KALLON KITSE CHAPTER 8

KALLON KITSE CHAPTER 8

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

daga wannan namiji ya fita sai wanan ya shigo, ta zauna gab da ita, tace “inaso muyi magana ammi.” ta dubata sosai cike da kula tace inajinki.

“toh ki sallameshi kana, ko muje dakina.” muje dakin ko zaifi,”

inaso ki shirya muje office din su jafar ki bashi hakuri, inaso in koma gidana Ammi, na gaji da zaman gidan nan.” sai a ranar magajiya ta tausayawa rayuwar ‘yarta, dan ta gano tana tare da kaunar jafar, ba kadan ba, dan haka ba musu ta dauki gyale, “wane shiri zanyi? Tayi murmushi nagode Ammi

hakuri ta bawa mutumin data ke tare dashi dazun tace, zasu iya haduwa anjima.

Jafar na tare da patient koda suka isa secreatry dinsa da sauri ta isar masa da sakon matarsa na waje, tana son ganinsa. Tsaki yayi yace, tace mata ta jirashi har saiya gama ganin marasa lafiya tukunna, ta fada mata, Ammi tace “kifada masa ba ita kadai bace, tare da mahaifiyarta ne.” yace su isa, da suka shiga yana tsaye da uniform dinsa, da farin coat wanda doctors ke sawa, da suka shigo suka nemi wuri suka zauna,

yadda fuskarsa babu annuri yasa ta kara rudewa, kuma yayi mata kyau yakara kwarjini a idonta,. Bayan sun gaisa Ammi ta soma bashi hakuri, da hannunsa ya dakatar da ita, “Ammi ba komai na hakura.

“toh kasan ya kamata ta koma gidanta ko?

“eh hakane tana iya ta koma, yadda Ammi taga sun sami shiga yasa ta gyara zama tace, “toh ya batun jamila, kasan dai baka kyauta bako jafaru, in kai ne akayiwa haka ai….. ,” ya katseta, “Ammi kin fadi abu mai muhimmanci na amince, bana so ta so da abunda ya wuce.

Da sauri marliya ta mike ta riko hannun Ammi suka fita, yabi bayansu da kallo, yana neman kariya daga sharrinsu, bayada matsala yanzu inbanda yaje ya nemi gafarar mahaifiyarsa, koda yake ya tura takardar neman hutu, dan dama yakai shekaru uku bai dauki hutu ba.

A ranar ta tattara yanata-yanata ta koma gidan mijinta, abun mamaki ta iske jamila a gidan abun na daurewa marliya kai, wai me jamila take nufi ne? Tatambayi kanta, ta karasa ciki, jamila na kwance kan kujera tana cin cingam, sanye da wani guntun wando sai ‘yar farar vest ajikinta, tayi saurin zama tna yiwa marliya kallon ke banza ce, anan gidan, bata yadda da hakan ba, saida taji wayarta na ringing, da sauri ta dauka, saboda jafaru ne, yace da ita, jamila na gidan ba ruwanki da ita, don ba zamanki takeyi ba, ki sani inada ikon ajiye abunda naga dama agidan tunda gidana ne, inkinga zaki iya zama to, in kuma bazaki iya ba saiki juya ki koma gidan uban naki, saina shigo.”

kwalla ne ya cika a idonta, kamar zasu zubo sai tayi ta maza ta hadiye su, jamila ta rinka dariya kamar taji abunda ake cewa acikin wayar. Tana fadin, “yaya dai marliya baby, kin sauko ne, ko kuwa har yanzu kina kan bakanki, nasai kin kasheni? Kiyi hakuri muyi zaman hakuri, ki yagi naki rabon nima inyagi nawa, tunda abun business ya zama.”

batace komaiba taja jikinta zuwa dakin barcinsu, taji shi a rufe, jamila ta kara kwashewa da dariya, har tana faduwa, “dakin Oga(jafar haka take kiransa) zaki shiga? Dakin gane kurenki, kinyi sa’a na rufe dakin da yau sai kinyi dana sanin shiga masa daki, ta nuna dayan dakin dake kusa dana baki, “kina iya kiyi amfani da wannan, in kinaso.” marliya tace,

“jamila kinsan duk wulakancinki nafiki iyawa ko? Dan haka kibi a hankali,

A da kenan marly, yanzu kam nima na isa yanka, nayiwa kaina alkawari nima saina rama wulakancin da kikamin marly, bazan taba mantaki ba a rayuwa, kece sanadin lalacewar rayuwata, ke kika maidani haka, nazama abun nuni a ‘yan uwana, inada yayye uku mata da maza biyu, duk sunyi aure bandani.” kuka ta saki mai tsumar da rai, ko kai kaji irin kukan da jamila keyi, saika tausaya mata.

Nan da nan jikin marliya yayi sanyi, tasan tabbas itace sanadin  da jamila ta zama abunda ta zama, dan cutarwa tasan ta cuta mata, toh amma meyasa zata nemi shiga rayuwarta da mijnta? Batasan tana iya komai akan wanda keson rabata da jafaru ba? Jamila ta katse mata tunani,” wulakanci yanzu na fara yi maki marliya.” tayi wuce tayi shigewarta dakin data ke zama aciki, bakin ciki kam marliya tayi shi, kuma tun ba yau ba, abun yafi na kullum, tasan tanada hannu a lalacewar jamila, ita taso hakan tunda ita ta nemeta, “zan gwada mata ita karamar ‘yar iska ce, sai nayi sanadinta, mu zuba nida ita mugani.” A nan falo ta zauna tana jiran shigowar jafar.

Bai shigo gidan ba sai kusan sha biyu da rabi, abun ya daurewa marliya kai, lallai ba karamin juriya zatayi ba dan yadda take zaton al’amarin ya wuce haka,

a yau ma haka ya shigo gidan a buge, ta mike tsaye tana fadin sannu da zuwa.” ko kallonta baiyi ba, ya wuce dakinsa, tayi saurin bin bayansa. Saida ta shiga dakin sosai yace, “ke me kike nufi? Anan zaki kwana kome? Ta tsaya tana kallonsa galala, baki sake, toh ina zanje? Ko ka manta ni matarka ce?

“ban manta ba amma inason privacy from now on, saboda haka kije ki zabi daki ki zauna, duk lokacin danake bukatarki zan nemeki.”

yana gama fadin haka ya shige bayi. Ita kuma tayi tsaye tana kallon kofar bayin Bakin cikine ya taso mata kamar ta bude baki tayi ihu, amma saita hakura dayin hakan.

Tanan inda take har ya fito, wanka yayi, sai a lokacin taga yadda yayi kiba, yayi mata kyau a ido, ta kasa dauke idonta akansa. Shi kuwa yi yayi kamar bai san da mutum a dakin ba, ya saka jallabiyarsa, ya shimfida darduma, ya soma sallah.

Daya idar ma baice da ita komaiba, ya hau gado zai kwanta saitayi saurin isa gunsa zata rikeshi, yayi saurin kaucewa, “kada kira yimin haka, saboda ni ba sa anki bane!

“dan Allah ka fadamin abunda nayi maka doctor, kasan na cancanci insan abunda nayi maka, kasan ni mai baka hakuri ce, doctor inka nayiwa Allah ka fadamin abunda nayi maka, ni matarka ce dole in damu da irin zaman da mukeyi? Yana kwance kan gado ya zuba mata ido, a ransa tunani yake yadda akayi ya auri tsohuwar mace, ko a ido ka kalleta kasan ta kwana biyu, sam babu alamun sassauci a fuskarsa yace, kin gama? Tasa gwiwarta akasa tana wani irin abu na masu ban tausayi, shikam ko kallo bata isheshi ba, itama ta lura da irin tsana da kyamar da yake nuna mata, “kitashi ki fita inaso in huta, bana son yawan surutu. Ya runtse idonsa, marliya jikinta ya gama sanyi, tasan jafar yayi nisa da tsanarta, toh meya kawo wannan sauyi cikin lokaci kankani abu kamar almara? Haka ta fita ta bar dakin gwiwa a sanyi.

Jafaru kam duk lamarinsa ya canja, abinda baya zato shi zaiyi shi a rayuwa, yanzu shi yakeyi saboda, shan barasa, da harkar ‘yan mata abun ba a cewa komai, anan mashayarsa yana zaune yana shan abinsa cikin hankali da nishadi, ji yayi ankira sunansa da karfin gaske, “JAFAR!!!.” ya dago ido ya kalli inda yaji ankira sunansa, abun mamaki bashir ya gani, cike da zagwadi suka rungume junansu, suna dariya na farin cikin ganin junansu, “aboki” inji bashir, “inkon Allah ashe rai kanga rai a inda baya tsammani? Me kakeyi nan jafar?.”

“kai meya kawoka nan garin? Suka kara rungume juna, sannan suka zauna. Jafar ya kira waiter yace a kawo musu kwalbar barasa uku, bashir ya dakatar dashi yace, a’a bana shan barasa, amma za a iya kawomin maltina.”

“kaddai ace kabar sha bashir?

“eh na bari, Allah ya taimakeni jafar, kai ya akayi ka fada shanta jafar?

Ajiyar zuciya yayi, “it’s long story bashir bazan iya fadamaka yanzu ba, me zai hana gobe mu hadu nan in fada maka?

“a’a nikam daka ganni nan na shigone dan akwai wani oga na daya sauka a cikin motel din yace, nayi magana akai musu barasar can confercuce acan muke meeting, amma da baka ganni nan ba, saidai mu hadu acan inda na sauka hamdala hotel, sai muyi lunch tare da karfe biyu, koya ka gani? Suka tafa “toh Allah ya kaimu.” har mota ya raka bashir, bayan ya kaiwa Ogan nasa sako.

Aranar jafar saida ya sha tayi masa yawa, don har saida aka tukashi gida. Marliya ta karasa dashi daki.

Suna isa ya zuba mata amai ajikinta, bayi tayi tana wanke jikinta, ta shiga uku haka rayuwarta zata zama kuma, dama ace farko haka rayuwar ta kasance inyaso daga baya taji dadi.

Washe gari kuwa harda dukanta yayi, wai wane dalili zaisa ta kwana masa daki, baya gargadeta da shigar masa dakiba? Haka tabar dakin tana kuka, tare da magiya, “sakayyar da zakayi min kenan?.”

tureta yayi da karfi, har saida ta buge kanta a bango, kwal kake ji, yace, “da yake ba kece sanadin maidani haka ba?.” nan da nan kanta ya kumbura, ita kuwa jamila inbanda dariya ba abunda takeyi, da sauri ta isa gun jafar tana lallashinsa, “yi hakuri Oga, zo muje ka karya, don Allah kyaleta.”

suka wuce zuwa kitchen, kuka mai karfin gaske marliya ta sake, “lallai ashe haka duniya take? Wata rana in kaine gobe ba kai bane, dubi yadda ake wulakantani,” ta fada cikin ranta, cike da takaici, don mene zata tsaya ana wulakanta ta? Ta kara tambayar kanta, dole ta nuna musu tafi karfin wulakanci, koda shiga kitchen kissing ta cimma sunayi, cike da muradin junansu, ai nan wani irin kishi ya taso mata, ta nufesu cike da masifa, abun mamaki, saita kasa ce musu komai, ihu ta rinkayi sai kace mahaukaciya, tuni jamila taji tsoro, amma shi gogan ko kallo ba isheshi ba, saima kara jawo jamila ajiki yake tayi, yana lasarta. Ita kuwa tana zukewa dan munafunci. Marliya ta dauko muciya ta nufosu dashi, jamila ta kwalawa akanta, sai kuwa jini ya barke, zata kara mata sai jafar ya rike hannunta ya fisge mucciyar, ya yar, ya fara galla mata mari, kamar guda hudu, sannan ya tureta ta fadi kasa, kara mikewa tayi, ta nufi jamila ta rike mata wuya, tareda cizonta a kumatunta, jamila sai ihu ta keyi, shikuwa jafaru, yanata kokarin yaga ya raba fada. Da kyar ya kwaci jamila, kanta da kumatunta jini kawai ke zuba, kamar fanfo, marliya dariya takeyi, wai ita a ganinta ta rama wulakancin da kuma takaici da jamila tasa ta aciki, shikuwa jafar police ya kira, cikin minti goma sha biyar da yake basuda nisa suka shigo, suka wuce da ita.

Washe gari inda sukayi alkawari da bashir, nan suka hadu. Saida suka gama cin abinci, sannan jafar yace, “yau kaga yadda na zama bashir, ba komai ya kaini wannan rayuwar ba sai mata dana aura,Basan yadda akayi na aureta ba, amma ni nasan ko kusa bazan taba tunanin aurenta ba, kuma haka dinne, na fara samun wani irin yanayi ne a tareda ni, kasan fa yanzu kusan ince nayi shekara hudu rabona da kebbi..”

“akan wane dalili jafar?

“wallahi ban saniba aboki, haka kawai, ni nasan tun ba yanzu ba, abun na damuna, amma ban iya fadawa kowa matsalata.”

“haba aboki meyasa kayi haka?

Wallahi bashir in nace ma ga abunda ke damuna toh wallahi nayi maka karya, dan labarin dana baka kan marliya wanda na sani kenan. Dan Allah bashir ka taimakeni domin ganinka yasa naga kamar matsalata ta kare.”

zan taimaka maka aboki, nima abunda ya shafeka ai ya shafeni aboki, dan haka shawarar da zan baka itace, zamuje wajen yayyenka mata mu fara dasu tukunna, koya ka gani? Hawaye ne suka taru cikin idonsa, amma basu zubo ba.

Nagode aboki, inasa ran zan samu leave din ranar jumma’a in Allah ya kaimu, ya zakaje ne kashirya?

Eh toh nima anyimin transfer nan garin, gobe zan shigo da iyalaina, kasan yanzu ‘ya’yana biyu ko?

“kai dan Allah bashir?

“na uku ma na ciki insha Allahu next month zata haifeshi.”

nima gaskiya irin naka zanyi, ta gida zan nema in aura.”

da kaga canji, dan dai nikam amina ta gama min komai, dan sanadinta na zama abunda na zama yanzu, saboda cikin dari ita keda tamanin, na ci gaban rayuwata.”

“hakane bashir, Allah nima ya bani wadda zata rikeni amana.”

toh marliy fa? Ai baka rabu da itaba.” hakane, bazan rabu da itaba har sai na gano yadda ta maidamin rayuwata ta zama haka, sannan saina rama wulakancin datayi min, bashir Allah ne kawai ya cetoni daga tsohuwar kilaki, Allah ya rabamu da irin wadanan matan amin.”

“sai musa ranar tafiya, ranar lahadi kenan next weak a lokacin munga zainab da salaha ko?

Badamuwa duk yadda kayi bashir shine dai-dai.”

washe gari bashir saida ya matsawa jafar, har saida yasa yaje yayi belling din marliya, ta dawo gida sannan ya wuce lagos yace, da yamma zasu shigo kaduna. Haka akayi kuwa, karfe bakwai saura, jafar ya taryesu a airport, gidan da akabawa bashir babu abunda babu aciki, gidane babba hawa daya, jafar ya siyo musu abinci suka ci, abun sha’awa ya rika bashi, yaran bashir duk sun taru a jikinsa suna wasa, ji yake da shima yayi auren kwarai daya ajiye iyali irin haka.

Haka yai ta sha’awarsu, har sai karfe tara da rabi yabar gidan bashir mashayarsa ya wuce, ranar ma abun har yafi na kullum, dan daki ya dauka, yana holewa da ‘yan mata, in wannan ta shigo wannan ta fice waccan ta shigo, Allah ya shirya amin.+

***** **** *****

can birnin kebbi kam, abubuwa suna tafiya dai-dai, sai dai na inna ba haka bane, duk kwanan nan saita tai ta mafarkin jafar, ta kasa fadawa kowa, saidai inta tashi tayi sadaka, tana rokon ALLAH yasa bawani mugun abu zai sameshi ba.

Suna zaune a falo ita da uwani, uwani ‘yar shagwaba, kanta na kan cinyar inna, sai sallama sukaji daga sama, muryar tayi musu wal,

About AIS

Check Also

KALLON KITSE CHAPTER 11

KALLON KITSE CHAPTER 11                     Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *