KALLON KITSE CHAPTER 14

KALLON KITSE CHAPTER 14

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Saboda ire-iren matan daya kwanta dasu babu wanda takai uwani a komai ma, toh shin daman meke burgesu ne da matan bariki? Ya kara tambayar kansa, ashe dama shi bai san dadin mace ba, sai a yau? Son uwani ne ya karu a zuciyar jafaru

godiya yakeyiwa Allah daya bashi mata irin uwani, sannan ya soma yiwa inna addu’a fatan shiga aljannatul firdaus.

Yana cikin haka yaji ana sallama daga waje, yayi saurin lekawa, mal. mamman ne, yallabai wayarka ce tun dazu take ringin shine nayi kaudin dauko maka.”

a’a haba wane kaudi kuma mal. Mamman? Kadaiyi taimako na gode wallahi.

Missed cal har sha biyu ya gani, da sauri ya duba number, number inna ce ta MTN, ah har sun iso?

Ya fada da sauri ya wuce dakinsa ya shirya, saida ya fadawa indo sannan ya wuce, shida mal. Mamman da driver Alh. Yunusa.

Matafiya dai andawo lafiya, sai dai har yanzu uwani na kwance tana barci, inna data tambayi indo sai ce mata tayi, ai bata da lafiya, saida jafar yayi mata allura.”

sam inna bata kawo komai a ranta ba, saidai tausaya mata datayi, dan haka ma tace kada a tadata a barta saita tashi dan kanta.” ai kuwa bata tashiba saida karfe uku da rabi na rana, ta shiga bayi tayi wanka, harda alwala.

Ta fito daure da tamul saita ga inna, ai saita fashe da kuka, a guje taje ta rungumeta, inna lallashi ta rinkayi, cike da kulawa, itama kanta tasan tayi missing din uwani sun dade a haka, kafin inna tace maza kiyi sallah nasan harda azahar bakiyi ba.”

a wannan yammacin uwani tana makale da inna, sunata hira abinsu, saidai uwani bata yadda ta gano abunda ke faruwa ba.

Da dare jafar ya shigo falon inna dan ya gaidata, suna cikin hira uwani ta shigo, ganin jafar saiya sa duk jikinta yayi sanyi, dalilin kallon dayake mata, bata kalleshi ba amma ta gaidashi, shidai idonsa na kan uwani, baima san da hakan ba saida inna tace “auta kanaji na kuwa?

Sannan hankalinsa ya dawo gunta, uwani tashi ki daukowa auta abinci.” ta mike tana tafiya a hankali.

Inna ta lura da hakan tun dazu, amma saita share dandai anriga da ance mata batada lafiya, kuma tasan halin uwan da raki, dan hakane bata tambayeta ba.

Uwani na barin wurin jafar yamike

yabi bayanta, “ina zuwa inna.”

bai jira amsarta ba ya fice. A kicin ya isheta, kai tsaye gunta ya nufa, da sauri ta nemi barin wurin, amma saiya riketa, “baby ya jikinki? na damu kwarai in ganki aisha.” ajiyar zuciya tayi, da sauki ta fada aciki, “ba inda yake miki ciwo? Ta girgiza kanta, babu, ta fada a takaice.

Toh ga maganinki, ya debo ruwa ya mika mata, yadda inna keyi mata, hakan tayi saida tasa shi acikin tuwo sannan ta hadiye, jafar kallonta dai yakeyi, ji yayi tace na shanye.”

ya lakaci hancinta, “mai raki.” ya karbi abincin ya fice.

Jafar ya koma kaduna cike da nishadi, dan ya samu abunda bai taba zato ba a rayuwarsa, har yanzu mamaki yakeyi, dama har yanzu akwai sauran virgin dama?

Koda yake dama baza a taba taruwa a zama daya ba.

Yana komawa ya samu an turashi can sudan a karkashin (UN) wato united nation don agaji a garin,

hakan ya kasance ne a dalilin hazaka da kuma nemar dama na tafiya. Sam baiso tafiyarba, amma ya zaiyi tunda yana neman cigaba a aikinsa? Dole haka ya wuce tunda ya rigaya da satin yabar gida.

Yau sati uku da kwana biyar rabon jafar da gida nigeria, sannan kuma a yau sati daya kenan da uwani ke fama da kanta, ta rasa abunda ke damunta, yau taji nan na mata ciwo, gobe taji wani wurin ne, ta rasa gane ainihin abunda ke damunta, ga kasala da sonyin barci duk a tare da ita, saidai bai hanata tayi duk abunda ta saba ba, dan bai kwantar da itaba, dan haka take gani yafi mata, idan inna ta gano akwai abunda yake damunta da tuni sun tafi asibiti, babu abunda taki jini kamar zuwa asibiti a rayuwarta.

Yau ma kamar kullum suna tareda lawisa a dakin uwani, sai lawisa ke cewa nikuwa in tambayeki mana, wai wane irin mai kike shafawa ne, naga kinyi farine sosai?

Harara ta wurga mata, ‘wane irin fari kuma, bayan kina gani a idonki, nashayin wanka a gabanki, man da dai nake shafawa shidin dai nake amfani dashi, ni wai yau hamza kwana biyu banyi waya dashiba.” inji uwani, insha Allahu yau saura kwana biyar ya dawo.”

don Allah da gaske?

Dana sani ban fada miki ba, kila so yake yayi suprising dinki.”

ai gara da kika fadamin,kinga sai in shirya kenan.

kinga sai in shirya kenan.”

ke uwani ban baki labari ba, na hadu da wani a bikin Nana dana fada miki zanje sati daya daya wuce.”

kai dan Allah ya yake? ya hadu?

Toh bawai ya wani hadu bane tunda yanada mata.”

kaji ki fa, dan mutum nada mata shine rashin haduwarsa?

Hum uwani kenan, bafa mata daya ba biyu gareshi, nikam bazan iyaba.” toh in Allah yayi shine mijinki fa ya zakiyi?

“kedai bari ‘yar uwa yanzu haka su inna (kakarta) sun san dashi, da yake family frinds dinmu ne….kai namij baida kunya, ko kinsan babban dansa warina ne?

Dan yana da da warinki shine me?

Gaskiya bazan iyaba uwani, nafa san matarsa ta farko, yadda take, je kiga yadda ta maida aunty murja ko mai aikin gidan albarka…”

kai don Allah, a’a nima naji tsoro amma ba nan take ba, zai iya yuwa ke kiyi nasara akanta.”

uhm-uhm uwani bazan iya ba.”

“ke dai baki sonsa ne ko?

Uwani ta tambaye ta.

Ajiyar zuciya tayi, “ba wai bazan iya son yusuf bane, a’a sai dai sam bana son ma in fara son nasa, saboda gaskiya matarsa nake tsoro, gashi iyayensa har sun fara kawo Baba zancen, nikuma har yanzu ma ban yadda nayi hira dashi ba. Uwani iyaye na nason wannan abun menene shawararki a gareni? Yau kwana biyu kenan da Baba yamin maganan yusuf, ya kuma nuna min yana so, itma Iya haka, itama tafi so, saboda mahaifiyar yusuf suna mutunci sosai da ita.” kwallah suka ciko a idonta, na rasa mafita uwani, yau kuma Baba yace in fada masa amsata, me zance uwani?

Itama uwanin cikin hawaye take, saboda itama tanada nata matsalar, ta riko hannun lawisa tace, ‘yar uwa nima a yau zan fada miki tawa matsalar, a ganina lokaci ne yayi da dole in fada miki, kin san yau wata na kusan takwas

da matsalar data adda beni, ta hanani sukuni, kullum take kadar dani, tare da hana min kwanciyar hankali….

Uwani taci gaba da cewa, na rasa ya zanyi da matsalar, kullum idanuna na zubar da hawaye.” lawisa ta zura mata idanu tana saurarenta, sam bata taba kawowa uwani tanada wani matsala ba.
Kin san Allah lawisa ina cikin damuwa matsananciya….” lawisa ta tsinkata, ki fadamin mana.” uwani tace, yau wata takwas kenan da auren uncle akaina! Lawisa ta zare idonta sosai, saidai bata ce komaiba, taci gaba da sauraren uwani, ajiyar zuciya tayi, sannan ta kwashe labari ta fada mata, “dan hakane inkin tuna na fada miki irin matar da yake aure, kuma inaso ki sani yana tare da ita, ai gara ke yusuf ba a gama dashi ba, ina nufin na rabashi da ‘yan uwansa, shifa uncle shekararsa hudu baizo gida ba, babu abunda yafi bani tsoro irin abunda akayiwa inna, ita kanta anyi mata asiri, da saura kadan ta haukace.
Lawisa inba dan Allah ya hanaba da sai dai a rasa su duka, sukarta fa taso ta haukata lawisa, toh nifa da aka kira kishiyar ta me zatayi min? Lawisa kam inbanda girgiza kai ba abunda takeyi, tama rasa abunda zata ce mata, sai ajiyar zuciya ta keyi, “babu abunda zatayi miki uwani, tunda Allah ya fito da zaluncinta a fili, na tabbata Allah bazai kyalesu ba, muci gaba da addu’a.
Hakane inji uwani, dan tun lokacin kam daga inna har su Baba ba wanda ya zauna, rokon Allah muka sa agaba, sannan kullum sai ankawo mana rubutu daga sokoto, daga inda ma yafi sokoto nisa ana kawowa, inna kuwa bata sha tare muke sha, nasan inna badan anfi karfinta ba da ba ayi hakan ba.
Sannan ni nasan inna mai kaunata ce, inna bata hadani da kowa ba!
Inda ace uncle na nan a yadda yake da da bazan damuba, amma irin wahalar data sha shike bata tsoro, da har take tausaya min duk da ba fadamin tayi ba, amma nasan abunda ke damunta kenan.
Lawisa nasan iyayen mu baza su taba zaluntar muba, sannan ki tuna Allah ya basu dama su zaba mana miji a auren fari, saboda haka nake baki shawara kije ki basu goyon baya, Allah yana ji kuma baya bacci, yasan biyayyace kika yiwa iyayenka, kuma shi zai saka mik, shine kuma zai kareki.
Ki sani a rayuwar mutum baki dayanta, tuni Allah ya riga daya shirya maka rayuwarka, abunda nake so dake shine kirika addu’a dan nikam nayi imani addu’a jagora ce a rayuwar dan Adam,
inada littafin addu’o’i da mukeyi da inna cikin dare, in mun tashi yin nafilfili, saboda hakane ma kije kiyi, insha Allahu zakiji komai yayi sauki. Sannan inaso mu rike junanmu amana, lawisa nasan na fiki zurfin ciki, toh amma bawai dan ban yarda dake bane, a’a kinsan hamza wankine, ni kuma shi nake so, dan haka nema nake neman hanyar da zanbi uncle ya sauwake min, sannan in fada muku abunda ke faruwa, dan inna ta bani tabbacin in Allah ya yarda zata san yadda zatayi ta raba auren tunda bana so, ita ma bata so.” haka dai abokan suka tashi cike da nazarin hirar da sukayi.
Ranar littini rana ce da uwani ta tashi da wani irin ciwon kai, ga zazzabi mai zafi data ke fama dashi, har karfe takwas na safe bata fito ba, inna ta leka dakin data ji tana ta zuba amai.
Nan da nan ta rame, saika ce wadda tayi sati ba lafiya, ga kuma wani irin fari datayi, hankalin inna ya tashi sosai, bata jira wani abu ba ta saka hijabi suka wuce asibiti, har a cikin mota ma ta rinka yunkurin amai, sai dai ba komai acikinta.
Suna isa asibiti inna ta wuce kai tsaye ofishin likita, da yake asibitin take zuwa an saba da ita, matar da ke cikin office din zata fito, ita kuma ta shiga, “doctor! Doctor!
Emergency ne, jikata tana mota aje a taimaka mata. Da saurin gaske likitar ta fito aka shiga da uwani dakin duba marasa lafiya.
Inna meke damunta?
Zazzabi ne tun shekaran jiya nake lura da yanayinta, nasan bata da lafiya, amma yarinyar nan tace, min ita lafiyarta lau, sam bata son zuwa asibiti, balle kuma in za a mata zancen allura.” da sauri aka danneta akayi mata allura, duk da bata da lafiya sai da aka danneta, sannan akasa mata ruwa.
Daki aka basu, doctor hadiza tace, idan ta tashi za a debi jininta da fitsarinta. Inna tace toh.
A lokacin hankalin inna ya kwanta, saida tasha ruwa biyu sannan ta samu kanta, ankuma debi jininta da fitsari an ce sai gobe za a kawo result, a wannan rana kadai da ciwon ya kwantar da ita harta zabge, tayi rama. Sai dai da sauki, dan har da dan abinci ta dan ci, duk da ba wani yawa ne dashi ba.
Washe gari kam da sauki sosai, dan tayi karin safe ba laif.
Wajajen goma da rabi doctor hadiza ta shigo, suna hada ido da uwani ta rika dariya, mai tsoro allura an tashi?
Inna tace haka kuwa take, tun fil azal tsoron allura, doctor hadiza ta samu wuri ta zauna suna gaisawa da inna. Bayan nan doctor tace, inna dama tanada aure ne?
Gaban uwani ya buga kamar zai fito, eh tanada aure kam, saidai bata tare da, mijin ma baya nan.” ajiyar zuciya tayi, toh sakamakon gwajin fitsari da akayi ya nuna tanada shigar ciki wata daya da ‘yan kwanaki.” inna ta zare ido, ita kuwa uwani kuka ta saki.+

Inna kuwa mamaki ne da tunani duk suka kamata a lokaci daya, ta dubi inda uwanin take, sannan tace ciki…ciki…toh ya akayi? Doctor Hadiza tace, inna aiba abun mamaki bane tunda tana da miji.”
da sauri inna tace, hakane, babu mamaki tunda akwai aure.”
toh ke mekike wa kuka bacin kiyi farin ciki? Doctor hadiza ta fada cike da zolaya, ko duk kukan farin ciki ne? Tunda kin samu sauki na sallameki, sai dai za a kawo magani da zaki rinka sha.” inna tayi godiya domin uwani kuka takeyi sosai, har a cikin mota bata daina ba, dole inna ta sauka daga fushinta ta fara lallashi dan sam bata son kukan uwanin.
Suna isa cikin falo uwani ta fara fadin inna kiyi hakuri, wallahi ba laifi na bane, uncle ne yayi min dole a ranar da zaku dawo daga umrah ki tambayi Baba kiji.”
inna ta rungumeta, “ai bance komaiba uwani, fushin da kika ga inayi dan baki fadamin ba, amma ai ba komai.” uwani najin ta fadi haka, sai tace, inna kin hakura?
Eh na hakura, kiyi shiru haka nan, kinga ba dadin jikinki kike jiba.
Saita sassauta kukan nata, “toh inna acire cikin mana, tunda kince raba auren zakiyi.” tunda ta fara maganar inna ta tsura mata ido, tana kallonta, aranta kuma mamaki ne ya kamata, lallai jikan data ke ta mafarkin samu shine za a zubar tun ba yau ba take so taga jinin jafaru, Allah bai kawo ba shine zata cire wanda ta samu yanzu?
Bazai yuwu ba. Saita tsinci kanta da cema uwani, “karki damu badai har yanzu baki sonsa ba? Da sauri tace ” eh inna bana sonsa.”
toh ki bari in Allah ya saukeki lafiya, sai yayi sakin.” nan da nan uwani ta saki fuskarta, tare da rungume inna tana godiya, tana nuna jin dadinta.
Inna kuwa aranta dadi ne ya kamata mara misaltuwa, batama san inda zata sa kanta ba, “oh Allah na gode maka, ya Allah ka sauketa lafiya, Amin.” ta kara tsurawa uwani ido, yarinta ke damun yarinyar nan. A dai-dai nan indo tayi sallama, “hum ‘yar shagwaba abun ne ya tashi ko? Tayi tambayar cikin zolaya.
Uwani ta mike zuwa daki, tare da buga kafarta a kasa, irin na shagwaba. Indo ta kalli inna jiki dai da sauki? Ajiyar zuciya tayi kafin tace, “hakane, da sauki, amma indo baki kyauta minba, ashe dan nan naki abunda ya aikata kenan, gashi har ciki ya tabbata…” guda indo ta saki, tana fadin Allah mun gode maka, ashe abun alheri ne ya faru? Kinsan Allah inna wannan auren Alheri ne, Allah ya sauketa lafiya.” da sauri inna ta amsa, Amin, amma to baki fadamin rashin lafiyar da uwanin takeyi ba kenan da muka dawo? Haba inna toh ba gashi abun ya nuna ba da kansa, gaskiya jafaru namijin duniya ne, Allah yasa albarka.”

***** ***** *******

jafaru kuwa dai har ya samu wata biyar cur a sudan, sannan suka fara shirin dawowa sai da ya samu sati a abuja, sannan ya shigo kaduna. Washe gari tunda safe ya kama hanyar kebbi, karfe sha daya saura ya isa kebbi, da sabuwar motarsa honda accourt V6 2008, baka ce, gashi tayi masa kyau sosai. Yana sanye da wandon kaki, sai ‘yar t. Shirt dinsa a jiki, fara sol. Ya dan rame, amma baiyi duhu ba.
Inna na zaune akan kafet din falonta, tana gyran caset din disc dinta, saita ji sallamar jafar, ya shigo cike da nishadi, itama cike da fara’a tace oyoyo auta saukar yaushe? Ya zauna daf da ita, yana cewa, “yau satinmu daya da kwanaki.”
aini ban zaci da wuri zaku dawo ba.” haka muma, Allah ne ya sauwake abun shiyasa muka dawo tunma watan daya shigene muka so dawowa, America ce ta rikemu, harta na so ta zabe wasu daga cikinmu muje muyi course a war sch. Na can, toh sai dai ni ban samuba, inna ya kwana biyu?
“lafiya lau auta, bari ingani me zan samo maka ne?
Ta tashi ta shiga kicin ta hado masa abinci, anyi sa’a kuwa indo ta gama.” sai da yaci yasha, a wannan karon ya tabbatar inna ta sauka sosai, dan ya lura ta fara sakin jik dashi.
Ita kuwa uwani yin jarabawa kawai takeyi, amma ba wani dadin jiknta take jiba, gashi yanzu ma suka fara neco, lawisa ke ce mata, “uwani dakin hakura da rubuta jarabawar nan, har sai kin sami sauki.”
a’a gaskiya bazan iyaba, saboda bana so sai wani shekara indawo, nafi so in na tafi na tafi kenan.
Toh Allah ya kara sauki.” daya ke sun fito bakin gate ne suna jira azo daukarsu, dayake uwani yanzu motarsu lawisa take bi, da yake mal. Mamman ya tafi ganin gida.
Jafaru ya koshi sosai yaushe rabonsa daya samu irin haka? Ya dawo inna ta kula dashi, har yama manta. Yadan kwanta suna dan hira, “auta inna ta kirashi.
Na’am ya fada tare da kallonta, watakan dan nace ka fita hanyar uwani shne kaki, har kaje kayi mata ciki akan dole ko? Gabansa yayi mummunan faduwa, dan yadda inna ta hade girar sama data kasa.
Sai dai inyi abunda zanyi, amma maganata banza ce agareka ko? Taci gaba da magana ranta duk abace. Da sauri ya dawo kusa da ita, Haba inna ya kamata ki hakura hakanan, wallahi ina son Aisha da zuciya daya, inna zan riketa amana.” banyarda ba jafaru, yaudaran mu kake y, ni kuma ban zan yarda ba, dan haka har yanzu ban hakura, inta haihu dole a raba aure nan kaji na fada maka? Tana gama fadan haka ta tashi ta wuce dakinta.

Haka ta tashi ta wuce dakin ta. Shikuwa duk hankalinsa ya tashi, ya zaiyi da ransa ne, wai me yayiwa inna da bata kaunarsa? Tuni idonsa sukayi jajir, kamar gauta. Ya mike ya fice.

Motarsa ya shiga kai tsaye makarantar su uwani ya nufa. Kowace ta tsurawa motar ido dan ta hadu, gashi wanda ke cikin motar ma ba abarshi abaya ba, sarai uwani ta ganshi kuma ta gane shine, toh amma ta kauda kanta gefe daya, suka ci gaba da hirarsu da lawisa, shima ya gane manufarta, saiya share ya bude motar, idonsa sanye da spider space, ina nufin irin madubin nan mai makalewa a idon mutum, yayi kyau sosai dan dama yana sanye da farar rigar nan da wandon kakinsa.

Duk wurin shi ake kallo, lawisa ta dubi uwani, ke wancan ba uncle bane kuwa? Uwani da tuni gabanta ke faduwa tace, haba dai, wane uncle kuma, shida baya gari.”

toh nidai gashi nan dan bazaki cemin ban san uncle ba….”

hamza ne ya katse musu maganarsu, “ku tashi mu tafi.” su duka suka kalleshi, tuni hankalinsu ya koma gun hamza dake yi musu magana, sannan mamaki cike a fuskarsu, “yaya yaushe ka shigo garin namune? Ya amsa idonsa akan uwani. Itama kallonsa take yi cike da kaunarsa a idonta, gashi shima yayi kyansa, duk da hankalinta baki daya baya gun hamza, yana gun uncle din nata, ta sani sarai komai na iya faruwa, amma tayi karfin hali suka tashi, suka shiga motar hamza.

Jafaru kuwa in ransa yayi dubu ya baci, dan ma ya manna glass a idon nasa, da ba haka ba da abun yayi muni. Tuni ya koma gun motarsa, ransa a bace yabi bayan motar hamza, saida yasan yanda yayi ya wuce hamza, yasha gabansa. Da sauri hamza ya ja burki ya tsaya, dama shima hamza ba a barshi abaya ba gun rugima, dan haka da sauri ya fita cikin motar cike da fushi, shima jafar da fushin ya fito, suka tsaya sunawa junansu kallon tsab! Har na kusan minti uku, sannan ne hamza yace mallam ya zakamin haka, ko kan titin na gidanku ne? Jafar yayi murmushin mugunta, sannan ya cire space din idonsa, idon nan nasa kamar garwashin wuta, “menene dalilinka na daukar min mata? Tambayar yazo masa a bazata, “mekake nufi, taya za ayi in dauko matarka?

Matata na cikin motar ka, bance mu tsaya muna exchange word ba, ita kawai nake so ta fito mu tafi.” ya juya ya kalli inda su lawisa suke yace “dama akwai matarsa a motar nan, ya tambaya yana kallon ‘yan matan guda biyu.

Lawisa da kyar ta iya magana, saida ya kara maimaitawa acikin tsawa, sannan tace, eh akwai.”

ban ganeba?

“yaya gaskiya ya fada uwani ce matar tasa.” hankalin hamza ya tashi sosai, ya kara matsawa kusa da kofar uwani, “hakane uwani wai wancan mijini ne? Tuni hawaye ya cika mata fuskarta, in banda tausayawa hamza da bakin cikin abunda jafar ya aikata shike damunta, bata iya cewa komaiba, sai shima jafar ya matso inda hamza yake yace, kaga kada in kara ganin matata a motarka dan in fada maka she is carring my baby, so ina so inja maka kunne, kar in sake koda wasa inga hakan ta kara faruwa.”

in hakan ta faru fa me zakayi? jafaru ya kara yi murmushi, na inya san yayi nasara akan abu, amma baice komaiba ya bude motar inda uwani ke zaune, ya jawo hannunta dole ta amince saboda tasan halinsa, inma taki yana iya daukanta, ya kuma dauki jakarta, har saida ya bude mata gaban motarsa ta shiga, ya zagayo ya bude tasa, sannan ya dubi hamza yace, da kuwa ka gane kurenka, idan har na kara ganin matata a motarka.” ya shiga ya wuce ya tayarwa hamza kura.

Jikin hamza yayi sanyi lamai, a haka ya daure ya shiga yabar wurin.

Cikin motar ba wanda ya kara cewa ci kanka har saida suka isa gida, da sauri uwani ta bude kofa ta fita. Ji tayi ya riko hannunta, “ina zaki? Zo nan saikin fadamin dalilin wulakanta ni.”

nan da nan ta kidime, tana fidda hawaye tare da kokarin kwace hannun nata daga rikon da yayi mata. Suna shiga daki ya cire mata hijabi din dake jikinta, yana yi mata kallon kurillah, “wancan dan iskan shine hamza ko? Yayi tambayar cike da bacin rai, bata taba ganinsa hakaba, duk irin fushinsa na yau yafi na kullum, ta marairace fuskarta kayi hakuri. Ya dubeta kada in sake ganinki da wannan mutumin.” da sauri ta amsa toh.

Ita dai so take ya saketa, dan rikon da yayi mata, ya koma ya kulle kofar da key, dan Allah nace kayi hakuri, bazan sake ba.

Ai na hakura, ya fada yana cire shirt dake jikinsa, ‘kijirani inyi wanka. Ya shiga bandaki, dole ta zauna kan kafet din falon, inka ganta kamar wadda aka sato, gashi batada ikon yin ihu inna taji, dan gabaki daya ya gyara dayan sashen dake cikin gidan, ya maida shi salfcontent, gashi ya shirya wurin sosai, ita dai ta zare ido sai kallo take yi, bata san lokacin da aka gyara sashen ba. Yayi mata kyau a ido gashi ya makala hoton mahaifinsa data inna a falon, kujerun falon su suka fi yi mata kyau.+

Da karfet ya shirya falon da kalar lemon green, sai aka dan jefa orange kala aciki, gaskiya falon ya kayatu kwarai ainun.

Shigowarsa falon ya katse mata tunani, “meye haka kin wani takurawa kanki? Ta daga ido ta dan dube shi, yana sanye da gajeren wando da singileti fara tas! Yazo ya riko hannunta, ‘haba baby ki saki jikinki mana, gidan mijinki fa kike.”

“ni zan shiga gun inna.

Wace inna kuma? Sai naji bugun zuciyar dan cikinki, sannan zaki bar wannan wurin.”

ta dan tsuke fuskarta, “wane irin da kuma? Don Allah ka bari in tafi, Allah yunwa nakeji.”

da gaske toh ki bari in dan duba ki mana, kafin ki tafi, ke ko irin tarba da akewa miji ke bakya yi, munfi wata biyu bama tare amma ko nuna min farin cikin zuwa na?

Ai kana da matar da zatayi maka wannan nikuma aro ce a gareka.” murmushi yayi sannan ya jawo ta dakin barcin shi, “zo kiga wani abu.” dakin barcin nasa ma yayi kyau, gado ne har gado aciki, komai an shirya shi yadda ya kamata, ji tayi ya sureta sai tsakiyar gadon, wani sabon kuka ta saki, sai dai shi baiko damuba, data gano abunda yake shirin yi, saita mike da sauri tayi sa’ar sauka daga kan gadon, a guje ta nufi kofar ta bude tayi falo, ya biyota yana fadin ‘yar tsoro, ba komai zanyi miki ba, ai nasan bakya jin dadi. Nidai ka bude min in fita.” kuka data keyi ba sassauci ya bashi tausayi, ya bude mata kofar ta fita, da sauri ta fice.

Tun daga wannan rana shiyake zuwa daukota daga makaranta, har ta gama rubuta jarabawarta, sannan laulayi ma ya mata sauki sosai, dan harta fara ciye-ciye.

Shikuma jafar tunda ta gama rubuta jarabawarta ya wuce kaduna.

Sam bai yadda sun zauna da inna ba, dan ko sun zauna ba hirar daya ke so take masa ba.

A kaduna kuwa, marliya sai addu’a

rayuwa kenan, inka ganta saika rantse da Allah ba ita bace, abun har yaso ya zama mata tabin hankali. Sau dayawa inka sameta saika ji tana ta surutai bartai, idan ma ka saurara bazaka gane abinda take fadi ba, Allah ya sauwake (ameen)

sabo da hakane randa jafar ya dawo, sun shigo tareda bashir, yana bashi labarin abun farin ciki daya sameshi, “kai aboki wallahi ako da yaushe inajin dadin shawararka, gashi a yau na tashi matata nada ciki.”

kai don Allah kace munyi kusan shan suna?

Eh! Mana sai dai tana wahala fa, tausayi take ban wallahi, dan ma tanada karfin hali ahaka take rubuta jarabawarta.

Da kyau, ashe harta gama kenan?

Alhamdulillahi, ta gama sai dai kai har yanzu inna taki bani hadin kai, kasan cewa tayi inta haihu, saina saki uwani? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ka bata hakuri kuwa jafar?

Uhm wane hakurine ban bada ba, tun abun na damuna harna sa ido, yanzu Allah kawai nasa agaba.

Daga bayansu sukaji an kyalkyale da dariya, da sauri suka juya suka ga ashe marliya ce, gashin kanta a tsaye kamar shuka, sannan kayan jikinta kamar wadda tai shekara batai wanka ba, fuskarta kuwa baza ce ita bace, dan yadda tai baiki.

Ta kyalkyacewa da dariya. Har tana dukawa, su kuwa ido suka sakar mata, “me naji ka fadi doctor? Matarka ciki ne da ita? Hummm lallai matarka ciki ne da ita? Saita kara kwashewa da dariya. Jafar ya juya mtss! Zo mu shiga gida bashir. Da gudu ta karasa ta sha gabansu, “ba inda zaku, saina fada muku gaskiya, nice…nice.” ta kara maimaitawa tare da zare idanunta, “wadda ba a gani a kyale, nice wadda nake yin abunda naso a rayuwata, idan ina son abu dole ne in sameshi, kota hali kaka. Kasan ya akayi na sameka? Ta fada tana kallon fuskar jafar, shikuwa tsura mata idonsa yayi, ina son sani marliya, dama abunda naketa jira kenan ko baki lura ba?

Toh yanzu zaka ji…”

bashir ya katseta toh ke mu isa falo mana kada…

Ta katseshi ba ruwanka gwani, bada kai nake magana ba.

“watch your mouth, marliya kada ki…” ta katse shi da cewa, “na bada kaina gun boka shanshani dan kawai in mallake ka jafar, saida yayi amfani dani sau ashirin da bakwai a yini daya, sannan na mallakeka jafar, ina sonka doctor, ban taba zama nayi tunani da namiji ba sai kai doctor, saboda hakane sonka ya makantani, nayi abunda ban taba yi arayuwata ba.” kuka ta saki mai ban tausayi. Duk jikinsu yayi sanyi, duk da bawai tausaya mata sukayi ba, illa takaici data basu, a take jafaru yace toh na sakeki saki uku! Babu aure a tsakanina dake har abada, na sakeki…” haba aboki ba ayi haka ba.

Haka kai ka gani, amma bazan iya zama da karuwa ba, na dauke shi tuntuni a matsayin kaddara, dan inba kaddara ba, da bazan dauki tsohuwar kilaki a matsayin matata ba. Yana gama fadin haka, ya kama hanyar falonsa, da sauri ta rike masa kafa, tana kuka doctor ina sonka! Kayi hakuri na gano kuskurena.” da karfi ya tureta, saika ce dabbar data gudiri mutum, nace na sakeki ko bakiji ba? Bana sonk ni! Sannan inkin manta in fada miki, in anyi saki uku babu aure tsakanin ma’aurata, kayan dake cikin gidan nan na baki, in kina so kisa mota tazo ta kwasan miki, zan baki daga yau zuwa karfe tara na safen washe gari, idan na dawo na sameki cikin wannan gidan, wallahi saina kasheki.”

About AIS

Check Also

KALLON KITSE CHAPTER 10

KALLON KITSE CHAPTER 10                     Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *