KALLON KITSE CHAPTER 6

KALLON KITSE CHAPTER 6                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ta saki kuka, “don me yayarka zata shigo min gida batare da tanemi izini naba? Kuma data shigo ko kallon arziki batayi minba, saima ta rinka yimin kallon da baimin dadi ba, saboda Allah wannan wane irin wulakanci ne, kaima daka dawo ko ka kula da hakan?

Duk ilahirin jikinsa rawa yakeyi, shima kaman yasa kuka yakeji, yayi sauri ya rungumeta yana bata hakuri, da kyar ya samu tayi shiru, harda su ajiyar zuciya.

Ya dauketa cak, sai cikin daki, anan ya nuna mata tafisu ‘yanci a idonsa, don saida ya tabbatar ta sauka, ya kyaleta, sannan yace ta kwantar da hankalinta, badai sune bata so ba, zamu zuba dasu.

Ta kalleshi a kadarance tace, meya kawota?

Ya tsura mata ido, bakomai wai tazone kawai mugaisa,

“ta dai zo ganin gulma, kaga daga yau banason ganin irin wadannan bakin, don basuda mutunci, ka gane ko? Ya hadiye miyau da karfi yace badamuwa zan kula, sannan suka ci gaba da soyayya.

Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, yau gashi jafar yakai kusan shekara biyu baije gida ba, koma ince ya manta dasu ko waya bayayi musu, tun abun na damunsa har ya hakura dan kansa. Ita kuwa uwar mulki ta samu yadda takeso, duk salary na jafar hanunta yake, ko kwandala baya karba, haka zata shirya itada mahaifiyar suje kasashe-kasashe abun ba a cewa komai, domin kuwa tayi nisa sosai, har lokacin da aka tura shi course lagos na watanni da dama itace ke ai watar da koma.

A taikace de bada shi kadai take harka ba, ba yanda bayyi da itaba su tafi lagos tare, taki tace, bakomai zata ringa kai masa ganinsa akai-akai, nan kuwa shirya masa karya tayi.

Ya samu kaman wata shida da tafiya su baba yunusa da kawu hashimu suka zo kaduna.

Marliya ba wulakancin da batayi masu ba, harda korarsu tayi tana fadin, “shin wai ku wasu irin mayu ne, ba yace baya yi dakuba, ko kun mata da nasa ya fada maku ku fita harkarsa?.

Kawu hashimu yace ke tsohuwar daga kiyi hankali…….” baba yunusa ya dakatar dashi da hannunsa, “kyaleta lokacinta ne zomu tafi.”

suka kama hanya suka tafi dan takaici basu saurara ba, suka wuce gusau gidan zainab, daga sama ta gansu itama, yadda ta gansu a zatatonta rasuwa akayi, ta kasa tsaida hankalin gu daya, ta shirya masu abinci, data ga basu damu su gaya mata wani abu ba yasa ta nutsu. Saida suka ci suka sha, sannan suka fita yin sallar isha’i bayan sun dawo suna tare da Alh. Tanimu ambursa, zainab ta shigo ta nemi wuri ta zauna, “baba ya bayan rabuwa?, ya amsa lafiya lau kinsan daga kaduna muke, dan mu duba jafar? Amma matar nan tashi ba karamar ‘yar duniya bace, ashe haka take muna jin labarinta, muna ganin kamar ba gaskiya bane, ashe ta wuce yadda muke zato? Bakisan korar kare tayi manaba? Zainab ta zaro ido “hardaku tayiwa wulakanci baba?.

Ajiyar zuciya yayi, “aiba abunda za a tashi dashi, in banda atashi tsaye da rokon Allah, wane a sa ido duk bata taso ba.

Fatima ta maida abun abin fushi, aiba fushi ya kamata tayi ba, addu’a za a tashi arinkayi, shekara cikin na uku kenan fa, rabon jafar da kebbi, in muka sa ido bamu san ciwon kanmu ba, shifa mutum ajizine bai taba cika cikakken mutum ba, kawu hashimu yace, zainab don Allah kiyi addu’a Allah ya dawo da yaron nan gida, wallahi ya shiga abunda bakwa tsammani ba.” hawaye ne tab da idonta, tace baba dan Allah kubawa inna hakuri ta dauki zafi sosai, dan inaga akwai lokacin da inya bugo ma ta daina dauka, saboda haka shima ya bari, sannan salaha ma ta fadamin abunda ya faru kwanakin baya dataje kaduna.”

baba yunusa ya gyara zama, “ke bakiga auren mansura bai zoba ai abun ya wuce gona da iri, dan haka bazamu sa ido ba, dole mutashi tsaye.”

“hakane baba Allah ya taimake mu”.

“amin”.

“gashi arziki sai karuwa yakeyi, kinga gidan da dama yake zaune aciki, ance nasane, gashi bai samu matar kwarai ba, shin waye mai dukiyar in yau akace babu shi? Dan haka dole mutashi tsaye, nikam yunusa wallahi sai nayi sanadin rabuwarsa da wannan ja’irar mace, insha Allahu ko nanda shekara goma, sainaga bayanta, Allah dai yayi mu rayu zata ga abunda ta manta dashi.”

ahaka sukaita shirye-shiryensu, tare da tunanin yadda zasuyi, abun bakaramin daure masu kai yayi ba, “jafar da yake son jama’a, ga zuciyar kyauta kowa yasan yaro mai tarbiyane, tunda ansan hakan ya za a samasa ido, mun cutar da kanmu da kanmu, Allah zai taimakemu insha Allahu!!

**** **** **** ****

tunda jafar ya bar kebbi haka inna kuwa batada kwanciyar hankali, saidai sam bata nunawa, tasan tayi kewar autanta, amma ya zatayi? Tunda ta aza ido kan matarsa, tasan ba abun kwarai bace, tun kuma daga lokacin tai mafarkin ta, da wata irin muguwar shiga, so daga nan saita ga marliya ta nufota da wuka, ko almakashi ta biyota, acikin mafarkin Allah ke bata ikon yin addu’a, saita bace. Wata rana kuma tayi mafarkin ta cakumota zata jefa cikin wani irin rami mai bala’in zurfi, duk da iri mafarkeyen data keyi bata taba fadawa kowa ba, itama kanta abun ya daure mata kai.itama kanta abun yana daure mata kai, toh ya ya haka? Ita da ko mainene zai tada mata hankali bata shiru, saita gayawa ‘ya’yanta, saboda sune abokan shawaranta, amma ikon allah har yau dasuka samu kamar shekara uku da dan autanta, bata taba kiran wani ta fada masa tashin hankalin datake ciki ba.

Su zainab sune suka damu, inma sunyi mata magana, saita canza zuwa wani tadin, abun yana daure mata kai, sam! Inna bata so ayi hirar jafar, duk da bata nuna fushinta a fili, su sun san tana cike da son fada mata wani abu, amma ta kasa, saita kirata a daki, zata ce mata wani abu, sai kuma kaji tace, barshi kawai, sai kuma ta dauko wani zancen ta rinka yi mata, tun uwani na damuwa har ta saba, dukda basa shiri da jafar itama abun ya dameta, dan dai duk abunda ya zama na inna, toh itama natane.

Uwani na zaune kicin tana yanka alayyahu taji sallamar su kawu, ta mike da sauri ta isa gun, tana gaishesu, suka amsa cike da fara’a,

baba yunusa yace, “toh ina uwr taki takene? Tayi murmushi da har hakoranta suka bayyana, tace, tadan fita amma bazata….” adai-dai lokacin sukaji sallamarta, ta shigo, ta isa cike da fara’a, suna gaisawa ta sami wuri ta zauna, “uwani kawo musu abinci, ko baki gama ba?. Tace “eh inna ban gamaba, amma saura kadan yayi.”

toh shikenan.

Ta maida kanta kansu baba yunusa suna kara gaisawa, yo ke fatima babbar magana ce ta kawomu kan yaron nan ne jafaru, mun lura sam ba abunda ya dameki da lalurar data sameshi, amma kisani duk wani fushi da dauke kai kan al’amarinsa duk bata tasoba, mudai hakuri muke badawa, kiyi hakuri ki rinka yin addu’a.”

gani yaya ta fadi kwance, nan da nan suka zuba salati, suna kiran sunanta, aikuwa nan da nan hankali ya tashi, suna kwallawa uwani kira ta kawo ruwa, irin kiran da sukeyi mata, shiyasa ta nufo dakin, dauke da ruwa a cup da gudu, indo ma da gudu ta nufo dakin, aikuwa ganin inna a kasa yasa uwani fashewa da kuka, ta karasa ta maida kanta kan cinyarta, tana fadin “inna dan Allah kada kimin haka.

Inna kece uwata, kece ubana, in kika barni na shiga uku! Dan Allah inna ki tashi inna.”

indo ma kuka ta fara, dan tsabar tausayin abinda uwani ke fadi, koba komai itama haka ta dauki inna, ta dauketa tamkar uwa data haifeta, nan da nan ta farka.

Hawayene ke zuba sharara daga fuskar inna, bata iya cewa komai ba, asibiti aka nufa da ita.

Nan da nan aka bata gado, duk iya bincike da akayi ba a gane komaiba, dan ba abunda ke damunta, lafiya lau take. Uwani ta kara rudewa, saika ce itace batada lafiyar, duk tabi ta rame cikin kwana hudu. Inna kuwa ita kadai tasan abunda takeji ajikinta, tana tunanin meyasa da anzo anyi mata maganar jafar saitaji batada lafiya? Sam bataso taji an ambaci sunansa, dan da anyi hakan duk saitaji ba dadi, kuma bata isa ta fadawa wani matsalarta ba, wannan abun yana daure mata kai.

A ran kwana na biyar baba yunusa yace, a maida ita gida, su zainab ma a yau suka iso, itada salaha, duk an hadu a falo ana shirin yadda za ayi, kawu yace ayima mal. Kasimu magana yana kan hanyar zuwa, sannan nasa wasu malamai kamar mutum uku anayin rokon Allah.” baba yunusa shima ya gyara murya, nima nasa anan mutum biyu da mal. Isa shima yana nan yana yin nasa kokarin, Allah ya bata lafiya.”

“amin”.

Zainab ta dubi baba yunusa, “baban mariya ma yace, yayi wasu malamai a can zamfara,

toh angode, Allah bada lada.” saida mal. Kasimu yazo, aka isa dashi cikin gida, sannan akayi masa iso gun inna, tana kwance, uwani na gefenta rike da hannunta, ba yadda ba ayida uwani ba ta fita amma taki.

Mal. Kasimu yace, “a kyaleta ba abunda zai sameta.” nan suka zauna gaban inna shida almajiransa, akasa radio ana karatun Alkur’ani mai girma, suma karatuna sukeyi,

can uwani taji inna ta saki hannayenta ta dubi idanun inna taga sunyi jajir, kamar garwashi, ai saita mike da sauri, tayi waje,

nan fa su mal. Kasimu suka ci gaba da karatu, ita kuwa inna sai wani irin ihu takeyi, kamar makoshinta zai fita. Sun sami kamr minti sha biyar kafin ta soma magana. “wai me kuke nufi? In fita daga jikinta? Toh bazan fita ba, sai kun gaji kun kyaleni, kuda kanku.” basu daina karatun ba taci gaba da ihu, can saita fadi kwance, ta kuma tashi zaune, yanayinta gaba ki daya ya canza, idon nan nata kamae gauta, ta mike tsaye tana fizge-fizge, waje tayi, wani almajirin ya rikota, ji sukayi tayi wurgi dashi, kamar kayan sawa.

Nan da nan suka taru a kanta, amma basu daina karatun ba,

mal. Kasimu yace waye kai, bakace bazaka fita ba? Toh ina zaka? Wallahi saina konaka daga sama har kasa, zaka sanni, ayar kur’ani nake amfani da ita, dole ka fita komai karfinka.” aikuwa watsi tayi da almajiran baki dayansu, ta nufoshi,Aikuwa watsi tayi da almajiran baki dayansu, ta nufoshi, mal. Kasimu tsaye yayi kikam, ta shake shi, duk yadda taso ta hana shi karatun, amma ta kasa, can ta fara kaiwa kasa da kanta. Gwiwarta a kasa tana fadi , tana fadin, nadaina wallahi zan fita, ka sassauta min.”

mal. Kasimu kuwa sai karatu yake tayi, suma almajiran sunyi tsaye sun zagayeta, sai zare ido datake ta famanyi. Tayi kwance kasa tanata fizge-fizge, tana fadin, nadaina zan fita, ku daina, nace zan fita.” mal. Kasimu yace, “toh fitaman, aiga hanya nan, kuma bari kaji da duk ka kara zuwa ko kusa da wannan wurin, toh wallahi saina tabata ka kone kurmus.”

“bazan zoba, ka daina karatun nan, kaga ka konamin kafata da bayana, ka bari haka nan, na tuba, nayi alkawari bazan dawo nanba”.

Basu dainaba, yace saika fadamin wanda ya aiko ka.”

“shanshani ne yace, kada in yadda in fada, dan na riga dana dau alkawari bazan fada ba, wayyo hannuna shima ya fara konewa, ku daina haka nan, zan fita, nayi alkawari ku daina.”

sannan suka sassauta. A bingire inna ta fadi kasa, tummm! Ka keji.

Mal. Kasimu ya duba idonta, sun koma yadda suke, sannan yace su tai, su kawo rubutun cikin galan da suka zo dashi, ya diba a hannunsa ya shafa mata a fuskarta.

Inna ta mike zaune, hawaye ta somayi, can mal. Kasimu ya dubeta, “Alhamdulillah! Ya fita, tashi ki zauna da kyau.”

godiya ta somayi, dan ta gano abinda ke damunta, “ba inda yake mik ciwo?.” ta girgiza kai, “babu, saidai inaso in kwanta, inyi barci.”

“toh ba damuwa ki kwanta.” ta haugado ta kwanta.

Uwani kam har lokacin bata daina kuka ba, su majina duk ta bata mata fuska, tana rungume da salaha, itama hawayen ne shar a fuskarta.

Mal. Kasimu ya fito shatab, yayi zufa kamar wanda aka watsawa ruwa ajikinsa, suna ganin ya fito kawu ya masta gunsa, yana yi masa sannu.

Ya amsa tare da cewa a taimaka masa da ruwan sanyi. Da sauri zainab ta dauko, su duka suka sha, suna hamdala, mal. Kasimu ya gyara zama sosai, sannan ya dubi baba yunusa, toh Allah ya taimaka abun yazo da sauki, tunda ya fita Alhamdulillahi, sai muyiwa Allah godiya, aljani ne aka turo mata, kafiri ne yanada kaifi sosai, duk wani farin ciki da baiwar Allah nan zata samu, saiya hana hakan, sannan yayi sanadin mantar da ita dan nata, yana yi mata illa can cikin jikinta, in aka fara yimata zancen dan nata, dan shiyasa bata so ayi mata maganarsa, sun sa mata bata iya fadin abunda ke damunta, ko in anyi mata maganarsa tana nuna damuwarta, shi dan a ina yake ne?

“yana kaduna”.

“a’ah babban magana dan nashi aikin zaifi wahala, saidai za’a taimaka ayita addu’a, saboda maiyin wannan aikin tana iya kisa akan duk wanda ya nemi ya rabata dashi, saidai a yawaita addu’a, har sai dan kansa yazo gida.

Akwai taimako da zanyi saidai ba wai abu na gaggawa bane, zai dau lokaci, inaso ne ya dawo gida da kansa, in muka ce ya dawo da gaggawa, aikin bazaiyi ba sosai, don haka don Allah inaso ku kula, kuyi amfani da abunda zan fada muku, kuyi ta addu’a ba dare ba rana, nima zamu tayi a can, insha Allahu zaku ga sakamako. Amma kuma saikun tashi tsaye, ni zan wuce.” kawu hashimu yace, “malam me zai hana ka bari har gobe?

“a’a gaskiya akwai abunda zanje inyi, saboda aikin da nayi yau ba karami bane, zai iya yiwuwa a kara nemanta da daddare, dole inje inyi wani aikin.”

“toh Allah bada sa’a, amma ita yaya shikenan ba wani abu da za ayi mata?

“eh ga rubuntun da zata sha data tashi daga barcin data keyi, shikenan insha Allahu ta rabu dashi har abada.” baba yunusa yamike sukayi waje da mal. Kasimu, su zainab akayi zaune kamar ana zaman makoki. Sun wuni cur, bamai bawa wani hakuri, hardai uwani duk tabi ta lalace, ko zata iya tuna rabonta da abinci?

Inna bata farka ba sai karfe tara na dare, koda ta bude idonta uwani ta gani zaune kusa da ita rike da hannunta, da sauri uwani ta kwallawa zainab kira, “momi, mami ta tashi.” da sauri ta iso ta bata rubutun malam tasha, sannan ta mike, yadda taga duk sun rame yasa ta saki murmushi, “ina so inyi wanka duk jikina yayi tsami.”

“inna ki bari kici abinci tukunna.”

“a’a uwani bari dai inyi wanka tukunna, sai inci.”

“ba inda ke maki ciwo inna?” ta rike hannun uwani sosai tace “babu”. Sai a lokacin ta saki fuskarta.

Bayan tayi wanka ta fito, uwani gabanta ta zauna tana kallonta, inna tace, saikace ke kikayi ciwon, duk kinbi kin rame uwani, dama gaki yadda kike ba wata kiba ba.”

tayi murmushi ta shige jikin inna tana dariya, “inna wallahi na zata zan rasa kine.”

“insha Allahu sainaga jikokina uwani, karki damu, lokaci bayyi ba tukunna.”

tun daga lokacin kowa ya tashi da addu’a badai kamar inna.

Uwani suna ta shirin jarabawa ta shiga aji biyar (s.s 2), tana zaune tana karatu, inna ta dubeta, uwani tashi ki dauko abinci muci.

“inna saidai in debo miki, amma ni na koshi.”

“kai tawan, a rika cin abinci, dubar ki ‘yar siririya kamar zaki karye.”

“inna kenan, ni kuwa gani nake nafi kowa ci.”

“a da ba, da kina karama, yanzu kam kin daina.”

“dama girma nasa rashin cin abinci? Inna gashi nikam na koshi dazun nan naci abinci.

About AIS

Check Also

KALLON KITSE CHAPTER 11

KALLON KITSE CHAPTER 11                     Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *