MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAI_DAMBU

MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAI_DAMBU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Lokacin da aka fito da Babyn, aka kawo musu k’in karb‘a yayi yana kallon Nurse din da ta kawo babyn, dakyar ya bud’e baki yace. “Ina mata ta?!” Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin jiki tace. “Tana ciki sai dai muna kokuwar dawo da numfashita ne, dan yana kwacewa.” 

Kamar wacce zai bugata da kasa yayo kanta. “Ina mata ta nace.” “Kay! hakur sir! Muna bakin kokarin mu akanta.” 

Shigewa tay! ta barshi a gurin, sai Safa da marwa yake. Ko kalfon yaron dake hannun Ghanwyu bai yi ba, suna tsaye Nurse din ta kuma fitowa ta amsht yaron ta shiga dashi, sannan ta koma, ciki bayan mintuna goma sha biyu ta kuma fitowa da sauri, ga baki daya sun birkitawa Ashraf lissafi. Dan kaiwa da komowar da suke kad’ai ya isa ya tabbatar maka SAFINAH tana cikin wani halt. 

Zama yayi ya cusa hannunshi cikin gashin kan shi, yana jin tashin hankalin da ya ci kaniyar wanda suke ciki. 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kuma abin takaici duk yadda Bilal yaso su mishi bayani basu kula shi ba, haka suka zuba musu ido har suka gama abinda zasu yi. Sannan suka fito daga d’akin kowanne su fuskar shi a cike da alhini suka fito. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dafa kafad’arshi likitan yayi yace. “Kay! hakuril” Ya wucce shi jikin shi ne ya dauki rawa, yace. “Mahl! Wallahi bazata mutu yanzun ba, karku ce min haka™ 

D’akin ya shiga, cikin d’imuwar da damuwa, ya isa gaban gadonta. Ya kura mata ido cikin tashin hankali ya rike hannunta, sannan yace. “Me yasa bana jin komai akan abinda idanuna suke nuna min, wallaht na kasa gasgatawa wai kece a kwance ba rai! Kinsan yadda nake jinki kuwa? SAFINAH ta ba haka ta shirya mana tayuwarmu ba, don Allah tashi kinji Safinatu na, don Allah ki rufa min asiri karki tafi ki barni Ni Www.bankinhausanovels.com.ng 

d’aya ina bukatar ki a rayuwata.” 

Yajima a kanta yana magana, sannan yayi shiru yana kallonta, a hankali ya juya zai bar d’akin dan sai lokacin hawaye Masu zafi suka biyo fuskar shi yace. “Na yafe miki!” 

Rike hannunsa yaji anyi da sauri ya juya, sannan nace mishi. *Gawa ta tashi.” Murmushi yayi tare da jan kumatuna, ya dawo ya rungume Ni, tare da sake dariya yace. “Me yasa?”” Kwantar da kaina nayi a kirjinshi nace. “Sabida ina matuka sonka! Fushin da kake yi dani ne yaja nayi haka, amma kayi hakuri.” 

Lumshe idanunshi yayi yana jin farin ciki amma ya kasa nuna min, sai janye Ni da yayi daga jikinsht ya fita. Yana fitowa ya sauke ajiyar zuciya yace. “Safinah bata da tunani ban ciwon jikinta sai na falla mata mari.” 

Dariya suka saka mishi shi kuma ya shafi kwantaccen beard dinshi, can sai ga Nurse suka zo suka fitar da Ni, zuwa d’akin da zan huta sannan suka min alluran barci. 

ake Sati uku da cire min yaron da yaci Sunan Abban shi, muna kiran shi Artah,(sunan daya daga cikin masu rawaito hadisi ne Artah bini Ashath) 

Duk wani kulawa ina samu a gurin Mahaifiyar Bilal, dan ji yake kamar ta lashe Ni, har muka yi suna bani komai sai na da nono, ita ke min komai na yaro a hankali take bani labarin iin Wahalar da tasha da bilal. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan tayiwa ya gashi ta shafe shi da mai, ya shigo d’akin sanye da manyan kayan sanyi da lokacin ana ganiyar sanyi a Moscow, kuma abinda na fahimta larabawa da turawa basa iya jumirin zama nda babu sanyi sabida yanayin su, fita tayt da Artah da kuma Ablah da ta isheni da ngima sai na nuna mata ciwon ta gam, 

Kallona yay! kasa kasa, yana lashe bakin shu, yace. “Saura wata nawa abani hakkina?!” 

Takawa nayi har inda yake, nace. “Hakkinka dole abaka shi matukar ina da koshin lafiya. Idan zaka iya bina a sannu, tsaf na shirya na baka hakkinka.” 

Mik’ewa yayi yaje ya rufe kofar sannan dan ba abin mamaki bane muga Ablah akanmu. 

Al’amarin Ashraf me girma ne a gareni, dan a sannu ya jiyar dani duk wata kewar shi, dan tun da muka dawo babu abinda ya shiga tsakaninmu, sai yajin da yayi min. Shafa fuskana yayi cikin nutsuwar da ya sameta a lokaci guda yace. Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Sannu king! Na takura ki ko? Sannu bay na bane soyayyarmu ce take motsa min’ 

Shiru nayi tare da lumshe idanuna, nace. “Ni kuma nayi kewar ka sosai.” 

“Ni kuma kewar tsiwar ki.” “Ashu! Nice matsiwaciya” “Ya hakuri! Ummun Artah” 

Gyara zaman duvet nayi a kirjina sannan nace mishi. “Ina ka ajtye Ablah?!” “Yar Bilal ce!” Tsuke fuska nayi sannan nace. “Kayi hakuri bazan bada Y’ata wa kowa ba, sabida ban shirya ganin b’acin rai ba.” Jan hancina yayi sannan yace. 

About AIS

Check Also

MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 7 BY MAI_DAMBU

MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 7 BY MAI_DAMBU “Zan yi sallah tukun.” Zare min hyab …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *