NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 2

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 2

Www.bankinhausanovels.com.ng 

_____Jin jina kai Inna tayi, sannan ta nufi hanyar d’akin da Momy take, ta ‘kwan ‘kwasa musu kofa, ta d’an jima a bakin ‘kofar, kafin Momy ta bud’e ta fito, “ina kwana hajiya”. Momy ta gaisar da hajiya+

cikin sakin fuska Inna ta amsawa surukar ta “ya ba’kun ta?”.

“Lafiya lau”. Momy ta bata amsa,

“to alhamdu lillah”.

A cewar Inna

ta dora da cewa “kiya ‘kuri na tashe ki kina tsaka da bacci”.

“babu komai Inna” cewar Momy,

Inna ta cigaba da cewa “daman Garba ne wai tun asuba yake ban d’aki”. Har yanzu bai fito ba, Siddi’ka tace “yau kamar bashi ba yana tayin wasu abu irin na taba’b-‘bu” shine nace “bari na tada ki muje bayin mugani ko lafiya”.

Momy tace “Hajiya Inna badon karkice na raina ki ba da bazani ba tunda shi bayajin magana”.

Inna tace “Ha’kuri zaki Aisha muje mugani ko lafiya kinga da ya idar da  sallar asuba yake tafiya gurin aiki, amma yau shuru”.

“To”. Momy tace badon ranta yaso ba, tabi inna ban ‘dakin

Koda su Momy suka ‘kara sa bakin bayin sunan shi Inna takira “Garba Garba”. kamar babu kowa a ciki, saboda bai amsa ba, saida Momy tace “sadeeq wai lafiyar ka?”.

Da wata iriyar  murya yace “wallahi Momy nima ban sani ba”.

Tace “au daman kana jin Hajiya na kiran ka kayi shuru, saboda ka raina mutane, ai sai ka fito ka bawa mutane guri, saboda gari ya waye”.

Yace “Momy bazan iya fitowa ba”.

“saboda me?”. Ta tambaya

Momy wlh yau Ban san me ke shirin faruwa dani ba, ko nayi gamo ne tun nafito sallar asuba na had’u da bala’i ko sallar ma banyi ba”. ?

Salati suka hauyi Inna natafa hannu kace “baka yi sallah ba tom wai me kake yi a cikin bayin ne haka?”. Cewar inna

Cikin jin zafin tambayar da Inna tayi mai sadeeq yace “Wai baki ji nace ina cikin bala’i bane, amma kike sake tamba ta”.

Momy ce ta daka mai tsawa “rufe min baki anan gurin ko na ci maka mutun ci, kuma kafito kabawa mutane guri suna son shiga bayan gida”.

Sadeeq yace “Amma Momy…”.

Katse shi tayi da “ko baka ji abinda nace maka bane”.

“naji”. Ya fad’a a ta ‘kaice,

d’an matsa wa suka yi nesa da bayin,

niku wa da tun tuni nike zaman jiran fitowar sa, da naji Momy tace “ya fito”. Sai Na ‘kara gyara zama na a kan kurer tsakar gida

Saida ya d’auki tsayin minti biyar kafin ya cire sakatar, ya bud’e ‘kofar ya fito, babu ko riga a  jikin sa, sai d’an gajeran wando, basu Inna kad’ai ba hatta ni da niyi  zaman jiran fitowar sa, saida na tashi tsaye saboda yadda yayi wani iri, kamar ba yaya sadeeq d’an gayu da ‘kwalisa ba

Yayi wani wuji wuji dashi ida nuwan sa sunyi jawur  se muts-tsuka su yake ga jikin sa duk ya karce sa da farce, harda shedan jini, ba ‘karamin ciwuka yajiwa jikin sa  saboda susa ba, hatta da fiskar sa bai bari ba akwai alamun karta, duk ya fad’a fuskar nan yayi zuru zuru,

mamaki ne kwance a kan fusko kin su Momy

Momy tace “Wai sadeeq me ke damun ka haka kamar me borin jini?”.

STORY CONTINUES BELOW

“momy nima bansani ba”. Ya bata amsa

Yanzu yaji sau ‘kin ‘kai-‘kayin da jikin sa ke yi, sai dai rad’ad’in da fatar jikin sa ke mai,

“to ai saika je ko jallabiya kasa mutafi asbiti”. Inji Inna,

“A a Inna ba sai kunje ba don asbitin gari zani kuma da nisa ku zauna a gida”. Ya fad’a yana tafiya

ta kusa dani yazo wuce wa, saida muka yi  ido hud’u  dashi  na kwashe da dariya?

kallan tsana yayi min, sannan yanu foni dagudu na mi’ke nanu fi bayan Momy ina haki, biyoni yayi shima,  da hannu Momy ta da katar dashi san-nan tace “amma walahi sadeeq kaji kunya kanwar kanwar ka itace abokiyar yinka, ba dole ta raina ka ba,

Wallahi ka bada maza wuce kabani guri, kamin ki’kam a gaba kamar wani soja, Ko wannan iftila’in daka fad’a be isheka ishara karabu da yarinyar mutane ba”. Momy ta fad’i haka tana nuna mai hanya da hannu

Badon yaso ba saidan yabi umarnin mahaifiyar sa,

had’a ido muka yi dashi nayi masa gwalo ina ‘kara yin dariya ciki ciki?

Yace “Zan kamaki  yarinya wallahi zakiyi bayani”.

Inna tace”Ai gashinan alhakin tane wannan abin da ke faruwa da kai, saboda Allah ba azzalimi ne ba saidai bawa ya zalinci kansa”.

“Kwarai ma kuwa”.  Momy tace

Jikin sa babu ‘kwari  ya wuce mu, tashi nayi nima nakoma d’aki, saboda na gabatar da sallar a subahi, sai a lokacin nayi sallar takwas saura, ina idar wa ko kan sallaya ban sauka ba nahau rawa da juyi, saboda na rama a binda sadeeq yayi min gado na koma saboda yau bazan je ‘yar kasuwa yin tsokanar safe ba bacci zan koma

♾️♾️♾️♾️♾️

Abangaren sadeeq kuwa koda yaje asbiti, kulawa ta mu samman suke bashi saboda asbitin su na ‘yan sanda yaje har gado aka bashi sannan aka saka mai ledar ‘karin ruwa, saboda yana bukatar ruwa ajikin sa

Harda allurar bacci a kamai saboda ya sami hutu

♾️♾️♾️♾️♾️

Koda na farka daka bacci ‘karfe sha d’aya saura11:00am naji dadin baccin sosai domin ya ragemin damuwa

Kamar yadda nasaba idan natashi bacci mi’ka nayi  babu ko salati, na sauka daga kan gadon, na d’auki brush d’ina na fito tsakar gida nayi, san-nan nanufi falon hajiya, acan na iske su Khadija suna cin waina da miya,

zama nayi kusa da Momy nace “ina kwana Momy”.

“lafiya lau”. Tace min “kin tashi lafiya?”.

Nace “eh Momy lafiya lau”. Saboda ni bana son doguwar gaisuwa

Tace “ba inda ke miki ciwo?”.

kai na d’aga mata

“madallah” ta ce masha Allah haka ake so

Inna na kallah naga ta tasa kwad’an zogale da kuli a gaban ta sai kaiwa baka takeyi,  d’an Murmushi na sakar mata,  ita ma ta maido min

Kana na gyara zama, na saka hannu a kular wainar su Khadija, ina ci ina lumshe ido saboda dad’i

Nace  “Inn wai wannan wainar wane gida ce”.

Tace “ta gidan su fulera ce matar d’an tsohon”.

“Haba koda naji”. Nafad’i yaka yayin da nike kai lomar waina a baki na

“Kice kinyi santi” Murmushi nayi kawai na cigaba da ai kawa cikina

Umar ma cewa “yayi ni rabon da naci

Waina me dad’in wannan wallahi na manta”.

“Umar duk santin ne haka”. Inji Khadija

Yace “ai kokema kinyi tunda naga kun-nen ki d’aya sai rawa yake yi”.

Kowa a d’akin saida ya dara

♾️♾️♾️♾️♾️

Bayan Sadeeq ya farko daka nan nauyan baccin da ya d’auke sa,  jikin sa babu kwari ya tashi a za filo a bayan sa ya jingi na, yana jin gaba d’aya jikin sa na mai ciwo, ga wata yunwa da ta ad’da beshi da kasala

Likatan ne yazo ya zauna agaban shi dayike a bokin sa ne kuma shima d’an sanda ne, yace “wai sadeeq dame kai amfani ne?”.

d’an shiru yayi kafin yace “nidai a binda nasani natashi da a suba lafiya ta ‘kalau amma da bayan na d’auki buta ta, naje bayi na dowo nafara jin yana yi na yana can zawa, koda na fara alwala ko fiska ban gama wan kewa ba, tsarkin da nayi yafara damu na,

Sai nasa aka kai min ruwan wanka, to na ‘kar-‘kare maka zance, daka zuba wannan ruwan a jikina kid’an ya sauya salo, sai azabar ta ‘karu bayan na sa a mi’ko min sabulun wanka, ba ba nasha wuya fa  sosoi, tun asuba nike a cikin bayi nine har ‘karfe ta kwas saura, wannan raunin duk ni najiwa kaina, saboda ‘kyai-‘kayin da jikina yayi min idan ban sosa ba bana jin dad’i”.

Dariya sosai Dr Farooq ya keyi, Sadeeq yace “dr banason iskanci fa nifa ban baka labari don kayi min dariya  ba, sai dan kayi  aikin ka”.

Dr Farooq yace “ba ba wallahi labarin naka ne gunin ban dariya, sai kace a cikin shirin film”.

Duka Sadeeq yakai wa Dr Farooq d’in, amma sai ya kau ce yana fad’in “shege ka samu kenan d’azun kamar wani lagwani kana ta num-far fashi kamar baza ka kai aniji ma ba”.

Sauko wa sadeeq yayi daga kan gadon, Dr Farooq yai saurin mi’kewa, d’akin suka fara za gayewa, Farooq d’in ya’ki barin sadeeq ya kamasa,

Dan kansa Sadeeq d’in da ya gaji ya ha’kira, ya janyo kujera ya zauna yana maida num-fashi, ruwan sanyi Dr Farooq ya d’auko a ciki firiji ya mi’ko masa, yana fad’in “maganin d’an iska kenan gobe ma ka ‘kara”.

Sadeeq d’in amsa kawai yayi be kula sa ba _______Ya ansa gorar ruwan ya fara  sha, saida ya shanye ruwan tas sannan yace “malam kayi min ba yanin matsala ta nasan dai ba waccar matsalar bace”.+

“Eh ba ita bace” Farooq ya bashi amsa

“Amma a bisa bin ciken danayi ya nuna kayi amfani da abu mai saka fatar jikin d’an Adam ‘kai-‘kayi acikin ruwan da kayi amfani dashi, sannan shima wannan rad’a d’in da kake ji kayi amfani da abu mafi zafi ajikin fata, shiya sa yake maka wannan rad’a d’in”. Dr Farooq ne yayi wannan bayanin

Shuru sadeeq yayi kamar meyin nazarin wani abu, be tuna komai ba, Dan haka ya ta’be baki yace “Nidai nasan ban saka komai cikin buta ta ba amma zanyi bincike, saboda abin da mamaki”.

“Dadai yafi”. Farooq ya bashi amsa ya kuma cewa “katashi muje akwai magun-gunan da zan rubuta maka zasu temaka sosai, wajen  rage maka rad’a d’in da kake ji”.

♾️♾️♾️♾️♾️

Ina zauna a kan kujera a tsakar gidan mu, ina dakan kayan miya yamma ne lilis, saiga Ladiyo kawata nan

Ta shigo jiki duk kwata, tun daka nesa nike d’aga mata hannu, saboda kada ta ‘karaso inda nake, bazan iya jure shakar warin kwatar da ke jikin ta ba

Ida nuwan ta  jawur dasu, alamun taci kuka ta ‘koshi,

saida nayi dariya mai isa ta san-nan nace “ya akayi ne Ladiyo

Ki kayi wanka da kwata a jikin ki kamar sabon shiga hauka”.

takaici na ne  ya ishi Ladiyo na dariyar da nike mata, kamar jira take na tambaye ta

Cikin shash-she’kar kuka take cemin “Umma ta ce, ta aike ni na kai mata ni’ka, bayan nakai annu’ko min akan hanyata ta dawo wa gida na had’u da su Habibalo, itada Larai sukai ta zagi na, na’ki kula su ni kuma, nayi ‘ko ‘karin ganin na cigaba da tafiya ta, amma suka hanani wuce wa, wai sai nayi dambe”. can saiga Atinen Malam Bala nan Shine tace “wa na kama wai jiya ni dake munwa ‘kanwar ta duka”.

“Ha’kuri na fara bata amma suka samin dariya, wai wallahi sai sun rama wa  ‘kan warsu dukan da da kika yi mata, shine suka had’u suka yimin dukan tsiya, san-nan suka jefani a cikin kwata”. Ta ‘karasa maganar hawaye sabbi suna zubo mata ta ciga ba da fad’in “basu tsaya iya nan ba saida Suka zubar da ‘kullun wainar da na markad’o”.

Wata muguwar dariya ce ta ‘kwace min ban san da zuwan ta ba, saida nayi mai isa ta

San-nan nace mata “wallahi Ladiyo ke sakarya ce ki ka tsaya kamar kayan wanki suka jib geki

?Baki iya koda mintsilun su ba, Hhmm ai da ni ce koda ya ‘kushi da cizo saina rama, kindai san hali na”.

“Ni yanzu da ki kazo ki ka fad’a min inyi miki me? ai da zuwa gida ma ki kayi  Umman ki ta miki dukan da zata miki da tuni ya wu ce, amma a nan kina ‘karawa kanki laifi ne a gun umman ki, kuma kin santa da jaraba”.

Wani sabon kuka Ladiyo ta kuma  fashe wa dashi,

ni kuwa sai ‘kyal-‘kyala dariya ni keyi harda rike ciki abin nema ya samu

dundu naji an d’uma min a baya na, Inna ce na gani,

tsuke baki na nayi nace “Inna kin samin ‘kashin mundi-ri’kin ki ai saiki karya ni”.

Cikin jaraba irin ta tso-faffi Inna tace “ja ira ba ke kika ja mata du kan ba, amma tana fad’a miki kina yi mata dariya”.

Ta juya ta kalli inda Ladiyo take tace “kema ai da naki laifin, Ladiyo kina san kiyi tsoka na amma ba kida ‘karfi, kuma tsoka na ta mara tsoro ce, tunda ba zaki iya cire tsoro ba, sai kide na biye wa Siddi’ka idan ba haka ba wataran karyaki za ai”.

STORY CONTINUES BELOW

Jin Inna tace za’a ‘balla Ladiyo yasa na ‘kara kwashe wa da dariya

cikin takaici na Ladiyo tace “ke ai  sunce idan suka kama ki ‘balla ki za suyi”. Ko waccen su tace “tana da cikin ki”.

Wani ‘katon a shar nayi, Inna dake kusa dani tace “A uzu billah”.

Naci gaba da cewa “ke ma kin sani kaf ‘kauyen nan, na ga gari uban kowa, na wuce ayi min harara bare zagi, kinga ina za aje ga duka, ke dai da ki ke sakarya sai kita tsayawa tunda sun gano lagwanki”.

Momy dake jinmu tunsanda Ladiyo ta shigo gidan, tazo ta mi’ko min kud’i 1000k tace “ungo mi’ka mata ta kaiwa  mamar ta”.

Saida na amsa kud’in san-nan nace “wallahi Momy dan  kece da bazan iya zuwa inda take ba, ba kuji yadda gidan nanan yad’au ka ba?”.

Duka Inna ta’kara kai min a karo na biyu, amma sai na kauce ina fad’in “ba zaki ‘karasa ni tun kafin lokaci na yayi ba da saura na”.

“Sha-‘kiyi ya”. Tace min har Talle ne zai yiwa Uadi gori?”.

“tab wai me kike nufi?”. Nace da Inna “ni kika yadawa magana ko wa?

Yo ai ko ke ba zaki nuna min wanka ba bare Ladiyo”.

Na ‘karisa fad’a ina murgud’a baki

Hanci na na toshe da dan kwali na san-nan na nufi gurin da Ladiyo take a tsaye, nesa kad’an da ita natsaya nace “mi’ko han-nun ki” mi’ko han-nun nata tayi, na saka mata kud’in nace “yau Allah ya ‘kwace ki wajen Umman ki, da kinci duka biyu”.

Godia Ladiyo tayi wa Momy sosai, zata wuce nace mata “mu had’u a yar kasuwa anjima”. da “Tom” tabani amsa

Inna kuwa sai mita take wai Ladiyo bata da wayau, Momy na bata ha’kuri tana cewa “sha’a nin yara kenan sai  ha’kuri”.

♾️♾️♾️♾️♾️

A bangaren sadeeq kuwa yana dawo wa  gida ana kiran sallar magriba, d’akin sa yabud’e ya ajiye ledar maganin da Dr  Farooq ya rubuta mai shi kuma ya siyo, saboda ba suda shi a abitin su kuma yace “zai rage masa zafin rad’a d’in da kaye ji”.

  Fi towa yayi daga gidan, yanufi masallaci, anan yayi alwala aka gabatar da sallar magriba da shi, bayan an idar mutane sun fara raguwa ya mi’ke, saboda ya biya bashin sallo lin da ake binsa, ai kuwa ya fara jero sallolin saida ya idar dasu  kaf, ashe a kwai wani mutum da ya lura da Sadeeq d’in, tun sanda yafara sallar, ba ‘kara min ma-ma-ki yayi ba da yaga matashi me jini ajika irin sadeeq ya tsaya yana had’a sallah

Beyi ‘kasa a gwuiwa ba, yaje ya mi’ka masa hannu saka yi musa baha, kana yace “yalla’bai Allah yasa dai lafiya naga sai salloli kake jerowa kuma ga dukkan alamun ba nafila bace farrila ce, saboda tun sanda ka fara nike lura da kai”.

shiru sadeeq  yayi, saida ya gama ‘karewa mutumin kallo tsaf dat-tijone dan gashin kansa ma a kwai fur-fura, gwau ran numfashi Sadeeq ya sauke, saboda bai san ya dat-tijan zai d’auki lamarin ba, amma zaifa d’a mai gaskiya tunda shi ya bu’kaci jin dalili

Bayani sadeeq d’in ya shiga yimai dallah dallah, a kayi sa’a dat-tijan ya fahimce sa, Fatan samun lafiya yayi masa, daga bisani ya mi’ka masa hannu suka kuma yin sallama dat-tijan ya tafi

♾️♾️♾️♾️♾️

Siddi’ka kuwa bata samu fita daka gida ba sai bayan sallar Isha’i koda Allah yabani sa’a nafi ta daga gida, ina tafe a   hanya ina tsokanar duk Wanda naci karo dashi, raina fes saboda Izuwa yanzu nayi tsokana har ba a dadi, nafi tare masu yin talla kuma nace “dole sai munyi dambe”. Duk wanda ya’ki biye min ayi sai na zubar masa da abin tallar na ruga da gudu ina dariya

Hankali na kwan ce nike tsoka na ta yanzu haka wata me gyad’a na tare, nayi nayi da ita muyi dambe amma ta’ki tace “ba abinda ya futo da Ita kenan ba”. Saida nayi shewa kamar ina gidan biki nace “yo ni abinda ya fito dani kenan ko kina so ko bakya so sai munyi dam-ben nan”. Na ‘karasa fad’a ina ‘ko ‘karin kama tiren gyadar, ban lura da kowa a gun ba ido na ya rufe, naji caraf an dam’ke min hannu, koda na waigo da kaina saboda nayi masifa, sai naga yayan yarinyar ne fuskar sa a murtuke babu alamar wasa yace “yau me ra bani da ke a gurin nan sai  Allah, zakici ubanki daman na dad’e ina Addu’ar irin wannan ranar sai gashi kin kawo kanki har gida, saboda kin addabe yaran unguwa ko ina yara labarin ki suke yi, kuma gaki ‘yar ‘karama bare nace jiki gareki kike tsorata su dashi”.

STORY CONTINUES BELOW

Sai yanzu na ‘karewa layin kallo a she a ‘kofar gidan su yarinyar nike

Inada taurin kai bazan ta’ba iya bashi ha’kuri ba, ko da kuwa zai kashe ni, cikin ‘karfin hali nace “dalla malam ka sakeni ko nayi maka sharri”.

ya d’aga han-nun sa da zummar ya mare ni, sai yaji ance “‘kara mata”.

Sai da gaba na yafad’i, saboda me muryan ko a mafar ki naji yayi magana sai na gane, bare kuma a zahiri

sauke hannu sa yayi, ya fasa mari na, ya maida duban sa izuwa inda yaji maganar, saiga yah Sadeeq ya bayyana cikin takun sa na isa da ‘kasaita

Har inda muke ya ‘kara so  be tambayi ba’asi ba, yaciro belt d’in wan-don sa yace wa matashin “ungo wannan kazane ta dashi nake ga kamar zaifi shigan ta kuma han-nunka baze maka zafi ba”.

A tsorace matashin  ya kalli yah Sadeeq saboda ya shaida shi kuma yasan ni kanwar sa ce

Cikin in-inar magana matashin yace “yalla’bai nama ha’kura tunda kayi magana”. sai a lokacin ya sakar min hannu

Da alamar yah sadeeq ba haka yaso ba, so yayi a daka ni, dan yabud’e baki zaiyi magana kenan na falla da gudu ina cewa “Allah ya isa ban yafe ba ku duka ‘kartan banza, masu fad’a da ‘yar cikin su”. ?

Duk kansu sunji a binda nace saboda na d’aga murya ta sosai, kuma dama haka nike so, shi dai mata shin ma-ma-ki abun ya bashi, a cikin ransa yake cewa “yalla’bai guda nama wannan rashin kunyar tabbas tunda nawa yalla’bai babu wanda bazan mawa ba”.

Yah sadeeq yanada Alheri bashida rowa yana so ya kyauta ta wa na ‘kasa da shi, saboda haka ya ciro kud’i daga aljihun sa ya bawa matashin ‘yan Naira Ashirin sababbi gada gal

Matashin ya ansa yana mai godiya 

Ban dawo gida ba sai 10:00 pm saura kamar dai jiya, bana kallon gaba na a guje na shigo cikin gidan, yah Sadeeq da d’auko kular a bincin sa kenan, na buge sa abinci ya zube, koda na lura da abinda nayi d’aki na na shige aguje  na saka saka ta, ina maida numfashi

su momy sunga abinda yafaru

Gurin Inna ya koma “Inna ina abincin yarinyar nan?”. Ya tambaye ta

“gayi can”. Tanu na masa wani kano dayike arufe cike da shinkafa da miya harda d’an naman kaza, d’auka yayi zai fita

Momy tace mai  “dawo mata da abincin ta kafin na  sa’ba maka”. Inna ce ta katse ta da fad’in “haba Aisha yanzu ai itace da laifi bakiga yadda ta zubar mai da abin-cin sa  ba, kuma idan bana tan ba mai zaici? kinsan Garba baicin abin-cin waje sai na gida, gashi dare yayi bare a sake girka masa wani”.

Ta cigaba da cewa “mutumin ma da ba lafiya gare sa ba”. yanzu fa yake ce mana “saida aka ‘kara masa ruwa da yaje asbiti kuma ance saiya ci abinci sannan yasha magani”.

“tunda ba tajin magana ita ta kwana haka, yi tafiyar ka Garba kaje ka ci abin cinka”.

Yace “na gode Inna” ya fice daga falon

khadija kuwa cewa tayi “wai Inna ina Siddi’ka ke zuwa ne haka idan tafita sai  dare take dawo wa kuma ba’a sanin sanda take fita”.

“Ina kuwa zata in ban da yar kasuwa, ai nan take zuwa taita tsokanar muta ne Sam bata san zaman gida, karatun ma yanzu taki shi kwata kwata, babu muhammadiya babu na zamani”.

“Allah ya kyauta” khadija tace “amma wallahi Sam Siddi’ka bata wa kanta adalci ba saboda a wannan zamanin ilimi shine kan gaba”.

Momy ce tace “ai gobe Daddyn ku zai zo inaga da ita zamu tafi, Hajiya saidai kiyi ha’kuri, tunda bazaki bimu ba, ko yar aiki sai a d’auko miki, amma karatun Siddi’ka yana da mutu’kar muhim-manci, idan ba abar ta tayi ba tom nan gaba bazata gode mana ba, zata d’auke mu a matsa yin azza-lumai ne”.

jin jina kai Inna tayi alamar gamsuwa tace “Allah yasa haka shine mafi alkairi”.

Umar ne yazo ya buga min ‘kofa daga ciki nace “waye anan?”.

“Umar ne”. Yace

Na bud’e masa ya shigo na maida ‘kofar na rufe, kamar dai jiya, yau ma tambaya ta yayi labarin abinda yafaru, na kuwa bashi labari harda had’uwa ta da yaya Sadeeq, yayi dariya sosai amma yace min “yayi fushi tunda ban nemeshi ba sanda zan tafi”.

Ha’kuri nashi ga basa da cewa “nima bansan zanyi nisa ba naje siyo alewa ne, naje da kai gobe”.

Yace “uhm abinda gobe Daddy zaizo kuma gida zamu tafi

Ji nayi gaba na na fad’uwa, amma saina daure nace “da gaske gobe Daddy zai zo?”. Umar yace “eh wallahi nima a bakin Momy naji”. Nace “to Allah ya kawo sa lafiya”.

“Ameen” Umar ya fad’a

“ina yaya Sadeeq?”. na tambayi Umar

Yace “ya d’auki a bin cin ki ya tafi d’a kin sa, kin san baida lafiya”.

ban san sanda dariya ta ‘kwace min ba,  saboda na manta da abinda yafaru, sai  yanzu da Umar ke fa d’in baida lafiya na tuna,

“wai lafiya yarki. Aunty Siddi’ka?”.

Nace ‘kalau Umar wani abu na tuna, shiyasa kaga ina dariya”.

“Muje tunda wancan mugun benan ko Indomie na girka don yunwa nike ji”._______Yana yin tsarin ginin gidan mu 2 bedroom ne amma a ko wani d’aki anyi kofar da mutum zai iya bi ba sai yabi ta falo ba, sai d’akuna biyu da suke a tsakar gida d’ayan na hanyar waje shine d’akin yah Sadeeq,sai wanda idan su Momy sun zo suke sauka a ciki, a kwai kitchen a tsakar gidan da bayi,+

Inna bata son amfani da kitchen din d’aki tafi sabawa da na waje,

amma ni nakan yi amfani dashi idan zanyi jagwal-gwa-lo na

Kitchen d’in na shiga na bud’e durowar da nasan muna ajiye Indomie a cikin ta na dauki guda d’aya

Gas na kunna ruwa na fara tafasa wa nazuba Indomie d’in sannan nakawo tarugu 1 nasaka nazuba mangyad’a a ciki ina juyawa, sai ga Khadija tale’ko kitchen d’in cikin zolaya tace min “ga yaya Sadeeq can afalo”.

yace “mai kwatar ki yau sai Allah”. Inna tayi bacci tun d’azu, Momy kuma ta tafi d’aki, daga ni sai Umar ne a falo.

hantar ciki na ce tafara kad’awa jikina yafara rawa na kasa magana, bani da tsoro amma ina tsoran had’uwa ta da yaya sadeeq saboda ba da wasa yake min ba, amma duk da haka idan rashin kunya ta, ta tashi ina yimasa

Ad’an kid’ime nace “bari na fasa ihu tun kamin yacin min kinga su Momy za suji su zosu zo su cece ni”.

Saka tafin hannaye na nayi na toshe kunnu wa na, saboda inyi ‘karar iya karfi na, zan ‘kwal-lara ‘kara kenan Khadija tayi saurin toshe min baki da tafin hannun ta, tana ‘kyal-‘kyala dariya

Tace “nad’auka ked’in jaruma ce a she ba haka bane kamar ba kece shekaran jiya kika cemin sai kin rama dukan da ya miki ba, taya zaki rama kina wannan tsoran?”.

“Kedalla malama sakeni nayi ihun neman agaji”.Nace mata

Tana dariya tace “tsokanar ki fa nikeyi”.

Sai alokacin nasaki ajiyar zuciya, nabi ta da duka ta fita tana dariya,

koda na duba Indomie na har ta dawu ta fara kamawa, kashe gas nayi, anan kitchen d’in na zauna, a cikin tukun yar naci, inaci ina santi saboda tayi mini dad’i kuma nayi mata irin  dahuwar da nikeso

Bayan na gama ci ne, na bud’e baki na sosai na saki wata uwar gyatsa babu ko alhamdu lillah

Na mi’ke tsaye nayi  mi’ka

D’aki na na wuce inda natar da Khadija na sharar baccin ta hankalin ta kwance, kan gadon nima na hau kusa da ita na kwanta ina jina wani iri kamar wani abu zai faru dani

Washe gari ban farka da asuba ba sai Misalin 8:9am Khadija babu irin tashin da bata yi min da asuba ba, akan nayi sallah amma na’ki sai ma ‘kara gyara kwan ciya ta da nayi, Kamar yadda nasaba tashi haka nayi babu ko addu’ar tashi daga bacci, na sauka a kan gadon, brush d’ina na d’auka, ina tatsa makilin ne Khadija ta shigo fiskarta d’auke da  murmushi, da ganin bakin ta a kwai magana, “au ashe kin tashi daman ke nazo tasa wallahi”. Ta fad’a tana matsowa kusa da ni

“eh na tashi” nace mata “wai yanaga kina ta murmushi ne?”.

Tace “ba dole ba Daddy fa yazo” shi yace “na taso ki saboda ya tambaye ni kina ina”. Nace kina bacci”.

“amma wannan karon yazo dawuri gaskiya” nafad”a ina ajiye makilin d’in hannu na

Tace “Eh”. naji yana cewa Inna “da karfe 2:pm jirgin su da zai wuce lagos zai tashi shiyasa yayi sammakon zuwa”.

Jin jina kai na nayi, alamar gamsuwa “to bari nayi sallah” nace tare muka futo  ta nufi d’akin hajiya Inna

Ni kuma na nufi rijiya na janyo ruwa na zuba a bokitin wanka, na kai bayi saida na fara yin wanka sannan na d’aura al’wala

STORY CONTINUES BELOW

Tawul na d’auro ajiki na, amma irin ‘katon nan ne, kuma na wanke kaina babu ko d’an kwali haka na fito daga cikin bayin

Adai-dai lokacin yah Sadeeq ya shigo cikin gidan, had’a ido mukayi, saida ya ‘kare min kallo tsaf, sannan yaja dogon tsaki, shasha ya fad’a afili, kana ya wuce ya shiga cikin falon

Saida ya wuce sannan nima na wuce d’aki na, wata doguwar rigar atamfa na ciro mai launin blue da ruwan hoda, baseline na sha a jiki na sannan na saka atamfar, na d’auki hijabi na nasaka na gabatar da sallar asuba

Bayan na idar na  nufi falon hajiya, ina jin gabana yana fad’uwa, narasa mai yisa amma tun jiya da Umar yace “Daddy zai zo” gaba na ke fad’uwa amman yanzu bugun zuciyar tawa yafi tsanan ta

Daure wa nayi, na shiga cikin falon baki na d’auke da  sallama, nasa mesu su duka harda yaya sadeeq d’in, suna karyawa, Daddy da Inna da yaya Sadeeq suna cin d’an wake,  Khadija Momy Umar. Kuma  waina suke ci

Daddy ne ya dube ni yace “wa’alaikum’ssalamu d’iya ta shigo ga wuri ki zauna, ya nuna min tsakanin sa da na yaya Sadeeq, na ‘karasa  na zauna a tsakanin nasu

Sannan nace “ina kwana Daddy”.

“Lafiya lau”. Yace min “na same ku lafiya?”.

“lafiya lau Daddy, ya hanya?”. nace

“Al’hamdu lillah “. yace min, yana mi’ko min cokali yace “bimismilah

me sunan manya”.

Ina lura da yanayin yah Sadeeq ya canza tun sanda na zauna, ya wani d’aure fiska sai mutsu mutsu yake yi, ina saka cokali na cikin kwanan yana cire nasa yami’ke tsaye, Daddy ne yakalle sa, yace masa “ya-ya ana cin abinci ka tashi”. na ‘koshi ne Daddy”.

“dawo ka zauna sai mun cinye da kai”.

Badan ran Sadeeq  yaso ba, haka ya dawo ya zauna ya maida cokalin sa, ina lura da yadda yake cin d’an waken kamar yana cin magani.

Misalin karfe goma 10:00am Daddy zaune a kan kujera Inna na kusa da shi Momy na 2 cter, ni da Khadija na zaune  a ‘kasa kusa da Momy, yah Sadeeq kuma na gefen Daddy zaune a ‘kasa kanshi a ‘kasa yana danna wayar sa

Daddy yayi gyaran murya

Sannan yafara da cewa “da farko ina ‘kara jad-dada godiya ta ga Allah ma d’aukakin sarki da yabin damar aiwatar da wannan ‘kudirin nawa, tsira da aminci ya tabbata ga fiyayyen halitta annabin mu Muhammad (S. A. W). Bakomai ne yasa na taraku anan ba, saidan ke Siddi’ka me sunan manya, ya fad’a yana kallo na, ina san yau d’in nan na  ai’watar da ‘kudirin mahaifiyar ki akan ki,

Ina fatan zaki yima na biyayya, nasan baki da matsala, saboda mun isa dake ne zamuyi abinda mukesan yi yanzu, ina so kisan bakida Wanda ya fimu a kaf fad’in duniya, bazamu ta’ba cutar da ke ba”.

Tun da Daddy ya fara magana gaba na ke fad’uwa, shin wani kalan ‘kudiri ne wannan da har Daddy yace ‘kudirin mahaifiya ta ne”. Banida wannan amsar saboda haka naci gaba da sauraran abinda Daddy zai cigaba da fad’a

Daddy ya cigaba da cewa “naso ace sauran ‘yan uwanku suna nanan, amma duk da haka kuma kun isa shaida,  kuma akwai abokai na guda biyu wa’inda tare dasu  zamu tafi lagos, nayi magana dasu, saboda muhimmancin abinda zan tattauna daku zasu biyo tanan”.

Kallon Hajiya Inna yayi yace “Hajiya ko  akwai abinda ki ke san fad’a”.

Tace “eh ina da abin fad’a”. yace “to muna saura ranki”.

Tace ” ‘Karami”. Haka Inna ke kiran Daddy karami “ni abinda ke damu na yadda, Garba ya tsani Siddi’ka, kamar ba ‘kanwar sa ba, Kaf ‘kauyen nan babu wanda bai san da zaman ‘kiyar-yar Siddi’ka a gun Garba ba, a gaban kowa nuna wa yake, a gida bai ‘kyale ta ba, motsi kad’an tayi ya make ta”.

Wani gwaran numfashi Daddy ya sauke, sannan ya fara yiwa Yaya Sadeeq fad’a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sosai Daddy yayi wa yaya Sadeeq fata fata

Sannan ya maida kallan sa I zuwa ga Momy yace “Aisha fa kina da abin da zaki ce”.

murmushi tayi irin  na su na manya tace “ai kai da Hajiya kun gama fad’an duk abinda zan fad’a, sai dai a’kara yiwa sadeeq fad’a a kuma ja mai kunne, sai muyi  musa fatan Allah yasa alkairi”.

“Ameeen” Inna tace yayin da Daddy yace “alhamdu lillah”.

Daddy yace “mai sunan manya matso nan kusa dani kinji”. Jikina a sanya ye na matsa kusa na zauna a d’ayan bangaren da ke kallon yaya Sadeeq  sai ban kamin harara yake a sace

nayi kamar bansan yanayi ba

Dafa kaina Daddy yayi yace “Allah yayi miki albarka”. “ameen”. Nace

Sannan yaci gaba da cewa “?????’?? ???? ??? ????? ?? ?????? ??? ????? ???? ???????? ????? ?? ??? ???? ??????? ????, ??? ????? ???? ???????? ????? ?? ?? ???? ????? ??”.

duk da ban wani san maye *Aure* ba amma naji sam ba aimin adalci ba

a tare nida yah Sadeeq  muka mi’ke tsaye, duk kannin mu idan mu a waje alamar rashin fahim ta.

” Koma ku zauna” Daddy ya fad’a, jikin mu babu ‘kwari haka muka koma muka zauna, Khadija ma dake zaune mama ki ne yacika ta shiko Umar ko ajikin sa Inna kuwa da momy daman sun san da batun

” ‘Kwarai kuwa abinda kukaji nafad’a haka ne ba mafar ki kuke yiba, domin wannan shine burin ‘kan wata Aminatu”. ‘Kwalla ce ta cika idonun sa yayin da ya kasa ‘karasa maganar Handkerchief yaciro cikin aljihun sa yana share ‘kwallar da ta zubo masa

Da irin murayan Wanda yake son yayi kuka, Daddy ya cigaba da cewa “auren ki da Sadeeq shine burin ta, bamu sani ba ko a raye take ko amace, kimanin shekaru goma sha biyu da wasu yan wattani akai kenan tun tana goyen ki”. ya nuna ni “nasan kunsan komai ba sai na ‘kara tada muku da zancen ba, saboda bana son na tada mana hankula”.

tuni inna tafara shash-she ‘kar kuka momy ce keta faman bata ha’kuri

Da ‘kyar aka shawo kan Inna tayi shuru

Ba ‘karya Dady yayi ba duka family an san labarin ‘batar mahaifiya ta amma bamu san yadda al’amarin ya faru ba

Daddy yaci gaba da fad’in “Siddi’ka sai dai kiyi ha’kuri, naje  har gidan ku da ‘kyar nasa mu ganin mahaifin ki, na je masa da batun auren ki, yace min shi babu ruwan sa  yama manta dake cikin ‘ya ‘yan sa  ba tun yauba ai ya fad’a mana ya bar mana ke, idan yanka ki zamu yi, muyi, shi baya da matsala babu ruwan sa”. ya ‘kara da cewa ai tun ranar da Amina  tabar gidan nan  na manta da duk wani abu daya sha feta yanzu haka abinda yasa bazan sa kar nuka su fidda min kaiba saboda baka sani ba, amma yanzu tunda kasani kada in’kara ganin ka akoafar gidana kai ba kai ba ko Siddi’ka d’iyata ce tazo sai nasa kar nuka suncin ye naman ta d’an ye, saboda haka Get out in my house”.

  jiki na babu ‘kwari Siddi’ka na fito daka gidan ku

Ban ta’ba jin tsanar mahai fina irin na yauba kuka nike sosai ina tir da halayen sa kowa a d’akin jikin sa yayi sanyi dady ne ke shafa min kai yana bani hakuri

“Siddi’ka ki cigaba da ha’kuri Allah zai miki canji da mafi alkairi, ki cigaba da kai kukan ki gurin Allah saboda shi Allah baya barin zalinci”. Kuma kamar yadda nace “yau za a d’aura miki aure da sadeeq idan anyi sallar juma’a babu fashi”.

SADEEQ ne zaiyi magana Daddy ya katse sa da fad’in “zan sa’ba maka sadeeq, Ko na tambaye ka ne?”.

bazan iya musa wa su Daddy, amma shin maye aure nashi ga uku nake fad’i a zuciya ta, yayin da nike jin bugun zuciya ta yana dad’a ‘karuwa

About AIS

Check Also

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 8

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 8 Www.bankinhausanovels.com.ng  Momy ta ce “amma sai ka kai Siddeeqah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *