga yanayin sa saboda haka ta shiga yi masa magiya da bige bakin ta

Yace “babu ruwana ki daina buge bakin ki idan kina so kada na zane ki to kija bakin ki kiyi shiru da abinda ya faru a tsakanin mu ko Khadeeja kada ki fadama mata bare Momy idan kika yi haka kin tsira saboda nima bani nayi miki ba aljanu na ne suka miki kuma kin san aljani bai san a dunga talla da abinda ya aikata sai ya makantar da ke ko ya kurmun taki saboda haka kija bakin ki kiyi shiru kuma ki tabbatar babu wanda ya ganki a lokacin da zaki fita daganan “.

Bakin ta narawa tace “to yaya”. Sai alokacin ya sake ta ta nufi kofar futa daga bedroom din duk ta dabur ce ko dan kwalinta ta manto shi gashi kanta babu kitso sai yanayin ta ya nuna kamar bata cikin hayyacin ta tafiya take tana sand’a a haka ta fito daga ban garen sa tana gaf da shiga dakin Ummi taji ance “daga ina kika fito?”. A dabur ce Siddeeqah ta juyo ta kalli Momy da ta tsura mata idanu, cikin in ina Siddeeqah tace “daga dakin yaya nike dazun dana kaima sa a binci na tsaya kallo har bacci ya kwashe ni sai yanzu da ya dawo ya tashe ni”.

“Amma ya na ganki a furgice yayi miki wani abu ne?”. Da sauri Siddeeqah tace “babu abinda yayi min saboda daga bacci na tashi”.

Saida Momy ta kare mata kallon tsaf tace “kada ki boye min idan yayi miki wani abun fa kada daga baya azo asami matsala ki fada min gaskiya”. Siddeeqah naso ta fadawa Momy abinda ya faru tuna kashedin da Sadeeq yayi mata yasa tace “Allah Momy babu abinda yayi min ki yadda dani Momy”. Badan Momy ta yadda ba tace “jeki kada ki manta da adduar bacci”.

“To Momy saida safe”

“Allah ya tashe mu lafiya _________Washe gari da misalin ‘karfe 11:00 gaba d’aya mutanen gidan zaune suke akan dining ana breakfast har da Daddy saboda jiya da daddare ya dawo, kasan cewar yau din asab ranar hutu ce babu school a tsanake muke breakfast d’in mu

tunda ya doso gurin ‘kamshin turaren sa ya dake hanci na ya bud’e ilahirin gurin da sanyan yan ‘kamshin sa d’aga kaina nayi ai kuwa karaf muka yi ido hud’u dashi tsura masa manyan  idanuwa na nayi ko kifta su bana yi gaskiya yaya Sadeeq karshen had’uwa ne kansa na fara kallah gashin nan na kansa ya gyara sa sai kyalli yake yi masha Allah sajan nan nasa bakinkirin dashi a gyare gunin ban sha’awa da dan gemun sa da bai wuce kamu daya ba ?yana sanye cikin wata riga blue mai layi layi hannun ta anyi masa ninki biyu da wani botiri mai kyau da ‘kyalli sanye yake da wandon jus lite blue mai kyau da tsada kasan bai kama sa sosai ba ban san sanda na bude baki da hanci ba na cigaba da kallon sa ashe  Momy ta lura da ni kawai magana ce bata yimin ba shikuwa gogan da ya ‘kara so kan dinning din sai yazo yayi kamar zai wuce ta kusa dani ya take min yatsun kafa ya   murza da karfi yayi gaba kamar bashi ne ba+

Wata uwar ‘kara na kwalla ina yarfe ‘yan yatsun hannu na gaba d’ayan su ido suka zuba min da son jin mai ya same ni wasu hawaye ne masu zafi suka fara kwaran yo min saboda naji zafin murje min yatsun ‘kafa da yayi “Sadeeq mai kayi mata”. Daddy ya fad’a yana duban sa zaman shi kenan akan kujera ya fito da ido waje alamar firgita yace “ni kuma Daddy yanzu fa na iso ko magana banyi mata ba”. Jinjina kai Daddy yayi alamar gamsuwa ya waigo ya kalleni yace “mai sunan manya me  ya sameki ne?”.

Ina shash-shekar kuka nace “yaya ne ya murje mun yatsun kafa na kuma ban san mai nayi masa ba”.

Gaba dayan su maida kallon su sakayi ga Sadeeq da ya curo waya yake dannawa a hasale Daddy yace “ai kaji abinda tace”. Fuskar  tausayi yayi ya dube ni yace “yarinya kiji tsoran Allah zaki mutu ki fad’i gaskiy saboda ni kinga da na shigo ma ko kallan ki banyi ba, ko dai aljani ne yayi miki siffa ta ya taka miki ‘kafa saboda ace ni ne?”.

Ido Siddeeqah ta ‘kura mai sai alokacin ta tuna yace yana da aljani idan ko hakane shine ya aljanin ne ya taka ta Allah sarki bai san yayi ba ashe

Kallan ta ta mayar akan Daddy tace “kamar yadda yaya”. Yace “ko aljani ne yayi siffar sa inaga hakane saboda wallahi…”.

“Ya isa”. Jiddah ta fad’a tana wuci kamar wacce aka mata wani abun ta d’ora da cewa “malama kada ki raina mana hankali na dad’e da sanin ke makar ya ciya ce ba tun yau ba saboda kinga Momy da Daddy suna goyan bayan ki sai ki dunga ‘kullawa yaya sharri ke ga annamimiya kina shiga tsakanin d’a da uwa wallahi…”

Tau tau! ‘karan marin da Siddeeqah ta wanke Jiddah dashi kowa a wurin mamaki yake! banda Sadeeq saboda yafi kowa sanin halin ta shammatar ta ta kuma yi ta dad’a mata wani tas! ?Gaba daya ji da ganin Jiddah sun tsaya cak sai wasu tau rari da take gani can kuma duhu ya rufe ta

ran Siddeeqah a ‘bace ta cukwuikwuyi wuyan rigar Jiddah “wallahi yau koni ko ke sai naji dalilin da yasa ki ka kirani da annamimiya”.

Tuni idanunun Jiddah suka furfito waje saboda sha’kar da Siddeeqah tayi mata daman ita ba wata mai ‘karfin azo agani bace sai tsinanniyar tsokana da kin ma’kure ta ta koma fuskar tausayi gashi ita kuma Siddeeqah babu hakuri wani lokacin har jira take ka taba ta tayi rashin mutunci yau jin zuciyar ta take asama saboda haka ta fara kaiwa Jiddah naushi a baki tana fad’in “wallahi saikin fad’a min inda na had’a  d’a da uwa idan ba haka ba mai…”.

“ke sake ta kafin na tashi na ‘babballaki”. Sadeeq ya fad’a yana nufo inda nike ni kuwa bil ha’k’ki naushin Jiddah nike abaki yanzu haka na fasa mata yana zubar jini

“Kada ka sake ka buge ta zan ‘bata maka rai saboda tayi min dai-dai tunda ba da ita ake yi ba ta ara ta yafa yanzu Khadija da Ummi da basu sa baki ba ai ba ayi dasu ba”. Momy ce tayi wannan maganar zaiyi magana Daddy yace “nima ai tayi min dai-dai saboda haka ko kallon banza ban yarda kayi mata ba”.

Khadija dai bazan ce taji dad’i ba saboda ita bata san fitina kana kallon fuskar ta kasan ba a yanayin jin dad’i take ba Ummi kuwa saboda farin ciki bakin ta ko rufuwa bai yi har kai naushi take kamar ita ke dukan saboda ba wani shiri take yi da Jiddahn ba kasan cewar ta ba ‘yar Momy ba yar yayan Momy ce wato kanwar Naseer da ke ‘kasar India karatu tun sanda mamar su ta rasu ta dawo gurin Momyn da zama a lokacin tana da 7 year’s old kuma ita ma sa’ar su Siddeeqahn ce a ran ta tace “da jiya na biyema Jiddah da da ni za a fara” soboda sanda ta shiga kitchen ta tarar da ita tana hada tea bata tanka mata ba ta hau fad’ar magan ganu kamar yadda ta saba

Umar har yafi Khadija damuwa saboda shi harda guntun hawayen

A lokacin da ya ‘kara so inda muke caraf ya d’auke ni daga kan Jiddah zai aje ni Momy tace “a a kasan fad’an Siddeeqah baya ‘karewa indai aka taba ta to sai ta rama kaita sama cikin dakin ka idan Jiddahn ta haura sama sai Siddeeqahn ta sauko”.

Ina ji ina gani yaya ya haura dani sama ba dan raina yaso ba dan ni da so samu ne a bar ni da ita na koya mata hankali saboda tana da raini da jin kai ni kuma bana jure wa dan ko babba ba ‘karamin nauyin sa ni keji ba idan har yaga yayi min ban rama ba

Kamar yadda Momy tace bai dire ni a ko ina ba sa a cikin falon sa ya maida kofar ya rufe da dan mukulli sannan ya zare ya saka a cikin al’jihun sa ya nemi kujera 2 cter ya kwanta ya lumshe ido

Sosoi bakin Jiddah ke zubar jini tuni Daddy ya wuce ban garen sa saboda yadda Jiddahn ke rusa ihu kamar wacce aka aikoma sa’kon mutuwa

Khadija dur ‘kushe gaban Jiddah cikin tausaya mata take mata sannu kana daga bisani tace “sannu Little sister zaki iya tashi mu tafi asbiti saboda aduba lafiyar ki?”.

Bata gama rufe baki ba Momy ta kara so daga tsaye tace ai daman ance jiki magayi gobe sai ki kara, ke kuma kin zo sai faman sannu kike mata ba ita tajawa kan ta ba? Maza d’auko mayafin ki kije ki” cewa “driver ya tada mota saboda ku kaita ayi mata dressing din bakin ta”.

“Wallahi Momy ko da ita ce da laifi bazan iya jure kallon ta cikin wani hali ba na kyale Siddeeka ne kawai saboda itama ‘yar uwa ta ce amma baki ji yadda zuciya ta ke mini ba a lokacin da abin ke faruwa”.

“Ai fa nan dama ke ki ka fi auki wajen  son yan uwan ki nasan ko kanki baki masa san da kike musu abu ne mai kyau amma ina baki shawarar da ki rage saboda kada wata rana ya za me miki matsala”.

Idanun Khadija ya kawo ‘kwalla ta dubi Momy tace “idan har kuna raye kuna ci gaba da samin albarka bazanyi da na sani akan ‘yan uwa ba ba insha Allah “.

“to Allah yasa”. Momy ta bata amsa tana barin gurin

Duban Umar Khadija tayi tace “kaje ka cewa Idi driver ya tada mota sannan idan ka dawo ka dakko mini gyale na dana Jiddah”.

About AIS

Check Also

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 8

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 8 Www.bankinhausanovels.com.ng  Momy ta ce “amma sai ka kai Siddeeqah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *